Abba gashi wai a dole sai ya Aurar da ita sai bi yake ya na tallanta. "Yanzu ba karatu nake ba ai Zaman Zawarci na ke yi. "Bab.. ban..gane ba Zawarci kuma? tsokanata ki ke yi?" murmushin takaici ta yi kafin ta ce "Ba Zolaya bace ita ce gaskiyar ni ban iya ɓoye-ɓoye ba gwara kasan wadda ka Aura, in har za ka iya ka so ni don Allah ba don wani abu ba, amma ni Bazawara ce." gyara zama ya yi gami da sauke gwauron numfashi kafin ya kalleta ya ce "Ki na da Ƴaƴa ne??" "Ba ni da ko ɗaya. "To ki sanar min abin da ya sa ku ka rabu ke da Mijin naki. shiru ta yi ta na tunani kafin ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya ba." tsaki ya zabga ya gyara zaman Hularsa ya tunkuɗota gaba sannan ya fara magana "Ai in na Aureki na ƙi cin Biri na ci Dila kenan, Matata Ma ta fiki Yarinta don dai kawai Ƙazama ce shi yasa na ke son ƙara Aure, amma da in Auri Bazawara ai gwara in zauna da Ƙazamar Matata har zuwa lokacin da zan samu Budurwa, wa ya san ma irin abin da ki ka yi Wancan ɗin ya sakeki? ai duk wanda ya ɗebarwa kansa Bazawara ya ɗebowa kansa aiki, me za ka samu a Kale in banda takaici, ni ba zan iya Auren sauran wani ba, ki gayawa Abbanki in zai sa ayi tallarki a dinga gayawa Mutane gaskiya, don a zamanin nan ko anzo dole a tafi don ba me yarda ya Auri Bazawara." ya na kaiwa nan ya miƙe ya kakkaɓe tijararriyar rigarsa ya yi hanyar fita.
Aaminat kuwa tin da ya fara hawaye su ka shiga tsere akan fuskarta, tashi ta yi ta shiga Gidan da gudu, a hanya su ka yi tawo mu gama da Umar, ya daka mata tsawa da cewa "Kehh!!!!! menene hakan ko ciwon hauka ya kamaka ki ne??" Kukan da ya ke cin ƙarfinta ne ya samu damar fitowa, cikin shashshekar kuka ta fara cewa "Kowa sai ya ce ba zai Auri Bazawara ba sai ka ce ita ta tsarawa kanta Ƙaddara?, idan ba su Aure mu ba a haka za mu Mutu cikin fuskantar ƙasƙanci da wulaƙanci kenan??, nima fa ban sani ba Ya Umar ban san Kamal zai yi min haka ba, Ban sani ba wallahi, kowa ya tsaneni har iyayena da ƴan Uwana, wallahi Tallahi ba ni da laifi, don son raina ba zan taɓa zaɓar irin wannan Rayuwar ba, Abba ya kawo min Mutane da yawa amma sai su ce ba za su Auri Bazawara ba."
Kukanta ne ya ƙara ƙarfi ta toshe bakinta da gefen Gyalenta sannan ta kutsa kai cikin gida. "Aamina!!! Aaamina!!!" Ya Umar ya shiga watsa mata kira
Bata tsaya ba taci gaba da tafiya, ta na shiga ta yi gamon katari da su Abba Umma Mama da sauran Yaran curko curko a tsakar gida don kuwa sun ji muryarta lokacim da ta ke yiwa Umar Magana. Mama ta ce "An yi abin da aka iya ko?"
ganin kowa ya tsirata da ido ya sa ta yi saranda ta kasa wucewa, Abba ya ce "Kukan me ki ke wa mutane?" "Abba shima cewa ya yi ba zai Auri Bazawara ba" Abba ya doka tsaki kafin ya ce "Ai tinda ba ƙaunar Auren nan ki ke ba sai ki zauna, ga ki ga gidan nan, kullum aikinki kenan ki ce sun ce ba za su Aureki ba idan kuma na tambayesu sai su ce Ƙarya ki ka yi musu, ai ga gida ga ɗaki sai kita zam." Umma ta ce "Allah i kyauta". daga haka ta bankaɗa labule ta shige ɗaki, Mama ta riƙe haɓa gami da cewa "Lallai Makircin yarinyar nan ya ƙara girma, ga yadda ta shigo da kuka kamar wadda ya sokawa wuƙa a Zuci??" Goge hawayen ta shiga yi cike da ɓacin rai ta ce "Wallahi Abba ba ni da laifi ba gaskiya su ke faɗa maka ba, ni dai ina neman Alfarma don Allah idan za'a ƙara kai Tallata a faɗa musu gaskiyar ni Bazawara ce, idan ba haka ba ko anyi Auren Wallahi dole a rabu don ba a ginashi a Tubalin gaskiya ba tin farko." a fusace Abba ya ce "Ɗan Iska ki ke neman maidani?? Kina nufin so nake na yaudaresu?? to tinda ba ƙaunar Zawarawa ake ba ba sai ace ke Budurwar bace ai Ƙaryar kare kai Halak, shashasha Mara kan gado." ya na gama faɗe ya yi fuuu ya bi iska su ka yi waje.
Mama ta ce "Ai kin gani, mun yi nasihar har mun gaji, ki ta korar samari Aamina wai ni ko Namijin Aljani gareki ne???"
Umar da ya dafe bango ya riƙe ƙugu ya na saurarensu sai a lokacin ya ce "Ta na fa da gaskiya Mama, fisabilillahi ko wanene ba zai taɓa lamunta ya Auri mace da sunan Budurwa ba bayan kuma Bazawara ce, kuma ko dama ace ni ne ko kuma Anas Ɗan uwana, nasan ku kanku iyayenmu ba za ku taɓa amincewa ba, mu sai mu haƙura amma ku iyayen ku zage sai kun nemawa Ƴaƴanku Ƴanci, Maganar gaskiya Ƙaramta ce wai a gayawa Mutum Budurwa ce ya zo ya tarar da wannan Kakar su wanen, kuma Bazawara ma" ya na kaiwa nan ya buga tsaki ya fice, Aaminat ta faɗa ɗaki ta ci gaba da kukanta sample sample.
Mama da su Fati su ka gama tsugunguninsu su ka tashi.
washegari
Daga Abba Umma Mama ba wanda ta gaisar ya Amsa sabi da fushin da su ke da ita. tin da ta gama Ƴan wanke-wanke da shararta ta shige ɗaki ba ta ƙara ko leƙe ba sai in za ta yi Alwala, sai yamma liƙis ta ji ciwon Jiki duk ya isheta don kuwa zaman guri ɗaya ba abin da ba ya haifar mata har ciwon kai, tashi ta yi ta sola wanka sannan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa, mafici ta ɗauka ta na kaɗawa ta ji daɗi sosai da ta ɗan motsa jikinta. Siyama ce ta yi sallama a tsakar gida ba tare da ta jira wani ya bata izinin shigowa ba ta danno kai don tasan in ta tasu ce ba za su barta ta ga Ƙawarta ba, Da sallama ta shiga ɗakin kafin ta ce "Aaminat Mutanen ɗaki." Aaminat ta yi dariya kafin ta ce "Na ji daɗin ganinki wallahi dama ni kaɗai nake zaune gashi su Fati ma ba sa nan bare in ji surutansu." Siyama ta ce "To surutan su Fatin har abin daɗi ne?" "Ai motsi ya fi laɓewa Siyam's." Siyama ta jinjina kai kafin ta ce "Ba fa zama zan yi ba, tashi mu je Gidanmu." ba gardama ta miƙe ta zura hijab sannan su ka fice.
Kafin su ƙarasa gidan Aaminat ta ce "Wai don Allah Siyama akwai wani aibu babba ne a tare da Bazawara?" cak ta tsaya gami da cewa "A'ahh!! tsaya kin ji na faɗa ne??" "Ke fa daɗi na dake Saurin rigimewa, bance kin faɗa ba tambayarki na yi ko kin ji labarai a wasu gurin, na ga kowa ƙyamata ya ke, kamar ma zargina ake." Kafin Siyama ta yi magana sai jin Hucin Mota su ka yi ta yo kansu da Mugun gudu, Su ka tsallake da gudu zuwa gefe. Me Motar Ko ya kula ya ci gaba da gudunsa.
Cikin Zafin nama Abdulkareem ya wawuri wani rangwamemen dutse ya wurga akan Glass ɗin Motar ya yi tsawa kwatsa-kwatsa, me Motar ya ja burki Ƙuuuuu, sannan ya fito a fusace, Majalisar tasu ya kalla cike da hargagi ya ce "Uban waye ya jefe min Mota ??? Ba ku da hankali ko?? ba ku san darajar Mota ba ko?? to wallahi ko waye sai an biyani Glass ɗina!!" Abdulkareem ya miƙe ya gyara kafaɗu sannan ya nufi gaban Matashin ya tsaya, a dake ya ce "ni ne na Fasata sai me??" "Sai Ubanka ya biyani, Mahaukaci ne kai?? ka san darajar Mota kuwa???" "Kai Malam kar ka sake ka zagi Ubana, kuma an fasa banza ba za a biyaka ba in ka na da ƙarfi ka ƙwata. Fass Matashin ya kwaɗawa Abdulkareem Mari, shafar fuskarsa ya yi kafin ya murmusa ya ce "Na gode" Cikin Sauri Aaminat da Siyama su ka yo riiiii zuwa gurin domin raba faɗa, Abdulkareem ya yi saurin cire Takalminsa ya wurga gabansu, cikin Ɗaga Murya ya ce "YaYa Aaminat kar ki tsallake layin da Takalmin nan yake." Aaminat ta zazzaro ido ta na kallonsa, shi kuwa ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, haka kawai sai ta tsinci kanta da komawa baya a memakon ta ƙarasa. Matashin ya ce "Godiya nace kai min?? ina ne gidan Ubanka??, kai Yaran nan ina ne gidan Uban wannan Yaron??" ya faɗa ya na Kallon su Haisam Cokali, sai ya ga sun sa masa ido kawai kowa ya ƙi magana, maida hankali ya yi akan Abdul ya na tambayarshi gidansu, duk Tambaya ɗaya Mari Ɗaya shi kuwa Abdulkareem aikinsa ya ce Ba zai faɗa ba, a ƙalla ya yi masa mari ya kai Shida kafin Abdulkareem ya ɗaga masa hannu gami da cewa "Kar ka Ƙara dukana". "Idan na ƙara za ka rama ne??" "Ka dai ji maganata kar ka Gani" "Ai dama ance Talakawa baƙin ciki garesu, shi yasa za ka fasa min Mota, To idan na bar unguwar nan ba tare da an biyani ba Allah i Tsine min." Abdulkareem ya yi dariya kafin ya ce "Ai ka mari kuɗinka kuma, Fuskata fara ce kyakkyawa a ƙalla duk Mari ɗaya Dubu Biyar ka ga ka Mari Dubu Talatin kenan, don haka Sai ka Zareta, ina nufin ka Zari ƙafarka in dena ganinta anan, Sakarai Mara wayo, a ganinka Namiji kamar ni zai zauna ka mareshi ne har haka sabi da na fito daga gidan Mahaukata? nasan Shekaru kawai za ka ban amma ba uwar da za ka nuna min, Na bari ka Mareni ne sabi da wadda ka so Kashewa Darajarta ta fi Ƙarfin Kuɗi ya Siya shi yasa na Sa jikina Fansa, idan kuma ba ka haƙura ba dik da haka ka kira POLICE wannan Katangar itace ta gidanmu, anan in ka yi gaba akwai Get A baya ma Akwai Get ta ko ina in ka je za ka iya shiga ka sa a zo a kamani Ni kuma Zan sa a Ɗaureka!!!"
Salma ta ce IN ba COMMENT ba Posting🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️
© INDO CE Tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 4
Bismillahirrahmanirrahim
"To in ba haka ba me ze sa ki ƙi Auren?"
"Allah Umma sa'a da ace zaku fahimce ni da zaku gane gaskiya" "ke dalla can jinake Abban ku kallum cikin nemo mi ki manema yake?" ta ƙarasa maganar tana tafiya ɗakin Mama.
"Yau kuma su Umma Sa'a ne a gidan namu?" "wallahi kuwa kin ganni ina su Fati da Umaima?" "suna ɗaki inaga bacci suke" aikuwa gara su huta tunda ga me aiki nan Aaminat" Umma ce ta shigo ɗakin da sallama suka amsa "Umma Sa'a sannu da zuwa ina wuni ya hanya?" "lafiya lau na sameku lafiya" Mama tayi zaram ta ce lafiya lau"
Umma ce ta ta shi ta nufi ɗan ƙaramin Falonsu firji ta buɗe ta ɗakko ruwa pure water ta zuba a faranti ta nufi ɗakin Mama da shi, "garuwa kisha" ta faɗa tana ajiye farantin a gaban Umma Sa'a.
Fati ce tashigo ɗakin ganin Umma sa'a yasa ta ɗan kyaɓe baki sannan tace "ina wuni" "lafiya lau ƴan mata masu tashe" suka yi dariya, Umaima tace "wallahi Umma Sa'a na daɗe ina son ki zo se gaki" "wai ina gari da Bazawarar ku? naji ta shuru kamar bata gidan ta na nan haka take kullum tana ɗaki"
tsaki Fati tayi tace "abin takaicin ma ta fiya ƙazanta" Mama ta muskuta gami da cewa "to kunga ta ina Aure ze zauna kowa ma ta Aura se ya sake ta dan kuwa mazan yanzu basa son ƙazamar mace"
haka suka ci gaba da fira akan wai Aaminat ita ke korar maneman ta acewar su me kuɗi take so.
Aaminat kuwa da ta gama wanke-wanken ta ga gidan kamar kango duk su na ɗaki su na hira ta ɗauki gyalenta ta fice zuwa gidan su Siyama.
Kamar daga sama ta ji Muryar Abdul ya na cewa "Ina zuwa YaYa Aaminat??" tsaki ta ja kafin ta ce "To ka aikeni ne??, kai ma ai abin tambaya ne me yasa yau ba ka je Kasuwa ba??" Ya ɗan shafa kai kafin ya ce "Ina da wani Case ne a Layin nan, wani kiwo ne da nake to kwana biyu banga abin da nake kiwon ba shine na tsaya jira ko sai da rana Rabo na zai rantse." ba ta ce komai ba ta ci gaba da tafiya, cikin sauri ya sha gabanta ta yi saurin ja da baya ta na wararo masa ido "Abdulkareem! wai don Allah ba ka gane ka shiga haƙƙina ne?? ba ka san ka na shiga rayuwata ba idan ka na yi min magana ka na katsalandan a cikin lamarina??" Murya ƙasaƙasa ya ce "Ki yi haƙuri YaYa Aameenat kinsan Zuciyar ɗan Adam kowacce da irin rauninta, da zan iya fita daga sabgarki da na yi tun kafin ki fara fusata da ni amma na kasa." ya ɗan tsagaita kafin ya ɗora da cewa "Ni hakan shine raunin tawa Zuciyar, ba na iya yi mata shamaki da shiga Gonarki, sai dai ki yi haƙuri da ni, yanzu ma tambayarki na ke son yi don kuwa naga kamar ba ki da lafiya." "Eh ba ni da lafiya ina ciwon kai ne, kuma na warke yanzu ba wata damuwa, ka bani hanya in wuce. "Zan ba ki hanya Aaminat amma sai na gama maganata, kin sha magani? ko kuma kin ga likita??" kamar za ta fashe da kuka ta ce "Abdulkareem Ciwon kaina ne, abin da bai shafeka ba ne wannan, idan na sha ba ka da asara idan ban sha ba baka da ita, me yasa?? me yasa ka ke son illata rayuwata ne Abdulkareem??, shin ba ɗaya daga cikin ƙannena na layin nan bane kai?? ka na tunanin akwai bambanci tsakaninka da su Bilal ne??" Zuciyarsa ta yi wani mugun rauni idanunsa su ka canja kala su ka cicciko da hawaye, cikin sanyi ya kalleta sannan ya ce "Tabbas ba ni da bambanci da su Bilal ni Namiji ne su ma Maza ne, kuma ba na ganin bambanci tsakanin ni da Anas da Umar Yayyenki, Aaminat ina son in tsayawa rayuwarki fiye da yadda Umar Zai tsaya miki, kar ki yi min mummumar fahimta, wallahi ko da sau ɗaya ban taɓa yin banzan tunani akanki ba, sai dai ina tunana ɗaukaka gobenki, Ba zan iya denawa ba har sai in na dena numfashi a Duniya ko da kuwa za ki jefa ni cikin rijiyar azaba, ni kaina ina jin ba daɗi idan na ɓata miki rai sai dai bansan me yake damuna ba da na kasa denawa, ta yuwu ma na haukace ne!" Ya ƙarasa maganar ya na murmushin da ya bawa hawayen idonsa damar sakkowa. girgiza kai ta yi cikin sauri, bakinta na rawa ta ce "Abdul ba ka haukace ba amma akwai wata cutar da take damunka, ka roƙi Allah i yaye maka ita domin za ta illata rayuwarka, ni kuma ba za ka iya tsaya min ba Allah ne kaɗai abin jinginata shine ya ke shiga lamurana, Iyaye ko Ƴan uwa ba wanda zai iya tsayawa Aaminat bare kai Yaron Maƙota, ka cire wannan tunanin daga Zuciyarka Abdul." ta na kaiwa nan ta ratse ta kusa da shi cikin gudu-gudu sauri-sauri ta shige gidan su Siyama, tin a Soro ta fashe da kuka ta ƙarasa ta na yin kayanta Anti ta ce "Subhanallah meke faruwa haka Aameenat??" zama ta yi gami da cewa "Nima ban sani ba Anti, bansan meke damuna ba amma nasan Ƙaddarorina a rayuwa su na da yawa." Siyama ta fito daga ɗaki ta na gyara kallabinta, sai da ta zauna sannan ta ce "Haba Aameenat na gaya miki wannan kukan ya yi yawa wallahi, komai kuka komai kuka?? ki samawa kanki Ƴanci daga wannan koke koken don Allah, a Duniyar nan fa kowa ki ka gani da kalar damuwarsa kowa ya na yawo da Jarrabawarsa to idan ki na kuka ta yaya za ki iya fuskantar Jarrabawarki har ki cinyeta?, ki yi shiru don Allah." gyaɗa kai ta yi ta na ƙoƙarin tsaida kukan sai dai da ta goge Ƙwallar da wata ta zubo.
Abdulkareem tin da ta yi gaba ta barshi ya kasa gaba ya kasa baya, Haisam Cokali ne ya iso gurin cike da iyayi da kwainane irin nasa ya ce "Master Allah i sa dai lafiya don wallahi gani na yi idanunka sun kawo ruwa." Abdulkareem ya numfasa ba tare da ya ce komai ba ya koma jikin gatangar gidansu ya jingina gami da zubawa guri ɗaya ido, Haisam Cokali ya ce "Wallahi daga gani yau Maza sun sha fama don kuwa gabaki ɗaya rauninka ya gama baiyana Oga" tsaki Abdulkareem ya ja kafin ya ce "Cokali zan Ɗauraye hannuna in kikkifa maka Mari wallahi". cikin sauri ya riƙe haɓa gami da cewa "Ni Ɗan nan rufani ka saya ni, abin ai bai yi zafin haka ba, maida wuƙar Allah i bada haƙuri ni tafiya ma zan yi." Abdulkareem ya ce "Haisam wai don Allah ka lura akwai wata cuta da take damuna?? ni ina ganin kamar lafiyata ƙalau ko ina alamun hauka?" Haisam ya tuntsire da dariya ya yi shewa ya tafa hannuwa sannan ya ce "Master namu Allah ya barka, to ai ni duk layin nan a Samari dai har ƴan shekara Talatin banga me hankali kamarka ba, kumw lafiyarka ƙalau tinda ba zazzaɓi ba ciwon kai." girgiza kai ya yi a sanyaye ya ce "Ta na da gaskiya sai dai na kasa gane kowane irin ciwo ne, nima kaina na san ba ni da lafiya". "Allah Sarki Master, don Allah sa ranka a inuwa ka je ka yi Sallah, ba ka jin Masallacin gidanku ma anyi kira??" Gyaɗa kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya nufi cikin gidan.
bai bi takan kowa ba ya yi Alwala ya bi Jam'in Sallar bayan an Idar ya shige cikin gida. ba shi ya fito ba sai yamma liƙis lokacin har an gama kasa Ƙwallo shi ake jira, ya na fitowa kuwa su ka fara.
Sun yi nisa cikin wasan Nana Kadija ta tawo tsogal-tsogal ta sha ado cikin wando ja Da baƙar Riga iya guiwa wadda aka yiwa adon duwatsu ta yi Rolling da ɗan ƙaramin Mayafi Ja, sai Glass No Respect baƙi ta haɗe girar sama da ta ƙasa, tsaki ta ja ganin sun cika layin su na Ƙwallo kamar mallakinsu, Walid ne ya kula da zuwanta ya ɗaga murya ya na cewa "Ku tsaya a wuce!" Banza su ka yi masa har sai da Abdulkareem ya ce "Dalla ku dakata mana ko bakwa gani ne?" su ka tsaya su na kallonta, ita kuwa ta girgiza sannan ta ci gaba da takawa kamar me tsoron Ƙasa, sai da ta zo saitin Abdulkareem sannan ta ja wani dogon tsaki ta tsartar da yawu ta bashi wani banzan kallo sannan ta yi gaba. cike da mamaki ya bi ta da kallo ya na cewa "Kaii!!?? ke zo nan, ni za ki kalla ki yiwa tsaki harda tsartar da yawu?" ta juyo a fitsare ta ƙare masa kallo sannan ta kuma wani tsakin, Muktar ya ce "Haba Master ba da kai take ba da mu take fa, ƙyaleta kawai." Fuska ya haɗe ya ce "Ku tara min ita in ji in ni sa'anta ne." Walid ya ce "Me za ka yi mata to? ka ƙyaleta mana ai ba da kai take ba." "Wallahi in ta bar sashin nan ba ku tare ta ba sai ran kowa ya ɓaci" ya na rufe baki su ka bi bayanta su ka sa ta a tsakiya, ya yi tsalle ya tsinko ƙaramin reshen bishiyar da suke ƙarƙashinta ya gyarata sannan ya nufi inda suke, Sai tsiwa take zuba musu bakinta ya ƙi mutuwa gashi sai keɓe baki take yi ita a dole ƙyamarsu take. buɗa masa su ka yi ya shigo tsakiyar ganinsa da bulala ya sa ta zaro ido ta na cewa "Wai meye hakan??" bulalar ya shiga sauke mata a gadon bayanta, tin ta na mazewa har ta fara kuka ta na roƙonsa, sai da ya daka iya son ransa sannan ya ce su bata guri, su ka buɗa mata hanya, Abdulkareem ya ƙara zuba mata ɗaya gami da cewa "Ƙetare Ƴar Bantan Uba ta Danƙi Harawa." Nana Kadija ta tsallake da gudu, duk ta watsar da iyayin nata ta fara gudu, ba ta tsaya ba sai da ta shige gida, ta je da kuka yare-yare.
Abdulkareem kuwa ko a jikinsa ya ce su ci gaba da Ƙwallon.
sai bayan sun tashi ya koma gida ya tarar da ita har lokacin kumburi take, ta yi murjai-murjai. Ummi ta ce "Babban Mutum me ya haɗaka da Nana Kadija??" "Au wai zuwa ta yi ta ce na daketa??, to me yasa ba ta gaya miki abin da ta yi min ba?" Ummi ta ce "Ba tambayarka na yi ba?? ka kama Budurwar Ƴa a gaban Yara ka zaneta haka ake yi??" "To Ummi tin da ba ta da kunya ai wallahi fin haka ma za ta samu, wai fa kallona ta yi ta min tsaki ta tsartar da yawu, ƙarshe dai kinsan cewa za ta yi wai ina wasa da ƳaƳan Talakawa, to ina ruwanta? ki ga ta na yawo a layi kamar figaggiyar tantabara ita a dole Ƴar Masu kuɗi, na bi kuɗin da gudu ba Silifas, sai na karya mata ƙafa idan ta ƙara yi min irin wannan iskancin" Cike da tsiwa ta ce "Eh ɗin ni na fi figaggiyar tantabarar ma, aikin kawai ba dole ma ka sa a dinga raina mutane ba ka na shiga cikin ƙazaman can kuna wasa, wai Ummi ba za ki hana shi wasa da su ba? Kuma wallahi Ummi indai ya ƙara dukana sai na rama ai jiki bai fi jiki ba, kwata-kwata shekara uku fa ko huɗu ka bani shine za ka maidani kamar ƴar cikinka, to wallahi ba ka isa ba." "Idan kin gama surutun sai ki tashi ki rama yanzu ai ga jiki ga tsoka, ko da minti Ɗaya na girmeki ai na girmeki dai, kuma ni Namiji ne a Matsayin Ubanki nake ɗaukar kaina." rasa abin cewa ta yi don haka ta ƙara fashewa da kuka, Ummi ta ce "A gaskiya Auta ni kaina raina ya ɓaci, abin ya isa haka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 16