An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Gimbiya Rahama
·
*SANIN GAIBU*
Labarin hadaka.
Na Gimbiya Rahma
A gurguje ya fito daga bandakin da ke manne jikin dakin baccin nasa. Agogonsa da ke ajiye a kan bed-side ya dauka tare da makalawa a hannunsa. Ya dauki makullin mota tare da surar wayarsa da ke ta faman ruri ya fita, tare da daga kiran, "Hello mum wallahi mun fito, muna hanyar zuwa."
Daga dayan bangaran ta amsa da cewa, "To don Allah ku hanzarta, mun dade tsaye muna jiran ku."
"To," ya amsa tare da sakkowa daga benen.
A falon kasa ya tarar da kaninsa Jibril yana jiran fitowarsa.
"Jibril, maza ka biyo ni mu tafi airport, su Hajiya tun dazu sun sauka zuwanmu kawai suke jira," ya kai karshen maganar yana kokarin fita daga falon.
Da sauri wanda aka kira da Jibril ya bi bayan dan uwan nasa domin aiwatar da abin da ya ce.
Tafe suke cikin mota suna hira jifa-jifa. Jibril da ke tukin motar ya dubi dan uwansa Tahir yana cewa: "Yaya wallahi na fuskanci makiya sun fara nuna halin a kan siyasar Dad dinmu. Kalli fa jiya da muka je kanfen yadda suke nuna bakin ciki a fili, saboda yadda Dad dinmu yake samun goyon bayan talakawan gari."
Murmushi Tahir ya yi sannan ya ce, "Ai Jibril dole sai mun dage da addu'a, don wallahi za su iya yin komai a kan ganin durkushewarmu."
***
Ko da shiga filin jirgin da ke jihar ta Sokoto, kai-tsaye wajen aje mota suka nufa tare da yin fakin su fito. Cikin dauki da son katari da iyayen nasu, suka nufi inda suka ga dandazon mutanen da ke tsattsaye, alamun su ma jiran masu daukarsu suke. Kaf suka gama zagaye wajen amma ba su ga ko mai kama da iyayen nasu ba. Cike da mamaki da kuma irin nice din sa ya ciro wayarsa da ke gaban aljihunsa ya fara latsawa. Har kiran ya katse ba a daga ba. Lambar Hajiyar tasu ya kira amma ga mamaki sai ya ji wayar a katse.
Duban Jibril ya yi da fadin, "Bros, ka ji na kira Dad bai dauka ba, ita kuma wayar Mom a kashe.
A firgice ya dago daga danna wayar da yake tare da fadin, "Bai daga ba kuma? to ko dai sun gaji da jiranmu ne suka tari tasi ne?"
"Haba! Jibril ya za a yi kamar Dad dan takarar gwamna ya hau tasi. Kawai dai ina tunanin ko sun samu wani ya kai su gida; ita kuma wayar Mum ba chaji."
Da wannan tunanin suka bar cikin filin jirgin tare da nufar gida.
Mai zai faru? Tun a bakin gate suka fara tambayar mai gadi. Amma ya ce tun fitar su ba wanda ya zo. Cike da tashin hankali Tahir ya dubi Jibril da cewa, "Mun shiga uku dan uwa, yanzu ya za mu yi?"
Cikin sanyin jiki, da murya Jibril ya ce, "Dole za mu koma can airport din, mu tambayi hukumar filin jirgin, tun da da zu da mu ka yi waya da Mum ta fadamun jirgin da suka hau."
"Me ke faruwa ne?"
Muryar mai gadi ta katse su daga maganar da su ke yi.
"Ba komai," Jibril ya fada a takaice.
****
Ko da suka isa filin jirgin, sai suka ga duk dandazon mutanen da suka tarar a dazu sun watse. Kai tsaye ofishin shugaban wajen suka nufa. Suka yi musu bayanin komai, inda shugaban ya dube su da fadin, "Gaskiya duk ilahirin wadanda suka sauka daga cikin jirginmu sun fita lafiya. Kuma kowa an zo an dauke shi. Amma tabbas ni da kaina har gaisawa mun yi da Alhaji Sammani Sanda a lokacin da yake kokarin shiga wata bakar mota kirar (Continue discussion)."
Cikin firgici Tahir ya dube shi da cewa, "Ai duk gidanmu irin motar nan baka guda daya ce, kuma ita ce yanzu mu ka zo da ita. Sannan kuma duk inda Dad dinmu zai je mu muke kai shi. Sam bai yarda direba ya kai shi ba. Kenan idan har haka ne tabbas iyayenmu sun fada mugun hannu."
"Kamar ya mugun hannu?"
Jibril ya tambaya a kidime.
"Sanin kanka ne Jibril kasan Dad din mu ba ya hawa kowacce mota. Ba kuma ya yarda kowa ya kai shi unguwa; daga ni sai kai. To kai yanzu mai kake tunani? Yanzu fa awa biyu kenan ba sa nan, ba kuma su isa gida ba, ga kuma duk wayoyinsu a kashe."
"Innalilahi wa'innailaihirraji'un."
Tahir ya furta a fili tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro...
Adam Abdullahi Gundutse
Admin
·
_____SANIN GAIBU____
02
Labarin hadaka.
Na Adam Gundutse.
"Inna lillahi wa Inna ilahi raji'un"
Tahir ya furta a fili gami da fashewa da kuka mai tsuma zuciyar duk wani Mai sauraro.
'Kanin sa Jibrin wanda ke tsaye daf dashi kafafuwansa na barazanar kasa daukar gangar jikinsa.zuciyarsa sai faman harbawa takeyi tamkar ta fasa kirjinsa ta fito saboda tsabar kaduwa da shiga ta'ajibi.hawaye ne ke barazanar gangarowa akan kumatun sa.
"Hazbunallahu wa ni'imal wakil.
Allazi iza asabatun musibatun 'kalu Innalillahi wa Inna ilahi raji'un"
Wannan addu'a ce kadai furucin da bakin sa yake iya furtawa. Lokaci guda ya daidaita natsuwarsa gami da dafa kafadun babban Yayan nasa.
"Yaya bamu da ishashshen lokacin kuka mu hanzarta nemar wa kanmu mafita.Kubutar da Dadyn mu shine abu mafi mushimmanci."
Cikin yanayi na tsananin damuwa ya dago kai ya kalle shi gami da jeho masa tambaya.
"Ina kake tunanin Dadynmu zai tafi tare da Umma a wannan lokacin ba tare da ya sanar da, daya daga cikin mu ba?.kada fa ka manta maganar da Dadyn ya Sha fada mana tun muna yara.mune akwatin adana sirrinsa.idan kuwa hakane wallahi Dad......."
Tahir ya katse shi da cewa
" Mu ajiye wannan batun a gefe tukun,sanar da 'Yan sanda shine abu mafi mushimmanci Yaya"
Lokaci guda suka mike gami da ficewa daga ofishin shugaban tashar jirgin da nufin tunkarar offishin Yan sanda dake zaune a tsohowar tashar jiragen sama.
Cikin hanzari Tahir yayiwa motar key lokaci guda ya fusgeta a gaggauce.kallo daya zaka yi musu kasan ba'a nutsuwarsu suke ba.
Ficewar su daga tashar jiragen keda wuya kira ya shigo wayar Tahir, Abin mamaki Abban nasu ne yake kira.A gaggawace ya rike handbrake motar ta tsaya cik.
"Kaga Abban mu ne ke Kira"
Ya nuna Masa fuskar wayar.Ajiyar zuciya Jibrin kawai yayi kana yace "Amsa kiran Dan Allah muji suna Ina shi da Umma?"
"Hello Daddy,
Hello,
Hello Daddy ko baka jina ne?"
Har yanzu Abban nasu bai ce uffan ba.Can daga bisani yaji anyi gyaran murya, Wadda ko bai
5y
Reply
Share
Adam Abdullahi Gundutse
Admin
·
Ko bai tambaya ba yasan wannan ba muryar mahaifin nasu bace.
"Hello dan Allah dawa nake magana?"
Wata mahaukaciyar dariya yaji an barke da ita a daya bangaren na tsawon yan dakiku.kana daga bisani aka fara magana.
"Sunana lauwali inkiya Barin Mai sai salati.Daukar rayuwaka shine take na.wargaza tattalin Arzikin mutanen da suka taba Izzata shine karfina. Mai da rayuwar 'Ya'Yan gata su koma mabarata akan titi shine muradina.Na gagari kowacce irin rundunar tsaro,. Sunana ya karade ko Ina a kasar Nan Amma an kasa cimmi inuwata.
Zan bar mahaifinku a raye idan har kuka bi wadannan sharudda da zan zayyano. Bijirewa umarnina shine kuskure mafi muni da zaku aikata a doron kasa"
Rabiu Sulaiman Sumaila
Admin
·
_____SANIN GAIBU____
03
Labarin Hadaka
Daga Rabiu Sulaiman Sumaila
..."Bijirewa umarnina shine kuskure mafi muni da zaku aikata a doran kasa"
'Hazbunallahu wa ni'imal wakil... Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Duk wadannan kalaman sunfito ne daga bakin Tahir acikin 'yan dakikun da basu wuce ashirin ba tareda maida dubansa zuwa ga Dan'uwan nasa Wanda tsawon lokacin da ya dauka manne da wayar a kunnensa gaba daya kallonsa yatattaru ne akan Tahir.
Tun kafin ya labarta masa wannan Mugun_jin da yayi ya tari numfashinsa...
Yaya Tahir, lafiya?.. Me.. me..menene yasamu su Abba?
Hannunsa yasa yayi masa alama da yadan saurara su gama wayar da dayan bangaren domin duk wani bata lokaci ayanzu bakomai bane illa barazana ga rayuwar iyayen nasu.
... "To Dan girman Allah Malam Lauwali kataimaka ka fadamin duk abin da kukeda bukata yanzu zan kawo muku. Nidai burina kada Ku taba lafiyar iyayena"...
" Hahahaaaa..!!! Idan kasake kirana da Malam to rangwame daya zanyi muku... wato Kan Mahaifiyarku da tuni dama yafara zubar da jini zan yanke alakarsu da gangar jikinta"...!
Sakamakon girman da idanuwan Tahir suka kara ne ya sanya Jibrin gaza yin hakuri inda yasake tambayarsa.
"Yaya Tahir ka sanar dani koma menene Dan Allah" cike da damuwa da kuma razana da suka bayyana a fuskarsa.
"Dan Allah kayi hakuri, Oga. Nadena kiranka da Malam. Ka fadamin duk abin da kukeda bukata, ko na wane kuma ko...
Ji yayi wayar ta yanke. Cikin hanzari yafara kokarin sake kira amma ya gwada har sau uku anki adauka.
" Subhanallahi... Dan'uwa muna cikin tashin hankali fa" Tahir ya fada yana duban Jibrin Wanda dama tuni ya kosa.
Ina jinka yaya Tahir,...Dan Allah meke faruwa?"
'Su Dady sacesu akayi.."!
"Su Dady sacesu akayi"!
"What..! Kana nufin Kidnapping?" Jibrin ya tambaya shima cikin fushi.
Alama kawai yayi masa da cewa hakane yayinda yayi wani irin cin_taya ya fizgi motar da gudu zuciyarsa cike da bakin ciki.
Cikin yan mintuna suka isa gida. Maigadin yabude musu suka shiga. Cikin hanzari bayan ya rufe ya taho da nufin yiwa Matafiyan barka da zuwa.
Tun kafin Maigadi ya bude baki yasamu amsar tunaninsa na shin ko ansamo su Alhajin Kafin su nemo Taxi din. Gani yayi Matasan guda biyu sunfito daga cikin motar ba tareda sunce masa Ci-Kanka ba sun shige gida alamar basu samo su Alhajin ba.
Shigarsu Falon gidan keda wuya Jibrin yabude baki da niyyar tambayar Tahir me yake shirin yi. Sai kuma ya rigashi magana.
"Kasan Masallacin Mal Mai Allo ?..kuma nawa suke kiran Sallar Azahar?" Tahir ya tambaya.
"Yaya ai inaga yakamata mufara zuwa mukai rahoto ofishin 'Yansanda daga baya mayi Sallar." Jibrin yabada amsa cike da nuna damuwa.
"Kaga bani hankalinka nan. Abin da yake faruwa shine, yayinda muke waya da wancan Azzalumin mutumin na samu wani Abu mai kama da satar amsa. Wato najiyo wani kiran Sallah, kuma yayimin kama sosai da kiran Sallar Ladanin Masallacin Malam Tanko Mai Allo".
A dan gajeran tunanin Jibrin ma zuciyarsa ta nuna masa lallai za'a iya amfani da wannan agano bakin zaren wannan Masifar da ta taso. Don haka cikin hanzari ya bawa Tahir amsa tareda gaskata tunanin.
" To aikuwa wannan aikin na Hukuma ne".
Cikin hanzari suka sake fitowa daga cikin gidan nasu a sukwane suka nufi inda Motar take domin kama hanyar Ofishin Yansanda. Amma kafin su isa inda Motar take Wayar Tahir din ce ta sake kara(ringing). Yaci burki yazaro. Ganin lambar da aka kirashi ne dazu wato ta Abbansu.
"Hello, Oga ina jinka. Dan Allah kayimin bayani yanda kakeso ayi" Cikin girmamawar dole Tahir yakewa Mutumin magana.
Daya bangaren aka amsa. "Kaje ka nemo Miliyan Hamsin saika rubuto mana sakon (SMS)". Zamu fada maka yanda za'ayi. Idan kaga dama ka sanar da Hukuma..."!!!#
SANIN GAIBU
04
Labarin hadaka
Gimbiya Rahma
"Kaje ka nemo Miliyan Hamsin, sai ka rubuto mana sakon (SMS), Za mu fada maka yadda za'ayi. Idan kuma kaga dama ka sanar da Hukuma..."!!!
Dif! sai kiran ya yanke, cikin kidima da gigita Tahir ke fadin, "Hello! Hello!! kana ji na oga..."
Amma ina tuni sun dade da yanke kiran, ko da ya kira sai ya ji wayar a kashe.
A kidimi ya dubi dan uwan nasa da cewa, "Jibrin, muna cikin wani hali. Shin ina za mu samu wadannan makudan kudin, ko za mu hada kudaden dake asusun mu, ina da tabbacin ko miliyan goma ba za su kai ba. Tabbas! SANIN GAIBU sai Allah, da ace mu ma, mun san ta da mun yi iya, yin mu don kubutar da mahaifan mu."
Duk sanyin na'urar sanyaya dakin, bai hana gumi ketowa daga fuskar Jibrin ba. Nan take ya ji duniyar tai masa zafi, cikin firgici ya fashe da kuka yana fadin,"Mum Dad! kune ginshikin duk wani farin ciki na mu, kune kuma rayuwarmu, ku kadai muka sani. Mun dauki alkawari ko za mu rasa komai namu, sai mun kubutar da ku daga hannun azzaluman nan."
Haka dai yai ta sambatu, in da Tahir ya kama hannunsa suka fita.
****
*TUNA BAYA*
Cikin shagwaba Tahir ya fada jikin, mahaifiyar ta su yana mai cewa, "Mum don Allah ki cewa Dad ya siyamun sabuwar mota."
Murmushi ta yi hade da cewa, "Dan gidan Daddy kenan, ai kasan dai yanzu Dad din na ku yana cikin halwar siyasa, duk kudaden sun tafi a wajen canfen. Ka yi hakuri zuwa bayan zabe lokacin komai ya yi setting."
"To Mum amma ya maganar tafiyar ku saudiyyan".
"Tafiya tana nan, nan da rana ita yau za mu tafi domin rokon Allah akan yin nasara, kasan makiya sun sa mu a gaba, dole sai mun je mun kai kukan mu wajen Allah".
Jibril da ke zaune yana latsa computer, ya dubi mahaifiyar ta su da cewa, "Wallahi mum ina mamakin yadda mutane suka fi son kan su, kirikiri ji yadda Alhaji Jamil Dan'iya. Ke yin adawa akan siyasar Dad din mu, kawai don ya ga yadda ya samu goyen baya."
"Ku dai kawai ku ci gaba da ta ya shi da addu'a, insha Allahu mu ne da nasara, tun da mun samu goyen bayan alummar gari." Cewar Mum din su.
Suna tsaka da wannan hirar Alhaji Sammani Sanda ya sakko daga saman benan da ke cikin falon, jikin sa sanye da wata dakakkiyar shadda.
# Wanene Alhaji Sammani sanda
Alhaji Sammani sanda. Haifaffen garin sokoto ne, yana da mata daya wato Hajiya Furera, da kuma 'yaya guda uku, Tahir shi ne babba, sai kuma Jibril sai aurarsu Farida, wacce ke zaune a kasan labanon, in da take karatu.
Alhaji Sammani, mai kudine, kuma mutum ne mai taimako da son mutane. Tun fari ya taba riki mukamin sakataren gwamnati, kasancewarsa mutum mai gaskiya da rikon amana yasa tsohon gwamna ya tsayar da shi takarar gwamna, tun lokacin da aka bashi takarar makiya su kai mar caa!.
Hakan ya sa ya kudiri aniyar taimakon mutane, idan ya samu nasara.
Alhaji Auwal, shi ne wadanda sauran mutanen su ka so a bawa takarar. Amma kasancewar sa mutum mai son kai da rashin gaskiya yasa tsohon gwamna kin bashi takara.
Duk da kasancewar Alhaji Sammani Sanda, yana da kudi hakan bai sa ya sangarta 'yayansa ba, duk abin da suke bukata a rayuwa, zai musu, amma ba ya ba su makudan kudi kawai don jin dadi.
*****
Cikin firgici da jin kalaman nasa, Alhaji Sammani yai saurin barin bakin kofar da yake kokarin budewa ya shiga, mamaki ne kwance saman fuskarsa, sam! bai taba tunanin cewa zai ji wannan magana daga bakin sa ba, da wannan mamaki ya isa gida tare da bayyanawa matarsa abin da yaji Alhaji Auwal Dan'iya yana fada..
****
Bayan Alhaji Sammani ya nemi waje ya zauna, sai ya dubi Tahir wanda ya dora kansa, a saman cinyar mahaifiyar tasa, ya ce, "Wai kai kuwa yaushe za ka girma ne Tahir, ji dai kaninka zaune abin sa amma kai kana jiki".
Ya kai karshen maganar yana mai fadada murmushinsa.
Duk suka kashe da dariya.
Sati na zagayowa Alhaji Sammani da Hajiya Furera, su ka nufi kasar saudiyya.
kwanansu goma a saudiyya suka nufi gida nijeriya, bayan sun sanar da iyalansu.
****
Kai tsaye Tahir da Jibril mota su ka nufa, tare da yi mata key su fice a guje daga cikin gidan...
________SANIN GAIBU_______
05
Labarin hadaka.
(Rukuni Na Biyu)
____Adam Abdullahi Gundutse____
Kai tsaye Tashir da jibrin mota suka nufa,tare da yi mata key su fice a guje daga cikin gidan.Cikin kankanin lokaci wani tunani ya d'arsu a zuciyar Jibrin Wanda a dai-dai wanna lokaci shi ne ke rike da sikiyarin motar,Hakan yasa yayi saurin take burkin motar gami da karkato duban sa izuwa ga Babban Yayan nasa kana yace
"Yaya Idan har abin da zuciyata take saka min gaskiyane.Bisa ga 'Dabi'ar Abban mu a daren kowacce rana yana rubuta mushimman kudure-kuduren sa na rayuwa Kama daga kan Wanda ya cimma da wanda yake Kan aikatawa har ya zuwa wad'anda zai tunkara.me zai hana ba zamu binciko (diary book) din Abban namu ba."
"Tunaninka akan dai-dai yake kanena "
Tashir ya fada cike da kwarin gyuiwa.
"Mu hanzarta komawa gidan domin duba littafin Daddy.ko Allah yasa ma samu madafa"
*** **** ****
Cikin sulusin dare, A can gabas da sokoto birnin shehu , A wani katafaren gidan gona mallakin Alhaji Auwal Dan'iya.
Manyan jiga-jigan yan siyasa ne guda uku zaune A Dakin hutun gidan gonar Wanda aka kawata da kayan alatu iri-iri.
Na farko tsohon shugaban yakin neman zaben Jam'iyya mai mulki Hon Bala barde wanda ya rasa kujerarsa a zaben daya gudana na shugabancin jam'iyyah.
Na biyu Alhaji Habu Dan kwairo shahararren attajiri Wanda ake ittifakin ya mallaki kudin da ba wani mahaluki da zai iya ja dashi a bangaren kudi a jahar.Burin mallakar karfin ikone ya shigo dashi siyasa. Shine Dan takarar Gwamna a jami'iyyar adawa wanda shine abokin karawar Alhaji Sammani Sanda.
Cikon na ukun Alhaji Auwal Dan'iya ne babban makiyin Alh sammani.
kowannen su fuska murtuke babu alamar tausayi ko tausasawa a tattare da su.Tsagwaron rashin imani gami da wutar hassada ce ke ruruwa a zukatan su.wannan Zama shine Zama na biyu da wadannan mutane suka yi.sunyi sa'ar cimma nasarar aikata dukkan hadafin zaman su na farko.
Hadafin su na farko shine sace Alh sammani,Na biyu ruguza tattalin arzikinsa.Na uku salwantar da rayuwar sa da ta matarsa Hajiya furera.
Da zarar hakansu ta cimma ruwa Alhaji Habu zaici zabe babu hamayya. Daga bisani Alhaji Auwal Dan'iya da Hon Bala Barde zasu chanza sheka daga tsohuwar jam'iyyah zuwa sabuwar gwamnati mai jiran gado.
A kowanne kuduri Alhaji Habu Dan kwairo yayi alkawarin Naira miliyan hamsin.
Lauwali b'arin mai sai salati.tsohon Dan ta'addane na yankan shakku.A duk lokacin da bukatar kau da wani daga doron kasa ta taso wa Alhaji Habu Dan kwairo, lauwali inkiya Barin Mai shine ke zartaswa.shine babban yaronsa a bangaren shik'a.A kowacce harkallah ya shiga shine bangon jinginar sa.
Lauwali da babban yaron sa Jatau sunyi amfani da fuskokin roba na Tashir da Jibrin wajen sace Alhaji Sammani Sanda da matarsa a tashar jirgin sama.
Kuskure mafi girma da Lauwali b'arin Mai yayi shine yin amfani da wayar Alhaji Sammani .Na biyu cin Amanar me gidansa da yayi har ya gaza danne kwadayinsa ya bukaci naira miliyan Hamsin daga wajen 'Ya'Yan Alhajin.wadanda dukka wadannan dalilai ka iya zamar silar tonuwar asirin su.
****
Lokaci guda suka tsaya cirko-cirko gami da tsirawa junansu idanu bayan samun rubutaccen bayani akan manakisar da ake Shirin shiryawa Mahaifin nasu.hatta tafiya saudiyyar da yayi tsananin abokanan adawar sane yasa ya nemarwa kansa sauki wajen yanke shawarar zuwa kasa Mai tsarki.
"Mu hanzarta sanar da kwamishinan Yan sanda halin da ake ciki."
Jibrin ya fada gami da sauraron Yayan nasa yaji me zai ce.
"Idan kuwa hakane kafin mu Kai musu kudin ya kamata mu gayyaci Yan jarida domin sune wakilan Al'umma."
"To Yaya A Ina zamu samu miliyan Hamsin ?"
Jibrin ya tambaya.
"Kada ka damu raina musu hankali zamu yi,Ina da Milyan biyar a asusuna su zan ciro mu shirya su a Akwati mu coga su."
"Allah yasa muyi nasara kada su hallaka mana mahaifa".
"Amin k'anena"
___SANIN GAIBU___
06
Labarin Hadaka
(Rukuni Na Biyu)
Daga Rabiu Sulaiman Sumaila.
'Amin k'anena'. Tahir ya amsa.
=============
Jatau yaron Lauwali ne abangaren ta'addanci saidai tsarin rayuwarsu ko kadan bai yi daidai da na junaba. Domin shi Lauwali yafara ne tun yana karami sakamakon tsantsar rashin ilimin addini ko na zamani. Yayin da shi kuwa Jatau yayi dukka biyun, saidai a bangaren bokone baisamu damar kaiwa inda yakeda buri ba saboda halin talauci. Nan yafara harkar Gyaran-Waya. Wannan dalilin ma shine sanadiyyar shigar Jatau wannan haramtacciyar Sana'a bayan haduwarsu ta dalilin gyaran waya da Lauwali yake yawan kawo masa wanda har suka saba dukda basu dade da fara mu'amula ba Jatau ya fahimci asalin waye Lauwali kasancewarsa cikakken Dakiki akowacce fuska. Domin mafi yawan lokuta idan ya kawowa gyaran wayar Jatau yaduba saiyaga ai bama wata matsala bace kodai tashiga Key ne ko kuma yayi kokarin yin kirane yakasa, wanda bakomai bane face kudinsa da yakare. Dadai sauran dalilai masu ban-haushi.
Lauwali yayi nasara wajen gayyatar Jatau ne zuwa wannan mummunar sana'a bisa wasu dalilai ciki harda BARAZANAR HALAKASHI. Da shigar Jatau wannan harka yayi bankwana da Sana'ar Gyaran-Waya. Idan kaga yana gyaran waya to tasace ko kuma ta Lauwali.
Lauwali ya aminta da Jatau sosai ko kuma ace yadogara da shi. Domin koda yaushe wayar Lauwalin ma tana hannun Jatau sai zeyi kirane kawai yake karba tunda yanzu koda yaushe suna tare.
==========
ASP Tiger, wani kwararren jami'in tsaro ne, wanda kuma gaskiyarsa da kuma kwarewar aiki akullum suke kara bayyana. Lokaci zuwa lokaci yakan zuwa yaduba irin bayanan da aka tattara na jerin laifuka sannan ya zabi wanda yafi kowanne muhimmanci wajen magance matsalar. Asalin sunansa shine ALIYU IDRIS, lakabin 'Tiger' ya samoshi ne sakamakon iya Kwamushen Masu Laifi. Duk irin Takadirancin masu laifi yakan sanyasu agaba yahana kansa hutu har sai yagansu acikin komarsu ta Hukuma. Babu irin Bad-da-Kamar da bayayi.
Rabiu Sulaiman Sumaila
Admin
·
SANIN GAIBU
(Cigaban 06)
..Mikewa yayi yafara zarya tsakanin Abokan zaman nasa sannan cikin fushi yafara fadin 'nifa agaskiya nafara gajiya da wannan tatsuniyar. Domin wankin hula yana nema yakaimu dare?' Alhaji Habu Dan Kwairo yafara bambami.
'Nan da gobe idan labari bai canjaba, to ni kuwa zan canja hanya. Ai KUTURU DA KUDINSA...!' Shiru yadanyi yana jiran martani.
======
" Yaya Tahir nifa a wannan Diary book din banga wani Abu da zamu dogara dashiba, amma naga ka dau hoton wannan shafin shikadai katurawa wani. Wa ka turawa kuma wannan tasiri hakan zeyi?' Jibrin ne ya fada cikin nuna karaya.
A gajarce Tahir ya bashi amsa. 'Abokina ASP Tiger'.
Shiru kawai Jibrin yayi amma babu abinda ya fahimta.
=========
"( _Ranka yadade, nifa nagaji da irin wadannan ayyukan ta'addancin. Dan Allah kataimakeni ka fitar dani. Ina matukar jin tsoron kada Hukuma ta kamamu tare ko kuma Oga yagano ba tare nake dasuba"._ ) sms kenan da Jatau ya rubuta tareda turawa wata lamba da ya adana acikin jerin lambobi na wayar Lauwali batareda saninsa ba tun da dadewa.
Kamar kullum, message din yana zuwa kamar dama jiransa akeyi, nan