Share this page
na kunna miki ce gidanki ya ƙone, amman sai nake ganin kamar har da wutar lahira ce take jirana, ki taimake ni ki yafe min Namra, na ci amanarki, na han'ince ki, na cutarda ke” Wani kuka take marar murya saboda bata son Hajiya Umaima ta ji. “Na yafe miki Mardiya shi ma Asim na yafe masa, Allah ya masa rahama” Ta miƙe tsaye tana hawaye. “Ki rufa min asiri karki faɗawa kowa sirrin, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa na bar Katsina na dawo nan ga aiki saboda na canjawa kai na rayuwa, kuma na rufawa kai na asiri da abunda zan ci, na taimaki uwata da ƙannena” “Babu wanda zai ji, na miki alƙawari ba zan taɓa faɗawa kowa ba” Sai da ta share hawayen sannan ta fice. Sai dai hakan be hana Abdool gane ta yi kuka ba. Tana zaunawa kusa da shi ya kalleta ya ce “Kin yi kuka saboda kinji Asim ya rasu ko?” Da sauri ta kalleshi. “Ka sani kenan?” “Abnam har gobe kina son Asim” “No ba haka ba ne, kawai ina tausayinsa ne” “Tausayi ne silar so” “Ba irin wacan tausayin ba” Ya miƙe tsaye tare da ɗansa, ya ɗauki car keys ɗinsa ya fice. Tana zaune a gurin ta ji tashin motarsa. Lumshe ido ta yi ta buɗe sannan ta ɗago tana amsa maganar da Hajiya Umaima ke mata. “Lafiya Babangida ya tafi?” “Wai zai ga wani abokinsa ne, yace idan an ɗan jima kisa direba ya kai ni” “Okay toh taso muje ɗaki ga abincin nan Mardiya zata kawo yau mun ranar girki” “Wallahi Hajiya na ci abinci” “Ai nasan kin ci abincin, karki so ma min musu ba tarbiya ba ce” Da murmushi Namra ta tashi ta bita suka shiga ɗaki. Kamin ta gama cin abinci ayi sallah la'asar har ta tsawwala saboda tunanin Abdool yana can gida cikin ɓacin rai. Tana gama sallah la'asar ta yi ma Hajiya Umaima magana tasa ka direba ya kai ta gida. Bata same shi a falo ba, hakan tasa ta nufi ɗakinsa, kwance ta hango shi saman gado, Sultan na saman ƙirjinsa idonsa a lumshe kamar mai bachi. Tasan ba bachi yake ba, domin be saba bachin yamma ba, sai dai wannan baya rasa nasaba da ɓacin ran da take tunanin ya sawa kansa akan abunda har ga Allah ba haka yake ba. Be buɗe ido ba har ta ƙarasa kusa da shi ta zauna saman gado. “Ya Omri...” “Abnam please, bana son na fara ganin laifinki, bana son zuciyata na ƙonuwa akan ki ina gudun na fara ganin baƙinki, dan Allah ki fita sai zuwa anjima” Ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Kwantawa tayi a gurin, sai ya buɗe ido ya kwantar da Sultan gefensa na dama ya juya mata baya. Hakan ya bata damar matseshi sosai ta kurɗo hannunta ta ƙasan haɓarsa ta ɗora shi dai-dai zuciyarsa. “Namra tana nan Ya Omri kuma tana nan a bayan ka, tun bayan abunda Asim yayi min sai na daina ganin maza a mutane ina musu kallon wani abu daban, amman daga lokacin da na ganka sai na ganka a mutun cikakkensa, kai ne mutumen da ya tsayar da zubar hawaye a lokacin da nake tunanin hawaye ba zasu taɓa tsayawa ba, kai nw ka dawo min da farinciki na da kuma na iyayena, Wallahi na rantse maka da Allah babu son kowa a zuciyata sai kai, ka shiga ka mamaye ko ina na zuciyata, ban taɓa mafarkin samu miji irinka ba, saboda ina tunanin kamar ba ayi ni dan jindaɗin rayuwar aure ba. Sai dai bana ganin laifin zuciyar mai Imani idan har taji tausayin rai da zata koma ga Allah yana kirawa kansa hallaka, irin wannan tausayin na ke ma Asim ba irin wancan wanda kai kake tunani ba” A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannunsa ya shafa hannunta da ke ƙirjinsa. “Kinji bugun zuciyata...! Duk ranar da kika so wani ba ni ba mutuwa zan yi Abnam don't ever try it” “Ina son ka mijina, ina son ka sosai” Juyowa yayi ya rumgumeta yana sumbartar goshinta, lafewa tayi a ƙirjinsa, hannunta yana gurin kunnenta tana wasa da shi, ɗayan kuma yana cikin yatsunsa. Basu tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah magariba, shi ya fara tashi yayi alwala sannan ya dawo gurin gadon ya sumbance ta ya sumbaci Sultan. “Tashi ki yi sallah magariba ta yi” Sai da ya fice sannan ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki. Be dawo gidan ba sai da aka yi sallah isha'i, ko da ya shigo ita ta gama nata sallah ta shirya cikin wani shegen riga da ɗan guntun wando, ta kama kalabar kanta ta yi masa tukkuwa wato tayi parking ɗinsa guri ɗaya. Ko da ya shigo tana tsaye gurin dinning tana haɗa ma Sultan madara. “Wow” Ya faɗa sannan ya ƙarasa kusa da ita ya zagaye kwankwansonta da hannayensa yasa halshensa yana wasa da kunenta. “Ba zaki daina bawa yaron nan madara ba ko?” “Ya cika ci da yawa idan ba a bashi madara ba zai riƙa tsutse ni ne” Ya juyo ta ita ya ɗagata ya ɗora saman dinning ɗin. “Ke baki cin abinci ko?” Ta matso da fuskarta har hancinta na gugar nasa. “Ni abincin mutane nake ci” Ɗayan hannunsa tasa ya ɗauke ta cak ya nufi ɗaki da ita. “Shi kuma yaro na abincin aljanu yake ci?” Tasa masa dariya hannayenta lanƙame da wuyansa. Ko da wasa Namra bata yarda ta tayarda firar Asim a gaban Abdallah ko da kuwa muagunarwar da yayi mata ne zata faɗa gudun kar ya ce ta tuna da su, yadda yake nuna mata kishi akan Asim baya nuna mata haka akan Lamido, wata ƙila saboda Abbah ya rigaya haɗa auren Lamido da Aisha ne, ko kuma dan yana ganin shi Asim ya taɓa aurenta ne. Tayi zaton idan zata je bikin auren Aisha sai ya saka mata dokoki kamar yadda yake mata a duk lokacin da yasan zata je bikin da zata haɗu da wasu mazan ko da kuwa ƴan uwanta ne ko nashi, ko mata ne wani lokacin ya kan cilasta mata rufe jikinta wai hakan ne mutuncinsa da na gidansu da kuma nata, sai ya ɗora mata da cewar baya son tana sakin jikinta ko da kuwa cikin mata ne ƴan uwanta domin a yanzu akwai ɓata gari, wanɗanda siffarki kawai zasu gani sheidan ya ƙawata musu sha'awarki. Ciki farinciki da annashuwa aka yi bikin Aisha da Lamido, ranar Assabar aka ɗaura aurenta kuma ranar aka kai amarya, a unguwar sama road dake cikin sokoto, a lokacin Sultan na da shekara ɗaya da wata takwas, Namra kuma na ɗauke da wani cikin duk da bata haye Sultan ba saboda Abdool ya hana wai zai cutu. Duk wanda ya ga Sultan baya buƙatar tambayar ɗan waye ne, domin kamaninsa ɗaya da Abdool kai baka ce ma Namra uwarsa ba ce kasancewarta black beauty Sultan kuma fari tas kamar ɗan larabawa. Family Lamido da kuma na Namra yanzu an koma kamar ƴan'uwa, tun da har auratayya ya shiga ciki, sai dai duk da haka Abdool be taba barin Namra taje Kaduna da sunan gaishe da Neine ba, wai ai zata iya haɗuwa da Lamido tun da yana yawan zuwa akai akai. sai Neine da Uwani sun je Abuja lokacin da ta haifi ƴarta ta biyu wato Fatima, daman suna son zuwa yi mata godiya, ta jidaɗin ziyarar haka ta haɗa musu goma ta arziki lokacin da zasu tafi, har tana waƙen sai ta zo Kaduna idan tayi arba'in duk da tasan Abdool ba zai barta ba. Wasa-wasa Namra ta zama uwar mata domin bayan ta haifi Fatima sai ta ƙara haifo Juwuriyya da Mai sunan Ummi wato Zuwaira, wacce ake kira da Nasrin, sai kuma mai sunan Anty Amarya da ake kira da Iman, sai a haihuwarta ta shida ta haifi Muhammad Kabir. Ko da wasa ta dake su Abdallah rufe ta yake da faɗa wai bata san zafin haihuwa ba tana cin amanar ƴaƴansa, duk wani horo da zata musu sai idan baya cikin gidan, domin ji yake yi da abunsa wai ita zata iya gudunsa amman ƴaransa ba zasu guje shi ba, ita kanta yana nuna mata kulawa yadda yake treating ɗinta ba zaka ɗauka ita ce ta zuba masa waɗannan yaran ba, sai idan ka gansu. Babu ruwansa da ta haifi yara da yawa kullum kamar amarya take a gunsa, ita kuma tana kula da jikinta sosai da duk wani abu da tasan mijinta na so. ALHAMDULILLAH. Godiya ta tabbata ga Ubangijin da ya bani ikon fara rubuta littafin nan, kuma na kammala. Ina roƙon Allah ya yafe min kuraranda na yi akan ganganci ko rashin sani. Zan yi amfanin da wannan damar na roƙi yafiyar duk wanda na ɓatawa a cikin rashin sani ko da gangan, mai rai ajizine, masu cewa littafin nan yayi tsawo dole zai zo a haka kasancewar labarin ya kasu gida uku ne, kuma dukan abunda yayi farko zai yi ƙarshe. Ku yi haƙuri da yadda labarin ya zo muku, fatana dai a ɗauki darasin da ke a ciki, kuma a guji mugun hali ko ɗabi'ar da ba ta ƙwarai ba. Allah ka ɗora mu a dai-dai ka bamu ikon bin gaskiya da tsareta, ka tsaremu daga mugun ji da mugun gani da tsaka mai wuyar sani da aikin inda na sani... SON SO FISABILILLAHI, godiya ta musamman ga Zagon Ƙasa paid group 1 and 2, da male abroadcast. Sai mun hadu a littafina na gaba *HAFSATU MANGA* _Yarinyar ƙauye_ I LOVE YOU ALL ♥️🌹😍😘❤💜🌷✨ Zan yi missing ɗin ku 😭😭😭 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 71 of 71