An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Izgili SARAUTA JAMILAH MUHD, AHMED (Mrs Bashir Salisu the Door) IZGILI JAMILA MUHAMMED HAKKIN MALLAKA Jamila mohd ahmed SHEKARAR BUGU 2014 GODIVA Ga Allah S.WA) ya bani ikon yin wannan rubutu, salati mara adadi ga shugaban halitta annabin mohmed (S.AW) GARGADI Ba'a yarda wani ko wata ya sauya wannan littafi ta wata siga ba, ko daukar wani abu a ciki ba tare da izinin mai littafin ba, a kiyayc Ban yi wannan littafi dan cin zarafin wani, ko wata ba, kagaggen labari nc, da na rubutu shi dan nishaɗantar da masu karatu, ba dan cinzan ko tuno asirin wani ba, dan haka IZGILI JAMILA MUHAMMED IZGILI C ikin mutukar nutsuwa take takunta wanda yawancin samari da mutane suke ganin yangance da ita amma kuma ba haka bane haka Allah yayota, ita bata sanin sanda take yin yangar haka tafiyarta take, dan ita a rayuwa bata iya sauri ba, komai nata cikin nutsuwa take yinsa gami da wata irin rausaya tamkar bishiya kuma natural ne daga Allah amma bayin kanta bane, dan ita bata sanin sanda take yi, sai dai ta ji kawayenta suna fadar wai ta ci ka yanga komai zata yi a yangance take yinsa duk sanda suka fadi haka sai dai ta yi dariya dan ta san idan zata kwana dubu tana gaya musu ita bata san yadda ake yin yangar ba bare ta yi, baza su yarda ba, dan haka take rabuwa da su, 5 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan ta san haka take ba wata yangar da take yi. Tun da ta taho ya kura mata ido kur ko kiftawa ba ya yi gaba daya hankalinsa baya kan abokin nasa da yake ta faman rattabo masa bayani ina shi kuwa hankalinsa ya yi gaba bai ma san me yake ba, gaba ɗaya yarinyar ta gama burgeshi. Nutsuwarta da shigarta sun burgeshi. Sanye take da dogon hijabi ruwan toka har kasa da duk alamu hijabin Islamiya ne dan tun ɗazu yake ganin 'yan mata masu kalar Hijabin su na wucewa sai dai ita har da nikabi a fuskarta kuma hijabinta har kasa ne saɓanin na wadanda ya ga ni, wata dai-dai gwiwa ne wasu ma dai dai cinya shi dai tun dazu daya fara ganinsu suna wucewa bai ga mai hijabi kamar nata ba saboda ita har wajen idan sahu yazo mata. IZGILI JAMILA MUHAMMED Ta wuce ta gefensu idanunsa kyam akanta suna yi mata rakiya. Alhaji Umar mai akwai da yakewa abokin nasa baya ni. Ya ji ya yi shiru ya dan kalli inda yake sai ya kula gaba daya hankalinsa da nutsuwarsa suna wani gurin can, basa kansa. Ya lura ya kurawa guri daya ido ya kalli inda yaga yana kalla bai ga komai ba sai kawai mutane da ya ga suna zirga zirgarsu yawancinsu duk 'yan Islamiya ne da suke ta tururuwarwar tafiya zuwa gidajen iyayen su. Ya dan taɓa kafaɗarsa gami da kiran sunansa. Alhaji Mansir dan kimanin shekaru saba'in da biyar, ya yi firgigit ya juyo gare shi tamkar wanda ya ta shi daga barci ya ce, “Am! Alhaji Umar me kake cewa ne?" 7 IZGILI JAMILA MUHAMMED Alhaji Umar ya ce, "Ina hankalinka ya tafi ne?" Alhaji Mansir ya ce, "Na dan tafi wani tunani." Alhaji Umar ya ci gaba da yi masa baya ni ya ce, “Mun yi dai dashi Nan da sati hudu zai turo mana da cikwan kudin dan wallahi sai da nai masa jan idanu, in shi yana takamar dan zamani ne to ni nashekaran jiya ne, dan na ga jiya naga yau, kuma sai dana jaddda masa in har lokacin yayi na ji babu labari to wallahi kotu zan maka shege dan baka ga yadda ya dinga bani hakuri ba da ya ga na je masa ba sauki yana ta makyarkyata da ya ji zancan Kotu yana bada hakuri nan na taho na barshi. ". Alhaji Mansir ya ce, "To shi ke nan ni zan tafi yadda mu kai da Alha ji Auwal game da aikin titunan nan zan ma waya.' " IZGILI JAMILA MUHAMMED Alhaji Umar mai Akwai ya ce, "To babu damuwa," Su kai Musabaha. Alha ji Mansir ya shiga dankararriyar motarsa ya tafi. Zaune take atsakar gidansu tana tankaɗan dawar tuwan dare Innarsu Kuwa tana daga can gefe tana kaɗa miyar Kuka, kuma suna ɗan taɓa hira mahaifinsu ne Malam Usuman ya yi Sallama gaba ɗaya suka amsa masa ya shigo hannunsa rike da dan autan Innarsu ɗaya Hannun kuwa bakar leda ce yake rike da ita Inna Lariya ta saki Kadin miyar da take yi ta shimfida masa wata sabuwar tabarma da take jingine gefe guda tana masa sannu da zuwa Hadiya da sauri ta karɓi ledar da take hannunsa ita ma ta nai masa sannu da zuwan Inna ta dauko kofin silbar dake ajiye a gefe guda 9 IZGILI JAMILA MUHAMMED wanda aka ci ka shi da sassanyar ruwan Tulunta ta a jiyewa maigidan tana karai masa sannu. Ya sha ruwan sosai sanyinsa ya ratsashi sannan yayi hamdala ya dire kofin shima ya nai mata sannu da gida. Aliyu dan Autan Inna yana daga gefe sai murmushi yake faman dukawa gaba daya ji yake tamkar an sakashi a gidan Aljanna saboda dadi ya san tunda yaga Abbansu da leda yasan yau da cin kayan dadi, shi yasa ji yake tamkar zai sume saboda murna, shi ma zai nunawa su Abdul Abokinsa kayan dadin da Abbansa ya siyo musu ko sa dainai masa gorin babbansa baya siyo musu tsarabar kasuwa kullum, Abdul sai ya yi masa dariya saboda shi Abdul din babansu ko da yaushe ya dawo daga kasuwa sai ya siyo musu kayan dadi su lemo, ayaba, . 10 IZGILI . JAMILA MUHAMMED abarba, Kwai, dafaffe, Biskit, youghort, wata rana har da gasheshen nama ko Kaza kuma ko babansu bai dawo da wuri ba to da sassafe sai Abdul ya ajiye ya nuna masa dan haka shi ma yau tunda Abbansu ya siyo musu tsarabar kasuwa to shi ma ba zai ci ba sai ya ajiye da safe ya nunawa Abdul ya dai nai masa dariya yana cewa babansu baya yo musu tsaraba idan zai dawo daga kasuwa, kalubalenku iyayan yara gaskiya da yawa iyayen yara abinda muke bama kyautawa yadda zamu dinga bawa yaranmu abu suna fita da shi suna nunawa yaran makota ko kuma yaran abokan zaman mu idan gidan haya ne ta yadda zaki ga an bawa yaro abu ya fita da shi cikin yaran gidansu yana ci a irin haka ana samun matsala babba, saboda wani yaran zai ‘yan musu wani kuwa sai dai ya ɗagawa sauran 11 IZGILI JAMILA MUHAMMED yaran hankali suna gani yana ci ba zai ba su ba, haka za ki ga yara suna rusa kuka duk su dagawa iyayen su mata hankali dole sai an basu irin abinda wane yake ci kun san yaro da gasa wata uwarma zaka ga ita ke tura yaranta waje cikin yara ya ci abin sai ka ga ta dauki abu ta ba shi sai ta maza je ka gurinsu wane ku yi wasa ko kuma fita tsakar gida gurin su wane ka ci mana, to gaskiya irin haka babu dadi ke dan asan kuna cin abu sai kin tura yaro dan a gani alhalin yana dagawa yaran mutane hankali. Akwai matan da suke cewa yaransu kada ka cinye duka mana ka rage da safe ka nu̟nawą su wane, da dai ire-iren haka, gaskiya mata mu daina irin wannan idan ke kuna da halin cin abu bai ka mata ki dinga turo yaranki suna dagawa wanda 12 i IZGILI JAMILA MUHAMMED kika san basu da halin wannan abin dan Allah mata mu daina Allah ka iya mana. Inna Lariya ta juyo tana kallon Malam din fuskarta fal da farin ciki ta ce, "Malam yau dai da alamar dawa Tai nama.? Tun da na ganka da leda.' " Shi ma murmushin ne akan fuskarsa ya ce, "Yau kam Alhamdulillah babu abinda zamu ce sai godiya." Ta ce, "Gaskiya kuwa, ba ka ga auta ba ma baki yaki rufuwa yarasa inda zai sa ransa saboda murna sai wata dariya yake ɓangalawa gaba daya su kai dariya har da Hadiya wadda take kaɗe zaninta ta matsar da garin tana cewa. "Abbu Kalli irin zaman ma da yai ." har da tankwashe kaafu.' Suka kuma yin dariya. Malam Usman ya ce, “Bari dai in bude tsarabar nan in raba kowa ya dauka 13 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan naga dattijo na ya kagara kowa ya ci ko ba haka ba." Ya ce, "Hakanne Abbu su ka kuma yin dariya." " Malam Usman ya kalli Hadiya ya ce, "Zo ki dauka ki wanke. Ta ce, "To" Cikin nutsuwarta ta dauki ledar daya tureta gefe ta dauko wata 'yar madaidaiciyar roba ta juye abin dake ciki mangwaro nene lafiyayyo lafiyayyo masu kyau manya manya. Ta wanke su tas sannan ta kawowa Innarsu dan ta san ita zata raba dai dai nan Bintu tai sallama ta shigo mallam ya kalleta ya juyo da kallonsa ga Innar da take raban Mangwaron ya ce. "Wai shin Lariya bansa dokar fitar yaran nan waje ba, In dai fitar ta wuce cikin wuce wannan lokacin. 14 IZGILI JAMILA MUHAMMED Cikin tsananin ladabin Innar har da dan dukawarta daga kan kujera ‘yar tsugunne da take kai ta ce, "Ka fada.?" Ya ce, "To to raina ni a kafara yi da zance bana san abu ayi sanin kanki ne babu abinda natsana irin a dinga barin yara mata suna kaiwa magriba a waje, har nake kafa miki misali da cewar ko aike ne in har magriba ta sawo jiki to ki dinga hakura har na dawo ni sai in je, shi ma dattijo sai da nai masa faɗa, da har na same shi a waje yana wasa ke kuma babu ruwanki da kisa ayi kiransa ya dawo gida tun da yamma ta yi ko.?" Inna Lariya cikin ladabi gami da kwantar da harshe ta ce, “Ka yi hakuri Malam dan Allah Allah ya huci zuciyarka wallahi dole ce ta sa na aiketa kuma bama ta da lafiya ba, gidan babansu na aiketa dan dazu Iya Saude ta aiko min 15 IZGILI JAMILA MUHAMMED idan nadaka garafuni in bata to nai duban duniyar nan ban gan shiba sai bayan ɗan aiken ya tafi sannan na ganshi dan sai da na caje ɗakina sosai to shi ne da suka ta so Islamiya na ce tai maza ta dawo amma dan Allah ka yi hakuri insha Allahu haka ba zata kuma faruwa ba, ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Allah yasa." Ta yi saurin cewa "Amin" Tai wa Abbu Sannu da zuwa sannan ta mika ledar da Iya ta aikota ta kawowa Innarta su Innar ta bude taga curin fura ne da kuma nono mai kyau ta ɗaure ta kalli Malam ta ce, "Yau shi kenan ba za a ci irin tuwan nawa ba dan ga shi nan iya tayi maka haji da Umra." Malam Usman ya saki dariya ya ce, "Lallai kuwa yau tuwanki ko kallo bai ishe ni ba dan haka yi maza ki dama min 16 " * IZGILI JAMILA MUHAMMED kafin in dawo daga masallaci dan ga kira nan a na yi." Yana gama maganar ya karɓi butar da Hadiya ta miko masa ya fara alwala su ma gaba daya suka mike dan bada farali Aliyu auta ne yai zaune yaki ta shi. Inna ta ce, "Ya dai dattijo.?' Ya ce, "Inna mangwaro." Nan tai dariya ta ce, "Kayi sallar mana tukunna ko kaga nace su dauka kai kuma na hanaka.” " Ya mike da sauri damin yabi Abbansu masallaci dan in dai bai je ba zai iya cewa kada a bashi mangwaron tun da bai bi jam'i ba. **** Yau ma kamar ganin da yai mata kwanakin baya sai dai yau tana rungume da alkur'ani ta zo ta wuce ta gabansa cikin nutsuwar nan tata ya rakata da idanu 17 IZGILI JAMILA MUHAMMED tana dan yin yanga baya ya ji samarin da suke kofar gidan da yake makoftaka da gidan Alhaji Umar mai akwai daya saurayin ya san shi dangi tane ɗaya ne bai sani ba, ɗaya saurayin ya ce, "Gata nan fa mutuniyar taka." Kanti ya juya baya. Bashi ya saki dariya ya ce, "Wallahi Allah ya suturu bakui in ji kishiyar mai dorina ina zan iya." Kanti ya juya baya "Ai ba zan iya koyaushe dan cinikin da nayi akasuwa su kare akantin nan mutane ba. Nura ya ce, "Yanzu ina jin ta daina tunda yai mata illa." 29 Bashi ya ce, "Ta daina me? Kallo kafarta ka gani mana malam tamkar ta turawa saboda tsahar mankanti fuskarce dai dai ta ga ji da man shi yasa ta lalace take rufeta yarinya sai shegen jiji da kai 18 IZGILI JAMILA MUHAMMED ke da fuska ta riga tai dameji har kece me wani ɗagawa mutane kai." Su ka sake dariya suka tafa Alhaji Mansir ya ce, "To me ye ma'anar Kanti. Ya juya baya sun santa ne ko̟ ku ma dai ita ma bata da nutsuwa tamkar su, dan kallo daya za kai musu ka san su din kwararrun 'yan duniya ne, haka zuciyar Alhaji mansir ta dinga masa tambayoyi barkatai wanda ba shi da amsar su, dai dai nan Alhaji Umar mai Akwai ya fito hannunsa dauke da wasu takardu ya karaso inda Alhaji mansir yake tsaye jikin motarsa, ya mika masa hannu gami da cewa “Ga_su_nan ka duba su, jibi jibin nan nake son tafiya Kaduna akan aikin makarantun nan. " Ya ce, "Insha Allahu zan yi kokarin ganin na gama su jibin su kai sallama ya shiga motarsa ya tafi. 19 IZGILI JAMILA MUHAMMED BAYAN SATI UKU Hadiya ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta kai dubanta ga Jana data ke ta faman baza powder Hadiya ta ce, "Dan Allah Jana kibar saka powder nan haka kin ga yamma ta yi kada Abbu ya dawo ya tarar bamu dawo ba gobe ba zai sake barina fita ba." Jana ta dan dauke idonta daga kallon Mirrow ta ce, "Dan Allah kada ki takuramin ki barni in yi kwalliyata cikin nutsuwa dan na sanki da shegiyar hayyata in ke bakya abu sai ki hana masu yi suyi." Hadiya ta ce, "Yanzu duk wannan baza eye shadow da wannan jam bakin da kika gabza ba ki yi minti sha biyar kina yi ba, ai ban miki magana ba, to sanin ki da nayi naga ko kin gama fentefenten naki ba gama kwalliyar bace dan sai ki kara 20 IZGILI JAMILA MUHAMMED PROSTY wani minti sha biyar din kawai kina kallon madubi kina kara baza powder ja na ta ajiye sosan da take shafa powder ta kara gyara zaman ɗaurin ɗankwalinta ta ce, "To da zaki ishe ni da Ina ta shafa powder ca nake ke ma kin shafa ko ke naki ba sai ni zaki hurawa wuta.' " baki gaAnty Meena ta shigo tana fadin ita ai shafawar masu hankali ta yi ba irin taki ba da sai a kusan karar da ita ashafawa daya, ke in dai zakiyi kwalliya sai ki shafa powder wajen sau goma. " Jana ta cuno baki tana kunkuni ita kuwa Hadiya dariya take mota ta ɗauki Hijabinta ta saka gami da ɗaura nikaf dinta ta ce, "To fi'ili madi ai sai mu tafi ko?' Jana ta kalleta wani takaicinta ya kamata tace dan Allah dubeta haka kawai kisa kanki a Uku ki dinga yawo cikin 21 IZGILI JAMILA MUHAMMED wannen zirmemen Hijah ki wani rufe fuska ke ba matar Liman ba zafi duk ya damc ki, dan Allah dubeki duba kayan dake jikin ki Hadiya tai saurin daga Nikaf dinta tana kallon Jana ta ce "Mc kayan nawa su ka yi.?" Jana ta ce, "Riga da siket ne ajikinki sun yi miki bala'in kyau sun yi cif-cif a jikinki tamkar ajikinki a ka dinka su saboda kyan da kayan su kai miki amma zaki kassara rayuwarki ki rufewa mutane, to ba a haka bane zaka samu mai son ka wanda zai ganka ya ga ka yi masa amma ke kullum zurum-zurum cikin hijab har da su nikaf shi yasa har yanzu baki da saurayi ko daya, to yaushe mutum zai ce yana sanki alhalin bai ga abinda yai masa a jikinki ba bare ya ce, yana son ki. Ta cije gefen danyatsanta ta ce, "Wayyo Allah garin dadina nesa in ji 22 IZGILI JAMILA MUHAMMED Angulu da ta lefa masai ai wallahi da ni Allah ya bawa farin ki gashinki, dirinki idanunki muryarki, wallahi ba karamin yaki zan yi ba don sai na saka samari runtsċ ido sai na daga musu ganye da duk wankan da nai sai na sumar da samari warwas Allah yai miki kira ba ta Allah Sarki ba ya yi miki halitta ba wadda miji zai ce shiga daka na yi ba, Amma kina cutar da masu sanki ni na tabbatar ko sau daya kika cire Hijab din nan da wannan Nikaf din na tabbatar sai kin saka maza karo." Anty Meena ta kaiwa bakin Jana duka ta ce, "To taki yin yadda kike so ke ganin fito da tsiraici waje shine wayewa to wallahi ba wayewa bace, sai ci baya wanne namijin ne kin gama tallar Nono da kugu awaje zai kwashe ki sai kace mara mafadi to bara in baki misali ke ce 23 IZGILI JAMILA MUHAMMED kika ga a titi ana sai da cincin ga wani abude kura da iska duk sun koɗashi ga kuma wani a cikin glass a rufe sai mai cincin zai baki nawajen nan wanda saboda kura da ta badeshi har ya fara canja kamannin shi, "Ai na san babu ta yanda za'ayi ki yarda ya baki wannanAlhalin kina ganin yarda yake sai dai ki ce na rufen nan kike so, saboda yafi mutunci to haka ma maza suke kallan duk wata mace mai bayyanar da jikinta mazan titi suna gani haka suke kallanta tamkar wannan buɗaddan cincin din da dattin duniya ya gama badeshi.. Hattara dai mata masu irin wannan hali masu gani cinyewarke nan to wallahi ci baya ne ba cinyewa bane bar ganin a nayi miki layi a gidan ku dan kina irin wannan shigar to ina mai tabbatar miki duk cikin masu zuwą gun naki babu 24 IZGILI JAMILA MUHAMMED wanda yake zuwa da zummar aure sai dai da niyar wata bukata ta shi, kuma da bukatarsa tabiya ba zai kara ko kallon inda kike ba to talla ki kai shi kuma ya taya kika sallama to kin ga kuwa taya zai kai ki gidansa harki zama uwar ‘ya'yansa, ke ma kin san (Impossible) Jana ta dauki ɗan yalolon mayafinta daya dace da atamfar jikinta da akaiwa dinkin riga da siket sun kamata dan-dam ta dauko post dinta ita ma kalar kayanta. Ta ce, "Sai mu tafi Sayyada." Anty Meena ta ce, “Ko baki faɗa ba mutane zasu fada su ce ita din Sayyada ce ke ko kunyar jerowa da ita baki ji ba, ita ta yi shigarta ta kirki mutum duk na cinsa ba zai ga ko ina nata ba, amma ke dubeki dan Allah wallahi Jana ki yiwa kanki faɗa, ki yi koyi da Hadiya ki dinga komai na ki da nutsuwa." 25 e. 2 IZGILI JAMILA MUHAMMED Jana ta figi ledar da Anty Meena ta shigo musu da ita, turaren wuta ne da Humra da take siyar da su ta basu turaren wutar ta kaiwa Iya mahaifiyarsu da kuma Inna mahaifiyar Hadiya Humrar ta suce ta basu sannan ta mikawa Hadiya dari biyu ta ce su hau adaidaita sahu. Hadiya ta ce, "Wallahi ki barshi Anty muna da kudin Mota." Anty Menna ta dan zare mata ido ta ce, "Karбi mana ai na san kuna da kudin motar na baku.” Hadiya kasancewarta mai da'a kuma ba a ai musu tarbiyar jayayya dana gaba, yasa ta karɓa tai mata godiya ta rakota har soro. A kokafar suka ga Jana ta cuge tana ta faman kumbure-kumbure. Anty Meena ta ce, "Ku gaishesu." Hadiya ta ce, "Za su ji." 26 IZGILI JAMILA MUHAMMED Ta gangara inda Jana take suka jera zuwa titi Anty Meena yayar Jana ce uwa daya uba daya ita cc a biyu a gidansu tana aure a Yalwa bata taɓa haihuwa ba. Jana suna tsaye abakin titin,suna jiran adai-daita sahu kasancewar duk wanda ya taho zaka same shi da mutane saboda yamma ta yi tun daga nesa ya hangota ya ganeta ita ce zuciyarshi ta gaya masa ya tsura musu ido yau ma dai irin shigar da ya ganta da ita ce sai dai wannan ba hijabin Islamiyar bane shi wannan kalarsa maron ne kalar flat din takalminta ne kuma sanye take da Nikaf dinta babu abinda kake gani sai kafarta kasancewar Hijabin dogo ne sosai. Idonsa ya kai ga wadda take kusa da ita ya kalleta yaga irin shigar da ta yi gaskiya ya yaba da nutsuwarta da hankalinta yana. kallo sai tsaida abin hawa 27 IZGILI JAMILA MUHAMMED suke amma ba su samu ba ya wuce ta gabansu yana ci gaba da fadin kamun kanta to shi dai duk ganin da yake yi mata cikin nutsuwa yake ganinta bai ma taɓa ganin fuskarta bato me yasa ya ji wannan samarin suna fada mata wani suna wai kanti ya juya baya mai hakan ke nufi? Wata zuciyar ta ce, masa kawai dan sunga ba kalarsu bace shi yasa suke jin haushinta har suke Igaya mata wani suna haka ya dinga tunani harya isa gida. ** . Hadiya tana sharar tsakar gida ta ji sallamar babbar kawarta tata Jana. Jana kawar Hadiya ce tun suna yara sun yi mutukar shakuwa ta yadda babu wadda za tai kwana biyu batare da ta nemi 'yar uwarta ba duk da babu ta yanda za ai su hadu batare da sun kafsa ba anan dai na yi musu da maganar Malam bahaushe da 28 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya ce, sai hali yazo daya ake abota to waɗannan aminan junan su sam ba haka bane dan ko wace da inda ta dosa inda hakan halaiyace inda Jana ta kasance mai san gayu da kece raini tana da rawar kai mutuka ga saurin fushi amma bata da wuyar saukowa. Tana da kirki bata kuma da kyashi ko hassada ita in dai dan uwanta ya samu to ji take tamkar ita ta samu sannan bata da rufi duk abinda ya dameta kai tsaye zata gayawa babbar aminiyarta bban abinda yasa suke samun matsala da kawartata shine ita dai Jana Allah ya yo ta mai san saka kananun dinkuna ce kuma idan tasa ba zata sami mayafi mai yalwa ta rufe jikinta ba, sai dai irin na 'yammatan zamani ita tana jin bakin ciki ganin yadda kullum Hadiya take faman jibgawa jikinta dogayan hijab har da su 29 IZGILI JAMILA MUHAMMED nikaf, sai kace a zamanin jahiliya ga dai kyau dan asali kyau zalla amma bashi da amfani tunda kullum ana rufcwa masu so basu gani ba bare su yi sha'awa yayinda Hadiya tata kasance kasance. marasan magana sannan bata san raini ko wulakancin sam bata da saurin fushi amma kuma bata da wuyar saukowa tana da shagaɓa mutuka da sangarta in dai a gaban Abbunta ne da Innarta tana da tausayi ita abu kankani sai ya sata kuka shi yasa Jana take ce mata mai arhar hawaye, ita abu kaɗan sai ya sata kuka. Ta dago da sauri tana dariya Jana ta kalleta ta dauke kanta ta karasa gefen tabarman dake shinfide suna gaisawa da Inna Hadiya tana sharar tana dariya dan ta san lefinta ta san kuma shi yasa Jana ta zo tana karasa sharar ta wanke hannuwanta 30 IZGILI JAMILA MUHAMMED. ta karaso kusa da ita tana fadin "Kawata ya dai.?" Tana dauke kanta Hadiya ta guntse dariyar da ta cika mata ciki ta ce, "To ta so mu shiga ciki sai ingaya miki uzurina da abinda yasa ban aiko miki da wuri ba." Jana ta bita ɗakinsu ta zauna kan 'yar yalolowar katifar Hadiya wadda saboda sidewa ta dawo tamkar tabarma, ta kalleta ta ce, "Uhm Ina jinki faɗa min dalilin da yasa da kika san ba zaki je ba me yasa baki aiko min da wuri ba.?" Hadiya ta zauna kusa da ita ta ce, "Ai ya kawata ni ma ba haka na so ba na san Bilkisu Ibrahim ba zata ji dadi ba, babu daya daga cikin mu daya je." Jana ta harareta ta ce, "Waya ja? Idan bake ba da kika san ba za ki je waliman nan ba tunda wuri ba sai ki aikomin ba in sami abokin tafiya kawai 31 IZGILI JAMILA MUHAMMED sai dana shirya ina ta jiranki sannan zaki wani ce min Inna bata nan, shi yasa ni ma Faina ya ɓaci kawai nace to nima na fasa zuwa. " Hadiya ta ce, "Haba sister me yasa kika fasa ai Amiru ɗazu ya gayamin dana ce ya je ya gaya miki ki bani kayan walimar ya ce ke ma ba ki je ba. Jana tana faɗin ‘yar rainin hankali bayan sai da kika bari duk 'yan tafiyar sụn tafi sannan kika wani aikomin ai na ji haushinki sai kuma daga baya na ji daɗima da bamu je ba. Hadiya ta ce, "Saboda me? Yanda kika kwallafa ranki akan walimar nan. " Jana ta tura mata wata leda da ta ganta da ita ta ce, "Bisket da chacolate din nan, na Bintu ne da Aliyu shi kuma túraren naki ne. 32 IZGILI JAMILA MUHAMMED Sannan ta ɗauki post din ta ta ajiye "ta a kusa da ita ta bude ta fito da wata dalleliyar waya mai shegen kyau daga gani kuma zatai dan karan tsada sabida haduwarta, Nokia ce gaskiya ta hadu. Hadiya ta ce, "Gaskiya mutuniyata wannan wayar ta hadu karshe. Kuma daga wa?" Jana tana daga kwance sai ta lumshe idanta tana shafa dan gashinta, da gaba daya tattalin arzikinta yake karewa akansa tai wani wal da idanunta ta ce. "Daga wa kuwa? In ba daga Hubbina ba." Hadiya ta ce, "Gaskiya ya burgeki da waya, ana ji da wannan Salim din." Jana ta ce, "Wallahi kuwa ai duk cikin samarina babu wanda nake so kamarsa, wallahi Hadiya in har narasa shi ban san yadda zanyi ba na san sonsa IZGILI JAMILA MUHAMMED mahadin rayuwata ne kin ga in bashi ba babu rayuwa." Nan da nan Idanu Jana suka kawo kwalla ta ci gaba "Har tsoro zuciyata take bani ganin irin son da take masa ina sansa har ban san yadda zan kwatanta miki ba, jiya da ya zo tamkar zai yi kuka yake gaya min babanshi ya zaɓa mata 'yar abokin babansa wallahi tun jiyan har yanzu bana cikin nutsuwa hankalina a tashe yake dan idan narasa shi komai yana iya faruwa." ." masa Sai hawaye ya wanke mata fuska tamkar an bude famfo. Hadiya ta ji waii matsanancin tausayinta ya kamata, ita dai bata san so ba dan bata taɓa jinsa ba amma zama da Jana sarkin soyayya yasa ta fara fahintar so, abu ne mai dadi amma idan an dace kuma mai mutukar hadari idan anyi IZGILI JAMILA MUHAMMED rashin dace ta koma fahintar rabaka da abin son ka ba karamin tashin hankali bane. Ta matsa a hankali ta dafa kafadar Jana da take ta sharɓar kuka ji take tamkar ta tayata, ita ma kwallar ta tarar mata ta dai daure dan kada ta kara dagawa Janar hankali ta ce. "Dan Allah Jana ki dinga daukan lamarin da sauki kuka ko tunani ba zasu yi miki magani ba ki dage da addu'a a yanzu ita ce magani in dai Salim mijin ki ne to fa labudda sai kin aure shi, idan kuma ba mijinki bane Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi kin ji dan Allah Jana ki sassautawa kanki dan kada ki saka kanki a wata matsala. Jana ta ce, "Na ji in Allah ya yarda zan dage da addu'a har mu ga abinda Allah zai yi." t IZGILI JAMILA MUHAMMED Hadiya ta yi dariya ta cc, “Ko ke fa my sister tayi dariya. Ya yi nisa cikin tunaninsa har bai ji abinda uwar gida sarautar matan take fadi ba, ta shafa fuskarsa ta ce, “Wai ni Alhaji me ke damunka kwana biyu, duk ka canjamin kana yawan zama shiru kana dogon tunanin har baka jin me ake cewa dan Allah idan wani abunene yake damunka ka tai maka ka gayamin dan wallahi idan baka gaya min ba ni ma zaka sani a wani hali.” Alhaji Mansir Kwangila ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Babu abinda yake damuna Zalifa kawai dai ina wani ɗan nazari ne amma karki saka komai a ranki." Ta kalle shi kawai sai kuma ta mike da sauri zata bar falon, ya yi saurin IZGILI JAMILA MUHAMMED janyota da karfi ta fado jikinsa please Zalifa baki yarda da abinda nace ba ko, to ki kwantarmin da hankalinki ba wani abin tashin hankali bane amma ba zan gaya miki shi yanzu ba sai dai na miki alkawari da zarar na gama bincike zaki ji komai." Ta yi sauri sauke ajiyar zuciya ta ce, "To Allah ya mu ji alheri.' " Ya ce "Alherin ma za ku ji” Ta ce, "Shi muke fatan ji a duk inda muke" Ya ce, "To yanzu hankalinki sai ya kwanta da har za ai min fushi dan kawai ki sani a uku.” " Ta saki wata irin dariya mai kara mata kyau ta ce, "To Ai ban ji dalilin sauyawartaka ba a 'yan kwanan kin nan ka ga kuwa hankalin nawa bai kwanta ba zai dai kwanta. 37 IZGILI JAMILA MUHAMMED Ya ce, "Tun da na ce zan gaya miki to zan gaya miki da zarar lokaci ya yi ta cc, "Allah ya nuna mana lokacin nan. " Ya ce, "Amin" Ta ce, "To ta so mu je dinning dan abinci ya dade da kammaluwa kai kawai yake jira." Ya mika mata hannunsa wai ta tashe shi ta ce, “Kaima kasan ba zan iya ba in ba so kake ai haihuwar guzuma ba ɗa kwance uwa kwance yadda kake ɗinnan kace in dɗaga ka, kai ma kasan ba zan iya ba." Ya tashi yana dariya ya ce, "Laifinwa bake kike dirkamin abincin da zan karuba na zata santi kike tun da banji kina complai din ina sakar miki nauyi ba, ya karashe maganar yana daga mata gira. Ta yi dariya tana faɗin Alhaji Kafa girma." 38 IZGILI WHY JAMILA MUHAMMED Ya ce, To bara in gama cin abinci sai ki yi bayanin girman da na yi." Suka yi dariya. **** Yau kimanin sati uku ke nan yana yin zuwa na musamman domin ya san shin ita din wacece so yake ya wani abu game da ita yana so ya san gidansu, amma shiru kake ji babu ita babu labarinta jiya akan idansa aka shiga makarantartasu kuma yana nan aka ta shi ya dinga baza ido ko zai ganta amma komai irin hijabinta bai gani ba, gaba daya kansa ya dau chaji to me yasa bata zuwa makarantar a yan kwanakin nan ya rasa wanda zai tanbaya labarinta to yau din ma haka ya gama zagayanshi daga farkon titi na koki har karshensa, amma duka baba dantela dva va shiga damuwa. IZGILI JAMILA MUHAMMED To ko dai alhaji umar zai samu ne akan maganar gaskiya yana san sanin wani abu daya danganceta dai-dai nan ya ji wayarsa tana ringin ya dauka Alhaji Umar ne ya dauka bayan sun gaisa ya ce, "Kamar kasan yanzu nake tunanin kiranka sai kuma ga shi ka ri gani alhaji Umar mai akwai ya yi dariya ya ce, "Daman na san zaka neme ni dan ka ji ya muka yi da manajan ko?" Alhaji Mansir kwangila ya ce, "Ni ba dan wannan ba, muhimmiyar maganar ce dani kana gida ne? Zan zo 99 Alhaji Umar yai dariya ya ce, "Maganarce ta ruɗaka har ka manta ina Katsina. " Alhaji Mansir ya dafa kai gaba daya ya manta abokinnasa baya nan tun jiya yana ta dukko ɗakin kara. Ya ce, “Ka ga IZGILI JAMILA MUHAMMED naranta gaba daya yanzu dai sai ka dawo ke nan. " Alhaji Umar ya ce, "To ka gayamin mana ko bata waya ba ce maganar 53 . Alhaji mansir ya ce, "Bata waya bace sai dai kawai idan Allah ya dawo da kai lafiya, nan suka shiga maganar kwangilar da shi Alhaji Umar din yaje nemar musu a gurin gwammanan Katsi nan kuma da dukkan alamu zasu samu. ****** Kwance yake cikin bahon wanka kamshin turarukan wankan suna ratsa shi yana busa tabarsa cikin gwanancewa sai da yaji ruwan ya huce sannan ya zubar dashi ya sake sabo, ya daɗe yana cuɗa jikinsa tamkar mai shirin canja fata sannan ya dauko wani dan guntun tawul ya daura a kugunsa ya dau wani kuma yana goge kanshi hade da jikinsa. 41 IZGILI JAMILA MUHAMMED Ya tsaya gaban tangamemen madubin dake manne jikin bango toilet din wanda kake ganin tun daga kafafunka har kanka gefensa kuwa wata 'yar durowace wadda samanta yake sheke da turarukan wanka sabulan wanka dana hannu, dana kai, dana kafa, tamkar kantin sai dasu, su man baki turarukan baki gasu nan dai burjik ya rataya ɗan karamin tawul din gurin da suke jajjere tamkar akantin sai dasu yake gaban dirowar ya ɗauko wani mooth freshner ya kuskure bakinsa sai da yai amfani da wajen kala biyar kuma kowacce da kamfaninta da kuma kamaninta. Daga farshe kuma ya dauko wani dogon turare ya ware bakinsa ya dinga fesawa ya direshi ya dauko mansa na ka shi na dore ya shafa sannan ya ɗauko man tafin hann shi ma na kamfanin dore 42 IZGILI JAMILA MUHAMMED dinne ya shafa, ya ɗauko turaren gaɓa gaɓa duk set din dore dinne dan shi yana aiki da duk kayan kamfanin tun yana germany har kyauta kamfanin sukai masa, saboda aiki da kayansu da yake yi. Ya dauki kum ya yiwa sumarsa sannan ya ɗauko kalolin mangashi ya shafewa ya shafawa wannan kyakkyawar sumar ta shi irin ta asalin larabawa baka siɗik da ita mai taushi gami da santsi ya ɗauki wani turare wanda kuɗin turaren kawai jarin wani talakanne. Yana fesawa kan nan da nan ya kara kaɗannaɗewa tamkar yanda sloon suke cirewa mata waɗan nan rabubin haka gashin ya kanannade. Yana fitowa ya ji enter comm din gidan tana kara tabbacin yana da bako ya kalli agogon dake girke a saman durowar dake gefen lafiyayyan kuma kayataccen 43 IZGILI JAMILA MUHAMMED bed dinshi wanda ya ji wata irin lumtsumemiyar katifar leda da kuma wani datsetstsen bed sheet karfe biyar da minti ashirin to ko waye yake shirin shiga rayuwarsa ya dan saki gajeran tsaki gami da cewa koma waye sai na gama abinda nake yi ya karasa gurin wata irin wardrop wadda ba zaka taɓa cewa wardrop bace saboda tana like a a jikin bango kuma. kalarta ruwan madara ce sai ta saje da fentin dakin saboda shi ma ruwan madara ne, kuma a like take tamkar bangon yana budeta yai tsaye gaban jerin kayannashi wanda kowanne dá gurinsa gurin kananun kaya daban haka suit gasu nan ararrataye babu kalar da babu ya rike kugunsa da hanayansa biyu yana bin kayan da kallo dan ya rasa wanda zai saka, can dai ya dauko wata fitled din T shirt fara ce tas ya saka ta kamashi ya 44 L IZGILI JAMILA MUHAMMED fito masa kirarsa ta cikakken namiji a gaban rigar an subutu hand some guy, rubutun an yi shi da wata kala mai sheke tamkar ruwan kwai. Ya sa ka stripes brown ya dɗauko turaran jiki ya saka ya yi kala biyar ya dire ya dauko wayoyinsa tare da jaridar weekly trust ya fito kayatccen falon nashi har yanzu ma buga kofar bai gaji ba, bai kuma yi zuciya yatafi ba. Ya ajiye jaridar tare da wayoyin nashi kan center table ya nufi farij dinsa ya dauko coke ya ɓinci ni bakinsa ya daga sai da ya shanye sannan ya jefar da gwangwani. Sanyi ya ratsashi ya karasa bakin kofar ya bude kofar. Katum Farida Saraki ta baiyana fuskarta cike da takaicin irin wulakancin da wannan mutumin yake mata, ta kai minti hamsin a wurin nan kuma ta san yana jin 45 IZGILI JAMILA MUHAMMED knoking din da tun dazu take ta ſaman yi amma saboda dan karan wulakancinsa sai yanzu sannan zai buɗde mata, duk takaicinsa da haushinsa ya isheta fadi take a zuciyarta in dai ya bude sai ta núna masa damuwarta da ɓacin ranta na irin wulakancin da yai y mata amma abin mamakin shi ne yana budewa tana yin ido budu da shi sai ta ji wani irin farin ciki ya cika mata zuciya tai tsalle ta dane shi shi ma riketan ya yi yana kiss din bakinta ai take tamkar zata sume saboda santsen harshinsa da wani irin fitinannan kamshi da yake fita daga bakin mai saka mutum a wani yanayin. Sun kai kimanin minti a shirin atsaye abakin kofar suna ta ya mutsa junansu suna cakudawa, can da abin ya girmama sai ya maida kofar ya ya ɗan danna mata key ya rungumeta ya cika 46. IZGILI JAMILA MUHAMMED hannunsa da albarkatun kirjinta su kai bedroom dinsa. Inna Lariya ta shigo dakin da kofin silba a hannunta ta dire shi gami da zama ta ce, "Hadiya ki tashi ga fura malam ya shigo miki da ita." Hadiya da take kodundune akan yalolowar katifarta tai magana daga kudundunen da take tace, "Inna na koshi." Inna ta ce, "Ai kuwa baki isa ba kin taɓa jin inda aka warke daga cuta alhalin ba ashan magani, ba kuma a cin abinci saboda tsabar gardama da kafiya irin naki to tunda nadama furar sai kin shata, idan` ma zaki samawa kanki lafiya ki ta shi to ki tashi dan wallahi sai kin sha, kin kuma sha sha mu gani tunda ga shi an sami kudi an sayo miki." 47 IZGILI JAMILA MUHAMMED Hadiya ta ture abin rufarta ta tashi zaune ji take kanta tamkar zai tsage saboda ciwon da yake yi mata ga kuma matsanancin zazzabi. Ta dauki furar tunda ta ji Inna ta rantse ta san dole ne ta shata ta fara sha tana yamutse fuska duk santa da kaunarta da furar ji ta yi tamkar maɗaci take sha tana yin kurɓa ɗaya biyu ta dire kofin ji take tamkar zata yi amai, Inna ta saka mata manyan idanuwanta ai babu ariziki ta dauki kofin dan ta san ma'anar kallon. Haka ta dinga daurewa tana sha sai da ta sha rabi sannan ta kalli Innar dan taga a wana yanayi take, da taga bata nuna komai ba sai ta a jiye ta ɓare magungunan ta bata ta karɓa ta ce, “Dake wata ce, ai da sai ki bari sai maganin da furar da kika sha sun fada miki sannan ki kwanta." IZGILI JAMILA MUHAMMED Hadiya ta hadiye maganin nan da kyar ta dauki mayafinta ta dukunkune a cikinsa amma bata kwanta ba, dai-dai nan su ka ji sallama Jana Inna ta dauki kofin ta fita tana amsa mata sallama. Jana suka gaisa da Inna, jana tana tambayar mai jiki Inna ta ce, "Da sauki tana ciki ki karasa." meJana ta shiga ɗakin ta zauna ta kalli Hadiya cikin tausayawa ta ce, "Sannu Hadiya." Hadiya ta ce "Yauwa." Jana ta ce, "Ya jikin naki.?" Ta ce, "Da sauki. Jana ta ce, "Iya ta ce, a karayi miki sannu.' Hadiya ta ce, "Ina amsawa." Jana ta ce, "Habib ma yana duba ki ya ce, ya na miki sannu.' Ta ce, "Ina amsawa." 49 " IZGILI JAMILA MUHAMMED Haka suka dinga yin hirar yan makaranta Islamiya da boko da yake duk ajinsu daya tana gaya mata wadanda suka ce ai mata sannu, saboda basu sami damar zuwa dubata ba, dan gaskiya Hadiya tana da farin jinin mutane da wuya ta zauna a guri ba a so ta ba, ba dan komai za a so ta, dan kyanta dan can din din ita kyakkyawa ce ta ajin farko kuma tana da san mutane tana da mutukar fara'a in dai ta sanka in bata sanka bane tana da wuyar lamari. Alhaji Mansir ya dauki lemon Edotic din da mai dakinsa Hajiya Zalifa ta tsiyaya mai ya kurɓa gami da daukan remote control ya rage sautin tangamemiyar T. b plasman dake like jikin bango girmanta ya shahara tamkar mutanan jiki zasu fito ya kalli gefensa IZGILI JAMILA MUHAMMED inda Hajiya Zalifa take dan kishingiɗe kan tuntum tana cin Tufa suna kuma ‘yar hira. Ta zuba kwalliya tamkar mai zuwa fadar shugaban kasa, daman gata mai kyau duk mptsin da tai wani fitinan nan kamshi ne yake tashi, Alhaji Mansir ya ci gaba da kallanta. Gaskiya yana san matarsa yana kaunarta ko dan gayunta sam bata tsufa tamkar yanzu aka kawo masa ita gidansa shi yasa yai ta ganin bakin danginsa da suke damunsa da zancan aure yanzu sun daina, ya riga yasan Zalifa ta mallake zuciyarsa babu sauran gurin da zai saka wata ‘ya mace, ya san ba zai iya hada daki da wata macen ba dan yadda yake santa yake san farin cikinta ba zai so damuwarta ba ita kuma a duk duniya babu abinda ta tsana sama da kishiya bata santa kwata-kwata 51 IZGILI JAMILA MUHAMMED . tana kishi da abinda take so tana bashi kulawa sosai tamkar wani jariri haka take tattalinsa tun a farkon auransu har zuwa yanzu. Yau kimanin shekara talatin da takwas ke nàn da yin aurensu amma bata taɓa ɓata masa rai ba, tana sani ba, sai dai a ajizanci irin na dan adam, tana sonsa tana kyautata masa, tana san 'yan uwansa, tana kyautata musu, tana sansu. so na gaskiya, Allah mai hikima ne da ya ce, muddin mutum yai sa'ar mace ta gari lallai rabin imaninsa ya cika, sai ya kyautata aiyukansa, dan ya samu rabauta, ranar gobe kiyama, gaskiya mace ta gari jin dadin namijin duniya, mace tagari ita ce, silar wanzar da zaman lafiya gaba daya ya shagala da kallonta yana fasalto abubuwan alkhairinta gaskiya duk iya zamansa da ita bai taɓa ganin wani abun 52 IZGILI JAMILA MUHAMMED assha kona Allah wadai data taɓa yiwa wani, wani abun narashin kyautatawa ko zamanin da 'yan uwansa da mahaifiyarsa suka saka mata karan tsana. Can hajiya Zaliya ta kula da hankalin Alhajin baya kanta dan sai magana take yi masa amma hankalinsa yana wani wajen bai ji ta ba ta dago dan taga mai ya ke yi sai taga ya zuba mata ido ashe tun dazu ita yake kallo ta mike zaune daga kishingiɗar da ta yi ta kira sunansa, yai saurin sauke ajiyar zuciya ya ce, "Na'am' " Ta matso kusa da shi har sunajin numfashin juna, ta saisaita muryarta tana wasa da zagayayyen gashin bakinsa ta ce, "Alhajina wai ni lafiya? Duk fa 'yan kwanakin nan haka kake kafiya yawan shiru da tunani. " 53 IZGILL JAMILA MUHAMMED Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Akan dai zancan nan da mu ka yi dake ne kwanaki, to wallahi yanzu abin ya dame ni sosai so nake in zaɓa masa kawai sai dai ince masa rana kaza dan nagaji da wannan shashancin banzar da yake yi. Dai dai nan wayarsa dake gefensa ta ɗauki ringin yana duba wayar yaga my son ya ce, “Kin ganshi ma ya danna ok ya fara maganar sosai da suka dan daɗe sannan ya mikawa mominsa tana yi masa fadan yaki zuwa ko ya makale Abuja. Ya ce, "Aiyuka ne Momi su kai min yawa amma insha Allahu zan zo karshen wannan satin. Ta ce, "Ka dai faɗa ne. 99 Sun dade suna magana sannan ta kashe wayar ta dubi Alhajin ta ce, "Dan Allah Alhaji ka sassautawa ranka ka daina yawan tunanin nan kar wani ciwo 54 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya kamaka kabi komai a hankali dan Allah. Ya yi dariya ya ce, "To ranki ya dade za'a yi yanda kike so gaba daya suka yi dariya." NIGHT CLUB Club din cike yake makil da ‘yan kosassun Abuja ‘ya'yan manya Club din yai mutukar tsaruwa tamkar a turai, zaka yi mamaki ainun da man akwai club kamar wannan a Nigeria saboda yadda ake zuba lalata tamkar a garin nasara, asarar duniya babu abinda ketashi sai wani tattausan Music mai ratsa kwanya kowa sai harkokinsa yake kwanciyar hankali wasu gurin shaye shayensu su kafi kauri yayinda wasu gurin rawa suka karkata dai-dai nan Hisham Mansir kwangila ya baiyana gaba ɗaya samarin gurin suka ruɗe da ihu cikin 55 IZGILI JAMILA MUHAMMED wadanda suke kusa suka dinga rungumarsa ya yinda wadanda suke nesa suke yi masa fito suna fadin Hey hand some. Cikin takunsa na kasaita gami da shariya yake ɗaga musu yatsansa biyu bai saurari ko ina ba sai can wata kujera ta musamman yana zama Joh mai aiki gurin ya russuna cikin girmamawa ya ce, "Yallaai barka da zuwa.' Cikin kallon nasa na ka'ida ya kalle shi ya ce, Cikin wata daɗɗan muryarsa "Guiness masu sanyi zaka kawo." " Cikin sauri ya ce, "An gama oga. Ya kishingida ya daga daradaran kyawawan idanunsa yana bin club din da kallo ya ajiye wayoyinsa akan table ya fito da kwalin sigarinshi daga aljihun ya 56 IZGILI JAMILA MUHAMMED mannata abaki ya dauko lighter ya kunna yana bulbular da hayakin. Nan take ya haɗa dan karamin gajimare cikin kwarewa yake fesar da hayakin tun shigowarsa. Hankalin 'yan matan gurin ya yo kansa sai shawagi suke ta gabansa ko da Allah zaisa ya kyasa, kowacce so take taga ta burgeshi tana so ta samu shiga a ce yau ya yi mu'amala da ita koda sau daya ne, dan ta san kudin da zai shaka mata ba kaɗan bane, wasu kuwa so suke ya kula su ko bai basu komai ba, ai abun burgewarsu ne kyakkyawa na bugawa a media kamarsa ya kulasu, to su abin alfaharinsu ne musliki dan wulakancin tabar hannunsa ta fisu daraja, a gurinsa, dan shi ko da zai mutu saboda bukatar mace in ba kin isaba kin kai kin kawo wajen haɗuwa gami da aji ba, to ko kallanki ba zai yi ba, 57 IZGILL JAMILA MUHAMMED balle har ya hada jikinsa da na ki dan shi ko cikin mata ba kowace kwashi kwaraf yake kulawa ba, sai ya tabbatar kina da abin kallon sannan zai kalla shi yasa wasu mazan abokansa suke ce masa ba kai kake kallonsu ba, kai ake kallo. Ya lumshi idansa yana jin wani yanayi mai dadi can idanunsa suka kai filin, rawar nan idansa ya hasko masa wata yarinya sai juyi take mai ban sha’awa ya kura mata ido yana kallanta, sanye take cikin wite yar bingilar riga wadda gaba daya cillyoyinia, awaje suke rigar kuwa bata da hannu gaban rigar anyi mata gidan bireziya mamanta rabi duk a waje, suke tana sanye da wasu dogayen, takalma wanda suka dace dashigart kanta yasha wata mici micin kalaba gashin kanti, fara ce, tas, kunnuwanta sanye da dogayen yari gaba daya ta gama 58 IZGILI JAMILA MUHAMMED tsuma shi ta yanda take sarrafa hips dinta tana takawa cikin aji dai-ɗai nan Joh ya dire masa kwalaban sassanyar agabansa da ya jerosu akaǹ\ wani dan madaidaicin faranti, da kuma wasu kananan kofuna na karau, ya saka opener ya buɗe masa ya zuba masa gami da dan rusunawa ya ce, "Oga ga shi nan." Hisham ya dauko kofin batare da ya dauke idanuwansa a gurinba ya ci gaba da tultulawa tumbinsa ruwan barasar yana wani kasa-kasa da marayun idanuwansa yana kare mata kallo, tamkar ance mata juyo sai ta hango mai tsada sunan da yawancin 'yan matan suke faɗa masa ya wani dalalo mata waɗannan fitinannun idanuwannan nasa. Sai ta ji wani irin matsanancin farin ciki ya kamata ta san ma'anar kallon cak ta tsaya da juyin da " 59 IZGILI JAMILA MUHAMMED take yi kuma ta fito daga filin cikin taku mai jan hankali ta baro gurin rawar. Ta kara so gurinsa tana zuwa taja kujera dake gefensa ta zauna ta ce, cikin harshen turanci ta ce, “Barka da dare hand some cikin kallonsa na isgilanci ya dage gira yana dallareta da wani shi'umin kallo cikin muryar kasaita ya ce, “Ke ma haka." Ta dauki daya kofin ta zuba itama ta fara kwararawa 'yan hanjinta gaskiya gaskiya kyakkyawa ce duk da dai baba bahaushiya bace yare ce, ya ce, "Me sunanki.?" Ta danyi dariya ta ce, kudurat ya ce, "Amma yau kika fara zuwa nan dan ban sanki ba.' biyu." Ta ce, "Wannan shi ne zuwa nan na Ya ce, "Kina rakiya.?" IZGILI OFREADGES JAMILA MUHAMMED fara." Ta ce, "Kabana yi, ai akanka sai na 27 Ya ce, "OK" ya ci gaba da dadɗaar abarsa sai da ya shanye kwalabe uku ita kuma kwalaba tasha ya yafito Joh ya taho da sauri ya dantso kudi ya bashi ya ce, "Duk wanda yasha ga kudinsa nan idan kuma da ciko sai mun badu." 99 Joh ya dinga godiya tamkar zai ari bakin Hisham. Ya juya ga Kudurat da giyar ta fara bugarwa ya ware hannun nasa ya ce, "Come on my baby." Ckin wani irin hali slow ta karasa tana kicin kicin sabule 'yar guntuwar rigarta na wasu surutai irin na wadda giya ta fara aiki, yai saurin rungumeta gami da rike mata hannu, ya rada mata a kunne ba anan zaki cire ba sai mun je gida, kin ji baby ta Infe inse yo kwashe wayoyinsa yai hanyar barin club din IZGILI JAMILA MUHAMMED samari suka dinga cewa Good night handsome guy, ya kuma daga musu yatsansa biyu ya shiga rantsatstsiyar motarsa ya bar club din. ****** Hadiya ce ke kokarin saka safarta sauri take yi ta shirya kada uwar haiyatar ta zo ta haiyaceta. Sanye take da kayan makarantar ‘yammata ta saka kayan sun karɓeta komai ta saka sai sun karɓeta ta nannade himilin gashinta cikin wani tabkeken ribon sai ta yi ɗaurin mai tuntu sai kace mai acuci maza. Inna taɗaga labulen hannunta dauke da dankaramin kofi mai dauke da kunun tsamiya sai tururuwa yake, yasha lemon tsami ta mika mata ta ce, "Maza ki kurɓe Wannan ko aa tsaitsaya nene ke da arayuwarki baki san cin abinci da wuri IZGILI JAMILA MUHAMMED wai ku 'yan boko ko? To ko su ma 'yan - bokon ma wasu ne masu ka idoji wasu " kuwa sak suke." ' Hadiya ta karɓi kunun tana ta kukkurɓa. Jana ce, ta kwaɗo sallama Inna ta amsa ta shigo ita ma sanye take da kayan makarantar dan hijabin nan ɓigil iya kugu. Hadiya ta ce, "To uwar haiyata to ai kya jira ni in gama karyawa tu kunna.' " Jana ta samu gurin zama tana gaida Inna Inna ta ce, "Ya mutan gidan?" Jana ta ce, "Lafiya kalau." Inna ta fita jimawa kaɗan ta dawo hannunta dauke da wani kofi ta mika Jana. Jana ta amsa ta ce, “daman kuwa wallahi ban karya ba dan yau iya dumame kawai ta yi bata dama koko ba saboda jiya ba wanda ya ci tuwan shiyasa 63 IZGILI JAMILA MUHAMMED yau ta ce, baza ta dama kokon ba duk wanda baya cin tuwon ya barshi cikinsa. Jana ta shanye kunun tas gaskiya Inna Lariya ta iya girki gata da masifar tsafta 'ya'yanta ma agurinta suka dauko tsaftar ta dan Hadiya tasha karbar kyaututtuka ba daya ba ba biyu ba, na dalibar da tafi kowa ladabi da tsafta. Hadiya ta fita da kofunan ta ce, "Wai ni dan Allah Jana mai yasa bakya jin magana ne.?" Jana ta dallaro mata wata shegiyar harara ta ce, "Rashin jin maganar me na yi? Uwar iya yi. " A Hadiya ta kai kofin can gefen tsakar gidansu Inda Innar take yin girki ta dawo - ta sako hijabinta. Shi ma babbane da kadan ake hango kafarta sannan ta saka nikaf dinta, suka yiwa Inna Sallama tayi musu fatan dawowa lafiya suna fitowa 64 IZGILI JAMILA MUHAMMED Jana ta ce, “Uwar fi'ili fadi ina jinki ki gayan abin da na yi, na rasa jin maganar da na yi?' Ta cikin nikaf dinta take magana ta ce, "Ta yanda naga kinsha wannan make up din tamkar mai shirin zuwa party." Jana ta dallara mata harara ta ce, "Au! Ke ki na zatan wannan horan da suke na yiwa mutum bulala da cewar ka goge kwalliyar da farin hijibinka zai razana ni ne, har in daina kwalliya to in ma da kina tunanin haka to ki daina dan wallahi in dai ba adaina powder a duniya ba, to har tsofana sai kin ganni da kwalliya." Hadiya ta saki dariya ta ce, "NI ban taɓa ganin sahibul kwalliya ba kamar ki, ke ciwo indai ba wanda za a kwantar a tayar ba to bafa zai hanaki yin kwalliya ba." 65 = IZGILI JAMILA MUHAMMED Jana ta ce, "Ita ce cikar mace, ba ki zauna a kasa banbance fuskar namijin a kasa gane taki **** Wayarsa dake ajive kan yar durowar gefen gadance take a Taman burari bai sanya akai ya manta bai kashe ta ba, duk karar ta dame shi can ya dan dago ya dauka ya katse, ya maida kansa suka ci gaba da sheɗanar da suke yi, shi da ‘yammatansa. Ya yi nisa cikin abinda yake yi na sheke ayarsu kwatsam ya sake jin kiran ya shigo cikin magagi irin na wanda ya fita daga cikin duniyar mu ya suri wayarsa zai kashe can idanunsa ya hango masa tamkar daddy na ya gani da sauri ya ture Farida saraki ya mike ya yo falo yana amsa wayar. 66 IZGILI JAMILA MUHAMMED Alhaji Mansir kwangila ya ce; "Ka bude min kofa gani a bakin kofa." Cikin matsananciyar kidima ya ce, "Daddy kana bakin kofa fa kace? Yaushe ka shigo garin.?" Ya ce, "Yau ko in ce ma yanzu, idan kuma kana mamaki ne to ka bude mana. " Ai da sauri Hisham ya cillar da wayarsa yai bedroom dinsa da gudu Farida Saraki da Kudurat zaune 'yam matansa da yake ji dasu dan duk gaba dayansu ba baya ba, suna iyawa dashi. Suna kwance akan gado haihuwar uwarsu da sauri ya daka musu tsawa ya ce, “Maza ku barmin gidana ga Daddy na nan ya zo." Cikin sauri ya zurma jallabiyar da yake sallah da ita ya bude dirowar gadon ya dauko kudi kowacce ya bata ya ce, 67 IZGILI JAMILA MUHAMMED “Sai na neme ku kada wadda tai gigin zuwa idan ba na kirata ba, yana gama fadar haka ya ce, Ku fito suka fito sai ya bude kofar. Kudirat ta saki dariya ta ce, "Handsome kalle kafa babu pant ana ganinka a haka zaka je gurin Daddy." Cikin sauri ya kalli jikinsa ai kuwa ana ganin nasa kasan cewar rigar ruwan madara ce kuma tana da yauki mannewa mutum take da sauri ya fada dakin ya sako gajeran wando ya fito dai-dai nan ya sake jin karar wayar ya san mai kiran batare da ya dauki wayar ba ya bude kofar yana washe baki daddy ya ce, "Ai ni da badan maigadinka ya ce, kana nan ba kuma naga duk motocinka suna nan da cewa zan yi baka gidan ko kuma ba ka yi murnar gani na ba my son?" Hisham ya ce, "Na yi murna mana daddy.' 68 IZGILI JAMILA MUHAMMED Daidai nan suka shigo cikin falon sosai Daddy ya kallu Kudurat da suke zaune a falon ya mai da kanshi ga Hisham din da yake tsaye da alamun tambaya a fuskarsa, Hisman ya ce, "Wadannan abokan aikinane wani aiki ne ya kawosu yanzu. Suka gaida daddy ya amsa musu fuska babu walwala su kai waje Hisman ya buɗe firij ya kawowa Daddy Ruwa da lemo yana kuma tambayar Mominsa. Daddy ya ce, "Tana lafiya.” Daddy ya gyara zama ya ce, “Wai ni shin Hisham sai yaushe za kai aure ne, ko yaushe akai maka magana daga kace wannan sai kace wan can kana ta faman zille-zille. Hisham ya ce, “Haba Daddy ni fa ba girma na yi ba, just 33 year ne fa ka ga da saura na. وو 69 IZGILI JAMILA MUHAMMED Daddy ya ce, "Da sauranka fa tunda ba kai sittin ba,mana tunda shi ne dai-dai lokacin ka ko?" Hisham ya ɓata fuska tabbacin baya son fadan nan ya ce, "Please Daddy ka bar maganar nan daga zuwanka ko hutawa ba ka yi ba, me ake da aure, aure ai takura ne. " Daddy ya saki baki yana kallan dan nasa tun ba yau ba ya daɗe yanayin dana sanin tura ɗan nashi kasar mai jan kunne karatu, tun yana tatsitsinsa gaskiya ya cuci kansa wannan Abu yana damunsa ya rasa yadda zai yi bai isa yai masa faɗa akan duk abinda yake yi ba sai ya ce, shi dai ana san a takura masa, duk ya dauko dabi'unsu na lalata. Daddy da idanuwansa suka fara canja launi saboda ɓacin rai ya ce, "To wallahi bari in gaya maka in dai ba kai 70 IZGILI JAMILA MUHAMMED wani abu kan maganar aure ba daga nan zuwa karshen watan nan tuni zan yi wani abu a kai, kuma sai na baka mamaki.' " Yana gama fadar hakan ya mike dan yın Alwala dan ya ji masallacin kusa da gidan suna kiran sallah. Alhaji Mansir kwangila shi da Alhaji Umar mai akwai suna zaune a falon gidan Alhaji Umar din bayan gaishe-gaishe irin na abokanai, Alhaji mansir ya ce, "Gaskiya ina cikin damuwa.?' Alhaji Umar ya ce, "Ikon Allah Alhaji me ke damunka Alhaji Mansir ya furzar da huci mai zafi ya ce, "Akan yaran wajena Hisham ne, wallahi ina cikin ɓacin ran kaishi turai karatu banda karatu har da shedana da duk wata lalata ta turawa duk ya kwaso, to shi yasa nake IZGILI JAMILA MUHAMMED san in yi masa aure, tun lokacin dana kama shi da giya a firji dinsa nake cikin damuwa shi yasa nake san yi masa aure kasan aure abu ne mai girma kuma yana gyara mutum to gaba daya daya na rasa yarinyar da zan zaɓa masa mai hankalin wadda zata juri halinsa ta dinga tuna masa idan taga yana abunda bai dace ba, to na yi tunanin na yi tunanin na kasa zaɓar masa to kawai sai sai nana tattara nabarwa Allah lamarinsa ya zaɓa masa mafi alkhairi na kuma dukufa da addu'a sosai. Wani ikon Allah banyi sati da fara tsaiwar daran nan ba na fara mafarkin wata yarinya, to amma banga fuskarta ba, tana sanye da dogon hijabi har kasa ta juya bayanta da yaro a hannunta to tun daga lokacin ya zama duk lokacin da na kwanta sai na yi mafarki, to kwanaki da 72 IZGILI JAMILA MUHAMMED na zo nan muna magana sai naga wata yarinya zata wuce Islamiyar." Alhaji Umar ya ce, Zawuya ke nan.?" Alhaji Mansir ya ce, “Ita, ya ci gaba da cewa "Wato ranar da na ganta sai naga nutsuwarta da hankalinta nasan ta fito daga gidan tarbiya shi ne nake san in tambayeka ko ka san 'yar inace tana saka nikaf." Alhaji Umar ya dan yi nazari ya ce, "Gaskiya ban san ta ba, sai dai akwai wani yarona kama sanshi dan Audu, to zan sa shi ya binciko mana in da take da kuma 'yar gidan waye." " Alhaji Mansir ya ce, "To shi ke nan suka ci gaba da hirarsu akan harkokinsu da kuma hirar duniya. Cikin wulakanci ya kalli mai gidan ya daka masa wata gigitacciyar tsawa ya IZGILI JAMILA MUHAMMED ce; "Saboda tsabar baka san aikinka ba ko kuma dan ka koshi zaka nuna halin naku na talakawa, daga kunci abinci sai ku ɓollo da salo na rashin mutunci. Baba Audu babu abinda yake in banda makyarkyata yana durkushe yana bawa ubangidan nashi hakuri tamkar zugashi yake, sai faman tujara yake yi masa da tozarci, kala-kala, tsohon zai baka tausayi mutuka saboda a kalla ba a kasara ba zai yi jika da shi, sai wulakanci yake yi masa, irin na zafin naman nan. Hisham ya ci gaba da yarfa ruwan rashin mutunci yace, "Saboda tsabar ka isa tun jiya abaka dakardu ka bani dan. tsabar raini kaki bani har sai da mutumin yayo min waya saboda ya ji shiru, sam baka da niyar bani, saboda ka fara farfaɗowa daga cutar talauci, data kama ka, yanzu kana jin aljihunka da nauyi shi 74 IZGILI JAMILA MUHAMMED ne kake ganin dai-dai kake da kowa tsiyar talaka ke nan, a ɗaukeshi ranga ranga a taimake shi daya fara koshi kai zai farayiwa rashin mutunci, shi yasa ni da talaka babu wani tausayi, ban ɗauki talaka a bakin komai ba, face, kaskantaccen bawa, wanda zai min bauta in biya shi, a duniya babu wata rana da talaka yake da ita, bashi kuma da wani amfani daya wuce mai kudi ya bautar dashi domin shi bawansa ne.' " Shi dai Baba Audu in ban da ban hakuri babu abinda yake yi sai da ya ji ya ɗan tsagaita sannan ya fara bayaninsa ya ce, "Wallahi yallaɓai sanda mutumin nan ya kawo takardun nan ka fita kuma baka sake dawowa ba zuwa kuma sanda ka shigo na manta sai yanzu na tuna, ina shirin kawo maka sai kuma ga ka, amma 75 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan Allah dan Annabi ka yi hakuri hakan ba zata sake-faruwa ba, in sha Allahu.' " Cikin Izgilanci gami da wulakanci ya karɓi takardun ya ce, "Kuma daga yau sai yau muddin haka ta kara faruwa to a bakin aikinka, sake kwatanta abinda ka yi, yana nufin ka koshi dai-dai kake da kowa. Dan haka yarage ruwanka, ka kiyaye, ko ka sake, aikatawa. Cikin takunsa na isa hade da kasaita ya bar wajen baba Audu ya dade tsugunne a inda ya barshi saboda tunda yake ba a taɓayi masa wulakanci da kaskanci irin na yau ba, sai kawai ya ji wani irin zazzafan hawaye suna zubo masa ace kamar wannan da yayi jika dashi a ce dan Allah ya yo shi talaka yana aikin a karkashinsa kan ya yi masa laifin da bai taka kara ya karya ba, zai zage 76 IZGILI JAMILA MUHAMMED haka, yana gaya masa irin wadannan maganganun. Ya mike daga durkuson da ya yi yana sharar kwalla cikin mutuwar jiki ya koma kan benci da yake kai dai-dai nan yaji sallama akansa ya dago da sauri yana amsawa Malam Saleh ne direban kamfanin ne ya zauna kusa dashi yana bashi baki ya ce, "Baba ka yi hakuri da abinda yallaɓai ya yi maka tunda Allah ya haɗamu zama dashi babu yadda zamu yi sai dai hakuri shi fa a duk duniya babu wulakantacce a gurinsa kamar talaka, babu wanda yake kyama yake tsangwama hade da kyara irin talaka, gani yake takalmin kafarshi yafi talaka, daraja, a gurinsa ka gan ni nan Baba yallaɓai ba jin kunyar na yi sa'an mahaifinsa baya iya cire hannu ya wanke min fuska da mari. T By lay mida on ideol 77 : IZGILI JAMILA MUHAMMED Baba Audu ya ce, "Me yai zafi malam Saleh?" Malam Saleh ya ce, "Ranar kaddara ce ta hau kaina ya aike ni ne to akan hanyata ne karfan nasara da bashi da tabbas sai kawai mota ta tsaya cak na yi na yi taki ta shi na rasa inda zansa raina dan yaja kunne na in yi sauri mutumin sauri yake zai bar kasar ne, gaba ɗaya hankalina ya gama ta shi kuskuran da na yi na rashin kiransa in gaya masa tun a lokacin kawai sai na fita ina ta 'yan dabaruna ga mi da ‘yan jogane-jogane na, na ma buɗe in jin motar ina ta jagwalgwalawata na bar wayata a cikin mota a she, shi mutumin da ya aike ni gurinsa yana tai masa waya ya ce, ban fa zo ba shi kuma zai yi missin din jirgin shi dan haka shi ya tafi, sai kuma wani lokacin, shi ne shima yallaɓai ya keta 78 IZGILI JAMILA MUHAMMED kiran wayata ina ni ban sani ba, danni ina waje ita wayar tana mota dan haka banji kiran da yake tayimin ba. Sai da akalla na yi kusan awa biyu da wasu 'yan mintoci sannan cikin ikon Allah sai ga shi ta tashi ai cikin sauri na rufeta saboda sai da ya gargade ni da lallai lallai in tabbatar duk yanda zan yi nan da minti arba'in in kasance a gurin, to gashi na kusanyin awa uku aikuwa wanda na je domin sa yama daɗe da tafiya cikin sanyi jiki naja motar na dawo na riga na sani nashi ga wani hali, yau sai Allah aikuwa tunda nai horn aka bude min na ganshi yana ta zirga-zirga tamkar mai nakuda na sanni kuma sai Allah, aikuwa ina tsayawa na fito na durkusa kafin ince wani abu sai jin wani shahararren mari na yi akan kuncina ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, 79 IZGILI JAMILA MUHAMMED ashe takardun wata kwangila ce zan karɓo masa da yake shirin shakar makudan kudade bana wasa ba, shi ke nan in ba wani ikon Allah ba ya rasa su. A ranar na dandani bakin ciki bana wasa ba wallahi da ina da yadda zan yi da tun a lokacin zan baar aikin nan, to bani da wata hanyar neman kudi, ga kuma iyali, dan ba karamar wahala na sha ba kafin Allah ya datar dani, na samu wannan aikin dan haka dan Allah Baba ka yi hakuri kuma ka dinga kiyayewa abinda zai ja ya ci mutuncinka, tun da shi baya ganin mutunci da kima hade da darajar talaka ba. Baba ya ce, "Kada ka damu insha Allahu haka ba zata sake kasancewa ba, zan kiyaye, tunda abin babu mutunci sai kai ka alkinta girmanka dan kada a sake ci maka mutunci.' 95 80 IZGILI JAMILA MUHAMMED Malam Sale ya ce, "Wannan gaskiya ne dole ne ka dinga kiyaye abinda zai sa a wulakanta ka." ****** Dan audu ne yake ta faman korawa Alhaji Umar mai da akwai tare da abokin nasa labari. Fuskar alhaji Mansir ta cika da annuri ya godewa Allah tunda ya taimaka aka samu gidan dashi har ya shiga damuwa da yasa yaji shiru bai sake ganinta ba, kuma ya ji dadin yadda Dan Audu ya bincika ya gama cika shi haka nan Allah yasa ka masa kaunarta tun ganin daya ke ta mafarki yana yawan ganinsa yana zaune a wani dokar daji ya nata kuka shi kaɗai sai ya ganta ta zo tana bashi hakuri tana lallashinsa duk da baya ganin fuskarta wani sa in kuma sai ya ganshi yana cikin fain ciki yana ta yin mrmushin amma ita tana kuka shiya sa ta 81 IZGILI JAMILA MUHAMMED tsananta da addu'a ya kuma sa'a taya shi saukar karatu duk juma'a akan dai Allah ya tabbatar da Alkhairi idan ita ce, mafi alkhairi ya kuma kawo sauki ciki lamarin ya kade fitina dake cikin al'amarin. Dan Audu ganin irin tarin fara'ar dake fuskar alhajin yasa ya kara kaimi yana kara koro wasu kuskuren zancen duk dai akokarinsa na ganin Alhaji yaga kokarinsa aikinnasa. hade da kwazansa akan Aikuwa kwalliya ta biya kudin sabulu dan kuwa Alhaji ya yi masa kyauta ta mu samman ya yinda Alhaji ya ce, tukukaicin ka ka gobe ka jira zai a kawo maka mashin shi ne tukuicin binciko min gidansu, da ka yi ya kuma dantso kudin da bai tsaya kirgawa ba ya ce, "Wannan kuma kasha ruwa ka ji, ladan kyakkyawan labarin. 82 IZGILI JAMILA MUHAMMED Dan audu tamkar zai shiɗe saboda murna godiya yake gami da jero dogayan addu'o'in tamkar wani saban maroki, yana karkawa yayi durkoso a gabansa yana faman jinjina masa hannu tamkar yanda akewa sarakai. Alhaji Mansir ya ce, "To dan Audu sai gobe ke nan. " Ya ce, "To ya alhaj." Alhaji ya fita yana kwararowa ‘ya'yan har jikoki dama tattaɓa kunnan alhaji kasan zuciyarsa yana ta kakkabin halin kwarai irin na wannan alhajin shi sam ba matsolo bane tamkar uban gidan nasa, da bai ajiye komai ba sai shegiyar rowa ta bala'i duk yanda kake da shi babbar kyautarsa ita ce, ya bawa mutum gudar dubu ɗaya, to lallai wata dakwalar budurwa ko bazawara ya kawo masa labarinta to kuwa zai samu gudar dubu ko 83 1 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma yinin ya yi yana wahalta masa, to idan ba daya daga cikin wannan ba ne to tsakaninsa da kai dari biyu ne sai kuwa idan yasan kanai masa wata ranar ne. Zai iya baka dari biyar shi ba abin kunya bane ka zo neman taimako gurinsa amatsayinka na yaransa ko kuma dan uwansa ya tattakura ya fito da naira hamsin ya ce, a sai wa yara garin rogo (kwaki) Duk unguwar Koki babu wanda bai sanshi ba, koda karamin yaro ne, ka tambaye shi gidan Alhaji Umar mai akwai to zai nuna maka sai fa in mai shan nono ne. Kowa yasanshi saboda tsabar son kudinsa da matsolancinsa uwa uba kin talaka ya ce, talaka ba shi da wani alfanu a gurin mai akwai. (Wato mai kudi) face, hidim ta masa shi kuma ya biya shi shi ne IZGILI JAMILA MUHAMMED kawai amfanin talaka a gurin mai akwai, alhaji Umar mai akwai ya yi mutukar tsanar talaka gani yake tamkar shi mutumin shi ya ɗorawa kansa talauci ba Allah ba, Alhaji Umar mai akwai shaharar ran mai auri saki ne gaba ɗaya kudinsa suna tafiya ne aa gurin aure aurensa mutane da dama sun ce auran dandano yake ga shi kuma baya san 'ya'yan abin Allah sai ya yo shi daga cikin masu rabon samun 'ya'ya, ko ya ya taɓa mace, sai ta samu rabo da shi kuma abinda yake ba kanta masa ke nan. Shi fa gani yake a duk duniya babu babbar matsalar irin zama da mace ɗaya yasha yiwa abokansa fada idan yana jin suna fadin matarsu daya ta ishe su ya kance ba kuda hankali ba kusan ciwon kanku ba, in banda rashin sanin me duniya take ciki, ya za ka zauna da mace, 85 IZGILI JAMILA MUHAMMED daya sai kace jaraba aini ko mata huɗu ba zan iya zubewa ba in yi shekara dasu batare da na yi can ji ba, ai gara adinga yi ana sabuntawa, aikuwa Alhaji Umar mai akwai ya auri mata kusan ashirin da uku, a kun dade da shi kina iya masa so sai shi ne zai barki ki yi shekara, to daga nan zai ɗaga miki jan kati idan ciki ne dake zai ce ya bar miki abinda yake cikinki duniya da lahira kada ki kuskura ki doso shi da wata matsala ta dan zai kuma yi miki ba, razanar ranku daga ke har yaran in dai kika kuskura kika danganta shi da wata matsala ta yaran zai kuma gaya miki zai fara rufawa yaran asiri, dan kada ai masa gorin ko yaran shege ne zai kuma gaya miki yana nan a amaṭsayinsa na ubansa, sai dai fa baya so idan ke kina so ya bar miki shi ke ka ɗai idan kema ba kya so to ga gidan marayu nan kina iya IZGILI JAMILA MUHAMMED sadashi da can, idan kuwa ke din irin barebarin nance, to uku ya yi yawa zai ce waje road shi din bai dauki mace a bakin komai ba face, ruwan kashe gobara, shi yasa baya daukan raini, ko wulakanci daga gurin kowa ce irin mace ba, da zaki kawo masa shakiyancin banza zai gaya miki ke din ba wata tsiya bace, agurinsa, dan idan ya so ana fita da kayanki ana shigo da na wata dan cewarsa mata sun yi yawa, tamkar ledar pure water ne, ga sunan burjik, duk inda ka zaga birni da kauye, dan haka shi a gurinsa, canja mace a gurinsa tamkar canja rigar jikinsa ne, duk sanda ya bukaci yasha iska zai canza ki da wadda ya ke so, shi yasa” yake mutukar ganin bakin abokin nasa, ganin tun wani shuɗadɗen zamani yake fama da mata daya Aisha, wallahi ba zai iya ba, sai wani ciwon ya shige shi, saboda 87 7 IZGILI JAMILA MUHAMMED bakin ciki da takaicin kaɗaici,, kullum babu wani canji sai kace masifa. Alhaji Umar ya karkatar da kai, yana kallon Abokin nasa ya ce, "Alhaji Wai duk murnar wannan maganar ne, yasa kake wannan rawar jikin hade da wannan batun kudi, tamkar wani wanda bai san ciwon su ba, akan wata can diyan talaka, irin wannan kyautar ko ka manta abinda dan Audu ya fada ne, ubanta ba kowa bane, face, talaka, a cikin talakawan ma na karshe a gun talauci ko baka ji sosai bane cewa ya yi ubanta fa faci yake yi, aini cewa nake daga jin baya nin Dan Audu ko duban mai rin kamaninta ba zaka sake yi ba, a matsayin Hisham na dan mai kudi wayayye, kyakkyawa me zai da wata Diyan talaka duk ‘ya'yan manyan masu sukuni karasa wadda zata zama sirikarka, matar danka, sai wata IZGILI JAMILA MUHAMMED ‘yar mai faci, kai wannan abu da bakin ciki yake, ina garin gami mai kuɗi da talaka, da har za kai sha'awar hada zuri'arka da ta shi.' " Alhaji Mansir Kwangila ya ce, "Wai ni shin Alhaji Umar mai ka ɗauki talaka ne, kaskantantacce, wulakantacce, kuma mara 'yanci, wanda duk sanda mai akwai (Mai kudi) ya mula yasha iska zai ciwa zarafi, ciwa zarafi, ya tozarta shi dan kawai Allah ya yishi mai shi, shi kuma ya yo shi mara shi, to ba haka bane, talaka mutum ne, tamkar kai, kuma ba'a bin wulakantawa bane saboda dinbin daraja da martabar da Allah yai wa bayinsa ‘yan adam Allah da kansa yake faɗa a cikin alkur'aninsa mai tsarki WALAKADI KARRAMNA BANI ADAM!!! Hakika ubangiji ya daraja ya girmama ɗan adam sai kai dan kawai Allah ya huwace maka 89% IZGILI JAMILA MUHAMMED za ka wulakanta mutum talaka, waya sani ma ko mutumin da kake wulakantawar ya fika a gurin Allah dan haka wallahi wallahi banga dalilin da zan kyamace talaka ba, wai dan kawai ni me shi ne, shi kuma mara shi, to haka Allah. ya nufin ya ganshi, kuma ba zan taɓa kin saba, wai dan yana faci, faci ai sana'ace, a gurin kane da ka raina shi har kake kiransa da al'amarin duniya ba yadda ka zata bane. Dan kana ganin kana da kudi to dare daya idan Allah yai nufin nuna ikonsa da buwayarsa. sai ya mai da shi kai da kake kiran koma ya fika sunan kaskantacce kuma kaskantattace matsayinka kake kiran kai kuma kadawo kamarsa, ko da yake ba za kai jarumtakar da ya yi ba, tunda ance ya daɗe a nan anguwar amma baka san shi ba, kaga hakan yana nufin ya iya da talaucinsa, tunda bai taba takowa kofar IZGILI JAMILA MUHAMMED gidanka da sunan maulaba, ka ga hakan yana nuni da cewar shi din mai jajircewane, da kuma tsayawa iya matsayin da Allah ya ajiye shi, kuma bai yi bakin ciki da yadda Allah ya yoshi marashi ba, bare ya dinga binbinin a gurin masu akwai ba suna wulakanta shi, kafin su dan watsa masa ‘yartsaba su nai masa dagawa, suna hura hanci ka ga kuwa akwai tarbiya a irin wannan gidan, sakamako 'ya'yanmu da muke barinsu babu tarbiya dan haka in dai ni Mansir ni ne mahaifin Hisham to fa bashi da wata matar aure idan ba 'yar gidan mai faci ba. Alhaji Umar ya tsurawa abokin nashi ido an ya kuwa kansa kalau, kai anya kuwa ko da yake daman yasan halinsa in dai akan talaka ne, yo mutumin da zai zauna gurin mai gadi suna hira, idan ka ganshi da ma aikatan gidansa 91 IZGILI JAMILA MUHAMMED yana kwasar dariya tamkar ba mai gidansu ba sai ka ga har wani share musu bakin yake tamkar ba mai kuɗi ba, shi yaga zai iya, shi yasa fa ko dariya baya iya yi a gidansa, dan kar wata ta yi gigin raina shi, in kaga dariyarsa, to yana majalisar su ta masu akwai ne." ****** " Shin wanene alhaji Mansir kwangila Alhaji Mansir Asalinsa dan garin Gombe ne mahaifinsa mai suna Alhaji Bawa, shahararren mai arziki ne sannane a cikin garin na Gombe, kai bama nan kadai ba, har da sauran garuruwan da ke cikin Nigeria ya shahara sosai dan kasuwa ne babu irin kasuwanci da ba ya taɓawa, ya kan sari Auduga ya sarrafa tata a kamfaninsa yana fita da ita kasashen duniya, idan ya ta shi dawowa shi kuma sai ya saro shinkafa da wasu kayayyakin 92 IZGILI JAMILA MUHAMMED da muke bukata buka, sannan yana da kamfanin Tumaturin gwangwani sannan yana da wani kamfani amma hadin gwiwa ne, a jafan da suke kera takalma masu shegen kyau, matar Alhaji Bawa, daya mai suna Rahina, ana kiranta da Hajjo Allah ya albarkace su da ‘ya'ya bakwai uku maza hudu. Mata ta farko mace ce mai suna Binta da ake kiranta Batulu, sai na biyu mai suna Mansir, daga mansir sai Barira sannan Hindu, sai najib, sai Safiya, da kuma dan autansu, Isma'il gaba dayansu, sun ta so cikin kulawa hade da tarbiya irinta addinin musulunci sam Alhaji Bawa shi da Hajjo basu saki yaran sun sangartasu ba, wai dan kasancewar mahaifinsu, wani ne, sun basu tarbiya ta gari dan gaba ɗayansu, sai da kowa ya sauke sun yi karatunsu na boko amma 93 IZGILI JAMILA MUHAMMED matan iyakar su secondry ake yi musu aure Inna Batulu anan Gombe take aure bata taɓa haihuwa ba. . Safiya Bauci take da yaranta Hindu Abuja ita ma dana ta yaran Barira ma anan Gomben take dan ita basu da nisa da gidan iyayan nasu maza ne ya ce, su yi karatu, duk anan gida Nigeria dan bai yarda ya tura dansa wata uwa duniya da sunan karatu ba, kuma garin da suka daurewa sheɗana da duk wata lalata kugu wanne karatun waɗannan makiya Allah zasu koyawa yaran da suke son musulmi ne su da a duk duniya basu da abokin gabar da ya wuce, musulmi, to wanne karatu zasu koya masa ban da su wayar masa kai, ya san ilimin lalata ni wallahi wannan abin yana damu na rashin sanin. ciwon kanmu, Nigeria wani bature ko ka taɓa ganin ya kawo dansa Nigeria ya ce, 94 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya yi karatu, sai mu da bama kishin kasar mu zamu ringa jidar ‘ya'yanmu tamkar gyada muna kaiwa makiyanmu masu burin ganin sun karmu sun rusa mu, su zamu bawa yaranmu. Ai wannan damar suke samu su koyawa yaranmu duk wata sheɗana, sai sun gama lalata musu tarbiya sannnan zasu turo mana su dan su zame mana annoba, su buwaye mu, dan haka Alhaji Bawa yana daya daga cikin mutane masu kyamatar tura yaransu karatu waje, gaba dayansu mazan sun yi karatun su ne a nan gida Nigeria. Alhaji Mansir ya yi karatun sane a Jima'ar A.B'U A.B'U Zariya inda ya yi karatunsa akan kasuwanci wato Business. Mansir ya dade bai yi aure ba, dan har sai da dan Auta Isma'il ya fara haɓaka Alhaji Mansir ya haɗu da Zalifa ne a Misra 95 : IZGILL JAMILA MUHAMMED lokacin ya ji kan wasu harkoki da suka kai shi Zalifa balarabiya ce, gaba da baya mahaifinta shi ne Wazirin Sarkin na Misra. Mansir ya haɗu da Zalifa ne ta sanadiyar 'ya'yanta wanda Allah ya haɗa su anan garin Kamfanin Babanta ya je, domin gogewa da sanin makamar aiki, domin ya fada har kar Kwangila to wata rana ne shi ya yanta Alhaji bashir ya gaiyace, shi cin abinci gidansa to sai Akai sa'a Zalifan ta je gidan yayan nata ita da kanwarta Nadiya, tun daga sannan soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu ansha fama kafin kasancewarsu matsayin ma'aurata, saboda iyayanta basa son tai musu nisa dagewarta ce, tasa iyayen suka hakura suka aura mata wanda take so batare da ɓata lokaci ba aka sha biki amarya ta tare a Nigeriya a 96 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma a garin ‘iyayan mijinta watan Gombe da farko iyayansa da yan uwansa duk suna son ta amma daga baya duk sai suka canja canja mata su ka bi suka tsangwameta ta kuma rasa dalili sai daga baya ta gane kan rashin haihuwar da bata yi bane, a zuciyarta tai mamaki shekara uku ne kawai da auran su shi ne har ake gwada mata tsana irin wannan ta shiga tsananin damuwa ta yadda dangin miji suke tsangwamarta suka mai da ita mujiya a cikinsu, duk ta bi ta rame, sai hanci da manyan idanuwanta da suka karayin manya idanuwanta da suka karayin waje, gaskiya Zalifa kyakkyawa ce dan ko cikin larabawan ma ita din mai kyau ce, amma duk irin abinda suke mata bata taɓa gayawa mijinta ba sai dai ko yaushe ya nai mata korafin ramar da take yi, ta yi yawa, to dole ne ta rame babu 97 IZGILI JAMILA MUHAMMED 'yan uwa akusa dangin mijin da take san su zama 'yan uwanta sun tsaneta basa son ta idan ta je inda suke suna kyararta ai dole ta shiga wani yanayi to abin Allah shekararsu biyar da aure Allah ya bawa zalifa ciki wai murna a gurin Mansir da Zalifa ba'a magana har ma da dangin nasa da suke kinta sai duk suka saki aka shiga tarairayarta, shi Alhaji mansir Bawa ya yi mutukar murna da Allah ya nufeshi da ganin jika, daga Mansir da yake Mansir yaro ne mai hankali da biyayya ga taimakon marasa karfi. Akwana a tashi har Allah ya sauki Zalifa lafiya ta haifi danta namiji wowowo fadin kyau ɓata baki ne vare. daka ganshi kasan jinin larabawa ne, saboda tsantsar kyaunsa duk wanda ya zo barka sai ya tafi da zancen yaron nan, Hmm! Zo ka ga bakin Alhaji Mansir yaki ng IZGILI JAMILA MUHAMMED rufawa sai Hidima yake ya kawo wannan ya kawo wancan dangin Zalifa ma ba a barsu a baya ba, ana igobe suna suma suka diro nigeria dauke da kwaryakwaryar kayan arziki dan danginta sun zo da dama, dan jirgi sukutum kakan yaro mahaifin Zalifa watan Wazirin Sarki Misra ya dira duk mai bukatar zuwa Nigeria. To fa ga jirgi nan a kai ka a dawo da kai, haka akai taron suna lafiya a ka gama lafiya Jariri ya ci suna Hisham. Hisham ya ta shi yaro mai-nutsuwa gami da hankali amma fa miskili ne na gasken gaske shekararsa biyu a duniya Allah ya yiwa kakansa Alhaji Bawa rasuwa, rasuwar da ta girgiza duk wani mutum daya kwana ya ta shi a cikin garin na Gombe jama'a sun ji mutuwar mutum na mutane irin Alhaji Bawa, mai kirki 99 IZGILI JAMILA MUHAMMED mai taimakon bayin Allah mai hidima a gurin jadda kalmar Allah. Ayyukan da yake gami da taimakon da yake sai dai Allah ya biya shi Islamiyyoyi da masallatai fanfuna burtsatse babu wanda yasan adadin da ya yi a cikin birnin na Gombe da ma kauyikansu sai dai mu ce, Allah ya ji kansa, halinsa na gari ya bishi, mutuwar Alhaji Bawa da shekara Alhaji Mansir ya tattaro ya dawo Kanon dabo mai mata mai mota mai dala da gworon dutse. saboda harkokinsa sun fi yawa a can kano da Abuja, a inda ya kera gidansa a Zoo road suka tare sai dai duk karshen wata yake zuwa Gombe domin duba hajiyar, sai da ya kaɗa ya raya ya ce, Hajya ta dawo amma ta tubure ta ce, babu inda zata saboda mutanan alhaji marigayi saboda duk wani abu da ake yi da babu 100 IZGILI JAMILA MUHAMMED wanda aka daina 'yan'yan ta maza sun tsaya mata musamman Alhaji mansir dan shi ne ya dauko kyauta irin ta mahaifinsa, da son talakawa mararshi, dan gaskiya yafi kannensa najib da Isma’il taimako dan su da Hajjo tai musu zancen duk wata ga abinda zasu kawo cewa su kai kai a bari wanda Baffa ya yi ya yi, ya isa, Allah ya bada lada. Batai mamakin jin irin wannan maganar daga bakinsu ba dan ta sansu ta san halinsu suna kyamatar talaka sun ce su da talaka ko a hanya, shi yasa kwandalarsu ba zasu bayar ba, dama da mahaifinsu yake yi ba asan ransu bane, dan dai ba yanda zasu yi ne, kuma saboda ba kudinsu bane, ko da yake shi najib sai da ya taɓa gayawa Hajjo gaskiya ta gayawa Baffa ya daina kashe musu kudi haka. 101 IZGILI JAMILA MUHAMMED Ta kalle shi da alamar tambaya ta ce, "Wana irin kudinku yake kashewa aikuwa babu kun ya babu tsoon Allah ya ce, Dukiyar Baffan nasu ai ta suce saboda haka gaskiya Baffa ya daina raban kudi da abinci ai sangarta su ake yi, su dinga zaman banza, zuciyarsu ta ida mutuwa, tunda suna da mai basu abinci har ma da nace fane, dan kada ta Allah ta kasance gadonsu ya zaru babu auki." Hajjo sai ta saka salati tana salallami fadi take oh ni Rahine yau naga. abinda ya ishe ni najib Allah ya shiryeka to ni dai ba za aji wannan maganar a bakina ba, idan ka matsu kai ka same shi sai kai masa maganar, shi yasa koda suka ce su ficikarsu bazasu bayar ba bata damu ba, ta gayawa Alhaji mansir ya ce, Dama bata yi musu magana ba. 102 IZGILI JAMILA MUHAMMED Hajjo kin san dai kome ye kike bukata zan yi miki su yarane daman niya dace in yi ko meye Hajjo ta ce, "Duk da haka kai ma ai zaka so su taimaka maka tunda abinda ai da yawa, kuma kamar yanda kudi suke zuwar maka suma haka kawai dai su haka Allah ya yosu in dai batu ne nasu bayar to fa ba za a ji bakinsu ba, saboda Allah rayuwa kuwa zata yiwu. a haka kana da shi ba zaka taimaki dan uwanka marasa shi ba. Alhaji Mansir ya ce, "Hajjo ki daina ganin laifinsu suna fa da iyali ga yara da wanne za su ji." Hajjo ta ce, "Da yake kai baka da iyalin ko haka dai ya dinga bata hakuri ya ce, tunda ya ce, zai iya zai iya dinne tunda mahaifinsu ya rasu, shi ya dauki nauyin yin sadakar da aka sabayi, duk safiya ana dama koko da kosan sadaka 103 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma kokon da sukarinsa bajau, da rana kuma ana yin wake da shinkafa da mai mutum sai dai ya nemi ya ji, kuma ba sai almajirai ba ko waye in dai yake ko ya kai kwanansa, duk girmansa sai an take masa shi abinci, duk ranar juma;a ana can ja kalar girkin da safe ana yin kunun tsamiya da fanke, da rana kuma ana yin tuwon shinkafa da miyar taushe, kuma gaba daya Alhaji mansir ne yake komai hatta da 'yan aikin da suke wannan aiyukan shi yake biyansu, kwandala babu ta wani dan uwansa kuma duk karshen Iwata yake zuwa ya saurari talakawan da mahaifinsa yake taimaka musu, wasu bikin 'ya zai yi babu gaba ba baya. Wani matarsa ce ta haihu babu Ragon suna wau rusaune ya rutsa da su, da dai sauransu duk kuma wanda ya kawowa Alhaji Mansir matsalarsa to sha 104 IZGILI JAMILA MUHAMMED Allahu sai ya taimaka masa sai mutumin nan ya yi farin ciki ya saka masa albarka. Hisham ya yi Primary dinsa wata tsadaddiyar makaranta dake cikin birnin na Kano mai suna Attaufeek Iliman an tahafees yaro ranar da ya gama primary, to ranar aka masa bikin sauka to shi ma Hisham haka daga nan sai alhaji Mansir ya kai shi Germany gidan kanwar Hajiya Zalifan watan Nadiya da take aure a can suke zaune a can ita da mijinta sai dai basu haihu ba a can yai Secondry dinsa yai kuma jami'a. Hisham ya zaɓi ya gaji dadinsu watan dai yana san zama controctor aikuwa sai da ya zama Hisham tun yana Secondry dinsa ya fara Harka da 'yan mata kasancewar kyakkyawa gaskiya Allah yai masa halitta gaskiya Hisham ya gama haduwa Hundred percent to jinin .105 IZGILI JAMILA MUHAMMED larabawa fa, da kuma fulani ga kulawa dole a ga kyau dan usuli duk inda kake neman kyakyakyawa to kana samun Hisam sai a shafa fatiha, saboda kyau ne tsabarsa babu mide babu abinda yake kara masa kyau irin wadannan kyawawan idanuwansa masu firgita 'yan mata ko da yaushe zaka gan su a lumshe. Hisham dogone amma ba irin zankalkal din nan ba ne yana da dan jiki watan murjewajiki dan shi ba irin ramammun nan bane sanna kuma shi ba mai jiki ainun ba ne, fari ne tas irin farin larabawa kana ganin sa zaka san shi din balarabe ne ta yadda ga shin kansa yake akananɗe mai kuma azabar santsi da baki irin na larabawa. Yana da dogon hanci, bakinsa dan dai-dai mai fararan hakora tas, tamkar kankara, idanunsa a lumshe tamkar mai 106 IZGILI JAMILA MUHAMMED jin barci yana kassara dubun nan 'yan mata da wannan kallon na shi mai ratsa JINI DA JIJIYA. Hisham Mansir Kwangila ke nan miskili mai murdadɗan hali yana da tsare gira ba shi da fara'a tunda yake shi bai san so ba, bai taɓa yin shi ba kuma baya son yasan shi bare ya yi shi, duk 'yan matan dayake yi bai taɓa cewa yana san su ba sai dan shi suce suna son sa... Ya yi 'yan mata 'ya'yan manya wadanda ba zai iya kirga su ba shi din mane min mata ne na sosai amma ba ko wacce kuci ku bamu ba shi din sai kin kai kin doke kin haɗu koma ki na da abinda ya yi masa shi ne zai ce miki bukatarsa shi yasa matansu suke rububinsa suke kuma son sa. Hisham sai da yai shekara goma sha tara a duniya sannan ya samu kanwa mai 107 IZGILI JAMILA MUHAMMED a sarar sunan Hajjo kakarsu wato Rahina, ake kiranta da Ummita, Hisham ko da ya kammala karatunsa bai dawo Nigeria ba, wani kamfanin zane zane ne suka dauke shi aiki sai da Alhaji Mansir ya yi da gaske sannan ya dawo gida amma duk da aka yadawo da ɗabi'ar nasara duniya ya koyi yadda ake daga kwalba mata kuma yanda suke sonsa duk inda ya shiga in dai da mata sai sun so shi dan Allah yai masa farin jini in dai ya shiga guri sai an so shi to kuma daman an ta shi garin ida suka dauki zina tamkar ado, kuma akai dacen shi din mai farin jinin matanne da kansu suke yi masa tallan kansu, burinsu dai da fatansu ya yarda dasu batare da ko kwandalarshi ba, su abin alfaharinsu ne kamarsa hadaɗden saurayi ya kwasa sai dai alhaji Mansir yai masa jan ido kuma an kammala ginin 108 IZGILI JAMILA MUHAMMED kamfaninsa na Abuja shi yasa ya matsu ya dawo domin ya kula da shi shi kuma alhaji Mansir din ya kula da na nan Kano din, ya kuma gaya masa ya siya masa fili a nan cikin garin Abujan idan yana da zanen gidan da yake sha'awa to ya turo masa ta computer sai Ai masa kafin ya dawo aikuwa har an kammala masa hohoho dan da shi gaskiya gida ya tsaru tamkar wani shugaban kasa. Gidan ya gama haduwa bada dadewa ba ya diro Nigera kasarmu ta gado, ya yinda ya kwashe tsayin shekaru ba ya kasar dan tunda ya gama primary ya tafi sau biyu kawai ya zo shi yasa yaga kasar ta canja masa, tamkar ba dan kasar ba, dan duk komai ya canza masa, ‘yan uwa ansha murnar dawowarsa, Ummita kanwarsa ma sai murnar dawowar yayanta take. 109. IZGILI JAMILA MUHAMMED Bayan ya huta yai raban tsaraba kowa aka bashi sai da yai wata biyu yana hutawa sannan ya tattara ya koma Abuja daman dawowarsa da sati akai kasaitacciyar walimar dawowarsa, tare da murnar bude kamfanin. An sha shagali an kar kudi tunda ya tare Abujan ya dada ci gaba da harka da matansa giya tamkar ruwan roba ya maida ta. Dan idan kuka ganta jejjere cikin firji dinsa ka dauka lemo ne. Gwani ne a harka da mata da kuma wiwi, sai taba da ita ma ya kware gurin shanta, to daga su baya karawa da komai duk wani rashin tarbiya da ya koyo ya kuma zubar da wanda iyayansa su kai masa; to bai daina sallah ba, kuma yana. yinta a kan lokaci, duk yanda ya kai da sheke a yarsa to da zarar lokacin sallah ya yi to zai watsar da koma mai yake, sai ya 110 IZGILI JAMILA MUHAMMED sauke farali, Hisham yana da mutukar tsafta ga ya shi kuma da tsantsani na jaraba. Ba ko wanne abinci yake ci ba, sai kina da maşifar tsafta shi a duk gidansu idan ba Momi ce tai masa abinci ba ba iya ci, da ba yacin girkin 'yan aikin gidansu, dan haka ba kowane restaurant yake cin abincinsu ba, sai irin kasaitattun nan, wanda sai manyan garin na Abuja, suke zuwa to irin su yake iya cin nasu, koma sai ya bada tsaftar gurin da ma'aikatansu zaka sha mamaki, mutuka yadda ya dauki al'adun turawa, da ɗabi'unsu to sai kuma bai dauki cimarsu ba gaba daya ma ba zai iya cin irin abincinsu ba, dan tunda yake bai taɓa ɗanɗana irin abincin nasu ba, kuma ya ɗauki tsawan shekaru goma sha tara zuwa a shirin a turai amma bai taɓa gigin dandanar cimarsu ba, don in har ya ce, IZGILI JAMILA MUHAMMED zai dandana to fa babu shakka sai ya tanadi gadon a Asibiti, saboda yasan sai ya kwanta ciwo dan shi a ganinsa babu babban abin kazanta irin abincinsu, dan shi ko gani ya yi suna wani jagulan girkin to fa ranar yini zai yi zuciyarsa na ta shi, sai ya yi amai, zai ji dadi. Shi a rayuwarshi babu abincin da zai ci ciki lafiya baka lafiya irin abincin mu na Nigeria. Aiko dole Anty Nadiya take yin irinsu tun bata saba ba har ta koya dan shi da kansa yake yi, tana ganin har ita ma ta iya take yi musu ai fa sai ta ga gaskiyar Hisham abincin Nigeria yafi na kowacce kasa dadi, a ido, zaka ganshi da tsafta hade da ban sha'awa, baki ga shi da dan karan dadi ranar da Hisham yai musu dan haka hohoho! Zo ka ga wawa su gurin Al Mubrak mijin Nadiya shi ma Balarabe ne 112 IZGILI JAMILA MUHAMMED aiki ne ya kawoshi Germany amma haifaffen Misra ne, danwaken fulawa ya yi musu, da man gyada ziryan da yajin da yasha magi ya yanyanka dafaffen kwai a ciki ai ji su tamkar kunnansu zai tsinke saboda dadi duk wata Momi take aiko musu da ka yayyakin amfani irin na Nageria har fulawa take aiko musu da ita su kuka, daddawa, karkashi, kuɓewa bushashshiya, zogale, wake, gyaɗa, man gyada, dakakken yaji, manja, kayan kamshi, man shanu, bushahhen kifi, ogun, ayodi, da dai sauran kayayyakin girki irin na Nigeria. Aikuwa Hisham ya zage ya danɗasa musu girkin da wata macen ma ba za ta yi test ɗn na shi ba, komai cikin tsafta Tentable gare shi kullum ga kalar girkin` da zai yi ya iya wainar fulawa, wadda baya gajiya da cinta, wake da shinkafa, IZGILI JAMILA MUHAMMED jallof din shinkafa ko taliya alkubus ma ya iya, arayuwa tuwo ne kawai bai iya ba, shi ma ba wai towanne bai san yanda ake ba ya san yanda ake yi tuka tukenne bai iya ba, duk sanda zai musu tuwo sai dai ya nunawa Nadiya ta tuka. To bata iya ba har ya koya musu, ita da Mijinta. Wai shi ma yana san ya iya saboda watarana ko idan Nadiyan bata da lafiya aikuwa tunda kowa ya iya shi ke nan idan daga Hisham ne ya riga dawowa makaranta sai ya girka musu abinci, idan Nadiya ce, sai ta yi dan ita ma karatu take anan jami'a da Hisham din yake, amma ba departement dinsu da ya ba, idan kuma mijin tane ya riga ta dawowa to shi zai musu abincin. Haka yai rayuwarsa cikin jin dadi gidan Anty shi tamkar kaninsu haka suka dauke shi ba dan ba shi yasa yake yadda IZGILI JAMILA MUHAMMED ya ke so, a kuma lokacin da yake so mahaifinsa ya shiga tashin hankali ne tun randa ya kama kwalaben giya burjik a dakinsa lokacin da ya dawo tun daga sannan yake san ya yi aure ko ya rage wani abun dan aure ni'ima gare shi yana sa arage duk wani iya shegen da ake yi tun daga lokacin yake tuntuɓarsa da zancen amma shi Hisham din ya share maganar a ganin sa me zai sa ya yi wani aure idan banda takurawa kai da saka wa kai tention to shi gara ya yi rayuwarsa a haka duk da ya san hakan da yake yi ba dai-dai bane, ga tarin zunubin da yake ta jibgawa kansa Zina ai babban laifi ne ko da yaushe idan wannan tunanin ya faɗo masa sai ya shiga ta shin hankalin irin laifukan da yake aikatawa, ya yi ta tuba gurin Allah amma ya kasa hana zuciyarsa aikatawa, saboda shi din baya iya ' IZGILI JAMILA MUHAMMED daurewa ko ya ce ya daina da zarar wata daga cikin 'yan matan nasa ta zo to fa shi ke nan zai koma ruwa, saboda tsabar sansa da 'yan mata suke yi ba shi yake kiransu ba su suke zuwa har inda yake kuma sai ya ga mai musu wulakanci saboda shi din IZGILANCI halinshi ne, ko dan jinin sarauta yana yawo a jininsa ne, yasa yake da shariya, da tsare gida, duk yanda kuke da shi karya ne ka ga dariyarsa shi sam baya dariya sai dai murmushi, shi ma mai gani daga Momy dinsa sai Daddy dinsa sai fa idan ya yaba da ke. Farkon haduwarku ba zai ce kin masa ba, ko yai miki magana sai dai ya dan yi miki murmushi, to har ku rabu da shi ma, ba zaki kara ganin ya yi miki ba, shi kuma duk yanda kika kai da nacinki yawan lokacin da za ku yi ke da shi wata ɗaya ne, da ga nan kuma sai wata, saboda 424116 IZGILI JAMILA MUHAMMED yan matan su suke nuna masa kaunarsa su suke kamar su ne namijin shi kuma shi ne macen shi yasa yake ja musu aji yake yi musu yadda yaga dama saboda su suke binsa ba shi yake binsu ba. Tir da wannan zamanin da 'yan mata suke ganin cinye wace waye wace dan kin buɗa baki kin cewa saurayi kina san shi wannan ba ɗabi'ar kamun kai bane, wai mai yasa mata muke wulakanta darajar mu, muke banzartar da kimar mu mace fa daraja gareta shi yasa Hisham bai ɗauki mace wata tsiya ba, saboda ya cam fasu duk matan waka suke basu da kintsi, saboda bai taɓa haduwa da ta garin ta kirki ba, wadda duk kyansa duk kuɗinsa haka duk ajinsa kuma duk mukaminsa karya yake ta bishi sai dai shi ya bita ko da kuwa shi ne shugaban kasa, dan har yau har gobe akwai na gari na kirki a IZGILL JAMILA MUHAMMED cikin 'yan matan masu kuma kima da daraja, sannan kuma da yawa a duniya shi din ne bai taba dacan haduwa da ta kirkin ba yanzu watansa tara ke nan da dawowa Nigeria. Sanda ya dawo da sati biyu suka 'koma saban gidan da Alhaji Mansir din ya tamfatsa a sultan road a ciki ma a kai bude saban kasaitacciyar walimar kamfanin na Abuja da kuma murna dawowar ɗan lelan Alhaji wanda Alhajin ya sangarta shi ya taɓarashi, su ka kuma barshi yake yadda ya ga dama ba kuma tare da sun tsawatar masa ba. AN DAWO LABARI Hadiya ce sun kuye bakin murhu tana faman hura wuta taki ta kama kasan cewar icen ɗanye ne saboda yana yi na damina ta ɗago da idanuwanta da suka yi jajir saboda a tsabar hayaki tana amsawa 118 IZGILI JAMILA MUHAMMED yaron da ya shigo sallamar da ya yi, yaron ya ce, “Wai wani Awaje ya ce, na sallama da Malam Usman.?' Ta ce "Kace yana zuwa. Ta mike daga durkson da ta yi tana karkade jikin ta ta yi sallama kofar ɗakin. Innar ta su, in da baban nasu yake kishingide yana sauraren gidan radio kano suna gabatar da zaɓan yamma Inna kuma bata nan ta tafi dubiya, amma ta san tana hanya tunda yamma ta yi, duk da dai bata wani jima da tafiya ba, dan sai bayan sallar la'asar sannan ta tafi. Malam Usman yasa hannu ya rage radio yana amsa mata sallamar ta durkusata ce, "Abbu ana sallama da kai'a waje." Ya ce, "Wa ye.?" Ta ce, "Ni ma ban sani ba." Ya dauki hularsa dake ajiye a gefensa yana kokarin sawa ya ce, "To 119 IZGILI JAMILA MUHAMMED 'yar gidan Abbunta maza je ki ci gaba da aikinki." wata Ta saki wata dariya mai ban sha'awa ta tafi ta ci gaba da aiyukanta shi ma Abbun fitowa ya yi dan ya ga mai sallamar yana fitowa yaga tsadaddiyar mota ta dallare masa idanu, saboda kyau sabunta tai shurum a kofar gidan nasa, tana hutawarta daga gefe kuma wasu kasaitattun Alhazawan birni ne tsaye a jikinsu sanye da dakakkun danyin shaddodi, sai zabga daddadan kamshin turare suke irin nasu na manya, ya dan ja turjiya ya tsaya turus, yana tunanin ina mai sallamar yake dan shi ko kusa bai yi tunanin wadannan hamshakan mutanan sune masu sallamar ba dan ya san shi dai shehu Usman mai faci duk cikin mutanan daya sani yake kuma har 120 IZGILL JAMILA MUHAMMED kar dasu ba shi da irin wadannan balle har yai tunanin su ne suke sallamar... Sallamar ya ji an yi masa yai saurin dawowa daga tunanin da yake yi, ya amsa sallamar shi ma cikin sakin fuskar tamkar dai suma da suke ta sakar masa, murmushin. Shi dai shiru ya yi yana kallonsu daya ne ya farayin magana ya ce, "Mu ne muke sallama." Ya ce, “To madalla Alhaji Yakubu babban na hannu daman Alhaji Mansir dinne dai har yanzu yake maganar ya cc, "Daman Mun zo gurin ka ne da wata muhimmiyar magana wadda take bukatar zama dan ni din ba gwanin tsaiwa banc. Ya fadi hakan yana dariya, wadda ta bayyanar da hakorin farin gwal din da yake bakinsa. Malam Usman ya kalli rugujajjen kofar gidan nasa mai dauke da jarkasa 121 IZGILI JAMILA MUHAMMED tumumu irin jajur din nan ya kai dubansa gurgurarriyar kofar shiga gidan ta katako mai barazanar rusowa. Ya dan saci kallonsu dubi irin danyun shaddojin dake jikinsu yanzu haka zasu dansu a cikin jarkasar nan wata zuciyar ta ce, to ya za'a ayi ai sun kallo yadda gurin yake kuma a hakan suke san su zauna. Ya dubi Alhaji Yakubu ya ce, "To bara in kawo abin zama. " Suka ce babu damuwa ya juya da sauri çikin gidan ya same ni ina kwasar tuwon dare ya ce. "Hadiya maza shiga daki ki dauko sabuwar tabarmar ledar nan cikin girmamawa ta ce, "To" Ta dauko da sauri ya ce, "Yauwa ki zubo ruwan sha ki kawowa baki." Ta amsa cikin girmamawa ta saurin karasa kwashe tuwan ta dauko saɓanin 122 IZGILI JAMILA MUHAMMED kwanon sha sabo fil ta sake ɗauraye shi ta tuttulo ruwan tulun Innar mai dan karen sanyi ga shi ruwan dadi. Farin fenti jikin kwanon shan sun tai maka gurin fito da farin ruwan gami da tsaftar sa tamkar irin ruwan da suka saba amfani da shi, ta shiga ɗaki ta ɗauko zumbulelen Hijab dinta da nikaf ta saka ta ɗauki ruwan ta yi soro inda take jiyo maganarsu duk da dai ba sosai ake jiyo maganar ba ta yi sallama cikin siririyar murya ta durukusa har kasa ta gaishe su Alhaji Mansir da yake cike da fara'a gami da wani matsanancin farin ciki ganinta a zuciyarsa fadi yake tarbiya da dadi gami da biyayya da sanin girman na gaba sai gurin diyan talakawa dubi dai irin yadda zube gwiwa bibbiyu saɓanin 'ya'yan masu dà shi, wadda wata ma ko kallan arziki abokanan babban nata basu isheta. 123 IZGILI JAMILA MUHAMMED Masu tarbiyar cikinsu ne zasu gaishe su daga tsaye, ko kuma a ce, sannunku. Daddadar muryarta mai cike da nutsuwa ce ta katse masa zancen zucin da yake yi, ta ce, “Ga ruwa." Alhaji Yakubu ya suri kwanan da ta ajiye sanyin ruwan da ya ratsa kwannan ya ratsa tafin hannunsa yayi saurin bude murfin, ruwan garai-garai gwanin kyau ya sha sanyin ruwan ya kwaranya a tumbinsa yai hamdala Alhaji Mansir ma ya sha su kai godiya ga Allah. Alhaji Yakubu ya gyara murya ya fara da gabatar da kansa ya ce "Ni suna na Alhaji Yakubu Galadanci, ni haifaffen garin nanne a galadanci iyayena suke amman ni ina zauna ne a Alu Aɓenue sai kuma abokina kuma aminina shi kuma sunansa Alhaji Mansir kwangila haifaffin 124 IZGILI JAMILA MUHAMMED garin Gombe ne amma anan garin shi yake yana zauna ne a Sultan Road kuma shi ne wanda yai dalilin zuwannmu nan.” " Malam Usman ya ce, "TO madalla Allah dai yasa lafiya .?" Alhaji Yakubu ya kuma sakin dariya ya ce, "Lafiya kalau, alhaji Daman dai yaga 'ya wajenka ne ya yaba da hankalinta da nutsuwa gami da tarbiya irin ta gidan nan shi ne ya yiwa dansa kamu, in dai babu wanda akaiwa * alkawarito yaran gurinsa yana son ta. " Malam Usman ya ja shiru na lokaci mai tsaho sai can ya ce, "To Alhaji hakikanin gaskiya ban yi mata miji ba, kasancewar ban bata damar sauraran samari ba, saboda karatu, take duk da dai ta kusa gamawa dan saura wata uku ne kurum ya rage ta gama, to amma wani hanzari ba gudu ba, kamar na so na ji 125 IZGILI JAMILA MUHAMMED kace shi Alhajin ne yayaba da ita ba shi yaron bane, ya ganta, ya ga yana son ta ba. Alhaji Yakubu ya cc, “Haka nace to mu din mu na yi ne kamar yanda shari'ar ta tsara gurin neman aure kuma muna bin yadda addini ya tanadar cewar idan zaku aurar da 'yar ku, hakkin iyaye ne su nemawa ‘yarsu miji na gari haka ma mijin suna iya zaɓa masa mata ta gari shi yasa muka zo da karfinmu saboda tarbiya irin ta gidanka mu kai kwaɗayin hada zuri'a da kai." Malam Usman ya sauke ajiyar zuciya, Gaskiya ya gamsu da duk wani bayani da kuka yi kuma shi ma zai so hada zuri'a da su dan ya fahinci su din dattawan kwarai ne, kuma ya gane su din ba daya suke da sauran ,masu kudin wannan zamani ba, da karan gidansu yafi ye musu talaka sau dubu, basu talaka mutum ba, ba wai dan kuɗinsu ba sai dan kamala da mutuncin da suka nuna ko 126 IZGILI JAMILA MUHAMMED kusa ko alama bai ga wani wulakanci ko tsantsanin da suka nuna masa ba tun zuwansu lallai ku a cikin masu kudin su din daban suke ya cc, su dan ba shi lokaci zai tuntuɓi mahaifyar yarinya ko da wanda ita yarinya take so suka cc to babu damuwa kamar yaushe yake ganin zasu dawo dan su ji yadda ake ciki ya ce idan Allah ya yarda nan da kwan uku suna iya dawowa su kai masa godiya ya ce, Ai babu komai ya rako su har kofar gida gurin motarsu ya nayi musu fatan alkhairi da addu'ar sauka lafiya.- Suna karayin musabaha, Bintu ita da dan Auta Aliyu suka dawo daga Tahfiz, suka durkusa har kasa suna gaishe su, suka amsa cikin fara'a gami da jin dadin yadda aka karramasu. Alhaji Yakubu ya fito da kuɗi a aljihunsa har sun mike ya kira su, suka farasa gabansa sosai suka kuma durkosawa ya mifa musu sababbin ‘yan dubu dubun da 127 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya kirgo guda goma ya mika musu yaran tamkar ashim film suka wani zabura a tare gami da mikewa har suna hada baki gurin cewar A'a mun gude su kai hanyar shiga gida Alhaji Yakubu ya juyo da kallansa ga Malam Usman ya ce, "Haba Alhaji ya za kai min haka yanzu ba zaka sa baki su karɓa ba, ni fa na niya ba wai rokona su ka yi ba, cewa nake ka karanta babu mai mai da hannun kyauta sai shadani, hakan yana da kyau hana yaro amsar Abubuwa a hannun mutane. Amma fa idan bai san su ba in dai mutum ya san yaro ka ba shi abu bai karɓa ba, sai ka ji babu dadi duk da yake karбar ma ko da yaron ya san yanda ya ba shi to hakan ma koyan kwadayi ne, cewa nake a iya zaman da mu ka dan yi yanzu da kai ka yarda damu din masoyanka ne, tunda har muna son hada zuri'a da kai nan ba da dadewa ba, insha Allahu, ai ina ganin mun zama daya ko ba haka banc.?" 128 IZGILI JAMILA MUHAMMED Malan Usman ya cc, "Hakkun amman ina ganin Alhaji kudin nan sun yi yawa." Alhaji Yakubu ya ce "Ba wani yawa da su ka yi in dai ka dauke mu da zuciya daya, kuma 'yan uwa ka ɗaukcmu." Malam Usuman ya cc, "Wallahi da zuciya daya na dauke ku. " Alhaji Yakubu ya ce, "To In dai haka ne to ka sa su su karɓa tun da ni ma babansu ne. 99 Malam Usman ya yi murmushi kawai ya juya zuwa soran gidan inda yai kiransu ya dawo gurin su Alhajin yana karayi musu godiya su kuma suka ce babu komai sune da godiya. Bintu ita da Aliyu suka durkusa suka ce, "Abbu gamu ya nuna su Alhaji ya ce, "Alhaji ne yake kiranku.' Suka karasa gurinsu ya mika musu kudin ya ce, "Abbunku ya ce, ku karɓa.' " 129 IZGILI JAMILA MUHAMMED Suka juyo suna kallon Abbun nasu. Malam Usnam ya ce, "Ku yi musu godiya." Ai fa yara suka dinga zararo godiya sai da Alhaji Mansir ya ce, "ya isa ku je gida ku sayi Buskit.' " Suka ta shi cikin nutsuwa suka shige gida babu wata harguwa irinta sauran yara, komai cikin nutsuwa suke yinsa nan dai suka sake sallama sannan suka ja motar suka tafi, da alkawarin za su dawo nan da kwana ukun. ****** Da daddare bayan sun gama cin tuwon dare sun baje suna shan iska suna kuma hira Malam Usman yai gyaran murya ya ce, "Lafiya baki tambaye ni in da dan autanki ya samu kudi ba.?" Inna ta yi dariya ta ce, "Malam ke nan ai tunda Hadiya ta bani kudin ta ce su Binta ne suka cc ka yi baki shi ne bakin suka basu 130 JAMILA MUHAMMED na san za kai min bayani, idan ka mustu to gajen hakurin na me ye, da zan tambayeka." Malam Usman ya yi dariya ya cc, “Ai daman tsokanarki na yi ni da na san halinki na rashin bindiddigi da san jin kwakwaf ai gaba daya suka saki dariya har da Bintu da take kwance barci ya fara di banta. Hadiya ta ce, zuciyarta gaskiya ina san iyayena akwai su da barkwanci sai ta samu kanta da addu'ar Allah ya bata miji na gari wanda zai dinga sata farin ciki ita da ‘ya'yania da zata haifa masa, sai kuma ta ji wata matsananciyar kunya ta kamata sai iske ganin iyayen nata tamkar sun ji a binda ta ce sai tai saurin zamewa ia kwanta ta juya baya ma'ana ta kalli bango can ta ji Abbun masu ya yiwa Innarsu bayanin mutanen da guka zo sai jadda kirkinsu yake idan dai ba kunnanta ne ya jiye mata ba dai-dai ba Pamarta so ta ji Abbun yana facin iyayen 131 IZGILI JAMILA MUHAMMED mai son tane suka zo tambayar idan ba a tsayar mata da miji ba. Ta sake ware kunnenta tana saurarensu aikuwa kunnanta ya jiye mata daidai haka ne yo waye wannan ai ina yake a ina ya ganta haka ta dinga yiwa kanta tambayoyin da bata da amsoshinsu tana jin Innar na fadawa Abbunta bata da wani wanda take so, saboda bai bata damar kula samari ba, ta ce, idan dai ka amince musu andaika kawai ka basu dama yaran ya zo su gana idan sun dai-daita shi ke nan idan kuma basu dai-daita ba to sai mu ce Allah ya hada kowa da rabonsa." 99. Malam ya ce, "Haka za a yi dan aminta gaskiya na aminta da su zan kuma yi musu bayanin nan dai suka shiga wata hirar ita kuwa ko da ta zo kwanciya kasa barci ta yi, tana ta tunane tunanen ta tana san sanin to shi din a ina ya santa da har zai aiko wakilansa, gidansu to ko kuma ya sayyadi 132 IZGILI JAMILA MUHAMMED Hafiz ne, wato malamin makarantar su ta Islamiya ne daman yan ajinsu suna yawan gaya mata ya Sayyadi Hafiz sonta yake in dai ya shigo ajinsu komai ya sa ko ta a cikin maganarsa da ya shafe ta, abu da bai shafeta ba sai ya sata a ciki kuma suna yawan faɗa mata ko kallan da yake mata ba irin wanda yake musu bane, kuma in dai tana guri fara'arsa tafi yawa, duk da dai shi din mai fara'a ne sai ta ji wani dadi marar musaltuwa yana ratsa ta, tai wani juyi ta rungumo filonta cikin zuciyarta. In dai kuwa shi ne ba karamin morewa da miji ta yi ba, dan kyakkyawa ne mai tsafta gami da fara'ar da take kara masa kyau, haka ta dawo daga tunane tunanenta har dai daga karshe barci ya dauketa ciki dama farkai farkai tai.' " Zaune yake cikin kasaitaccen falon nasa tamkar fadar sarauniya, sanye yake da 133 ; IZGILI JAMILA MUHAMMED short nicker fari tas, da singilet ya ɗoro farar kyakkyawa kafarsa kan dan karamin table din glass din da yake gabansa falo yana fitar da wani sassanyan room freshner tar da sanyin Air Condition sai ya bada wani irin sanyin dadi mai ratsa zuciya yatsurawa tangamemiyar TB din ido ire-iren film din fitsarar da ya saba gani yan zun ma su yake kallo gefe daya kuma tabarsa yake busawa cike da kwarcwa ya yi nisa cikin kallon nasa ya ji Enter comm dinsa tana kadawa ya dan saki tsaki gami da share mai Knocking din, koma waye ya gaji yai daina. Ya kara jan wani dogon tsaki anya kuwa mai Knocking mayu ba, ya kallo agogon nan bai dake hada a iri can da kusurwar falon ya ce, "Idan ban da rashin zuciya da kuma naci, mutum yai minti ashiri da biyar yana buga kofa anki zuwa a bude ba sai ka tafi ba, tunda ba a maraba da kai aikuwa mai buga kofar babu alamar zai 134 IZGILI JAMILA MUHAMMED barshi yai kallon nan yai kiran sabuwar buduwarsa Lindy da take gyara masa daki da sauri ta fito bai ko kalli inda take ba, yai mata nuni da kofa ta san abindą yake nufi ta bude ta bude kofar wata kedara ce irin ta sanye da wata 'yar bingilar riga da wani ta dada ɓaбɓake kofar sanan cikin turanci dogon takalmi. Kudurat ce tsohuwar budurwasa Linda take magana ba gami da wani kyaɓe tana mata wani kallon hadarin ka ji, ta ce, "Wa ki ke nema kuma gurin wa ki ka zo.?" Kudurat ta fusata daman ta san yana tare da wata tunda tai kusan minti talatin tsaye tana bugu duk da dai daman wulakanci gami da IZGILANCI halinsa ne ko shi kaɗai ne ma yanai mata wadda tafi haka da shi ne ya bude ba zata ji haushi ba amma tunda wannan shegiyar ce to kuwa in dai ta kawo mata rainin hankali zata ci ubanta. 135 大 IZGILL JAMILA MUHAM Kudurat ta galla mata watan harara ta ce, "Ke har kin isa ki tambaye ni gurin wanda na zo, to bara ki ji ko uban ki ne mai gadin gidan nan bai isa ya yi min wannan tambayar ba." Lindy bata bari ta sauke numfashi ba ta yarfeta da mari, Ai sai kokawa ta harke sai ga su cikin falon suna dam batawa yai saurin mikewa tsayo ya daka musu wata matsiyaciyar tsawa ya cc, "Good dambe agidana to yau zaku ci ubanku.!! Kashi masu karatu ku biyo ni a littafi na biyu dan jin yanda zata kasanc taku mai kaunarku. 136 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels