Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels RUƊANI. Labarin haɗaka (Rukuni na biyar). Rubutu na A. 📝Hauwa Shehu "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'unn, innalillahi wa Inna ilaihirraji'unn, innalillahi wa Inna ilaihirraji'unn. Kalmar da yake ta nanatawa kenan, lokacin da yake tafiya sauri-sauri gudu-gudu rungume da ita a hannunsa. Duk bayan daƙiƙa ɗaya zuwa biyu sai ya kai dubansa gareta, yanayin yadda numfashinta ke tafiyar hawainiya ne ke bashi tsoro, tabbas tana cikin wani hali, kuma komai zai iya faruwa idan ba'a dauki matakin gaggawa ba, hawaye Masu zafi ne kebin kuncinsa. Meyasa wanda ka aminta dashi shine zaici amanar ka? Meyasa wanda ka ɗauka a matsayin garkuwa shi zai jefa ka cikin garari? Meyasa wanda ka ke kallo a matsayin bango shi zai jagoranci rushe taka rayuwar? Wannan wani irin zamani ne muke ciki wanda ƙananan ya'yan mu da ƙannen mu basu tsira ba? Koda kuwa mun kulle su a cikin gidajen mu. Kaico..! Da wannan zamani mai cike da RUƊANI. Da wannan tarin tambayoyin a zuciyarsa ya ƙarasa kofar gidan, ya fara bugawa da ƙarfi, bugu yake ba ƙaƙƙautawa, kamar mai shirin cire ƙyauran. Daga cikin gidan mahaifiyar nurse Hindu ta kalli agogo, ƙarfe biyu da minti goma sha ɗaya na dare. Motsin hindu taji tana ƙoƙarin buɗe kofa, wannan ba sabon abu bane, domin yawanci mata a unguwar idan nakudar dare ta kama su, nan suke zuwa haihuwa. Uhmm....! Allah ya raba lafiya ta mai da kai ta kwanta gami da jan bargo ta lulluɓe fuskarta. A hankila Hindu ta buɗe kofa, turus ta tsaya tana binsa da kallon, cikin mamaki, fargaba da tsoro tace, Aliyu lafiya da wannan tsohon daren? "Lafiyar dai Nazo nema, muna tsananin bukatar taimakon ki a wannan lokacin. Ya faɗa yana kokarin miƙa mata Ilham yarinya yar kimanin shekaru hudu. Touch light din dake hannunta ta kunna tana haska fuskar Ilham Tabbas yarinyar tana cikin mayuwacin hali, numfashinta daƙyar yake fita. To amma me ya sameta? Wannan itace tambayar da Hindu tayiwa Aliyu. Cikin inda-inda yace, "kin gane ko, kawai ina kwance a ɗaki na jiyo ihunta, shine na fito naganta a wannan halin, don haka yanzu ba lokacin bincike bane, rayuwar yarinyar shine kan gaba, don Allah, na roƙeki ki taimaka ki ceci rayuwarta. "Shigo. Ta bashi umarni yayin da ta juya cikin soron ta nufi ƙofar wani daki ta buɗe. Da alama a dakin take duba marasa lafiya idan tana gida. Da hannu tayi masa alamun ya kwantar da ilham akan gadon majinyatar dake dakin. Ba tare da bata lokaci ba ya kwantar da ita sannan yaja baya, ita kuma Hindu ta ƙarasa wajen domin ceto rayuwarta. Wani irin juyowa tayi a ranaze tana masa kallon tuhuma. Jini..! ta furta a kiɗime. Kau da kansa yayi gefe, ba tare da yace komai ba. Itama bata tsammaci jin wata kalma daga gareshi ba, da hanzari ta janye zanin dake jikin Ilham wanda kawo yanzu ya gama jiƙewa da jini. Zaro ido tayi, "Subahanallah..! Ta furta da ƙarfi. Me nake gani haka? Ƙanwar ka, haba Aliyu mai yasa ka aikata haka? Da kinsan kusancin da ke tsakanin mu da wanda ya aikata wannan abun da kin fi haka shiga ruɗani. ya ayyana haka a ranshi. A zahiri kuma sai yace, "Kada ki yanke hukunci akan abinda baki da masaniya, kawai kiyi aikin ki, ni ban aikata komai ba. Babu wani abu da zan iya yi yanzu, domin taɓa Ilham a wannan halin ganganci ne, kawai ku tafi asibiti, ina mai baka shawara da kafin ku wuce asibitin, ka samo jami'in tsaro, idan ba haka ba ko a asibiti bazasu du ba taba, domin matsalar da ta ɗanganci fyade babbar matsala ce. Gumi ne ya fara ƙaryo masa ta ko ina jin an ambaci jami'an tsaro, sam baya buƙatar su a yanzu, zuwa asibitin ma duk bai taso ba, domin yin hakan, tamkar ya sanarwar da duniya abin da ya faru ne, kuma haka zai taɓa martaba da kimar gidansu, wannan matsalar cikin gida ce, kuma a gida za'a magance ta. Daukar Ilham yayi ya saɓata a kafadarsa, cikin kaushin murya ya fara magana. Tunda bazaki taimaka ba shikenan, amma ina so in gargaɗeki da kaga ki kuskura ki bawa Kowa wannan labarin, abinda kika gani a daren yau tattare da yarinyar nan ki ɗauke shi a matsayin sirri wanda zaki adana a zuciyar ki har tsahon rayuwar ki, idan kuma ki kayi gan-gancin furta wata kalma dangane da wannan lamarin to zan iya kashe ki. Bai jira abinda zata ce ba yasa kai ya fice. Imam Abdullahi Usman · RUDANI 002 (Labarin hadaka) Rukuni na Biyar Imam Bandirawo Zuwa yanzu tashin hankalin da yake tattare dashi, ya ninka na d'azu Sau ba'adadi. Yasan dai babu yadda za'ay, yanufi Asibiti da Ilham wacce ke sume Ahalin yanzu ba. Sam wannan maganar ma bata taso ba. Tayaya zai tonawa kansa da Ahalinsa Asiri...? Da wane ido duniya zata kallesu..? Dr emmanual, shine ya fado masa arai. Bugu biyu ana uku ya jiyo muryar likitan, da gurbatacciyar hausar yana tambaya wane. "Babu lokacin yi maka wannan bayani, muna bukatar taimakon gaggawa" Aliyun ya fada, da wata gajiyayyiyar murya. Daga cikin shagon inyamurin likitan ya bude, gami da haskeshi da fitilar touch light, lokaci guda kuma ya kauda hasken daga gareshi. Ga dukkan Alamu, manufar haskashin itace gane da wadda yake magana. Aliyu ya kwantar da ilham, bisa wani dan karamin gado bayan ya shiga dakin. Lokaci guda likatan ya lalubo makunnar lantarki ya kunna. Haske ya wadata a dakin, shikam Aliyu ya rikice, ya rude yarasa Abun yi, duk wani tunani nasa ya kubce. Ya kai dubansa zuwa ga likatan dake kallon ilham cikin halin ko'inkula. "Likita dan Allah ka taimake mu, kada tarasa rayuwarta" Aliyu yafada da wata iriyar marainiyar murya. Lokaci guda likitan ya karasa wajenda ilham ke kwance, gami da dubata. Arazana ya dago yana kallon Aliyu "Taimako na zakai likita dan Allah, ka ceto rayuwarta" likitan ya bushe da dariya gami da dafa Aliyu yace " Ba aikin Allah zanyi maka ba, Aikin kudi zan maka". Yana gama fadin hakan, ya nufi inda kayan aikinsa suke. Acan gida kuwa, Hankalin Umma yai k'ololuwar tashi. Duk tanemi wata nutsuwa tata tarasa. Ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Sai kai, komo take, fargaba, juyayi gami da Alhini sun Addabeta. Muhammad Maiyo Niniko RUDANI 003 Labarin hadaka Rukuni na biyar c Muhammad Maiyo Acan gida kuwa, Hankalin Umma yai kololuwar tashi. Duk tanemi wata nutsuwa tata tarasa. Ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Sai kai, komo take, fargaba, juyayi gami da Alhini sun Addabeta. Taya haka za ta kasance, taki yadda akan abinda ya faru da gaske ne, tafi so a ce mafarki take. Me yasa zai yi wa karamar yarinya irin ilham fyade? yaci amanarta kuma ya zama dole ta dauki matakin da ya dace akai,tunanin halin da ilham take ciki ya kara daga mata hankali. Yanzu ya za ta yi kenan? ya kamata ta nemi Aliyu Tasan a wane hali ilham take ciki. A dai dai lokacin da duk wadannan abubuwa ke faruwa, Ibrahim ne ya kulle kansa a daki, dana Sani da nadamar abubuwanda ya aikata sun cika zuciyarsa, me yasa ya aikata haka yanzu da wane ido zai kalli sauran mutanen gidan? YA kamata ya san abin yi kafin gari ya waye ko dai ya bar musu gidan ne? Domin ya sani tabbas Aliyu ba zai bar wannan magana ba duk da irin kusanci da dangantakar da ke tsakanin su. Gashi Aliyu ne ya kama shi yana yi wa kanwarsa fyade.Nan take tunanin abinda ya faru ya Dawo cikin zuciyarsa. Da misalin karfe sha daya ne na dare abin ya faru bayan ya Dawo gida da tunanin taya zai ga ilham a wannan dare? Sannan taya ya zai fara aikata hakan a gareta? Nan take zuciyar shi ta fara bashi shawarwarin yadda zai bullowa al amarin, bayan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi kawai sai ya nufi dakin sa domain ya jira lokacin da ya gama tsarawa. RUDANI 04 Labarin Haɗaka. Rukuni na biyar (zagaye na biyu) Hauwa Shehu. Bayan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi kawai sai ya nufi dakin sa domain ya jira lokacin da ya gama tsarawa. *** *** *** Sha ɗaya da minti arba'in da taƙwas gida yayi tsit baka jin motsin komai, wannan dalilin ne ya tabbatar masa da cewa kowa yayi bacci. Ya mike a hankali cikin sanɗa, dakin Aliyu dake jikin nashi dakin ya fara lekawa, kwance ya hangoshi kan katifa yana makar bacci. Saɗaf-sadaf ya wuce ta ƙofar dakin umma, a hankali ya murɗa mabuɗin kofar su Ilham, su biyu ne ke bacci a kan gadon ita da yayarta Yusra, Ilham ce muradin sa, saboda da ita suka fi sabawa, kasancewar Yusra yarinya ce mai tsiwa shiyasa baya shiga harkar ta. Hannu yasa ya dauko ta daga kan gadon, firgigit ta buɗe ido tana mutstsuke -mutstsuke ganin fuskar Uncle Ibrahim yasa ta saki murmushi gami da buɗe baki zatayi magana. Da hanzari yasa hannu ya rufe mata baki gami da raɗa mata a kunne. "Akwai sweet da chocolate dayawa wanda zan baki a daki na, kina so ko? Ta daga masa kai alamun "Eh. Dakin sa ya wuce da ita ya zaunar da ita akan katifa ya zube mata tarin chocolates a gaba, ɗauka tayi ta fara sha hankalin ta kwance. A haka ya fara aiwatar da kudirinsa ita kuma batayi yunkurin hanawa ba, domin duk a tunanin ta wasa ne, tunda ko a gaban umma yana ɗaukar ta yayi mata wasa. Shi kuwa ba tare da tsoron Allah ba ya fara ƙoƙarin keta mata haddi, wani irin azababban zafin da ta fara ji ne yasa ta fara kuka tana cewa zafi, zafi. Bai saurareta ba yaci gaba da abin da yake yi domin zuciyarsa ta riga ta kwaɗaitu da aikata hakan. Kamar a mafarki Aliyu ya yake jin kuka ƙasa-ƙasa, tashi yayi zaune ya na ƙara kasa kunne, zuciyarsa tana raya masa a dakin Uncle Ibrahim ake kukan amma ya kasa gasgata ta. Ihu ta saki da ƙarfi a lokacin da mai auku ta auku. A gigice Aliyu ya shiga dakin, abinda idanun sa suka gani ne ya ƙara rikita shi, nan da nan zuciyarsa ta ingiza shi ya fara kaiwa Ibrahim naushi ta ko ina, Ibrahim baiyi yunkurin karewa ba domin zuwa yanzu ya fara nadamar abin da ya aikata, hakan ya bawa Aliyu dama shaƙe Ibrahim a bangon yana kara kai masa kutufo. Umma ce ta faɗo dakin tana tambayar lafiya? Ilham ta hanga kwance a mummunan halin, cikin rashin fahimtar abin da ke faruwa ta ƙarasa gaban Ilham, Ras!! Gabanta yayi mummunan faɗuwa. Inna'lillahi wa innailaihirraji'un, nan da nan zuciya ta karye, ƙafafuwan ta suka fara kyarma da har suka gaza daukar ta, durƙushewa tayi ta fashe da kuka mai tsanani ta na jijjiga Ilham tana faɗin karki mutu, don Allah karki mutu Ilham. Dai-dai lokacin Aliyu ya saki Ibrahim ya nufo kansu, ganin halin da Ilham ke ciki ya sa ya dauke ta, cikin dauriya yacewa umma kiyi hakuri zan kaita a dubata yanzun nan, Bazata mutu ba umma, Ilham bazata mutu ba, Insha Allahu. Lokacin da Ibrahim ya gama tunanin abin da ya faru a wannan daren sai ya sake fashewa da kuka, yayi nadamar abin da ya aikata, to tayaya akayi yaci Amanar Wanshi da matar Wan nashi, da ma ita kanta Ilham. mutanen da suka amince masa. Musambabin zamanshi a gidan shine don ya zama garkuwa a garesu, ya cike gurbin ɗan uwansa mahaifin Ilham idan baya gari, saboda ya kasance matafiyi ne. Ilham itace yarinyar da yafi so a duk duniya saboda tsabar shaƙuwa har kiransa ake yi da Dadyn Ilham, to amma wani irin son zuciya ne ya kaishi ga aikata mata haka? Yarinyar da aka haifa a gabanshi, ya kuma reneta, shin me yaja hankalin sa game da ita? Tabbas wannan sharrin shaidan ne. A bangaren Dr. Emmanuel kuwa ya shefe sama da minti talatin a kan Ilham, kafin ya juyo ga Aliyu yace " Munci Nasara aiki da dai-dai ta numfashinta. RUD'ANI 005 Labarin had'aka ( Rukuni na biyar) Imam Bandirawo✍️✍️ Wata matashiyar nutsuwa ce ta ziyarci zuciyarsa. Ya kalli Ilham dake kwance magashiya, sai yanzu wasu siraran Hawaye suka samu nasarar fitowa cikin kwayar idanuwansa. Dr emmanual ya cigaba da aikinsa na kokarin ceto rayuwar yarinya ilham, wacce ke kwance rai A hannun Allah. Bayan zuwa wani lokaci, likitan ya d'ago, ya dubi Aliyu dake zaune yace " yanzu nayi mata Allurar bacci, zata samu nutsuwa, zuwa wani lokaci. Zaka iya kwantawa kai bacci zuwa wani lokaci." Gama fadin hakan keda wuya, likitan ya nufi kofar ficewa cikin shagon, wacce zata sadashi da cikin gidansa. Koda zuwansa bakin kofa, yaja ya tsaya, bayan ya riqe kofar gami da bushewa da wani murmushi marar fassara, yace "ina fatan bazaka manta cewar aikin makudan kudi nai maka ba?" Yana gama fadin hakan ya bace daga dakin. Aliyu yai ajiyar zuciya gami da jinginar da kansa da bangon shagon. Kamar yadda Aliyu bai runtsa ba, hakama A bangaren umma. kwana tai tana kaikoma, har yanzu da tasoma jin Alamun kiraye kirayen Sallar Asubahi. Aliyu rungume da Ilham, ya shigo gidan, jikinsa A mace. Cikin hanzari umma ta karasa gareshi. Sai dai kuma, jin jarumin namiji kamar danta Aliyu yana shesshekar kuka Ya sake daga mata hankali. "Shikenan Abinda Ake gudu ya faru" ta fada aranta. " umma ta mutu" muryar Aliyun cikin shesshekar kuka, ta tabbatar mata mugun hasashenta. RUDANI 006 LABARIN HADAKA RUKUNI NA BIYAR C Muhammad Maiyo "Shikenan Abinda Ake gudu ya faru" ta fada aranta. " umma ta mutu" muryar Aliyun cikin shesshekar kuka, ta tabbatar mata mugun hasashenta. Nan take ba tare da bata lokaci ba umma tayi kasa ta fadi sumammiya. Hankalin Aliyu ya kara tashi ya rasa ya zai yi, ga gawar ilham a hannunsa ga kuma umma ta suma, ya shiga RUDANI da rashin me ya kaamta yayi. Nan take ya fara karanta innalillahi wa inna ilaihirraji un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha. Da taimakon Allah ya samu nutsuwa a cikin zuciyarsa, ya ajiye gawar ilham a gefe guda sannan ya nufin kan mahaifiyarsa umma domain ya ceci ranta, bayan daukan wasu dakikai da yayi akanta cikin taimakon Allah sai ta samu ta farfado. Shi ko Ibrahim tun a daren da abin ya faru ya samu ya sulale daga cikin gidan ba tare da sanin kowa ba, nadama da danasanin abinda ya aikata sun cika masa zuciya, har yaji ya fara tsanan kansa, ya aikata abinda har ya koma ga ubangijinsa ba zai taba mantawa ba. Da wane ido zai kalli Aliyu sannan da wane ido zai kalli mutanen cikin gidansu duk da amince masa da suka yi? ya sani baza su taba yafe masa ba. Taya zai fuskanci Dan uwansa da wannan con amanar idan ya dawo? Nan take ya yankewa kanshi abinda ya kamata yayi idan gari ya waye. A can cikin gida kuma da safe mutanen cikin unguwa suka tashi da labarin rasuwar ilham. Nan take jama a suka taru aka yi jana izarta aka kaita gidan gaskiya. Bayan da jama a sun fara raguwa sai Aliyu ya samu mahaifiyarsa a gefe suka tattauna akan matakin da ya kamata a dauka a kan Ibrahim don bai kamata a kyale shi ba. Har garin Allah ya waye Ibrahim bai samu ya runtsa ba, kana ganin sa kasan yana cikin damuwa. Da misalin karfe tara na safe Ibrahim ya kai kansa police station, ya mika kansa ya tabbatar musu da cewa shi mai laifi ne a kama shi, domin kuwa ya aikata fyade a yar yayansa. Saboda haka ya kawo kansa da kansa domin a yanke masa hukunci. Alhamdulillah a nan muka kawo karshen labarin littafin RUDANI. Wanda muka rubuta Hauwa shehu Imam Bandirawo Muhammad Maiyo Muke muku fatan alkhairi. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 1 of 1