An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
001 SHARRI JAKADA NE
Rukuni na shida 6
Gasar tsangayar marubuta 2020
Shuraihu Usman
Sowa hadi da ihun jama’a ne ke tashi a dankareren filin, dubunnan jama’ar da sukaiwa filin mamayar tururuwa sunyi dafifi a gaban wani makeken mumbarin katako,suna ihu suna fadin “sai kayi sai ka zarce wlh, makiyanka sai dai su mutu” .
A saman mumbarin nan kuwa wani dattijone sanye da fararen kaya yana washe baki gamida daga wa mutanen nan hannu, daga bayan dattijon wasu jibga-jibgan mutane ne masu kirar adawa, sunasanye da bakaken kwat,fuskarsu adaure tamau tamkar wayanda aka aiko ma da sakon mutuwa.
Dattijon ya daga hannu jama’a sukai tsit ya fara bayani “ruwa” jama’a suka amsa da “daga Allah” yasake maimaitawa a karo na biyu mutanen suka sake bashi amsa da amsar dasuka bashi a farko. Cikin murmushi dattijon yace “lokaci yayi kana zamani yazo da kowani karabiti ke mafarkin shugabanci, sun gaza gane kalmar shugaba me take nufi, burinsu kawai su hau mulki su cika aljifansu da dukiyar haram su bar talakawa cikin mawuyacin hali. Alhamdulillah jama’a kun zabemu da fari kuma kunga gingimemen aikin da muka dauko na shimfida muku titi a unguwanninku, sannan ga aikin kwalbati da muka faro wanda a yanzu an ci rabin aikin, ga fitilun kan hanya duka da muka sanya maku,tsaya fadin tarin ayyukan da gwamnatinmu tai maku ma bata baki ne, kundai gani da idanunku sun mulke ku a baya kunga yanayin kamun ludayinsu, shin zaku hada nasu da namu” ya karisa maganar tasa cikin daga murya
jama’an dake rike da fastocin dattijon suka amsa da “A’a”
“zabi na gareku, kuke da wuka da nama a hannunku ku sani kuri’unku sune ‘yan cinku,makaminku,martabarku hakanan kuma babban jigonku wurin tabbatar da dorewar shuwagabaninku na gari tahanyar kada wa jami’iyya mai alamar ruwan sama kuri’a ranar zabe” dattijon mai suna Alhaji Murtala ya sake fadi cikin daga murya,daga karshe yace “jama’a ku fito kwanku da kwarkwatarku ku zabi jam’iya mai alamar ruwan sama, ruwa daga Allah.”
Jama’a suka dau sowa suna fadin “sai ka zarce a kujerar sanata, sai ka zarce”
yana gama fadin hakan ya yafito daya daga cikin masu take masa baya lokaci guda ya sauko daga kan mumbarin ya durfafi wurinda motarsa ke fake,masu take masa baya da jami’an tsaron lafiyarshi suka biyoshi, yana karisowa ya bude bayan motar ya dauko wata ‘yar karamar jaka ya bude,damin kudi bandir uku yan ‘dari bibbiyu ya dauko ya mikawa mutumin nan yace “amshi kwasan yadda za’ai ku rabawa mutane” lokaci guda dattijon ya juyo,direbansa da tuni cikin shirin bude masa kofa yake yai maza ya bude kofar gidan baya, Alh murtala ya shige direban mai zungureren kai da dogon baki ya juyo yace dashi “your excellency, gida zamu tafi ko masaukin bak’in ka”
“akwai muhimmin tattaunawar da zamuyi a masaukin bak’ina dun haka ka kaini can” sanata Alhaji Murtala ya fadi yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu
************
“Alhaji bana jin his excellency zai samu zuwa yau, duba fa har karfe biyar tayi bai hallara ba” wata kyakkyawar budurwa da bazata gaza shekaru ashirin da biyar ba ta fadi yayin data ke feso hayakin taba daga bakinta
Mutumin data kira da alhajin babban mutum ne tsarar Alhaji murtala yana da shirgegiyar tumbi da akowanne lokaci take barazanar fasa rigar dake jikinsa, daga gefen damansa wata budurwace yar shekara a shirin ta dora kafa guda akan guda tana zukar sigari.
“Alhaji magana fa nake dakai kayi min shiru” budurwar datai magana da fari ta sake fadi daidai lokacin dataiwa sigarin hannunta zukar karshe
Alhaji mahiru ya dubeta yace “to me kike son nace dake ne jamila, sanin kanki ne his excellency ko meeting sukeyi da shugaban kasa zai iya katsewa ya tahonan bare kuma ma kamfen, na tabbata yanzu haka yana hanya anjima kadan zai kariso”
Budurwar da aka kira da jamila ta dubi budurwan dake gefen Alhaji mahiru tace “yar shila cillo min kwalin tabar nan nawa yakai killer” ba musu yar shila ta wurga mata kwalin taban, jamila ta zaro kara guda ta cinna mai wuta, ta zuka sannan ta feso hayakin ta baki da hanci
“naga halama yau ‘yar shaye-shaye kuke ji bazan tashi na baku wuri kafin sanata ya kariso” Alhaji mahiru ya fadi gamida mikewa tsaye.
“Assalumu’alaikum” Alhaji murtala ya fadi yayin da ya shigo cikin rantsastsiyar falon gidan da ya k’awatu matuka da kayan k’awa,ya washe wagegen bakin sa sanda idanuwansa sukai tozali da jamila…
Iliyas Ishak Gundutse
SHARRI JAKADA NE.....
002
Labarin hadin guiwa
Gasar Tsangaya ta 2020
Shuraih Usman
Isah Isah Almachinawy
SHARRI JAKADA NE....
002
Labarin hadin guiwa
Gasar tsangaya 2020
Group 6
Shuraih Usman
Isah Almachinawy
.
.
Ya washe wagegen bakinsa bayan ya yi tozali da Jamila, kai tsaye kuma ya sake waigawa ga yarinyar dake a gefen abokin sa Alh. Mahiru cikin kallonsa na kurilla. Baya ko shakka wannan iya ce tsarabar da Jamila ta yiwo masa, yarinyar kyakkyawa ce komai ya ji. Sai dai ta banbanta da irin yaran da Jamila ta saba kawo masa, don kuwa ta sani shi a tsarinsa yafi son a kawo masa kaya daga kauye, tunda shi yafi son a ce shi ya fara shigar mace kafin kowanne namiji, irin wadannan kuwa dole sai a kauye. Amma ga wannan yarinyar daga haduwarsu sai wani gwalangoso da yauki take yi masa.
Suka tafa shi da abokin sa Alh Mahiru wanda ko shakka ba yayi ya san shi zai dauki Jamila, don kuwa shi dama ya kan yi sati bai kwana a gida ba.
Alh Mahiru shahararren Dan kwangila ne wanda sunan kamfaninsa ya yi shuhura a fannin gine-ginen gidaje da tituna, haka kuma ya kan shigo da kayayyakin kyale-kyale na kawata gidaje ofisoshi. Abin da wasu basu sani ba ma shi ne, matsawar lokacin da Alh Murtala ya shafe yana gudanar da mulkinsa a wannan zangon, duk wata kwangila ta gine-gine shi ne yake karba. Kuma bisa yarjejeniya suke yi don Kawai su handami kudin talakawa. Idan aiki zai ci milyan sittin, to Alh. Murtala zai wallafa bayani ne ga talakawa kan cewar aikin zai lashe milyan dari da hamsin, kuma haka za a fitar. Tare suke biye-biyen mata cikin sirri alhalin kowannensu yana da matarsa ta sunna a gida har da 'ya'ya. Ga kudi ga suttira ga ababen hawa duk an jifge a gida. Amma an fito kwararo ana lalata 'ya'yan wasu. A iya cewa ma Alh. Murtala yafi kulawa da iyali in an kwatantashi da abokinsa Alh. Mahiru wanda shi kullum yana kan hanya daga wannan kasa zuwa waccan, in ya dawo Najeriya kuma kullum yana cikin taro da ma'aikatan kamfaninsa ko kuma wasu kamfanonin takwarorinsa.
A gurguje suka yi sallama saboda dare ya yi. Alh. Mahiru ya janye Jamila suka nufi hotel yayin da Alh. Murtala ya jagoranci 'Yar shila suka kutsa cikin katafaren gidan hannayensu rike da juna suna mutsikawa ba tare da sun lura da wani matashin Dan adawa sanye cikin bakaken kaya da fuskar katako yana haskasu da karamar karamar kyamara ba daga cikin fulawoyin da suka yi wa katangar harabar gidan kawanya ba.
*** *** ***
Mai gadin ya kalli dan saurayin cikin takaici, yana mai bakin cikin yadda Hajiya ke ha'intar Alhaji don Kawai ta ga baya samun damar kwana a gida saboda yanayin kasuwancinsa. Alhalin duk don ita 'ya'yanta yake ta wannan fafutikar, a zuciyarsa ya ji dama ace Alhaji ya dawo gida cikin wannan Daren....tunanin sa ya katse lokacin da ya tuna ai shima Alhajin abin tuhuma ne, don kuwa In har namiji lafiyayye ne, to da wahala ya ajiye zukekiyar mace mai kyawun sura irin Hajiya kuma ya rika tsallakewa yana barinta na tsawon sati ba a gida.
003 SHARRI JAKADA NE
GASAR TSANGAYA 2020
RUKUNI NA SHIDA 6
Labarin hadaka na
Shuraih usman
Iliyas ishak gundutse
Jijjiga kai Lado mai gadi yayi, yadau buta ya shige dakinsa dake jikin dankareren gate din gidan, zuciyarsa na tofin ala tsine ga hajiya sa’a uwardakin Alhaji Murtala.
Daga cikin makareren gidan da aka kashe milyoyin takardun abuja wurin gina shi, hajiya sa’a ce zaune kan luntsumemen kujera, wani kyakyawan saurayi na zaune a gefenta, saurayin na rike da kofin gilashi mai dauke da koren lemu a ciki. “har ga Allah hajiya ba so nake mu rika harka dake cikin gidannan ba, kullum a tsorace nake, don kema kinsan mijinki zai iya dawowa a kowanne lokaci, kuma ga ‘ya’yanki suma, rannan fa dakyar na sha lokacin dana zo fita mukai kicibus da hassanu shi kuma yana shigowa. Nama ci sa’a hankalinshi baizo gareni ba, barin ma shegen mai gadin nan naku da kullum muka shigo sai ya bimu da kallo da dagwa-dagwan idanunsa, yauma ina lura da shi har tsaki yake yana tafa hannuwa,ni bansan me ye dalilin da ya sa bakya son mu je hotel ba” saurayin ya fada yana kokarin ajjiye kofin bisa faffadar teburin gilashin dake gabanshi.
Hajiya sa’a ta sauke ajiyar zuciya ta ce “haba haruna kai kenan kullum magana guda, a kullum maganar ka kenan, Alhaji da ‘ya’yana sune matsalarka, nasha fada ma ka na kanyi kwanaki hudu zuwa sati banga idon Alhaji a gidan nan ba, su kuwa ‘ya’yana sun dade da komawa makaranta rannan ma hassanu wata matsalace ta dawo da shi, dan Allah ka saki jikin ka babu abunda zai faru.
Saurayin da hajiya ta kira da haruna ya juyo ya fuskanci hajiya sa’a ya ce “ai ni hajiya hankalina ne ke tashi, dadai za ki ruga kama mana hotel ai da yafi, ko shakka bana yi duk sanda Alhaji ya tambayi mai gadin nan naki zai iya warware masa bakin jaka ya tona mana asiri.”
“to shikenan gobe hotel zamu nufa, tunda haka kace yanzu dai hankalin ka ya kwanta” hajiya sa’a ta fadi tana kwance kallabinta, haruna ya yi murmushin jin dadin fuskantarsa da hajiya tayi ya ce “yauwa hajiya ko ke fa”.
Ta mike ta nufi dakinta haruna ya biyo ta a baya, in ka dubi hajiya sa’a da haruna a wannan lokaci ka ce uwace da d’anta.
*** *** ***
“Inna lillahi wa’inna ilaihirra ji’un” Alhaji murtala ya fadi yana kallon fuskar wayarsa dake dauke da rikitaccen al’amarin da bai taba zato ba, kuma bai taba tsammani ba fuskarsa ta fallasa asirin tsantsar tashin hankalin daya ke ciki, cikin sauri ya mike daga kan lalallausar katifar daya ke kwance. ‘Yar shila dake gefensa ta dago tana shafa bayansa cikin kissa da salon ‘yan matan bariki ta ce “Alhaji me ya farune naga lokaci guda hankalin ka ya tashi” ko saurararta bai yi ba ya janyo kayansa ya saka ya fara kokarin kiran Alhaji mahiru a waya, bugu daya ya dauka ko sallama bai tsaya yi masa ba ya ce “marmaza ka taho mu hadu da kai a gidana dake hayin ‘dan bawa” iya abunda ya ce da shi kenan ya kashe wayar yana shirin tafiya ya tuna bai sallami ‘yar shila ba, rafar dubu d’add’aya ya cire ya ajjiye mata akan gadon sannan ya fice.
***
Motar hajiya sa’a ce ta faka a harabar shahararren tangamemen hotel din dake garin, haruna ne ya fito daga cikin motar ya shige cikin hotel din, bayan shudewan ‘yan mintuna ya dawo hannunsa rike da d’an makulli, ya samu hajiya sa’a ya sanar da ita ya gama komai.
Haruna da hajiya sa’a ne kwance cikin ni’imtaccen dakin daya yalwatu da daddadan sanyin na’urar sanyaya daki (Air condition) suna aikata masha’a, suna cikin alfashan ne suka ga farin haske ya dallare masu fuska, sannan sautin da kyamara ke fitarwa yayin daukar hoto ya karade kunnuwansu.
***
“shi kenan Asirinmu ya tonu “ Alhaji mahiru ya fadi yana tafa hannuwansa, “ni babu abunda ke kona min zuciya ma kamar hoton hajiya, inda ace abun iya kanmu ya tsaya to da da sauki nasan yadda zan magance matsalar.” Alhaji murtala ya fadi yana duban fuskar wayarsa da razananniyar fuskarsa. Hoton hajiya sa’a ce da haruna rungume da juna suna aikata alfasha, ya wuce da hoton zuwa na gaba, hoton alhaji mahiru ne rike da hannun jamila yayin da suke kokarin hawa mota, hoto na gaba kuma hoton sa ne da ‘yar shila tana janye da hannunsa zasu shige daki...
SHARRI JAKADA NE.....
004
Labarin hadaka
Gasar Tsangaya 2020
Rukuni na 6
Iliyas Ishak Gundutse
Shuraih Usman
Idanuwan Alh. Mahiru suka zazzaro tamkar an yi masa kamshin mutuwa, ya dauke fuskarsa ga barin kallon fuskar wayar abokin nasa, haka kuma ya kasa cewa komai don kuwa a halin yanzu hatta yawu babu a bakinsa, ya kafe tuntuni. Sannan harshensa ya harde ta yadda ko sunansa ba lallai ya iya furtawa ba.
Mutanen biyu suka yi cirko-cirko a tsaye tamkar zakaru a filin daga. Kowannensu yana cikin sake-sake da tufka don goge wannan mummuman tozali da ya ziyarci idanun su. Zuwa can Alh. Murtala ya gyara muryarsa kana ya tambayi abokin sa muryarsa na karkarwa .
"Daga wane sashi kake tsammanin wannan farmakin?" Alh Mahiru ya numfasa shima kafin ya ce .
"Daga bakina ya kamata tambayar ta fito, kunnuwana su saurari amsar daga bakin ka. Kai ne kake cikin harkar da take da tarin abokan adawa ta yadda za a yi bakin kokarin bibiyar duk wani tasgaro cikin al'amuranka don a illata tafiyarka a siyasance. Don haka ka auna fahimtarka don tantance kwayoyin aya da tsakuwa."
Shiru ta shiga tsakani kafin kwakwalwar Alh. Murtala ta dawo daidai don fara aiki. Ya Sanya hannayensa biyu ya sharce gumin da ya fara sintiri daga goshinsa zuwa kumatu har zuwa harabar idanunsa. Sai yanzu ya fahimci inda al'amarin ya Sanya gaba, lallai akwai lauje a cikin nadi.
Zuciyarsa ta sake dawo da taswirar fuskar wayar dauke da hotunan wannan badakala. Ga hotonsa tare da Jamila turmi da ta6arya, a wani sashin kuma abokin sa Alh. Mahiru tare da 'Yar shila.....ga hoton uwar gidansa kuma a wani shafin uwar gidansa ce Haj. Sa'adatu tare da wani yaro suna ha'intarsa....ya yi saurin dafe kirjinsa wanda ake ta fa burumtu da gwagwarmaya sakamakon boren da zuciyarsa ke yi na burin faso kirjinsa don aiwatar da zanga-zangar lumana, sai dai kuma a yadda yake jin yadda wani abu ya taso ya tokare masa a kirji da kuma irin sukuwar da yake ji a kirjin nasa mai kama da sukuwar dawakai a filin gasar fitar da gwanin mahayi, ko shakka babu wani abu na iya faruwa dashi a kowanne lokaci.
*** *** ***
Haj Sa'adatu ta yi gaggawar tattaro dan abin da hannunta zai iya kamowa na daga tattausan bargon da aka yiwa katafaren gadon shimfida ta watsa shi a tsaraitaccen jikinta a makare, don kuwa tuni abin da aka nema akansu an samu, babu shakka an shammace su ta yadda hannun agogo ba zai ta6a komawa baya ba. Ta tsayar da kallonta tsai akan dan saurayi Haruna matashin da bai wuce shekaru ashirin da tara zuwa talatin ba. Wanda har yanzu bai gama wartsakewa ba. Sannan kuma babu alamun dimuwa a tare dashi bisa bakon yanayin da ya ziyarcesu. Watakila ko bai gama sanin hakikanin lamarin ba ne. Oho! Sa'adatu ta fara sauke ajiyar zuciya tare da shassheka alamun fashewarta da kuka a kowanne lokacin daga yanzu.
Ba ta San dalilin yin hakan ba, ba ta San daga inda aka shiryo mata wannan nufakar ba. Sai dai ta San akwai illolin da wannan aiki zai iya jawowa rayuwarta gaba daya. Don kuwa ko ba ta ga ainahin hoton ba, to ta San fuskar ta ta samu muhalli sosai a majigin da zai fitar da hoton. A zuciyarta ta ji dama ace cikin barci ta yi mafarkin faruwar wannan mummuman al'amarin?
Ko shakka babu duk Wanda ya dauki wannan hoton, to akwai abin da ya ke son aikatawa da shi, kuma akanta za a yi aikin.....tunanin ta ya tsaya can! Lokacin da ta tuna yadda Haruna ya takurata akan lallai sai sun zo hotel maimakon su yi a gida, to gashi kuma zuwansu hotel a karon farko an illata ta. Anya kuwa Haruna bashi da sa hannu kan wannan sha'ani? Tabbas akwai hannunsa, don kuwa babu wata Matsala da hoton zai kawowa rayuwarsa kasancewar babu Wanda ya San shi. Ta sake jin fargaba ta ru6anya a gareta da ta auna yadda fuskar mijinta zata zama da kuma matakin da zai dauka akanta idan yayi tozali da wannan mugun hoto..
005 SHARRI JAKADA NE
GASAR TSANGAYA 2020
labarin hadaka na
Shuraih Usman
Iliyas ishak gundutse
Cikin halin firgici da matsanancin tashin hankalin da hajiya sa'adatu ta tsinci kanta a ciki, ta mike daga kan katifar,ta nufi wurin da tai jifa da kayanta ta dauko ta sanya, sai a sannan haruna ya dawo cikin hayyacinsa ya dubi hajiya sa'a da ta gama sanya kaya tana kokarin daukar jakarta, fuskarta na dauke da tarin tashin hankali hadi da firgici wa'yanda mintoci kadan da suka shude basa tare da ita, "hajiya me kuma ya faru naga lokaci guda kin mike alhalin bamu gama abunda ya kawo mu ba." haruna ya fadi shima yana kokarin tashi daga katifar.
a kufule hajiya sa'adatu ta nufo haruna da ke kokarin zura wando, mari ta sauke masa har guda biyu sannan cikin sheshshekar kuka ta ce da shi "kai munafiki annamimi, me nai maka dakai min haka,me ka nema daga gareni ka rasa, kudi,mota da gida duk na mallaka maka su kyauta, shine kayi min butulci kaci amanata. To bazan fada maka wallahi muddin ka sake wani yaga hoton nan sai na sa an kashe ka."
baki bude haruna ya tsaya yana kallon hajiya cikin mamaki da kasa gane inda zancenta ya nufa babu abunda ya sake harzuka tunanin dan tsamurarren saurayin kamar kalmar kisa da yaji hajiya ta ambata, yadai daure ya ce"hajiya ban fahimci zancenki ba, wani hoto kike magana akai".
harara hajiya sa'adatu ta jefesa da shi lokaci guda kuma ta matso gabansa ta ce "so kake ka ce idanuwanka basu gane maka farin hasken daya haskake dakin nan dazu ba ko so kake kace kunnuwanka basu jiye maka sautin daukar kamara ba."
"hajiya duk yaushe kenan wannan abu ya faru wallahi bana da masaniya akan duk abubuwan da kika lissafto din nan"
***
“Sa’adatu! Sa’adatu!! Sa’adatu!!!, wai ina ki ka shige ne” Alhaji murtala ne ke kwala wa hajiya kira lokacin daya shigo cikin kayataccen falon gidan, fuskarsa a murtuke hannunsa rike da wayarsa, hajiya sa’adatu dake cikin dakinta a kwance tana tunanin abubuwan da zasu biyo baya muddin hotonta ya bazu a duniya, sai yanzu take nadamar alfashan da suke aikatawa ita da haruna, babu abunda ke zarya cikin zuciyarta kamar ‘ya’yanta Hasanu da Abdullahi, da wani ido zata kallesu, shikenan fa ta janyo masu abun gori da aibatawa a duniya, wasu siraran hawayen nadama suka yi futar dodon kod’i daga idanunta, tana cikin wannan haline kwatsam ta jiyo muryar Alhaji yana kwarma mata kira, mikewa tayi ta nufi falo ta tarar da shi a tsaye yana huci tamkar bakin kububuwa “kin cuceni sa’adatu,kuma kin lalata min siyasata,” Alhaji ya ce da ita yana nuno mata fuskar wayarsa,
Hajiya ta amshi wayar ta ga hotonta ne da haruna rungume da juna sannan cike da gadara ta mikowa alhaji wayarsa ta ce “toh me ya faru” baki bude alhaji ya tsaya yana duban hajiya cikin mamaki da tu’ajjibi ya ce”amma kuwa Allah ya wadaranki, kuma Allah ya isa tsakani na dake, tunda irin rayuwar da kike so kenan kije na sake…” maganar tasa ta katse daidai lokacin da hajiya ta nuno masa fuskar wayarta inda yai arba da hotonsa da ‘yar shila kwance bisa katifa guda suna aikata alfasha.
*** ***
Alhaji murtala ne zaune cikin kasaitacciyar gidan gonarsa yana sake-saken hanyar da zai bi wurin ganin ya dakile tonar asirinsa da Abokinsa, wayarsa ce ta fara burari ya dau wayar ya kara a kunne “Alhaji murtala kake kowa, magana zanyi dakai ina so ka kasa kunne ka saurareni, nine na dau hotunan alfashan da kuke aikatawa kai da amininka da matarka” wata kakkausar murya ta fada daga cikin wayar.
Tashin hankalin da alhaji murtala ke ciki ta dadu, cikin rawar murya ya ce “malam wanene kai, ka fadi ko nawa kake bukata zan baka amma dan Allah kar ka yada hotunan nan a duniy…”
“yimin shiru maha’inci” kakkausar muryar ta katse zancen alhaji murtala da fadin haka sannan ta cigaba “bana gargade ka da ka tsaya ka saurareni ba ne ba, bana kiraka bane don ka kalallameni da maganar banza ba, na kiraka ne don na sanar dakai daka shirya nome abunda ka shuka, kaida maha’incin amininka. Gobe duniya zatai karin kumallo da hotunan ku dama wasu sirruka da ya jib’an ci handama da babakare da kukewa dukiyar al’umma, shakka babu a gobe ne duniya zata san asalin siffarku.”
SHARRI JAKADA NE....
006
Labarin hadaka
Na Tsangaya 2020
Rukuni na shida
Na
Iliyas Ishak Gundutse
Shuraih Usman
Gwangwamemiyar muryar mai kama da an tayar da tahuna ta ci gaba da sintiri a dodon kunnen Alh. Murtala wanda yake tsaye babu kuzari yana sauraren muryar tamkar yadda dalibi mai ke nazarin darasi a gaban malami a cikin aji gabannin jarrabawa. Muryar ta ci gaba da amsa kuwwa a dodon kunnensa had zuwa tsakiyar kansa....
"Matsawar lokaci muna tare da kai a siyasance, mun sadaukar da komai namu don ganin mun kafa gwamnatinka a farkon takararka, ba don komai ba sai don alkawarurrukan da kayi mana, Ashe duk yaudara ne, ka rika sanyamu muna kashe 'yan uwannu saboda tuntuni ka lalata tunanin mu da karya da yaudara, ka rika raba mana kwayoyi da makamai muna saran duk wani wanda yayi adawa da kai, Ashe kaima adawa kake yi damu. Don haka yau ranar wanka ce babu batun 6oyon cibi, kamar yadda muka fahimci shugabanci bai dace da kai ba, lokaci yayi da sauran jama'a suma zasu fahimci haka. Za6i daya ne gareka cikin biyu, ko ka janye takararka ko mu saki hotunan da ka bani, ko da yake kafin hotunanma ya kamata ka Dan baiwa idanuna abinci da wannan bidiyon." Ya ji muryar ta dan saurara kafin ta ci gaba.
"Sako zai shigo wayarka nan da dakiku goma......
Jim kadan da shigowar