Share this page
3 / 4
kiran sallar isha'i. Kallonta ya yi a maraice yana neman yaji ta ce "tashi kaje". Lura da hakan da tayi ne ya sanya ta cewa "ɗan bara na gwada naga". Kallonsa ta yi kana ta ce "tashi kaje masallaci." Da hanzari ya miƙa, ai kuwa saiji ya yi ta ce "koma ka zauna ba inda zaka". Komawa ya yi ya zauna kuwa yana me faman sakin murmushin yaƙe. Sosai ta jinjina wa aikin bokan nata, ta saki murmushin gefen baki tana ayyana irin yadda zata wata ya da wannan damar data samu. ★★★★★★ Haka rayuwa ta yi ta tafiya, gaba ɗaya Ƙasim ya fice daga hayyacinsa idan ka ganshi kamar ba Ƙasim ɗin nan bane gayen gaske ba. Gaba ɗaya baya fita ko ina har gurin aiki ya daina zuwa bauta ka ɗai yake yiwa ZULFA'U, har wankin yanzu shi keyi mata , ita kuwa sai dai ta sanya ƙafa ta kalme ta fice yawon gantalin ta, wani lokacin ta dawo wani lokacin kuwa a can take kwana. Sosai hankalin Hajiya Umma ya tashi ganin tun ranar daya fice daga gidan ya kimanin mako biyu kenan amma bashi ba labarinsa, idan an kira sa a waya ma baya ɗagawa idan ancin sa'ane tana gidan take sa hannu ta danne wayar ta mutu, sai gashi da tafiya ta yi tafiya gaba ɗaya ma ta ɗauke wayar tasa ta kashe takai can ƙasan bed ta jefar da'ita. Kallon Hussaina dake zaune tana kuka ta yi kana ta ce "wai anya yaronnan lafiya take kuwa?". "Waye Umma?". "Wancen mijin Hajiya mana, rabon sa da nan tun lokacin da aka gaya masa dawowan ta ya fice da hanzari kamar ya kifa a ƙasa." "Ko mu shirya muje mu dibo ne?." "Zaku iya da fitinar matarsa?", ai Umma ba gurinta za muje ba gidan yayanmu za muje." "Tau bara su Uwata, {Maimunatu take nufi cox sunan mahaifiyarta ne hakan} ,su dawo ku shirya kuje dan Allah koda ta yi muku wata tijara karku bi takanta kuyi abinda ya kaiku kawai ku fito." "Karki damu Umma bara naje na shirya kamin su shigo." Yau ko da suka tashi da manyan baƙi suka ci karo, Hajiya Turai ce da ƙawarta Ruƙayya wacce suke cewa Ruka yau suka kawo masu ziyara, bakajin komai a ɗakin sai shewarsu a ɗakin. Cikin ƙasa ƙasa da murya Hajiya Turai ta ce "gaskiya na jinjina wa wannan bokan , ashe haka aiki ya ci ina can gida miƙe da ƙafafuwa?." "Uhummmm bari Hajjata, gaba ɗaya yanzu ko ina bana bari ya tafi, duk da sallah fa idan bance yaje ya yi ba wallahi baya yinta, kinga yadda dana buɗe masa idanuwana yake wani fizge fizge?, humm ai yanzu duniya take sabuwa a gurina, ke idan bada wannan ba Ƙasim ba zai barni na wataya ba, inajin yau saura 2days mu ɗaga zuwa ƙasar Amurika wajen shaƙatawa nida Alh na." Taɓewa suka yi suna ci gaba da buga shewa, ɗan ɗauke fuska ta yi sannan ta ce bara ku ga "Ƙasim!, kira ɗaya ta yi masa ya fito da hanzarinsa jikinsa har rawa ya keyi ya duƙa yana ƙara gaidasu Hajiya Turai kana ya kalleta ya ce "gani", "baka ga na yi baƙi bane da bazaka fito ka ɗaura masa girki da wuri bane halan?." Jikinsa naci gaba da rawa ya ce "afuwa ranki ya daɗe yanzu nake niyar fitowa." Ba tare data ce komai ba ta nuna masa hanyar kitchin miƙewa ya yi da sauri ya nufi kitchin ɗin, yayinda Ruka ta bishi da kallon tausayawa, ita dai haka kawai Allah ya sanya mata tausayin bawan Allahn nan ganin yadda Allah ya jarabcesa ta hanyar mace , ko macen shu'uma. Fitowar sa daga kitchin hannunsa ɗauke da tire saƙe da white rice da miya wacce taji naman kaza zallah sai tururi ta keyi , ya yi dai dai da sallamar da su Hassana su kayi a babban Parlour. Ko kallon gunda suke beyi ba ya nufi gabansu Hajiya Turai ya janyo Centre table ya ɗaura abincin a sama sannan ya miƙe. Karaf idanuwansa suka sauka a kan ƴan uwan nasa waƴanda ke kallonsa cike da tausayawa. Hussaina ce ta ce "Yaya halan ka yi rashin lafiya ne?, kallon ZULFA'U ya yi wacce gaba ɗaya ita dasu Turai suka zubo masu idanuwa. Ganin yadda ya kalleta a marece ya sanya su suma kallon gunda take zaune, ɗauke kanta ta yi daga gare su ta mayar kansa kana ta buga masa tsawa "kai maza jeka kawowa su Hajiya ruwa da jus mana kazo ka tsare mutane da idanuwa." Da hanzarinsa ya fice daga Parlourn ya nufi kitchin, fridge ya buɗe ya ɗauko masu ruwa masu sanyi da lemon kwalba ya ɗauro a kan ture ya kawo ya dire masu, ƙara kallon su Hassana ya yi waƴanda ke tsaye har lokacin suna kallon ikon Allah kana ya juya ya kalli ZULFA'U wacce ta mayar da hankalinta kan su Hajiya Turai. Sun jima a tsaye shima haka yana tsaye kansa a ƙasa ya yin da zuciyarsa yake jin tamkar ta buga ji yake yi kamar ya rufe ta da duka amman inaaah kome yayi niyar aikatawa sai yaji bazai iya ba. "To mukam mun wuce , Allah ya saukaƙa ya mayar wa mugu da muguntarsa", muryar Hassana dake wannan maganar ce ta daki dodon kunnen sa. Ganin har sun samu damar ficewa daga Parlourn ne ya sanya shi duƙar da kansa ƙasa, ji yake yi kamar ya bisu. Ganin yadda suka dawo a hasale ya sanya Hajiya Umma miƙewa daga wajen da take zaune ta nufi ɗaki. A tare suka sauke ajiyar zuciya baran ma Maimunatu da jikinta ya sanyaye. Jikinta ne ya bata ba lafiya ba, ta kalle su tace "lafiya kuwa!". "Hassana ce ta caɓe maganar da "ina lafiya kuwa Umma?, kinga yadda Yaya ya koma lokaci ɗaya kuwa?". Nan Hassana ta zayyane mata abinda idanuwansu suka gano. Shuru ɗakin ya ɗauka kowa yana tunanin abin. Miƙewa Umma ta yi sannan ta ce "banga ta zama ba ai, bara naje wajen Malam Nasiru ya sanya ayi masa saukar alƙur'anic ya tanya mu addu'a, don wannan kam sai Allah ya saka mana tsakaninmu da ita." Haka su Hajiya Turai suka wuni a gidan dukkanin ɗawainiyar su Ƙasim ne keyinta , sai bayan isha'i sannan suka fice daga gidan su dukan su har uwar gayyar. Suna ficewa shima ya fice ya nufi gidan Hajiya Umma, da kukan sa da komai yana bawa Umma haƙuri, janshi ta yi a cikin jikinta tana bashi baki da kuma tofa masa addu'oi a saman kansa, ba jimawa baccin wahala ya suresa...... 🖊️ *Follow me on wattpad@MaryamIbrahim244.* *ABINDA BABBA YA HANGO.......!* _Short Story._ *MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.* *Whattpad@MaryamIbrahim244.* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *YADDA AKE LEMON KWAKWA DA MASARA* *A yau Uwargida na kawo muku yadda ake sarafa Lemon Masara da kuma kayan hadi-hadi sa yadda zakiyi hadin a shakaratu lafiya.* *KAYAN HADI* *• Masara* *• Kwakwa* *• Sukari* *• Madara* *• Filebo* *YADDA AKE HADAWA* *Da farko uwargida za ki samu masara danya sai ki cire ta daga jikinta, sai ki dafa ta, ko kuma ki siya a wajen masu saida dafaffiyar masara amma su baki mai laushi. Idan kika dafa ruwan ya huce sai ki tsame masarar ki markada ta sannan ki tace.* *Sai ki sami kwakwarki ki cire bayanta sannan sai ki goga ta sannan ki markada ta ki kuma tace. Idan kika kammala tacewa sai ki sami mazubi ki juye dukkanin ruwan kwakwar da na masarar a ciki sannan sai ki sami madarar ruwa ki zuba. (amma ana iya sa madarar gari ) sai ki dauko sukari ki zuba a ciki. Sannan ki sa a cikin na’urar sanyaya abubuwa ta firinji ko ki samu kankara ki hada da ita. Idan ya yi sanyi sai a dauko a sha.* *ASHA DAƊI LAFIYA* *بسم الله الرحمن الرحيم.* *EPISODE 31_35.* 🖊️Kwanan sa uku a gidan yana jinyar haɗi da shan ruwan addu'oin da Malam Nasiru ke aiko masa safe da rana da maraice, sosai yake jin kamar ƙullin dake gabansa yana kwance wa, harya fara jin sahai dashi, duk da haka kuwa duk bayan kwana uku sai an kawo masa rubutun tsarin jiki. Sai da ya yi sati biyu a gidan har wannan karon ba ZULFA'U ba labarinta ko nemansa a waya bata yi ba, a ranar daya cika 2weeks ranar ya fara zuwa aiki, sosai ya taradda ayukka birjik a gabansa bugu da ƙari kayan da suka yi order sun iso tun last week dan ma Bash yana kula da waƴansu abubuwan. Yinin ranar kacokan a office ya yi sa, yana tashi kuwa ya wuce gidansu, sosai abinda ya faru dashi a baya ke damunsa har kunyar haɗa idanuwa dasu Hussaina yake ji uwa uba Maimunatu wacce mafi yawon lukutta a sanshen nasu take wuni tare dasu ƴan biyu dama sune kaɗai ƙawayenta. A ranar da suka fice daga gidan kai tsaye club suka nufa , suka sha suka ƙoshi kana suka wuce gidan Hajiya Turai. Tun a Parlour suka fara aikata masha'arsu su biyu Ruka da Turai Zuly na gefe tana kallonsu duk da ba cikin hayyacinta take ba amman abin na matukar baƙanta mata rai. Ta runtse idanuwanta kenan koda ta buɗe ta gansu a gabata a lokacin ne taji kamar ana ƙara tunkuɗa ta a kansu ba shiri ta faɗa cikinsu suka ci gaba da aikata muwar ɗabi 'arsu. Sosai suka ji daɗin hulɗar su da Zuly duk da wannan ne karo na farko, ko bayan dawowarta hayyacinta bata ji komai ba saima burgeta da abin yaci gaba da yi, tun daga ranar basu da aiki sai aikata ɓarna, da sunci sun ƙoshi suka kwankwaɗi kwayoyin su sai kawai su faɗa....... Wa iyazu billah! Ubangiji Allah ya tsare mana imanin mu ya karemu da aikata aikin dana sani, Allah ya kare mu da miya gun ƙaddarori, Amin ya Allah🙏🏽. Cikin ƙanƙanin lokaci Zuly tayi fice a harkar su ta neman jinsi da jinsi. Kasancewarta ta fisu diri da komai ya sanya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk wacce ke wannan harkar tasan da ita. Sai da ta yi sati uku sannan ta dawo gida, taci ka da mamakin ganin baya gidan daga baya kuwa ta yi watsi da lamarin. Zaune take a Parlour ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta dake riƙe da hannunta ne ta hau ruri ganin me kiranne ya sanya ta saurin miƙewa tsaye tana fiddo da idanuwa waje , gaba ɗaya ta manta da sunyi magana da Haruna kan zata bashi kuɗi sai yanzu data ga kiransa. Bedroom ta nufa ta janyo veil da jikkarta ta nufi waje. Key ta yiwa motar ta nufi hanyar gidan Haruna tana mai addu'ar Allah yasa lafiya don tun ɗazu yake faman kiranta a waya. Bakin ƙofar gidan tayi parking ta fito da sauri ta faɗa gidan. Suna zaune a tsakar gidan ya yinda Baby ke kwance ba lafiya , matar Haruna sai fifita take yi mata, shi kuwa waya ce a kunnensa yana ƙara danna mata calling. Ganinta kawai suka yi ta faɗo gidan yana tambayar lafiya kuwa. A tare suka miƙe, maryama na yi mata barka da zuwa tana mai shimfida mata tabarma a gefen wacce Baby take sama, ya yinda shi kuwa ya murtuƙe fuska kamar be taɓa dariya ba. "Ka zauna mana Haruna ka yimin bayani meya sami Baby?", ya faɗa yana me taɓa jikin yarinyar dake bacci. "Ke zan tambaya ai, fisabilillahi kin kyauta mana kenan?, Yau kusan wata biyu fa ina nemanki amman gaba ɗaya kinyi watsi da mu, tun last week nake neman layin ki bana samu sai yanzu dana je gidan Turai ta bani new number ki". "Ka ga Haruna ba wannan ba meke damun Baby?". "Zazzaɓi ne mai zafi ya rufe ta na kaita asibiti suka rubuto maguna to babu kuɗi hannuna ban samu siyo ba." "Ɗauki min takardar naje na siyo", ta faɗa tana zuge zip ɗin jakkata. Kuɗi ta ɗibo 10k ta bawa Maryama tana faɗan "a yi haƙuri dasu", kana ta ɗauko 70k ta miƙawa Haruna, "hamsin waƴanda kace, ashirin kuwa ka siyi ɗan wani abu, idan na fita zan dawo ma da gumi." Jikinsa na rawa yasa hannu biyu ya ƙarɓa suna ta zuba godiya a gareta. Ficewa ta yi daga gidan taje siyo maganin. Bata jima ba kuwa sai gata da maganin da kayan abinci niƙi niƙi, haka su Haruna suka dinga yin godiya sosai da sosai. Sai da ta jawa Haruna kunne a kan ya kula da Baby sosai duk abinda take so ya hanzarta kiranta idan tana ƙasar zata zo idan bata nan zata aiko mata dashi. Har bakin motar ta ya rakata sannan ya dawo cikin gida yana murna anan suka game da Maryama suka ci gaba da murnar na. Idanuwan ZULFA'U sun buɗe sosai da harkar neman ƴan uwanta mata haka kuma har yau tana tare da Alh Sambo wanda keyi mata ɓarin nera. Yau suna tashi daga club kai tsaye gidanta suka nufa, tun a Parlour suka fara aikata masha'arsu su biyu ne wannan karon ita da Hajiya Turai, sosai suka shagala har basu san lokacin daya shigo gidan ba. Jin gurnani kamar na dabbobi ya sanya sa saurin shigowa Parlourn sai dai me? . Abinda ya ganine ya yi masifar tada mashi da hankali, jikinsa har tsuma yake yi yayinda idanuwansa suke fitar da hawayen takaici da kuma mugun ganin da ya yi dasu. Juyawa ya yi ya fice daga Parlourn yana me sa key ya kullesa , bayan gidan ya nufa ya cire rigar jikinsa ya wurgar da ita kana ya hau iccen darbejiya ya tsinko sa da yawan gaske kana ya jiɗo. Kai tsaye Parlourn ya koma har lokacin suna nan yadda ya barsu, rufe idanuwansa ya yi kana ya dumfare su gadan gadan. Jin duka kawai suka yi a bayansu ba shiri suka rabu da juna, sai neman agaji. Sai da yayi masu lilis dukkanin fatar jikinsu saida ta kwalɗe sannan ya barsu. Ɗakinsa ya nufa ya ɗauko biro da talkarda ya rubuta mata saki uku kana ya dawo ya wurga mata taƙardar yana faɗan "kije na sakaki saki uku bani bake macuciya, makirar Allah wacce bata tsoron Allah, Ubangiji Allah ya yimin sakayya dake bazan taɓa yafe maki ba!." "Kinsa na bijirewa iyayena , na tabbata da badan ruɗina da kika yi ba, da bazan taɓa bijirewa iyayena ba, kije Allah ya fiki, dama hausawa sunce " *ABINDA BABBA YA HANGO YARO KOYA HAU TSAUNI BAZAI GANSHI BA!,* Irin abinda iyayena suka so nunamin kenan dan gane dake, amman da yake kin riga kin gama dani a lokacin bana ji bana gani , naƙi ƴar uwata na zaɓe ki sai gashi kin nunamin halin naku na karuwai." Ganin ta tsaresa da idanuwanta tana ci gaba da kuka ne ya sanya shi zare mata idanuwa "yace dan gidan ku ki daina kallona tunkan na ƙara maki wani, kiyi maza ki tada wannan almurar daga nan ku fice min daga gida tunkan na aikaku police wallahi." Jikinta na rawa ta hau tada Hajiya Turai wacce ta suman wahala. Sai da ta yayyafa mata ruwa kana ta farfaɗo ba shiri suka kwashi ƴan abinda ba'a rasa ba suka yi gidan Hajiya Turai.........🖊️ *Follow me on wattpad@MaryamIbrahim244.* *ABINDA BABBA YA HANGO.......!* _Short Story._ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 *MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.* *Whattpad@MaryamIbrahim244.* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *Ina miƙa godiya ta marar adadi zuwa ga👇🏽.* *80k* *M.K* *N yareemah.* *Yusuf Nuhu.* *Hussaini Abu Sameer.* *Allah ya biya ku da mafificin Alkheereensa, Alkheereen ku ga Doctor baya faɗuwa, godiya marar adadi.* *SPECIAL GIFT TO AREWA WRITERS ASSOCIATION😘.* *بسم الله الرحمن الرحيم.* 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 *LAST PAGE.* *EPISODE 36_40.* 🖊️Sosai hankalin Umma ya tashi lokacin daya zayyane mata abinda ya faru. Kallonsa ta yi ta ce "ai da ba sakinta zaka yi ba, irinsu kyaunta a dinga ɗaurasu a kan hanya ko Allah zaisa su dawo hanyar data dace, amman tunda harka zartas da hukuncin Allah yasa hakan shiya fi alkheree ya haɗa ka da mace ta gari." Da "Amin ya amsa", yana meci gaba da dana sani a cikin ransa , gaba ɗaya wata irin kunyar Umma yake ji, jikinsa a sanyaye ya ce "Umma dan Allah ki yafemin wallahi Allah ni kaina ba zance ga dalilin daya sa na nace mata ba." Ɗan murmusawa ta yi sannan ta ce "ni tun yaushe komai ya wuce a guna, ai dama *DUK ABINDA BABBA YA HANGO YARO KOYA HAU TSAUNI BAZAI GANSHI BA!*, tun lokacin daka zomin da zancen yarinyar hankalina be kwanta da ita ba, sai da nasa akayimin bincike aka zomin da labari marar daɗin ji dangane da'ita , amman naso na lurar da kai a lokacin ka ƙi, kaga ai kanka kayiwa bani ba, na tabbata har abada ba zaka taɓa samun macce ƙirki irin wacce naso ka aura ba, na jima banga yarinya wacce take da hankali da nutsuwa da kamala irinta ba, amman dama haka Allah ya nufa ba matar ka bace shi'isa, ni yanzu ba abinda ya dameni sai dai na ce Allah yasa hakan shiya fi alkheree a gareka dama mu baki ɗayanmu, ya baka mace ta gari, don kasan ba zaka zauna min a haka ba mata ba, gaka gasu ƴan biyu gwanda naji dasu su da suke mata." "Idan hankalinka ya kwanta nan da wata ɗaya sai ka fara neman matar aure don shine rufin asirin ka." Sosai kalaman Umma suka shigesa, bama kamar maganar auren da yaji ta sanyo tun yanzu, dan shi kam yana ga bashi ba wani aure , tunda har matan haka suke ko wacce muaradinta ta cutar dakai. Ya jima a gurin sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa tun na samartaka. Sosai su ƴan biyu su kayi murnar jin labarin sakin da yayansu ya yiwa Zuly, sunyi murna har saida Umma ta dinga yi masu faɗan su daina ba kyau. ★★★★★★ Sosai suka ji jiki don kuwa ba ƙaramin duka yayi masu ba, suna isa gidan Hajiya Turaia Parlour suka zube suna sauke numfashi, kiran Ruka Hajiya Turai ta yi bada jimawa ba saiga ta, zare idanuwa ta yi tana tambayarsu waya yi masu wannan ɗanyen aikin. Ba wacce ta bata amsa ,suka mika mata key ta jasu sai hospital, magunguna aka rubuto masu kana aka yi masu dresing ɗin ciwukkan. Gida suka dawo anan Parlour suka dinga jinya har lokacin da suka samu sauƙi. *Bayan wata biyu* Zuwa wannan lokacin komai ya wuce a gurin Ƙasim ba abinda ya ke gabansa sai neman na kansa. Umma kuwa tasa masa idanuwa akan batun aure shi kuwa gaba ɗaya kansa ya kwance , don shikam wacce zuciyarsa ke so yana jin kunyar tun kararta da zancen , gashi Umma ta sanyo sa gaba kasan cewar saura wata ɗaya bikin su ƴan biyu don tana don a haɗa da nasa. Yana kammala cin abinci ta kallesa sannan ta ce "naga kana yimin yawo da hankali fa a kan zancen da nake yi maka, to wallahi ka kiyaye ni". Duƙar da kansa ƙasa ya yi sannan ya ce "Umma na samu wacce nake so fa, kawai na kasa tunkarar tane da maganar". "Tome akayi kenan?, ai da'ita da babu duk ɗaya , gwanda ma kaje ka gaya mata yafi don nikam Allah na gaji da ganin ka haka , ace mutum kullum cikin azumi yake haba ka yiwa kankaWa'azi mana,." Ɗan sosa kansa ya yi sannan ya ce "tau Umma zan gwada nagani." Da haka ya miƙe ya nufi ɗakinsa yana tunanin ta gunda zai ɓullowa lamarin. Bayan ya dawo daga sallar isha'i ya harɗe cikin farar shadda sky blue sai tashin ƙamshi ya keyi, kai tsaye cikin gidan ya nufa gurin ƙanen mahaifinsa wato mahaifi ga Maimunatu malam Shehu. Bayan sun gaisa ne ya duƙar da kansa ƙasa kana ya hau koro masa bayani. Sosai ya ji daɗin lamarin ko bakomai za a ƙara ƙarfafa zumunci. Damar tuntuɓar ta ya bashi don suji ta bakinta. Cike da ƙwarin gwiwa kuwa ya nufi zauren gidan yana jiran Malam ya turo masa ita kamar yadda ya ce. Tun daga shigarsa gidan ya kira ta ita da mahaiyarta Inna Kulu yayi masu bayani. Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe lokacin da taji wai yazo neman ta. Cike da murna kuwa ta ɗan gyara fuskarta ta fita zuwa gurin da yake. Wacece Maimunatu?. Ƴa ɗaya tilo a gurin Malam Shehu da Inna hauwah, yarinya ce ƴar shekaru 18 da haihuwa, baƙa ce amman ba irin bakinnan sosai ba, ƴar guntuwa da ita , yarinya mai hankali da nutsuwa uwa uba ilimin Islama dake cikin kanta. Wannan kenan. Tana fitowa ta taradda dashi anan gurin da ya nema ya yi tsaye, gaidashi ta yi sannan suka yi shuru su dukan su. Sai bayan ƴan mintuna kana ya ɗago da kansa yana kallonta , cikin sanyin murya ya yi mata bayanin abinda ke tafe dashi. Ba wani ɓata lokaci ta yi na'am kuwa don dama tana son abinta bata tsaya wani ja'inja ba ta amince. Soyayya suke gudanar wa mai cike da tsafta da girmama jun Ba'a ɗauki tsawon lokaci kuwa aka sanya ranar aurensu lokaci ɗaya dana su ƴan biyu. Lokacin biki sai ƙaratowa ya keyi, shirye shirye akeyi ako wanne ɓangare baranma Umma da zata aurar da ƴara har uku. Ya sayar da gidan da suka yi rayuwa da Zuly ya siyi wani a kusa dasu Umma, gidane babba mai ɗauke da ɗakuna huɗu da babban Parlour, sai kitchin. Sosai shima ta nasa ɓangaren yake shirye shiryen bikin idan ka ga yadda yake rawar ƙafa zaka yi zaton wannan ne auren sa na farko. Yaune suka gudanar da wanki amarya, sosai aka yi shagali na ban mamaki, amare sunyi kyau abinsu idan ka gansu kamar ka ɗauke su ka tsere sai fitar da annuri fuskansu ke yi. Ranar juma'a aka ɗaura aure bayan an jiɗo daga sallar juma'a, ɗaurin auren daya samu halartar mutane da yawan gaske. Da daddare a kayi masu nasiha sosai kana daga bisani aka miƙa su a ɗakunan mazajen su. Tau sai muce Allah ya bada zaman lafiya. *Zuly.* Sosai take cin duniyarta da tsinke , yanzu bata ma cika zama a Nigeria ba , idan ka ganta yanzu ba zaka taɓa gazgata ita bace , lokaci ɗaya ta canja. Ko yanzu tafe suke ita da Alh Sambo da Hajiya Turai a cikin mota daworsu kenan daga Dubai yawon shakatawa, sun hau titi kenan wata babbar mota tabi takan motar su, koda a ka fito dasu daga cikin motar Alh Sambo rai ya yi halinsa itama Hajiya Turai ta rigamu gidan gaskiya Zuly ka ɗaice wacce gaba ɗaya ƙafafuwan ta sun samu matsala. Kai tsaye asibi aka kaita , dole sai da aka yanke dukkanin ƙafafuwan ta. Sosai duniya ta juya mata baya , bata da komai face ƴar keken da take kai a sama ita ke tuƙa kanta duk inda zata. *Tau Rabbu yasa muyi kyakkyawan ƙarshe.* Amarci ake ci ba kama hannun yaro, sunyi kyau sunyi haske sosai, suna ci gaba da rainon ɗan ƙaramin cikin dake jikinta. *Tau Rabbu ya raba lpy.* *TAMMAT BI HAMDALLAH.* *Duka duka anan nakawo ƙarshen wannan ɗan taƙaitaccen labarin ina roƙon Ubangiji Allah yasa abinda na rubuta al'umma suyi aiki dashi wanda bashi da kyau marar amfani kuwa Ubangiji Allah yasa ayi watsi dashi.* *Kura kurrain da na rubuta Ubangiji Allah ya yafemin.* *Kuyi haƙuri da yadda labarin yazo a ɗan tsito ba laifina bane lokaci ne be bani damar hakan ba, kuci gaba da bibiyata a ko ina.* *Wattpad@MaryamIbrahim.* *Facebook@مريم ابرهيم.* *whatsApp@* 08136402046 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and

Chapter 3 of 4