Share this page
7 / 7
ta haihu za su kusanci juna, bayan an sake ɗaura musu aure, sannan kafin nan da zai aura Ruma, shine yanzu aka sauke gaba ɗaya. “Damuwata ɗaya wai Fahad, Fahad..........yaron da ko gaishe Ni ba ya yi saboda ba ma wani jituwa da uwarsa. Shine wai zan bawa ƴa ta............hmmmmm............” da sauri Ruma ta katseta tare da share hawayenta tana cewa. “Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Duk ƴar iskan da ta aura Ayan ta shiga uku.............sai ta kwammaci dama mutuwa ta yi da rayuwa da Ayan ɗina...........Na tsane shi Ammee wallahi na ji ya fita min a rai...........tun.....tun ina yarinya nake sonsa.....ko sau ɗaya bai ta ɓa min magana mai daɗi ba...a...a...amma haka nake ta nace mai, kullum ce min yake Ya baya sona. To nima daga yau bazan ƙara son shi ba har abadaaaaa....." Da haka wani irin kuka ya ƙwace mata. Jikin Ammee ta faɗa tana kuka sosai, ganin haka ran A.G ya ƙara ɓa ci sosai, kafin ya yi wani motsi sai aka kuma murdo handle ɗin kofar aka shigo. Baba Yusuf ne ya shigo shima ranshi a matukar ɓa ce. Yana jin iri kukan da Ruma ke yi hankalinsa ya kuma tashi, dan kuwa a duniyar nan ba ya son ganin ɓa cin ranta ko kaɗan. “Ruma, is okay. Ni na ce na warware alƙawarin auren da ke tsakanin ku, saboda Ayan sam baya sonki. Kuma mun tabbar da maganarsa, sau biyu muna zuwa asibitoci ana kwaji kuma dukka result ɗaya ne, sannan har yarinya da ta aikata musu haka mun sameta, ta yi ta kuka akan kuskuren da ta yi........Amma ganin yarda kika shiga damuwa shi kenan zan yi ma......” da sauri Ruma ta ɗago tana cewa. “Dad wallahi ko maza sun ƙare ba zan aura Ayan ba....na tsanesa wallahi." Ta faɗa tana nufa bedroom ɗin ta da mugun sauri har tana bugewa da fridge amma ba ta sani ba. Da idanuwa suka bi ta har ta shige. “AYAN.... AYAN.....me yasa? Hmmmmm." Sai Dad ya haɗiye sauran maganar yana nufan nasa room ɗin. Tafiya yake yana ayyana abubuwa da yawa akan Ayan. “Ina zuwa." Ammee ta faɗa tana bin bayan Ruma. Dafe kai A.G ya yi sannan ya fita daga ɗakin yana fatan su haɗu da Ayan ko yayane ya faɗa mai ɓakar magana, dama ba wani shiri suke ba saboda halinsu be zo ɗaya ba sam. Ammee na shiga ta ci gaba da rarrashin Ruma har sai da kukan ya tsagaita sai faman sauke ajiyan zuciya take mai sauti sosai. “Ki bar kuka, wallahi Ayan sai yasan ya yi kuskure, sai ya san ya cuci kansa....ke kinsan kaf gidan nan gaba ɗaya iyeyenku maza sunfi sonsa da ƙaunarsa. Shi yasa tun fari na fara dasa miki soyayyarsa, to a yanzu ya ja ma kansa dan kuwa da wannan ɓacin ran zan yi amfani wajen cusa tsanarsa wajen Dad sannan da sauran ƴan gidan......a yanzu nasan babu wanda za su ba Shugabancin masana'ata shine Fahad........kuma kin ga yanzu shi za ki aura, sai ki samu ki janyo hankalinsa sosai, sauran kuma sai bayan an yi bikin.” ta faɗa tana kallon fuskar Ruma. “Shike nan, amma wallahi sai na rama abin da ya yi min, ya auro duk wacce zai aure, ai duk tsiya za ta shigo *GIƊAƊO MANSION*, sai na tarwatsa mai farin cikinsa.........sannan hatta Uwarsa da Ƙanwarsa da nake ganin su sa gemu, duk da banso ba............to ya shafesu......Balle Sarah da Ayan yake sonta hmmmm." Ta faɗa tana ƙwafa. “Karki damu ƴata ai kowa wannan al'amarin ya shafa.....auren nan kamar zubar da Wasiyyar Kakan kune." Ta faɗa tana ɗaukan mugayen alwashi akan Ƴan ɗakin su Ayan....... Baba Yusuf ne zaune a gefan gado yana jin zuciyarsa na mai raɗaɗi sosai, daa yana son Ayan sosai, dan ya fi ƙaunarsa akan yarda yake sun A.G, sai dai tun faruwar al'amarin nan ya fara fitar mai a rai, balle yau shi yasa ya ce ba zai aura Ruma ba. Wani irin kallo yake mai irin na wanda ya ci mutuncin Mahaifinsu *GIƊAƊO*. “Ayan sai na sa ka yi kuka da idanuwanka akan abin da ka yi ma Ƴa ta, sannan ka ci mutuncin Kakanku sai ka kwammaci da ba ka san ƴar iskan da za ka aura ba gobe." Ya faɗa yana rintse idanunsa tare da tafe kai, dan al'amarin ya mai zafi sosai. *AYAN* Zaune yake akan kujeran dake garden, wajen akwai tsaftatatciyar iska mai bushawa sosai, dan kuwa akwai bishiyoyi sosai. Shi kaɗai ne zaune ya ƙura ma Swimming pool ido kaman me na zarin adadin ruwan dake ciki, amma a zahiri ya tafi duniyar tunani ne. _Abubuwa sun faru wanda tun daga farko shi ya tsara komai bai san matsala za ta iya biyowa baya ba. Kamar yasani sai da ya je asibiti biyu wanda yasan tabbas ƴan gidan na zuwa. Roƙon doctor's ya yi akan idan ƴan uwansa sun zo su ce akwai ciki sannan ga adadin lokacinsa. Alhamdulillah haka komai ya ta fi mai, sannan sai da suka nema wata a department ɗin A'isha ta amsa ita ta aikata haka. Abin da yake sanya shi damuwa shine *Ummee* gaba ɗaya hankalinta a tashe yake tun bayan bayyanar komai ga ƴan gidan, ranar Ummee tasha kuka, amma saboda tasan ba da gangan ya yi ba sai ta sauka daga fushin. Amma wunin yau kuwa, babu annuri a tare da ita, sai ya ji duk babu daɗi, so yake zuwa an jima ya leƙata sai ya ƙara ba ta haƙuri.) “M.D.” jin an kira sunansa babu sakayawa ya sa ya kalla A.G dake nufosa cikin fusata da ɓacin rai. Kaf gidan babu mai kiran sunan sa saboda sunana Baba Giɗoɗa ne, shi yasa yake da farin jini, wasu sukan danganta hakan sunan da ci ne. Miƙewa Ayan ya yi, dai-dai nan A.G ya iso gabansa yana wani muzurai kamar damusa. Dama sam ba sa shiri, ko gaisawa ba ta wani haɗasu duk da zasu aura ƙannan juna ne. “Akan me yasa ka fasa auren Ruma? Eh akan me yasa? Wannan ai rashin mutumci ne, yarinya tun yaushe take sonka duk abin da kake mata haka take ci gaba da sonka amma a yau wai an sauke auren ku!!.” ya kai nan kaman wanda zai buga Ayan. Tsayinsu ɗaya amma Ayan ya fi A.G cika, da haiba, amma bayan wannan komai suna da shi ne zaratan maza, jarumai masu siffar ƙarfi da jarumta. Ayan kuwa murmushi ya yi mai sanyi sannan ya ce. “Abbeey (Bana Yusuf) da kansa ya ce anfasa, dama ni ba so nake ba, kuma da kake cewa tuntuni take sona, shin ni na aiketa? Na fita hakƙinta tun da tasan bana sonta......” “Hmmmmm nima na fasa auren ƙanwarka!.” ya faɗa duk da yana mugun son Sarah. “Wallahi da na fi kowa murna, kai kanka kasan ba sanka take ba. Hmmm wannan labarin ne mai daɗi, Bara na je na sanar ma Sarah.” da haka ya kewayeshi ya nufa Main door. Ayan be son ya jima yana magana da A.G dan zasu samu babban matsala, A.G akwai shi da naci, shi kuma be son maimaita abu ɗaya, kuma yasan A.G komai zai faru sai ya auri Sarah Dan ba ƙaramin sonta yake ba. Murmushi kawai ya yi ya shiga ciki. A.G ƙafa yasa ya buge kujerar dake gabansa, ɗan huci ya fara yi kaman wanda ya ci gudu, sai kuma ya zauna yana tunanin ta ina zai fara. “Tunda ba ka so, to wallahi sai na aureta............eh sai na aureta......Ina son Sarah amma saboda kai Ayan zan ƙuntata mata, zan sa ta sha wahala sosai, sai daga baya na ba ta haƙuri, amma yarda Ƙanwata ta yi kuka, haka zan sanya ta ka ƙanwa.” ya faɗa cikin ɗaukan alwashi sannan ta furzar da iska daga bakinsa.. ****************** Ummee ce zaune kan prayer mat tana kallon Yaranta su huɗu da Allah ya ba ta, ita da Ammee sune kawai masu yara huɗu-huɗu, amma sauran suna da yawa. Dan Baba Musa yaransa 9 maza huɗu mata biyar, duk sun yi aure a cikin gidan. Sannan shima Baba Yunus yaransa 8, 5 sun yi aure , sai Namiji ɗaya Fahad da kuma mata biyu amma su ba su girma sosai ba. Baba Yunus matansa biyu, haka Baba Musa shima, amma Abba matarsa ta biyun ta rasu tun shekarun baya, yarinyarta ɗaya, ƙanwar Sarah ce amma ita booding school. Rufaida ita ce babba a ɗakin ta aura Yaron Baban Musa na farko, sai Abdulrahman shi kuma ƴar ɗakin Baba Yunus ya aura, sai Ayan da kuma Sarah. Duk suna zaune jikinsu a mace da abin da ke faruwa. “Ummee...." Da Sauri Ummee ta ɗaga mai hannu alamun ya yi shuru. Shurun ya yi yana kallon ƙasa. “Ni ba wai auren wata ne ban so ba, kai yanzu har kana fatan ka auro wata ta shigo gidan nan?...........kai yanzu idan ka kawo ƴar mutane nan gidan ba ka cuce ta ba?............idan kana kusa babu wanda zai yi mata komai, amma idan ka fita ba?........mu kanmu ya muke a cikin gidan nan..........sannan abubuwan nan da suka faru kowa ransa ya ɓaci da kai sosai, hatta Abba shiru kawai ya yi, ni dai da ka ji nawa ka aura Ruma ɗin, ko dan ita maiyuwa mu samu wata iska mai daɗi a gidan.” ta kai tana jin babu daɗi, sannan ta ci gaba. “Kamar yarda Abbanku ya ce............*Rabo*, shine zai kawo A'isha gidan nan. Ina fatan Allah ya baku zuri'a ɗayyiba.” da haka ta miƙe ta shige room ɗin ta. Jikinsu duk ya yi sanyi, tabbas a gaba ɗaya gidan suna samun takura da matsi, dan ma suna da baki shine suke san iska. Sai gashi Ayan ya rikito musu babban aiki. “Ni yanzu Sarah na ke ji...........A ganin su Ammee za su bar maganar nan ne? Za su iya ɗaukan fansa akan Sarah." Rufaida ta faɗa cikin damuwa. “Anya Ahmad zai iya bari a cutar da ita? Yana sonta sosai.” faɗin Abdulrahman sai Ayan ya ce. “Hakane, amma kuma ba wani zama yake ba. Sai dai mu ai muna nan.” ya faɗa yana riƙo hannun Sarah. “Yaya Ayan, karku damu Ni na yarda da mutum ba zai tsallake ƙaddarar sa ba. Yanzu dai gobe ne auren na ka ko?.” sai ya yi murmushi yana mai ɗaga mata kai. “Angon da babu shiri, gidan ma kaman ba biki ba.........” “Maman Hibba (Rufaida) shi kansa angon ba wani natsuwa ga rai ba. Fatana a kawo amarya lafiya ba tare da anyi rikici ba.” “Ameen Sarah.” da haka suka sauya hiran akan na bikin duk da babu abin da za'a yi sai dai walima, haka dai suka tsara kuma suna fatan komai ya tafi lafiya dan sunsan ƴan gidan nan balle wannan shine karo na farko da za'a kawo mace cikin gidan.........✍️ END. > Ya Allah 😓, hmmmm ba zance komai ba gaskiya. > Nifa har yanzu ba mu shiga labarin ba, wasa kawai muke yi 😬😬😬. > Typing mood 😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩🥴. A nan zan katse muku dan kar na baku cittan da yawa. Sai dai ku sani bamu yi komai a labarin ba. 1. Shin ya rayuwar A'isha da Ayan za ta kasance a *GIƊAƊO MANSION* 🔥. 2. Ya *Ƴar NOLLYWOOD* 🔥 ne? Kusan dramer da zai biyo baya kuwa..........Za ta yi? Ta yaya? Idan ta yi mai zai biyo baya?........kai jama'a ku dai jiraye Ni a book 2. Ina faɗa musu kwanan Zafin na sa daban ne, dan 1 bisa 5 muka yi, wannan duk sharan fage ne, ainihin cittar yana book 2. BOOK TWO IS FIVE HUNDRED ONLY ₦500. Ga Mai so ya min maganan direct....... 08126151523/07038436703 Pretty Sk ce 😁🥰🥰🥰🥰🥰. I love You All my FAN'S 😘. Akwai wani book da zan sadaukarwa wa ku insha Allah mai suna SAKEENAT 😓, ba zan ce komai ba ku dai nema kawai 👌👌👌👌❤️ *SAKEENAT ABDULLAHI ✍️😁* ```TALLAH! TALLAH!! TALLAH!! Na Book 2.``` _________ _GIƊAƊO MANSION_ Wannan daren akwai jama'ar da suka kasa barci, wasu sun yi amma ba na daɗin rai ba, duk da akan abin da ya faru, mutane da yawa sun shirya tarwatsa farin cikin da ya rage ma Ummee da Ayan, sun shirya hargitsa rayuwar ƙaruwar da ya kawo, sun shirya haka tuggu iri-iri a cikin gidan, da dama kowa ya kwanta rai a ɓace, ya yin da suke tunanin Ayan yana can shi da ƴar iskan ƙaruwarsa suna jin daɗin juna..........✍️ ________“Uhmmm dama ina da sha'awar film ne.......duk da a yanzu karatu nake amma ina so.........shine na ce ba ra na tambaya ke. ” ina tura mai ya gani dan haka na gyara zama na sosai ina jiran amsarsa. “Ok, sai dai ni ban san wani manya a fina-finan kannywood ba, kinsa Ni NOLLYWOOD nake yi, amma zan bincika miki.” Murmushi na yi ina tura mai. “Sir A.G, NOLLYWOOD ɗin nake so.”........✍️ ______“Ƙanwata, ai na yi fushi ace ba ki ta ɓa nema na a waya ba sai yau, ko gaisuwa ai.......” da sauri ya ji ta katseshi cike da masifa tana cewa. “Ni ba gaisuwa na kira mu yi ba. A yanzu kai miji ne ga Yayata, to Kira na yi dan na yi maka fashin ɓaƙi, nasan ba lallai ka gane hausan ba idan A'isha ta faɗa maka........Amana na baka ita, ka kula da ita fiye da komai, ka sanyata farin ciki a kodayaushe, hakan zai faranta min, amma idan wani ya sanyata kuka hmmmmmm to ta na da mai kare mata wato Ni.” tana kai wa nan ta katse kiran..........✍️ ________ (_Assalamu Alaikum, Barka da wannan lokacin A.G.....sunana Inayah maybe ka manta amma kai ka ban number ka. PLS akwai maganar da nake so mu yi is very important.... thanks.-) ............✍️ _________ *Inayah* Na rasa meke min daɗi, nasan yau Yayata za ta sha kuka sosai, shi yasa ni fa banson na yi aure, haka kurin a rabani da iyaye ne, na koma wani gidan, cikin wani family ɗin, na zama kamar mai aiki, miji ya min duk abinda yake so, ya kwana da ni kuma na tashi na yi mai girki.......hmmm shiyasa ban kawo aure a jerin rayuwata sam.........✍️ _________“I'm fine the Star of NOLLYWOOD.” ganin yana online ya sa na koma na kwanta ina jiran reply ɗin sa. Ganin yana on typing yasa na ji wani sanyi yana ratsani sosai, murmushi ya ƙi barin fuskanta, sai na ji duk na ƙosa na ga saƙon da zai turo min....................✍️ _______“To ki faɗa akan menene zan yi alƙawarin.” “So nake ki yi min alƙawari, idan har wani abu ya sameki mara daɗi da mai daɗi za ki faɗa min, bance da sirrin aurenki ba, amma duk abin da ya kamata na sani, to ki faɗa min. A family house aka ce za ki zauna. Maybe akwai wanda za su yi kishi da ƙyawun da Allah ya miki. To Ni dai duk uban da ya shiga harkan ki, ki faɗa min, zan ji da kowa, nan da 8 month zan dawo, to a gidan ki zan cinye hutun, komai da za'a miki kawai ki tara in na zo zan ji da komai, dan duk wanda ya taɓa ki dole ne yi mai wankin babban bargo.” A'isha murmushi ta yi mai sauti. “Sai aka ce miki kowa ne irin ki, kowa ne mai neman faɗa. Kai wallahi na za ci wani abun ne za ki ce.”........... Jama'a mudai haɗu kawai____________₦500 ONLY. 8126151523-Opay number. Sakina Abdullahi 😁👌🥰🥰🥰🥰🥰🥰 *📢 Assalamu Alaikum Everyone!* Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖 Idan kina son: ✅ Sabbin *updates* ✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi ✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman* To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi: 💰 *₦300 only* kafin mu gama. 🕒 Bayan an gama: *₦500* 🌟 *V.I.P Access*: *₦1000* _Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_ Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi. ```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number: 8126151523.``` ~SING BY PRETTY SK~ *ALHAMDULILLAH ❣️* PRETTY SK CE ✍️ 😘😬 LIKES 👍 SHARING 📱📲 COMMENTS 🔥😁 *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇: 📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥* > 8126151523/07038436703 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7