Share this page
2 / 5
kashe mashi kudi shi kadai ita wanan abun tana ganin kwaruwane a gareta ita da yaranta. Domin yayanta suke kasuwa da mahaifin wanda ta cusasu da karfi da yaji tare da uban da bin boka da malamai da komai haka suka shiga harkan kasuwancin mahaifin nasu ake damawa dasu. Yayin da itako take cikin walwala don diyanta sune a kasuwa suke abinda suke so donshine bata rabuwa da kudi ita ko wani lokaci. Hakkurin kishiyar ta yasa take nuna halin ko in kula da duk abindake gudana a gidan ta cire rai ga komai da sukeyi a cikin dukiyan mijinsu duk da wata rana ana dan kwantala mata sai dai hakan ba sosai ba sai can ba a rasa ba. Duk da hakan kuma baisa an barta ba anbar ko a bar dan tilo daya danta a cikinsu ba wanda kamar ya tsone masu ido yake a wajensu duk da bai saka kanshi cikin harkan da suke kyashinshi saboda ganin da suke suke da yawa a gidan. Hakan sam bai taba damunshi a ransa tunda ya taso ya gane suna hattaransa a cikinsu don tun yana yaro suke nuna basu kaunar ya shigesu. Su hudune maza jere mahaifiyarsu ta haifa sai tazo ta samu mace tajerasu har su ukku mata bayan mazan tana goyon danta na ukkune Alh yakubu ya auro maman Aliyu da suke kira da Hauwa gatsau ba sakaye kamar yadda uwarsu take kiranta dashi a bakinta suma haka suka taso suna kiranta da Hauwa ba wanda ya tsawata daga uwar har uban. Saidai yadda hjy Asmau taso hakan bai samu ba kasancewar Alh yakubu mutum ne mai ilimin addini duk abindake gabansa bai hanashi zuwa daukan darasi daya taso yana dauka don asalinshi karatu ya shigo dashi gari dama. Dalilin haduwanshi dasu malam Inuwa kenan abin ya juye ya zama masu zumuta har kuma aure yashigo tsakaninsu kamar yadda akasari a kasan hausa ake wanan gamayan. Wanda yasa hjy Asmau daukan hakan a cin amana don komai da akeyi gidanje a tarene amma basu duba hakan ba suka dauki ya suka bashi aure don a ruguje mata farin cikinta. Alh yayj kokari a lokacin wajen tausa Asmau ya lankwasa ta komai ya tafi mai daidai ake zaman lafiyan zahiri ba fitina saina boye da akeyi kamar yadda nayi bayani a baya. Koda zancen tafiyan Aliyu ya fito ta kasa boye bakin cikin a lokacin hakan yasa ta hau fada tunda safe tana fadin halan shi wayafi da zaice ba zai tsaya ayi wahala tare dashi ba saidai a kwashe kudi masu yawa a mika mashi yaje yayi bushashanshi dasu wai yaje makaranta. Ita ta gaji da wanan gaskiya dole a canza lissafi yadda aka bashi kudi ya tafi hakama yanzu za a rika ba kowa daidai da abinda aka bashi. Ta gane watau wahalane ba a son yayi shiyasa aka tsiru da karatu meke cikin karantun yanzu banda wahalan banza me ake ganewa ga boko don kawai a cucesu za a dauko zancen zuwa karatu har kasan waje. Duk abin nan hjy Hauwa na daki tana ji bata leko ba duk da bata kira suna ba tasan da Aliyu ake wanan fadan hakan yasa ta shiga tunane watau kiran dayace malam nayiwa mijin nasu ke nan akan karatunshine yakai karabn mahaifin nasu ashe ? Jin abin tayi yawa haka kuma rashin lekowanta shima fitinane yasa hauwa din mikewa ta fito tana fadin hjy wani abu ya farune kuma ? A hasale ta juyo tana fadin haka zakice mana dama banda Aliyu daya mace kan saiya tafi wanan karatun shiririta naahi harda kai karan Alh wurin su malam yayi. Tunda su suka haifishi kuma matsoraci yana gudun su debe mashi ya kasa cewa ,a,a to ba zan yarda ba yadda aka bashi kudin tafiya haka za aba ko wani yaro shima matukar ana son zaman lafiya a gidan nan. Ya dai matsa sai yayi karatun nan karatun nan ni kamar dole narasa me yake damun rayuwan yaron nan uwar ta fada a sanyayye ita kuma hjy Asmau a cikin hasala take fasin koma dai meye shiya sani ni ina ruwana nadai fada wanan karon ba zan yarda ba kura da shan bugu gardi da karbe kudin shi. In anyi magana Alh yace ba ruwanshi a cikin zancen karatunsa to nagaji da jin wanan shirin da kai bai dauka ta juya ta shige dakinta. Koda ya shigo gidan daukan abin karyawa yana gaidasu a ciki hjy babba ta amsa mai gaisuwan nasa ya juya ya tafi don ya saba ganin hakan a gareta wani lokaci abinda ka taso a cikinsane kasani. Dakin mahaifiyarsa ya nufa ya sameta zaune tayi tagumi ya gaida ita da kwana duban inda suke aje mai abinci yayi ya hango kulanshi don gidane da tunda safe za a karya da shinkafa da wake da mai da yaji ko ayi dan wanken filawa da koko shine abin karyawansu gidan. Ba zancen shan shayi ko wani kayan dadi saboda yawansu don ita hjy Asmau yaranta bakwai ga kuma yayan dangi biyu nata a hanunta datake riko suna kasuwanci da mijisu haka kuma akwai yan uwan shi Alh dake zaune a karkashinshi gidan suna tare dasu. Yayin da hjy Hauwa a yanzu yaranta hudu masu rai biyu maza dake bin Aliyu sun rasu sai mata ukku a bayanshi shi shikadaine namiji a dakinsu ke nan. Haidar karan malam kakai ashe wajensu malam kan zancen karatun ka haba Haidar meyasa kake son ja min magana a cikin gidan nan. Fuskansa ya shafo ya kai zaune a kasa ya soma fadin mama idam ba can naje ba kinsan Alh ya kafe ba zai barni ba ni kuma ina son zuwa karatun nan wallahi. Ka bar dangata yan uwana a cikin harkan gidan nan don Allah kana ja masu zagi da tozarci dama hanyar haka ake nema a fadawa mutum magana a fakaice. Yanzu mama kada inje wajensu wa nake dasu bayan ku a duniyan nan idan basu ba nayi da baba ya barni jn tafi ga dama ya samu amma don wani dalili na baba sai yace ba zan tafi ba mama ? Tunda ba dole bane tafiyan nan ka barshi mana don Allah banson abinda zai kawo fitina ya hana zaman lafiya kasan halin mamaku idan abinta ya motsa ? Kiyi hakkuri mama don Allah ki barni in tafi ki dai min addua shi nake bukata a wajen ki addua ina yi kaima kasani nagode mama ya fada ya dukar da kanshi kasa shiru yayi yana tunane. Yasan tunda uwar tayi magana dole akwai abinda ya faru dayasa harta tareshi da zancen ba kowa bane kuma yasan mamace zata bata mata rai kan zancen tafiyan nasa tunda yasan bata son karatunshi da yakeyi. Muryan mahaifiyar yaji tana tambayanshi yaushene tafiyan naku ya dago kai da idanuwansa da sukai ja don damuwa yace karshen watan nan insha Allahu. Tafiya yazo hakane kusa dama ashe kanata shiri akan zancen banyi tsamanin Alh zai taimaka maka da wani abu ba mai tsoka don haka zan baka sarkana kaje kasuwa ka sayar ka rike kudin ka kara. Da sauri yace a,a mama bar sarkanki don Allah ba sai kin sayar da sarkaki ba akwai kudin dana jima ina tarawa a wajena ina ganin zasu isheni kuma gwaunati tace zata dinga tallafa muna idan muje sai inyi maneji yadda na saba a baya. Amma kasan can ba nan bane wajene na kazo nazo ba zancen taimako a irin wajen nan yace mama kada ki damu akwai Allah ba zan zauna ba zan nemi abinyi a can din insha Allahu. Tausayi yaba uwar tayi shiru tana ajiyan zuciya ita dai duk da ance uwa bata ganin laifin danta duk da haka bataga matsalan da ake kira mashi yana dashi ba ko za,ace yayi abu idan abincika shike da gaskiya. Amma an dauki tsangwaman duniya a dora gareshi ko laifi wani yayi jafin a fadi suna mutanen gidan zasuce halan Aliyu ko ? Irin hakan yasa ya koyi nisanta kanshi da kowa nagidan iyakanshi dasu gaisuwa kowa ya kama hanyar gabanshi suna mashi kallon dan wahala ne shi. Koda Alh ya dawo hjy Asmau ta tayar da zancen cikin daga murya ya soma fada yana fadin na aikeshine da zan bashi kudina ko kwandala ba zan iya tabawa a kudina in kara mashi ba. Shi da yace zaiyi sai yaje can ya nemi mafita da zai fisheshi shiya san dabara itako sai fadi takeyi ni da kada ai min barazana idan bangani ba akai mai ai Allah ya ganan min tasa kai ta fice daga dakin. Sauri takeyi cikin kodaddun tufafin makarantanta da suka kode sukai fari don tsufa tayi bi a canza mata tufafi abin ya faskara ba halin hakan ana neman abinda rayuwa zaici ba zancen tufafin akeyi ba a yanzu gidan. Duk saurin maryam saida ta tsaya gaban wani mashin ta duba fuskanta kana ta kara gaba daidai kwanan gidansu ta tsinkayi kawarta mairo taji ta fada tun daga nisa don tasan bata son sunan donshi intaso batawa maryam din rai take kiranta da wanan sunan na mairo. Fuska ta daure tayi kamar bata ganta ba hakan da tayi bai hanata karasowa wurinta ba tana fadin tun dazun nake nemanki ai in fada maki babanmu ya sayo sabuwar mota yace wanan a dinga kai mu makaranta dashi. Nayi maku murna muma Allah ya bamu gidan mu kin jiki don Allah kuda ko maahin kuna nema a gidan ku bakiga tsaleliyar motar da Abba ya saya bane fa. Muma wata rana Allah zaiba baban mu ya sayo muna ta kara fada dariya salman ta kwashe dashi maryam ta watsa mata harara ta nufi gidansu. Haka din ne don da yamma taga motar a kofan gidan tare da baban nasu da wasu ana duba don gulman maryam tasa kai ta shiga gidan. Sallamanta maman su salma din ta dago kai ta kallota ita dai kawai take jin tsanar yarinyar a ranta badon tayi mata wani abu ba haka dai kawai jininsu bai hadu da maryam din bane gata kuma da yarta tip da taya suke ko yaushe suna lake da juna . In fada ya kama suyi dambensu ko a cikin gidansu maryam dinne ta fita da kuka ko bacin rai bai hana gobe kuma ta koma gidan acigaba don ko bataje ba salma din zata biyu ta har nasu gidan. Labe labe ta soma yadda ta saba don koda take yarinya ta san irin tsanar da maman kawar nata tayi mata donshi take shan jinin jikinta idan mama din tana waje ta shigo. Ke baki iya gaisuwa bane kin shigo kina zarewa mutane shegun idanunki kamar me neman wani abu to kawar taki bata nan sunje gidan kakansu tun dazun. Saiki kama gabanki jin hakan yasa maryam din ta juya da sauri don barin gidan din bata da tsoron Allah take fadin nidai yaki nan zo ki wanke min kwanukancan kan ki tafi. Maryam din duk da satan hanya tayi tazo gidan bai hana taje ta wanke kwanukan ba tana zaune tana waya tana bada labarin zancen sayen motan mijin nata. Matar irin yan barikin matan nan ne masu coge dan kwali a goshi bakinta baki shi kansa maryam har gobe idan ta shigo gidan take yawan kallonta don mamaki take yadda yanayin bakinta ya bambamta dana sauran mutane data sani ga kuma tsaga a fuskanta wanan yakan bawa maryam din mamaki matuka. Har takusa gamawa waya takeyi tana sauri ta samu tabar gidan lokacin su Salma din suka shigo gidan da yan uwanta bata kula da maryam dakewa uwarta aiki ba akbarkacin ta sai shagwaban data zube sunawa uwar suna bata labarin gidan kakan nasu. Yarta ce ke fadin ke salma ga kawarki can fa tana muna wanke wanke sai lokacin matar gidan ta juyo tana fadin ai salma idan baki daina kwaso min yarinyar nan mai siffan yan ruwa kina shigo min da ita gida ba sai naci kaniyarki wata rana. Haba dai mama gata tana maki aiki kina kuma zaginta kafin uwar tayi magana uban ya shigo yana fadin yauwa gakuma a hade baein baku alkawarunku tun kan na manta da hakan. Yasa hannu a aljihu ya debo kudi sabbi fil yana mika masu saida yabawa kowa maryam na rabe a bango don tagama zata tafi saurawa dayan yar salma din tace ga mairo can daddy abata . Wata mairo kuma mairo yarsace da za a bata ke kin gama kizo kije gidan ku banson gantali marance yayi haba dai keko ina kawar salmace bari man in bata ? Ya mikowa maryam din wanda ya zaro uwar tabi da harara tana fasin daidai zaka bata dasu haba dai alh ina laifin ka bata ko dari biyu ? Barta dai a bata rabontane ya ratsa da ita ya mikawa maryam din kudin har kasa takai tana karba tare da fadin angode Allah umfana yace amin yar albarka kunga yadda ake yaba kyauta ba kamar ku ba kun amshe babu godiya. Wanan ce zata koya masu wani dabi,an kwarai ke fita dan Allah tun kan na amshe kudin nan daga hannun ki yanzun nan kuwa bai min wuya kin sani. Da sauri maryam din ta juya ta fita daga gidan tana sauke numfashi sai lokacin ta tuna da aiken mama dataja mata kunne kan tayi sauri hakan yasa ta karasa taje ta sayo gishirin kwana ta samu ta nade kudin yadda wani ba zai taba ganinsu a jikinta ta nufi gida. Tun daga nisa ta hango mama na leke a kofan gida hakan yasa ta kara sauri aiko tana zuwa mama din ta figi gishirinta tana fada takai mata rankwasa a kai tare da ja mata kunne tana zaginta da gantalala kin san gidan ubanda kika tsaya. Kinci arziki yau kudin nan basu fadi ba don wallahi da an biyani kudina don bansan babu ni a wajena don Allah bace min da gani shasha kawai. Haka suka karaso ciki mama sin nata zabga mata zagi dake alakantata da tsiya wanda ba a son anawa dan musulmi shi a bakin mutum. Wuri ta samu ta zauna don har lokacin tana sababi da ita tana fadin abinci harya bushe ace yarinya daga karbo min gishiri kina can kina ta zubar dinki na gado ? Uwar dai bata daga kai ta kallesu ba sai aikin gabanta takeyi ba wankau da yan matan unguwan suke kawo mata harma da wasu matan aure dashi take samun na dan laluran daki wani lokaci. Kyalewan da inna din tayi shine kuma ya batawa mama din rai ta koma fadin ba doke a kyaleni ba tunda an mashemi mara hankali a gidan kamar mairo za a aika ace ta tsaya shirirta in ba sakarci ba ? Nazo ina magana kowa ya zuba min ido ana kallona gobe in aiketa in halinane yar iskan yarinya kawai mara mutunci in ina da rana kowa sai yaji a gidan nan. To me kike son ince kuma yanzu bayam wanan fadan da kike mata inyi magana kuma kice naji haushi kina mata fada shiyasa ni yanzu in kuna abinku ban saka maku baki wallahi. Ke mairo ina kikaje tun dazun ke meyasa bakijim maganane wai baki gudun baki kullum a cikin laifi kike kika kara hakan saina karyaki a gidan nan muryam mahaifinne yake fadin haka ga yar tashi . Mama data gama yarfa mai race daga baya ke nan ai mu zuba da kowa a gidan nan ni za a nunawa mairo yar soce in yar soce mugani a kasa don Allah ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/18, 9:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , 3️⃣ HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sai bsyan shigan mama din daki na banye habar zani nafito da kudin wurin baban mu naje na mika mai ina fada mai babansu salma ne ya ban kudin. Na kwashe yadda mukayi na fada mai hakan yasa innan mu tabar abinda takeyi tazo tana saurare ko basuyi abinda sukeyi ba lokacin watau magana da inkiya irinta kurame na dade da sanin kamar suna tsoron mamane itace basu son su daga murya taji. Naga babana yace a bari yaje ya mike ya fita inna ta jani zuwa daki tana min tambayan daya ban tsoro donni a lokacin dana karbo kudin sam banji komai a raina ba sai yanzu danaga action dinsu tsoro ya shigeni. Nasan inna ta hango fitowan mamane yasa naga ta barni ta fita muryan mama din naji tana fadin ina kuma shiya tafi yanzu na barshi zaune ai ko wani makircin aka samu kowanku yabar tsakar gidan mafarin akiyoyin mutane su shigi suyi min barna. Nagama baku abinci kuyi min sakaiyan tsiya abincin na duba ba wani abinci bane fa namu rabon kanzone na kasan tukuya ake kwaso muna nida innan mu da kannena biyu. Shine kuma ko yaushe akai magana mama tace tana ciyar damu daga mu har ubanmu bamu da daman dogon motsi a gidan gorine zai biyo baya yasa innan mu bata wani motsi tana kuma yini a wahalce ga aikin gida ga nata sana,an. Shiko baba yana zuwa kofan gidan ya tura yaro a sallamo Alh ya dan jima bai fito sai gashi ya fito tun kafin ya karaso ya soma fadin a,a mlm Abdullahi kaine ashe ? Nine Alh suka gaisa ya soma fadin yarinya ce yar wajena ta koma gida muna da wa yan nan kudin wai cewa kaika bata ? Murmushi Alh ya sauke kafin yace kwarai don nabawa yarana kamar yadda na saba idan dan wani abu ya shiga hannuna tana wajen yasa itama na mika mata don rabonta ya ratsa tunda tana wajen lokacin. Amma Alh kamar kudin sunyi yawa ai mlm Abdullahi yarkafa yatace nima kuma bayan hakan muma muna more mata a gidan don yanzu haka idan kaga tulin kayan data wake a gidan na abinci sai kayi mamaki don haka don mun mata alheri ai bai zama wani abu ba. To Alh kasan yaran yanzu duk da bata da irin rayuwan nan amma dan yau baka shedanshi hankalinmu ya tashi sosai wallahi da ganin kudin nan . Wallahi ita da yan uwanta na rabawa kada kaji komai baba ya dubi kudin a hannunsa ya juya ya sauke ajiyan zuciya yace to Alh mun gode Allah ya karawa arziki albarka. Amin nima nagode naji kuma dadin tasowan da kayi kazo ka bincika hakan daga gareni ga wanan kaima ka kara ayiwa iyali hidima dashi wancan kuma kudin cin tarane na basu ai ba wani abuba don yanzu idan na koma saina dauki lokaci ban dawo garin nan ba yasa nake masu hakan. Ya mikawa baba kudin yayi godiya sosai ya bada baya ya koma fadin da yamma bayan magariba azo a amshi dan wani abu don iyali. Haka baba ya dawo gida kafin ya dawo na kula da tashin hankalin da mahaifiyana take ciki don gudun jin mugun labari akan kudin bayan sakani daki da tayi ta tsure nayi mata rantsuwan cewa wallahi bani yayi kuma dadewan da nayi wanke wanke hjy tasa nayi mata . A lokacin maman su hafsa din bata koje makka ba kudi daine ya fara tasowa mahaifinsu suke jin kansu a cikin unguwar. A lokacin abu biyu sukafi tsayawa inna a rai na farko kardai ace dauko kudin nayi bada sanin su ba don kudin a ganinsu yafi gaban kyauta ga yaro. Sai nabiyu kuma rokon Allah take Allah yasa ba wanan bawan Allah ya kasance irin masu batawa mutane diyansuba yazo ya lalata mata yarinya ga banza ta shiga wani ukkun kusa da tara. Saiga baba ya dawo ya zauna ya bude abincinsa yaci gaba daci mama ko ta kara shiga firgici ina kallon sanda ya saci ganin mama yayi mata inkiya da hannu alaman babu komai ai. Lokacin na sake labule ina ajiyan zuciya na jawo matattacen roban abincin da mama kan dan watsa muna kazo na dan kyafata ina kaiwa cikina abincin cikon wani yanayi na tausayin mu. Baba na gamawa ya fita daga gidan har mama na zolayanshi da yau kuma me aka samune za a fita yace kinsan abin Allah bari dai in fita in ga garin. Ba,ako jima ba sai gashi ya dawo da cefane irin ta maza mama dake duke saida ta mike tana kallonshi cikin mamaki a kofan mama din ya aje yana fadin aina fada maki abin Allah yawa gareshi gashi ko kin gani na fita a cikin sa,a yau. Malam wanan ba karamin cefane bane fa kayo muna ya kai zaune ya soma fadin meye ranan samu ga mutum Rakiya idan Allah ya kawo alheri iyali su sheda hakan. Duk zancen da baba keyi idon mama yana a kan ledojin daya shigo dasu din kafin ta bar aikin da takeyi ta karaso wajen kayan ta duka ta soma budewa tana jagula. Dan shimkafane da ba zaifi sa,i ukku ba sai alaihu da kayan miya budan bakin mama sai cewa tayi Ai kawo roba a raba da sauri baba ya dago yace me za a raba kuma a nan Rakiya ? Ohh to kai kaga hakan ai gara a raba don idan ya kare kuma kowa yaci barnanshi kuma ni yanzu na gane ai kowa ya samu kansa ya sani ashe ? Wai meya kawo zancen nan kuma Rakiya tace meye ma bai kawo ba Allah ya kyauta ina ta fada ta dago kai tana fadin inna Isa dauko roban ki kawo mata da dan gora. Isan banza isan baka isa ba watau ke har kinga abincin yau mijin ki ya kawo zakiyi min maganan bamza ko dadina da gobe saurin zuwa. Yanzu kuma yaya mena fada don Allah kince a kawo roba nace ta dauko nasan tunda kika fadi hakan sai an raba shine kuma laifi yanzu. Ai da kin sani kada ki bata bakinki indai wanan dan abinda kike gani har yasa zakiyi min rashin kunya yau a gidan kece kika taso a hakan a tsiyace ni ban saba da wanan rayuwan ba sai da aka dauko muna alkakai a gida yanzu. Baba na kurum baice komai ba tana fada tana rabawa da suna sunan daki kinga ke nan mu za a kwara a dakin mu don gwangwani gwangani tayiwa kowa da sunanshi har wa yanda basa nan saida ta cire masu. Ina tsaye na rakube ina dana sanin bawa baba wanan kudin gashi yanzu gaba daya ya koma hannun mama ke nan da dan abincin daya sawo muna. Nasan ya gaji

Chapter 2 of 5