sashen. A hankali na tura k’ofar na shiga. Shiru babban parlorn nasa baka jin k’arar komai sai na A.c da take ta aiki ba ji ba gani. Fitulun wajen ma a kashe suke. Karatun k’ur’ani ne kawai yake tashi a parlourn cikin k’ira’ar shureim. Na gama zagaye parlorn da idona ban gan shi ba, don haka na isa k’ofa guda da take parlorn da na tabbatar nan ne d’akin nasa.
Yana zaune a gefen gadon daga k’asa saman sallaya ya kifa kansa a jikin gadon. Jin motsina ya saka shi d’aga kai. Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin yarda idanunsa suka ka’da suka yi jawur kamar gaurashi. Idan ba idanu na ne suka min gizo ba sai naga kamar hawaye ne a kwance a k’asan idanun. Mayar da idonsa ya yi ya lumshe bai sake kallona ba alamu sun nuna baya son gani na.
Zuciyata a jagule tana wani irin bugu da k’arfin gaske na k’arasa wajensa. Zama na yi a gefen gadon murya cike da rauni na furta “Ustazuna, wata takarda na gani a cikin kayan da ka kawo, zuciyata ta kasa amincewa hannunka ne ya rubuta ta. Ban kuma fahimceka ba.”
Shiru kamar ba zai amsa ba, idanun dai still a lumshe daga inda nake ina ganin yarda k’irjinsa yake bugu. “Ustaz, magana fa nake.” “Taki ce.” Ya fa’da muryarsa a shak’e. Ido na waro ina furta “Saki Ustaz!” Ya bu’de idon nasa ya nutsasu cikin nawa, a hankali ya d’aga lab’b’ansa kamar baya so ya furta “K’warai kuwa AYSHA, don haka ki tabbata kin fice kin daga gida k’arfe bakwai na safe….”
Ina daga zaunen na dinga jin wani irin jiri yana d’ibana. “Ko zan san dalili?” Wannan karan madadin amsa min mik’ewa ya yi yana zabga tsaki ya furta “Ban sani ba…” Shiru na yi na lumshe idona ina hak’ilo da yak’i da b’acin ran da yake son dannen numfashi. “Tashi ki fita zan rufe k’ofata..” Ya furta yana nuna min k’ofa.. Ya fa’da yana juya min baya… Jikina a salub’e na mik’e ina jin kamar k’afarta wa ba Zata iya d’aukata ba saboda rawar da jikina yake yi na zallar tashin hankali. Da k’yar na ja jiki na isa bak’in k’ofar daidai lokacin da na jiyo ina kallon Ustaz ina cije leb’ena shima kallon nawa yake hawaye ba zuba daga idonsa. Na ja k’ofar da k’arfin gaske na fice daga d’akin.
Zuciyata har Tafasa take saboda tsananin b’acin rai. Na zauna a gefen gadona ina mayar da numfashi tabbas Uztaz ya cuceni a shekaruna sha takwas kacal ya mayar da ni k’aramar bazawara? Shin halaccin da zai yiwa Iyayena kenan? Tabbas ya amsa sunansa Butulu? Yanzu me Zan je na ce a gidan mu? Ya rasa irin sakin da zai yi min sai irin wannan na tozarci da wulak’anci saki a ranar aurenka daren amarcinka? Yaya mutane za su yiwa abin fassara? Dole ne a jefa min ayar tambaya musamman kowa da ya san Ustaz ya san Babban Malami na da ake watsa tafseer d’insa a gidajen sunna na t.v. Babban Malami ne da gwamnatin k’asa baki d’aya take ji da shi duk da dai ba wani shekaru ne da shi ba ba zai wuce shekaru 32 ba.
Toilet na shiga bayan da zuciyata ta tabbatar min ba ni da wanda zan fuskanta a wannan gab’ar sai Ubangiji. Don haka na yi alwala na fito na tada sallah akan daddumar da Abba ya bani d’azu da safe ita da Alk’ur’ani da Riga da Hijab na sallah farare tas har da carbi da wani turare mai k’amshin gaske, yana furta “AYSHA, kin ga wa’dannan sune garkuwarki a gidan miji idan kika rik’esu kin samu makamin k’are dangi.” Ina sallahr ina hawaye na kaiwa Allah kuka na, na bayyana masa rauni na na kuma rok’eshi ya shige min gaba a dukkan lamari na.”
Ban tashi daga sallaya ba sai k’arfe uku da naji kaina ya fara ciwo abin mamaki sai na ji na samu k’arfi da nutsuwar zuciya. Na ji komai ya faru gareni daga Allah yake duk da tabbas Ustaz ya cuceni. Abu guda nafi buk’ata a yanzu na ji dalilin sakin da ya yi min, sai dai na yi alk’awarin ni da kai na ba zan sake tambayarsa ba don ko don ganinsa bana yi.
Barci ne sosai ya d’auke ni, kasancewar garin sanyi ne dare yana tsawaita don haka sallar asuba sa daf da k’arfe shidda ake yi, shi yasa na samu barci sosai duk da ba wai zance na yi isashshe ba ne. Ina sallame sallahr ko kayan sallar ban cire ba na fice da su da sauri a jikina.
Shiru layin amma a haka na dinga tattaki har na je bakin titi. Allah kuma ya taimakeni na samu adaidaita sahu. “Shara’da phase 2 kawai nace masa.
Har k’ofar gidanmu ya ajiye ni ta hanyar kwatance da na masa.
Duk da a tsorace nake da ganin Abbana hakan bai hana ni shiga gidan da k’warin gwiwata ba. Y’an biki ko watsewa ba su yi ba, don wasu daga garuruwa daban daban suka zo. Sai dai gidan shiru da alama kowa gajiyar biki ta saka ana sallah an kwanta sai wa’danda suke aiki a bayan gidan ta can na dinga jin d’an hayaniya da sautin kwanuka na tashi.
Jama’ar da suke kwance a
Parlor wa’danda duk k’annen Mami na ne da na Umma na suka dinga bi na da kallon mamaki baki a sake. Anty Sharifa ta ce “Ke AYSHA lafiya?” Mami da fitowarta daga d’akinta kenan itama hangame bakin ta yi tana ware ido ta furta “Ni Fa’dima me Zan gani haka? Ke Aysha Uban me ya fito da ke da sassafe haka?” Ta fa’da tana jan hannuna hankali a tashe ta furta “Ai dama sai da na gayawa Abbanku kin yi k’ank’anta da aure, shekara sha bakwai don ko sha takwas d’in baki cika ba, yanzu haka wani bak’on al’amari kika gani da yafi k’arfinki yasa kika gudo?” Anty Sharifa k’anwar Umma ta ce “Ah haba! Sai kace ba y’ar yanzu ba, ai duk da take k’anwar Maza na san ta san me aure ya k’unsa ko da ta hanyar k’awaye da karance karancen littafine…” Mami ta d’an harareta “Me AYSHA ta sani? Karatun littafin take ita? Ko k’awayen arziki AYSHA bata da su balle su sanar da ita aure da abinda ya k’unsa…” Ta fa’da tana jan hannuna muka shige Uwar d’akinta.
Zaunar da ni ta yi a bakin gado, bayan ta koma ta rufe d’akin da key tana furta “Bana son saka ido da munafunci yanzu duk ido zai dawo kan ki, kema kin yi wauta Aysha. Me ya kai ki fitowa don kawai Mijinki ya kusanceki Ai shine auren muma duk haka ake mana da haka kuma kowa yake sabawa… kowace macen aure da kika gani haka ne yake faruwa da ita koda yaushe, don haka tun kafin sauran mutane da Ubanki su ji ki tashi maza naje na mayar da ke, bana son na ji komai wannan sirrinki ne ke da Mijinki. Maza tashi mu tafi kafin mutane su fara miki kallon mara wayo mai gudun
Miji.”
Hawaye ne suka fara zuba min, ganin ita Mami na inda take hange daban da abinda ya kawo ni gidan. Na turo bakina ina furta “Ni fa ba wannan bane, ko hannu bai rik’e min ba fa.”
Mami ta d’an bu’de idonta ta furta “To menene idan ba wannan ba?” “Ya sake ni…” Wani irin ja da baya Mami ta yi idonta a waje tana kallona baki a bu’de ta shiga shock sosai cikin wani irin yanayi ta furta “What? Ya sake ki Aysha? Shi Ahmad d’in ne ya sake ki? A kwana guda da kika yi a gidansa to Uban me kika masa?” Hawaye ne suka fara ambaliya a fuskata na gayawa Mami duk abinda ya faru ban b’oye mata komai ba. Dariya Mami ta yi tana furta “Sharrin D’a Namiji! Ga abinda nake gudu ya zo. Sai ki tashi mu je wajen Abbanki na bashi tukuicin alheri da Ahmad ya kawo masa, ya mayar masa da y’a k’aramar bazawara Ahmad dai mai nagartattun halayen da Ubanki yake faman b’ab’atu akai.” Ido na waro waje ganin tana ja hannuna “Tashi mu je mana.” Na ja hannun ina girgiza kai “Mami, ba zan iya zuwa wajen Abba ba, Allah ina tsoro, ban san yarda zai d’au lamarin ba.” Wani kallo ta min cikin b’acin rai ta furta “Tashi na ce miki mu je ko? Iyakacinsa dai dake fa’da, tunda ba zai iya zare miki ranki ba.” Ta fa’da a fusace ta kuma fincikeni muka fita wajen.
Abin haushi Jama’a an fito gaba d’aya kowa sai baza ido yake ana kallon mu. Kallo guda Mami ta musu suka dinga bajewa suna ba mu hanya. Ban yi mamaki ba don ni da kai na na san an samu topic.
Abba na zaune yana lazimin safiya. Umma ce a gefensa tana ha’da masa coffee da ya saba sha duk safiya. Da alama shi bai san abinda ya faru ba. Balle Umma da tun jiyan bata fita daga sashensa ba.
A razane duk suka zuba mana idonsu musamman Umma da har Cokalin hannunta yake fa’duwa. “FATIMA lafiya kuwa? Naga Aysha da sassafe.” Umma ta fa’da tashin hankalinta na sake bayyana a saman fuskarta.
Zama Mami ta yi a gefen Kujerar da yake kusa da Abba, ta saka ni a gefenta ta furta “Lafiyar kenan Umma, sai dai d’an gaban goshin naku ya muku Aiken tukuicin sakamakon alherin da kuka masa…”
Abba da yake laziminsa ya d’ago ya d’an zubawa Mami ido don ya san halin kayarsa sarai danger ce wutar baya. Umma kuwa cup d’in ta ajiye tana sake furta “Me ya faru to? amma fa Mammin Aysha ya kamata ki yiwa y’ar taki fa’da ta san fa ta girma, aure kuma ba wasan yara ba ne. Idan ban da shashashanci menene na dako wannan Uban sammakon, koma menene ba ga waya ba me yasa ba zata sanar miki ba? Sai ta d’ebo jiki ta taho ta saka y’an biki su tafi da ita a bakin duniya tunda ko gama watsewa ba su yi ba. Aa sam wannan wauta ce da shirme.” Mami wani kallo ta mata sai kuma ta cije baki.
“Kamawa ta yi, ta dako uban sammakon babu gaira ba dalili ba abinda zai sakata fitowa daga gidan Mijin da aka kai ta jiya.” Mami ta fa’da tana hura hanci da jijjiga k’afa. Umma dai shiru ta yi don ba mamaki ta lura idan ta cigaba da magana tata ce zata yi zafi.
Abbana yana jin su bai yi magana ba ya cigaba da laziminsa. Sai da ya idar sannan ya ‘d’au coffee d’insa ya shanye ya zuba min kallon da na kusan jin kayan cikina suna shirin fitowa. “Ke wace irin shashasha ce Aysha? Daga kai ki gidan Miji jiya yau ki fito? Kin d’auka auren wasa ne? Me ya fito da ke?”
Madadin amsa masa jiki na ne ya dinga rawa kamar yarda zuciyata take bugawa. “Ba magana nake miki ba?” Ya sake fa’da da Tsawar gaske, hakan da yasa har ban san sanda na rik’e Mami da kyau ba ina makyarkyata “A’a Alhaji, kada ka sake hargitsata Ai ba laifinta ba ne fitowar dole ne ta fito tunda ya saketa…..” Gaba d’aya bakinsu a ha’de suka furta “Saki Fatima?” Ta jijjiga kai tana murmushi ha’de da furta “Sakamakon halaccin da kuka masa ne, duk duniya kuna ganin ba wanda ya cancanta kamar Ustaz Ahmad. Kullum zancenku nagartaccen mutum ne mai ilimin addini da ya shahara a duniyar Malamai. Yau ga ilimin nasa nan ya fara nuna muku….” D’akin tsit ya yi Abba jikinsa har rawa yake. Umma kuwa zama ta yi jab’ar a k’asa ta rik’e kanta kawai jikinta na rawa….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 4..
Da mamaki Umma take kallonta su Yaya Muhammad suma suka zuba mata ido. Ya Usman da ya kasa shiru ya ce “Au ke kuma auren ne ba kya son ta yi? Shi yasa zata ke k’unshe fuskarta, amma kamar wannan ba dabara ba ce..” Harara ta watsa masa tana furta “To kanari Uban surutu, ni na ce maka bana son ta yi aure? Auren ne dai ba yanzu zata yi shi ba sai ta yi dogon karatun da na tabbatar zata iya k’watar y’ancin kanta a
Wajen namiji sannan zan amince ta yi aure, haka kawai ba za’a aurar da ita da duhun kai ba shikkenan ta zama sai kace baiwa wajen namiji…” Cikin mamaki suka zuba mata ido, Umma kanta ta yi mamakin furucin Mamin, sai dai data tuna Mamin gidansu gangariyar y’an boko ne sai bata yi mamaki ba ta saki ajiyar zuciya kawai tana furta “Allah ya taimaka, ya nuna mana lokacin…” Yaya Muhammad gyara zama ya yi yana tab’e baki ya furta “Amma dai wannan kamar ba shawara ba ce mai b’illewa, Saboda kowa yanzu burinsa a ce y’arsa ta yi aure sai ta yi karatun a nata gidan Mijin….” “Sai ka bari sai ka haifi taka y’ar Muhammad ba wannan ba…” ta fa’da a zafafe tana nuna ni. Ta ja hannuna muka wuce samanta.
Tana banbamin fa’da har da rantsuwar nan gaba idan Muhammad bai yi wasa ba sai ta mare shi.
A kashegarin ranar kuwa bayan na yi wanka Mami ta tsantsara min kwalliya cikin shigar kayan hausawa da suka min matuk’ar kyau. Murna na dinga yi don kam dama ina son su Mamin ce bata ba ni damar sakawa ba.
Sanda na fita tsakargida idanun masu aiki duk a kaina suke, sunan ta dariya ganin kwalliyar da aka min. Har Iya ta kasa shiru ta ce “Lallai Aishatun Mami ta girma… Ma sha Allah a yi shekaru irin na dabino.”
Abba da yake zaune daga can gefe shi da su Yaya Muhd, baki sake ya dinga kallona yana furta “Inye Aishatun ba, irin wannan
Kwalliya haka? Waye ya siyo
Miki kayan hausawa…” ina dariya na zauna daf da shi an furta “‘Mami na ce, ita ta siyo min su da yawa ta ce na daina saka wa’dancan kayan yahudun.” Jan hancina Abba ya yi ya ce “Ai ke ce Yahudun.” Sannan ya juya yana kallon su Ya. Muhd ya furta “Kun ga abinda na gaya muku ko? Na gaya muku kada ku tada hankalinku a kan yarinyar nan Fatima ba zata yi sanadin gurb’acewar tarbiyyarta ba..Fateema mace ce data san abinda take yi.” Shiru su ka yi suna cigaba da shan kununsu Ya Ali ne ya furta “Ba shakka, to Allah yasa dai ba da wata manu…” wani kallo naga Umma ta masa sai ya ja bakinsa ya tsuke yana dariya.
Tun daga ranar ya zama na saba saka kayan hausawa, kuma ko aike na waje za’a yi Mami na bata bari na fita ba nik’ab har hakan ya zame min
Jiki. Sai dai a fuskar Umma
Wani lokacin ina kallon yanayinta kamar hakan baya mata da’di, sai dai ba yarda zata yi ne. Duk inda na je kuwa sha’awar shigata ake, don kowa ya ganni ya san d’iyar wacece? D’iyar mace mai mutunci wacce ta san ciwon kanta, kuma yake bawa y’arta tarbiyya, ba wacce da kanta take saka y’a’yanta shigar banza ba don kawai su kawo mata mazan aure ta dinga kuma zuga su da fa’din sun yi kyau.
Sanda na fara period kuwa, Mami hana aikena ta yi. Saboda wani irin kyau da na dinga zubawa, mak’erin y’an mata na ji suna cewa ya fara k’era ni. Don haka ta shiga taka tsantsan da ni. Idan Ya. Muhd ya yi magana ta hau masa masifa don haka ya gani ya zuba mata ido kamar yarda kowa ya yi.
Sanda maganar aurensu ta bujiro da y’ay’an abokin Abba Mami na jin iya secondary kawai suka gama. Ta dinga tab’e baki tana fa’din “Amma Sadik kun yi bak’ar dabara, yanzu meye riba a auren k’wailayen mata?” Ya Muhd don takaici kasa mata magana ya yi, Ya. SADIK MURMUSHI ya saki yana furta “Ai auren irinsu Mami ya fi riba, ko bakomai zasu bi duk wani tsari da aka shar’anta musu..” Ta ja tsaki ta furta “Mugunta zaku musu ba, ai shikkenan shi yasa duk bala’i ba zan yarda AYSHA ta yi aure daga gama secondary ba dole ko degree sai ta yi, idan ma bata yi masters ba…” Ya Muhd da yake tsaye ya tura hular sa goshi yana furta “A dai rage dogon buri, idan yarinya ta yi girma da yawa yanzu mazan ma gudun aurenta suke, don sun san tafi k’arfinsu…” Yana ji ta k’unduma wani zagi ya shige d’akinsu yana dariya.
Haka kuwa aka yi, bayan wani lokaci aka gudanar da bikin Ya. Muhd da Ya sadik. Muhd da Khadija, Yaya Sadik kuma da Nafisa a lokacin ina Js 3. Amma duk wata cika ta matantaka ta bayyana a surar jiki na.
★★★✍️
Ina SS 2… al’amarin ya faru. Mun taso daga Islamiyya ni da k’awata Asma’u, muna tafe muna hira a hankali cikin nutsuwa. Ranar ganin ba kowa a layin sai na ‘dage hijabi na. Asma’u ta kalleni da mamaki ta ce “Yau kuma Aysha? Lallai kina son idan Mami ta ji labari har ni ta ha’da ta ci mutunci na kenan?” Tab’e baki na yi, ina yamutsa na fuska na ce “Ai layin ba kowa….kuma ma waye bai sanni a layin nan ba?” Cigaba ta yi da bani labarin wani series da ake yi a Mbc bollywood wanda na yi missing ban kalla ba, sabida girki da Mami ta saka ni a daidai lokacin.
Murmushi kawai nake saki… Zuciyata ce ta wani irin bugawa daidai lokacin da muka ha’da ido da shi yana tsaye a gefen wani gida da ake gini ba’a k’arasa ba…” Da sauri na ja nik’ab d’ina na mayar ina jin yarda sautin bugun zuciyatta ya tsananta. Tabbas na san fuskarsa a sunna t.v matashin Malamine da yake tafseer a duk azimi. Ba wanda bai san Ustaz Ahmad ba. Saboda yarda yake d’an gayu komansa mai kyau ne yana kuma ji da tashen Naira. Asma’u ta furta k’asa k’asa “Ke AYSHA kamar Dr. Ahmad sulaiman ko?” Ban amsa mata ba, k’irjina dai ya cigaba da bugu. Sam zuciyata kasa cigaba ta yi da saurarar labarin da Asma take bani saboda wani yanayi da na fa’da mai girman gaske..
Tabbas tunda nake ban tab’a ganin mutumin da jallabiyya ta yiwa kyau kamar wannan mutumin ba. Ga wani azababben k’amshin turarensa da ya maye wajen gaba d’aya. A kallon da na masa sai naga ashe har ya fi kyau a fili. Yana da haske sai dai ba sosai ba. Idanunsa farare tas kuma mayalwata. Cikakkiyar gira ce da shi da gashin ido kamar yarda gashin kansa yake cikakke kuma bak’i si’dik. Duka wannan na gani ne a guntun kallon da na masa.
Asma tana shiga gida nima na fa’da gidanmu da sauri tunda mak’ota muke da su. Shi kuma Ustaz gidan da yazo gidan yana kallon gidanmu.
Ban bari kowa ya ji shigowata ba na haye sama da sauri na shiga d’akina. Haka kawai nake don sake ganinsa don na san windown d’akina yana kallon gidan da yazo. Ina d’aga labulan kuwa na hango shi yana tsaye still suna magana da Lawal da ya kasance d’an mak’otan mu. Idanunsa na ga ya juyo yana kallon gidan mu kamar mai nazarin wani abu… Daidai lokacin Mami ta shigo tana k’wala min kira. Da sauri na saki labulan windown alamar rashin gaskiya bayyane k’uru k’uru a cikin idanuna. Ba ta yi min magana ba sai takowa da ta yi zuwa gaban windown ta d’aga labulan tana furta “Uban me kike kallo anan d’in?” Idanunta ya sauka akan Ustaz da sauri ta juyo tana kallona baki sake ta furta “Namiji kike kallo Aysha? To Uban me ya ha’da ki da shi?”
Hantar cikina ta ka’da… bakina na rawa na furta “Babu komai Mami….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
Wancan group d’in ya cika Wanda Bai samu Shiga group 1 ba ya Shiga 2. Amma don Allah idan kana group 1 kada ka Shiga 2 don duk Abu d’aya ne.
A shiga group, ba Zan juri posting a kowane group ba, ba kuma Zan juri a dinga cewa Na tura daga farko ta private ba. Hankalinka kwance ka shiga group kawai. Nagode[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 5.
Mami ta zabga tsaki tana sakin labulan tana kallo na ta furta “Idan ma shi kike kallon, ki tsaya ki saurareni da kyau.” Ta fa’da tana jan kunnena “Koda wasa kada ki sake ki saka wani namiji a ranki, a yanzu dai kam don ko me zai faru ba zan bari a aurar da ke ba, sai na cika burina na kin zama wani abu a fannin ilimin boko.” D’aga kai na na yi, ina lumshe idona. Ta fice da sauri ina jin b’acin rai ma ya mantar da ita abinda ya kawo ta.
Bu’de idona na yi a hankali ina sakin ajiyar zuciya. Ba tare da damuwa ba na sake yaye labulan d’akin. Daidai lokacin da Ustaz ya d’ago yana sake kallon gidan mu, ban damu ba na tsaya na kalleshi sosai don na san ba zai ganni ba, glass d’in yana da duhu daga waje ba’a ganin wanda yake ciki.
Na saki ajiyar zuciya ina kallon sanda ya shiga motar sa yana sake bawa Lawal hannu suka yi misabiha. Ya ja motar ya bar wajen. “Allah ya yi halitta…” Na furta a hankali ina kai wa saman gado na zauna. Har a lokacin yanayin bugun zuciyata bai koma daidai ba.
Shikkenan na samu abin yi tun daga ranar da na gan shi, ban sake komawa daidai ba. Kullum cikin tunaninsa nake da burin sake ganinsa koda sau ‘d’aya ne a rayuwata.
Ranar da sati ya zagayo ranar wata lahadi still mun dawo Islamiyya da Asma’u kamar wancan lokacin. Asma ce take ta surutunta ni kuwa bakina shiru, don wani irin yanayi nake ji a zuciyata ga bugun zuciyartawa ya sauya. Muna doso layinmu na ji mayataccen k’amshin turarensa wanda ba zan tab’a mantawa ba. Da sauri na sauke Nik’ab d’in don kuwa na tabbatar shine duk da bayansa kawai na gani still sanye yake da jallabiya mai kyau brown kansa da hula tashi ka fiya nace mai tsadar. Muna doso ta inda suke zamu wuce don dole sai ta nan d’in na ji k’afafuna sun fara rawa kamar ba zasu d’aukeni ba. Duk da nik’ab ne a idanuna na ga ya ‘dago yana kallon inda muke sai kuma suka yi shiru da hirar da suke. Da k’yar na saita kaina na nutsu muka shige su. Sai da na shiga gate d’in gidanmu sannan na saki ajiyar zuciya a hankali ina furta “Ya rabbi! Me ke faruwa da ni ne?”
Bayan kwana biyu ina zaune a ajin mu ja Islamiyya. Aka aiko kirana. A matsayin da nake kai na shugabar makaranta na san ba wani abu bane don an aiko kirana d’in, amma wannan karan sai na ji zuciyata ta buga sosai. Ido na tsurawa mai kiran nawa. Har ya ji haushi ya furta “AYSHA magana fa nake.” Da sauri na amsa da “To gani nan.”
A Office d’in Headmaster na tsaya ina knocking a hankali. Muryar Malam d’in na ji yana furta “Bismillah Ayshatu…” Na yi sallama na shiga, k’amshin turarensa ya doso hancina har ban san sanda na ware ido ganin Ustaz a zaune ba idonsa akan wani littafi da ke hannunsa. Wallahi Allah ne ya yi ba zan fa’di ba, Saboda zallar rashin nutsuwa. Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da yatsuna. Har Malam ya gama rubutunsa ya d’ago yana kallona “Gaisuwa fa Ayshatu?” Da sauri na juya na kalli Ustaz da ya yi kamar bai san da ni ba a wajen. “Ina yini?” Bai d’ago ba na ji dai ya masa murya a k’asa “Lafiya..” D’an tab’e bakina na yi duk da na ji haushinsa, na mayar da hankalina kan Malam. “Ki je maza ki sanar da duk ajujuwa akwai assembly idan an idar da sallah..” Na amsa da sauri don burina fita daga office d’in kafin halin da nake ciki ya bayyana…”
Haka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12