Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
mu zai iya haifar mana da matsala." Та sunkuyar da kai. Ya vi ajiyar zuciya. Shi bai ga, wata manufa ta gudu ba tunda idan sun gudu ba a mstaayin ma'aurata ba ya ya za su yi? "Gaskiya Asama'u mu hakura zuwa wayewar gari ni na san yadda zan yi za mu samu nasara in Allah ya so." Ta girgiza kai. Abin da ta tuna shi ne idan Aminu ya iva da ivayensa ya zai yi da nata iyayen? Ba zai iya hana su aiwatar da abin da suke shirin yi ba. "Gaskiya Aminu babu dabara ga zaman mu, amma idan ka ce haka ba komai ni zan tafi..." "Ina za ki?" Y'a katseta. "Duk inda ta kama." Ta share hawayen dake idanunta "Na gode Amin ne san yanzu ka nuna min 46 kauna." Shisshikar kukan da ke barazana a gareta ta katse ta. ita. Ya san ba'a ta yi masa don haka sai ya je kusa da "Asama'u.....na rantse da Allah ina matukar kaunarki, kar ki ga na ki amincewa da wannan gudu namu ki yi tsammanin ba na sonki ne, sam ba haka bane na dai yi ne kawai domin na tseratar da mu daga cikin fushin Ubangiji da kuma gujewa ga afkawa ga fushin iyayenmu." Ya yi shiru "Asama'u mu yi hakuri mu zauna, ni na ce miki na san abin da zan yi." Ta girgiza kanta "Ba hali." Ta ce a zuciyarta. Amma da ta yi wani tunani sai ta ce dashi. "Ba komai Aminu na amince zan koma gida." Ba wani abu ta tuna ba da ya wuce cewa idan ta bari suka ci gaba da jayayya da Aminu gari sai ya waye mata. Ita fa ta yi damara kuma ta yi azamar barin gida kuma babu gudu babu ja da baya. ce. Suka fito da nufin ya rakata har kofar gida,sai ta "Aminu nan ma ya isa, ka san watakila yanzu baba ya tashi saboda zuwa masallaci sallar Asuba kar ya ganmu tare." Ya gyada kai cikin gamsuwa. "To sai da safen." Ya koma ciki. Ta yi ajiyar zuciya cikin murnar ganin ta yi nasarar kubcewa tarnakin rashin gudun da Aminu ke kokarin saka mata. Alhaji Masa'ud ya saki baki cikin mamaki sa'ar da ya fito falo ya ga kofar falon a bude. Ya riga ya san babu mai budewa in dai ba shi ba. To waye ya bude. Ya isa ga kofar ya leka kamar me tunanin zai ga wanda ya bude kofar amma babu abin da kwayar idanunsa ta dauko masa sai irin duhun da ke cikė da barandar gidan. A hankali cikin dimbin mamaki ya jawo kofar ya rufe ya nufi saman benen dakin matarsa Hadiza. Yana hawa ya iske kofar dakin Asama'u a bude, bai tsaya yin wata-wataba ya kutsa kai cikin dakin, ba kowa a ciki. "Asama'u! Asama'u!! Asama'u!!!" Shiru ba amsa. Ya fito da sauri ya isa dakin Hadiza, ga mamakinsa sai ya tarar a kulle. Ya bubbuga kofar, sai da ya buga kamar sau uku sannan ta bude. Alamun barci tattare a fuskarta. Ta murtsuke idnaunta "Alhaji lafiya?" "Ina Asama'u?" Ya amsa mata da tambaya. "Asama'u?" Ta nanata. "Ba ta nan ne?" Ya gyada kai "Ban gànta a daki ba kuma bata nan, kofar falon ma a bude take." Hadiza ta dafe kirji "To tana ina.....kuma wa ya bude?" "Ban sani ba." Ya amsa a tsorace. Ta yiwo waje da sauri, ya bi ta a baya kamar jela suka koma dakin Asama'u. Trbbas bata nan. "To ina ta yi?" Hadiza ta bukata sa'ar da ta isa ga gadon ta daga kayan na Asama'u wanda ta sauya. Ta dubi Alhaji Masa'ud. "Alhaji waman kayan dake jikinta ne jlya." Ta kai dubanta ga sif din ajiyar kaya na Asama'u ganinsabude. Da sauri ta isa ga sif din,kamar an yi kiran sunanta ta baya ta waigo ta dubi maigidanta ta ce. bude "Sauya kayanta ta yi Alhaji kuma ina ganin ita ta gidan nan ta fita." Alhaji ya yi ajiyar zuciya. Ya gyada kai "Ba shakka." "To ina ta je?" Hadiza ta bukata. Ya wara hannu alamar bai sani ba. Hadiza ta kuma ficewa daga dakin, bai yi kasa a gwiwa ba ya bi ta har bakin kofar falon. Ta ja ta tsaya. "Bana jin ta bar gidan nan." "Saboda me kika ce haka, kuma tana ina? Nuna min ita." Ya ce a harzuke. Ta girgiza kai "To ina maigadi?" Lallai tana da gaskiya sai yanzu ma shima ya tuna da maigadin. Taбbas idan zata fita sai maigadi ya sani. Wannan tunani yasa kai tsaye ya nufi babbar kofar gidan, matarsa Hadiza ta dafa masa baya. Har yanzu maigadin barci yake ta shararawa. Alhaji Masa'ud ya mari kafarsa da tafin hannu. Firgigit! Maigadi Uba ya tashi. Cikin magagin barci yan soma 'ya soshe-soshe. "Kai! Uba ina Asama'u" Alhaji Masa'ud ya bukata cikin tsawa. Uba maigadi ya wartsake saboda fahimtar cewa Alhaji ne a kansa. Da sauri ya mikc. "Asama'u.....ban ganta ba." Ya ce a tsorace. "To tana ina?" A wannan karon Hadiza ce ta tambaya. "Wallahi Hajiya ban ganta ba..." "To kai kana ina?" Ta kuma bukata. U "Ina nan." Cikin fushi Alhaji ya daka masa tsawa ya ce. "Kana nan kana ta faman barci ko?" Ya sosa habarsa "Ba haka bane Alhaji..." "To menene? Yanzu wannan kofar a rufe take?" Alhaji Masa'ud ya nuna babbar kofar ganin ta a bude. Uba ya kai dubansa kofar. Babu shakka a bude takc. Ya tafi da sauri ya dafa kofar sai ta wangamc. Lallai ta tabbata Asama'u ta gudu. Alhaji Masa'ud ya ji kansa ya dau zafi. "Yanzu ina zai samu Asama'u kuma ya ya zai yi da mutanen da ya gayyato daurin aure yau?" Ya ji zuciyarsa ta kuma kunci da ya tuno da Aminu. Amsar a ina 'yar sa take yanzu ya samu. Kawai tana wajen Aminu. * Aminu ya fito daga wanka, tawul daukc a kafadarsa. A gurguje ya sanya kayansa kana ya yi waje kansa ko hula babu. Dakin mahaifinsa ya nufa. Da sallama ya shiga. Mahaifinsa da ke tsaye a tsakiyar falon ya amsa. "Aminu lafiya kuwa?" Ya bukata da gaggawa saboda karantar abu biyu da ya yi. Na farko dai ya san dan nasa bai saba zuwa gaida shi da sassafc haka bha. Na biyu kuma ya ga ransa a bace. zauna. Ya samu wajc ya zauna, shima Alhaji Gambo ya "Aminu ya ya dai?" Ya kuma bukata. Ya daga kai ya dubi mahaifinsa muryaa tausashe 56 ya ce. "Baba na zo neman wata alfarma ne." "Alfarma?" Ya nanata "Ta me fa?" "Baba na dai dawo ne ina neman alfarmar ka amince da aurena da Asama'u." Ya murtuke fuska. "Kai Aminu wai me yasa kake son mayar dani karamin yaro ne? Na fada maka tsakaninka da mutanen nan babu ko ga maciji amma kai...." Ya yi shiru cikin cije lebe. Aminu kuma marairaicewa ya yi. "Na san da haka baba amma ni dai yau alfarma nake nema, ka ceto rayuwata Baba idan ba haka ba zan halaka. Yau ake so a daura mata aure da wani wanda bata Kauna." Ya yi shiru. Alhaji Gambo ya yi matukar farin cikin jin cewa za a daura auren Asama'u da wani yau. Ya girgiza kai. "Ba zan iya taimakonka ba, a cikin irin wannan yanayin. domin da ka san abinda ke tsakanina da mahaifin wannan yarinya da kai ma baka neme ta ba." "Ko menene a tsakaninku zan iya nemanta baba." Ya cè a cikin zuciyarsa, amma a fili ya ce. "Ni dai yau alfarma na ke nema gareka baba ka je ka roki Alhaji ya aura min ita." Ya daka masa tsawa "Na ce ma ba zai yiwu ba ka hakura kawai." Aminu ya sunkuyar da kansa da ya tuna damar da suka samu jiya amma ya ki yarda su gudu. Yanzu ya yi mata Bakiyar da ba ruwa kenan? "Nan da nan sai ya shiga tunanin hanyar da zai bi 51 don sanin irin wannan gaba dake tsakanin mahaifinsa da mahaifin Asama'u. Ya dubi mahaifinsa da zummar tuntufarsa akan sanin makasudin wannan gaba, sai Alhaji ya mike. "Ka gama...? Idan ka gama to ka tashi ka tafi kana batamin lokači, ka ji ko?". Ba zai iya musu ba, don haka sai ya mike ya nufi waje zuciyarsa na saka masa ya tafi gidansu Asama'u. Ya durfafi kofar idan su Asama'u, kai tsaye ya wuce in da maigadi yake. "Sannu Malam Uba." "Yauwa sannunka dai......" Uba va amsa cike da mamakin ganin Aminu, mutumin da aka ce ya dauke Asama'u. Cikin mamaki ya kara da cewa. ya ce. "Aminu ina Asama'u?" Ya dubeshi a fusace. "Ina na zo nema, tana ciki?" Maigadi Uba ya kalli Aminu sama da kasa a raine "Ban gane abin da kake nufi ba. Ina Asama....?" "Na ce ma ita na zo nema." "To ai kai zamu tambaya inda take domin ta fice da daddare an ce kuma ana tsammanin tana wajenka." Gabansa ne ya fara faduwa kafin fuskarsa ta sauya, tabbas yanzu ya san Asama'u guduwa ta vi. To amma ina labbaci? Fuska a yakune ya dubi maigadi. "Ban gane abinda kake nufi ba, kana nufin yanzu Asama'un ba a ganta ba?" "Ka fini sani." Uba ya ce masa cikin gadara, domin a tunaninsa Aminu na kokarin raina masa wayo ne bavan an ce Asamalu tana wajensa. Kume dole ne ya yi hakan 52 tunda an ce sakacinsa ne ya ba Asama'u damar guduwa. Aminu ya dukar da kai cikin tsananin damuwa. "Gaskiya Aminu babu dabara ga zaman mu, amma idan ka ce haka ba komai ni zan tafi." "Ina za ki?" "Duk inda ta kama." Ya tuno abin da ya faru tsakaninsa da Asama'u a daren yau. Yanzu ya yarda a irin furucin da ya fita daga bakin Asama'u ba shakka za ta iya guduwa. "To amma ina zata?" Shi ne abinda yanzu zuciyarsa ke son sani. Lallai yana matukar son Asama'u domin yanzu da yake a tsaye zazzabine ke yunkurin lullubeshi. Bai damu da hakan ba, yanzu tunaninsa. Ina zai samu Asama'u? "Duk inda take sai na nemota, don ba zan iya rayuwa babu ita ba..." Zuciyarsa ta ambata. Cikin fushi ya juya ya nufi gida ya bar maigadi Uba anan. Jikinsa a sanyaye ya shiga dakinsa kai tsaye ya nufi gadonsa ba tarc da ya tube takalmansa ba. Ya fada a kai rub da ciki. Cikin kunar zuciya va ke furta. "Asama'u ina kika tafi ne? Ya ya kika yi min haka? Me ya sa ba ki jirani ba? Kina sona kuw...." Tunaninsa va katse sa'ar da ya tuna lokacin da Asama'u'tá zo ta nemi su tafi ya ce bai yarda ba. "Ba laifinki ba ne...ba laifinki ba ne....Asama'n" Ya shiga furtawa cikin sassanyar murvar nadamaa 53 A hankali ya birkice daga rub da cikin da ya yi zuwa riginginc. Ya zuba wa silin ido ko kiftawa ba ya yi. Sannu a hankali sai wani tunani ya darsu a zuciyarsa tunanin daya fatattaki zargin da ya ke yiwa kan sa da wanda yake yiwa masoyiyarsa. Tunanin kafiyar mahaifansu, ba shakka ita ce ta kawo faruwar wannan guduwa ta Asama'u kuma ba shakka ita ce ke yunkurin ingiza keyarsa shima ga barin garin. Ya yi nannauyar ajiyar zuciya, a lokaci guda fwalla mai dumin gaske, ta soma gangarowa daga cikin idanunsa tana bi ta kumatunsa izuwa matashin kan da ya dora kansa a kai. Lallai yana da bukatar sanin wannan mummunar gaba ta iyayensu da makasudinta, wadda har take barazanar kawar da rayuka biyu daga doron kasa. "Baba me ya hada ka da mahaifin Asama'u." Ya shiga ambata a fili kamar wanda ke magana da mahaifin nasa. Bai samu amsa ba, ba ya kuma tunanin samu, kuma koda zai samu ma baya bukatar yanzu. Babban abin da yake bukata a yanzu wanda ya fi damunsa shi ne sanin inda masoyiyarsa ta tafi. "Oh! Yanzu ko a wannc hali Asama'u ta ke, dadi ko wuya, oho?" Zuciyarsa ce ta saka masa. Ta ke sai ya ji kamar an tsikara masa allura. Ya yi zumbur ya tashi zaune, kai tsaye ya mike tsaye, cikin kuzari kamar ba abin da ke damunsa ya nufi babbar jakarsa da ke dauke da kayansa, ya bude. Ya soma birkice kayan da yake ciki. Ba wani abu yake nema ba kudi vake nema. Ya daukosu sababbi fil da su Ya mayar da jakar ya 54 rufe, sannan ya tashi ya nufi teburin littattafansa ya dauki makullin motar sa da gaggawa ya yi waje, har ya nufi dakin mahaifinsa sai ya kuma komawa ya dauki hoton Asama'u da ke ajiye cikin dubban hotunan dake cikin album, ya kuma ficewa. A daidai lokacin ne motar 'yan sanda cike da su ta ja ta tsaya agaban kofar gidansu Aminu, baro-baro rubuce a jikin motar,ANTI CRIME. 'Yan sandan suka fara diddirowa hannunsu rike da bindigogi kamar sa ci babu. Alhaji Masa'ud dake bin su cikin tashi motar shima ya bude ya fito. "Nan ne gidan." Ya ce cikin fushi. Daya daga cikin 'yan sandan ya isa kofar gidan ya tsaya, kamar an wurgoshi ya fito. "Yauwa! shi ne wannan!" Alhaji Masa'ud ya ce a harzuke yana nuna Aminu da ya fito cikin sauri. Kamar kura taga kare 'yan sandan suka nufi Aminu kowanne na gyara zaman bindigar a hannunsa. dashi. "Malam you are under arest." Wani sajen ya ce "Menene ya faru?" Aminu ya bukata a rikice ganin wani dan baki kakkauran kurtun fan sanda na kokarin dadumarsa. "Za ka ci ubanka ne...sai an je can kasan abinda ka yi munafuki...6arawon mata." Alhaji Masa'ud ya cс а fusace. A daidai lokacin ne Alhaji Gambo mahaifin Aminu ya fito. Dumu-dumu ya ga dansa Aminu a hannun yan sanda suna jan sa,Alhaji Masa'ud babban makiyinsa na ta kwarara masa zagi...! 55 Zan ci gaba a na biyu Ya ya za a yi tsakanin Alhaji Gambo da Alhaji Masa'ud babban makiyinsa,Alhaji Gambo zai bari a tafi da dansa kuwa? A ina Asama'u take,wacce rayuwa ta kasance a ciki bayan barin ta gida? Za ta dawo kuwa? Ko za a nemo ta ne? Idan ta samu waye zai aureta tsakanin masoyinta na hakika Aminu da dan uwanta Yusif? Ku biyo 'yar uwarku Zainab Lawal Brigade 08029460293 Don samun amsar wadannan tambayoyi.... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3