da nan sai amsa ta dawo.
_(.."Kada ka damu komai yakusa zuwa karshe. Kuma nayi maka dukkan tanadin abinda ze wankeka a fuskar shari'a."_)
"Jatau kabar wayarnan haka kada chajin yakare. Baka gajiya da Game. Kuma akwai sako mai Muhimmanci da nake jira" Gwansamemiyar muryar Lauwali Jatau yaji, inda kamar koda yaushe,yayi hanzarin goge sakonnin tareda komawa kan wasa (Game).
"Nagama ma Oga. Game din tanamin dadi domin saura kadan yaragemin in hallaka Boss din. Kaima Oga dan bakasan yanda Wasan yakeba, da ka koya". Daidai lokacin ne ya mika masa wayar.
====
"Kada kidamu Tawan, domin tuni abubuwa sunkusa zuwa karshe. Family dinku kuwa Insha Allahu sun tsira daga sharrin wadannan miyagun" amsar da ASP yatura kenan a WhtsApp. A kullum sukan yi chat da Abokiyar hirar tasa wacce tuni soyayya tadade da kulluwa. PHARY BABY kamar yanda take a Facebook.
SANIN GAIBU...(Cigaban 06)
Jibrin wanda yayi wani uban tagumi ya dubi Tahir "wai yanzu menene abinyi?"
Ga mamakinsa kawai sai yaga Tahir yayi murmushi "kada kadamu yanzu ake tabbatarmin kudin karbo su Dady yasamu. Alh. Habu Dan Kwairo ne yabiya kudin".
"What! Amma a mafarki ko? Tayaya za'ayi abokin hamayyar dady yabiya kudin karboshi?"
Murmushin dai Tahir ya kara yi. "Wannan duk shirin ASP Tiger ne! Anan yasanar da shi duk yanda Abotarsu ta fara harma irin kokarin da yaketayi da dadewa.
Lauwali ne yadubi fuskar wayarsa sannan yamikawa Jatau. " Duba kaga shin wannan kuwa ba sakon Mutanen bane?"
Da hanzari Lauwali, Jatau,sauran Yan-Dabar su Alh Sammani da Haj Furera atsakiyarsu,suka rankaya zuwa bakin gate din Tangamemen Gidan dake daura da Masallacin Mal Tanko Mai Allo da nufin karbo jakar kudinsu kamar yanda Jatau ya karanta a sakon da aka turo musu.
Wani siririn mutum suka tarar tsallaken titin rike da jaka gindin wata sabuwar mota kuma da alama babu kowa cikinta. Tuni suka karasa sukayi Hannun-Kuturu-da-Makaho Su Alhaji aka bude musu motar suka shiga bayan tabbatarwa da cikar kudin.
Aikuwa motar tana barin layin saiga rundunar Jami'an sunfito daga cikin wannan Masallacin sunkai su hamsin kowa da Bindiga. Atakaice dai nan akayi caraf dasu.
======
Barde ne yakoma gefe yana kiran waya aboye 'Ya ake ciki, ka cire dukka million hamsin din?' To maza katafi tsohon kangona na bayan gari ka jirani kasan muna tare sa me kudin. Kuma idan yasan ba'ayi yanda yaceba...zanzo dai muhadu".
'To Chairman angama. Ina jiranka agurin'. Sulu ya katse wayar yayi murmushin mugunta adaidai lokacin da ya faka Motar abakin Gate na wani Kango juyo yace "Yawwa, Sir. Kada kudamu Abokan aikina suna cikin wannan Gidan, zamu jira zuwan Bala Barde. Nan dai Alhajin ya amsa da cewa ba matsala.
Jim kadan sai ga motar shugaban jam'iyya tayi fakin,lokacin asuba tayi danhaka zaka ganeshi kasancewarsa Mai katon Tumbi.
Yana hango Sulu yayi saurin yimasa alama da ya miko masa jakar kudin.
SANIN GAIBU... (Cigaban 06)
Ta gefensa yaji anyi masa kashedi " Oga wannan gilashin motar taka baze hana harsashin bindigar nan saduwa da wannan katuwar fuskar taka ba. Don haka kafito cikin salama".
Da rawar jiki Bala Barde yafito jiki yana rawa cike da mamakin irin cin amanar da Yardajjen Yaronsa Sulu yayi masa.
====
Kafin wayewar gari canma Gidan gona jami'an tsaro ne da taimakon Bayanan-Sirri suka kai sumame inda sukayi caraf da dukkan mahalarta Haramtaccen taron da akeyi tun tsakar dare. Babu bata lokaci aka tattarasu zuwa Ofishin Hukumar Tsaron ta jaha, inda anan ne suka tarar da Bala Barde wanda ya fada musu Uzirinsa na Karya ya baro gurin taron.
=====
Lallai SANIN GAIBU... Sai Allah!..
Kasancewar baya samun bacci sosai tasa yau Jibrin ko sallar Asuba baisamu yayiba. Saida yaji ana buga masa kofar daki sannan yatashi firgigit. Tahir ne yake fada masa cewa yayi maza yafito zasuje Station domin sutaho da su Dady.
Baisan lokacin da yayi jifa da pillow din da yake kwance akaiba yayi maza yafito agurguje yayi Sallah sannan ya tarar da Tahir a Mota suka harba. Ahanya kuwa shikansa bai san adadin tambayoyin da yariga wullawa Yayan nasaba kuma duk yasamu amsoshinsu.
=====
Kwarewar Jami'an Tsaron wannan jaha musamman kasancewar ASP Tiger daya daga cikinsu takai matuka.
Cikin wannan wuni saida aka tuhumi dukkan wanda yakeda hannu cikin wannan Badakalar. Yayinda Shahararrun kafafen yada labarai irin su #Tsangaya_TV, #Tsangaya_FM, #Tsangaya_Newspaper da sauran kamfanonin yada labarai aranar suka ajiye duk wani labari saida suka tabbatar Al'ummar wannan gari sunji dukkan abinda ya faru da Gwaninsu wato ALHAJI SAMMANI. Nan fa farin-jininsa ya kara nunkawa.
Koda lokacin da aka buga gangar siyasa yazo ko kamfen al'umma basu barshi yayiba. Kuma cikin Ruwan-Sanyi yayi Tazarce.
#WalhamduLillahiKasiran...!
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels