Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mi'kewa 'kafarta tari'ke takai minti biyar tsaye awurin kafin tasamu tafito. Sunajin alamun tafiya suduka suka maida kallonsu wurin. Ganin Fauziyya da 'katon ciki yasa Sani yin Hocking, dan kasa motsi yayi, duka tunaninshi da kome nashi yayi sumar wucin gadi. Muryar Fauziyya ce tadawo dashi dai-dai "Mal Sani kananan kenan?" "Eh wlh inanan aunty, yafad'a yana 'ka'karo murmushi kamar Wanda akayima dole. "Aunty yaushe kikadawo ne?" "Tunjiya nadawo ai, dayake dare ne" "Kai Amma nayi matukar farinciki, Allah tsare gaba" "Ameen Sani nagode, ya maganar wanke-wanke kuma?" "Kai aunty yaushe rabona da wanke-wanke, idan Kinga nazo gidannan yanzu zuwa nayi kawai mu gaisa" "Ah Sani kacemin kazama babban yaro, kadaina wanke-wanke, to Allah ya taimaka" tana gama fad'in haka tawuce d'akinta tabarsu. Kallon Sani khairat tayi tace "kaje kawai zamuyi magana" Haka Sani yaja 'kafarshi yafita daga gidan Yana layi da tangadi kamar Wanda yashawu, saboda tsabar 6acin rai, Wai yanzu Fauziyya ce da wannan 'katon cikin, to yanzu ta'ina zaya bulloma wannan Al'amarin, haka ya isa gida ya zauna tunani kala-kala cunkushe a kwalwarshi. Washe gari tun 'karfe takwas na safe Fauziyya da Salim suka fito cikin shiri, zai sauketa asibiti tasake bucking domin zuwa awo, daga Nan zaiwuce wurin aiki. D'akin khairat yashiga yabata kudin cefane sannan yagayamata zai sauke Fauziyya asibiti. Nan yake tambayarta "waike yaushe zaki Fara zuwa awo, naga baki ta6ayin maganar Fara zuwa awo ba" Yamutsa fuska tayi tace "nifa banason zuwa awo, nifa asibiti idanba doleba bason zuwanshi nakeba, ko haihuwar idan Allah yakawomani da sau'ki nafiso inyita d'akina bawanda yaji bawanda yagani, sai dai aganni da babyna kawai" "Amma Kinsan zuwa awo Yanada matukar muhimmaci gamai ciki, tananne ake gane idan akwai wata matsala Kuma ashawo kanta tun kafin lokacin haihuwa, ana gane ingancin lafiyar jaririn dake cikine ta hanyar zuwa awo, sannan Kuma ana koyama mata yanda zasu raini yaransu bayan sun haihu da yanda zasu kula da lafiyarsu" "Hmmm zanyi tunani idan naji zan iya zanje, idan kuma bazan iyaba gaskiya bazan wahalar dakaina ba" Fauziyya tana tsaye tsakar gida tana jiran salim ganin yanda yadad'e d'akin khairat Kuma tana jiyo maganarsu sama-sama yasa taji wani irin kishi, jitake kamar taje ta fiddo Salim daga d'akin, ganin fitowarshi yasa tad'an saki fuskarta dan bataso ya fahimci halinda take ciki. "Muje ko" yafad'a yayi gaba tabi bayanshi, Asibitin dai dasuke zuwa nan Salim yakaita, dan suduka Nan sukeda file, kudi yabata yace idan tagama tahau napep takoma gida. Khairat tana ganin fitar Salim da Fauziyya takira Sani tace tanason ganinshi yanzu, Gayamata yayi sundanyi wata 'yar tafiya Amma Nanda awa d'aya darabi zai iso, Zaman jiranshi kawai take tanayi tana kallon agogo lokaci zuwa lokaci, tamatsu yazo suyi magana kafin Fauziyya tadawo gidan. Yana isowa yawuce d'akin khairat din Kai tsaye, falo suka zauna suka Fara tattauna matsalar su. Lokacin Fauziyya itama tadawo gidan dan batawani dad'eba a asibitin tagama abunda take. Tanata sallama taji shuru, sai surutu take jiyowa sama-sama daga d'akin khairat, Jin an ambaci sunanta yasata son jin maganar da akeyi. Matsawa tayi kusa da window d'in d'akin ta la6e. Muryar khairat taji tana cewa "ai yanzu cikinta yayi girma maganin zubarda ciki bazai iya yimashi komeba, hanya d'ayace zamubi mukashe abunda ke cikinta shine muhad'a baki da likitan asibitin datake awo, idan taje awo yayimata Allurar dazatasa tahaihu cikin 'kan-kanin lokacin, kaga tunda lokacin haihuwar beyiba koma miye acikin zaizo ba Rai" "Anya wannan hanyar mai 6illewa ce, bakigani za'a iya samun matsala, idan Kuma likitan ya'ki amincewa fa?" "Hmm Sani kenan, badai kud'i ke magana ba, zanbashi kud'i masu yawa nasan zai amince da bu'kata ta" Dafe 'kirji Fauziyya tayi, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, kawai take mai-maitawa a zuciyarta, Sauri tayi tafita daga gidan, ta dai-daita nutsuwarta sannan tadawo tasake kwad'a sallama da 'karfi kamar dama yanzu tadawo, da sauri khairat tafito tana Yan kame-kame "ah kindawo kenan, wlh Nima inanan narasa d'an aike shine nabugama sani waya yazo ya taimaka yayomin cefane" "Allah sarki" Fauziyya tafad'a tashige d'akinta. Koda tashiga jikinta duk yayi sanyi, tunani take "Wai abunda taji da gaske ne kokuwa mafarki take, Wai yau khairat da Sani *ALMAJIRIN GIDANA* ake 'ko'akarin had'a kai acutar dani akashe abunda ke cikina, ya subhanallah, menayimaku haka me yayi zafi, ya Allah ka kareni ka tsareni daga sharrin masu sharri. Ranar haka tawuni sukuku, Salim nadawoawa take har d'akinsa, kallonta yayi yace "Maman twowins andawo ko?" Harararshi tayi tace "waima twowins nifa d'aya zan haifa, Kai bakasan wahalar haihuwarba shiyasa kakemin fatan twowins" "Aike naga kinsan wahalarta tunda wannan itace ta bakwai" Dariya tayi tace "ai dai zanyi d'in Kuma zanji" Kamota yayi ya zaunarda ita kusadashi yace "zo gayamin ya akayi aaibitin?" "Ba'ayi komeba Babu ma'aikata Inga zankoma general hospital kawai sai inri'ka awona acan" "Kinaga babu wata matsala" "Ba matsala yanda wannan asibitin zasu kula dani suma can haka zasuyimin, kawai dai atayamu addu'a Allah saukemu lafiya, nida amarya bansan waye zaifara Haihuwa ba" "Ke Zaki Fara bakiga cikinkiba yayi ukkun nata girma" Dariya sukayi suduka, Fauziyya tace "Allah girman cinnan na damuna" tayi maganar cikin muryar shagwaba. Kwai-kwayon muryarta Salim yayi yace "Allah girman cikinnan na burgeni nikuma" Rufe fuskarta tayi da hannu tace "banaso Allah" Dariya yasamata. Haka sukacigaba da fira cikin farinciki, harta manta da kudirin khairat da Sani akanta. _______________________ Satin Fauziyya d'aya da dawowa Salim yasa tashirya yakaita gidan Mamarshi, mamakine ya kamata ganinta datayi da ciki, ba kunya kuma tafara Ina takasa Ina taka aza da ita. Harda cewa "mahakurci mawadaci, kaga ikon Allah ashe zansamu jikoki har biyu kusan lokaci guda, keda khairat Allah sa ku sauka lafiya, gaskiya naji dad'in wannan abu" Fauziyya dai murmushi kawai take tana mamakin rashin kunya irinna mamar Salim. Ranar gidan tawuni sai bayan la'asar Salim yazo ya d'auketa har bakin 'kofa mama tayimasu rakiya tace "ki gaidamin khairat d'in idan nasamu lokaci zanzo har gida in'kara dubaku" *Bayan watanni hud'u* Cikin khairat Dana Fauziyya duka yashiga wata tara, khairat cikinta beyi wani girmaba, dan idan ka kalleshi zaka d'auka bai wuce wata shidda zuwa bakwai ba. yayinda cikin Fauziyya yayi wani mugun girma, zama da kyar tashi da kyar, gawani irin kumburi da 'kafafunta sukayi suntum. Khairat da Sani dai sunyi iya 'ko'karinsu na ganin sun zubarda cikin Fauziyya Amma abun ya faskara dan Zakaran da Allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. Kulawa sosai Salim yakebasu suduka, Fauziyya Kuma saboda halinda take ciki wata 'kanwar mamar Salim ce tadawo gidan dazama wacce suke Kira Inna Rabi dan tari'ka kula da ita d'akinma Fauziyyar take kwana, Inna rabi macece mai kirki da sanin darajar d'an Adam, ko kad'an halinsu ba d'ayabane dana mamar Salim. Tana matukar son Fauziyya ganin yanda take girmamata Kuma takemata ladabi. khairat Kuma bataji dad'in zaman Inna Rabi a gidanba dan gani take kamar antakurata anhanata sakewa, Kuma ga Inna Rabin kamar zatayi sa idon tsiya acewar khairat din. Sani Kuma dole tasa yahakura ya'kale khairat dan tanunamashi duk wani jin dad'i dole suha'kura dashi har Allah ya sauketa lafiya. Bahaka Sani yasoba amma ba yanda zeyi dole yahakura ya shafama khairat lalfiya. Amma sai dai yakasa daurewa dan khairat tariga tasaba mashi bazai iya kwana bakwai batareda ya kusancetaba, saboda haka kullum cikin matsananciyar sha'awa yake. Zuby ce tafad'o mashi arai wacce tuni takemashi tallar kanta yanacewa akai kasuwa, Batareda bata lokaciba yaje gidan Zuby yagayamata ya amince da bukatar ta, dama abunda take nema Nan sukacigaba da badalarsu. Mmn khady ce πŸ‘πŸ» Mmn khady ce πŸ’ƒπŸ» [10/3, 7:00 PM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Duniya Juyi* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 42 *Aha masoya jiyafa Naga ruwan comment, gaskiya naji dad'i sosai banida bakin godiya kawai dai iya wuya..... Comment dinku nasani nishad'i mussamman GROUP din ALMAJIRIN GIDANA NOVEL FANS 1 & 2 dakuma GROUP din ZEE MMN KHADY FAN'S jiya khairat taga ruwan 'yan barka, gaskiya kunyima Sani Kara, Bari muga Yana Fauziyya zai kasance* *AKAFTA* πŸ€ΈπŸ»β€β™€ Kafin wani lokaci Inna Rabi da Maman Salim da Maman Fauziyya da Salim duka suna asibitin. Fauziyya Kuma ana lebour kusan awa d'aya tana ciki Amma bataji ciwon komeba shiyasa har yanzu Bata yarda cewa haihuwa zatayiba. A zuciyarta cewa tace "Niko miyasa wannan narse d'in tayimin haka, haka kawai takawoni nan batareda wani daliliba, tasa duk mutane sunzo to yanzu idankuma ban haihubafa ai naji kunya" Haka tayita sa'ka da war-wara, tana cikin wannan tunanin taji cikinta yayi wata irin murd'awa lokaci d'aya, tare da wani irin ciwon 'kugu, dafe kugunta tayi tace "washhh, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Kuma saitaji ciwon ya lafa kusan minti bakwai, saikuma yakuma tasowa haka dai tayitayi kusan awa d'aya, kafin abun ya kankama, yanzu Fauziyya ta tabbatar ma kanta da lallai haihuwa zatayi, dan ciwo takeji sosai, danma Allah yayota macece mai dauriya. Su Inna Rabi da Maman Fauziyya da Maman Salim da Salim duka suna bakin 'kofar labour room sun kasa zaune sunkasa tsaye, addu'oi kawai sukema Fauziyya Allah sauketa lpy. Wata nurse ce tafito tace "Ina masu Fauziyya, da sauri mamar Salim jiki na kyarma tace "gamu nan" tareda Isa wurin narse d'in. "Ku kawo zani Allah ya sauketa lpy, da sauri mama tami'ko sabon fallen zani Wanda suka taho dashi cikin kayan daza'a bu'kata. Amsa nurse d'in tayi tace "saura guda" Kallo sukabi nurse d'in dashi. "Eh saura guda, saboda zani biyu muke bu'kata domin Fauziyya 'yanbiyu ta Haifa mace da namiji" Ai tana rufe baki Inna Rabi ta ri'ke hanci ta rangad'a wata mashahuriyar gud'a wacce tajawo duka hankalin jama'ar dake wurin. Ai mamar Salim kuwa tsabar murna rawa tafara takawa tana kwaso shoki, tana wani turo duwawu tana juyi, duka mutanen wurin babu Wanda bai daraba. Salim dai murmushi kawai yake saki, azahiri amma a zuciyarshi yafi Kowa farinciki, jiyake kamar abarshi yashiga yagano baby's d'inshi da Fauziyyarshi. Kusan minti talatin sannan akagama gyara Fauziyya da baby's d'inta aka maidosu d'akin hutawa, sannan akaba su mama izinin shiga su ganta. Ai ana shiga Mamar Salim tayi d'af da baby's d'in duka biyun ta ri'ke tanata kallonsu fuskarta cikeda farinciki, juyowa tayi wurin Fauziyya tana jeramata sannu, Maman Fauziyya kuwa wurin d'iyarta tanufa tana jeramata sannu tana tambayarta abunda ke damunta, "Babu abunda ke damuna yanzu Mama, nagodema Allah na haihu cikin sau'ki batareda wata matsalaba" "Alhmdlh" Mama ta fad'i. "Inna Rabi dake gafe tace "Allah shine abun godiya" Salim kuwa gefe guda yakoma dan bazai iya komeba indai su mama nanan, sukan had'a Ido shida Fauziyya lokaci zuwa lokaci murmushi yake sakarmata, sannan yayimata Alamar sannu da hannu. Idan tagani sai dai itama tayi murmushi ta sadda kanta 'kasa. Mamar Salim ankama baby's anri'ke batada niyyar badawa, saida Inna Rabi tace "Yaya kibada yaran mugansu muma" Mi'kama Inna Rabi macen tayi tana dariya tace "amshi wannan kishiyace babu abunda zanyi da ita, 'kara inrugumi angona" Dariya sukayi suduka, Inna Rabi tace "Nima ai nafison angon, waye keson kishiya a duniyar nan" Mamar Fauziyya tana jinsu Kuma tana kallonsu bata sakamasu baki sai dai tayi murmushi, Inna Rabi tagama ganin baby sannan tami'kama Mamar Fauziyya, amsa tayi ta kalli 'yan jikokinta wani irin so da 'kaunarsu na shiga zuciyarta, yaran sun d'ebo kamannin mahaifinsu sak, har Kara namijin idanunsa irinna Fauziyya ne, Amma macen kamar Salim yayi kaki babu abunda tabaro nashi. Yaran kyawawa farare tas, gasu da girmansu kamar ba twowins ba. Waya mamar Fauziyya tafiddo takira aunty Safiya, bayan sun gaisa mama ta tambayi lafiyar su Walid duka akacemata suna lafiya sannan tace "ganinan asibiti ri'ke da babyn Fauziyya" Cikin tsananin d'oki da farinciki tace "Mama yaushe Fauziyya ta haihu?" "Yau yanzuma ba dad'ewa gamunan ma asibiti ri'ke da twowins" "Twowins Mama" aunty Safiya tafad'i cikin tsananin murna da farinciki, sannan tacigaba da cewa "haba Babu mamaki wannan girman ciki na Fauziyya, Allah ya raya baby's sainazo" Mamar Fauziyya ce taga rashin dacewar abunda akayi ace har yanzu Salim bai d'auki baby's d'inba Kuma Yana wurin" Zuwa tayi har inda yake tami'kamashi duka yaran, sannan tayimasu sallama tawuce gida, tunda dai Fauziyya ta haihu lafiya ai 'kara tawuce hakanan. Salim kuwa yanajin yaran rungume jikinshi yaji farincinsa ya 'karu fiyeda Wanda yake ciki, 'kurama yaran Ido yayi wani irin sonsu da 'kaunarsu nashiga zuciyarshi. Addu'a yayimasu tare dayimasu hud'uba. Wurin 'karfe biyu da rabi na rana likita ya sallamesu suka wuce gida cike da farinciki tareda baby d'insu. Duk abunnan khairat tana gida itada Khalid d'inta batasan wainar da ake toyawa ba. Tadai San Fauziyya tatafi awo amma batasan ta haihuba. Sallamar Mamar Salim tajiyo da Inna Rabi, amsa sallamar tayi tafito waje Khalid na goye a bayanta. Ganin Fauziyya tayi babu ciki ga Mama d'auke da baby Inna Rabi ma d'auke da wani baby d'in. Kallo kawai tabisu dashi zuciyarta d'auke da tambayoyi barkatai Wanda sai ahankali zatasamu amsar su. Inna Rabi suna shiga d'aki ta mi'kama Fauziyya babyn dake hannunta tafito domin d'ora ruwan zafi. Har yanzu khairat na tsaye inda suka barta, kallonta Inna Rabi tayi tace "kije mana ki gano 'yan'biyu Khalid angirma ansamu 'kanne" Murmushi khairat tayi tace "aini abunne ya d'auremin Kai naga daga zuwa awo andawo da baby's" "Abun Allah kenan yawuce ya d'aure Kai, kedai shiga kigano Yan tagwaye" Inna Rabi tafad'a ta'kara gaba wurin dafa ruwan zafinta tabar khairat tsaye tama rasa miye zatayi. D'akin Fauziyya tashiga da sallama ta zauna mama tamikamata Baby's amsa tayi ta zubamasu ido, yaran sun matukar Bata sha'awa, a zuciyarta Kuma jitake inama ace itace Fauziyya, wannan sune 'ya'yan Salim Kuma jininsa ba Khalid ba. Wasu hawaye ne suka taru suka cikamata Ido, suna niyyar gaganrowa tayi saurin sa hannu tagoge batareda Kowa yalura ba. Tad'an dad'e d'auke da baby's d'in kafin ta kwantar dasu tawuce d'akinta. Dama Allah Allah take tadawo d'akin takira Sani tayimashi albishir, koba kome tayi farinciki da haihuwar Fauziyya tasan Sani zai ha'kura da 'kudirin daya d'aukarma kanshi na aurenta, tunda yataba gayamata indai Fauziyya ta haihu to yaha'kura da aurenta. Kiran wayarshi tayi tanata ringing bai d'agaba lokacin Yana gidan Zuby, suna she'ke ayarsu. Saida takira yakai sau ukku acikon na hud'unnne zuby dake kwance jikinshi tasa hannu ta d'auko dan 'karar wayar Yana damunta tace "kad'aga Mana khairat ce fa, d'agawa tayi takaramashi a kunne. "Hello ya akayi?" yafad'a cikin wata irin murya. Shiru yayi da alama tana Kora mashi bayani ne. "What"...... Yafad'a da 'karfi tareda tashi zaune yature zuby dake kwance jikinshi yari'ke wayar gam a kunnenshi. 'kuramashi Ido zuby tayi tamatsu yagama wayar taji mike faruwa. Saida yagama ya ajiye wayar gefe sannan zuby tarungomshi jikinta "miya faru haka baby na, naga dagayin waya kashiga wani yanayi" "Fauziyya ce ta haihu" yafad'a batareda ya kalli zuby dinba. "Wayyo dad'i, wani farincikine ya mamaye zuciyar zuby, idan Bata mantaba tatabayima sanin tayin aurenta yace shifa Fauziyya ce kad'ai macenda zai aura, amma yayimata Al'kawarin idan har Fauziyya ta haihu da Salim yaha'kura da aurenta Kuma zai aureta. ______________________________ Tundaga ranar da Fauziyya ta haihu har zuwa yau damuke kwana biyar da Haihuwar mutane keta tururuwar zuwa ganin baby's, kullum gidan cike yake kamar ranar suna. Salim kuwa yataka muhimmiyar rawa wurin yin kome awadace, kullum za'aci asha kome lpy lao. _______________________________ Sani dai ya amince da maganar aurenshi da zuby, batareda sanin khairat ba, Dan khairat batama San Yana tare da zuby ba. Sati d'aya aka tsaida za'ayi aure inda zuby tabashi ma'kudan kud'i yayi hidimar aurenta. Dan duk wata dukiyar zuby kusan yanzu tana hannun Sani tami'kamashi yanata watayawa abunshi. *Bayan kwana biyu* Yau itace ranar sunan 'yan biyun Salim. Kuma yau Salim yasamu 'karin girma a wurin aikinshi, Farinciki biyu. Fauziyya anfito Mai jego, tasha make up, wani tsadadden less tasaka, maroon Mai kwalliyar green da golden, tayi wani fitinannen kyau. Aunty tun jiya sukazo harda baban Walid, trolley biyu tayoma Fauziyya d'aya kayan twowins daya kayan Fauziyya. Baban Walid Kuma mijin Aunty Safiya Salim ya baiwa kyautar have million 500k Gaskiya haihuwar tazomasu da Alkhairi sosai. Maman Salim dataji labarin irin abun Alkhairi da aka samu murna tayi sosai tace "wannan yara haihuwar ku Alkhairi ce" Ansha taron suna gidafa yacika ma'kil babu masaka tsinke can na hango tawagar Yan group din ALMAJIRIN GIDANA NOVEL FANS anata cin rangem, bayan angama Kuma aka shiga fagen rawa inda Mrs DJ ke bada tashi gudaummuwar. Kai nikaina ba'a barni abayaba sunan Fauziyya dole nakwaso shoki πŸƒπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€ Khairat Kuma tunda ta haihu Babu abunda yashiga tsakaninta da Sani dukda taso hakan amma yabata ha'kuri akan tabari tagama wanka Kuma tagyra kanta sosai. 6angaren Salim kau Yana ba khairat kulawa itada Khalid ammafa babu maganar kashe arna. Mmn khady ce πŸ’ƒπŸ» [10/3, 7:00 PM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Duniya Juyi* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 41 Bayan wani lokaci, misalin karfe 6 na yamma khairat tana zaune tana yanke farce, taji cikinta yad'an murd'a ahankali, gabantane yayi mummunan fad'uwa dan kusan kullum tunda cikinta yashiga wata na tara sai cikinta yad'an murd'a, gabanta Kuma saiya fad'i saboda ko kad'an bataso tariga Fauziyya haihuwa, Yau abun ba iri d'aya bane Dana sauran ranakun, dan ciwon cikin 'karuwa yake da kad'an-kad'an. Haka tayita daurewa tana cijewa, Koda Salim yadawo gidan wurin 'karfe tara na dare bata yarda yagane halinda take cikiba, Wasa-wasa haka khairat tayita fama da ciwo har 'karfe d'ayan dare tun tanajin ciwon na d'agawa tahuta har bacci-bacci ke d'ibarta kafin yasake motsawa Kuma ta farka, yanzu yadaina dad'ewa daya motsa ko minti biyu ba'ayi yake sake tasowa, magowa tafarayi tsakar d'aki tana burgima, abun ba sau'ki. Takasa zaune takasa tsaye tsakanin falo da bedroom. Tsakanin 'karfe shidda na yamma zuwa 'karfe shidda nasafe khairat tagama jigatuwa tafita hayyyacinta, dan za'a iya cewa batasan inda kanta yakeba. Bayan Salim yadawo daga masallacine yashiga d'akinta yatadata tayi sallah dan yasan ba abun mamaki bane bata tashiba har yanzu. Halinda ya isketa ciki ba 'karamin d'agamashi hankali yayiba, dan falo yayi Karo da ita a yashe ko d'aga kanta Bata iyawa, ga Jini sai faman bin 'kafafunta yake. "Subhanallah, khairat ya akayi haka? Dama bakida lafiya baki gayamaniba" Ido kawai take binshi dashi dankuwa babu baki. Da sauri Salim yanufi d'akin Fauziyya yasanardasu halinda khairat d'in take ciki, Inna Rabi ce tayi saurin zuwa d'akin ta matu'kar tausayama halinda taga khairat d'in. Kamata tayi takaita toilet tagyaramata jikinta tare da canja mata Kaya, dai-dai lokacin Salim yazo da mota Fauziyya da Inna Rabi suka Kama khairat d'in suka kaita mota tareda Inna Rabi suka tafi asibitin. Fauziyya Kuma komawa tayi tagyra d'akin khairat d'in duk inda tabata da Jini ta goge, takunna tsintsiyar'kamshi tajawo d'akin sannan takoma nata d'akin, cike da tsananin tausayin khairat, "dama haka ake shan azaba wurin Haihuwa, ya Allah kakawomin tawa da sauki, itama Allah ya sau'ka'ka mata yasa ta haihu lafiya. Zama Fauziyya tayi tanata tunani jikinta duk yayi sanyi, Sani ne yashigo gidan, d'akin Fauziyya yanufa ganin d'akin khairat arufe, fitowa Fauziyya tayi tace "Sani Kaine" "Eh wlh aunty, ina khairat ne" "Khairat tana asibiti batada lpy, anama sa ran haihuwace" "Haihuwa?" Sani yafad'i cikeda mamaki da tsoro da fargaba. "Eh haka nake tunani" "To Allah dai ya sauketa lpy" Sani yafad'i "Ameen Sani, ammafa khairat tanajin jiki sosai wlh" Haka suka d'anyi fira sama-sama, kafin Sanin yabar gidan. Yana fita Kai tsaye asibitin yanufa, Salim da Inna Rabi ya iske bakin labour room, sai raba idanu suke suna jiran tsammani, zuwansu asibitin kusan mace bakwai ta haihu, Amma khairat har yanzu ba labari. Wasa-wasa 'har 'karfe shidda na yamma khairat bata haihuba, duk wata dabara daya kamata likitoci suyi sunyi amma abun ya faskara, saboda haka khairat sai an dangano da theater room. Likitan dakanshi yakira Salim yasanar dashi "a gaskiya matarka tana tsakanin rayuwa da mutuwa, cikin biyu dole ayi d'aya, kodai ayi gaggawar yimata CS aceto rayuwarta data abunda ke cikinta, kokuma ana gaf da rasa ranta itada d'anda ke cikinta, saboda ta galabaita yanzu batada 'karfinda zata iya Haihuwa da kanta, hakama d'anda ke cikinta yagama Shan wahala zai iya rasa ranshi idan aka 'kara Kai wani lokaci" Cikin tsananin rud'ewa Salim yace "Doctor ayi duk abunda yakamata" Nantake akaba Salim takarda yasa hannu, cikin 'kan'kanin lokaci akagama shirya kome aka fito da khairat cikin green d'in Kaya Kan gadon da ake tura marar lafiya, tagaban Sani aka wuce operation room da ita, binsu kawai yayi da kallo, yau ce rana ta farko da yaji tausayin khairat ya d'arsu a zuciyarshi. Fauziyya tana gida hankalinta har yanzu ya'ki kwantawa wayar Salim takira Nan yake sanar da ita C's za'ayima khairat. Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, shine abunda ta rin'ka mai-maitawa, fatanta Allah ya sauki khairat lpy itakuma Allah yakawomata tata da sauki. Misalin karfe sha d'ayan dare aka fito da khairat daga theater, Alhmdlh anyi nasarar fiddo santalelen jariri mai Kama da khairat, kyakkyawa dashi zubin larabawa. Godiya Salim yayima Allah, Nan take yakira Fauziyya yagayamata, tanuna farincinta sosai, sannan yakira mamarshi yagayamata haihuwar, har rawa tataka dan murna, yau tasamu jika, danma dare yayi sosai aida tataho asibitin yanzu, addu'ar samun lafiya tayima khairat itada abunda ta Haifa. Hajiya Habi maman khairat Mama takira tagayamata haihuwar d'iyarta, Wai kada kaso kaga murna wurinta, ai da wannan daren kasa daurewa tayi saida ta dangano da asibitin taga lafiyar 'yarta da jikanta. Washe gari tunda safe Fauziyya tashirya zuwa asibitin, Salim yakaita bayan tahad'a masu kayan breakfast. Kwance ta iske khairat Kan gado, ga baby kusa da ita abin gwanin birgewa, hannu tasa ta d'auki babyn ta'kuramashi Ido, azuciyarta jitake inama ace itace ri'ke da babynta haka, Sannu tayima khairat, tayimata yajiki, Amsawa tayi murya 'kasa-'kasa dan har yanzu tanajin jiki. Sani ne yashigo d'akin, suduka binshi sukayi da Ido, gaidshesu yayi, Inna Rabi ta amsa, sannan yayimasu yamai jiki, kafin ya jawo kujera ya zauna, Fauziyya tami'kamashi baby, jiki ba kyarma ya 'karba, zubama jaririn ido yayi Yana sa'ka da war-wara a zuciyarshi, Shima babyn bud'e idanunshi yayi kyar yazubasu Kan Sani. Khairat Kuma tunda Sani yazo asibitin ya kar6i babyn gabanta ke wani irin mugun fad'uwa, gani take Kamar zaiwuce dashi yace yatafi da d'anshi. Salim kuwa yasha hidima tundaga ranar da aka kawo Fauziyya asibitin har zuwa yanzu. Mamar Salim tazo asibitin taga jaririn, sai nan nan take dashi, har tawai tarikayimashi dayana kuka tana wa'ka. Kai d'an jikalle, jikalle na, waya ta6amin Kai yanzu in d'au 'kota 🀣 (Kunjifa su Mama masu jika) Kwanan khairat ukku asibiti, jikinta ya war-ware aka sallameta, Kullum gidan Salim cike yake dayan ganin baby, 'kawayen khairat da 'kawayen Hajiya Habi, da mutanen maman Salim sai zuwa ake barka. Sati na zagayowa akasha shagalin suna, jariri yaci Suna Khalid, shagalin sunafa anyishi ba Kama hannun yaro, dan Salim yasaki bakin Aljihu, mai jego anyi gwanin kyau kamar ba'itabace ta haihu. *Bayan sati biyu* Khairat na kwance falo Kan kafet d'in tsakiyar d'akin, Khalid na kwance gabanta yanata yan motse-motsenshi na jarirai, yayi 'kiba gwanin sha'awa ya'kara fari ga sumar kanshi kwance lub, irinta larabawa da fulani. Sallamar Sani tajiyo, gabanta ya fad'i tayi saurin tashi zaune tad'auki Khalid ta rungumeshi jikinta. Tana jiyo sanda Sani ya gaida Inna Rabi, Yana Kuma tambayarta ya Khalid, tace "lpy lao suna ciki shida mamarshi" D'akin Sani yashiga Kai tsaye ya iske khairat ri'ke da Khalid, hannu kawai yami'kamata Alamar takawoshi, ba musu tami'kamashi jikinta na kyarma. Kallon Khalid Sani keyi yanajin wani irin soda 'kaunarshi nashiga zuciyarshi. Khairat kuma 'kuramashi Ido tayi, ko kad'an bataso Sani Yana yawan zuwa ganin Khalid, ganitake kamar zai rabata dashi, gashi itama tad'auki son dunyi tad'orama Khalid d'in, jitake kamar idan Sani ya d'aukeshi zai tafi dashi ne. 6angaren Fauziyya har yanzu Babu wani labari har gashi Khalid yakai wata d'aya a duniya, yayi wata irin 'kiba idan ka kalleshi dole ya burgeka kyakkyawa dashi. ________________________________ Yauce ranar zuwa awon Fauziyya saboda haka tun 'karfe takwas na safe tabar gidan zuwa asibiti. A asibiti kuwa anatayima mata awo har layi yazo Kan Fauziyya, tana hawan gado narse d'in tafara aunata, saita tsaya tace "miye sunanki ma?" "Sunana Fauziyya" "Am malama Fauziyya bakijin wani ciwo haka ajikinki?" "Banajin kome" Fauziyya tafad'a tana kallon narse d'in. "To Amma Kuma gashi kinfara Labour," "Labour kuma, Kai gaskiya badai labour ba, nifa ko ciwon Kai banaji" Murmushi narse d'in tayi tace "kije labour room kawai", Murmushi Fauziyya tayi, itafa abun mamaki yake Bata wai taje labour room, bayan tasan ita batajin ciwon kome, Kuma tasan labour fa ba wasa bane barantana taga yanda khairat ta wahala. Haka dai nurse tamatsa mata sukaje labour room sannan tace yakamata takira wani daga gida dan bazai yiyu ace tahaihu babu Kowa wurintaba. Haka Fauziyya takira Salim tagayamashi, duk da dai tana kokonton azuciyarta, Inna Rabi Salim ya d'auka suka nufi asibitin, kafin yazo Kuma takira mamarta itama ba dad'ewa tazo asibitin, mamar Salim ma da sauri tazo asibitin Dan Salim d'in takira yake gayamata Yana asibiti Fauziyya ce zata haihu. *Munayimaku tallar shahararren man gashi Mai suna ASHKHAD AFRICAN HAIR GROW, man gashine Wanda akahad'a da sinadaran gyaran gashi yanasa tsawon gashi

Chapter 11 of 13