sakon bidiyon ne Alh. Murtala ya tsinkayesu zaune cikin falo yayin ganawarsu da wasu cikin takwarorinsa masu rike da madafun iko suna hira cikin annashuwa, kan teburin da ke gabansu cike da kayan ciye-ciye da shaye-shaye. Alh. Murtala ne yake cewa a cikin bidiyon.
"Ai tuni na manta da batun yiwa talakawa aiki a cikin mulkina, idan ka fitar da talakawa daga cikin kunci ka basu jin dadi tamkar ka daidaita su da kan ka ne, don haka kun zama dai dai, ka basu damar da zasu kai 'ya'yansu makarantu dai dai da makarantun da ka kai 'ya'yanka. Kaga kuwa da zarar sun samu ilimi to shi kenan sun samu wayewa ta yadda in ka he Neman kuri'unsu lokacin za6e kudinka ba zasu yi amfani ba, sannan in kayi masu karya kai tsaye zasu fahimci karya kake yi masu, kuma wata rana a cikin su za a samu jagororin da zasu jagoranci 'ya'yanmu tunda mun basu ilimi. Sun San Kansu da 'yancinsu, shi kenan sun zama dai dai da mu. Amma idan ka barsu cikin jahilci to ka barsu cikin duhu, ba abin da zasu iya yi na jayayya da kai, zaka iya sayawa matasansu kwaya da makamai ka basu ka turasu duk wurin da kaso, su yi abin da make so, in sun gama sun dawo ka basu na abinci. In lokacin za6e yayi duk India ka yi rabon kudi shi kenan ka dawo da kwarjininka."
Alh. Murtala ya ci gaba da kallon fuskar wayar cikin takaici. Tabbas ya San watsuwar wannan bidiyon a cikin al'umma tamkar an sanya magogi an goge sunansa ne a da'irar siyasa....
Ya kara waya a kunne bayan amonta ya dame shi da sauti
"Muryar ta ci gaba baka da za6i bayan daya cikin biyun nan. Ko ka janye takararka ko kuma talakawa su yi Karin kumallo da wadannan hotuna gami da bidiyon da ka gani yanzu....
*** ***
Hankalin Alh. mahiru ba a kwance yake ba ta yadda har baya iya sanin Inda yake Dora kafarsa lokacin da ya shigo hotel din.. A sanadin haka ne ya rasa tantance dakin sa ya bar Jamila bayan abokin sa Alh. Mahiru ya kira shi. Dakin da ya bude ba shi ne dakin da suka kama da Jamila ba, don kuwa a wannan dakin matarsa Hajiya kubra ya bani rungume da wata mata tsirara suna sumbatar junansu a yanayin madigo.
SHARRI JAKADA NE....
006 Zagaye na 2
Labarin Tsangaya 2020
Rukuni na shida
Iliyas Ishak Gundutse
Shuraih Usman
Kammalawa.
Cikin kunan zuciya da shakakkiyar murya Alh mahiru ya dakawa matan biyu tsawa, kana ya nuna matarsa Hajiya kubra ya CE da ita rai a bace
"Dama irin ha'intar da kike yi Mani kenan in bani nan? Munafuka. To yau Allah Ya Toni asirinki." Abin mamaki sai yaga Sam Haj. Kubra bata tsorata da ganin sa ko jin kalamansa ba. Maimakon haka ma sai yaga ta taso daga kan gadon ba tare da ta nemi sanya kayanta dqke yashe a tsakar dakin ba, ta nufi Inda ta yasar da Jakarta ta dauko wayarta ta nufi Inda yake tana kallonshi a shelake fuskarta dauke da murmushin isa da takama, ta danna wasu madannai na wayar kana ta mika masa gami da fadin.
"Ai tayaka nake yi. Gani nayi kamar ka auro mana ita ne, tunda kullum kana tare da ita, ni kuma ka yasar da ni a gida, shi yasa in ka yi nesa da ita ni kuma nake wakiltarka."
Hoton bidiyon ya fara tafiya, yayin da taurarin ciki suka fara motsawa. Hotunan suka bayar da surar Alh. Mahiru kwance shi da wata yarinya suna aikata mashaa. Yarinyar ta tambayeshi.
"Wai Alhaji baka da aurene naga kullum sai ka kirawo ni?" Ya CE da ita. "Ai ni ban yi aure don in rika kasqncewa a gida kullum ba. Nayi aure ne saboda dalilai uku. Na farko don kada mutane su fahimci INA da irinku a waje, dalili ma biyu kuma saboda rashin lafiya in ta kamani, na San irinku matan bariki ba zaku iya jinyata ba, amma ita wacce na aura auren sunnah dole ta yi jinyata. Dalilin na uku kuma shi ne, matata kyakkyawa ce. Ita ce take haskani ta fitar da ni kunya a duk wani taro da zamu yi in har ya hada da matayenmu."
Idanun Alh. Mahiru suka zazzaro ya kalli matarsa kana ya dubi fuskar wayar. Tabbas daya ga daya biyu zata bayar, Wanda ya yi wannan bidiyon shi ne Wanda ya yi na wayar abokinsa Alh Murtala.... Tumaninsa ya katse lokacin da ya ji wayarsa ta dauki ruri alamun shigo war kira. Ya kara wayar a kunnensa tare da fadin "INA jinka Manaja ya aka yi?" A daya sashin aka amsa masa da cewa. "Alh babu lafiya. A halin yanzu Babban reshenmu ya kama da wuta 'yan kwana-kwana sun yi iya yin su, amma basu yi nasara na, komai ya kone." Alhaji mahiru ya fadi kasa sumamme.
Sakamakon da likitoci suka fitar game da halin da Alh. Mahiru ke ciki ya nuna Alhaji yana kamu da matsanancin ciwon zuciya tare da rasa barin jikinsa na hagu.
*** *** ***
A lokacin da Alhaji murtala ya bayyanawa uwar jam'iyya kudirinsa na janyewa daga takarar ba tare dalilin yin hakqn ba, lokacin ya zowa uwar jam'iyya a kure ta yadda hukumar za6e ba zata amince su yi madadinsa da wani Dan takarar ba, hakan na nufin dole jam'iyyar ta rasa kujerar Sanata a yankin, abin ya damu duk wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar wacce ita CE ke da shugabanci a kasar. Ai kuwa ba a jima ba hukumar yaki da handamar dukiyar kasa ta diro masa daga gwamnatin tarayya. Aka haramta masa mallakar wasu manyan kadarorinsa.
Jigon Labarin
1) Yana muna yadda wasu jagorori ke daulashe harkar ilimi don su bar mabiyansu a cikin duhu, ta yadda zasu rasa sanin 'yanci da hakkunansu don kada su basu matsala lokacin farautar kuri'u, ko kuma su zamo jagorori wata rana.
2) Yana bayyana yadda wasu manyan 'yan kasuwa da jami'an gwamnati ke shagaltar da lokutansu a waje saboda tarulam da suka shafi kamfuna ko siyasa, a karshe maimakon su ka ga iyalqnsu, sai su kare ga matayen bariki. Wanda hakan ke sanyawa matayensu tunanin mafita ta kowacce hanya, tunda dai ba zasu iya yiwa hamshakan mazajensu tawaye a raba auren ba, don gudun fadawa hannun talakan DQ ba zai iya biya masu hadamammun bukatunsu ba.
Allah abin godiya.
Karshe.
Iliyas Ishak Gundutse
Shuraih Usman
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels