shiru, dan babu mai rarrashin ta a kusa, Toilet ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta zauna kanta na mata wani irin ciwo, ga yunwa dake nuk'urk'usar cikinta dan bata karya ba ta tafi school. Da k'yar ta daure ta yi Sallar sannan ta sakko ƙasa, tea ta haɗa mai kauri tasha, duk da tasha tea d'in amma ba ta dena jin ba daɗi a jikinta ba, haka dai ta daure ta shiga kiciniyar ɗora girki kar Mama ta dawo ta tarar ba ta yi ba. Washegari ta tashi ba ta jin daɗin jikinta ko kaɗan, amma ta ta'allak'a hakan da period ɗinta da ya kusa, dan ta na cin wahala ba kaɗan ba idan za ta yi. Ta na kwance a kan gadonta lullub'e da duvet Mama ta shigo ɗakin, Janye duvet d'in Mama ta yi ta na faɗin "Neehal wanne irin bacci ki ke haka har 10 ta wuce ba ki tashi ba?" Neehal ta buɗe idonta a hankali ta ce "Ba na jin daɗi ne Mama" Mama ta ce "Ayya sorry Daughter, Month ɗinki ya yi ko, ki tashi ki lallaɓa ki yi wanka ki sha ko tea ne, sai kisha magani" Neehal ta ce "Ai bai zo ba,ciwon kawai na ke ji" Mama ta ce "Ki dai tashi ki sha" Neehal ta yunk'ura ta tashi zaune tana taune lips d'inta.
Ƙarfe 12 Aunty Sadiya ta ƙaraso gidan da atamfofi da leshuka da yadin bridal shower na k'awayen amarya, aka zube su a falo. Neehal ta na kwance a kan doguwar kujera ba ta ko motsa ba duk da ta na jin duk budurin zuwan Aunty Sadiyan, sai ma runtse idanunta da ta ƙara yi zuciyarta na bugawa. Aunty Sadiya ta kalli sashen da take ta ce "Neehal lafiya kuwa take bacci da ranar nan?" Mama ta ce "Ba ta jin daɗi ne, ciwon mararta ne ya tashi, amma na bata magani tasha, shine bacci ya ɗauketa" Aunty Sadiya cike da tausayawa ta ce "Ayya Allah ya ba ta lafiya, Amarya ba lafiya ai babu kanta, dan ma insha Allahu ta na yin Aure za ta dena ciwon marar" Mama ta ce "Allah ya sa, kin san ta da shegen shan zak'i kamar me, na hanata na hanata amma ta ƙi denawa" Aunty Sadiya ta ce "Allah ya sauwak'e, bari na kira Haneefah ta zo ta ɗibi na freinds ɗinsu" Mama ta ce "Ya kamata kam, tunda bikin ya matso su kai ɗinkuna, nima bari na ɗibi na mutanena." Su na duba kayan su na cigaba da tattaunawa akan bikin, Mama ta na sanar da Aunty Sadiya Abubuwan da za'ayi, ba wani jan bikin za'ayi ba, Events uku kawai za'ayi, daga Kamu/Mother's day, sai Dinner da Yini, sai bridal shower na k'awayen Amarya. Gabad'aya sun riga da sun yi bucking na events din da za'ayi, duk wata siyayya ta Amarya itama sun kammala ta, yanzu lefe kawai suke jira sai a sanya satittikan bikin. Sai da Haneefah ta zo sannan ta tashi Neehal daga baccin gasken da ya d'auketa, ta tashi zaune ta na taune lips ɗinta, ka na ganinta ka ga mai cuta, Aunty Sadiya da Haneefah suka shiga yi mata sannu. Mama ta kawo mata abinci ta ɗan tsakura ta ci ta ƙara shan magani, ranar dai haka ta wuni ba ta jin daɗi, Anwar da su ka yi waya hankalinshi ya tashi da ya ji ba ta da lafiya, sai da ya zo ya duba ta da daddare hankalinsa ya ɗan kwanta, tun da ya ga jikinta ba rijib take a kwance ba. Washegari, ta tashi jikin nata da sauƙi, dan period d'in nata bai zo ba har yau, yau ma exam d'in safe ce da su, amma ba ta dawo ba gida da wuri ba, saboda sun tsaya ɗaukar pics da friends ɗinta, tunda sun gama exam d'in sai dai fatan samun result mai kyau, suka yi sallama da freinds ɗinta su na faɗin sai sun zo bikinta, ita dai Neehal yaƙe kawai take yi dan zuciyarta babu daɗi ko kaɗan. Ta na dawowa gida Mama ta sanar mata da zuwan wadda za ta mata gyaran jiki daga Maiduguri gobe Insha Allah, Hajiya ma goben za ta zo tunda ran Lahadi za'akawo lefe amma maza ne za su kawo.
Da daddare Neehal ta na kwance a ɗakin Mama, sai juyi take akan gado saboda murd'awar da cikinta yake mata, hawaye ne kawai yake fita daga idanunta, wani amai ne ya taho mata ta tashi da gudu ta nufi toilet ta shiga kelayashi, ta na yin aman ta na jin fitar jinin a jikinta, Ta na sassauke Numfashin azaba ta gyara jikinta ta sanya pad, kuskure bakinta ta yi ta janyo ƙafarta da ta fara riƙe mata ta dawo ɗaki ta kwanta. Mama ta shigo ɗakin ta dube ta cikin tausayawa ta ce "Sannu Daughter ya jikin?" Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" Sosai Mama take tausayin Neehal lokacin period ɗinta, saboda azaba take sha ba ta wasa ba, ciwon mara, baya, k'ugu duk take yi, ƙafafunta duka su riƙe, yau ko gurin aiki ba ta je ba, sai Haneefah ce ta je ta maye gurbinta. Time ɗin da Dad ya zo dubata bacci ya ɗauke ta. Washegari dai da ta tashi jikin nata da sauƙi sai dai ba ta warware tas ba. Da safe ta na cin Irish da soyayyen kwai ɗin da Mama ta kawo mata ta tilasta mata ta sha Ameen ya shigo ɗakin, jin kamashin turarensa ya sa ta d'ago kanta da sauri ta na kallonsa, gabanta ne ta ji ya fad'i ba ta san dalili ba, satar kallonsa ta shiga yi ta ga ya canza sosai ba kamar kwanaki ba, ramar da ya yi duk babu ita sai ma wani fresh da haske daya ƙara, lumshe idonta ta yi a hankali ta ce "Ina kwana?" Kamar bai ji ba sai kuma can ya ce "Lafiya, ya jikin? Ba ta yi mamakin sanin ba ta da lafiya da ya yi ba, domin kowa na gidan ya san time ɗin period ɗinta saboda azabar da take sha a lokacin yin period ɗin nata. Cikin raunin murya ta ce "Da sauƙi" Juyawa ya yi ya fita ganin Mama batanan, a falon ƙasa su ka haɗu da Mama ta dawo daga part din Dad, Mama ta na dubanshi ta ce "Welcome, har ka zo kenan?" Ya ce "Ehh, ina kwana?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau, ya aiki" Ya ce "Alhamdulillah, ya naku?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau" Zai nufi part d'in Dad Mama ta ce "Idan ka dawo ina son ganinka" Ya ce "Toh." Misalin ƙarfe goma na safe Aunty Sadiya da Aunty A'isha da yarinyar gurinta Maryam su ka zo gidan, domin yin snacks na karɓar kayan lefe, Neehal dai ta na shan Magani ta kwanta bacci ya ɗauketa dan jiya ba ta samu wani baccin kirki ba, saboda ciwo. Yauma ba ta samu damar zuwa gurin aiki ba, Hajiya da yamma ta ƙaraso gidan da tulin kayanta dan sai bayan biki za ta tafi, wadda za ta yi wa Neehal gyaran jiki Mama ta kira ta, ta ce ta bari sai Monday tun da Neehal ɗin ba ta jin daɗi. Bayan sallar isha'i bayan su Mama sun gama aiki ta samu Ameen a ɗakinsa, Ameen ya tattara duka hankalinshi akan Mama jin ta ce za su yi Magana. Mama tana dubanshi ta ce "Gobe za ka koma Lagos ko jibi?" Ya ce "Gobe da safe" da mamaki Mama ta ce "Da safe kuma?" Ya ce "Ehh" Ta ce gobe fa za'akawo lefen Neehal kuma sai da yamma, kuma maza ne za su kawo" Ya ce "Am sorry Mum, amma ba zan samu damar tsayawa ba, dan akwai wani important thing da zan yi" Mama ta ce "Sunday ce fa, saboda gudun haka fa ya sa aka sa weekend, kar wani uzurin ya tsaida wani" ya yi shiru bai ce komai ba, Mama ta mik'e ta ce "Dole ne koma uzurin mene da kai ka jira a karb'i kayan da kai, ka ji na faɗa maka" Ta na faɗin haka ta fice daga ɗakin, Ameen ya bita da kallo.
Washegari Sunday Ranar kawo kayan lefe, tun safe su Mama su kai packagin kayan snacks d'in da soyayyen naman kaza gami da lemuka, yamma kawai suke jira masu kawo kayan su zo. Neehal yau ta lallaɓa ta shirya ta tafi gurin aiki, duk da Mama ta so hanata amma ta ce mata ta ji sauƙi za ta iya zuwa. Mama na kitchen Ameen ya shigo ya same ta da shirinsa na tafiya. Mama ta masa wani kallo bayan ta amsa sallamar da ya yi, Ya ce "Ina kwana Mum" Mama ta ce "Lafiya k'alau" Ya ce "Am sorry Mum zan wuce Lagos yanzu, nima ba son raina ba ne uzurin da zan yi a can mai ƙarfi ne" Mama ta ce "Uhm, uzurin har na fi umarnina kenan a gurinka?" Ya ce "A'a Mum, kar ki ce haka Please" Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa, Ya ce "Am sorry" Mama ta ce "Na yi sorry ɗin ka je Allah ya kiyaye, amma ka sani ko kananan ko ba kanan ba za'a fasa komai ba, idan ma ka ga dama karka halacci taron bikin" ya yi murmushi kawai ya ƙaraso kusa da ita ya yi hugging d'inta tare da faɗin "Thank you Mum, Allah ya sa su zo lafiya su tafi lafiya bye" Mama ba ta ce komai ba, ya sake ta ya fice. Mama ta bishi da kallo, abinda ya sa ta barshi ya tafi tasan uzurin da yake faɗa ba ƙarami ba ne, dan Ameen ba ya taɓa mata musu a kan duk wani abun da za ta sa shi ya yi, komai wuyarsa kuwa.
Ƙarfe 12 na rana Mama su na zaune a falo ita da Hajiya da uncle Mahmud da ya zo shima dan karɓar lefen ɗin, wayar ta shiga ringing, ɗauka ta yi ta duba ta ga Ammin Anwar ce ke kiranta, murmushi ta yi ta d'aga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama, ba tare da Ammi ta amsa sallamar da Mama ta mata ba, cikin tsananin ruɗu da matsanancin tashin hankali ta ce..........✍️
_*Duk mai son shiga group ɗin NEEHAL FAN'S ta mun magana ta Number na 09066710753, amma in kin tabbatar za ki na comments and share.*_
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*0️⃣4️⃣*
.............Mama bayan ta gama haɗa break fast din ta ɗibi na Dad ta haɗa masa a cikin tire, tana ƙoƙarin fita Dije mai aiki ta shigo kitchen d'in, ta risina ta ce "Ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya kalau Dije, yawwa dama na gama sai ki haɗa wanke_wanke ki yi ki gyara kitchen d'in" cikin girmamawa Dije ta ce "Toh Hajiya" Mama ta fita daga kitchen d'in, Zulai mai aiki ta na mopping a falon, ganin Mama ya sa ta ajiye mopper ɗin hannunta ta taho da sauri ta na faɗin "Sannu da fitowa Hajiya" Mama ta ce "Yawwa mun tashi Lafiya" Zulai ta ce "Lafiya ƙalau Hajiya" tana ƙoƙarin karɓar kayan hannun Mama, Mama ta ce "Ki barshi ki je ki ci gaba da aikin ki kawai, idan kun gama sai ku ɗibi abinci a kitchen ku karya" Zulai ta ce "Toh Hajiya" ta koma ta cigaba da aikinta, Mama kuma ta nufi part din Dad.
Dad ya na bedroom d'insa, Mama ta ajiye masa break fast d'insa a kan dinning sannan ta nufi bedroom d'innasa, da sallama ta shiga ya na zaune akan gadonsa ya na operating system, d'agowa ya yi ya na duban Mama tare da amsa mata sallamar da ta yi, Mama ta zauna a gefensa ta na faɗin "Your break is ready" Dad ya yi murmushi ya ce "Godiya nake matar Aljannah" Mama ta yi murmushi ta tashi ta ɗauke system ɗin gabansa ta ajiye a kan bedside locker ta ce "Mu je ka yi break idan ka gama sai ka cigaba da aikin" Dad ya yi murmushi ya mik'e ya bi bayan Mama suka fita zuwa falonsa, Mama ta koma ta ɗauko tea plaks ta dawo ta yi sarving ɗin su suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bayan sun gama Mama ta yi hamdala ta na goge bakinta da tissue ta ce "Wai Ni kuwa Dad ya ku ka yi da Son jiya?" Dad ya ce "Na masa magana a kan ya kamata zuwa yanzu a ce ya na da iyali shima ya ce Insha Allah bayan bikin daughter zai fitar da mata shima" Mama ta sauke numfashi ta ce "Amma Dad me ka fuskanta ya na damun Ameen, tun jiya da yawo gabad'aya hankalina ya kasa kwanciya da yanayin da na gan shi" Dad ya ce "Nima a nawa ɓangaren hakane Doctor, abun da ya ƙara tayar mun da hankali da Muhammad ramar da ya yi da kuma yanda ka na kallonshi za ka hango zallar damuwa a tattare da shi, kuma duk abin da yake damun Muhammad ba ƙaramin abu ba ne, dan kin san Muhammad tun ya na ɗan ƙaramin shi, yaro ne mai juriya, haƙuri, kawaici gami da tawakkali, zai yi wuya ka gane ya na cikin damuwa ko ka fuskanta, idan har ba shi ya furta maka ba, wannan dalilin ya sa nasan lallai abin da yake damunsa ba ƙaramin abu ba ne" Mama ta sauke wani gwauran numfashi tare da dafe kanta ba ta ce komai ba, Dad ya kama hannunta cikin lallami ya fara mata magana da faɗin "Kinga Doctor ki kwantar da hankalinki, Insha Allahu ba wata matsala ba ce, ba na son in ga kina damuwarnan, kamar yadda ya ce mu dinga masa addu'a ki dinga masa, Insha Allahu koma meke damunsa Allah zai yaye masa" Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya sa" Dad ya saki hannunta tare da mik'ewa ya na faɗin "Yawwa ko kefa, ba na son na ga ki na yawan damuwarnan ko kaɗan, dama naga kwana biyu kin ɗan fa ɗa" Mama ta mik'e itama ta na faɗin "To ba dole ba Dad ka ga ina rama, autatah za ta tafi, ai ahakanma ina ƙoƙarin b'oye damuwata dan kar ta damu itama" Dad da ya fara tafiya ya ce "To ya za'ai sai haƙuri, Ni kaina na fara kewar daughter tun yanzu"
Bayan Mama ta gama gyara part d'in Dad ta haɗa masa ruwan wanka ya yi, ta dawo part d'inta ta baro shi ya na aiki tun da Yau Sunday ba fita zai yi ba. Ɗakin Hajiya ta shiga ta tarar da ita ta na haɗa kaya, Mama ta zauna a gefen gado ta ce "Hajiya ashe kin tashi, har General ya na cewa zai zo ya gaishe ki, na ce ya bari sai anjima dan nasan da k'yar in kin tashi" Hajiya ta ce "Na tashi mana, ko zan zauna ina ta barci har wannan lokacin kamar wata marar aikin yi" Mama ta ce "ai na san ki ne Hajiya da son bacci" Hajiya ta ce "To yau ban yi ba, tun ɗazu na tashi nake haɗa kayana ba sai goben ta yi Mahmud ɗin ya zo ba in yi ta kame_kamen ban gama shiri ba" Mama ta ce "Ai da kin barshi Hajiya na haɗa miki ko kuma na turo su Dije su haɗa miki, tun da ko karyawa ba ki yi ba" Hajiya ta kama hab'a ta ce "Rufa mini asiri, masu aiki da haɗa mun kaya, lalacewar tawa bata kai haka ba, kema na hutashsheki tun da ba wani abu na aiki nake a gidan ba, dan haɗa kaya dai ba zai mun wahala ba" Mama ta ce "Shikenan bari na kawo miki abincinki" Mama ba ta jira amsar Hajiya ba, ta mik'e ta fice.
Ƙarfe 11 Ameen ya shigo falon Mama, su na zaune ita da Hajiya suna kallo, Mama ta bishi da kallo har ya zauna a gefenta, cikin muryarsa kamar baya son magana ya ce "Morning Mum, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya k'alau and you?" Ya ce "Fyn" Mama ta ce "Masha Allah, yau za ka wuce Lagos ɗin ko sai gobe?" A hankali ya ce "Tomorrow in the morning" Mama ta ce "Allah ya kai mu" Hajiya dake saurarensu ta keɓe fuska ta ce "In Mutum bai kula ni ba, sai me? Daga yau ma ba ƙara gani na za ka yi a gidanku ba, sai wani lokacin kuma" ɗan Murmushi Ameen ya yi bai ce komai ba, sai ma mik'ewa da ya yi ya nufi part d'in Dad, Hajiya ta bishi da harara" Mama ba ta ce komai ba, sanin da ta yi ba'a shiga tsakanin Hajiya da Ameen, dan Hajiya ko wata ta yi ba ta zo gidan ba, da kanshi ya ke zuwa har Gombe ya ɗaukota.
Kafin la'asar Neehal ta dawo gida, tare suka taho gidan yau da Haneefah, a falo suka tarar da su Mama da kannenta guda biyu mata masu kama da ita, sun zo yiwa Hajiya sallama, Aunty A'isha da Aunty Sadiya, Neehal ta tafi da sauri ta rungume Aunty Sadiya dan tafi kusa da kofa, Haneefah kuma ta rungume Aunty A'isha, Neehal ta ce "Aunty Sadiyata welcome" Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Yawwa my daughter, ya aiki?" Neehal ta ɓata fuska cike da shagwab'a ta ce "Alhamdulillah, sai gajiya" Aunty Sadiya ta ce "Sorry dear, za ta tafi itama" sakin Aunty Safiya ta yi ta koma ta yi hugging Aunty A'isha tare da gaisheta" Aunty A'isha na murmushi ta ce "Lafiya k'alau, Neehal yanzu an gujeni ko, yaushe rabonku da gidana" Neehal ta ce "Kai Aunty ko wata fa ban yi da zuwa ba" Aunty Aisha' ta ce "To ai da ko sati ba kya yi ba ki zo ba, ko Anwar d'inne ya hana ki fita?" Haneefah tay karaf ta ce "Baruwan Angonmu, Mama ce ke hanamu fita" Mama ta harare ta ta ce "Ta yaya zan bar ku ku fita ba'amun aiki ba, duk randa fa ba su je aiki ba ko school, wuni suke a d'aki su na shiririta, sai na je na fatattako suke saukowa su yi abun da ya dace, can gidan Barrister ma ta ce in sun je haka suke, kamar wasu yara" Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, ta zauna kusa da Hajiya, wadda ta ƙurawa TV ido ta na kallo. Aunty A'isha ta yi murmushi kawai, Haneefah ta dubi Aunty Sadiya ta ce "Aunty Sadiya dama ina shirin kiranki, wasu freinds ɗinmu sun turo mun kuɗin ankon Neehal bari na miki transfer yanzu" Aunty Sadiya ta ce "Toh, na atamfa ne ko na less?" Haneefah ta ce "Duka" Neehal ta lumshe idonta gabanta na faɗuwa, tunawa da ta yi nan da 2 months fa inda rai da lafiya an yi aurenta, shikenan za ta bar Mamanta da Yayanta da Dad ɗinta mutane mafi soyuwa a gareta, ƙoƙarin mai da kwallar da ta ciko idanta ta yi ta mik'e ta wuce sama. Da yamma bayan su Neehal sun ci abinci sun yi wanka suka tafi gidansu Haneefah, Mommy ta na zaune a falo suka shigo gabad'aya suka yi kanta suka ruk'unk'ume ta, Mommy ta ce "Uhm, Allah ya kawo ku, Kwana biyu bakina shiru amma yau za ku zo ku samun ciwon kai" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kai Mommy ko irin yar tarb'ar nan ma babu" Mommy ta ce "Ban san ta ba, ba kuma zan yi ba, a ɗaga mun jiki Ni, ba daɗi nake ji ba" Haneefah ta tashi daga jikin Mama tana faɗin "Shiyasa wlh gwara gidan Mama sau dubu da nan" ta ƙarashe zancen ta na shigewa kitchen. Mommy ta ce "Ni da za ki tattara kayanki, ki koma gidan Maman da kin taimaka mun" Neehal ta yi dariya ta ce "Ai ba za ki iya kwana 2 ba ki ga Besty ba, abun da ko kwana ɗaya ta yi kinta kiranta a waya kina ta dawo" Mama ta ce ''Ai dan ba Ni da mai mun aiki ne, amma ba wai kewarta nake ba" Haneefah ta dawo falon ta na duban Mama ta ce "Mama cake za mu yi wa ya Anwar, na gidan Mama kwananne ne, kuma na duba kitchen kamar ba ki da butter" Mama ta ce "Babu kam, amma bari na ba wa idi ya karb'o, tun da ɗana za'aiwa" Neehal ta ce "Au da mu za mu ci, ba za ki bayar a siyo ba?" Mommy ta ce "Sai dai ku siyo da kanku ko kuma ku haƙura da cin" Haneefah ta ce "Mommy nan da wasu watanni fa kin dena ganinmu a kai a kai, ki dinga lallaɓamu fa" Mommy ba ta kula ta ba ta shige ɗakinta dan ɗakko kuɗi. Neehal ta dubi Haneefah da damuwa a fuskarta ta ce "Besty Yau gabad'aya ban ga Yayana ba, ba na jin daɗi" Haneefah ta ce "Why?" Neehal ta ce "Da safe da zan fita, na san ya na bacci, da muka dawo kuma ban ga car ɗinshi ba, na tambayi Mama shi, ta ce sun fita tare da Dad" Haneefah ta ce "ki kirashi mana" Neehal ta ce "Good idea" ta ƙarashe zancen tare da zaro wayarta daga cikin small handbag ɗinta mai kyau, kiran duka numbobin sa ta yi amma bai ɗauka ba.
Bayan Magriba Neehal na zaune a gaban madubin ɗakinta ta na d'aura ɗankwalin atamfar da ke jikinta, dawowarta kenan daga gidansu Haneefah ta sauya kaya ta fara shiryawa kafin Anwar ya ƙaraso. Wayarta dake kan mudubinne ta fara ringing cikin amon sautin wak'a mai daɗi irin ta masoya, murmusawa ta yi ta kai hannu ta ɗauki wayar dan tasan Anwar ne ya ƙaraso tun da shi kaɗai ta sawa wannan ringintone ɗin, ta ɗaga kiran tare yin sallama cikin siririyar muryarta, Anwar ya amsa tare da faɗin "Gimbiyata na ƙaraso" ta yi murmushin jin daɗi mai sauti ta ce "You Are Welcome Sir" shima murmushin ya yi tare da katse wayar, Neehal ta ƙarasa daurinta ta feshe jikinta da da daɗaɗan turarukanta masu sanyin ƙamshi, wanda idan mutum ba matsowa kusa da ita ya yi ba, ba zai ji k'amshin ba. Ɗakin Mama ta lek'a ta sanar mata Anwar ya zo ta fita, Mama ta ce sai ta dawo, ta kuma gaishe da Anwar ɗin, a falon ƙasa ta tarar da su Dije su na kallo, ta dube su ta ce "Aunty Dije dan Allah idan babu damuwa ki ɗan biyo ni da cake ɗin can, zan ɗau drinks ne" Dije ta je "Haba uwar ɗakina babu damuwar komai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Toh Nagode" Zulai ta ce "Kawai ki wuce zamu kawo miki har ruwanma, kar yay ta jiranki" Neehal ta ce "Toh Nagode sosai"
Ya na zaune a kan fararen kujerun da suke zama koyaushe dan yin zancen, ya na latsa wayarsa, ya na sanye cikin wata shadda light blue, da ta haska choculate colour ɗin fatarsa wadda ta nuna zallar jin daɗin da yake ciki, Anwar Kyakkyawane a jin farko a sahun kyawawa, dogo ne amma bashi da jiki sosai. Neehal ta ƙaraso gurin tare da yin sallama, Anwar ya d'ago ya na bin ta da wani kallo k'auna, wadda ya sata saurin sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya, ya amsa mata sallamar ya na ƙara k'ura mata ido, Neehal ta turo baki gaba cikin shagwab'arta ta ce "Ina yini" ya yi murmushi ganin yanda ta yi, kasancewar gidansu Neehal akwai wadatuwar haske sosai komun dare, shiyasa ya ke kallonta tar" ya ce "Lafiya k'alau, ya Mama" ta ce "Tananan k'alau ta na gaisheka" ya ce "Ina amsawa tare da ajiye wayarsa a kan ɗan table ɗin robar da ke gabansu, cike da soyayya da kulawa ya ce "Me ya faru ne, na ga kamar Queen na fushi da Ni" Neehal ta ƙara shagwab'e fuska ta ce "Nothing, kawai kai ne na ga ka na ta kallo na" murmushi Anwar ya yi me sauti ya ce "Dan mutum ya kalli matarsa laifine, ni fa gaskiya kunyar nan ta ki ta na cutata, dan ma kwanaki kaɗan suka rage ki zama mallakina na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 66