Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce ranar tare war ta gidan Alhaji Tukar, kai ka ce ba Mariya ba ce. ta yi kyau abin ta kamar ba ita ba da yamma bayan sallar la'asar aka zo a ka ɗauke kai tsaye aka uwce da ita gidan ta ta ke gwarinfa. Ma sha Allah gida ne ya haɗu. komai akwai a gidan babu abin da zata bu ƙata. Bayan ƴan kawo amarya su tafi ƙana nan yaran Alhaji Tukur suka zo suka zagaye ta suna murna an kawo masu sabuwar mommy ita kuma ta saki jiki suna ta fira. Sai bayan salar isha'i Alhaji Tukur ya shigo gidan sai da ya gama duba ɗakin manyan yaran shi ya ga duk suna nan san nan ya yi ma su sallama ya kulle gidan. Abin da ya gani bayan ya shiga cikin gidan ne ya sa shi farin ciki ɗan Mariya ya ga ni zaune cikin ƴa'ƴan suna fira suna cin abinci da zara ta dafa masu. Sosai ya gode ma Allah san nan ya shiga da sallama duk suka yi mashi sannu da zuwa ya basu lida ɗaya da ke hannun shi ya ce "su je ɗakin su su ci." Suna murna suka rungume Mariya da suke ce mata Mommy Suka yi masu sai da safe. Bayan sun shiga cikin ɗakin su Alhaji ya kama hannun Mariya suka shi ga inda ya kasan ce ɗakin ta. Suna shiga ya rungume ta ya na mata godiya ganin da ga zuwan ta fara sakar ma ƴa'ƴan shi fuska. Bayan ya gama ma ta godiya suka yi nafila daga nan kuma aka shiga wata hidimar. Eshan ya rufe gida ya hana kowa shiga wai ba za'a zo a takura masu ba . Ga shi kuma wasu duk yau zasu wuce sai da aka kira Mame aka faɗa mata san nan ya buɗe wainda suka shiga dan sai da su ka yi da na sanin shi. Suna zama suka ga gan shi ya dauko Amira a ƙafa ɗa ya zo ya zaunar da ita akan kujera ya na ce wa "sannu Beby." Ƴan uwan Mame da Abba da Da su Ammi da ke falon duk sai kunya ta kama so. Shi ya shiga kicin ya dauko ma su ruwa da lemu san nan ya kawo ma su ya na ce wa " ga wannan ku sha matar gidan bata da lafiya ga ta nan na jin jiki ko tafiya bata iya yi." Wata inna talatu ce cikin ƴan uwan Abba da ta ce "yau naga abin da ya ishe ne Muhammad sai yau shi za ka sauya ne?" Su dai kam har kar gaban shi kawai ya ke daga karshe ma zuwa ya yi ya daura kan Amira a cinyar shi. Amira kunya ta ishe ta kamar ƙasa ta buɗe ta shiga haka ta ke ji." Ganin abin na shi na yi ne ya sa suka ta shi suka gudu dan idan suka zauna zasu ga abin da yafi ƙarfin su. Suna fita ya kwashi da dariya ya na cewa "ai maganin ku kenan in banda gulma me zai kawo ku gidan mutane tun da safe wai kun zo ku yi sallama Ni nasan ba sallama ta kawo ku ba." Gidan Ahmed suka shiga Hafsat jikin ta da sauƙi amma tana ita takawa ƙaɗan ƙadan amma da ka gan ta gasan daure wa kai take. Ita da kanta ta fito suka gaisa san nan suka suka yi masu sallama suka tafi gidan Abdul. Suna zuwa suka gan shi a falo zaune yana duba system da alama aiki ya ke me mahinman ci. Suka shiga suka zauna bayan sun gaisa suka tambaye shi ina Amarya? Budar bakin shi sai cewa ya yi " bata Lafiya ta kwanta ta na huta wa." Baki sake suke kallon shi dama ai halin su ɗaya da wan can rasa kunya ɓeran tanka wato Eshan. Haka suka ƙara ci zaman su suka ta shi suna ta magana akan rashin kunyar da suka yi masu. Bayan sun fita gidan Eshan ya dauka waya ya kira Ahmad be ɗaga ba dan haka ya ƙira Abdul ya faɗa masa. Shi kuma Abdul ya ce "zai yi maganin su shine ya fito falo ya zauna yana jiran shigowar su aka kira shi akace ya duba system ɗin shi ya duba saƙo. Haka suka koma gida suna faɗin abinda su Eshan su ka yi. Ammi ba ta ji daɗin abin da suka yi ba. Ko da aka faɗa ma Mame sai da ta ƙira su tayi ma su faɗa. Ta bangaren Yusurah ma haka ta kasan ce mutane na zuwa ganin amarya. Alhaji Tukur ya yi mamakin yanda ya samu Mariya. San da suka ta shi zara har tayi masu abin kari ta kawo ta aje masu. Mariya tunda ta tashi ta ke jin kunyar shi dan ko ido ba ta so su haɗa. Washa gari Aka yi ƙarin girman su Eshan inda aka Bama Eshan muƙamin shugaban sojojin Najeriya Shikuma Ahmed aka bashi mate Makin shi. Alhamdulilah rayuwa suke cike da kwanciyar hankali suna kula da matan su yan da ya da ce. BAYAN WATA TAKWAS Abubuwa da ya wa sun faru na daɗi da akasin haka. Ta bangaren Amare kuma ku wa ce nada cikin ta sun kusa haihuwa Mame mahaifiyar Ahmed tayi aure inda wani abokin Abbi da ya kawo mashi ziyara ya gan ta ya ce ya na so babu ɓata lokaci akayi bikin su suna zaune unguwa ɗaya da su Ammi. Yau watan Mommyn Yusurah biyar da rasuwa bayan jinya da tayi an ji mutuwar ta Sosai. Ministar garin Abuja ya kai ziyara giɗan yare inda ya ce zai taimake wasu cikin ikon Allah sunan Umma ya fita aka fito da ita yanzu haka tana zaune a gidan su. Bayan fatuwar ta Ammi ta roƙe Abbi ya da wo da ita ya ce sai yayi Shawara. Amarya ta haihu matar Daddyn Yusurah inda ta haifi yarta mace aka sa mata sunan mommy Yusurah suna Kiran ta da Hibba. Yau Amira ta tashi da wani kalar ciwon mara suna tunanin ba haihuwa ba ce dan IDD din ta bai cika ga ganin yan da ciwon ke ta nukur kusar ta ya sa Eshan ya kira gida. Kai tsaye asibiti suka wuce suna zuwa aka ce ai haihuwa ce ta tashi. Jin an ce haihuwa hankalin Eshan ya tashi ya ma rasa me zai yi sai da Ammi ta kama shi tana mai nasiha ta ce ya yi mata Addu'a in Sha Allah zata sauka lafiya. Can cikin lebor room Kuma suna ta ƙoƙarin ganin ta haihu da kanta amma abin ya gagara hakan ya sa suka ce sai an mata CS dan da alama ba yaro ɗaya bane. Hannu Eshan ya sa aka shiga da ita CS cikin ikon Allah aka ciro mata yara uku biyu maza ɗaya mata kuma da ita da yaran ta lafiyar su ƙalu. Wayo zu kuga murna wagan Eshan likitar da ta faɗa ya dauka key na motar shi ta ɗamƙa mata suma saura ya yi waya yasa aka kawo masu ta so. Haihuwar Amira ta zagaye Family ko ina. Ranar suna aka yanka raguna inda yara suka sunan Abba da Ahmed macan kuma aka saka mata sunan Ammi. Inda za dinga ce ma me sunan Abba Ariyan me sunan Ahmed kuma fahat macan kuma suhailat. Bayan haihuwar Amira da kwana goma ita Farha ta haihu ta haifi ɗiyar ta mace aka sa mata suna Fatima zasuna kiran ta da zara. Anyi taro an tashi lafiya. Bayan ƴan kwanaki kuma Hafsat da Yusurah suka haihu rana ɗaya Hafsat ta haifi yara biyu inda ɗaya ya ci sunan Eshan za suna kiran shi da Aiman ɗaya kuma ya ci sunan mahaiyar ta zasuna kiran ta da Afra. Yusurah kuma ta haifi yar ta mace ita kuma ta ci sunan mahaifiyar Haidar za suna kiran da ta Islam. Yau ne Abbi ya maida Umma ta nemi yafiyar Ammi san nan ta kuma nemin ta su Amira. Yan zu komai ya saitu kowa yana rayuwar shi da iyalan shi hankali kwance. BAYAN SHEKARA BIYAR A Wainan shekaran abubuwa da yawa sun faru a ciki harda karatun su Amira inda ta karanci aikin koto ta zama babbar lauya. Faraha da Hafsat kuma sun karan bangaren likitanci yanzu sun zama manyan likitoci. Yusurah kuma malamar makaranta dama shi ta ke so. Mariya yan zu haihuwar ta biyu suma hankali kwanci. Malam Sa'idu ya chanza gida dan da kudin da Mariya ta ba shi ya ƙara ma kasuwan cin shi ƙarfi yanzu ya zama babban ɗan kasuwa. Umma ma ta ƙara haihuwar mace aka sa mata sunan Ammi. Ya yanzu Umma ta dauka Ammi tamkar Yayar ta. Ita ma Ammi ta dauke ta tamkar ƙanwa. Yau ta kama Amir zai dawo daga US shekara uku kenan da tafiyar sa a yanzu ya zama babban likita. Amira ce take ta fama da yara sun zo su ci abinci amma sanki zuwa zuna ta wasa yara ne kusan su bakwai. Yaran Yusurah dana Farha dana Hafsah ne aka kawo gidan da yake duk week end yaran na zuwa hutu. Ma sha Allah Amira ta yi girma ta zama wata mama guda da ita kamar ba ita ba ce warda sai tayi Bara zata sama masu abin cin da zasu ci kamar ba ita ba ce kayan sawa da yawa suke gagar ta abubuwa da ya a dai. Amma a yanzu baza ka ce tayi kalar wannan rayuwar ba. Su Yusurah ne suka shigo da sallama ma sha Allah suma sun yi girama kamar ba suba kowace na ji da kanta sun haɗa kan su gwanin birgewa. Da gudu yaran suka tafi suna muranar ganin su. San nan suka shiga cikin falo ba su daɗe da zama saiga su Eshan sun shigo. Da na kalle su sai da na ƙara kallon su sun dan manyan ta amma ba sosai ba kuɗi da ilimi ya biye duk wannan dan yanzu sun haɗa hannun jari suna kasuwan ci. Mariya ta na zaune suna fira da yaran harda manyan ciki wasa ma duk sunyi aure zara ma tayi aure. Alhaji Tukur ne ya shigo su ka yi mashi Barka da zuwa. Mariya ta yi ma magana ya ce "ta zo zasu yi magana." Bayan ta shiga ɗakin wata takarda ya ba ta ya ce "ta shirya da sun dawo Saudiya zata koma school kuma ya bata kuɗi masu yawa ya ce tana yin sana'a." Mariya ta rasa me zata yi kawai sai ta fashi da kuka. Shi kuma ya tsaya yana kallon ta ganin baza ta daina ba ya sa ya jata zuwa kan gado ya haɗe bakin su yana kissing nata ta ko ina yana cewa yau beby nike so kikara min. Su Amira de mazajen su suka dunguna zuwa gidan su Ammi suna zuwa suka ga sun fito za su tafi aripot su dauko Amir dan saura minti goma jirgin su ya sauka. Su duka suka dunguma zuwa aripot sanda suka isa jirgin su har ya iso. Amir yana fitowa da gudu ya yi kan Amira ya na dariya ya na zuwa ya rungume ta suka fa shi da kuka. Ba kukan komai suke kuka ne na sabo kuka ne na sauyawar da rayuwar su tayi. Sun birge kowa a wajan. Bayan sun gama kuka suka juya wajan su Ammi ya gaishe da su suka dunguma zuwa gida. Suna zuwa bayan an gama cin abincin su Eshan suka ce zu fito su ga wani abu. Suna fita suka ga sababin motoci kowa ya ba matar sa key din moto. Ko wace ta rungume mijin ta ta na murna. Amir ne ya zo ya na ɗaga camera Happy Family kowa ya ɗago suna dariya. ALHAMDULILAH ALHAMDULILAHI ALHAMDULILAHI ANAN LITTAFIN DAFIN ZUCIYA YA ZO KARSHI YA ALLAH KUKUREN DAKE CIKIN SHI ALLAH YA YA FINMIN ALKAIRIN DA KE CIKIN ALLAH YA HAƊA MU DA SHI BAKI ƊAYA. INA ME MIƘA GODIYA DA FATAN ALHERI GA WAI NAN BAYIN ALLAH HAƘIƘA KU ƊIN NA GARI NE MASU SAN GANIN CIGA BAN KOWA NA GODE SOSAI Maman ihsan Zeenasir Halimatusulaimansada299 Jamila lawal zango Maryam Umar star Sakina Ismail camerun Sa'adatu ta batulu Barester Maryam Anas Brandon Princess minal Pending Amarya Autass Roufieyn Baba🫀🦋❤️‍🩹 Kharat❤️ Dr Hafiza Mansura Isma'il Abdullahi GODIYA TA MUSAMMAN GA NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHIM INA MAKI FATAN ALHERI An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14