wani babban Company da ake ji dashi a garuruwa da dama.
ZULFA'U asalinta ƴar jihar Nijar ce suna zaune ita da iyayenta acan wani ƙauye dake cikin Nijar, buzaye ne waƴanda gaba ɗaya basu da burin komai a rayuwarsu sai na kuɗi , hakan ya sanya su turota aikatau domin tasar masu kuɗi a cikin garin Sokoto dake makwabtaka da kasar tasu.
Bayan ta shiga garin Sokoto kasan cewar ba wani wanda ta sani a haka ta yi ta yawon neman wanda zai taimaka mata.
Lokacin ne ta gamu da Hajiya Turai duk da ta girmeta amman a haka suke rayuwarsu da'ita har izuwa lokacin da zaman su ya koma Kano kasan cewar a ita Hajiya Turai macece me buɗewar ido wacce ke zaman kanta.
Lokacin da suka shiga garin Kano lokacin ne idanuwan ZULFA'U suka daɗa buɗe wa , nan aka shiga wartsake wa da mazan titi.
A wajen jajibe jajibenta ne ta samo Haruna yaron wani Alh da take hulɗa dashi ne, sau ɗaya ƙaddara ta faɗa kansa ta hanyar tarayya da'ita.
Bayan watanni ta fuskanci tana ɗauke da juna biyu sosai hankalinta dana Hajiya Turai ya tashi lokacin da sukaje asibiti aka tabbatar masu da cikin ne sai dai ya yi kwari sosai.
Kasancewar duk wanda ta samu hulɗa ta keyi dashi ya sanya ba zata kawo uban cikin nata ba, shawarar liƙawa Haruna suka yanke, lokaci ɗaya suka je masa da batun cikin.
Hankalinsa ya tashi najin wannan mummunan labarin amman daga baya sai ya fawwala wa Allah komai yasa hannu biyu ya karbi abin.
Bayan wata tara ta haifo ƴarta macce wacce ko alama bata yi kama da Haruna ba, amman kasan cewar ba asan inda za'a nufa da'ita ba ala dole aka liƙawa Haruna.
Da yake bai taɓa haihuwa ba dashi har matarsa Maryama macce mai haƙuri mai kawai ci, tasa hannu biyu ta karbi yarinyar tun tana ƙanƙanuwarta taci sunan Zainab suna ce mata Baby.
Ita ke ɗaukar dukkanin ɗawainiyarsu.
Ko nawa Haruna ya ce yana buƙata bata shayin basa.
Lokacin data fara haɗuwa da Ƙasim sosai ta ruɗe a kansa, tajewa da Hajiya Turai da zancen lokaci ɗaya suka kai sunan sa gurin boka sai gashi kuwa ya kawo kansa gurinta da sunan aure.
A lokacin kuwa an sanya ranar auren Alƙasim da ƴar wan Babansa Maimunatu amman lokaci ɗaya ya ce ba zai aureta ba shi yana da wacce yake so.
Sosai akayi daru da Alh Shu'aibu kamin ya yadda akayi auren amman da sharaɗin duk abinda ya biyo baya ba ruwansa dashi har Hajiya Umma cire hannunsu suka yi akan lamarin auren.
Da yake suna zaune a family hause ne ai kuwa nan zance ya karaɗai ko ina Ƙasim buzuwa zai aura, amman a haka iyayensa suka kulle kunnuwansu suka zuba masa idanuwa, sun sai tabbata ba zaiya gane illar abinda yake da niyar yi ba sai zuwa gaba.
A haka aka sha hidimar bikin Ƙasim da ZULFA'U ba tare da sanin nata iyayen ba, don kuwa tun bayan barowarta garin nasu har yau bata wai wayi gida ba.
Sai bayan auren ne matsaloli da yawa suka fara Kunno Kai a cikin gidan.
Bata sallah sai taga dama , bata aikin gida bata dafa abinci yaso ya ɗauko ƴar aiki amman inaáh tsananin kishi ya sanya ta hana ɗaukar mata ƴar aiki duk da tana da buƙata da'ita.
Bayan aurensu da wata biyu Allah ya yiwa Alh Shu'aibu rasuwa mutuwar data girgiza al'umma da dama kasan cewarsu mutum wanda yasan yadda yake tafiyar da rayuwarsa.
Ƙiri ƙiri ZULFA'U taƙi zuwa gidan gaisuwa a haka har aka watse kwana uku bata leƙa ba, tun bayan aurensu sau ɗaya ta taɓa zuwa gidan.
A cewar ta ƴan uwansa basa sonta don haka itama bata sonsu.
Haka ya sanya mata idanuwa ko wacce safiya muaradinta ta cancaɗa kwalliya ta fice zuwa gidan Hajiya Turai daga can su wuce wurin watsewarsu.
Hajiya Umma kuwa ganin irin matar da ɗan nata ya aura ya sanya bata zauna ba ta miƙe tsaye wajen nemawa ɗan nata tsarin Allah daga sharrin ZULFA'U. A haka kuma tana yi masa addu'ar Allah ya ƙarkato mata da hankalinsa wajen su, bata da burin daya wuce taga ɗanta ya auri ƴar mutunci don samun jikoki daga tsatso mai kyau, har yau tana yi masa addu'ar mallakar Maimunatu a matsayin matar aure.
Sosai take cin duniyarta da tsinke bari ki ba wanda bata yi domin ganin ta tara abin duniya, akai akai takan je gidan Haruna diba ƴar tata wacce yanzu a ƙalla tayi shekaru shida, kana daga bisani ta cika su da abin duniya ta tafiyarta.
Kiran wayarta ya yi akan yana son ya canja wa Baby makaranta da kuma son ya saya mata ƴan kayan sawa.
Wannan ne musabbabin tashin tashinar da suke yi da Ƙasim, ta buƙaci dubu ɗari yayinda shi kuwa be jima da kwashe dukkanin kuɗaɗen sa ba ya tura domin a shigo masa da atamfofin da zai dinga sayarwa.
Wannan kenan!
*Back to story!......🖊️*
*Follow me on wattpad@MaryamIbrahim244.*
*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*
_Short Story._*
*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*
*Whattpad@MaryamIbrahim244.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*LEMON KANKANA DA LEMON TSAMI*
*Kayan hadi*
*• Kankana*
*• Lemon tsami/* *Lemonade*
*• Sukari/sirof*
*• Flavour*
*YADDA AKE HADAWA*
*Uwargida za ki fara dafa sukarinki ya zama ruwa amma fa kada ki bar shi ya kone idan ya dahu shi ne abin da ake kira sirof sai ki ajiye a gefe guda. Shi wannan sirof din ya fi saukin amfani a kan ki yi amfani da sukari na ainihi.*
*Sai ki yanka kankanarki ki fitar da kwallayen sannan ki markade yadda za ta yi laushi sosai.*
*Sa ki samu kofin da kike hada lemo ki zuba a ciki sannan ki kawo lemon ana sayar da shi a manyan shagunan kayan masarufi idan kuma ba ki da shi za ki iya yin amfani da lemon tsami.*
*Idan kika matse sai ki ki tace shi da kyau ki tabbatar babu komai a ciki sai ki juye a kan kankanar nan sai ki dauko sirof dinki ki zuba ki kuma kawo filebo mai kanshin kankana ki zuba, sai ki juya ki sa a firiji don yin sanyi.*
*بسم الله الرحمن الرحيم.*
*EPISODE 16_20.*
🖊️Sai bayan ta sauke Hajiya Turai a ƙofar gidan tane kana ta fara tunanin ta yadda zata samu damar da zata aiwatar da ƙudirinta.
Sosai ta shiga tunani , ta dai san tsawon shekara ɗaya da wata uku da aurensu da Ƙasim sau ɗaya ne kachal ta taɓa zuwa gidan su.
Nan kuma wani tunanin ne ya koma tarbonta , ta tuna ko rasuwar mahaifinsa bata je gaisuwa ba.
Sosai ta shiga cikin ruɗani sai can kuma ta ce "dole ne ma yau ɗin nan mu shirya da Ƙasim.
Cike da ƙwarin gwiwa ta shiga gidan parking space ta nufa ta yi parking kana ta yi cikin gidan.
Karo na farko tun bayan aurensu data nufi kitchin da niyar ɗaura girki.
Sai da ta gyara kitchin ɗin sama sama ta wanke waƴansu kwanukan suma sama sama , kana ta ɗaura girki.
White fice da stew wacce taji kayan lambu, ta girka sannan ta janyo sabbin kuloli ta sanyawa megidan sannan ta sanywa Hajiya Umma a cikin wata haɗaɗɗiyar kula kana ta kawo maganin ta sanya a cikin miya ta motse.
Bedroom ta nufa ta cire kayanta ta ɗaura towel ta nufi ban ɗaki, ta silalo wanka wanda rabonta da wanka ta yi 2weeks kullum sai dai a feshe jiki da turare a bi hanya.
Gaban mirror ta zauna kana fara fente fuskarta da kayan shafa iri iri , daga bisani kuma ta janyo wata doguwar riga roba mai adon stone stone ta sanya ta janyo wani baƙin ɗankwali ta buga ɗauri ta feshe dukkanin ilahirin jikinta da turare.
Sosai kyaunta ya fito ta yi fess da'ita kamar a sace ta a gudu.
Parlour ta koma ta harɗe cikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Sai bayan sallar magrib sannan ya shigo gidan gabansa na faman buga wa.
A Parlour ya tarar da'ita ta harɗe sai faman ƙyalli takeyi, da saurinta ta miƙa ta tarbo shi.
Kana ta taimaka masa ya yi wanka , shi dai duk mamakin canjin da yasa mu ya cika masa ciki, amman ba damar tambaya yanzu.
Parlour suka fito ta gabatar masa da abinci , wannan karon mamakinsa kasa ɓoyuwa ya yi saida ya fito fili.
Ganin yana batun yi mata magana ne ya sanya ta saurin ɗaura farcen ta a kan bakinsa, kana ta zuba masa abincin.
Saida ya cika cikinsa maƙil kana ta gabatar masa da abin Hajiya Umma cike da tsantsar mamaki haɗi da murnar ta fara kulawa da lamarinsa har dana mahaifiyar sa ya fice da abincin daga gidan ya nufi gidansu.
Sashen Hajiya Umma ya nufa hannunsa ɗauke da basket bakinnan nasa ya kasa rufuwa dan tsananin murna.
Zaune suke a Parlour Hussaina da Maimunatu sai Hassana dake bedroom ita da Hajiya Umma.
Sallama ya yi amsawa suka yi su dukansu suna masu zubawa ƙofar shiga ɗakin idanuwa.
Karafff idanuwasa suka faɗa cikin nata, da hanzarinta ta miƙe tana me yiwa Hussaina sallama yayin da gabata ya dinga faɗuwa.
Gaidashi ta yi da hanzarinta kana ta fice daga ɗakin ta nufi sashen su.
Gaidashi Hussaina ta yi , amsawa ya yi yana tambayar ina Hajiya da Hassana?.
Nuna masa bedroom ta yi da hannunta kana ta ce "suna ciki kayan guga suke jerawa."
Harya miƙe da niyar shiga ɗakin saiga Hajiya Umma ta fito daga cikin ɗakin ,mace me tsananin kwarjini haɗi da kamala.
Ɗan basarwa ta yi sannan ta ce "an kaine a tafe da daran nan?."
Hassana ce data fito daga bedroom ɗin ta sanya dariya sannan ta ce "oh ba'a fadan sunan sa sai dai ace kaine?".
Filon dake gefensa ya janyo haɗi da wurga mata shi, da sauri ta kauce tana faman ƙumshe dariyarta.
Gaisawa suka yi sosai da mahaifiyar tasa da ƴan ƙannan nasa , sannan ya ya ce "Hajiya ga saƙonan inji ZULFA'U ta ce tana gaida ku."
Riƙe baki Hajiya Umma ta yi sannan ta ce "yau kuma?, Ikon Allah, ashe inada rabo da abin gidan ka."
Sosai kalaman suka girgiza sai sai dai ba halin nuna wa yanzunnan Hajiya Umma ta wanke sa.
Ɗan basarwa ya yi sannan ya kalli Hussaina ya ce "Husy yaushe zaki kawowa Matana ziyara?, inanan lalle daku ne kawai, gaba ɗaya sau biyu kawai kuka taɓa zuwa gida na."
Kallonsa ta yi ta ce "sorry big broz zamu zo insha Allahu karatu ne ya sanyo mu ganba wallahi."
"Tau Allah ya taimaka" ya faɗa yana me miƙewa tsaye, sallama suka yi sannan ya fice daga cikin gidan.
Buɗe kulolin abincin Hajiya Umma ta sanya Hassana ta yi sannan ta ce "ban yarda da abincinnan ba, don haka ɗaukesa kiji ki bawa alamjirai shinkafar miyar ki zubar da ita a magudanar ruwa."
Jiki a sanyaye ta miƙe ta yi abinda aka sanya ta, ita kanta bata lamunta da abincin ba.
Kallon Hussaini Hajiya ta yi ta ce "ina Uwata ?".
"Yaya na shigowa ta fice".
Gyaɗa kai kawai ta yi ba tare data ce komai ba.
Bayan ya koma gida take tambayarsa "Hajiya taci abincin kuwa?."
Gudun fitinarta ya sanya shi ce mata "eh".
Murmushin gefen baki ta saki kana ta ce "okey", haɗi da nufar bedroom.
Shima miƙewa ya yi yabi bayanta jikinsa sai faman rawa yake yi.
Washe gari.
Allah Allah ta keyi taji ankira sa a waya, amman har ya fice daga cikin gidan zuwa gurin aiki ba wani kira daya shigo cikin wayarsa.
Yana ficewa itama ta xari mayafi ta nufi gidan Hajiya Turai.
Yau kam duk wanda ya ganshi ya san yana cikin annushuwa kasan cewar fuskarsa a sake ba kamar kwanakin da suka shuɗe.
Yana tashi daga gurin aiki kai tsaye gida ya nufanto ransa wasai dashi, har matsuwa ya yi ya ganshi a gidan.
Sai dai me?
Tun a parking space ya fahimci babu mota ɗaya, ransa ne ya yi masifar ɓaci , kifar da kansa ya yi a saman sitiyarin motar yana me furzar da iska a bakinsa.
Ya jima a gurin kana ya ɓalle murfin motar ya fice daga ciki.
A Parlour ya zube yana me ƙara jin tsantsar tsanar halayen ZULFA'U a karo na farko daya fara daya sanin bijirewa maganar iyayensa.
"Tabbas sai yanzu na ƙara tabbar da karin maganar nan ta malam ba haushe da yake cewa *"ABINDA BABBA YA HANGO YARO KOYA HAU TSAUNI BAZAI GANSHI BA"* , ya faɗa a bayyane yana me ƙara miƙewa a saman kujera.
Har wuraren ƙarfe 9pm ba ita ba labarinta, zuwa wannan lokacin ya daina mamakin abin har yazo yana bashi tsoro "kar dai ace ƴar mutane wani abune ya sameta", ya faɗa yana me firi firi da idanuwa.
Wayarsa ya fiddo ya lalubo number wayarta ya danna mata calling sai dai harta tsinke ba ta ɗaga ba.
Sosai hankalinsa ya ƙara tashi, yana meci gaba da danna wa wayar calling.
Haka tayi ta ringing ba aɗaga ba.
A dai dai wannan lokacin kuwa suna can suna faman cashewa a tsakiyar maza, sosai take juya mazaunai cikin wata ƴar figegiyar riga wacce iya kacinta cibi, sai wanto data sanya fensir wanda ya kai har kan ƙafafuwan ta.
Gashin kanta wanda yake a kwance ko yaushe sai faman reto ya keyi.
Gaba ɗaya bata ji bata gani a wannan lokacin, cashewa kawai takeyi.
Yayinda Hajiya Turai ke zaune gefe sai faman kwankwaɗar win take yi lokaci lokaci tana sakin wani murmushi wanda na rasa gane na miye.
Ratsowa ya fara yi ta cikin mutanen dake tsaye suna faman yi mata liƙin kuɗi ya yin da waƴansu suke ta faman ɗaukan video a wayoyinsu.
Jin an riƙo hannunta ya sanyata saurin kallon wanda ya riƙe ta.
Saurin shigewa jikinsa ta yi tana mai sauke nishin gajiya.
Glass cup ɗin da ake miƙo mata ya sanya hannu ya ƙarɓa kana ya aza mata shi a saman bakinta.
Sha tashi sosai kamin ta yi gefe da kanta.
Miƙa mawa wanda ya miƙo masa cup ɗin ya yi sannan ya sangameta suka fice daga filin......🖊️
*Follow me on wattpad@MaryamIbrahim244.*
*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*
_Short Story._
*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*
*Whattpad@MaryamIbrahim244.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*LEMON KARAS*
*Abubuwan hadawa*
*Karas*
*Cittah*
*Sugar*
*Flavour*
*Yanda ake hadawa*
*Da farko zaki wanke karas dinki ya wanku sosai sai ki yanka kanana ki zuba a bilenda. Sai ki wanke cittah itama kiyanka kanana ki zuba a bilenda kisa ruwa ki markada da karas dinki, yayi laushi. Sannan sai ki tace kisa sugar da flavour. Ki juya sosai sai ki sa a firinji yayi sanyi.*
*Shi karas yanada kyau sosai wajen kara lafiyar ido*
*بسم الله الرحمن الرحيم.*
*EPISODE 21_25.*
.🖊️Ɗakin daya kama musu ya nufa da ita kai tsaye yana faman shashafa sassan jikinta, ya yinda ita kuwa sai faman ƙara shigewa jikinsa ta keyi.
Kallonsa ta yi da idanuwanta da suka fara canjawa cikin sarƙewar murya ta ce "Alh yaushe ka dawo?."
Janyeta daga jinsa ya yi ya hau rage kayan dake jikinsa , saida ya koma daga shi Sai ƴar ciki da three quater, kana ya zauna a gefenta yana shafar fuskarta ya ce "yanzu yanzun nan muka sauka, nasan kina nan shi'isa kai tsaye nayo nan, don kinsan na yi missing ɗinki irin sosai ɗin nan ", ya faɗa tana mai kashe mata ido ɗaya.
Haka wannan daren suka sheƙe ayarsu ba kunya balle tsoron Allah.
Ubangiji Allah ya tsare mana imanin mu, Amin ya Allah.
Gaba ɗaya hankalinsa ya gama tashi, ganin har 12am ba ita ba labarinta.
Zuwan sa kusan uku gidan Hajiya Turai sai dai har lokacin da yayi zuwa na uku ba ita ba labarinta a ƙargame ƙofar gidan take a haka ya juya ya nufi gida, cike da tashin hankalin ina ta nufa.
Gaba ɗaya ya rasa gunda zai sanya kansa, ba tada gurin zuwa sai gidan Hajiya Turai wacce tace masa ƙanwar mahaifiyarta ce.
Har ƙarfe 2am ba ita , kala yana kiran wayarta tana shiga har aka fara ce masa switch off.
Ƙarfe 6am ya koma jan mota ya nufi gidan Hajiya Turai, a ƙargame har yanzu garkar take.
Ya jima a wurin kana ya ja motar ya bar gurin.
Kai tsaye family hause ɗinsu ya nufa.
Sashen Hajiya Umma ya nufa hankalinsa a tashe yake sanar da'ita komai.
Itama jikinta ya yi sanyi saka yau , amman bata nuna masa damuwarta ba ta daice Allah ya bayyana ta.
Ƙarfe 12pm jirgi ya lula dasu cikin gajime rai daga Kano zuwa Lagos ita da Alh Sambo zai halarci wani taron ƙarawa juna tsayi na tsawon mako biyu.
A babban hotel ɗin dake cikin birnin Lagos suka sauka, sosai yana yin garin ya tafi da imaninta.
Wannan ne karo na farko data taɓa shiga garin.
Sabon sim card ta sanya a cikin sabuwar wayar da Alh Sambo ya mallaka mata a daren jiya, don ta manta da wayarta a gurin Hajiya Turai.
Gaba ɗaya Allah ya shafe mata sanin wai ita matar aure ce, sosai suke ɓarje lokacin su ita da Alh Sambon ta, wanda ke sakar mata maƙudan kuɗaɗe ita kuwa ta buɗe jikka sai kwasar nata rabo ta keyi.
★★★★★★
Har gurin jami'an tsaro case ɗin ɓatan ZULFA'U yakai amman har tsawon kwana uku bata ba labarin ta.
Duk ya fice daga hayyacinsa, ya yi baƙi ya rame sai uwar sumar daya tara a saman kansa, tunaninsa ɗaya ko a wanne hali take?.
Sosai Hajiya Umma ke kwantar masa da hankali , amman gaba ɗaya baya kamar wanda ake ƙara zautawa.
Yawo yake yi a cikin mota yana ci gaba da zagaye ciki da wajen Kano waiko Allah zaisa ya ganta , amman ko mai kama da ita bai gani ba.
A haka ya gaji ya koma gida ya zube yana mai sakarwa Hajiya Umma kuka kamar ƙaramin yaro.
Sosai hankalinta ya tashi ganin tilon ɗanta yana kuka a kan macce sai da bayadda ta iya sai addu'ar Allah ya bayyana masa matar sa ko hankalin kowa ya kwanta.
Sai da suka yi sati biyu a can Lagos kana da maraicen ranar litinin jirginsu ya sauka a filin jirgin saman malam Aminu kano.
A bakin ƙofar gidan Hajiya Turai motar Alh Sambo ta yi parking, kayan tsarabarta aka hau jibge mata , ta jima a cikin motar suna ci gaba da sharholiyarsu kana ta fito tana yauƙi tana ƙarawa ta nufi cikin gidan.
Da murna Hajiya Turai ta shiga tarbonta haɗi da ajiye mata kayan ciye ciye iri iri, tana me zama kusa da ita tana latsa fatan jikin ta.
Sai fadan ta keyi "kai lallai garin Lagos bana zan sauka, kinga yadda kika canja cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kuwa?".
Dariya suka sanya lokaci ɗaya suna taɓa wa kana ta ce "Hajiya ai dole ne kinga yadda Alh ke kula dani kuwa?, hummm ai ingaya maki abin baya ma faɗuwa sai kin gane ma idanuwanki zaki gasgata."
Sosai suka ci gaba da fira suna masu bude manya manyan jakun kuna da Alh Sambo ya shaƙo mata da kayan tsara ba, kama daga kayan maƙulashe har izuwa kan suturar sawa, uwa uba maƙudan kuɗaɗen daya keyi mata ɓari a ko wacce safiya waƴanda bata san a dadinsu ba.
Hajiya Turai sai santin kaya ta keyi tana mai yabawa Alh Sambo.
Ko a ranar a gidan Hajiya Turai ta kwana da zummar washe gari su bazama neman bokan da zaiyi masu aiki akan Ƙasim don a kulle masa baki, a cewar ta zata fara biyan Alh Sambo zuwa ƙasashen duniya da yake fita yawon shakatawa.
Washe gari haka suka shirya cikin ƙasaitacciyar shiga , kana suka haye saman sabuwar motar da Alh Sambo ya mallaka mata jiya, suka shiga cikin gari.
Sun jima suna yawon shakatawa sannan suka nufi wani ƙauye da akayi masu kwatance aikin bokan kamar yanka wuƙa yake.
Sosai suka ci tafiya sai da suka wahala sosai sannan suka isa gurin.
Daji ne sosai baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye ya yida bukkar bokan take a tsakiyar dajin sai uban layin da suka cimma wa.
A haka suka yi zaman jiran layi kusan magarib suka samu layin yazo kansu.
Shiga suka yi cikin bukkar da talkame ɗaya ɗaya kana da ashariya a bakinsu , wannan itace ƙa idar shiga wurin bokan.
Kallonsa su kayi da niyar yi masa bayani ya dakatar dasu ta hanyar ɗaga masu hannu.
Sosai suka yi mamakin jin yaddah yake zayyane masu abinda ke tafe dasu, har mamakin nasu ya bayyana a kan fuskarsu.
Umurnin zube masa kuɗi ya basu kana ya ce "kuje yau ɗin nan zaki ga aiki da cikawa, sai yadda kika yi dashi, ko kwanciya ya yi idan baki ce tashi ba bashi ba tashi a gurin, sai dai da sharaɗin zaki daina sallah harna tsawon makonni uku."
Cike da farin ciki ta amsa masa da angama, kana suka fito daga cikin bukkar hankalinsu kwance suka nufi gida.
A bakin ƙofar gidan Hajiya Turai ta yi parking sannan ta fita ta fito da tsarabarta ta sanya a bayan mota kana taja motar ta nufi hanyar gidanta ranta wasai dashi.
Cike da murna Ayuba ya buɗe mata get ɗin shiga gidan, yana mamakin a ransa ashe dama ba ɓata ta yi ba, bai ƙara mamaki ba sai lokacin da ya ga ta fito da jakun kuna daga bayan motar tana mai kwala masa kira ya shigar mata dasu.
Bayan ya gama shigar mata da komai cikin gidan, ya dawo bakin get yana neman layin uban gidansa.
Bugu ɗaya ya ɗaga wayar cikin sanyayyiyar murya yana me amsa masa sallamar da yayi masa.
Gaya masa dawowar Hajiyar gidan yanzunnan, a matuƙar ƙiɗime ya miƙe daga kwance da yake a saman carpet ɗin Hajiya Umma, yana me lalubar key ɗin motar.
Yana tafe yana gayawa Hajiya Umma anga ZULFA'U, cike da mamaki take binsa da kallo harya ɓacewa ganinta, addu'ar kariya taci gaba da yi masa daga sharrin makirar matar sa.
Tafiyar 40minutes sai gashi cikin 10minutes ya isa gidan.
Ko dai daita parking ɗin motar beyi ba ya fice da gudun tsiya ya faɗa gidan yana kwala mata kira, "Zuly Zuly Zuly!!!."
Turus ya yi lokacin daya ganta hakimce a saman kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya sai girgiza su take yi.
Kallonsa ta yi sheƙeƙe kana ta ce "lafiya kake kwalamin kira tun daga waje , sai kace wacce ta yi ma sata?."
Murmushin yaƙe ya saki sannan ya ce "lafiya qlw kawai nayi kewarki ne."
"Okey" kawai ta ce.
Sannan ta sake kallonsa ta ce "plx dear ɗan shiga kitchin ka samar min wani abu na sanyawa cikina , Allah tun safe rabona da abinci."
Jikinsa na rawa ya nufi kitchin ɗin yana me mamakin kansa na kasa yi mata musu da ya yi.....🖊️
*Follow me on wattpad@MaryamIbrahim244.*
*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*
*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*
*Whattpad@MaryamIbrahim244.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*LEMON ARDEB*
*Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya.*
*Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba. Wannan ardeb dai yana nan ne kamar lemun tsamiya. Kuma yana da alaka da mutanen Maiduguri.*
*A irin wannan yanayi da muka shiga ana yawan hada wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi.* *Akwai hanyoyi biyu da ake bi don yin wannan hadin.*
*KAYAN HADI*
*Tsamiya*
*Siga*
*Masoro*
*Kanamfari*
*Citta*
*Ruwa*
*A samu tsamiya a wanke tsaf ya fita sannan a jikata ta jiku sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari. Sannan a dora tukunya a wuta, bayan tayi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa. A dauko wannan jikakkiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan; Kuma sanya shi a gidan sanyi domin dandano ya fito sosai.*
*Daya hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace. A dora tukunya a wuta bayan tukunya tayi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Hadin ‘ardeb’ ya hadu*
*بسم الله الرحمن الرحيم.*
*EPISODE 26_30.*
🖊️Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya kammala ya ɗauko ya kawo mata har Parlour, cikin jin daɗi ta hau ci tana lumshe idanuwa "ba ƙarya ya iya girki ashe", ta faɗa cikin ranta.
Tana kammalawa ta miƙe ta nufi bedroom tana bashi umurnin kamin ta fito daga cikin ɗaki ya kankanta Parlourn ya yi shara da morping.
Jikinsa har rawa yake yi gurin sharar, yana kammala shara harya ɗauko bokitin morping kiran sallar magarib ne ya ratsa dodon kunnen sa.
Ɗan jim ya yi yana shawarar yaje ko ya bari harya kammala?, amman inaáh sai kawai ya ci gaba da morping ɗin.
Sai da ya mayar da Parlourn fess dashi sannan ya yi zaune yana jiran fitowar ta.
Wanka ta feso cikin ƙananan kaya sai ƙamashin turare dake fita daga cikin jikinta, fuskarnan tasha uban make up sai ƙyalli ta keyi.
Gurin zama ta nema ta zauna tana mai ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai faman ƙarewa Parlourn kallo ta keyi.
Ta gefen ido yake kallon kalar shigar da ta yi, yayinda ita kuwa ta yi kamar bata gansa a gurin ba.
Sunanan zaune kamar kurame a kayi