Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [6/16, 10:37 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 0️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI. YABO DA GODIYA YA TABBATA GA ALLAH MA DAUKAKI DAYA BAMU IKO DA DAMAN FARA WANAN LITTAFIN MAI SUNA HAWAYEN KADA KWANTONE ,,,,, YADDA ALLAH UBANGIJI YA BAN IKON FARA NOVEL DIN NAN LAFIYA UBANGIJI ALLAH YASA MUGA KARSHENSHI LAFIYA DANI DAKU DUKKA ALLAHUMA AMIN,,,,,,,,,, Duk saurin da takeyi bai hanata komawa baya wajen motan data glass dinshi baki ba ta tsaya kamar kullum tana karewa kanta kallo a cikin tsiwa irin na yarinta da yara keyi. Wanan al,adan maryamu ce bata ganin glass ko mirrow bata tsaya ta duba kanta a cikinshi ba ko takai hannu ta rubuta sunan ta datake koyo da boko MARYAMU a cikin karkatacen rubutu irin na dan koyo daga primary level. Ba ruwanta da damuwa da motan waye ko ina motar ta fito ita dai haukan kurciyanta kawai na bata yin hakan ko yaushe. Tana gamawa ta gyara kwanon nikan dake kanta tayi gaba a cikin sauri wanda ke cikin motar zaune da bata kula dashi ba ya gyara zama cikin mamaki yana bin yarinyar da kallo. Tun isowanta wajen tana shirmenta yaso ya fito daga motan ya tsawata mata sai kuma ya dakata yana kallo mamaki harta gama ta wuce bai bar mamaki ba don abin ya zama mai bokon lamari. Haka ya fito moto da fargaban yaran unguwar kada bayanshi wani yayi mai ta,asa a jikin motanshi tunda gashi sun fara da zane a gabanshi ya karasa inda zai shiga tare da fita zancen wanan yarinyar. Gidane mai kama da ginan zamani na dauri amma duk da anwuce zamanin wanan ginan kana ganin gidan zaka shedaa baya an zuba zamani a gidan cigaban zamani yasa aka fisu a yanzu. Ya jima a ciki koda ya fito rana ya danyi ga yabayin zafin dake damun garin a lokacin haka ya shiga mota ya kunna AC yabar unguwan tare da dinbin tunane a zuciyarshi. Ba komai yake tunane ba sai zancen mahafinsa akan tafiyasa daya kwalfawa rai don zuwa karo ilimi waje inda mahaifinsa ya kafe da baida ra,ayin hakan shi ko wani irin katatune anayinsa a nan kasa don haka ya tsaya yayi karatunsa a nan yana kuma taimaka mashi da wasu abubuwa na kasuwanci daya soma bayan ritayanshi. A gaskiya hakan ba ra,ayinsa bane kasuwanci yafi bukatan yayi karatu ya zama ma,aikacin gwaunati ya more iliminsa a nan. Don shine ya taso zuwa gidan kakansa malam Inuwa don ya gaya mashi halinda suke ciki da mahaifin nasa inda yayi sa,a ya bashi goyon bayan tafiyan da yake son yi din. Shi yabawa sako yana neman mahaifinsa idan ya koma gida don haka yake tunane da wani irin fuska zaiwa mahaifin magana bai tuhumi karansa yakai wajen kakan nasaba. Saida ya gama komai bayan sallah isha,i ya shigo gidan direct kofan mahaifiyarsu ya tsaya yana sallama kafin ta bashi izinin ya shigo. Ya shiga tun bai zauna ba ya fara gaida ita ta amsa mai tare da tambayan yau ina ka shiga tun safe na aika a duboka sau biyu baka nan. Yace tun bayan azahar ina gidan nan ban fita ko ina ba dazun dai naje gidan malam na gaidasu yama ce in fadawa baba yana magana dashi idan ya dawo. Kallon tuhuma ta aikawa dan nata kamar zatayi magana kuma tayi shiru sai zuwa can tace a can kaci abincin rana ke nan yace shiyasa ban nema ba anan kinsan halin malam idan kaje gidansa sai kaci tuwo ko fura zaka fito. Shine kyau ai wanda yasan mutunci bako yake hakan amma bako yazo wurin ka ko ruwa ka kasa daukowa ka bashi irin na yaran yanzu ai hakan ba mutunci bane. Shi malam har yanzu ai bai yarda akidunsa na mutanen daba komai na bahaushe yana tafiya da al,adane tare da addini malam sunan yanzu dori sukayi kawai saman al,adan bahaushe don ko kiristan dake rayuwa a arewa al,adansu dabance data sauran kabilu. Haka yasa ake gauraye dasu wani idan ba an fadama ba ba zaka bata gane cewa shidin ba addinin musulunci yake bi ba saboda al,adda daya gaureye na bahaushe. Ko suna zakaga na musulmi sak amma addini daban shiyasa suke shammatan mu wani lokacin don kallon bai daya yan kudu ke muna dasu basu yarda cewa suna cika addinin suba ma. Su suka sani mama ni a tunanena duk dan arewan daya tsaya bai addinin musulunci kamar gangancine a garesu hakan tunda sun san komai game da addinin islma don a gauraye muke dasu sunsan komai daya shafi islama amma ganin dama ya hana su shiga su fahinta. Muryan maigidanne da yashigo yana magana da dayar matar gidan inna yasa tace da dan nata aiga Alh nan ya shigo sai kaje ka sameshi ka fada mai sakon malam din. Ya mike a daidai lokacin daya daga labulen kofan yana fadin kina ciki ke nan da wanan zafin na rasa me yan Nepan nan suke nufi da mutane basu bada wuta yadda ya kamata ga mutane ? Amma karshen wata nayi zasu zo su kwalawa mutum sallama a kofan gida a kawo takardan wuta idan baka bayar ba harsu nemi yi maka rashin mutunci. A daidai lokacin saurayin yakai kasa yana fadin baba ina wuni ya kallosa kallon kai kuma fa ? bai sa ba saima cewa da yayi da dan nasa ina kaje baka zo kasuwa ba yau ? Saida ya dan sosa keya yayi kasa da kai yana fadin kodana tashi da safe na makara sai na shirya naje gaidasu malam can nayi sallah azahar yacema yana gaida kai idan nazo in fadama yana son ganin ka. To shi malam din yace yana son ganina shekaran jiyan nan muka rabu dashi fa Allah ya kaimu gobe zanje inji ko meye ya saki labulen dakin ya juya yabar kofan dakin. Matar ta mike tabi bayanshi don zuwa yi masa hidima kamar yadda yake ga addini da al,adan bahaushe a yayin da maigida ya dawo daga tsabgan rayuwa ke mace zaki mike zuwa hidima mashi tun daga kan ruwan sha abunci ruwan wanka da sauran abubuwan rayuwa Allah bamu ikon tsare hanyar tsiran mu Amin. Habib dan gidan Alh yakubu mai gwal da sunan ya samo asali tun fara sana,ar mahaifinsu kamar yadda akanwa mutum inkiya da sana,arshi ko sunan gidansu haka wanan sunan na gwal yabi sunan Alh yakubu din har zuwa girmanshi. Suma yaran gidan suka taso da wanan inkiyan ta mahaifisu matukar ba anfadi suna da inkiya ba yawancin mutane basu saurin gano wanda ake nufi. Ba laifi ga Alh yakubu don har yanzu yana shanawa a kasuwa duk da harkan gwal an barshi sosai amma sunan yana nan a hakan bai mutu a bakin mutane ba. Alh yakubu magidancine mai mata biyu rak a tsawon rayuwan aurenshi da hjy maimuna uwargida da suke kira mama sai Safiya wace suka lakawa inna yanzu . Zamane irin na matan hausawa akeyi irin zaman da sai mai fahinta zai iya gano sirin boye dake gidan zama irin na kakani da akayi a baya wanda har yanzu din nan akwai irin gidajen dake kamanta hakan suna rufe abinda ke boye a zaman tsakani. Hakane a wanan gidan ba zaki taba fahintar meke akwai ko yake gudana ba sai wanda yai zurfi a cikinsu koshi sai dan kwankwanto zai fahinci ana dan goga kishin boye a tsakani. Duk da su kansu din suna iya kokarinsu wajen tausan zuciyarsu sam ko abu ya faru zasu bawa kansu hakkuri a wuce wajen ba riko balle har wani ya shigo ya fahinci hakana garesu. Wanan zamane da iyayye da kakanni sukayi a baya zama na rufin asiri da tausan zuciya kan abokon hurda bawai ba a samun sabani bane kamar zaman takewan yanzu suna samu koma ince har yafi na yanzu din zafi. Amma sai a taushe a nuna ba komai a tafi a hakan har Allah yasa mairabawa yazo ya raba lafiya ana alhinin juna na rabuwa . Ba komai yasa hakan ba kuwa saboda cire kyashine da hassada na dindin da basuyi irin muna yanzu yasa baki taba fahintar halin da gida ke ciki a lokacin. Tafe take tana yan wakokinta na yara irin na da daga bayanta take jin ana ambantar sunanta da karfi ke maryama ke mairo hakan yasa ta shiga dan waige waige duk da ta sheda muryan kawar cin mushetace ta cikin unguwace salma. Wace kusan kansu daya wanan akidace garenu mata idan akwai yar sa,anki a unguwa ko makwabtanku zakiga kun shaku sosai da juna koda ya kasance ba shiri a tsakaninku wanan dan shakuwan sai anyishi na wasan kasa inji manya. Duk da tsakanin maryam da salma akwai yar tsama amma hakan baisa sun rabu ba a rana dolene sai daya ya leka daya koda a sacene don wani lokaci itin hakan iyayye sukan kasa hakkuri idan yaro ya kawo karan dan uwa sai uwa taga laifin dayan tacewa yarta ko danta kada in kara ganin ki da wani ko wance . Abin yara alokacin dake uwa kikai magana lokacin zasuji dadin manewa juna saidai bakin cikin hakan ya gumeki ke uwa ubangiji Allah ka shiryawa musulmi zuria. Zance zaman salma da mairo zamane na tsarguwa don ita maryam akwaita da tsokana abu ba abuba fadane amma kuma bata da riko gata bata da rowa amma akwai tsiwa da jin kai ga son bada umurni duk da ba wai girmuwan kawar nata tayi ba. Ada lokacin da mahaifin maryam keda abin hannunsa makarantan bokonsu daya ta kudi suke zuwa haka islamiyansuma dayace ta kudi mai tsada amma a yanzu iftila,in daya samu mahaifinsu na kariyan arzki yasa maryam din ta koma karatu a makarantan gwaunati. Yayin da salma har yanzu take a makarantar kudi saidai hakan bai rabasu ba tsakaninsu gida dayane a tsakanin gidajen nasu anan suke zaune amma duk da hakan sai daya taga daya a wuni. Ba komai yajawa mahafin maryam talaucewa ba sai yan hukuman custom da suka kama kayansu yayi bi har ya gaji amma ba acinma nasara ba yanzu ya hakkura baida komai sai hakkuri shida iyalinshi. Wani lokaci hausawan mu suna da camfi da zaran magidanci ya auri mace arzikinshi yaja baya wanan mace za,a fara camfata ana fadin itace mai kashin ribas itace keda farar kafa takawowa namiji talauci ya tsiyace. Yayin da irin matan nan sukan shiga wani yanayi na damuwa har su nemi rabuwa da mijin a lokacin saboda zunde da yawan gori da suke sha musanman a wajen dakin miji. Wanan abin ba macen kadai abin yake shafa ba harda zuri,anta idan Allah ya kawo rabo tsakaninta da mijin kusan wanan rayuwan su maryam ke fuskanta a gidan nasu da yan uwan mahaifinsu. Mukan manta da Allah ne ke bayarwa ya kuma karbe abinsa lokacin da yaga dama idan kuma yaga daman hakan ya maidowa mutum da abinsa harma yafi na farkon . Mata da yawa sukan shiga wanan bakin rayuwan tsamgwaman a gidajen aurensu saidai hakkuri da dangana irin na malam bahaushen musulmi yakan sa a jure a rugumi kaddara hakana. Wani kuma mai raunin imani zai sallama macen a rabu don ko arzikin nasa zai dawo ba aiwa Allah dabaran hakan don yana da wuya idan haka din ya faru har arzikin ya dawo yadda akeso . Mairo ina kika fito haka da kwano a kai salma ta fada tana kokarin jawo kwanon dake kan kawar nata a fusace maryam din ciki fusata take fadin bari mana karki zubarwa mutane da nikansu gidan malam zankai wa inna nikanta data kawo gidan mu. Dariyan shakiyanci ta farawa maryam din tana fasin yar dakon nika ke nan ku baku barin yiwa matar nan dakon nikane tana kama kudinta tana lalewa ta bar mamanki da nika ku kuma kuna dakon kaiwa don kawai a baku abinci. Kam uba salma kinga irin abindake hadani dakw ko yasa banson wasa dake umma ai uwatace da zakice kada inkai mata nika ? Dan Allah ja can wazaki boyewa ni nafa san komai mairo takai hannunta tana diban nikan daga cikin kwanon da sauri mairo ta kara buge mata hannun a fusace. Hakan yasa nikan ya dan zube aiko ta aje kwanon da sauri tayi cikon salma din da fada duk da salman ta darata tsayi bata jira komai ba ta dauketa ta daga sama ta sake. Fada sosai ya kaure a tsakaninsu lokaci guda saida mai shagon ya taso ya rabasu yana masifa kowansu taje gefe daya tana huci kamar zakanya. Kuftawa maryam din tayi don bata samu sa,an salman ba yadda take so a ranan hakan ya bata haushi har ta kuta don kudai bakuji kamar kaji kullum a cikin dabe kuma a jima a ganku tare ? A cikin tsigar rashin tsoro maryam din tace da maishagon wallahi ko gobe ta sake zagin gidan mu saina murji bakinta kuwa mu dai murji juna daga nace innan ki tanawa mamansu hassan nika kina dako zakice na zageki ? Kice din inba tsoro ba haka salma din tayi shiru batace komai ba ta juya ta kama hanyar gidansu ko jiyowa batayi ba . Nikan ta duka ta dauka tana masifa ta nufi gidan malam din dashi bata ko tsira ba don hjy uwa masifa ta hauta dashi tace ta wullakanta mata nika don ga bakin ruba nan yayi kaca kace saita fadawa mamansu kada a kara bata nikanta ta kawo masu ita ta gaji da wullakanci kada a goga mata tsiyan gado. Duk da maryam ba wani shekarune da ita ba wanan kalman na tsiya da innan su hassan ke yawan kirawa innansu ya zauna mata a rai gashi har makwabta sun soma fada masu yanzu. Juyawa tayi ta fita tabar gidan a hasale ko kudin bata tsaya karbarwa mama din ba ta koma gida dakinsu ta shige kai tsaye ta kwanta bisa gadonsu na katako daya tsira a dakin yanzu don duk inna ta tsinci kayan dakin nata tayi laluran rayuwa dasu. Banda wanan gadon da wani rubaben kujera sai ledan kasa daya gama jin jiki suke maneji dashi a dakin a can kwana daya kuma tsufin akwatunane da suka sha jiki tun na auren inna din guda ukku irin na plastic roba din nan a gefe daya an dora wani kan wani. Muryan mamace ke fasin waini kan ita mairo har yanzu bata dawo kai nikan nan bane ta bani kudina tun basu salwanta ba. Anya kuwa kamar naga shigowan mairo gidan nan kuwa bata dakin uwarta kuwa kinsan halin mairo da tsiwa ai yanzu haka kudinne bata karbo ba kuma bata iya fadi. A,a malam nikan tsaya kada ta goga min tsiya ina jiran kudi inyi amfani dasu ta dawo ta shige dakin uwarta ta kyaleni zaune ina zaman jiranta. Mairo ta fada tana daga labulen dakin innansu din in akwai abinda ta tsana shine wanan sunan mairo din da mama ta laka mata da har yan waje da yawa suka kama a bakinsu yanzu suke kiranta da mairo din. Ga yar wullakancin banza niko nakasan nan naki ke hadani dake yarinya karama da tsiwan tsiya kinfi karfin ki amsa min ina kirankine ? Mama nacevai bata ban kudi ba na aje tana ta min fada wai,,,,,, sallaman da aka kwalane almajirin gidan malam take fadin waiga kudin nika inji hjy . Harara mama din ta watsa mata tana sake labulen taje gun yaron dake miko mata kudin yana fadin wai tace a daina ba mairo nika tana kai mata don Allah . Ko yanzu saida ta zubar kafinta kawo mata shi wai a daina bata kinji ko abinda ta dawo tanawa cika da batsewa ke nan don tasan abinda tayi ashe ? Zakiko gani ga kwaryan ki donni ba boyar uban kowa bane da zan zauna inawa kartai cefane kuna kwance kikai nika kawai saikije ki zubarwa mutane da hatsinsu. Haba ya isa mana tunda tace abar bata ba sai a bari ba uban dake zaune saman tabarma da redio a gefensa ke fadin hakan. Ai kaji matsalanka kasan halin mairo sarai da shirirta ana magana kuma zaka wani tare mata yanzu ka hana ayi magana. To yanzu me nace don Allah halin mairone kuma bako a gareki kikanso bata ranki a banza wani lokacin ta juya zuwa dakin ta ba tare da tace mashi komai ba. Tunkan ta karasa muryan maryam din ke fadin ina abincina mama cikin daga murya yadda zata iya jinta ko kallonta batayi ba ta shige daki yarinyar ta bita da kallo. Muryan mahaifintane a shake yake fadin yaki nan zoki dauki gutun nan kije kici kema kinsan halin mamaki ai tunda kukai haka ba zata baki abincin nan ba yau. Inna dai dake duke tana wanki batako dago kai ba har sukaci suka sude batace komai ba sai zancen zucin da takeyi a kasan zuciyarta. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/18, 9:02 AM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yanzun dai malam karana Aliyu ya kawo gurin ku yana ganin ni ban isa nasa shi yin abinda nake so a rayuwata mena rage rayuwan Aliyu dashi malam ? Babu tsohon ya bashi amsa cikin katseshi saidai ina son kayi amfani da iliminka ka tuna ba a canzawa mutum kaddaransa. Addu zakayi Allah yasa hakan shine alherinsa dashi damu baki daya iya gata yaron nan ya samu kuma an nuna mashi amma kaga ya nace shi karatu zai tafi ya karo ba zai tsaya kasuwanci sai kayi tunane ka barshi. Rayuwa fa kowa da kalan tasa haka ra,ayin wani daban da naka koda kuwa kana ganin ka isa juya mai naka ra,ayi . Kwarai kuwa malam don gashi nagani Aliyu ya nuna min bam isa ba niba zan hanashi zuwa karo karatunsa ba tunda hakan yake ra,ayi. Saidai ya tattaro min kaddarana ya mayar min da abina naba wa yanda suke min hidima suke tausayina suka san zafina da martabana yace sai yayi diploma na barshi yaje jami,a malam yamzu kuma ya dauko zamcen wani karatu can har kasan waje ? Allah ya bashi sa,an hakan malam ya gyara zama tace Amin yanzun naji kayi magana muyi addu,a Allah yasa hakanne alheri ya amsa a cikin bacin rai da amin. To kokai fa dan yau ka barshi kawai yace aina barshi amma ya dawo min da motana da,,,,,,, Alh yakubu na dai fahinci bada son ranka yaron nan zai tafi ba ? Ko daya wallahi tunda bashi kadaine Allah ya ban ba mai zaisa in kwallafa raina gareshi yaje Allah ya bashi sa,a Amin malam yace don ba zan gaji da amsawa ba gareka. Ranan dai basu tsaya wani dogon zance ba tsakaninsu yadda suka saba su fadawa juna damuwansu idan su hadu duk da yanzu sarakuta ya shiga tsakaninsu hakan bai hana halakansu tafiya yadda yake ba. Wanda hakanne kuma ke kawo matsala a tsakaninshi da iyalinshi da hjy Naito matarshi ke gani don suna aminai da malam di har ya auri yar malam din basi fasa hakan ba a tsakanin don haka malam din ke kitsa mai wani abin yakeyi wani lokaci. Ai Aliyu bashi bane dansa kadai don yace shi karatu zaiyi ba kasuwanci ba zaisa aita biye mashi ana faman

Chapter 1 of 5