Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Real ßukar Mustapha Damaturu (DAƘIƘA SITTIN!) Ita dai dama ba kasafai a ke samun ta ba, idan kuwa ka sa me ta to yi ƙoƙari kayi amfani da ita tun kafin ta kuɓuce maka! Ni dai tawa damar ba ta zo mini da wani abu na a zo a gani ba! Domin ba bu abinda ta haifar mini face tarin da-nasa-ni da nadama, wanda a kullum take ɗa ɗa ƙaruwa a cikin zuciyata. A rayuwa mutane iri biyu muke da su masu nasara, da marasa nasara, sannan ƙaddararmu ita ce kaɗai tagirmi gobenmu, da ace mutum yasan ƙaddararsa ta gobe da tini ya yi gaggawar magance ta tun a yau, kafin zuwa gobe lokaci ya cimma sa. Kamar yadda rashin sanin ita ta je fa ni na kasance a cikin mutane marasa nasarar. Lallai mafi girman kuskure a rayuwar duniya shi ne mutum ya nemi canza wa kansa ƙaddararsa ta hanyar amfani da ƙarfi-da-yaji! Ji nake tamkar duniyata ta banbanta da ta sauran bil'adama, domin wata iriyar duniya ce mai cike da ababen ban mamaki da na al'ajabi, kai harma da na ban tsoro. A taƙaice dai duniyata tana kama ne da irin duniyoyin nan na cikin mafarkai ko tatsuniyoyi. Kada kuyi mamakin jin cewar hatta fatalwai su na zuwa duniyata su azabtar da ni tare da bani tsoro, sannan ba bu bacci ko gyangyaɗi a duniyata, saboda kullum idanuna biyu ragas tamkar fara! Nutsuwa da kwanciyar hankali sun guje ni, masifa da bala'i sun zamo mini abokan fira, tashin hankali kuwa ya zamo tunanina na ko yaushe. A shekaru huɗun da suka gabata ne, watarana abokina Bala Shamuwa ya ɗauke ni izuwa cakwalkwalin Mallam Ɗanjatau, wanda jama'a suke yi masa kallon malami, amma kuwa a gaskiyar zance ƙasurgumin boka ne! Gidansa yana can bayan garinmu. Cikin wani wagegen ɗaki ya sanya ni, na zauna a gaban wani farin ƙyalle wanda ya rufe jikin ilahirin bangon ɗakin, sannan ya zauna a bayana. Sanye yake da wasu jajayen kaya ja zir, tamkar mai shan jini! Cikin muryarsa mai hargagi da hamami wanda yake kama da muryar dodonni, ya ce da ni, "Yaro za ka yi arziƙi, za ka yi kuɗi kamar yadda ke so, kuma za ka zarce duk wani mai arziƙin dake cikin garin nan, amma fa akwai ƙalubale mai girman gaske a gabanka, kuma ya kamata ka sani ba'a shiga daƙin nan a fita lafiya, ina nufin sai wani ya mutu! Ko ka kashe, ko kai da kanka ka mutu!" Na tsorata ainun da jin batunsa, ko in kashe ko ni kaina in mutu? Haka nayita tambayar kaina sau ba bu adadi, daga ƙarshe dai na yanke shawarar to fa da ni in mutu gara kowama ya mutu, saboda akwai burika masu tarin yawa a ƙunshe dake gabana da nake son in cimma. Abin da idanuna suka kallah ya bayyana a jikin bangon ɗakin ya yi matuƙar girgiza ni, kuma ya bani tsoro! Hoton mahaifiyata ce ta bayyana a jikin farin ƙyallen dake liƙe a jikin bangon ɗakin, sannan ya miƙo mini wani dogon takobi, ya ce da ni, "Nasan duk duniya ba bu wanda ka ke so sama da wannan tsohuwar, shi arziƙi kuwa ba a yinsa da gaggawa har sai an sadaukar da wani abu mai muhimmanci, karɓi wannan takobin ka soke ta zata mutu, amma kai kuwa daga yau kakarka ta yenke saƙa! Sannan kada ka manta da abinda na faɗa maka, ko ka sadaukar da ita, ko mu fansheka a madadinta, Daƙiƙa Sittin kacal ka ke da ita, idan ka haura dakika sittin ba ka zartar da komi ba to tabbas zaka mutu yanzun nan, kuma a nan wurin". Ban taɓa sanin daƙiƙa sittin bata da yawa ba sai a wan can ranar, kafin in ankara har sun kusan cika, nayi yunƙurin juyo wa in tambayshi, ya ce da ni, "A a kada ka juyo baka da damar tambayar komi, idan kuwa ba ka yarda ba ka juyo to zaka mutu!" A nan ma na ƙara tsorata, hawaye ne suka fara gangaro wa daga cikin idanuna. Na rufe idanuna zan soketa da takobin, ya sake ce da ni kada in rufe idanuna a bude zan soketa, abin ya ɗaure mini, kai wai shi da yake bayana amma kuma yasan dukkan motsina, lallai boka shege ne. Dolena idanuna a bude na soki mahaifiyata da takobin dake hannuna, lokaci guda hoton mahaifiya ya zama ja alamar jini ta bace! Na fashe da kuka. "Tashi ka tafi tsinanne! za ka yi arziƙi nan da kwanaki arba'in". Inji boka Ɗanjatau... Jibrin Adamu Jibrin Rano Author Admin DAƘIƘA SITTIN 02 ©Jibrin AJR "Tashi ka tafi tsinanne! Zaka yi arziƙi nan da kwanaki arba'in." Na tsinkayi kakkausan lafazin boka Ɗan-jatau. Kamar wanda ya yi mankas da barasa, kamar kuma wanda aka yi majaujawa da shi haka na tashi a rafkane ina tangaɗi zan fita. "Dakata!" Ya sake kwatsa min tsawar dana jita kamar saukar aradu. "Da gaba ka shigo, da baya zaka fita idan kana son idanuwanka." Ban saniba ne ko don ya yi magana ne, ko kuma da gaske ne oho dai? amma tabbas dishi-dishi nake gani, gaba ɗaya duniyar tambal-tambal take yi dani kamar ƙwarya a kan teku. Kamar sabon ɗan shayi haka nake tafiya a tattale cikin sanɗa har na samu na isa bakin ƙofar inda ƙafafuna suka ci karo da wani abu ta bayana. "Tsuguna ka ɗauka!" Ya ja hankalina har a lokacin muryar shi a kausashe. "Ka riƙe shi da kyau yanzu shi ne zuciyar duniyarka, shi zai ɓulɓulo da arziƙinka kamar yadda zai iya zama ajalinka!" Na sake shafa ɗan guntun tulun da kyau ina mamakin yadda za a ce yanzu tulu shi ne rayuwata. "Zai zamo arziƙinka ne idan ka kiyaye sharruɗan da zan gindaya maka, hakanan ƙin kiyaye waɗannan sharuɗan shi zai tarwatsa rayuwarka da ta ragowar ahalinka fiye da yadda nakiya zata tarwatsa dutse." Ni dai cikin ƙosawa da zantukansa da zaman ɗakin na miƙa hannuna baya na ɗauki ɗan guntun tulun da na ƙarewa kallo bayan na zagayo da shi gabana, wanda saman shi yake rufe da wani ɗaurarren jan ƙyalle. "A cikin kwanaki arba'in ɗin nan dole ne kullum wannan tulun ya kasance a kan wuta, sannan kada ka kuskura ka yi gigin buɗe wannan jan ƙyallen da aka rufe bakin shi da shi duk rintsi da tsanani har sai an cika kwanaki arba'in ɗin da zai zama mabuɗin arziƙinka." Yana zuwa nan a zancensa ya rafka wata sowa, lokaci guda kuma ya fara ɓaɓɓaka dariya. "Idan ka kiyaye buƙatarka zata biya ɗan samari! Idan ka kiyaye buƙatarka zata biya halakakke!" Amsa kuwwar zancensa ya yita gare a zauren kunnuwana har bayan na fita a cikin bukkar. "Ka samu maɓoya mai kyau ɗan samari! Ka samu maɓoya mai kyau halakakke!" Na sake jiwo sowar shi a cikin bukkar ta shi kamar yasan tunani nake yi na gurin da zan ajiye wannan tulu ba tare da wani ya gani ko ya taɓa ba. A waje na tarar da Bala Ɗan-shamuwa ya taso da sauri daga ƙasan inuwar itaciyar da yake yana kallona da ɗan tuluna kamar wanda ya warke makanta. "Yaya kuka yi da shi? Mene ne a ciki?" Ya tambaye ni yana kallon tulun da ke hannuna. Ban samu sararin ba shi amsa ba na miƙa masa tulun, a zuciyata ina alla-alla na isa gida da wuri na duba 'shin da gaske ne na kashe Ummanmu ko tsokanata bokan yake yi?' "Wai mene ne a ciki?" Bala Ɗan-shamuwa ya sake tambayata. Ganin ya matsa lamba gudun kar ya buɗe jan ƙyallen na ba shi amsa. "Ban san mene ne a ciki ba ya ce kar a buɗa. Mu je cisƙalinka ka ajiye mana ita. ina so na je gida ne naga wani abu!" "Eh tunda ka ji ya ce hakan to kar a buɗa idan ba haka ba asirin yana iya karyewa." Na ji ya tari numfashina. Ni dai ban sake magana ba a hanzarce na ƙarasa inda muka ajiye argan keken abokina Musa da na aro. Na hau na zauna shima Ɗan-shamuwa ya hau bayan na fara taka keken da duk ƙarfina. "Wai saurin me kake yi ne haka? Ka tafi da mu a hankali fa kar mu fasa tulun nan, kasan keken babu burki." Na ji Ɗan-shamuwa yana yi min ƙorafin gudun da bansan ina yi ba. A iya yadda nake jin keken ji nake yi kamar a guri ɗaya nake ƙwaƙura shi, ga hanyar tamu itama da naga kamar an ƙara mata tsaho. A ɗan bayan gari inda cisƙalin Ɗan-shamuwa ɗan malam ya ƙi halin malam yake na ajiye shi na ce ya adana min tulun zan dawo. Kafin ya amsa tuni na yi gaba bayan ya sauka. "Wayyo Allah na shiga uku Umma ta mutu ta barmu." Na jiyo furucin ƙanwata tun daga waje, ta dangan karan da ana iya hango dishi-dishin mutane na hango cincirindonsu. 'Tabbas mafarki nake yi ba gaskiya ba.' Na faɗawa zuciyata bisa tabbas da nake dashi bazan iya kashe Ummata ba. Na tino daƙiƙa sittin ɗin da aka yimin rintonsu, da abin da ya biyo baya a cikinta... DAƘIƘA SITTIN 03 ANaM Dorayi Na tino daƙiƙa sittin ɗin da aka yimin rintonsu, da abin da ya biyo baya a cikinta.... Da ƙyar na iya jan ƙafafuna na ƙarasa gidan, ƙanwata ta rugo da gudu, ta kama hannuwana tana faɗin, "Yaya Umma ta mutu, zo mu je ka gan ta, ta mutu tana anbaton sunanka, wayyo yayanmu." Dam! Na ji kamar an buga min guduma a ka, jin yanayin da Umma ta mutu, kukana yai cak, ji nake kamar in fita da gudu in shaƙe Dan-jatau, amma inna! Na zama raƙumi da akala. Bata tsaya da ni ba sai gaban gawar, inna durƙusawa na ji wata tsawa! "Kar ka kuskura ka taɓa gawar nan matsiyaci, maza tashi ka je ka ka ɗora tulunka bisa wuta, idan kuma ba haka ba... Hahahaha! Ya tintsire da dariya sannan fusakarsa ta ɓace." Firgigit! Na dawo hayyacina, sannan na fara waigen jama'ar da ke zaune dan ganin ko suma sun ji tsawar da aka daka min. Ban ga alamar sun ji ba, na miƙe tsam na yi waje. Inna fita na iske wata jama'ar daƙar jugun-jugun, na hango Shamuwa cikin abokaina. Na samu guri na zauna, dan tabbas bani da ƙwarin gwaiwar tafiya ga umarnin boka. Muna nan har aka yi wa Umma wanka, aka kawo mana ruwan alwala, muka sallace ta aka tafi kai ta makwanci. Riƙe da hannuwana abokaina suke har makabartar, sabida wasu zantuka da suka ji inna furtawa, ba me iya gane me nake cewa, sannan inna ta ƙoƙarin rugawa da gudu, haka ya sa su zaton ko duk zafin mutuwar ce. Ni kuwa duniyar ce tini ta fara canja min, dan kuwa cikin makarar Ummana gani nake wuta na ci da battar nan a kai, wasu halittu da na kasa tantance su, sun kewaye ta suna ta dalalar da yawu suna ƙoƙarin buɗe ta, a duk lokacin da ɗaya ya kai hannu sai wutar ta yi sfuuuuu! Ta wuce jan ƙyallen za ta kamo hannunsa, sai ya janye hannun... A tsaitsaye na iya kaiwa har lokacin da aka binne ta, dan kuwa fuskar Dan-jatau ce ta kuma bayyana a gabana tana faɗin, "Ka yi gaggawar hura wuta kafin ka yi bankwana da arziki ka koma ceton ranka, Hahahaha!" A taƙaice, cikin firgici da ɗimuwar da ban taɓa shigar ta ba aka janye ni daga maƙabatar, bayan mutane sun yi ta cincirindon gaisawa da ni. Wannan daren shi ne mafi munin dare a rayuwata. A wannan karon ganin battar nan na yi kan murhun wutar ta kusa mutuwa, sun fara iya taɓa jan ƙyallen da ke daure da battar, da zarar sun taɓa sai in ji jiki na ya ɗau zafi kamar an ɗora min dutsen guga, sai kuma wutar ta yi irin harshen da take yi lokacin suna kan makarar Ummana, sai in firgigit in tashi. Cikin wannan azabar na kasance har gari ya waye, kuma wannan shi ya zama mafarin azabar da nake sha, waccan a kullum sai ta sauya salo ta kuma fi ta jiya. Na ɗauki alwashin, lallai sai na ga bayan Ɗan-jatau tinda ya yi min sanadiyyar mahaifiya, saidai abun da ban sani ba haka shi ne mafi girman gangancin tinanin da na taɓa yi a rayuwata. Cikin kwanaki uku da aka yi ana zaman makoki kullum sai Shamuwa ya zo yana tanbaya ta, "wai mene ka bani ajiya, yake ɗumama min makwanci?" Ba na iya ce masa komai. Ranar da aka yi sadakar uku Shamuwa ya ja ni, wai lallai sai na karɓi ajiya ta, shi ba zai iya dakon halaka ba. Mu ka isa Cisƙalin nasa, ya shiga ya kai hannu zai ɗauki battar nan ya ji ta yi zafi kamar an tafasa ta, ya fito da gudu yana karkaɗe hannu yana juyi, da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa, sannan ya fara bayani. "Me-dubu-dubu ni fa na kasa fahimtarka, na sani wannan sakwarkwacewar taka ba alhinin mutuwar Umma ba ne, dan ya samo asali ne daga gidan Mallam Dan-jatau..." Jin ya anbaci bokan da Mallam ya sanya ni watsa masa wata muguwar harara. "Wanene Mallam ɗin? Shamuwa ka cutar da rayuwata, duk son kuɗina ba zan taɓa iya halaka wani a kan na yi kuɗi ba..." Bai bari na dire zancen ba ya kwaɗa min kirarin da a da nake jin daɗin in ji an yi min. "Alaji me dubu-dubu, Allah ya sa ba rako muka zo ba..." Wanda idan da lokacin inna maitar zama me-kuɗi ne da karasa masa zan yi, In ce, 'In ko rako muka zo gwara mu koma...' DAKIƘA SITTIN 04 ©Real_Bukar_Damaturu Da na lura naga cewar al'amarin na neman zautar da ni tuni nayi sallama da abokina Shamuwa Ɗan-malam na runtuma hanyar gidan boka Ɗan-jatau, ina zuwa na iske shi kwance ya kishingiɗe iya taɓa baccin safe a cakwalkwalinsa. Iya baccin amma sai jinsa nayi ya fara magana, ya ce da ni, "Yaro nasan abin da ya kawo ka, zuwa kayi ka sanar da ni cewar ka fasa, baka son kayi arziƙin, to amma in tambayeka mana me amfanin baɗi ba bu rai? Sannan me amfanin ci ba ƙiba!" Shiru nayi na kasa amsa masa da tambayoyin da ya yi mini. Ya kada baki ya kuma ce da ni, "Mahaifiyarka dai ta mutu, kuma tuni tsuntsayen Inna uwar Aljanu sun kwashe hanjinta sun cinye, hakazalika sun sadaukar da jininta ga Komaɗau sarkin Aljanun gabas! Kai kuma yanzu ka taho kana kuka tare da ƙudirinka na shirin fasa abinda kayi niyyar yi, gashi kuma har ka ɗauki hanya, anya baka makara ba kuwa? Zan so kasani mahaifiyarka dai ta mutu, kuma ba za ta sake dawowa ba. Nayi imani da uban aljanu Jalkatau ɗan-tsidau! Matukar ka fasa wannan abin to tabbas zaka haukace nan da kwanaki bakwai!" Ya kuma tsoratar da ni na fara kuka a karo na biyu, na tambaye shi, to ya ya yake son in yi? Ya ce da ni, "Alfarma na ƙarshen da zan yi maka shi ne, yi maza kaje ka karɓi tulun a wajen abokinka, ka je ka samu wani wuri ka ɓoye tare da tulun, ka ɗaura shi a bisa wuta kuma ka ci gaba da ba shi wutan har na tsawon kwanaki arba'in. Daga nan ka dawo mini da shi. Idan kunne yaji jiki ya tsire! Sakamakon saɓawa waɗan nan umarnin da nake baka shi ne, ka haukace ka yi tsindir ka nausa kudu, sannan ka tonawa kanka asiri da bakinka". Daga gidan boka Ɗan-jatau kai tsaye na wuce cisƙalin abokina Shamuwa, na ɗauki tulun na fice naje shago na sayi ashana fakiti biyu da kuma kalanzir rabin galan na nufi yamma ina kuka ba tare da sanin takamaimai Inda na dosa ba. Sai da na baiwa garinmu ratar da ta haura na mil ashirin da biyar sannan na tsaya, anan nayi kwanaki arba'in cif-cif, ban da ruwan da nake sha daga wani gulɓin dake kusa da ni, ko abinci ba na ci. Nasha cin namun mushen dabbobin daji a lokuta da dama, saboda rashin abinda zan saka a cikina, kayan jikina ya yaiyage, na rame nayi baƙi ƙirin da ni, na komo kamar wanda ya fito a gidan yari ko kuma ya kuɓuta a gidan ƴan yankan kai. A ranar da kwanaki arba'in ɗin suka cika ji nake tamkar wanda aka yi wa kyautar duniyar sukutum! Don wallahi na gaji da rayuwar daji tare da dabbobi. Ai kuwa a wannan ranar ne na ƙara afkuwa cikin wani sabon tashin hankalin a karo na biyu. Da na ɗauko tulun izuwa gidan boka Ɗan-jatau ne ya karɓa ya buɗe jar ƙyallen da aka rube bakin tulun da shi, wasu fararen tattabaru ne su bakwai suka fita a cikin tulun, suka firke sama tun ina kallon su har suka ɓace mini. Ya ce da ni, "Waɗan nan tsuntsayen na Inna ce Uwar Aljanu, zasu ka yi ma ta saƙo ne akan ka cika dukkan sherudɗan da ta gindaya ma ka. Idan ka koma gida zaka tarar da wani akwati na baƙin ƙarfe a ajiye cikin daƙinka, duk bayan kwanaki bakwai ka ke yanka baƙin taure da kuma baƙar akuya ta baya, idan kuma zaka yankan ka tabbata ka juya wa alƙibila baya, sannan ka yanka su kana mai danna manya-manyan ashariya, saboda Inna uwar aljanu tafi son ashar sama da komi! Idan dare ya yi ka buɗe akwatin zaka gan shi cike fal da kuɗi kada ka tsorata kuɗinka ne, amma fa kada ka bari kowa ya kalli wannan akwatin idan ba kai ba, sai kuma abu na ƙarshe da ya rage maka, a yau ɗin nan da dare kafin gari ya waye ka kashe abokinka Shamuwa Ɗan-malam! Ka ƙwaƙule idonsa guda ɗaya ka jefa a cikin akwatin, Daga gobe ka fara yanka baƙaƙen dabbobin, tashi ka fice tsinane!" Lokaci guda gumi ya fara karyo mini, yanzu duk sheƙuwarmu da abokina Bala Shamuwa haka zan kashe shi, in ƙwaƙule idonsa? To kuma idan na koma gida in ce da mutane daga ina nake har na tsawon kwanaki arba'in a dai-dai lokacin da na rasa mahaifiyata, musamman ma ƙanwata?... DAƘIƘA SITTIN 05 ©Jibrin AJR Kamar ulu da kwarashi haka ƙwaƙwalwa da zuciyata suke ta yimin saƙa kala-kala tana kwancewa. 'Ta yaya ma ni zan iya kashe babban abokina da muka taso tare tun jan sawu?' Na shiga tambayar kaina. "...idan ba haka ba zaka haukace ka tonawa kanka asiri na kisan mahaifiyarka da ka yi, daga ƙarshe kuma uwar aljanu ta hallaka ka kaima tunda ka bijire mata." Na tuno da gargaɗin boka Ɗan-jatau. 'Ni kuwa da wani ido zan kalli duniya na sanar da su cewa ni na kashe ummata da bakina? Ai tofin Allah Ya tsine da zan sha ya fi duk zunubin da zan ɗauka, gwara kawai shima na kashe shi.' Na fara samun ƙwarin gwiwa. 'In banda abinka dama wa ya ɗaukeka kana zaman-zamanka ya kaika wajen wannan maƙetacin bokan idan ba shi ba? Ai shima kawai gwara ya samu sakamakon abin da ya aikata na sawa da ya yi ka kashe ummanka.' Wani ɓari na zuciyata ya ci gaba da zuga ni, wanda kuma tabbas na ɗauki zugar. 'Ƙwarai kuwa sai na kashe shi a daren yau.' Na sake rayawa ina tafe, 'amma ta yaya zan kashe shi ba tare da wani ya sani ba?' "Kawai ka ba shi guba ya ci ya mutu sai ka ƙwaƙwale idon ka cika umarnin boka." Na ji kamar an raɗa min a kunne. Na waiga hagu da damana banga kowa ba, amma tabbas dai wannan shawara ce mai kyau. A haka na wuni ina shirya yadda zan yi har zuwa dare lokacin sawu ya ɗauke, na tafi cisƙalin Bala da yake a nan yake kwana. Na yi masa sallama ya fito yana haskani inata tiri-tiri da baƙar laida a hannuna. "Me ka zo yi gunnan kai kuwa a daren nan?" Ya watso min tambayar da ko amsata ban yiba na kutsa kai na shige cikin cisƙalin. Ganin haka shima ya biyoni a baya. "Wai lafiya kuwa?" Ya sake tambayata ganin kamar ina cikin damuwa. "Lafiya ƙalau, na kasa bacci ne kawai na ce bari na zo gunka." Ya tuntsire da dariya. "Lallai mai dubu-dubu ka rikito aradu, yau kai ne har da kasa bacci?" Ban tamka masa ba kawai na miƙa masa laidar gurasar da na sakawa guba, lokaci guda nima na buɗe tawa da babu guba na fara ci. "Ai kuwa ka kyauta min, don dama da yunwa na kwanta." Ya karɓa ya fara hambuɗawa. Sai na ji kamar na hana shi ci amma dai kawai na daure. Sai da ya ci ya yi ƙyat ya kora da ruwa zama ya gagara saboda cewa da ya yi cikin shi yana murɗa masa. Yanayin yadda naga yana murƙususu da buge-buge bansan lokacin da na fara kuka ba, kawai sai na fita a cisƙalin don bazan iya kallon wannan rashin imanin ba. Gaba ɗaya sai na ji duniyar ta gundire r da talaucina na baya bai taɓa sawa na ji ba. 'Yanzu mene ne amfanin wannan arziƙin da duk waɗan da ya kamata su ci shi basa raye? Da farko Umma yanzu kuma Bala, to dama su waye makusanta na sama da su.' Wata nadama mara iyaka ta kama ni har na ji na fasa ƙwaƙwale masa idon duk abin da zai faru ya faru. Aikuwa ban gama tunanin hakan ba na ji cikina ya yi wata irin ƙullewa kamar ana tsinka min hanji. Na rusa ihu na tumu a ƙasa saboda azaba, a maimakon na ji sauƙi sai na ji an sheƙe da wata irar dariya. "A haka zaka mutu idan har ka ce zaka saɓa umarnin uwar Aljanu." Raɗaɗin da nake ji ya tilasta ni cikin jan ciki na shige cisƙalin da wuƙar da na taho da ita. Kamar a zare sartse haka na

Chapter 1 of 2