Share this page
4 / 4
tsohuwace mai kawo min abinci?" Neda ta kunna wata na'ura sai ga warmers na abinci suna tahowa har gaban Hana, kawar da maganar Neda ɗin tayi, saboda ganin abincin da aka kawo mata, wani irin daɗi taje ji idan tana cin abincin gidan, iri-iren waɗanda take gani a TV ne, sai gashi yu itace take cinsa a bakinta, Lokacin da takai lomar farko idanunta suka sauka akan kusar Neda, sai yanzu ta tuno maganar da sukeyi ɗazu, Hana tace "yauwa ko kinsan inda Neda take" "Na gaya miki nice Neda, idan baki yarda ba zan iya fara baki labari tun daga ranar da kika shigo gidan nan" Hana tayi shiru, saboda lamarin ya girmeta, kuma ya zarce tunanin ta, yo idan ba mafarki ba, tayaya za ace tsohuwar mace irin Neda ta koma budurwa mai kyau haka?, Tana tunanin tana kai loma bakinta, Sheyk Rayyan ne zaune a parlor hannunsa riƙe da waya ya karata a kunne, waya yakeyi da wannan tsohon cikin natsuwa da izza, yace "bayan dawowata Japan wani babban lamari yana son faruwa, tabbas idan har hakan ta kasance zan yi nadamar ƙulla alaƙar sirri daku" Tsohon yace "sheyk Rayyan, karka manta, a halin yanzu littafin jinin tsarkaka ya zamo rayuwarka da ruhinka, dan haka karka taɓa wasa dashi, Sheyk Rayyan yace "har yanzu baka fahimci abinda nake faɗa bane?" Da Larabci suke maganar Tsohon yace "na fahimci komai maganar aurenka da Hana yazo ne a cikin littafin Jinin tsarkaka wanda a gaba sai kafin kowa alfahari da hakan, ina mai tayaka murna, a yanzu da ko yaushe littafin Jinin tsarkaka bazai taɓa yi maka zaɓin abinda zai cutar dakai ba.." Tsohon ya katse kiran, yabar Sheyk Rayyan cikin duhu, wanda har yanzu ya kasa fahimtar gaba da baya, tashi yayi tsaye, ji yake kamar yaje ya shaƙe Hana ta mutu ko zai samu sauƙi a cikin zuciyarsa, "Menene amfani da alkairi a cikin auren waccar tsinanniyar yarinyar?" Sheyk ya faɗa yana dunƙule hannunsa na dama yana dukan na hagu dashi, rurin wayarsa ne ya katse masa tunani, number da ya gani ne yasa shi zaro idanu waje, kafin ya ɗaga cikin ladabi da tunda nake ban taɓa jin yayi ba, naji yace Papa (Baba), can yayi shiru yana saurarar maganar dake fitowa daga cikin wayar, tashi ɗaya mood ɗinsa ya sauya, murya a tausashe yace "Allah ya kawoku" Ya ajiye wayar, a inda na lura dashi, tashin hankalin da yake ciki na yanzu ya ninka na ɗazu dan haka ya sauka zuwa Hidden Japanese garden ɗinsa anan ya sauka, zuciyarsa tayi zafi sosai, ya rasa mafita, dama a komai bai yarda da kowa ba face Neda, ta kasance sirrinsa da komai nasa, sometimes har abinda zai iya faruwa gobe idan ya tsananta bincike tana iya gaya masa, takowa takeyi a hankali, tana sanye da gown iya guwaiwa, rigar dark green ce, tayi mata kyau, sai hula dake a kanta, hannunta riƙe da Glass cup na (Lemon sour) lemon ya kasance yanada ɗanɗano na barasa idan har anyi masa haɗin bugarwa yana bugarwa sosai, sai dai shi wannan babu wannan haɗin a cikinsa, Ɗan risinawa da kanta tayi, kana tace "sir gashi, da fatan na sameka lafiya" Sheyk yayi mata nuni da gurin zama ba tare da ya amsa mata ba, kafin ya kurɓi Lemon sour ɗon, ya ɗan lumshe idanunta, "Neda.." Sheyk ya kira sunanta. Amsawa tayi da cewa "Sir.." Sheyk yace "ina cikin tashin hankali sosai, bani da wanda nake gayawa sirrina sama dake, inason ki bani shawara.." Neda tace "Sir, babu damuwa ka gayamin abinda yake damunka ni kuma zanyi maka maganinsa ta hanyar baka ingantacciyar shawara" Sheyk yaja dogon numfashi, kafin yace "su Papa suna hanya shi da Momma, please help me, mai kike tunanin ya kamata inyi, game da Hana da na ajiyeta ne saboda in ɗauki fansar abinda tayimin, so nake na koya mata hankali ta inda babu wanda zata sake yiwa ƙarya.." Neda tace "Sir, duk wannan mai sauƙi ne, Abu na farko, tunda dai ba anan gidan suke sauka ba, ya kamata ka ci gaba da ɓoyeta har zuwa wani lokaci, kuma karkayi sake har a gano tana gidanka" "Nagode" Sheyk ya faɗa yana yi mata alama da zaki iya tafiya da hannu, Papa ne ya sake kiran waya, yace wa Sheyk sun ƙaraso suna hanyar zuwa gidansa, Already wancan gidan da suke sauka a gyare yake, Sheyk yace "komai yana lafiya, Papa a wuce daku wancan gidan" Momma tace "komai abinsa ai dai muna tare dashi dai, maganar aure ne baya so tunda muka zo ai ƙarya ta ƙare, ko da waye zamu haɗashi aure, ƙanwarsa Zimal tace "taɓɓ Momma kin mance ko waye yayah ko?" Ƙaninsa mai suna Raif yace "wlhi ni kallon guguwa Mai ƙarfi nake yi masa, saboda Yayah baya dariya, Zimal tayi dariya harda toshe baki. Momma tace "koshi waye" A wancan gidan suka sauka, gidane babba mai kyau, wanda aka ƙawatashi da kayan alatu na zamani, everythings na more rayuwa akwai a wannan gidan, masu girki da sauransu, A ƙayataccen parlon suka zazzauna, parlon ya kasance haɗaɗe, yana kewaye da lallausar kujeru masu leda farare, sai makeken TV da ya kusa mamaye bango ɗaya, sannan frame na hoton Sheyk da family ɗinsa, wato Papa Momma day Zimal da Raif, dukansu fuskarsu ɗauke da murmishi Banda mutum ɗaya, fuskarsa kamar hadari yayinda idanuwansa suka kasance farare tass kamar madara, Tsakiyar parlon akwai wani lallausan Capet mai kyau, daga tsakiyar Capet ɗin akwai wasu pillow na fata masu ado kamar na sarauta, da Zimal da raif ko wanne da ɗakinsa, har Momma da Papa, ƴar aiki ce ta fito daga kitchen tana yi musu sannu da isowa, tare da gabatar musu da abinci a saman dinning table, Zimal ta miƙe da sauri tana cewa "thanks, cikin ƙasa da murya tace "kamar tasan yunwa nakeji" Bayan sun huta suka ɗunguma zuwa dinning room, wanda aka cika shi da kalolin abinci na Japan dana ƙasarsu Labanon, cikin farin ciki suke cin abincin da nishaɗi, gefe guda kuma Momma da Papa suna jimamin rashin zuwan babban ɗan nasu, Papa ne ya ajiye spoon kana ya tashi a gurin, fuskarta tana nuni da yanayi na damuwa, muryarsa babu walwala yace "har me Rayyan yakeyi da ba zai zo ya ganmu ba, shekara ɗaya kenan rabon da mu haɗu dashi.." Momma ma ta tashi a kan kujerar, kana ta dawo gurin Papa ta zauna a ɗan kusa dashi, sannan tace "Rayyan sam bashi da don iyaye mune dai muka damu dashi" Zimal tace "dama kun daina wahalar da kanku, Yayah bai damu daku ba.." Momma tace "shirrruuu.." bana son jin wannan maganar, karki sake" Gama maganar Momma yayi dai-dai da isowar Sheyk cikin parlon Neda na bayansa, yayinda Sarkin fada yake gefensa haɗe da wasu security guda ɗaya, sheyk yayi musu alama da su fita, banda Neda dake biye dashi a baya, Raif nayin ido biyu da Neda ya wani haɗiyi miyau tare da yi mata murmishi, mayar masa tayi lokacin da idanunta ya sauka anan Raif, Sheyk ya zauna a saman kujerar da ta kasance idan ya shigo gidan yake zama, Cikin shiga ta kamala da haɗe fuska babu walwala a cikin fuskar tasa, yace "inayi muku Barka da isowa Japan, da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya" Papa yace "lafiya ba lafiya ba, saboda akwai matsala" Cike da nuna kulawa Sheyk yace "Papa matsala kuma, kamar ta me?" Papa yace "kamar ta rashin walwalar da yake saman fuskarka, sam baka farincikin zuwanmu" Sheyk yaja dogon numfashi, kafin yace "wato Papa ina cikin wani hali ne, amma soon komai zai zo ƙarshe" Papa ya miƙe tsaye, kana yace "mu iyayenka ne baka da wanda ya fimu, saboda me bazaka kawo kukanka garemu ba, saboda bazamu kasa share maka kukan ba?" Sheyk ya girgiza kai yana murmishin gefen baki, ɗago idanun da zaiyi ya hango Raif shi da Neda a dinning, da sauri ya miƙe cikin daƙilalliyar murya yace "Neda mai ya kaiki gurinsa?" Neda tai ƙasa da kanta, tare da ɗan risinar da kanta tace "an sorry Sir" Sheyk yai saurin nuna mata hanyar fita, lokacin da takai bakin ƙofa yace "ki jirani a mota" Momma ta washe haƙora tare da tashi ta dawo kusa da kujerar da Sheyk yake zaune, kafin tace "ashe dai yaron nawa ya iya zaɓe, wannan zuƙeƙiyar yarinya haka, ga kyau ga shi komai dai-dai, zanso ace ta zamo surukata ta dinga haifo min tagawayen jikoki masu kyau irinta...! 🤣Nace Momma kin ɗibo da zafi FAKE DADDY 💞Mahaifin Bogi💞 *(Love and Romantic story)* Page 19-20 Sheyk ya kalli ƙofar da Neda ta bi da idanu masu cike da tunani, kafin ya juya ga Momma da Papa. Ya jingina baya kan kujera, ya saki ajiyar zuciya. “Momma, Papa... akwai abubuwan da ba kowa ya isa ya fahimta ba.” Momma ta kalle shi da murmushi mai ɗauke da tambaya. Rayyan bamu fahimci abinda kake nufi ba, bata cikin al'adarmu ko me? Sheyk ya ɗan ɗaga gira ɗaya, cikin murya mai cike da kasaita yace, "Eh Momma. Neda ba mutum bace kamar yadda kuke gani. Ba jini da rai take da shi ba. Aiki kawai take mini ita wani ɓangare ce daga tsarin da nake gudanarwa" Papa ya zaro ido cikin razana, Momma ta miƙe tsaye hannayenta na dafe da ƙirji, "Aiki? Wanne irin aiki kake nufi Rayyan? Mutum ko fatalwa ce?" Sheyk ya yi ɗan murmushi mai ɗauke da taushi, yana kallon hannayensa kamar yana tuno wani abu mai tsanani. Kafin yace "Na samo ta ne daga wani wuri da babu wanda zai iya shiga sai wanda ya san sirrin, Na buƙaci halitta da zata kare ni daga makiya, kuma da ita ne nake haɗa dukkan abubuwan sirri na…" Momma ta yi shiru, idonta na kan ɗanta kamar tana son tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa. "To me yasa take kama da ɗan’adam?" Momma ta jego masa tambaya tana daga tsaye, Sheyk ya ɗanyi murmishi kana yace "Saboda duk wanda ya kalleta, sai yaga kamalar mace ta duniya. Amma a asali, jiki ne da aka sassaƙa da Jinin Tsarkaka domin bin umarnina. Ta na iya yin komai idan na buƙata" Sheyk yaci gaba da cewa "Na sameta ne kafin in samu littafin jinin tsarkaka, Papa ya dafe goshi hankalinsa a tashe, saboda a inda maganganu ke fitowa daga bakin babu alamar tsoro ko nadama, Papa yaja dogon numfashi kafin yace "Rayyan, wannan abin da kake ciki yana da hatsari. Mutum baya wasa da irin waɗannan abubuwa. Kana nufin kai kanka ka buɗe ƙofa ta wani abu da ba kowa yake iya rufe shi ba?" Sheyk ne ya ɗago da kansa idanunsa sun ɗan sauya launi, na ɗan wani lokaci kafin ya ɗanyi takaitaccen murmishi sannan yace "Papa, wannan ƙofa tuni ta buɗe tun da na karɓi littafin Jinin Tsarkaka. Abin da nake nema yanzu shi ne ƙarshen komai, wanda shine yake da wahalar damu.." Momma ta ɗan motsa baki cikin tsoro da shakku, Wani abin mamaki, duk labarin da Sheyk ya bawa su Momma, Neda na jinsa, zaune take a cikin motar cikin nutsuwa, hannunta a haɗe saman cinyoyinta, idanunta a lumshe kamar tana jiran umarni. Amma a yau... akwai wani abu daban, Wani zafi ne mai sosa zuciya ke yawo a kirjinta, yana tafiya har cikin jinin jikinta, idan tana da jini kenan, Tana jin kamar zuciyarta tana bugawa a hankali, abu wanda bai taɓa faruwa da ita ba tun lokacin da aka halicceta, Neda ta zauna a cikin motar cikin nutsuwa, hannunta a haɗe saman cinyoyinta, idanunta a lumshe kamar tana jiran umarni. Amma a yau... akwai wani abu daban. Wani sanyi mai sosa zuciya ke yawo a kirjinta, yana tafiya har cikin jinin jikinta — idan tana da jini kenan. Tana jin kamar zuciyarta tana bugawa a hankali, abu wanda bai taɓa faruwa da ita ba tun lokacin da aka halicceta. "Me ke faruwa dani?" ta furta a hankali, idanunta na haskawa da shuɗin launi na ɗan lokaci kafin su koma yadda suke. Tana jin muryar Sheyk daga cikin gida, yana ci gaba da bawa su Momma labarin inda aka tsarata, muryar da ke cike da izza, muryar wanda jikinta ya saba amsawa ba tare da jinkiri ba, Amma a yau, ba umarni yake yi mata ba, Yana magana ne game da ita. "Ba mutum bace, Aiki kawai take yimin" Kalmar ta bugi dodon kunnenta, ta shiga zuciyarta kamar ƙibiya, Tana jin wani abu ya motsi a ƙirjinta, kamar tana so ta yi kuka amma ba ta da hawaye. Tana son ta ce masa “Ni fa ina ji, Sheyk… ni fa ina numfashi saboda kai.” Amma harshenta ya ƙi motsi, saboda tsarin da aka yi ta bai yarda ta faɗi kalmomi irin haka ba. A hankali ta ɗaga hannunta, ta kalli tafin hannunta wanda babu tsoka a jikinsa, babu z jini, amma tana jin ɗumi a cikinta. Sheyk ne ya fito cikin taƙama, Yana tafiya a hankali, har ya iso gurin motar, Momma da Papa suna biye dashi, dama tuni su Zimal da raif sun wuce can garden basu san su me Momma suka tattauna akai ba, Lokacin da ya shiga motar, security da Sarkin fada suka shiga tasu, "Ki kunna mota." Neda ta yi hakan ba tare da ta ce komai ba, amma zuciyarta tana cike da tarin tambayoyi saboda yau ne tasan ko ita wacece, tunda aka ƙirƙireta bata taɓa tunanin komai ba, sai dai tasan bata ci bata sha, "Shin idan ba mutum bace, me yasa zuciyarta ke bugawa saboda shi?" Bayan sun dawo gida zuciyarsa cike da tunanin inda zai kai hana saboda baya son su Momma Susan tana cikin gidansa, idan har ɗaya daga cikinsu yayi ido biyu da ita komai yana iya faruwa, da wannan tunanin ya wuce bedroom ɗinsa zuciyarsa na a cike da jimamin halarcin da littafin jinin tsarkaka yayi masa, Tun bayan tafiyarsu Hana na nan zaune, har yamma tayi babu wanda ya kawo mata abinci bare ruwa, cikinta ya dinga ƙullewa, tayi kuka har ta gaji, ta takure a gefe numfashinta na yin sama-sama, ga mamakinta yau ta ƙofar ɗakin ya shigo, tanajin sallamarsa a ciki-ciki ta ɗago manyan idanuwanta tana dubansa, muryarta a sanyaye tace "Dady yunwa nake ji, first time ya wanka mata mari yana huci kamar wani zaki, uban waye Dadynki bayan na gaya miki ni ba mahaifinki bane, sannan sai kin girbi abinda kika shuka, har yanzu ina mamakin rashin ɗaukar ƙwaƙwaran mataki da banyi ba a kanki, dan haka yau ki ƙaddara sai kin sha azaba, yai maganar yana janyo gashin kanta, so yake yayi sex da ita daga ƙarshe yasa Neda ta fitar da ita can wajen gari yasar da ita, yau kam ya ƙuduri aniyar ba jinin tsarkaka ba ko jinin daukaka ne ya haɗa aurensa da Hana sai ya warwareshi, Tana a tsugunne a gurin jikinta na karkarwa ya sanya lallausan hannunsa a saman nata hannun, da niyyar ya janyota, hannunsu ya manne dana juna, Hana ta zaro idanu, a cikin jikinta sai take jin kamar an saka mata gam, muryarta na rawa tace "ka...kayi...kayi...kayi haƙuri ba ni bace" Abin mamaki wanda baya ƙarewa, shi da yabar littafin jinin tsarkaka a ɗakinsa sai gashi cikin ɗakin da yake gurin Hana, sai watso musu taurari yake, cikin wata murya mai daɗi amo da saurare, littafin Na fitar da ƙamshi da iska wanda yasa gashin kansu karkaɗawa kamar an kunna fanka mai gudu, "Nine littafin jinin tsarkaka, wannan damar da nazo maka da ita shine dama na ƙarshe, ka amince da auren yarinyar da ta shigo cikin rayuwarka, wato Hana, ko ka jurewa shiga ko wanne irin ƙalu bale na rayuwa amsarka muke jira...." Complete document ɗinsa dubu ɗaya ne account number 3175689751 Name Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224 Downloaded From https://tknovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4