ya cika!! Akwai matsala kenan!!!
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
27
Ummul dai yau ta shirya zuwa yawon zaga garin dabatasan wane garin bane, dan haka ta fito da hijabin ta sanye tana neman hanyar daze sadata da gate d'in gidan tayi hanyar waje abinta kan Ameen ya dawo.... Tana k'arasawa taga gate d'in a k'ulle ta ciki mamaki ya kamata ta shiga waige waige, idan har aciki aka rufe toko tabbas da akwai wanda ya rufe d'in tunda Ameen baya nan me hakan yake nufi kenan? Tasoma shiga ko kwanto game da al'arin Ameen, ga alama ma babu wani gida a kusa dasu bata hango roof ata saman gidan ganin tunanin ta baze k'areta da komai ba ya sanya ta juya kawai zuwa cikin gidan kanta yana matuk'ar sara mata tana cikin k'unci da bak'in ciki da takaicin kalar rayuwar datakeyi.....
***************
Islam tanaso tace zataje gun Hafsat amma bataga fuska ba agun maheer, hasalima tun daga ranar bata k'ara ji yayi maganar hafsat ba, takula yaji haushin abinda ta masa......Haka ta daure ta kirasa a awaya
"Honey dama zancene dan Allah kozanje na duba hafsat?"
"Ok kamala yana zuwa nanda 30 mns" shine abinda ya fad'a tare da katse kiran... Bata wasu en damu ba dai tace "Nagode honey" Bece k'ala ba ya datse kiran...ranshi a matuk'ar b'ace yake dukkanin abinda Anty Nasara ta aikatawa Hafsat a kunnen sa yana ji, kasa tsayawa jin sauran yayi islam ma ya d'auki wayar tane sabida ya kula rashin walwalarsa ya sanyata acikin damuwa, ita kuwa Anty wlhy dashi take zancen!!
*************
Be nemi Hafsat ba yabar gidan gaba d'aya koda islam tazo shi yabar gidan, A d'aki ta samu Nanuwa tana kukan ta juyin duniya tayi amma tak'i sanar mata me aka mata, sema daga baya takewa islam magana ta roki a karb'o mata kayanta daga kano gaba d'aya.....
****************
Bayan isha ya shigo part d'in nasu,kai tsaye d'akinsu ya nufa su yaran su sophie, bayan sun gayar dashi ya kallesu fuska a had'e
"Zuwa nayi in gayamuku naji dukkanin abinda Nasara ta sakaku kukayi ina tsaye jikin k'ofar d'akin kuma ke shauty na tabbatar kin ganni ko? Toku sani wlhy dama kunsan halina, kuskure daya naji kunwa yarinyar cen Allah ne kadai ze rabani daku, danjin zataje london tare daku bashi zesha a kitsa muku mugun abu kuma ku dauka ba, ina gargadin ku akan fita harkar ta idan ba hakaba zan muku mummunan hukunci kuma zan gayawa Abba ya miyar daku Bayero university duk a huta" Am batar za'a maidasu nan yafi komai d'aga musu hankali suka hau ban baki da ban hakuri....daganan d'akin Nancy ya wuce ya tarar islam na ciki suna tare, bayan sun gaisa yace da islam
"Zamuje gida ki sauka k'asa kiwa Umma sallama" Ba musu tawa hafsa sallama ta sauka ya fuskance ta sosai
"Na sanarwa Baba iro ya bayarda kayan ki dake kano duka, credentials dinki kadai nace ya turo a motan haya gobe, to ma driver daya kaishi ze dawo dasu,koda wani matsalar ne?
" Ni a gaskiya da akwai sababbin kayana fa danakeso acikinsu, kayana na bikin ummu da komai fa yanacen, hijab dayane anan kuma babu Niqafi" kallon mamamki ya mata yace
"To Nancy ba anan sena siya miki wani kayan ba" mik'ewa tayi ta soma doddoka k'afanta a k'asa
"Wlhy Allah ni inason kayana, dan annbi kace a kawomun" shiru yayi nad'an lokaci kanya zaro waya ya kira Baba iro akan a hado da wasu daga cikin sababbin kayanta da kuma takardun sannan nikafanta amma banda hijabai.....Ba msu yace to ya kalleta
"Ya isa,hijaban ki shirya gobe zakuje da islam kasuwa seku siyo ko kuwa?" Shiru tayi secen tace
"Yaa Maheer inason inga ummana dake Niger kan in tafi inda kukace" Dariya ta bashi wai inda kukace😀 .....
"Nanda kwanaki uku ki shirya nizan kaiki da kaina" murna tashigayi har ya hango hakan zataje Niger, Sophy ce ta rugo d'akin
"Yaa Maheer wai kazo inji umma, anty islam daga tasha agwaluma taketa kelaya amai harta kasa tashi ma" Yariga ta fice a d'akin da gudinshi yaje k'asa, be damu da umman dake kusa da islam ba ya d'ago ta zuwa jikinsa, kallon umma yayi sabida neman k'arin bayani tace
"Kaga waifa agwaluma yaran nan kesha shine tana ganinshi tayi zallo abata, anan gidan ko girkinmu batasanci sabida kunya har nayi mamakin agabana take cewa a samma ta abu nasan islam da kunya, shine fa tanashn biyu se naga ta ruga tun tana zuwa ta dawo harta gagara yanzu na share wanda tayi anan acikin minti biyar tayi yakai so hudu fa" kansu karayin magana se wanin aman, duk ajikin maheer tayishi be kulaba yakira fareedah, kai tsaye asibitin su aka kaita, gwajin farko ya nuna zaman ciki daram na wata d'aya da satuka uku harda kwanaki.....Murna a wurin Maheer ba'a ko maganar ta, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin farin ciki, ita uwar rakiyar wato Nancy ma har mamaki yake bata yanda ya sake yau se nisha di yake yi Islam se nan2 ake yi da ita tamkar ze maidata cikin sa....an samu nasarar tsayar da aman ma har ta samu bacci abinta.
**************
Yaso suje tare da islam Niger amma umma ta hana azuwan ta dawo gunta tunda batada lapiya, sophie da sha'awa su musu rakiya tunda kwana uku ne kurin zasuyi......
***************
Sokoto suka fara zuwa, tasha mamakin hakan a gidansu suka kwana d'aya, se washe gari suka doshi hanyar niger anan tasamu damar daukar abubuwan ta masu muhimmanci datake buk'ata bata kuma samu matsala dasu fiyya ba tun zuwansu washe gari suka wuce Niger......
A hanya se Bacci Nancy keyi gashi itane agaba, kamala kejan motar yayinda maheer da kannensa ke bayan motar a zaune, haka har suka isa garin Niger atare.....Mahaifiyarta taji dad'in ganin ta takumayi farin cikin jin tabar hannun azzaluman cen, tayiwa maheer godiya sosai, seda sukayi adadin kwana kin su sannan suka juyo zuwa kanon dabo inda koda suka karasu Nancy ta samu visa na zuwa london karatu inda tare da Maheer d'in zasuje se yaga yanda za'ayi ta samu komai cox ko maganar admission ba'ayi ba sesunje sabida k'urewar lokaci!
*******************
*London*
A babban birnin london sukawa kansu masauki a wani k'ayataccen gida me kyau tsarin ginin turawa yayi kyau sosai, 3 bedroom flat ne se wani cute parlor dake hade da kitchen da dining d'insa, Har yanzu dai Maheer baya sakewa Nancy, yayinda su kuwa su sophie suke matuk'ar jin haushin ta akan niqafin datake mannawa, sun tabbatar a london tayi kad'an tayi yawo acikin sa shisa ma suka gayawa maheer ya mata magana.
Kallon sosai ya mata bayan daya kirata yace da ita cikin isa
"Niqafan nan dakika zo dasu dole ki ajiyesu, bazasu lamunta ba anan kam, su komai da camera sukeyi kar wani ya aikata wani abu zargi ya tabbata akanki tunda face dinki a rufe yake, ya kamata ki sani nanba gida bane, tunda yake dama fuskar ki ba al'aura bace ba seki hakura da wannan aqidar" shiru batace masa komai ba yaci gaba
"Kin fara pure English yanzu wanne zakiyi anan?" Kallonshi tayi idansu suka gauraya lokaci d'aya k'irjin dukkansu ya buga, ta kasa d'auke idanta akan nasa, shi d'inma ya rasa dabarun yi ayau idanshi akanta baya ko k'iftawa, murmushin dabasuda niyyan yiwa juna suka sakarwa juna kan daga bisani yace
"Yaya dai sefa ince sekin biya kud'in wannan kallon, kinga fine boi kin wani kafeni da ido" shagwab'e fuska tayi
"Allah ni yaa maheer ban kalle ba, kaine ma kake kallona shisa har kaga ina kallon naka" dariya ya d'anyi
"Kin sani dai matana batada k'aton goshi ni banason mace me qaton goshi" tabare fuska tayi ta tunzuro baki
"Ni yanzu kawai se a rik'a cemun wai me goshi,bayan nasan wlhy ni nafika kyau so dubu" Besan dalilin jin yanason ci gaba da wasan ba, seya tsinci kansa cikin nisha d'i yana k'ara fad'ad'a fara'ar sa yace
"Oho dai nidai banason k'aton goshi da wani k'aton kanta a wurin" dariya itama tayi ta zauna da kyau
"Yaa Maheer yanzu wane course zanyi wai?" Murmushi ya mata
"Ke kika zab'i English dacen?" Girgiza kanta tayi alamar aa tace
"Noo Law na saka ban samu bane" gyaran zaman sa yae
"Kijewa law d'in mana ko kuwa?" Haka dai yayi convincing nata ta yadda zata yi law din....
A wannan daren kasa bacci Maheer yayi ya gama k'udurcewa kansa cewar lallai seya mallaki Hafsat!!! Ya fahimvi ba wani zagaye santa yakeyi sona hak'ika bawai na wasa ba, to Amma ta yaya? A yanda yakeji ze koma Niger ya ajiye aikin lecturing ya dawo ya rik'awa Abba wasu harkokinsa na nan, daga nan ya dakko islam tazo itama taci gaba da karatunta, babu sassaucin daze samu a nesanta kanshi da Nancy face siyan fashewar zuciyar sa!!!!
Tayaya zaman nan ze yiyu? Anya ba yanzu muka fara wasan ba kuwa? Da alama akwai sauran rina a kaba.
Mom Nu'aiym ce.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
29
Islam ta k'urawa babynta ido cikeda so da k'auna da kuma tausayi me tsanani!! Bata tab'a kawowa aranta duniya zata mata atishawar tsaki haka ba, bata tab'a kawowa ranta akwai ranar dazata haihu babu dangi a tare da ita, bata tab'a kawowa ranta zata haifi 'ya ba uba ba, ko a mafarki bata zata zata haihu ba asibiti ba, ta samu rauni amma bame kulawa da ita, Bata tab'a zata zata haihu ta rasa romon dataga ana yiwa masu jego ba, tasha ji Baba Azumi na fad'en idan ta haihu kunu zata dinga mata me kyau jikinta yayi k'wari da wuri, tasha ji Baba Azumi na fad'ar zata mata wankan iccen Dogon yaro na ruwa me shegen zafi, Baba Azumi taci burin sanyata a kujerar mata ta dinga turara mata kasanta ance yana maganin tusar gaban da mata keyi bayan sun haihu.....Bata tab'a zata, zata a haihu. Babu uba ko wani jigon dazewa abinda ta haifa Hud'uba da kiran salla ba, Bata tab'a koda a mafarki tunanin cewar zatafi haifi abinda ze rasa sunan da za'a kirasa dashi Ashe Ameenu ninketa yayi baibai ta hanyar sanyawa ainahin fuskar sa *WATA FUSKAR!!* ya danne wata salahar Fuskar da Mummunan *WATA FUSKAR!!* sa lallai tana cikin B'akin ciki, tasha ji yana fad'a cewan Duk sanda ya haifi Namiji ze bashi sunan mahaifinsa na ainahi wato Musa idan kuma Macece ze sanya mata sunan mahaifiyarsa wato *NANA KHADEEJAH* da wannan ta dauki jinjirar ta mata huduba da kanta tana sharar k'wallah lokaci d'aya kuma tana mata kiran sallah ta mata hudu ba da sunan Nana khadeeja....tausayi sosai ta baiwa Naja daya sanya ta kasa daurewa ta sanya kuka.
********************
Abubuwa sun soma yiwa Baba Azumi yawa sosai, ta soma neman sukunin ta ta rasa, bashi ya mata dabaibayi wanda taketa ci da sunan ummul zatazo amma shiru kakeji tamkar an shuka dusa kwanakin cen gwal d'inta ta eba ta siyar babu yanda ta iya akan zata rage bashi yanzu gashi marasa mutuncin mutane sun taso ta agaba, har yanzu a k'asan ranta ummul take jira ta tabbatar ummul tanacen abunta k'asar waje tana hutawa, bata raba d'aya biyu cikin ummul ya kusa zuwa duniya da wannan take ganin dole su dawo gida.....yau dai kam rana ta b'acewa Baba Azumi sabida tanaji tana kuma gani aka zo aka wuce da ita station akan bashi belinta an gagara karbowa sabida yayan ummul yace shiba ruwanshi yayita gargadin su akan hakan wata er sandar mace har duka ta tik'a mata tsabat haushin datake bata sabida had'e kai masu binta bashin sukayi suka kai k'ararta, taci azaba kan abada belinta, se fad'i takeyi suyi hakuri 'yarta ummjl tazo wai me kudi take aure dansunje yawon shan iskane turai amma dasunzo zata bada, wasu kam kallon mahaukaciya tuquru suke mata.
*****
Maheer ya dawo Niger ansha love shida islam se narkewa take wai ita adole me ciki, shi kuwa ko motsin kirki tayi seyaji a ranshi bayan zuwansa da one month suka juya zuwa London inda itama tunda jikinta yae kwari aka soma nemar mata gurbin karatu a turai din inda ta samu nasarar shiga level one a bangaren turancin data faro....dayake su cen abinsu akwai tsari sanda kayi joining college sannan semester ka ze fara....
Tir k'ashi!!!
Yau a parlor islam ce kwance tana narka shagwab'a tayi matashin kai da cinyar Maheer dayake biye mata ya sanya hannunsa yana wasa da sumar kanta dake a kwance, ita lallai yau chicken byte takeso, kuma anje siya sunce seda safe gashi 8 yayi, kiran Sophie yayi tazo tace gata
"Kin iya chicken byte ne?" Ya tambayeta kanshi tsaye kallon shi tayi ta dan saci kallon islam, a ranta tace wato matarnan tunda tazo muke cikin takura indai tana ganin yaa mahee durun uwa iri iri ko,
"Ea bazance ban iyaba amma muma Nancy ke mana, tafi kowa iyawa" jinjina kansa yae
"Jeki ki kiramun Hafsatun" juyawa tayi aranta tace so daya mukayi a gaban Nancyn Allah yasa ya kwab'e" tana zuwa ta turo ta, k'irjinta na dokawa ta iso parlor d'in tunda sukazo da islam batada sukuni, tarasa mesa takejinta a takure sannan kuma batason ganinsu kullum.manne da juna tarasa dalilin jin hakan, ada tasan taso maheer amma yanzu ta sani koda a k'afa zasu d'aura mata shi bazata jasa ba sabida sam ita bazata iyaba, tanada wasu dalilai data barwa kanta sani..
"Yaa Maheer sannu da gida"
"Yauwa sannu Hafsat, am chicken bytes zakiwa baby, shi takejin ci kuma near by shops dinnan babu wai seda safe suke ta cewa" wani k'ututun bak'in ciki ne ya tasowa Hafsat amma seta kanne tace
"E babu damuwa, munada kayan hadin barinje na hada mata" Bece komai ba ta juya tana had'awa tana mita harta kammala ta kawo, agabansu ta ajiye tana kallon islam da wasa irin na ftnds dinnan tace
"Maman biyu ga wannan karki cinyemu" murmushi islam tayi sannan cikin isa tace da ita
"Kekuwa ina d'an drink dazan had'a da? " miyarda dubanta tayi zuwaga maheer ta shagwab'e fuska
"Ni honey kace da ita ta had'amun ko smoothie ne dabashi da wuya nafison Banana smoothie yafi rik'e ciki" kallon mamaki hafsat ta mata shi kuwa Maheer yace
"Kinji me tace kije ki had'o kin wani tsayawa mutane akai" zuwa wannan lokacin seda tayi kuka a kitchen tana mamakin sauyawa halin qawarta.....
**********
A wannan daren Nancy ta kwana tana bak'in cikin faruwar wannan abin,tasani Maheer baya mata wulakanci shida sophie amma shauty da islam suna yawan kaita mak'ura aciki islam tafi bata mamaki, ita bazata fito ta mata wulakanci ba amma sedai tana mata abubuwan datake so taga sun k'ureta tayi wani abin daze ja mata raini!!! Mamakin wannan halin na islam na cikin damuwar ta......Bazatace Komai ba akan wannan abin tayi alkawari zata jure amma tasan wuyace zata shata ta hango wulakanci tsantsa acikin take taken da islam keyi tun zuwanta, ta dinga mata abubuwa tamkar wata 'yar aiki tana tunzurata zuwa bango, amma ba komai zata jure!!!
**********
Duk wani juyin da maheer zeyi tunanin Nancy ne danqal acikin kansa, yana cikin tsantsar damuwa mara adadi, yana kula sosai da yanayin islam da yanayin d'abi'un datake nunawa agaban na Nancy, bayaso ya mata magana ne tazo tana mar wani kallo na daban,yasan mata seya sanya wani abu aranta daze k'ara dagula zaman, yana hango yanayin Nancy da kuma b'acin ran datake shiga duk sanda ta mata irin wannan abun, ya kula ma tun dawowar da yae da islam Nancy walwalarta ta ragu sosai, ya kula kuma takan zauna skul ko bata komai har yamma sabida batason ganin abubuwan da islam keyi sam ya kula tana cikkn damuwa abun yana damunsa!!!
Mom Nua'iym ce
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
31
A hankali ya soma laluben inda ze qarajin kukan amma shiru be jiyo komai ba, yayi bincikensa sosai amma ba abinda ya gani a kitchen d'in juyawa yayi da zummar komawa d'akin har yakai k'ofar yajiyo k'arar jinjirai da k'arfin Gaske sekace wacce aka tsikara da sauri ya juyo ya kalli k'ofar store d'in kukan taci gaba dayi bil haq da iya kacin k'arfinta tamkar wacce ake ciza dukda yake kana ciwo sautin kukanne alamar bakin a toshe yake da wani abin, da sauri ya juya zuwa store ya soma binciken shi besha wahalar neman taba sabida kukan dataketa k'arayi da sauri ya zaro ta a kwalin yana huci ya kuma haska kwalin da fitilar wayarshi cinnakune a saman zanin datake kai sunkai biyar warwareta daga cikin d'ankwalin datake yayi nanma wani cinnakan ne alamar shi yake cizon ta, riqeta yayi ya soma sosa wurin a hankali yana shhhhhh alamar tayi shiru cikeda tausayawa a kafad'arsa ya d'aurata ya soma sosa mata bayan a hankali be koma d'akin ba yafi 15 mns yana sosa mata wurin a hankali hartayi bacci juyawa da ita yayi d'akin dayabar Ummul ya shiga a hankali, tana zaune tana kuka me ban tausayi....rungume yarinyar yayi ajikinsa yana mata murmushi me k'ayatarwa dabema san yana yiba sosai ya k'urawa yarinyar ido baya ko k'iftawa ba k'aramun kamanni takeyi da late mahaifiyar saba, har acikin baccin yamutsa fuska takeyi alamar tanajin zafin cizon da cinnaka ya mata, har cikin ranshi yakejin wani azababben rad'ad'i akan cizon da cinnaka ya manna wa 'yarsa....tunda yake a duniya be tab'a jin yana son wani abu ko mutum ko aljan sama dayanda yaji yanason wannan abar ta hannun shiba!!! Ko Ummul dayake so bata kai kwatankwacin san dayakewa wannan babyn ba, kallon ummul yayi yace
"Ki Nutsu kimun bayani niba abinda zan miki, yaushe kika haihu naga yarinyar tayi kwar'i sumar kanta kurin ya nuna hakan" d'ago jajayen idanuwanta tayi tace
"Watannin Nana khadeeja biyu kenan a duniya, bakwaini aka haifeta kamar yanda na fad'a maka, nafi sati ina b'oyonta akan ance kana raba iyaye da yaransu tunda take bata tab'a yin kuka ba idan na b'oyeta yau, na barwa Allah akan Nana nikam, tunda yake ubangiji ya bayyana maka ita cikin sauk'i shiyasan me yake nufi da Nana, ni bazance maka komai ba illa kurin kaji tsoron Allah mad'aukaki dukkanin abinda kakeyi yana kallonka" Wata iriyar zufa ce take tsatsafowa Ameenu babu wannan shirmen aranshi waishi ya mik'a 'yarshi shi kenan kuma idan ya bayar baze k'ara ganintaba har abada gashi Alhj Baba ya sanar masa ana kaisu wasu garuruwanne masu kud'in dabasa haihuwa ne ke siyan yara da tsadar dayaga suna siya suna adopting nasu, dukda an sanar masa basa shan wahala ko kad'an amma seyaji a ranshi ko Nawa za'a bashi akan Nana baze iya bada itaba gashi Har Alhj Baba ya gama cinikin kome aka haifa mace ko Namiji kallonta yayi
"Ummul Sunan Mamana kika baiwa wannan jinjirar? D'aga masa kanta tayi tace
"Wannan shine sunan danaji kace zaka sakawa yarinya idan macece shine nacika maka burin ka" nisawa yayi yace cikin takaici
"Da hannuna nake siyar da yarana ummul, bakuma siyar dasu nake dan komai ba sedan ina ganin ina tara uwar dukiya akansu, an sanar mun turawa ke siyan yaran musamman wanda basa haihuwa suna adopting d'insu suna basu gatan daya dace dasu.....yarana sunkai goma sha biyar dana zubar na bada kyauta wasu duk iyayensu aure mukayi wasu matan banza ne wasu hayarsu nakeyi, yanzu dakikace naji tsoron Allah wani tunani yazomun shin idan anje dasu qasashen turwa wane addini ake koyar dasu? Wa danne irin sunaye ake kiransu dashi shin anya zanga annabi kuwa, wani zubin idan akamun haihuwa banako kallon jinjirayrn nake badasu amma akan Nana Khadeeja bazan iyaba ummul, bazan kara siyar da yarana akan wannan abin duniyar ba inada dukiyar dazan rayu acikinta har abada inada gidajen mai iri iri inada kampanin silipas bazan iya qayyademiki adadin abubuwan dana mallaka ba, na dad'e ina tunain cewan had'uwana dake alkhairi ne na jima ina miki kallon ke alherice ashe hakan, Allah na tuba ka yafemun laifuffukana na baya"
Dubansa ya miyar zuwaga ummul kan yace
"Alhj Baba mutum ne me tsananin san abun duniya, shine ya d'aurani akan wannan mummunan turbar ta banza, yanzu nasan ze iyayin komai akan zan hanashi wannan jinjirar, koda yake dama bayason wanda suka sha nonon uwarsu bare ma wanan watanninta biyu" kallonshi tayi
"Sekace abun tsafi Ameen, anya kuwa wasu ke siyan yaran nan kodai tsafi ake dasu?" Kallonta yayi amma beyi magana ba yana nazarin kalamanta ne kurun secen yace
"Tunda nake mik'a jinjiraye ban tab'a sanin me akeyi dasuba face abinda na gaya miki Allah ne shaidana, amma kuma ummul maganar kin nan ta zomun da wani tunani, bana mantawa akwai wani yaronmu da yarinyarshi ta haihu da kwana biyu daya kawo jaririn mayar masa akayi akan yasha nonon uwar sa baida wani amfani....wani zubin nikanyi mamakin dalilin sato matan da ake masu tsohon ciki idan sun haihu a kaisu kan hanya a wurgar a dauke jinjirayen duk akan abu d'aya waishi neman duniya kuma bama wannan ba idan suna son jinjiraye babu a k'asarsune? Wlhy ummul nikan jima ina nazqrin abubuwan nan amma yaya zanyi da Alhaj Baba shine gatana banida kowa" shiru sukayi dukkansu suna kallon juna k'arar wayarshi ne ya miyar dasu duniyar dasuke a tare suka kalli screen na wayar *ALHJI BABA* shine rubuce ajikin fuskar wayar...miyarda duban su sukayi akan fuskokin juna bayan da kuran ya yanke lokaci d'aya zuciyoyin dukansu suna lugud'e!!! Murya na rawa yace
"Mesa Yake duk wanda ke qoqarin guduwa daganan gidan seyace baya ganin gabansa bare bayan sa, abubuwa da dama dasuka shafi nan gidan ban saniba ummul!!! Wannan tsafin da kika ambata ya rikirkitani koda kuma kinzo da waya ke naki baze shigaba amma ni zan samu wanda nakeso kuma zasu krani, anya babu zancrn ki kuwa anya babu tsafin to amma tayaya? Ni komai na Alhj Baba nasani ki taimakeni ummul ina cikin tsananin rud'u wlhy" shiru sukayi sanda kiran ya k'ara shigowa se gumi yake had'awa tamkar wanda ya had'iyi kunama"......
**************
Koda wasa Nancy bata zata Maheer zezo mata da wannan zancen ba!! Bata burin aurar sa, tunani ya mata waya wannan ya bata damar kiran Mahal ta tbayeshi gameda labarin soyayyar sa akan ta tada, yana amince mata tace yaje yawa Baba iro magana a shirya komai, indai ze aureta karatunta ma zata ajiye, dad'i ya kamashi yace da ita zema barta ta dawo kuma yamata alqawarin farin ciki na har abada.....
*Bayan sati d'aya*
Maheer yana kwance a parlor wayan Daddh ya shigo masa, d'agawa yayi yana murmushi suka gaisa yace dashi
"K'anwar ka tayi muji fa, malam iro ya kirani a waya yana neman izini kozan bada ita, nace duk yanda nace nikam nace a tsarina seta kammala karatunta amma zamu iya tsyar dashi matsayin manemin auren nata" gyaran zaman shi yayi sabida harya dawo zaune yace
"Abba wacce daga ciki?"
"Kanajin nace malam iro ai kasan Hafsat nake magana ko!!! " k'irjinsa me yayi wani irin mugun dokawa da tunda yake a ranshi be tab'a jin fad'uwar gaba irin wannan ba, lokaci d'aya ya tsarke ya soma tari sosai
"Sannu idan ya fad'a maka ka kirani nanda awanni uku zan shiga meeting yanzu.......
Tunda Maheer yake be tab'a shiga wannan tashin hankalin ba, ya jima bega tashin hankali ba irin wannan, se yanzu ya yarjewa kanshi yanawa Hafsat *son so* wanda be tab'a yiwa wani ko wataba yana cikin tashin hankali, yaya Hafsat zata masa haka?? Anya tayi masa adalci kuwa tasan me yakeji kuwa?...
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
30
Yau kusan wata d'aya da sati biyu kenan da haihuwar Ummul yarinyarta tayi girma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 20