An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*ABINDA BABBA YA HANGO........!*
_Short Story🤌🏽_
*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*
*Whattpad@MaryamIbrahim244.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Godiya*
*Har kullum ina ƙara godiya ga Allahu subhanahu wata'ala, domin kuwa ikon sane da yardarsa ya sanya harna ɗaura hannayena gurin fara rubuta wannan labarin.*
*Jan kunne.*
*Wannan labarin na yi sane domin na ilmantar da al'umma, don haka kar wacce ta kuskura ta juyamin labari, idan hakan ta kasance hukuma ce zata rabani dake.*
*Nusarwa.*
*Wannan ƙirƙirar ren labari ne, banyi dan wani ko wata ba na yi ne domin ilmantar tawa, bana buƙatar cece kuce.*
*Gaisuwa da fatan alkheree zuwa ga ƴan uwa da abokanan arziƙi, DOCTOR na ƙara godiya a gareku , kuna raina gaba ɗayan ku kamar yadda nasan ina ranku, much luv💋.*
*Yadda ake haɗa lemon Na’a-Na’a da Kokumba*
*Kayan Haɗi.*
*• Na’a-Na’a*
*• KokumSiFilebo*
*• Sukari/Sirof*
*• Filebo*
*Yadda ake yi*
*Da farko uwargida za ki samu Na’a-Na’a irin koriyar nan sosai sai ki wanke ta sosai ki tabbatar duk kasar da ke jiki ta fita tas sannan sai ki markada ta a bilenda daga nan sai ki tace ki ajiye ruwan a gefe guda, sai ki samu Kokumba mai kyau ki yanyanka ta sannan ki markada ki tace.*
*Sai ki dafa sukari wanda zai zama abin da ake kira sirof.*
*Sai ki samo babban kofinki ki juye tattaccen ruwan Na’a-Na’a da na Kokumba a ciki ki dauko sirof din nan ki zuba a kai. Sai ki samu filebo mai kamshi ki zuba a ciki.*
*Shi ke nan sai ki sa a firiji, idan ya yi sanyi sai sha, ko a saka kankara a ciki asha.*
*بسم الله الرحمن الرحيم.*
*EPISODE 1_5.*
🖊️Waya ce a hannunta sai faman sarrafata takeyi, gabanta kuwa kayan marmari ne sai faman cika baki take yi dasu tana sarrafa wayar hannunta.
Shigowarsa ɗakin ne ya sanya fuskanta canjawa daga yanayin da take ciki zuwa wani launin, jikinsa na rawa ya ƙara sa gurinta yana me faman washe baki , ita kuwa sai ƙara ɗaure fuska take yi haɗi da ɗauke kai daga gurinda yake zuwa wani sashen.
"Dan Allah hubby ki yi haƙuri indan kuɗin da ki kayi magana ne insha Allahu yau zuwa gobe zan nemosu na baki."
Ƙara ɗaure fuska ta yi sannan cikin ƙasaita ta ce "okey, zaka iya riƙe duk waƴansu zan tuka naka har lokacin da kazo da kuɗin, kai kullum a kayi ma maganar kuɗi ka iya faɗan babu babu, iyayen kuɗin dashi uban naka ya mutu ya barma fa?, albashin da kake ƙarɓa me kake yi dashi ne?."
Cije leɓensa bakinsa ya yi cike dajin ɗacin furucin ta a garesa , sai dai ba damar maganar dan yasan ko maganar ya yi wata magana ce zata ƙara caɓa masa.
Jikinsa a sanyaye ya ƙara kai kallonsa kanta , harya buɗe baki da niyar yin magana ta yi azamar ɗaga masa hannu sannan ta miƙe hannunta riƙe da tanfatsetsiyar wayarta ta nufi hanyar ficewa daga ɗakin ba tare data bashi izinin yin maganar da yayi niyar yi ba.
Zama ya yi a gurinda ta tashi sannan ya sanya hannunsa na dama ya dafe kansa dashi , lokaci ɗaya yana mejin kamar ya kurma ihu sai dai ba damar hakan a garesa.
Miƙewa shima ya yi jikinsa a saɓule ya fice daga cikin ɗakin.
A harabar gidan ya iskota zaune a gurin shuke shuken gidan , gurin anyi sane domin shaƙatawa, sai amsa waya take yi, tana faman ɗaure fuska.
Gurin da take ya nufa yana me addu'ar Allah yasa ta kulasa a wannan lokacin, sai dai tunkan ya isa gurin ta yi azamar miƙewa ta nufi hanyar shiga sashen nata.
Jikinsa a sanyaye ya juya yana me fito da key daga cikin aljihunsa.
Tunkan ya isa gurin da motaci ke parke, wata haɗaɗɗiyar mota baƙa dake parke a cikin jerin motacin da aƙalla zasu kai shida , murfin motar ya buɗe, yana isa gurin ya yi azamar faɗawa cikin motar ya yi mata key.
Get man ne ya yi azamar wangale gate ɗin ganin yadda uban gidan nasa ya janyo motar.
Tafiya ya ke yi amman shi kansa besan inda ya dosa ba, parking ya yi a gefen titi yana me dukan sitiyarin motar da hannunsa kana ya kwantar da kansa jikin sitiyarin yana me busar da iskar daya tara cikin bakinsa.
Ya jima a gurin yana me saƙawa da warware wa, sai dai har tsawon 20minutes ya rasa wacce hanya zaibi a wannan lokacin domin ya samowa ZULFA'U kuɗin data ke buƙata ba, gaba ɗaya kansa ya ɗauki caji sai faman tunane tunane ya keyi.
Jan motar ya yi ya koma gidan yana me addu'ar Allah yasa wannan karon ta sauraresa.
Sai da yayi addu'oi kana ya sanya ƙafarsa cikin parlourn, sai dai bakowa a ciki, cikin ɗakunan ya fara nemanta amman ko ina ba alamun ta, har banɗaki ya leƙa nan ma bata ciki.
Fitowa ya yi daga ɗakin ya nufi harabar gidan sai yanzu idanuwansa suka sauka a jerin motacin gidan, ba ƙwaya ɗaya "wannan na nufin ta fice kenan?", wai sai yaushe ZULFA'U zata daina wulaƙanta ni ne?, me take nufi da ni ne?, so ta keyi na dinga shiga bank bank ina wawuso mata kuɗa ɗai ina kawo mata ne?."
Tafe kansa ya yi dake faman sara masa , ya jima a gurin tsaye yana tunanin ina ta shiga ne?, ganin ba mafita ya sanya sa komawa cikin ɗakin.
Ruwa ya watso kana ya fito ya nufi kitchin, kamar yadda ya zata hakan ce ya cimma, kwanuka ne watse a ko ina cikin kitchin ɗin , ƙudaje sai faman bibiyarsu suke yi, a haka wai ake rayuwa a cikin sa.
Ƙarewa ko ina kallo ya tsaya yi wurin kamar baƙon wajensa , lokaci ɗaya zuciyarsa ta dinga juyawa ba shiri ya fice daga kitchin ɗin ba tare daya ɗauki ko cokali daga cikin kitchin ɗin ba.
Parlour ya dawo ya buɗe ƙatuwar freezer dake malale a gurin , sai dai me?, ita kanta freezer yana buɗe ta tsami tsami ya dinga bugosa.
Ba shiri ya mayar ya rufe yana me girgiza kai da neman Allah ya kawo masa ɗauki.
Ɗaki ya koma ya ɗauko ₦500 kana ya fito gurinda mai gadin get yake, bashi ya yi yana faɗan "dan Allah malam Ayuba tai maka karɓomin RC ƙwaya ɗaya a shagon Inusa".
Ƙarɓar kuɗin ya yi yana me fice daga cikin gidan, shi kuwa ya zauna a saman benci yana me rafka tagumi.
"Ohni Ƙasim wai ina ZULFA'U ta nufa ne?", ya faɗa yana ƙara rarraba idanuwa a cikin farfajiyar gidan.
★★★★★★
"Kaga Haruna ka juya ka koma gida na gaya ma cikin satinnan ina nan zuwa, kuɗin ne ba'a samu ba da zaran ya samo min kuɗin zaka jini."
Wanda aka kira da Haruna ya ɗago kansa yana kallonta sannan ya ce "ni gaskiya na fara gajiya ZULFA'U, ta yaya zaki zo nan ki zauna alhalin kinsan kuma kin baro mu can, me hakan ke nufi? kin fison wannan sakaran dani kenan?."
"Ba haka bane Haruna, kai kasan na daban ne ai, ba wani gabanka da bayan ka, kaine fa zaɓin raina wancen fa?, na auresa ne domin mu samu namu rabon".
"Kai kanka kasan da inason sa Allah ba yadda za'ayi na tsaya sauraren ka don kasan ya fika da komai."
Ɗaure fuska ya yi tamau kana ya ɗauke kai, ya fara kici kicin buɗe murfin motar.
Ganin abinda yake da niyar yine ya sanya ta saurin dakatar dashi ta hanyar cewa "me yayi zafi kuma?, gaskiya ce na faɗa ma, kuma kaine ka nemi hakan ai."
Cikin ƙakkausar murya ya ce "buɗe min mota na fice kije can gun wanda ya fini da komai ai dama shi kika zaɓa ni kin watsar dani a titi."
"Sorry nawa , ka dinga tausar zuciyarka mana."
Zip ɗin Jakartata zuge sannan ta fito da kuɗi a ƙalla zasu kai dubu goma ta ce "ungo wannan kaje a siyawa su baby sweet da rabi rabi ka ɗauka naka ne."
Jikinsa na rawa ya sanya hannu ya ƙarɓi kuɗin yana me faman washe baki.
"Godiya nakeyi tawa, buɗe min murfin na fita kinga 6 ta kusa."
"Okey ka kulamin da baby, kwanannan zata dawo guna ma insha Allahu."
Ficewa ya yi daga cikin motar yana ɗaga mata hannu.
Ɗan acaɓa ya tara ya haye, tana ganin haka ta yi wa motar ta key ta nufi hanyar gida.....🖊️
*Follow me on whattpad@MaryamIbrahim244.*
*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*
_Short Story🤌🏽._
*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*
*Whattpad@MaryamIbrahim244.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Yadda ake hada lemon ayaba da kwakwa*
*Kayan haɗi*
*•Ayaba*
*•Kwakwa*
*•Sukari*
*•Ruwan kwakwa*
*•Madara*
*•Filebo*
*Yadda ake yin haɗin*
*Da farko uwargida za ki tsiyaye ruwan da ke cikin kwakwarki, ki ajiye shi a gefe guda.*
*Sai ki kankare bakin bayan kwakwar sannan sai ki wanke ta.*
*Daga nan sai ki yanyanka kwakwar kanana sannan sai ki zuba a bilenda ki kawo ruwan kwakwar nan ki zuba akai sai ki markaɗa.*
*Idan ki ka tabbatar ya markaɗu sai ki sami mataci ki tace za ki iya kara ruwa kaɗan akai.* *Idan kika gama sai ki ajiye ruwan kwakwar a gefe.*
*Sai kuma ki ɗauko ayabarki ki yanyanka ta kanana sai ki zuba ruwan kwakwar nan da kika tace a cikin bilendar sannan ki zuba ayabar nan akai sai ki markaɗa. Idan kika tabbatar ya markaɗu sai ki sami babban kofi ki juye a ciki sannan ki ɗauko sukari da madara ki zuba akai sannan sai ki ɗauko filebo mai ɗanɗanon kwakwa ko ayaba ki zuba don ya kara fito wa lemon ɗanɗano.*
*Daga nan sai ki juya idan ya yi daidai sai ki sa a firiji, idan ya yi sanyi sai a ɗauko a zuba a kofi asha.*
*بسم الله الرحمن الرحيم.*
*EPISODE 6_10.*
🖊️A parking space ta yi parking kana ta fito daga cikin motar tana taku a hankali kamar wacce bata son taka ƙasa.
Jin shigowar mota cikin gidan yasanya sa saurin yaye labulen taga yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, fara ce sol kyakkyawar gaske sai ƴar zagayayyinyar fuskarta mai ɗauke da dara daran idanuwana sai hancinta me tsayin gaske ya yin da bakinta yake zagaye ɗauke da manya manyan pink lips doguwa ce ba sosai ba, bata da wani jikin azo a gani daga ganin ta kaga kalar buzaye.
Sauke idanuwansa ya yi a kanta a cikin ransa yana faɗan "ga kyau har kyau amman ba a gurin daya dace ba.
Shigowarta ɗakin tana taku a hankali yayin da bakinta ke fitar da sautin ƙarar cingam ya sanya shi mayar da hankalinsa kanta.
Ko kallon gurinda yake ba tayi ba ta yi shigewarta ɗakinta tana faman juya mazaunai.
Tashi ya yi daga kan kujerar da yake yabi bayan ta, yana shiga ɗakin ana kwaɗa kiran sallah.
Da hanzarinsa ya fice daga ɗakin ya nufi harabar gidan suka gabatar da alwala kana suka nufi masallaci shi da Ayuba.
Sai da suka gabatar da isha'i sannan suka dawo gidan.
Sallama ya yi wa Ayuba sannan ya shige , bakinsa ɗauke da addu'oin samun nasarar shawo kanta.
Sai dai me?.
A ƙargame ya tarar da ɗakin nata , jikinsa a sanyaye ya nufi nasa ɗakin.
Zubewa ya yi a saman gado yana me tunanin wai inane zaije ya samowa ZULFA'U kuɗin nan ko hankalinsa ya kwanta.
Wayarsa ya janyo yana duba date , jikinsa ne ya yi sanyi ganin 9feb, "ko yanzu da sauran lokaci kamin a fara albashi", ya faɗa yana mai ƙara duba wayar domin ya tabbatar da gaske ne ko kuwa idanuwansa ne keyi masa gizau.
"Lallai haka ne kam" ya faɗa yana me wurgar da wayar gefen gadon.
Bacci yake ji amman baya jin zai iya baccin kirki matuƙar ZULFA'U bata saurare sa ba, sai dai ta yaya?.
"Ai kedai bari Hajiya Turai gobe zanje wajen nakan tudu don naga kwana kinnan kansa ya fara hayaƙi, duba ki ga yau kwana biyu kenan fa da yi masa maganar ina buƙatar dubu ɗari kachal amman ya tsaya yimin kwana kwana, yana son ya ce min bashi da dubu ɗari ne , zan shigo ki raka ni."
Banji me wancen ɓangaren aka ceba, sai kawai naji ga ta kwashe da dariya kana ta ce "barshi saina nuna masa dani yake zance, Allah zan bashi mamaki."
Ko wannan karon banji me waccen ta faɗa ba , na daiji ta ce "okey saina shigo, ki shirya da wuri wuri tun 8am zan shigo."
Kana ta yanke wayar, tana me ƙara gyara kwanciyarta a saman makeken gadon ta.
Ya jima yana juyi kamin ya samu ɓarawo ya sace sa wato bacci.
★★★★★★
Kiran sallar farko a saman kunnensa a kayi sa, miƙewa zaune ya yi yana me karanto addu'ar tashi daga bacci, kana ya sauko daga kan gadon ya nufi banɗakin dake cikin ɗakin.
Ruwa ya watsa kana ya zura jallabiya fara ya fito, ɗakinta ya ƙwankwasa duk da yasan ba tashin zata yi ba, amman ai gwanda ya fitar mata da haƙƙinta.
Lokacin da taji bugun ƙofar tsaki kawai taja ta ƙara jan rufa tana me ƙara lafewa a saman gadon.
Jin shuru ko motsinta beji ba yasan yashi , yi gaba don gudun kada jam'i ya wuce sa.
Sai 7am ya shigo gidan hannunsa riƙe da carbi , a saman benci ya zauna suna gaisawa da Ayuba me gadi.
7:10 ya miƙe ya nufi ɗakinsa domin shirin zuwa wajen aiki.
Sai 7:30 ta miƙe daga kan shimfiɗar ta nufi ban ɗaki, brush kawai tayi ta fito ta janyo jikkar da take ajiye kayan maƙulashe a ciki , fitowa ta yi da manya manyan biscuit ta hauci, sai da taji cikinta ya ɗauka sannan ta kwashe ragowar ta mayar a cikin jikkar sannan ta miƙe ta janyo mai ta hau shafawa.
Shiri ta yi sosai kamar wacce zata je gasar kyawawan mata , ba tare da tayi sallah ba balle shi wanka ta rataya ƴar jikkarta a kafaɗa kana ta janyo ɗakinta ta rufe.
Ba kowa a Parlour hakan ne yasanya ta ficewa daga cikin sa ba tare da wani jinkiri ba.
Jin tashin mota ne yasanya sa saurin fitowa daga cikin ɗakin hannunsa riƙe da key ɗin motarsa.
Tun kan yakai da ficewa daga cikin parlourn yaji ya daina jin kukan motar.
Komawa ya yi cikin parlourn ya zube a saman kujera yana faɗan "Ya Allahu."
Ya jima gurin zaune ganin ba sarki sai Allah ya fice daga cikin gidan gaba ɗaya ya nufi ma aikatar su.
Tafe take a cikin motar kiɗa kawai ke tashi a ciki, ita kuwa sai faman girgiza kai take yi alamun waƙar na shigarta.
A dai dai wani ɗan madai daicin gida ta yi parking tana me fitowa daga cikin motar, kana ta nufi cikin gidan.
Gida ne ɗan madai daici, mai ɗauke da ɗakuna biyu , daga shigarka gidan zaka fara cin karo da ledodin kayan ciye ciye bar katai ba tsari.
Tsalla ke ledodin ta fara yi kamin ta sadu da ainihin gidan.
Cikin ɗaki ta yi kai tsaye.
Kwance take saman katifa daga ita sai ɗan guntun wando sai breziya da take sanye da'ita.
Ta yi ɗay ɗay ɗay a saman katifar ya yinda gashin kanta yake babbaje dashi , sai sharar bacci take yi.
Duka ta duma mata a saman cinya wanda ya sanyata saurin miƙewa tana gantsare ƙirji.
Harara ta wurga mata sannan ta ce "kinzo kinyi wannan kwanciyar bakyama gudun kina bacci kiji.......".
Harara itama ta sakar mata sannan tace "to meye naki a ciki?."
"Oya ni dai ba faɗa nazo yi ba, miƙe kije ki shirya muje , kinsan ko yanzu mun makara sai mun isko layi sosai".
"Karki ga laifina kiga laifin Ruka don itace bata tadani ba, kuma sai da na gaya mata gunda za muje amman tana gama shirinta ta fice ta barni a kwance."
"Ruka anan gidan ta kwana ne?".
"Eh mana, mutuwa ake fashi ko hisabi¿."
"Ba'a fashin komai amman ya kamata kuzo ku daina wannan ɗabi'ar gaskiya ba mai kyau bace ba."
"Ke yanzu gurin da zakije guri ne mai kyau?" Hajiya Turai ta faɗa.
"Ko bamai kyau bane ba, Allah yafi wannan lalacin da kukeyi, ni kin gannin nan komai iskanci na wallahi bazan iya neman ƴar uwata mace ba, kyamar abin nake yi gaba ɗaya, plx kuma kuzo ku daina dan Allah."
Wucewa ta yi ta nufi hanyar waje ba tare data ce da'ita komai ba.
Taɓe baki ta yi tana faɗan "ai dukan ku bakwason gaskiya."
Zaune yake a saman kujera , gaba ɗaya ya zurfafa duniyar tunani.
Harya shigo office ɗin besan ya shigo ba, sai da ya sakar masa dun du a baya sannan ya yi firgigit yana rarraba idanuwa.
Jan kujerar dake fuskantar tashi ya yi ya zauna sannan ya kallesa ya ce "wai anya abokina lafiya kake kuwa kwana biyu?."
Sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce "ba lafiya ba kam, wallahi Bash ina cikin tashin hankali kwana biyunnan, gaba ɗaya al'amuran ZULFA'U suna neman su kwance min kai, mace gaba ɗaya bata da lokacin komai da kowa saina yawo da neman kuɗin?, gaba ɗaya 2days ta fitineni saina bata dubu ɗari bansan me zata yi dasu ba."
"Ni kuwa kaga yanzu ba kuɗi a hannuna shekaran jiya na harhaɗa kuɗina gaba ɗaya na bayar a shigomin da waƴansu a tamfinnai sabon design a ƙasar Jamus, kuma gashi ta fitine ni gashi yau 10 balle nasamu a abani albashina a wancen gurin da nake ."........ 🖊️
*Follow me on whattpad@MaryamIbrahim244.*
*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*
_Short Story._
*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*
*Whattpad@MaryamIbrahim244.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*YADDA AKE DAFA SHINKAFAR KWAKWA*
*Yana da kyau uwargida ta san yadda ake dafa nau'ukan shinkafa. Kada ta tsaya a shinkafa fara da dage-dage ko jalof din shinkafa kawai.*
*Yana da kyau idan za ta dafa shinkafarta, ta dan kawata ta da su ganye domin karin jini da lafiya a jiki. Idan a sati kina dafa shinkafa ba tare da yi mata wani hadi ba to tabbas ne abincinki zai fita daga ran maigida.*
*ABUBUWAN DA AKE BUKATA*
*Garin kwakwa ko markadaddiyar kwakwa*
*- Shinkafa*
*- Karas*
*- Koren tattasai*
*- Koren wake kanana (Peas)*
*YADDA AKE HADAWA*
*A dora ruwa a wuta. Idan ya tafasa sai a zuba shinkafa har sai shinkafar ta tafasa na tsawon minti 15 sannan sai a wanke da ruwa a sa a matsami a ajiye._ _A kankare karas, sannan a wanke kamin a yayyanka shi kanana.*
*A wanke tattasai da koren wake da koren kanana (Peas) sai a yayyankasu amma banda (Peas) din.*
*Bayan an kankare bayan kwakwar an markada farin, sai a zuba ruwa sosai. Da ruwan kwakwar za ayi sanwar dahuwar.*
*A zuba ruwan kwakwar a tukunya bayan ya tafasa sannan a zuba wannan ajiyayyen shinkafar idan ta kusa dahuwa sai a zuba yankakken koren tattasai da karas da koren wake da kuma koren wake kanana (Peas) a rufe da murfi a rage wutar girkin.*
*Bayan mintuna biyar, sai a gauraya wannan shinkafar a sauke. Shikenan an kammala._ _Ko da maigida ba mai son cin shinkafa bane zaki ga ya fara sha'awar cin irin wannan girkin. Za a iya hada wannan girkin da miyar kaza ko miyar kifi.*
*بسم الله الرحمن الرحيم.*
*EPISODE 11_15.*
🖊️"Sorry abokina , kasan mata zama dasu sai da haƙuri don haka ka ƙara haƙuri wata rana sai labari".
Girgiza kai kawai ya yi , kana suka ɗauko maganar shigo da kayan da za'ayi jibi.
Zaune suke a cikin wani ɗaki wanda gaba ɗaya sa kayan tarkacen tsubbu ne a ciki, sai wani sunku cecen mutum baƙiƙirin dashi sai ƙaton cikin dake maƙale da jikinsa, baya sanye da komai na dangane da sutura sai wani ƙyalle daya ɗaura a ƙugunsa, buɗan idanuwa kawai ya keyi yana faman lashe baki.
Kallonsu ya yi sannan cikin muryarsa mai firgitarwa ya ce "dole ne aikin ki ya dinga gaba yana dawowa baya, mahaifiyarsa ce tsaye a kansa bata bacci kullum itace ke faman wargaza mana aikinmu."
Cikin marai raicewar murya ta ce "yanzu ya za'ayi kenan ya shugaba?."
"Idan har kina son aikinmu ya yi kyau a kansa ba makawa sai an kawar da waccen tsohuwar, muddin tana raye ba zaki taɓa cin galaba a kan ɗanta ba."
Ɗan jimm ta yi sannan ta ce "to a kawar mana da'ita don kuwa akan na mallaki komai na Ƙasim ba abinda bazan iya aikata wa ba."
Wani ƙullin magani ya miƙo mata sannan ya ce "ki tabbatar da kin sanya mata wannan a cikin abinci, da zaran taci sa to tabbas sai dai wata ba ita ba, mutanen mu basa iya tunkarar gidan sune, dasu zamu sanya domin su kawar mana da ita cikin sauƙi, amman ko wannan me sauƙi ne kije ki jarraba ki gani."
Ƙarɓar maganin ta yi sannan ta ce "godiya nake yi shugaba."
Kallonsa Hajiya Turai ta yi sannan ta ce "ni kuwa maganin farin jinin maza da mata nake nema shugaba, wanda da zaran naga mutum na nuna ra'ayina a kansa mace ko namiji su biyoni ba gardamar komai."
"Dariya ya kwashe da ita wacce ta sanya ɗakin amsawa gaba ɗaya, ya ɗauki kusan 2minutes kana ya dakata ya kalleta ya ce "Turai Turai! ba sauƙi kika ce!."
"Gyáɗa kai ta yi alamar tabbatar masa da zancen sa kana ta ce "a taimakanin dashi ko nawa ne zan bayar."
Waƴansu ruwa ya janyo daga cikin wani kwano baƙiƙirin dashi kana ya ce "ki dinga wanke fuskarki da wannan idan zaki fita , harna tsawon kwana uku, iname gaya maki ba wanda ko wacce ta isa taja dake matuƙar kika nemi biyan buƙata."
Ƙarɓar ruwan ta yi tana zuba godiya kana suka ajiye masa maƙudan kuɗaɗe suka fito.
Tafiya mai nisa suka yi kamin su kawo gunda suka yi parking ɗin motar su.
Key ta yi wa motar suka nufi cikin gari cike da murna da tunanin samun nasara.
*ASALIN LABARIN.*
Alƙasim Shu'aibu Idrees, shine cikakken sunan sa haifaffen garin Kano su huɗu Allah ya bawa iyayensu shine babba kuma namiji, sai ƙanwarsa mebi masa Hauwa dake aure anan Kano sai kuma Shamsiya itama ta yi aure anan Kano sai ƴan biyu wato Hassana da Hussaina dake shekarar ƙarshe a secondry school ta ƴan mata dake kano.
Mahaifinsu gwargwado yana da rufin asirin Allah, dukkanin su sunyi karatun boko dana islama dai dai gwargwado.
Kamin Allah ya ƙarɓi ransa sai da ya tabbatar ya ɗaura ɗan nasa a harkar kasuwanci dama kuma yana aiki da