Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels FURUCIINAB LAWAN BRIGADE Uwargidan Lawan Muazu Kazaurc) FURUCI1 Copyright © ZAINAB LAWAN BRIGADE HAKKIN MALLAКА (M) ZAINAB LAWAN BRIGADE FADAKARWA Na rubuta wannan littafi ba da nufin tozarci ko cin zarafin wasu ba, idan an ga wani abu da ya yi daidai da abin da ya faru a zahiri to arashi ne. GARGADI Daukar wani abu don yin amfani dashi a cikin wannan littafi, babban kuskure ne. Duk wani abu da ake son dauka yana da kyau a dauka da sanin marubuciyar. 2005 BABI NA DAYA e yanzu haka za mu yi dake ko Asama'u? "KBabu dama mu ba ki shawara a matsayinmu na iyayen ki ki yarda ko? To shi kenan mu zuba mu gani mu da ke ma ga kwararre." Hadiza ta yi cikin shiru ta dauke kallonta daga kan diyar tata zuwa gefe, takaicin kin bin umarnin su da Asama'u ta yi. Ita kuwa Asama'u sai ta dukar da kai hawaye na ta fita daga idanunta. Suna zaune a haka sai suka ji sallama a bakin kofar falon. "Wa'alaikin salam!" Hadiza ta amsa. Wata dattijuwar mata wadda zata iya kaiwa shekara sittin, ta daga labulen falon ta shigo. Hadiza ta yi dan murmushi. "A'a sannu da zuwa Goggo." Cс. Tsohuwar ta mayar mata da murmushi, ita ma ta 5 "Yawwa sannu Ta-Maigari." Ta karasa kan daya daga cikin kujerun taushin da suka yiwa falon kawanya, ta zauna. A lokacin ne ta lura da Asama'u dake zaune dirshan akan kilishin dake malale da falon. "A'a....kin ci gidanku...'yar nema ba kya ganin mutane nc?" Asama'u ta dago kai idanunta cike da hawaye ta ce a sanyayc. "Sannu da zuwa Gog..." "A'a lafiya, me ya sameki?" Goggo ta katse ta ganin hawaye na zuba a idanunta. Asama'u ta dukar da kai ba tare da amsa ba. Goggo ta dubi Hadiza. "Ta-Maigari wa ya tabа min 'yar uwa?" Hadiza ta yi murmushin yake ta cе. "Wai akan Babanta ya ce bai amince da soyayyar ta da wannan yaro Aminu dan gidan Alhaji Gambo ba, shi ne ta zauna anan take yiwa mutane kuka." Goggo ta dubi Asama'u sannan ta kuma duban Hadiza. "To shí menene zai sa ya hanata wanda take so?" Hadiza ta dukar da kai "Kin san akwai. dadaddiyar gaba tsakaninsu da Baban wannan yaro. Kuma ni banda abinta ma, tun tasowartà a gidan nan ta ۲ taba ganin an aurar da wata 'ya ga bare." "Kin ga ya isa." Goggo ta katse ta. "Me yàsa kuke abu kamar kananan yara, dama shi addinin Musulunci ya yarda da wannan tsari na sai dan gida kawai za a aúrar wa da 'ya ko ko ya ya, da za ki ce wani tunda ta taso bata taba gani ba....wannan har wani abin birgewa ne?" Hadiza ta nisa "Ki yi hakuri Goggo, ni ma ba tsari na bane kin san halin sa...." "Ba ruwana da wani halinsa, ke ma ai dakc. Me yasa idan yana yi ba kya kwabarsa? To ni ba zan taba yarda da wannan ba." Hadiza ta cira kai ta dube ta. Ba shakka ta fahimci ran Goggo ya 6aci, wannan kuwa ta san ya biyo bayan rashin sanin irin zafin da Alhaji ya dauka a dangane da abin ne. Ta kuma nisawa. "Allah ya huçi zuciyarki Goggo, nima abin ya fi karfina ne, don gaskiya da farko ban so hakan ba amma ganin irin furucin Alhaji yake yi na cewa da ya aurar da Asama'u -ga dan gidan Alhaji Gambo gwanda yamutu...." "Eh!" Goggo ta dafe baki "Gwanda ya mutu fa ya ce?" Ta gyada kai "To kwa zai mutun in dai akan aure ne. Wa ya fada masa akan aure sunnar ma'aiki ana yin wannan kalami?" Ta tsagaita "Yanzu yana ina?" "Ya fita tun dazu." Hadiza ta amsa a sanyaye. Goggo ta nisa "Na so ace yana nan don na bashi wani labari na wani mutum da ya yi makamancin irin wannan faruci don ya san aure ba a hana shi." Tana rufe baki sai suka ji sallam. Wanda take nema ne ya shigo da saurinsa. Mantuwa ya yi don har ya kusan zuwa ofis ya tuna bai dauki wasu muhimman takardu ba, saboda ya fita yana fada akan dole sai 'yar sa Asama'u ta rabu da masoyinta 1 Aminu. Ya yi turus! Ganin mahaifiyarsa, da hanzari ya durkusa har kasa, ya ce "Sannu da zuwa Goggo....ina kwana?" "Lafiya kalau." Ta amsa kamar ba ta so. "Tashi ka zuana ina son magana da kai dama yanzu na ke tambayarka aka ce ka fita." Ya tashi ya zauna jiki a sanyaye. "Kai me ya sa kakc kokarin raba wannan 'ya da wanda take so?" Ta kura masa idanu tana jiran jin abin da zai ce. "Wacce 'ya kenan?" Ya bukata kansa a duke. "Wacce 'ya kake da ita yanzu a gidan nan?" Та mayar masa da tambaya. Tun farko ya san wadda take nufi amma saboda sanin cewa zuciyar shi ba zata taba amincewa da aurar da 'yar sa Asama'u ga dan babban makiyinsa Aminu ba, shi yasa ya tambaya. "Ba ka ce komai ba...ba da kai nake ba?" Ta ci gaba a zafafe ganin ya yi shiru. In ban da yana shayin Gwaggo da ba abin da zai hana ya hau ta da fada. Kamar yadda ya ajiye a zuciyarsa babu mutumin da ya isa ya yi masa wannan maganar ba tare da ya mayar masa da martani ba. To amma ita wannan mahaifiyarsa ce, ko ba komai akwai darajar haihuwa. Abu daya kawai-ya dace ya yi mata shi ne ya nuna mata yanzu zai je wajen aiki ne jama'a suna jiransa idan ya taso zai je gida ya samcta, shi kenan ya huta. Muryarsa a marairace ya cc. 8 "Goggo wannan maganar doguwa ce, ki yi hakuri yanzu ana jirana a wajen aiki..." "Au Allah.....ana jiranka a wajen aiki wato aikin ya fi maganata kenan ko?" "Ba haka banc Gwaggo." "To ya ya ne?" Ya dukar da kai "Allah ya huci zuciyarki, ina sauraronki." ma?" Ta harareshi "Au har ka manta tambayar da na yi Ya girgiza kai "Ban manta ba. Gwaggo ni kaďai ne na san abin da ya sa na ki amincewa da wannan al'amari, saboda..." "Ka ga Malam dakata bana son dogon turanci. -Ka gani ka kiyayi kanka da yunkurin tarwatsa hanyar gina sunnar ma'aiki, idan ba haka ba ba shakka za ka yi karkon kifi a rayuwar ka. Akwai mutane da dama da suka bi irin wannan hanya da ka ke shirin bi suka yi dana-sani. To wai kai menene ma tsakaninka da Alhaji Gambo da har zaka dauki karan tsana ka dorawa Tansa?" Alhaji Masa'ud ya sosa keya cikin rashin sanin yadda zai ce. "To ka ga saurareni da kyau ina so ka nutsu don zan baka labarin wani mutum mai irin wannan hali naka wanda daga karshe ya yi mummunar makoma, don ka kiyaye domin an ce in ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta shafawa naka ruwa." Ta yi shiru. Alhaji Masa'ud ya matsu kwarai ya tafi wajen 9 aiki amma gudun kar Gwaggo ta ce ya fifita aiki akan maganar ta sai ya tsaya don jin labarin nata. "Kana ji ko? Wannan labari da zan baka ya faru ne a lokacin da na je Maiduguri gidan yayarka." A unguwar da na zauna an yi wani Alhaji hamshakin mai kudi mai suna Alhaji Salisu wasu kuma suna kiransa rumbun naira. Mai kudi ne sosai na gani na fada, to amma sai aka wayi gari suna matsananciyar gabar gani a fada da wani makwabncinsa da mafi yawancin mutane ba su san menene makasudin ta ba. To amma da tafiya ta yi nisa cikin gama ya gama sai aka gano dalilin gabar tasu. Gabar tasu ta samo asaline tun suna samari. Sun nemi mace daya ne da aure a wancan lokacin wanda 21AD bayan gwagwamarya da aka yi shi Alhaji Rabo ya yi nasarar kasa Alhaji Salisu ta hanyar" aure Suwaiba (matar da suke so su biyu) To tun fa daga wannan gaba ta kullu sosai abin ya zama ko ga maciji ba sayi a tsakaninsu. Suna nan zaune cikin wannan hali na yau fada gobe masifa bayan shekaru masu yawa sai Ubangiji ya kulla wani abu a tsakaninsu. Wato dan gidan shi Malam Rabon ya ga 'yar gidan Alhaji Salisu ya ce yana so. Bai kuwa sha wahala ba yarinya ta amince duk da suna sane da abin da ke faruwa tsakanin iyayensu. Kai tun yara suna soyayyarsu a boye ta fara fitowa fili. Ran nan Alhaji Salisu na gida wani dan fadarsa ya je ya sanar dashi tsaf game da abin da ke faruwa. A 10 wannan rana sai da ya yi kamar ya cinye 'yar sa Salamatu danya don tsananin fada, sannan ya kafa mata wasu sharudda na cewa duk ranar da ya kara ganinta da wannan shegen yaron sai ya kasheta. Ya sha fadar wannan kalma cewa gwanda ya kasheta ya huta da ta auri wannan yaro Khalifa. Amma ina yadda kasan ana zubawa wuta fetur soyayyarsu sai kara habaka take yi kamar wutar daji. Da dai abubuwa suka fara bunkasa sai Alhaji Salisu ya nemi ganin Alhaji Rabo don yi masa gargadi akan ya jawa dan sa kunne shi kuma ya ce da ya take gidan Alhaji Salisu gwanda ya zama gurgu. Dalilin wannan abu da ya faru saį shima Khalifa ya soma fuskantar barazana ta ya rabu da Salamatu ko ya tsine masa amma yaro sam ya ki saurare. Kai gaba dai gaba dai saboda takura sai haduwa ta yiwa wadannan yara wahala. Ita Salamatu an sa ta ma a kulle kwata-kwata ba ta fita shi kuma Khalifa kullum fadan safe daban na yamma daban. Da suka rasa yadda za su yi sai suka sauya salo na gudanar da soyayyar aa rubuce, wato ta wasika amma ina sai suka ji wannan ma bai yi ba. Ana nan sai suka kuma sauyawa suka dauki wata dabara a kullum sai su rika haduwa akan hanyarta ta zuwa makaranta wannan yasa gaba daya Salamatu ta daina zuwa makaranta abinda yasa aka gane wannan shiri nasu shi ne. Akwai lokacin da shugabar makarantar tasu ta ga kwata-kwata Salamatu ta bar zuwa makaranta sai ta tashi da kamta ta zo gidan. Ta ko yi sa'a Alhaji yana nan. 11 Ta kwashe dalilin zuwan ta tsaf ta sanar dashi. A wannan rana ya yi matukar mamaki, kuma Salamatu ta daku. Haka dai aka ci gaba da wannan abu kuma kullum furucin Alhaji Salisu shi ne aure tsakanin 'yarsa Salamatu da Khalifa sai dai idan ba shi da rai. To daga karshe dai na gaya ma mutuwar ya yi kuma an daura auren. To yanzu mecece ribar Alhaji Salisu a wannan al'amari? Ka ga lallai ya kamata ka yi gaggawar ajiye wannan tunani naka ka bar wannan'ya da masoyinta" Ta yi shiru tana maida numfashi Alhaji Masa'ud ya numfasa gami da jinjina kai amma fa ba wai ya yi hakan bane saboda tsoro da labarin da Gwaggo ta-bashi ba ne, a'a ya yi hakan ne da ya tuno da matsanancinyar gabar da ke tsakaninsa da Alhaji Gambo da kuma gamsuwa da kalaman kin amincewa da zuciyarsa ke rada masa. "Ban ji ka ce komai ba ko baka yarda da abin da na gaya maka ba?" Gwaggo ta ce cikin fushi. "Na ji Gwaggo amma zan duba al'amarin." Ya dubi agogonsa "Yanzu ana jirana a wajen aiki." Gwaggo ta kada kai "A to na dai gaya maka wannan ba tsari bane ka sake tunani. Tashi ka je." Ya mike jiki a sanyaye ya nufi daki. Zuciyarsa makare da tunaninnika iri-iri. Asama'u dake kwance akan gadonta ta yi juyi, 12 tsawon sa'a biyu ta dauka a kwance tana tunani tun sanda Gwago ta bar gidan. Tsawon wannan lokaci abu guda take tunawa shi ne masoyinta Aminu. Ko da yake ta dan samu sa'ida daga lokacin da Gwaggo ta zo gidan zuwa yanzu saboda furucin da ta ji mahaifinta ya yi na cewa zai duba yiwuwar aurenta da Aminu duk da cewa ta san ba abu ne tabbatacce mahaifinta ya amince da hakan ba. Ta tashi zaung a hankali ta zuba tagumi hannu bibbiyu. "Wai menene farkon wannan gaba da ke tsakanin mahaifinta da mahaifin Aminu alhali suna unguwa guda kuma ma gida yana kallon gida. Ko irin abin da ya faru tsakanin Alhaji rabo da Alhaji Salisu ne ya faru da su?" Wannan ita ce tambayar da zuciyarta ke yawaitą yi mata tun data shigo dakin. "Lallai akwai bukatar na sani." Zuciyarta ta ci gaba da ambata. Kamar amsa sai ta ji an bankado kofar dakin babu ko sallama. Hadiza ce, ranta a 6acc ta ce. "Ke ki zo in ji Babanki." Asama'u ta ji gabanta ya yi mummunar faduwa, kafin ta amsa Hadiza ta yi waje. Ta tashi jikinta a sanyaye ta nufi dakin mahaifin nata. A zaune ta same shi kan kujcra fuskarshi a turbune. Bayan ta samu waje ta zauna sai ta ce cikin taushin murva. "Baba gani." 13 Ya yi kamar bai jiba sai da aka samu kamar minti biyar ya dubcta. "Asama'u me yasa sam-sam ba kya jin abinda nake fada miki, kin raina ni ko?" Da sauri ta girgiza kai. "To menene nufin ki idan ba raini ba?" Shiru bata yi magana ba. A hasale ya kuma cewa "Wato don na ce bana son ganinki da wannan yaron sai ki ka je kika fadawa Gwagg?" san..." "Wallahi ba ni na fada mata ba Baba ni ban ma "Ke rufa min baki shashasha, ina magana kina magana." Ya katseta cikin tsawa. Ya nuna ta da yatsa. "Ya kamata ki sani daga yau sai yau kamar yadda na sanar dake kar na kuma ganinki da Aminu idan ba haka ba kuma wallahi sai na babballaki. Kuma ina tabbatar miki ina nan akan bakana ta kin amincewa da hada zuri'a ta da Alhaji Gambo don kar ki ga na cewa Gwaggo zan duba. Dana hada zuri'a ta da wannan gidan gwanda ace na mutu..."Ya yi shiru yana huci "Tashi ki bani waje munafuka." Ta mike simi-simi ta fice daga dakin ta nufi nata dakin rai a bacc. Tana shiga ta zauna akan kujera ta shiga tunanin wanda ake kokarin rabata dashi. "To wai me ye dalili tana zaman-zamanta da masoyinta za a rabata da shi?" Cewar zuciyarta. Ta mike a hankali sakamakon wani tunani da ya darsu a zuciyara ta nufi tagar dakinta, cikin sa'a kuwa 14 sai ta hango abin da zuciyar tata ke marari, Aminu. Yana sanye da wando da riga na shudiyar shadda kansa dauke da hula damanga, kafafunsa saye cikin bakin takalmin fata, sau ciki. Ta kura masa idanu ko kiftawa bata yi cikin fatan ganin sun hada idanu. Kamar an nuna masa ita sai Aminu ya kai dubansa ga tagogin saman benen gdian su Asama'un. Suna hada idanu suka yiwa juna murmushi, duk da bacin rai da kuncin da Asama'u ke ciki hakan bai hanata dagawa masoyinta hannu ba. Ya daga mata hannu shima cikin tsananin farin ciki. Nan da nan sai suka shiga zance da hannu kamar kurame, sun kai tsawon mintina uku a haka, daga karshe suka yanke da-yamma za su hadu. Ya jima a inda suka ce za su hadu yana jiranta, can sai ya hangota ta taho. Tana sanye cikin leshi kore mai cin baki fari. Tun daga nesa ta soma sakar masa murmushi. "Sannu da zuwa." Ya ce da ita tun kafin ta yi magana bayan ta isa gareshi. Ta yi murmushi, ta 'dubi fuskar kyakkyawan agogon da ke daure a hannunta. " "Ka yi hakuri na bata maka lokaci ko?" Ya girgiza kai "Kin 6ata wa kanki dai." "Saboda me?" Ta bukata. 15 1. "Saboda masoyinki kika 6atawa." Ta yi dariya "To na ba kaina hakuri kenan?" "Shi ne abin da ya dace." Suka yi dariya. Sannu a hankali ta zauna kusa dashi. "Kana ta tunanin ko ba zan zo ba ko?" Ya yi dariya "Kamar kin sani ai na dauka ba ki samu sarari ba." Ta kalleshi "Kamar ya ya ban samu sarari bа?" - "Wajen samun damar fitowa daga gida." Ya amsa kai tsaye. Ta dan yi fari da idanunta "A haba, ai kaima ka san ko ban sami dama ba saj na zo." "Ta ya ya ba ki samu dama ba kuma ki zo?" Ta dukar da kai "Ta zuciyata domin kullum tana tare da tunaninka." Aminu ya yi sassanyar ajiyar zuciya saboda jin dadin abinda ta fada. Ya dubeta cikin raha ya ce "To tunda kullum ina tare da ke a zuciya, kin ga ba sai mun hadu ba kenan a zahiri." Ta harareshi "Ai kuma zuciyar ba zata taba samun sa'ida ba har sai ta mallaki wanda ta ke kauna, mallakar da za su zama tsintsiya madauri guda." Ya cije lébc "Asama'u wannan jan aiki ne babba a gabanmu." dubanta. "Me ya sa ka ce haka?" Ta bukata. "Saboda iyayenmu ba sa so." Ya amsa yana Asama'u ta yi jim na dan lokaci kana ta dago kai 16 ta dubeshi. "Ka kwantar da hankalinka masoyina, da yardar Allah sai mun yi rinjayc akan iyayenmu domin Ubangiji ya ga zuciyar mu aure muke son yi don raya sunnar manzonsa, kai dai kawai ka ci gaba da yi mana addu'a a duk lokacin da ka yi sallah." Ta tsagaita Wannan kira da karin kwarin gwiwa shi ne abin da Asama'u kullum ke yi ga Aminu domin kwantar masa da hankali, duk da dai ta san akwai babban aiki a gabansu, saboda rashin jituwar iyayensu. Duk da barazanar iyayc da masoyan ke fuskanta haka soyayyar Asama'u da Aminu ta ci gaba da gudana, kullum yammaci sai ta saci jiki ta tafi inda suka saba haduwa da masoyinta su yi ta hirar su. Kasancewar kiwon mutum akc ba na dabba ba sai ya zamana an fara fahimtar wannan shiri na masoyan musamman ma Asama'u da kullum take fakewa da cewa zata je kai ziyara wajen kawayenta. Kamar yadda ta saba yau ma ta tsantsara kwalliya ta fito ta nufi dakin mahaifiyarta. "Momi zani gidansu Nafisa." Ta ce da mahaifiyarta, bayan ta gaida ita. Hadiza ta dubeta da kyau "Wacce Nafisa?" "Nafisa Yahaya... wata 'yar ajin mu ce." Ta amsa har yanzu kai a duke. Hadiza ta nisa. Bata gamsu sosai da abin da 'yar 17 tata ta fada ba, to amma saboda ba sosai ta fiye son takura mata ba sai ta ce. "To ki yi sauri ki dawo kafin babanki ya dawo, kin ga ko jiya ma da ya dawo ba kya nan ya yi fada....kin ji ko?" Ta gyada kai "To momi." Ta mike ta nufi waje zuciyarta fari kal, saboda murnar za ta ga masoyinta. Kamar kullum yana nan zaune yana jiranta. Da yake kansa a duke yake bai ga tahowarta ba sai da ta kusa zuwa dab da shi sannan ya ji kamshin daddadan turarenta ya bugi hancinsa. Ya daga kai da sauri ya dubeta, tana tsayc a gabansa cikin fara'a. "Ranki ya dade amaryar Aminu:" Ta yi fari gami da lumshe idanu "Da wa kuke musu a raba ku, domin abin da ka fada babu kuskure?" Ya yi murmushi "Allah sarki Asama'u ai abokan musun manya nc ba za ki iya rabawa ba sai dai mu bar wa Allah." Ta yi murmushi gami da nisawa, ta san abin da ya fada hakan yake. Ta tsugunna gabansa a hankali, suka zubawa juna idanu, Kowanne zuciyarsa tunbatse da tsantsar kauna. Ya dan muskuta kadan yasa hankici ya share mata wajen zama kusa da shi sannan ya duebata. "Bismillah mana?" Bata yi musu ba ta mike ta zauna a kusa dashi. "Asama'u dama yau ina son yin' wala shawara dake" Ta dubeshi a nutse "Ta me fa? 18 Ya kauda kansa daga dubanta. "Ina son yin kunar bakin wake ne don shaidawa mahaifina hadafi na na aurenki." Ya yi shiru yana saurarenta. Ta girgiza kai bayan dan gajeren tunani da ta yi. "Aminu anya kuwa lokaci ya yi?" "Saboda me ya sa kika ce haka?" Ta sunkuyar da kai "Saboda tsoron kar a raba mu." Ya yi murmushin karfin hali. "In dai wannan ne tunaninki Asama'u ko mun bari zuwa nan gaba ma abin da zai faru kenan, kinga gwanda yanzu na yi a san abin yi.." Ta dago kai suka hada ido, ta kuma dukar da kanta. "Kar ki damu da wannan, ki kwantar da hankalinki da izinin Allah alheri ne zai biyo baya." Ta nisa "To Allah ya sa." BABI NA BIYU yakkyawan falo ne me kyan fasali, dauke yake Kda kayan alatu na zamani. Zaune akan daya daga cikin kujerun laushin da ke falon Alhaji Gambo ne ke kallon labaran tara. Cikin cikakkiyar nutsuwa Aminu ya yi sallama ya shiga falon. "Ina wuni Baba?" Ya ambata bayan ya samu waje ya zauna. "Lafiya Aminu." Ya amsa yana dubansa "Ina ka shiga dazu ne nake nemanka?" Ya sosa kansa "Wallahi na je wajen Garba ne, kuma..." "Ya isa." Ya katseshi "Dama motar da nake ce ma na saya ma ce aka kawota." Ya sa hannu a aljihu ya 20 A dauko dan mukulli. "Ga shi." karba. Aminu ya tashi da foki ya je ya durkusa ya "An gode Baba....Allah koma ya saka da alhcri." Ya murna. wajen zamansa yana duban makullin cike da Alhaji Gambo ya dubeshi. "To yanzu kuma saura hakki guda naka a kaina wanda ya kamata na sauke, shi ne ka némo wadda kake so na aura ma, idan kuma kana da ita yanzu ma kana iya fada ko 'yar wace ce." Aminu ya ji farin ciki ya rufe shi, dama yana daga ckin nufinsa sanar da mahaifin nasa a yanzu koda bai bashi wannan damar ba, balle da yanzu ya ba shi. nisa. Shiru ya dan tsawaita tsakaninsu, can Aminu ya "Baba dama na so na zo da wannan maganar to amma..." Ya yi shiru. Alhaji Gambo ya gyada kai cikin murna "Yauwa ko kai fa. Wace ce kuma 'yar wane ne?" Ya bukata cikin zakuwa. Aminu ya daga kai ya dubi mahaifinsa ga mamakinsa sai ya ji zuciyarsa ta shiga harbawa amma sai ya daure ya ce. "Baba sunanta Asama'u....kuma 'yar wajen Alhaji Masa'ud ce, makwabcinka." Ya dukar da kai. "Alhaji Masa'ud....Alhaji Masa'ud?" Alhaji Gambo ya maimaita cikin kokarin son Karin bayani. 21 Ya kuma duban mahaifinsa "Ta nan gidan da yake kallon namu." Ya yi masa gwari-gwari. Yanzu ya gane wanda yake nufi, nan da nan sai ya ji numfahinsa na kokarin daukewa saboda tsabar takaici, cikin rudani ya ce. "Haba Aminu, ai ruwa ba sa'an kwando bane, ko kadan wannan yarinya ba ta dace da kai ba, saboda haka ba ma na son na ji ka sake ambatar sunan wannan yarinya a gidan nan." Aminu ya cira kai da sauri ya dubi mahaifinsa. "To Baba ai ita kadai ce wadda nake so....?" Ya daga masa hannu (alamar ya saurara) "Aminu kar ka kuskura ka yaudari kanka domin ka san abinda ba zai taba yiwuwa bane ace zuri'ata ta nemi zuri'ar gidan makiyina....sam! -Wannan ba za ta sabu ba." Aminu ya yi yunkuri da nufin sake cewa wani abu sai mahaifinsa ya dakatar dashi ya ce cikin tsawa. "Kar ka kuma cewa da ni komai idan ka nemo wata yarinyar daban ba wannan ba zan iya tsaya maka tun daga naira daya har zuwa naira dubu dari biyar amma idan wannan 'yar matsiyatan ce ba zan taba aminta ba....tashi ka tafi." Bashi da abin cewa don haka ya mike jiki a sanyayc ya fice cike da takaici da kunar rai. A wannan rana kusan yadda ya ga rana haka ya ga dare cike da tunanin yadda zai 6ullowa wannan al'amari don mallakar abar kaunarsa. 22 Gaban Asama'u ya yi mummunar bugawa sa'ar da ta tsinkayi inda suka saba haduwa da masoyinta ta hango baya nan. ranta. "Na shiga uku....yau ko bai zo bane?" Та се a Ta yi 'yan waige-waiganta bayan ta isa wajen bashi ba dalilinsa, sai wata mota kirar HONDA PRELUDE tsaye a gefe. Ta kai kusan minti biyu a haka tana ta dube-dube, tana kokarin juyawa ne sai ta yi an yi hon daga cikin motar nan, tana waigo wa taga Aminunta ya fito daga cikin motąr

Chapter 1 of 3