rura wuta ba.
Idan bata karfafeshi ba yau, waye zai zama karfinsa???
Nenne me zata ce in taji? Banda Allah ya kara? Ta dade tana cewa dasu bata kin Hasinah, amma tsintacciyar mage bata mage. Shi garin banza duk kyawunsa a farau-farau din banza ne.
Abin nufi wato mara tsarkin asali da kyawun nasaba ba duka keda tsarki ba. Shiyasa har gobe ba’a yi auren ba, ake ta jan lokaci. Don neman yarda da albarkar Nenne.
Ashe da rabon zancen Nenne zai tabbata gaskiya tun tana raye kuma tun gabanin cikar alkawarin dake tsakaninshi da Haseenah?
Taiwo ta kara fada a fili cikin girgiza kai “lallai tsintacciyar mage bata mage”. Kuma “Garin banza a farau-farau din banza yake karewa!”.
A tunanin ta Hasinah zata dubi maraicinta da daga darajarta da Abdulrasheed yayi a tsakanin mata tsararrakinta, musamman fiddota da yayi daga gidan marayu na garin Ambursa ya dauketa cikin mutunci ya kaiwa ‘yar uwarsa, ta yi sakandire ta ‘ya’yan gata, kafin daga nan ya kawota kasar Japan, yasa a makaranta, cikin ire-iren marayun da yake ponsoring scholarship dinsu a kasashen waje ba wanda ya kawo jikinsa wato inda yake zaune sai Haseenah, a tunaninta ko wannan ya isa yasa Haseenah ta tsayar da soyayyarta da sha’awarta da hankalinta akan sa shikadai, ta zame masa matar rufin asiri, ba kamar sauran ‘yammatan da ke haukar son shi don wasu kyale-kyale nasa ba, kamar kasancewarsa “basarake” kuma “celebrity”. Sannan gashi “Handsome Yoruba Demon” da shaidanun matan Africa dake kasashen ketare ke rububi don son sheke aya dashi kawai ba.
Ta dauka Hasinah zata barranta kanta daga masu neman soyayya ta watsewa bayan shigarta Jami’a, ta dauka Haseenah zata zama mai kamewa data iyawa maraicinta, ta dauka zata tsaya ga matsayin da Allah ya bata na fiancée din da Abdulrasheed ya yarda zai aura da zuciya daya cikin dimbin matan dake son shi da suka fita gata da kyawun nasaba, ko don kasancewarta musulma kuma bahaushiya, ashe kame kai ba daga yare ko kabila yake ba, saboda kyawun surar dan uwanta ma kadai ya ishi duk wata mace mai lafiya da dogon buri akan samun miji na nunawa sa’a tinkahon duk da zata yi a kan kowanne da namiji.
Taiwo ta zabi su bar maganar nan a tsakaninsu. Suka binneta a ranar, ya zama wani sirri ne da ko iyayensu bazasu iya fadawa ba.
Taji ta tsani Hasinah daga yau, da shima Toks din, wato dan uwansu (Tokumbo) fiye ma da yadda Abdulrasheed ke ikirarin ya tsanesu. Bata taba tsammanin akwai dan akuya cikin zuri’rsu ba sai yau.
Shi ya san cewa (he has someone on his corner), all the time he need (a kowanne lokaci ya bukata), wata wadda zai iya kira (his own person) wato tashi, a duk sanda ya bida, wadda ba kowa bace sai ‘yar uwar tagwaitakarsa “Dr. Murjanatu-Taiwo Akanni”. Kafadar da zai jingina akai yayi kuka ko dariya a lokuta na bacin rai irin wadannan.
***** **** ****
WAIWAYE ADON TAFIYA (2)
(AMBURSA ORPHANAGE)
A
mbursa karamin gari ne a jihar Birnin Kebbi. Prince ya saba da irin wadannan tafiye-tafiyen cikin garuruwa da kauyukan Arewa a duk lokacin da yazo kasarshi ta haihuwa, kasancewar rayuwarshi tafi yawa a yankin Tokyo ta (Japan).
Dabi’arsa ce kaunar marayu, don haka duk inda ya samu labarin akwai gidan marayu ya kan ziyarta, komai nisan garin daga inda yake, baya kasa a gwiwa zai je don kai tallafi. Idan yaje din kuma sai ya zaga ciki ya gansu, ya gaisa dasu, ya shafa kawunnansu, yana mai godewa Allah cikin zuciyarsa dashi yayi masa ni’imar iyaye, masu kykkyawan asali daga tsatso mai albarka, iyayen ma jajirtattu irin ‘Nenne’ da ‘Dade’ da ba duk duniya ake da irin su ba.
Shi ba attajiri bane a lokacin dalibi ne, amma yanada attajirar zuciya, ‘philanthrophy’ musamman ga marayu a cikin jininsu ne na iyaye da kakanni.
Kusan zamu iya cewa ya gaji wannan (positive attitude) din na son marayu da son inganta rayuwarsu ne daga Kakansa. Sarki Akanni mai ran karfe. A zuciyarsa yana tausayin maraya a duk inda ya ganshi, yana kuma jin maraicin da suke ji a ransa, ba don shi din maraya bane.
Yana yawan kwatantawa a ransa inda ace shine su, yake rayuwar da suke yi a kange, babu Nenne da Dade a gefensa, a samansa da kasansa, ko yaya rayuwa zata kasance masa?
Yana kan hanyarsa ta isa gidan marayun Ambursa ne daga Birni Kebbi, inda yaje halartar daurin auren abokin karatunsa Bello Dasuki. Bello D. abokinsa ne tuntuni da sukayi karatun sakandire tare a Japan a lokacin Baban Bello Jakada ne acan, dan asalin Birnin Kebbi. Don haka ne bai ji kiwar yin tattaki tun daga Lagos ya halarci daurin aurensa ba.
Hira ce tayi hira tsakanin shi da Bello Dasuki bayan kammala reception na daurin aure, Dasukin na tsokanarsa da UBAN MARAYU! Inda sabo ya saba da wannan sunan daga bakin Dasukin, tun daga lokacin da ya nemi rakiyarsa zuwa wani gidan marayu a Bauchi. Dasuki yace dashi cikin hira ai kwanannan suma an bude musu sabon gidan marayu a garin iyayensa wato Ambursa.
Zancen ya wuce, kamar bai ji ba ma, suka shiga wata hirar ta abubuwan da suka shafesu na POLO.
Har sukayi sallama da Bello Dasuki zai wuce Airport, inda daga nan zai tashi zuwa gida Lagos, bai gaya masa zai ziyarci gidan marayun nan da ya bashi labari ba. Kawai tunaninsa na alkhairi ya gaya masa akwai bukatar yaje sabon gidan marayunnan ya gani, domin akwai wasu kudade tare dashi masu dan dama da yayi niyyar kaiwa gidan marayu na jihar Gombe, kuma ya tuna bazai samu zuwa Gombe ganin Kakarsa Oummana kafin ya wuce Japan ba lokaci zaya kure masa, tunda kuma daga Birnin Kebbin zuwa Ambursa babu nisa bari kawai ya karasa can, ya basu tallafin sannan su wuce Airport din Sokoto.
Umarni yayiwa direban Bello Dasuki wanda ya dauko shi a motar Dasukin, da ya karkata kan motar ya juya dashi zuwa Ambursa. Ya ce dashi ko basu san wajen ba suyi ta tambaya.
Don haka suka tasarma kauyen Ambursa, kuma koda suka shiga garin basu sha wahalar tambaya ba kasancewarsa kwararren direba kuma dan gari, suka samu sabon gidan marayun, wanda ba’a dade da kafashi a jihar Kebbi ba, sakamakon yawaitar tsintar ‘ya’ya da walagigin marayu a jihar. A saman gidan manyan rubutu ne da shudiyar kala an rubuta AMBURSA ORPHANAGE.
Shugabar gidan marayun Mrs. Taibat ta karbeshi sosai, domin da gani babu tambaya; irin bakin da suke maraba-lale dasu ne, wato ‘ya’yan manyan kasa masu zuciyar taimako. Wato masu kawo tallafin kudi, ko na karatu ko na suttura ko abinci ga yaran, duk da bata san waye shi ba, amma ko daga yanayin tafiyarsa da kasaitarsa da maganarsa tasan dan manya ne, mai alaqa da sarauta.
Don haka ita da kanta tayi masa jagora har wajen jarirai da ake kulawa dasu da madara, daga nan suka isa gun toddlers, ya gansu, ya shafa kansu harda yi musu wasa sosai kasancewarsa mai son yara.
Sannan ta kaishi bangaren yara mata masu tashen balaga (teens) ‘yan makaranta. Anan idanunsa ya kyallo masa ita, bahaushiya ce, babu ko tantama mai kyau ce sosai, daga duba na farko zaka ga kyawun nata a zahiri, duk ‘yammatan sun lura da shigowar Madam tareda bakon, amma ita yarinyar bata lura ba, suka soma gaishe su duk hankalinta bai kai kansu ba, sai da Madam Taibat tace “Haseenah baki ga baki bane?”
Da sauri yarinyar ta dago jin an ambaci sunanta, yayi mata murmushi ya karaso har gabanta yace “sannu da karatu Haseenah!” ta amsa, ta kuma gaishe shi sai ya karbi littafin hannunta yana dubawa. “Basic Science and Technology” ya ga an rubuta a jiki. (For junior secondary schools). Yarinyar zatayi sa’ar Hakeem dan abokiyar tagwaitakarsa Murjanatu. Don haka kawai babu shawara da Nenne yace bari ya dauketa daga nan ya kaiwa Murja in yaso ta hadata da Hakeem su cigaba da makaranta. Kyawunta ya fisgeshi sosai a matsayinsa na namiji, sannan jan ajinta. Dama ance irin wadannan ‘ya’yan kyau ne dasu.
“Ajinki nawa Haseenah?”
“Bana na gama JSS” (tana magana kai a sama, cikin ko’in kula) da gani ba wadatar tarbiyyah.
“Kinada burin cigaba?”
“Sosai ma kuwa, Enginiya nake so na zama”. Sosai yaji yarinyar ta bashi tausayi ko don yadda take magana kanta tsaye da boldness kamar ba marainiya a gidan marayu ba, don mostly yaran zaka same su basu da karsashi, basu da ko guts na karfin gwiwar kallon mutane ma cikin ido, sabida (inferiority complex) dake dabaibaye dasu, amma ita kar take kallonsa cikin ido, idanunta a tsaitsaye, ko kuma don kasancewar fanninsa kenan wanda ta zaba din a matsayin burinta yasa yaji ta burge shi?
Don haka koda suka koma ofis shida Mrs Taibat yayi abinda bai taba yi ba tunda yake zuwa gidan marayu daban daban, watau yabi duk process din da ake bi na daukar yaro a gidan, na daga cike-ciken takardu ha a karshe yayi (adopting) dinta.
Amma a ransa ya san ba dai ya kaiwa Nenne ba, yayi abunsa kai tsaye without a second thought, saidai ya kaiwa Murjanatu, it ace mai biyewa komai yake so mai kyau ko mara kyau, in yaso ya dinga daukar nauyin karatunta a makarantar kwana, shi dai yaji ransa na son kyakkyawar yarinyar, in yaso in akayi hutu ta zauna gidan Murjanatu har ta isa shiga jami’a ya nema mata admission a fannin Engineering din duk da take so. Ko iya haka aka tsaya ya gina rayuwarta, tunda in ta gama zata iya samun aikin da zai isheta kula da kanta har watarana ta tallafi gidan marayunsu da marayu ‘yan uwanta.
***** ***** ****
Ya damka amanar yarinyar a hannun wato Aunty Murjanatu, ya kuma fara biyan komai na karatunta tareda Hakeem yaron Murja. Lokacin ba’a haifi Kiki ba. Murja ta kaisu makarantar kwana ta British int’l school a garin Lagos. Kasancewar duk abinda dan uwanta ke so bata opposing tana taya shi ne su cimma abinnan.
Ta dade da sanin philanthrophic heart dinshi, na cikin dabi’un shi masu kyau, da suka banbanta shi da sauran matasan zuri’arsu kaf!
Ta yarda ta amince babu mutum mai zuciyar halin girma da daukar girma tun bai girma ba cikin jikokin gidansu kamar Prince, duk wani hali irin na Kakansu Emir Abdulrasheed ya kwashe shi ya bar kowa da sudin kwano. A kafatanin zurri’ar gidansu ba mai kyakkyawar zuciya ta taimakon mara galihu irin ta dan uwanta Prince. Tun daga kan kannen mahaifin su, har zuwa tulin ‘ya’yan da suka haifa, ba wanda baya shan rabar taimakonsa (in one way or the other).
Shi Da daya ne tamkar da goma ga iyayensu. Gidansu ba’a tara ‘ya’ya maza ba, shikadai ne namiji a cikinmata amma ya tarewa iyayensu gurbin misalin yara maza goma!
**** **** ****
Shekaru uku suka zo suka wuce da tarin cigaba ga yarinya Haseenah, bai yi kasa a guiwa ba yana biyan kudin karatunta tare dana Hakeem duk shekara, wadda da aka tashi bata permanent name a makaranta sai ya bata surname da sunan marigayin abokinsa Bello Ambursa, wanda ya rasu gaba kadan da daurin aurensa.
Hakika Prince ya ji mutuwar Bello ba dan kadan ba, kullum ya ga Hasinah sai ya tuno shi har kaunarshi da Bello Ambursa ta shafi Haseenah Ambursa, ko bakomai sanadinsa yaje har inda take ya daukota. Daga kan Bello bai kara yin aboki ba sai Tokumbo wanda dama Cousin dinsa ne da suka taso tare.
Duk sanda ya zo kasar Najeriya zai je wajenta a makaranta suyi ta tadi, in kuma suna hutu ne tana gidan Murjanatu acan yake ganinta har sabo mai tsanani ya gitta a tsakaninsu.
A haka har Haseenah ta gama sakandire, a shekarar data kammala ya samar mata gurbi ya kuma yi sponsoring karatunta a wata jami’a a kasar da yake nasa karatun a lokacin, wato Tokyo.
Wannan ne ya kawo kusanci na kamshin soyayya tsakanin sa da marainiyar da yake riko Haseenah, wanda (in no time) ya rikide musu zuwa soyayya. Har shi da Murjanatu suka yanke shawarar ya aureta kawai, don a zamanta a Japan duk da a hostel take rayuwa, tofa kullum tana like dashi a gidansa fiyeda sanda take hannun Murjanatu da gaisuwa da hirar makaranta kadai ke shiga tsakaninsu, acan kuwa bata san kowa ba sai shi, shiyasa koyaushe take like dashi a gidansa a lokutan da bata da karatu, musamman da idanunta suka fara budewa da maza ta san menene soyayya.
Sun yanke shawarar shawo kan Nenne don ta yarda ya auri Haseenah shida Murjanatu gudun sharrin shaidan ya gifta tsakaninsu, to kullum suna tare a inda ba idon kowa nasu a kansu, yace da Murjanatu yana tsoron watarana ayi abinda ba shikenan ba duk da yana fin karfin zuciyarsa, amma Nenne ta kafe ta ki. Soyayyarsu shi da Hasinah tayi tsananin karfi a lokacin har suka soma sakin layi. Sun buga sun buga da Nenne ta bari ayi auren har lokacin ta ki, don zaman da take yi dasu ma Nenne bata so, tafi so kowanne irin taimako zata yi maka tayi maka shi daga nesa, ba tareda ta dauko ka ta saka cikin zuri’arta ba gudun kada a bata mata tarbiyyarsu. Wannan ne dalilin da yasa suka kawo har lokacin da Hasinah ta shiga mataki na uku a jami’a suna soyayya ba tareda sunyi aure ba.
A irin hakane har ta saba da cousin dinsa mai zuwa gidansa lokaci-lokaci yana sauka a wurinsa wato Adetokumbo Akanni.
Tokumbo a Japan yake harkokin kasuwancinsa, Automobile Business Mogul ne. A daya gefen shi da Murjanatu suna cigaba da fama da Nenne akan dai ta yarda ayi auren haka, amma Nenne tayi tsalle ta dire tace sai a bayan ranta danta zai auri adopted orphan.
A girman nasaba irin tasu, wannan babban abin gori ne a gareta ko a wurin faccaloli, ace duk matan duniya da wadanda ke cikin family din mahaifinsa da nata ace wai Prince ya rasa matar aure sai akan Haseenah da take tsintacciya zai kare kamar wanda uwa tacewa jeka ka gani?
Cikin wannan rikicin suke shi da Nenne har kawo yau, Murjanatu na taya shi fighting gun Nenne don shi Dade dinsu duniya ta shaida mijin tace din Nenne ne, shima da bakinsa yana fada “I obey her decisions because she leave no stone unturned”. Duk hukuncin da Nenne tayi bashi da ja, saboda tsabar yarda da sahihiyar soyayyarsa gareta.
A ganinsu shi da Murjanatu babu wadda zai aura da zata girmama shi, ta kaunace shi saboda Allah irin Haseenah, ga Prince da son girma musamman daga matar da yakeso, kai duk bayeraben basarake akwai tsananin son respect daga mace, a ganinsu ita kadai zata aure shi ba don arzikin su ko don tarin “FAME” dinsa ba (shahararsa a idon duniya).
Duk wata mace da zata aure shi a halin yanzu abubuwan da zata duba kenan (sarauta, kyau, arziki, da shahararsa), sun yi amanna banda ‘yar da ya raina ya ginawa rayuwa da kansa, har a yau take jera kafada da ‘yammata masu gata da ilmi ‘ya’yan manyan Najeriya a jami’ar da take wato Haseenah Bello Ambursa.
Hasinah ta tsinci kanta rana daya a soyayyar ubangidanta kamar koma fiye dashi, bata kuma san daga wane lokaci shakuwarsu ta rikide zuwa soyayyah ba. Duk da banbancin yare dake tsakaninsu, ita Hasinah bata tuna cewa ma ita bahaushiya ce saboda cakuduwa dasu Aunty Murja dashi kansa Prince da ba hausar yake yi bama kwatakwata, ko ya iya ko bai iya ba Allah masani. Duk da ita Haseenah na ganin bata kai matsayin da Prince zai aure ta ba, amma kaninsa Tokumbo dake tare da shi kuma suke shiri itada shi irin sosai kullum yana yawan karfafata da cewa.
“If she’s lucky…. Probably zata iya samun auren PRINCE!”
A bakin Tokumbo Haseenah taji cewa Mamanshi ma bahaushiya aka auro musu ita, tazo ta haifesu shi da su Murja. Shiyasa taga shi da Prince duk da suke ‘yan maza zarr basa kama da juna.
Yace su din surki ne na yare guda biyu; Fulani/Yoruba wato sun hada duka jinin yammaci da arewacin Najeriya, ba kamar sauran ‘ya’yan family dinsu ba da gabansu da bayansu Yarbawa ne.
**** **** ****
Taiwo tayi ajiyar zuciya data tuna asalin haduwar shi da Hasinah da kuma irin sakayyar da Hasinah tayi musu yau. Ita ba suruka ta dauki Haseenah bama face ’yarta ko kanwarta. Don haka taji ciwon lalacewarta duk da tayi iya kokarinta a kanta.
Tafi ganin laifin Haseenah akan na Tokumbo. Ko maiyasa? Don itace mace, kuma ita ta bada kafa har ya sayi mutunci da martabarta daga ido da zuciyar Prince.
Ta tabbatar Hasinah tayi rashi, rashin da duk duniya ya kamata ta taru ta jajanta mata, domin tabbas tayi rashin mai kaunarta da gaskiya sabida son duniya, kwadayi da biyewa zuciya da rashin sanin girman zina da illarta aikatata ga mai yinta a addinin musulunci. But who knows? Ko itama ta hanyar da aka sameta kenan? Sannan bata yi islamiyya ba.
Dr. Taiwo, ‘yar uwa mai rike sirrin dan uwanta, ko bai roketa ba, ya san wannan magana zata cigaba da zama sirri ne a tsakaninsu su kadai, sai ko Allah da ya halicce su, da kuma Hasinan da Adetokumbon. Ko iyayensu tayi alkawarin bazasu ji wannan mummunar maganar daga bakinsu ba.
Domin wani abu ne da zai kawo hargitsi mai girma ga zuri’ar Akanni gabadaya, watakila har ya jawo rarrabuwar kai, wanda basa fata. Jiharsu bakidaya ta shaida hadin kan zuri’ar Akanni da duniya bakidaya, na kasancewarsu tsintsiya madaurinki guda, don in wani ya yarda Adetokumbo zai aikata hakan a gareshi, duba da irin amintakar dake tsakaninsu, da irin taimakon da Abdulrasheed din keyi ga business din Tokumbo, wani bazai taba yarda ba, za’a ce sharri ne, ba don komai ba sai don kasancewar zuri’ar Sarki Akanni tsaftatacciyar zuri’ar kabilar Yoruba da basu yarda da ko bakar al’adar nan tasu ta a fara yin ciki a waje kafin aure ba, sannan bai da amini kaf zuri’arsu irin Adetokumbo Abdulfatahi Akanni.
Adetokumbo shine (favourite cousin) dinsa a cikin tarin kannensa maza da suke ‘yan maza zar kaf a family din Emir Abdulrasheed Akanni, wanda ya kasance Da yake ga Dan Iyan of Ilorin, daya daga cikin kannen mahaifinsa.
**** **** ****
ASALINSU
(ILORIN EMIRATE)
B
ari mu dauko tarihin tun daga tushe, wato asalin kafuwar masarautar Ilorin. Kamar yadda kowa ya riga ya sani Masarautar Ilorin da aka fi sani da ‘Ilorin Emirate’ tana nan a jihar Kwara a yammacin Najeriya, tana daya daga cikin manyan masarautun Najeriya masu dimbin arziki, Ilorin Emirate, wata babbar attajirar masarautar Musulman Yarbawa ce a kasarmu mai dimbin albarka, wadda kafuwar tarihinta ya faro ne daga rayuwar Shaihu Salih Janta, da aka fi sani da (Shehu Alimi).
Kenan su din duk da kasancewarsu Sarakai, kuma manyan sarakunan kabilar Yoruba, to manyan Malamai ne, ma’abota sani na na addinin Musulunci da kyakkyawan riko dashi. Su din, har ila yau, sun kasance Shehunnan Yarbawa ne masu dauke da sani na Alqur’ani da Hadisi, wadanda sukayi gadon sahihiyar sarauta ta malunta da arziki mai dimbin yawa daga Kakan-Kakan su Shehu Alimi, sarautarsu sarauta ce mai asali da da kyakkyawar nasaba tun kafuwar kasar Ilorin.
Ilorin Emirate, ta kasance (multiethnic Muslim Kingdom) wato cakude take da kabilu da yarurruka daban – daban na kasar Najeriya guda hudu, wadanda suka hadu suka samar da Ilorin Emirate din, sun hada da; Balogun Gambari (Hausa), Balogun Ajikobi (Yoruba), Balogun Fulani (Fulani), Balogun Alanamu (Yoruba).
Kowanne bangare wato kowanne Balogun, nada (district head) wato sarkin dake wakiltar wannan bangaren/yankin, karkashin babban Sarki Emir of Ilorin, dattijo mai ran karfe Sarkin wannan zamanin da muke ciki a lokacin yanzu, wato Emir AbdulRasheed Dan Abdullateef Akanni.
Engnr. Edrees Abdulrasheed Akanni, ya kasance Da na farko ga Sarkin Ilorin; Maimartaba Sarki AbdulRasheedu Akanni, (the 11th Yoruba-Speaking Fulani Emir) wato Sarkin Ilori na goma sha daya.
Engnr. Idris shikadai ne Da a wurin mahaifiyarsa marigayiya Olori Murjanatu (Olori na nufin Queen bisa ga al’adar masarautar), tun Edrees yana yaro ta rasu sanadin cutar sankarar mahaifa.
Sai bayan rasuwarta ne aka bawa Emir Abdulrasheed Sarautar mahaifinsa, aka kuma kawo masa mata har hudu daga garuruwan yammacin Najeriya daban-daban ya sake aure, sune suka haifa masa sauran ‘ya’yan sa maza guda tara, har Edrees da matarsa ta farko Morjanatu ta haifa in an hada su goma kenan gabadaya maza ‘ya’yan Sarkin na Ilorin.
Emir Abdulrasheed da ya tashi yiwa dansa na fari aure wato Edrees Akanni, sai ya tsallaka ya auro masa Gimbiyar Gombe mai suna (Sappa) diyar abokinsa maimartaba Sarkin Gombe, Ahmadu Umar Jalloh (CFR) daga can cikin yankin jihar Gombe dake arewacin Najeriya.
Engr. Idris Akanni tun lokacin da mahaifinsa ya aura masa Sappa Allah ya zuba masa matsananciyar soyayyarta, aure ne na gata irin na ‘ya’yan sarakuna don bai wuce shekaru 27 ba lokacin da aka aura masa Sappa, ita kuma bata fice 17 ba, tun daga lokacin yake kula da ita, don yana matukar son ta kamar ya hadiyeta.
Sappa a hannun mijinta Engnr. Idris ta karasa girma ta kuma san rayuwa, ya shiga da ita duniya ta budi ido, wata irin soyayya