Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zaman ciki ajikinta na kimanin wata ukku da sati biyu. Lokacinda likitan ke sanar dasu, Fauziyya batasan lokacinda wani murmushi Mai d'auke da farinciki ya zubucemataba ba, saboda tsabar Jin dad'i. Magunguna aka rubutamata baban Walid yaje pharmacy ya siyo sannan ya saukesu gida yawuce wurin aiki yanata zaulayar Fauziyya, itadai sai murmushi kawai take tana rufe fuskarta dan wani masifar kunyar baban Walid din takeji. *(Konidai naji dad'i nima saida na murmusa jin Fauziyya nada ciki kusan girma d'aya Dana khairat, Ashe kenan za'ayi twowins gidan salim)* Mmn khady ce πŸ€¦πŸ»β€β™€ [9/20, 7:28 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 35 *Cigiya Cigiya Cigiya, Jama'a ina cigiyar Maman twowins kwana biyu banji comment d'inkiba, Allah sa dai lafiya kike, nayi missing d'inki irin sosai d'innan, khairat da Sani ma sunce in gayamaki sunyi miss dinki*.. *Gaisuwa gareku naji dad'i dakuka kasance cikin tarin masoyana* Mmn Abdul Ashfaty Ummu Aimana Mmn Mash'hud Dakuma *Asiya (Muneefa)* inayinki sosai da sosai. Suna dawowa gida Aunty Safiya takira Mama a waya ta sanar da ita Fauziyya nada ciki, hamdala Mama tayima Allah tace "yau Allah yakawo 'karshen Zarginda Salim da mahaifiyarshi sukema Fauziyya, ashe dama da cikin akayi sakin, Allah kenan maiyin yanda yaso, a duk lokacinda yaso" Baban Fauziyya ma da'aka sanar dashi yayi matukar farinciki, koba kome yasan sanadiyyar cikinda Fauziyya ke d'auke dashi zata koma gidan mijinta. Fauziyya kuwa tanajin sanda Aunty Safiya takira Mama tagayamata wani irin farincikine ke Kara lulle6eta, wai yau itace d'auke da cikin Salim, Shafa cikinta tayi Wanda bazaka ganshi kace akwai ciki na wata hud'u ba, tace Allah nagodema koba kome nasan Salim zai Gane banida masaniya akan abunda yake tunanin na aikata. Tunanin yanda zatayi ta 'karbi wayarta daga Hannun Aunty Safiya take tagayama Salim kyakkyawan Albishir amma tanajin nauyin tambayar ta wayar. *Bayan sati biyu* Aunty Safiya zaune falo tana yankema walida farce, Fauziyya tashigo da sallama, sanye take cikin wata ba'kar doguwar Riga, irin na larabawan Dubai, tayi rolling da mayafin rigar, tayi matukar yin kyau, ga wani irin haske mai sheki da fatar jikinta keyi, tayi luf da ita kamar balarabiyar. Amsa sallamar Aunty Safiya tayi, wuri Fauziyya tasamu ta zauna kan daya daga jerin 'kawatattun kujerun dake d'akin tace "washhh Allah Aunty nagaji sosai, ni wlh jinake kamar na daina zuwa awo d'innan, wlh duk ranar danaje da ciwon kai nake dawowa" Harararta Aunty Safiya tayi tace "ki daina zuwa awo saboda kina raguwa ko, ke kullum Kara ragwanci kikeyi kamar kanki farau ciki, to wlh idan Zaki saki jiki kidage kisaki, idan Kika koma gidanki yazakiyi da aikin gida, kohaka Zaki ri'ka langabewa, bakisan anaso mace mai ciki tari'ka motsa jikiba, (exercise) hakan ba 'karamin amfani gareshiba, ko Haihuwa kikazo zakiga kin haihu cikin sauki da yardar Allah" Yanzu kitashi kije ki watsa ruwa zakiji gajiyar taragu, kizo kici abinci wayarki nanan nasakamaki charge saiki d'auko" "To aunty" Fauziyya tafad'a tanufi d'akinta cikin zumud'i da farinciki, aranta tanacewa Salim shine mutum na farko dazata Fara Kira, yau zataji muryar Hubby d'inta masoyinta, iya tsawon lokacin data d'auka bata tare dashi bakuma tajin muryarsa Koda a waya, ba 'karamar azabtar da zuciyarta hakan yayiba, Dan dai ba yanda zatayi dole ta daure tabi nagaba da itane, ammafa ta azabtu iya azabtuwa. A bangaren khairat yau tatashi da wani irin zazzabi da ciwon kai, ga wani irin kasala dake addabarta, tun tana daurewa har dai taji bata iyawa duk da tasan dalilin rashin lafiyar nata, Rasa inda zata sanya kanta tayi gashi Salim tunda Fauziyya tabar gidan baya kulata, sunan dai suna gida d'aya Kuma tana matarshi amma babu wani abu dazaka gani tsakaninsu Wanda zai nunama itada Salim mata da miji ne. Daurewa tayi ta lallaba tanufi d'akin Salim dukda jiri dake d'ibarta, da sallama tashiga d'akin, amsa sallamar yayi batareda ya kalli inda takeba. Zama tayi gefen gadonshi cikin murya 'kasa-'kasa irinta marar lafiya jikinta na kyarma tace "Dan Allah Salim ka taimaka ka kaini asibiti wlh tunjiya banyi bacciba Ina fama da matsanancin ciwon Kai" 'dagowa Salim yayi ya kalleta, yaga yanda tarame sai wani uban fari data 'kara, idanunta duk sun fad'a, kana ganinta zaka tabbatar da tsananin azabar ciwon dake addabarta. Take yaji wani irin tausayinta yadira azuciyarshi, yace "kije ki shirya inkaiki asibiti" "To" kawai tace tanufi d'akinta, jim kad'an saigata tafito sanye da wani makimancin hijab, kallo Salim yabita dashi dan tunda yake da khairat yasanta baitaba ganinta da hijab ba, tun kafin tayi aure har yanzuma datayi auren batasa hijab, shi baimayi tsammanin za'a samu hijab cikin kayantaba. Kan mashin d'insa ya d'auketa suka nufi asibitin. Suna Isa suka yanki Kati sannan sukaje office din likita. 'yan' tambayoyi yayima khairat tana bashi amsa, inda Kuma taga akwai 'karin bayani tayimashi, siring yasa ya zu'ki jininta yakira wata narse yaturata Lab ayi gwaji, bayan minti ashirin tadawo d'auke da takardar sakamako. Marar gaskiya ance ko cikin ruwa ji6i yake, hakane kuwa ya kasnace da khairat, dankuwa tunda narse d'in tashigo da takardar sakamakon gwajin jikinta ke kyarma, Amma tana 'ko'karin dakewa dan gudun kada Salim ya fuskanci halinda take ciki. Amsar takardar likita yayi yasaka farin glass d'inshi yagama dubawa sannan yad'ago ya kalli Salim fusakarshi d'auke da murmushi yami'kama Salim hannu sukayi musabuha, yace "Congratulations, Ina tayaka murna matarka na d'auke da ciki.... Wani muguwar fad'uwar gaba khairat taji, had'eda firgita. Cigaba da magana likitan yayi, "ciki na tsawon wata hud..... Kafin likitan ya'karasa fad'in abunda zaifad'a khairat tafasa wata uwar 'kara tareda durkushe inda take tana dafe cikinta, tana fad'in wayyo cikina....zanmutu.. wayyo Salim zanmutu. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Salim yafad'a doctor dan Allah taimaka mana, yafad'a Yana ri'ke khairat wacce keta faman magowa tana ri'ke cikinta... (Oh ni su khairat an iya pretending)πŸ€” Da sauri likita yakira wannan narse d'in aka Kama khairat aka d'orata kan wani gado dake cikin office d'in, wata Allura likita yayimata kafin ad'auramata drip, bacci kuwa yayi awon gaba da ita. Ganin tayi bacci yasa Salim fita daga office d'in ya fiddo wayarshi cikeda farinciki yakira number Mama yasanar da ita halinda khairat take ciki, zokaga murna wurin Mama, hada taka rawa, suna gama waya tahau Shirin zuwa asibitin. Salim fa bakinshi yaki rufuwa saboda farinciki, dan shima yanaso yaga kwanshi a duniya, amma yaso ace wannan cikin tareda Fauziyya ne. Amma ko khairat d'inma yayi farinciki Ashe dama rabone yasa haka yafaru tsakaninsu sau d'aya tak har ansamu rabo, Allah kenan. Aifa Kuma sai tunanin Fauziyya yadawomashi sabo fill, dukda dama kullum da tunaninta yake kwana dashi yake tashi. *Kuyi manage da wannan muhad'u gobe inshaAllah dan jin Yaya zata Kaya tsakanin Mamar Salim da khairat, akwaifa bada'kala* Mmn khady ce πŸ€¦πŸ»β€β™€ [9/21, 7:48 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 36 *A'ishatu Ahmad Usaman* *Ummu Affan* *Samart lady* *Mum Ahmad* *Rukayya Abdussalam* *Wannan shafin nakune inajin dadin yanda kuke bani lokacinku kuke sharhi akan littafina, Nagode Allah bar zumunci iya wuya ana jone* Kusan awa biyu sannan khairat tafarka daga baccin daya d'auketa sakamakon Allurar da likitan yayimata, da mummunan fad'uwar gaba tatashi, dan tana zaton ko likitan yagayama Salim watannin cikin nata. lokacin Kuma drip d'inda aka sanyamata ya 'kare, wannan nurse d'ince tsaye kanta taciremata kanula sannan tafita daga d'akin, ko minti biyu batayiba da fita Salim yashigo khairat na ganinshi tayi wani irin razana tana niyyar saukowa daga Kan gadon, saurin ri'keta Salim yayima yace "Haba khairat miyasa kike haka, kobakisan abunda ke tattare dake bane, yakamata kinutsu kada kijawomin asara Kuma" Wani irin murmushi jin dad'i khairat tayi koba kome tasan Salim baisan watannin cikintaba, langa6ar da Kai tayi tace "kagayama likita ya sallameni nawarke banison zama asibiti" "Eh dama yace idan ruwan ya'kare zamu iya tafiya, yanzu kitashi mutafi, Amma Zaki iya hawan mashin d'in kodai insamo mota?" "A'a bakome zanhau mashin d'in ainaji sau'ki sosai," Tashi tayi tana Sanya hijab d'inta Salim d'in na gyaramata, Mama tayo sallama, Amsawa Salim yayi tareda matsawa nesa kad'an da khairat d'in cikedajin kunyar yanda Mama ta iskesu. Kallonshi Mama tayi tayi wani guntun murmushi Wanda ita kad'ai tasan ma'anarshi. Karasawa tayi wurin khairat d'in takama hannunta tana jeramata sannu, itako sai wannan langa6ewa take, ita adole gamai ciki. Salim ne yace "ai yanzuma zamu wuce gida, Allah ma ya taimaka da mumsha ban-ban tunda muna Shirin tafiya kina zuwa" "To Alhmdlh, tunda nazo kaje kasamo Mana mai napep saimu hau nida ita, kaikuma saika biyomu a mashin d'in" "To" kawai Salim yafad'a sannan yahau mashin d'insa yatafi, bayan mintuna goma saigashi yadawo da Mai napep, Mama dake ri'ke da hannun khairat tanata riritata kamar wata jaririya, suka shiga napep d'in Salim yabiya kud'in sannan suka d'auki hanya. 6anagaren Fauziyya kuma, tunda Aunty Safiya tabata wayarta Bata bud'etaba sai yanzu tana zaune tsakiyar gadon d'akinta kad'aici duk ya addabeta, su Walid da Ahmed da walida basunan sunfita Shan ice cream suda dady d'insu. Wayar ta d'auko ta danna fawa, tana kallo takawo haske tagama loading...... Sannan ta kunnu, Sim yafara updating.... Yana gamawa tareda shigowar sa'konnin Salim, kusan guda bakwai. Zama Fauziyya tayi tafara duba sa'kon d'aya bayan d'aya. Na farko dai Yana sanar da ita yadawo gida Yana jiranta d'akinsa, mamakine yakamata data duba lokacin shigowar sa'kon dakuma kwanan watanshi yayi dai-dai da ranar da Salim d'in yarubuta mata takardar Saki, sauran sa'konnin Kuma yanaso tagayamashi inda take, wani sa'kon Kuma rantsuwa yakemata da Allah shifa bai saketaba, a wani massage d'in Kuma Yana ro'konta Alfarma data taimake rayuwarshi duk inda take tagayamashi ko inane zaizo ya sameta. Fauziyya tana gama karanta sa'konnin tafashe da kuka, wani irin tausayin kansu itada Salim yakamata, wannan wane irin murd'adden Al'marine, Fitowa tayi daga d'akin tana kuka tanufi d'akin Aunty Safiya, kusan Karo sukayi da ita tana niyyar fitowa daga d'akin. Kallon Fauziyya tayi wacce duk tabi tarud'e ga hawaye share-share a fuskarta tace "ke lafiya meya faru naganki haka"? Wayarta tami'kamata tace Aunty Safiya ki karanata wannan sa'konnin Wanda Salim yayimanine duka" Amsar wayar Aunty Safiya tayi tafara karantawa Fauziyya nakarayimata bayani inda bata ganeba. Sauke ajiyar Zuciya Aunty Safiya tayi tace, to ikon Allah sai kallo, to tunda yace haka ki kirashi kigayamashi inda kike yazo saumuji 'karin bayani daga wurishi" "To shikenan Aunty" haka tafad'a ta amshi wayarta takoma d'aki. Komawa tayi kan gado ta zauna ta tattaro duka nutsuwarta ta lalubo number Salim ta danna Kira, tanata ringing ba'a d'agaba, sai gab da zata tsinke taji and'aga. Shiru tayi tana share hawaye, tanajiran taji me Salim zaifad'a. Cikeda mamakin ganin Kiran Fauziyya Salim yafara magana "my wife kece kodai mafarki nake, Ashe dama Zaki iya tafiya kibarni, haba Fauziyya miyayi zafi haka, kome nayimaki baikamata ki hukuntani ta wannan hanyar ba" Cikin muryar kuka Fauziyya tace "Hubby nice yakamata infad'i haka bakaiba, saboda laifinda ban aikataba kuma banida masaniya akanshi ka sakeni...... Katseta yayi "ki daina furta kalmar saki Fauziyya, wlh tlh bansakekiba, har yanzu har yau har gobe matsayin matata kike saboda nidai nasan ban sakekiba" Sauke ajiyar Zuciya tayi, dan ita abun yagama d'auremata Kai, to idan Salim yace baisaketaba waye yarubuta takardar saki ya ajiyemata, kawai dai yanaso yayimata yawo da hankali ne....Amma ga rubutunshi 6aro-baro "Yanzu kina Ina kigayamin plz" "Hmm Ina Abuja" "Dama can Kika gudu, Aiko gobe Ina zuwa, danma yanzu yamma yayi sosai, amma gobe inshaAllah asubanci zanyo inzo in d'auki matata" Murmushi Fauziyya tayi Wanda saida Salim yajiyo sautinshi, shima murmushi yayimata kafin sucigaba da firar missing d'in juna dasukayi. *Kuyi manage da wannan da bazanyi typing ba sai gobe ganin yanda masoya keta jira yasa nayimaku wannan,* Mmn khady ce πŸ€ΈπŸ»β€β™€ 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Duniya Juyi* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 37 *FAN'S ZANGAYAMAKU DALILIN DAYASA JIYA BAKUJINIBA, WLH BACIN RAINE KAWAI, AKWAI WANI BANZA DAKIKI, WAISHI IBRAHIM USMAN BINDIN KAKE KO UBANWA OHO DAI, YANANAN YANA AMFANI DA BASIRAR MU MU MASUYIN LITTAFI KYAUTA, SHIKUMA YANA KWASHEWA YANA SAIDAWA, WAI YABUD'E GROUP BAZAI SAKAKABA SAIKA TURA KATIN 200, KUMA BAWANI LITTAFI BANE NA DABAN YAKE TURAWA SAI NAMU MU MASUYIN FREE, AKA GAYAMAKA IDAN SON KUD'I NE KAFIMUNE, MU BAMUYI NIYYAR SIYARDA LITTAFIN MUBA, BAIKAMATA ACE KAI KANA SIYAR MANA BA, SABODA TSABAR RASHIN KUNYA HAR KIRANKA NAYI TA WAYA WAI DAN IN TABBATAR DUKDA NAGA POST DINDA KAYI NA TALLAR GROUP DIN KAKE KARA JADDADAMIN SAINA TURA KATIN 200 SANNAN KATURAMIN, NIDA LITTAFINA, TO KABUDE KUNNENKA KA SAURARENI DA BABBAR MURYA, WLH KAYI GAGGAWAR DAINA SIYAR MANA DA LITTAFI IDAN KUMA BA HAKABA WLH ZAMUYI MAGANINKA SHEGE ZAUNE GARI BANZA KAWAI, KAJE KANEMI SANA'A DAN WANNAN HAKKIN WASUNE KAKECI, IDAN KUMA KA'KI JI WLH BAKA'KI GANIBA, YAUSHE ZAMU ZAUNA MUYI WAHALAR TYPING DA WAYARMU DA HANNUNMU DA CAHRGE DINMU DA DATARMU SANNAN ACE KUMA WANI YAFIMU CIN GAJIYAR ABUN, BE YIWUWA KURA DASHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, DUKDA NASAN IRE IRENKA SUNADA YAWA TO WLH KU GUJI HAKKIN MUTANE KU DAINA, NIDAI NAFAD'A DUK WANDA YA SIYARMIN DA LITTAFI ALLAH YA ISA BANYAFEBA, KUMA KUDIN DAYA AMSA YACI WUTA BAL-BAL* πŸ”₯ *Kukuma FAN'S kudaina biyema irin wadannan banzayen, idankuma zaku iya biyan wani 'katon banza kud'i yaturomaku littafin Dana nashiba, Kara muma mu maida na kud'i Kowa yahuta* πŸ€’ Khairat Kuma tunda suka dawo gida ta kwanta Kan gado tanata wannan lankwasa, ita gamai ciki, itako Mama sai nan-nan take da ita. Jitayi tagaji da kwanciyar, wayarta ta d'auko ta dawo falo ta zauna kan kujera tabud'e data tafara chat, Mama na zaune gefe sai jeramata sannu takeyi, Amma saboda tsabar wulakanci batama d'agowa ta kalleta balle Kuma ta amsa. Kusan minti talatin suna zaune ahaka, khairat sai chat takeyi tana murmushi lokaci zuwa lokaci, kafin tad'ago ta kalli Mama cikin muryar shagwaba tace "Yunwa nakeji, Kuma bazan iya shiga kitchen ba" Jiki na rawa Mama tace "Miye kikeso sainashiga na dafa maki, dama ai baikamata ace kinshiga kitchen ba, kamata yayi kizauna kihuta duk wani aiki ki ajiyeshi har Allah ya saukeki lpy" Murmushin gefen baki khairat tayi tace "ok, tokishiga kitchen kidafamin taliya jallouf kisamin daddawa" Mi'kewa mama tayi, tanufi kitchen tana fadin "to taliya kikeso, yanzu zandafa maki, Yar Albarka, Allah dai yayimaki Albarka kin kawomana farinciki agida" Haka mama tashiga kitchen ta ta'kar'kare tafara aiki, minti Sha biyar ta gama dahuwar taliya saiko 'kamshin daddawa ke tashi, zubowa tayi a plate tasako spoon takawo gaban khairat ta ajiye, "to gashi sai ci ko" Dagowa khairat tayi wacce har yanzu taketa chat d'inta hankali kwance, ta kalli taliyar ta yamutsa fuska. sannan tace "Mama pork Zaki kawomin banacin taliya da spoon, kamar wata 'yar 'kauye, jiki na kyarma mama tashiga kitchen ta d'auko pork takawo, amsa khairat tayi tasaka cikin taliyar ta d'auko plate d'in takawoshi saitin kirjinta tad'ebo taliyy tana Shirin kaiwa baki, saikuma tawani 6ata fuska, ta maida, ta ajiye plate d'in tace Mama bazan iya cin wannan taliyar ba daddawa yayi yawa, Kuma yanzu banima son taliyar ma d'anwake nakeso" "D'anwake 'yar nan, badamuwa Bari inyimaki d'anwaken, shiga tayi kitchen ta ta'kar'kare takwaba d'anwake tagama tazubo takwoma khairat, guda d'aya kawai tasaka abaki tafara kakarin amai, Da sauri mama ta iso gareta tana jeramata sannu, tana tambayarta "kodai bazaki iyacin d'anwakenba?" Daga Kai khairat tayi tace banason na fulawa, da kinhad'a alabo da wake kinkai ni'ka danaci, Amma Babu kome kabarshi kawai, kiyimin "wainar filawa nakeso" Jiki na rawa Mama tace "badamuwa ai sai inyimaki, ai kome da dalili akeyinsa, ai bazantaba bari ki wahalaba saboda kinkawomin farinciki arayuwata, nadad'e inason ganin jikana bansamu hakaba saidaga gareki, Allah yayimaki Albarka bari inyimaki wainar fulawar" Komawa kitchen mama tayi tafara aikin wainar fulawar. Khairat naganin shigewarta ta kwashe da dariyar mugunta, ganin yanda Mama keta rawar 'kafa akanta wai ita zata samu jika. Shiko Salim tunda yaji labarin Fauziyya baikarabi takan khairat ba, shirye-shiryen zuwa Abuja kawai yakeyi. Aranar dai haka Mama ta wuni tana bautama khairat, kamar wata 'yar aikinta, sai dare mama tabar gidan dukta gaji jikinta yayi likis saboda uban aikin datayi, dan Koda tagama girke-girkenta Wanda Babu Wanda khairat taci aciki, saida tashare kitchen d'in tagoge sannan tafito tashare tsakar gidan tayi moping. *(Ah ni su mama an bautama d'an Sani)* 🀣 *Jama'a Wai Baku cigiyar Sani* Yau itace ranar da Sani ya yanke zaije gidansu Fauziyya yaga halinda take ciki dan tunda tabar gidan Salim bai'kara ganintaba, Yana Kuma Kiran wayarta lokaci zuwa lokaci amma kullum abu d'aya ake gayamashi shine wayar na kashe. Wanka Sani yad'auka cikin wata fitinanniyar shadda dark blue, yasha hula kalar shaddar, sai takalminshi black, sanifa yafito yayi gwanin kyau ga wani irin turare daya bad'a sai 'kamshi ketashi ajikinshi. Koda ya isa 'kofar gidansu Fauziyya tsasayawa yayi Yana tunanin yanda zai 6ulloma al'amarin, yakai minti goma 'kofar gidan kafin yayi tamaza yashiga da sallama. Mamar Fauziyya na zaune kan tabarma tana Shan iskan yammaci, ta amsa sallamar. Zama yayi kan wata kujera irin ta roba dinnan dake ajiye gefe guda, ya gaida mama cikin ladabi ta amsamashi. Shiru sukayi nad'an wani lokaci sannan Sani yace "amm Mama dama zuwa nayi mu gaisa da Aunty Fauziyya" "Allah sarki, Aiko Fauziyya batanan ai tadad'e rabonta da garinnan" "Ashe batanan to mama Ina tatafi ne?" "Tana Abuja" "Abuja" Sani ya mai-maita kalmar cikeda takaicin rashin tako sa'ar dayayi. "Sai yaushe zata dawo Kuma" Eh to Nima bansaniba, Amma zata dawo nan bada dad'ewaba inshaAllah" "To Allah maidota lpy, Amma nace Kota canja layine Naga idan nakira layinta kullum kashe" "Bata canja layiba shine dai take amfani dashi, ko d'azu muyi waya da ita" "Owk zankirata, wlh mama banji dad'in abunda yafaru tsakaninta da Salim ba, tunda Fauziyya tabaro gidannan Nima naji duk ya fitarmin Rai" "To yaza'ayi da 'kaddarar Allah, haka Allah ya kaddara, idan Allah yasa zamansu Bai 'kareba sai kaga an dai-daita" Gyara zama Sani yayi yace "bani fatan dai-daitawa tsakanin Aunty Fauziyya da Salim, dan wlh Mama Fauziyya zaman ha'kuri kawai takeyi a gidanshi, wannan mutumin ba 'karamin mugu bane Yana muzguna mata kawai dai Allah yasa ita macece mai ha'kuri amma in banda haka da yanzu igoyoyin aurensu duka sun 'kare, gaskiya Fauziyya mace ce wacce samun irinta a wannan zamanin sai an tona" Tunda Sani yafara magana Mama ke saurareshi ta sauke ajiyar Zuciya tace "to Allah dai yazama bafi Alkhairi" "Ameen" Sani yafad'a, shiru yaratsa nawani d'an lokaci sannan yatashi yace" nizan wuce" "To sai anjima" Lokacin gab da magrib Sani yabaro gidansu Fauziyya, gidan khairat yawuce Kai tsaye zuciyarshi cike da takaicin rashin ganin Fauziyya, Zaune ya iske khairat falo tana kallon wani Nigerian film, shima Zama yayi kan kujerar dake fuskantarta, kallo tabishi dashi tace "ah Sani wannan d'aukar wanka haka ina zuwa"? "Ina zuwa kokuma Ina akaje dai" Yabata amsa "To Ina kaje haka?" "Ina zanje kau Wanda yawuce gidansu Fauziyya, sai dai Kuma nayi rashin sa'a ashe Fauziyya tunda tabar gidannan tana Abuja" Wani mugun dad'ine ya mamaye zuciyar khairat, yanzu hankalinta ya kwanta, dama bataso Sani ya auri Fauziyya saboda tana kishinsa, Kuma yanda yake nuna tsantsar soyayyar Fauziyya tabbas idan ya aureta itakuma zai zubata kwandon shara, wani abun farincikin Kuma tayima Salim nisa Kuma da alama baisan inda takeba, kenan ita wannan Abu ita yayima amfani tajefi tsuntsu biyu da dutse daya. Sani yakatsemasu shirun yace "nifa yunwa nakeji kisamomin abunda zanci, "akwai abinci kusn kala hud'u wane kakeso inkawoma, akwai d'anwake, akwai taliya dafuwar daddawa, akwai wainar fulawa" Kallo Sani yabita dashi yace "miye ke damunki haka duk Kika zauna kikayi wannan abun" Dariya khairat tayi tace "banice nayiba wata 'yar aiki nasamu tayita bautamin baji bagani" "Yar aiki Kuma, yaushe aka kawota gidannan bansaniba" Dariya khairat takwashe da ita tace "Mamar Salim ai itace sabuwar 'yar aikin dana samu, Dan yau ta bautamin yanda kasan sarki da bawa, Kuma tayi hakane duk dan cikin dake tare dani" Dariya Sani yayi yace "woooo ke khairat kina wuta Ina binki da fetur, gaskiya ke babbace dole asaramaki, watako kina nufin wannan cikin yazama na Salim" "Sosaima Kuma wlh bakaga yanda yaketa murnaba" Kai Amma naji dad'i kice d'ana zai taso cikin so da kulawa, dan Mamar Salim tana masifar son ganin jikanta, shima Kuma Salim d'in yanason ganin d'ansa" Murmushi khairat tayi tace "yanzu dai fad'i miye zakaci inkawoma" "Tab ai wlh Babu abunda zanci, bayan kince Mamar Salim ta girka, kawai kishiga kitchen kidafamin ko indomie ne, Kinsan ba abincin Kowa nake iya ciba daga na Fauziyya sai naki" Tashi khairat tayi tanufi kitchen dan batason ran Sani yabaci Amma in banda haka Babu abunda zaisa tashiga kitchen, mintuna goma Sha biyar tagama hada imdomie da kwai, takawoma Sani yafara dibarshi, saida ya cinye tass yakora da ruwa, sannan ya kalli khairat yace kawomin wainar fulawar inji idan tayi dad'i" Babu yanda khairat ta iya haka tanufi kitchen takawomashi had'eda yaji cikin vowel, amsa yayi yadauki guda ya dangwala yaji yaci, kallon khairat yayi yace "wow Ashe dai wannan matar danike gani haka ta iya wainar fulawa, kinji kuwa yanda tayi dadi" cigaba yayi dacin wainar yanata dankara yaji kamar tsohon maye, haka yatada wainar tass yakuma bi da ruwa. Fira sukacigaba dayi, sai bayan sallar isha'i Sani yabar gidan dan yasan Salim na gab da dawowa. Fitar Sani badadewa Salim yashigo gidan hannunsa d'auke da Leda, d'akin khairat yashiga, zaune ya isketa har yanzu film din take kallo, sannu yayimata ta amsa ciki-ciki tana wannan langa6ewa, ledar dake hannunshi yami'kamata amsa tayi tana bud'ewa robar ice cream tagani guda biyu, take miyanta ya tsinke, tabud'e roba d'aya tafarasha, ice cream din yayimata dad'i sosai, kallo Salim yabita dashi azuciyarshi yanajin tsanarta, baisan yanda akayiba har yanzu yakasa jin son khairat, dukda cikinshi datake d'auke dashi, tunda akayimashi albishir din tanada ciki yakeso yakoyama kanshi sonta amma zuciyarshi ta'ki kar6ar tayin dayakemata, uwa uba Kuma dayasamu labarin one love d'insa Fauziyya. Kallon khairat yayi yace "gobe idan Allah ya kaimu munada wata semina, kifadamin abunda kike bu'kata dan tun asuba zamubar garinnan, "Ai babu abunda babu, sai dai kud'i zakabada saboda tsaro" Kud'i ya fiddo Mai yawa daga aljihunsa yami'kamata batareda yace komiba yami'ke zai bar d'akin, har yakai bakin 'kofa tace "Kuma kwana nawa zakuyi?" "Eh to zadai mutafi sai yanda yakama, amma nasan bazamu wuce kwana biyu ba, kila Kuma yafi haka" "To Allah ya ya tsare" "Ameen" Yafad'a Yana komawa d'akinsa yashiga shirya kayanshi, washe gari da shirinsa yafita ana gama sallar asuba yawuce tasha, golf ce kan layi, saboda haka ba dad'ewa tacika suka d'auki hanya, *Sai muce Salim Allah kiyaye hanya, dama ance garin masoyi baya nisa Koda yakai bernin sin, yau dai Salim yatafi garin Fauziyya* 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Duniya Juyi* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 40 πŸ’ƒπŸ» *Oyoyo Maman twowins tadawo jama'a kutayani murna, kullum inata cigiya Ina faman Kiran waya bani samu ashe ba lafiya, Allah ubangiji ya'kara lpy, Allah sa zakkar jikine, Allah Kuma yaraya Mana twowins, Allah karo wasu three wins, muzo mukwaso shoki da shaku,shaku, Kai hadama zanku zanyi dan murna*🀣 *Comment d'inki akan littafina Yana matu'kar Sani farinciki, iya wuya muna tare* 🀞🏻 Duk da haka khairat bata ha'kura da Kiran number sani ba, cigaba tayi da Kira. Sani Kuma Yana ganin Kiran ya'ki dagawa dan gani yake kamar idan yad'aga kome zai iya faruwa, jiyakema kamar idan yad'aga muryar Salim zaiji, dan tun jiya wani mugun tsoron salim yakamatashi. Khairat gajiya tayi da Kira ta ajiye wayar tahakura, Sai bayan kusan awa hud'u da Kiran sannan yayi tamaza azuciyarshi yace baridai inkira inji miye yasaka taketa kirana haka, tun farkoma bai kamata in'ki d'agawaba, fad'uwar gaba asarar namiji. Aiko Yana Kira ringing d'aya khairat tad'aga dama jira take. "Hello Sani Ina kashiga inata faman kiranka tun d'azu" "Inafa zanshiga inanan Ina fama da jikina har yanzu bai gama warwarewa ba" "To ingayamaka akwai labari, kazo gidanan yanzu kagani da idonka" "Mezan gani? Kawai kigayamin anan dan nanda kwana bakwai bazanzo gidankiba kidai gayamin kawai" "Kara kazo d'in dai tunda nace kazo, gani yakore ji" "To shikenan ganinan zuwa, amma wlh idan Naga bawani serious abu bane yasa kika kirani wlh sai rayuka sun 6aci" "Eh naji kadaizo d'in kagani" Suna gama wayar Sani ya canja Kaya wurin 'karfe tara da minti goma ya iso gidan, lokacin Salim yariga yatafi wurin aiki. Sallama yayi, khairat ce ta amsa tayi saurin fitowa daga d'aki. Wani kallo tayimashi tareda yimashi nuni da d'akin Fauziyya. Kallon d'akin Sani yayi gabanshi yafad'i cikin murya 'kasa-'kasa yace badai tadawoba" Murmushi khairat tayi tace "dukta dawowa mai sau'kine sai kaganata zakaga babban abun mamaki" Fauziyya daga d'aki tanajiyo lokacinda Sani yashigo, fitowa takeso tayi su gaisa, sai dai tana

Chapter 10 of 13