ji an zare min raɗaɗin bayan na cire masa idon, a haka ina kuka na tafi gida a cikin wannan tsakiyar daren.
Bayan na shiga gida ina tafe bansan inda nake jefa ƙafata ba na zunguri wani farantin ƙarfe da aka zuba kwanuka suka zubo suka karaɗe gidan da ƙara. Ban damu ba na shiga ɗakina, abin mamaki akwatin da boka ya faɗa min tana can ƙurya.
Na buɗe ina saka ƙwayar idon Bala kenan ƙanwata ta shigo, ta kalleni ta kalli akwatin.
"Yaya lafiya kuwa yau kwananka arba'in baka gidan nan? Daga ina kake a wannan daren ɗauke da akwati?" Ko kaɗan bana jin abin da take cewa, a maimakon hakan kawai tunanin gargaɗin boka nake yi.
"Kar ka kuskura ka bari wani yaga wannan akwatin..."
DaKIKA SITTIN
06
ANaM Dorayi
Ko kaɗan bana jin abin da take cewa, a maimakon hakan kawai tunanin gargaɗin boka nake yi...
Na ji wani ɗumi yana bin fuskata, ko da na shafa sai na ji hawaye ne suka rige-rigen zubowa daga idanuna, 'Yanzu duk wahalar da na sha ta tashi a banza kenan! Anya ba zan kashe ƙanwar tawa ba,' Zuciyata ta fara ziga ni. Na yunƙura a guje na yo kanta, ta fita da gudu, kafin na cinmata ta koma ɗakinta ta rufe, na juya cikin kumar zuciya. Babban abin da ya ƙara hautsina tinanina shine, rashin ganin akwatin a cikin ɗakin, har takalmina sai da na ɗaga inna neman ta, amma kas-da-bis na rasa ta. Wata mahaukaciyar dariya na ji ta karaɗe ilahirin ɗakin, na rasa daga ina take, na ji kasa na barazanar tsagewa in afka sama kuma tana ƙoƙarin ruftowa ta danne ni, na yunƙura zan fita daga ɗakin ƙafafuwana suka gaza ja na, na ji ɗakin ya ƙara karadewa da wata ƙara kamar tsawa a lokacin damuna, na ɗaga kai, fuskar Dan-jatau ce murtke, ya fara faɗin, "ka yi kuskure mafi girma a rayuwarka matsiyaci, ka yi hannun riga da arziki sannan ka zama abokin tashin hankali da ɓakin-ciki. Ya ƙara tintsirewa da wata mahaukaciyar dariya sannan ya ɓace. Take na ji; inama ban taɓa marmarin zama me kuɗi ba; inama ban cika rayuwata da burukan da a hanyar cikasu na rugurguje rayuwar waɗanda sune jigajigan da nake son kyautatawa idan na zama me-kuɗin. A takaice dai wanna rana na kwana cikin firgici da tarin danasani.
Washegari garin ya karaɗe da labarin mutuwar abokina Dan-mallam. Na tafi da ƙwarin gwaiwa domin halartar janazarsa amma na kasa sakewa, na kasa zama gu daya, na kasa kallon jama'a in yi musu gaisuwa. Abun da ya ƙara ɗaga min hankali shine, yanda 'yan-sanda suka haro ni gadan-gadan, da zuwan su suka yi min sallama sannan suka gabatar da kansu a matsayin masu bincike kan kisan abokina. Bayan sun min 'yan tambayoyi suka buƙaci nan gaba idan hali ya yi za su gayyace ni Police. Na ƙara firgita ainun da cewar za su gayyace ni, 'shikenan mutuwata ta zo nima,' na ayyana a zuciyata. Aka fito da gawarsa za mu tafi maƙabarta, muna cikin tafiya ya taso daga makarar ya yo kaina, gadan-gadan riƙe da idanuwansa a hannu, ai kuwa na juya a guje, duk ƙoƙarin da aka yi na ganin an riƙe ni ya tashi a banza dan ban taɓa ji na da karfi sama da wannan ranar ba. Tin daga wannan ranar har kawo yau; ban ƙara samun sukuni cikin a rayuwata ba, ban kuma sanya duk wani dangina a ido ba, na kasance tsakanin rayayyu da matattu, domin na manta da duk wani jin daɗin rayuwa, kullum cikin azaba kala-kala, waɗanda na garaci mutuwata da su. Hankalina kuwa, shi bai gushe ba kuma ban zama ciki masu cikakkiyar nutsuwar da ke rarrabe kyakkyawan yanayi da wanda nake ciki ba. Daji da dabbobinsa suka zama abokan hira ta, su ke sanyaya zuciyata, don na garaci ganin Kura ta zahiri da irin abubuwan da ke bani tsoro."
Cikin wannan yanayi na kasance har kawo yanzu da hankakina ya fara dawowa na fara tinanin yanda rayuwata ta kasance a baya, hakan kuma ya faru ne bisa bayyanar da Ummana ta yi a gare ni a watarana, cikin siffar da na saba ganin ta a duk lokacin da za ta yi min nasiha. Yanzun ma nasihar ta fara yi min, " Mutuwa da talauci lokaci ne da su, babu wani da'adam da ya isa ya kaucewa dayansu idan sun zama kaddararsa, cikakken mumini shi ke yarda da ƙaddararsa a yanda ta zo masa, ba ya zargin wani cikin kasancewar sa a yanayin da ya tsinci kansa, ka kyautatawa Allah zato, ka jajirce da nema a gurinsa, zai wadata ka..." Ta buɗe baki za ta cigaba da maganar Dan-jatau ya bayyana, ya tinkaro ni gadan-gadan Ummana ta juya a fusace tana ta karanta ayoyin da ta daɗe tana nanata min a rayuwata, tana ce min kariya ce daga dukkanin sharri, kafin wani lokaci ya fara tumuwa da kasa yana fitar da kunfa daga bakinsa... A haka ya bayyana cikin siffarsa ta zahiri a matsayin matacce. zuwa can kuma gangar jikinsa ta bi iska. Na kai duba zuwa ga Ummana na hange ta a sama tana faɗin, "Ka koma cikin jama'a ka kyautata rayuwarka da su, sannan ka dage da neman yafiyar Allah, ni kama na yafe maka. Allah yai maka albarka."
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels