shi ma zai mana amfani wajen ruguza Daularsu, Ke fa yanzu idon gani ce garemu ni da ɗan uwanki Safyan ki yi ƙoƙari ki share mana kukanmu.
"To Mom zan yi duk yadda ki ka ce.
ta yi dariyar farin ciki tare da cewa "Haka na ke so Ƴata, akwai wani turaren wuta ya na nan na ware miki shi daban, sai kin fuskanci ya kusa shigowa sai ki saka shi, kullum fa kar ki manta."
"Ai ba zan manta da irin wannan ba Mom don wallahi so na ke ya zama idan na ce yi sai ya yi idan na ce bari ya bari, so nake na zama me iko da kowa kamar yadda Mamarshi take.
daidai lokacin Laila ƴar ƙanwar Mom, ta shigo ɗakin tare da cewa "Mom ga ƴan ɗaukar Amarya."
da sauri ta tashi jiki na rawa ta fita domin tarbarsu.
Laila ta ce "Zakiyyat Manya Amarya a gidan Maalik Ɗiya Ɗaya Tilo a gidan Alhaji Boza Masu kuɗin Kasarmu idon ganinmu, sai ki tashi ki shirya daga nan ki yi can, wallahi sai na ji dama ni ce zan Auri me kuɗi."
Zakiyyat ta yi wani yauƙi yalala tare da yin farrr da ido, cike da jijjji da kai ta ce "Faɗi da ihu ki ƙara da wayyo, kuma sai gani sai hange Sama ta fi ƙarfin Zungura da kara, Maalik ya yi miki nisa Mallakin Zakiyyat ne."
Laila ta ce "Na sani ba sai kin faɗa ba, kuma ba zan fara haɗa kaina da ke ba, nidai fatana ki tashi ki fara shiri, na ƙagu in je in ga inda za'a kai ki wallahi.
Zakiyya ta murmusa ba tare da ta yi magana ba.
10:00PM
an kaita gidanta har kowa ya tafi gidan ya rage daga ita sai halinta, ta tashi ta yi wasu ƴan gyare -gyare da fece-fece sabi da shigowar Maalik.
tin ta na jira ido biyu har bacci ya yi awon gaba da ita ba ta farka ba sai 07:00 lokacin ta tashi ta ɗauro Alwala domin gabatar da Sallar Asbahi, bayan ta idar ta dudduba gidan ko Maalik ya shigo sai dai ba ta ga Alama ba, zuwa yanzu hankalinta ya fara tashi ta fara tunanin ko lafiya bai shigo gidan shi ba? haka tai ta saƙe-saƙe iri-iri gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi.
Yau fitar wuri su ka yi shi da Shahmeer domin tabbatar da ingancin abin da kamfunansu su ke yi domin kuwa cikin ɗan datsin nan in ba ta waya ba ba su bibiyi lamuran ba.
02:19pm wayarsa ce ta ke ƙara ya ɗauka ba tare da ya duba ko waye ba, ya yi sallama sannan ya yi shiru don jin waye zai amsa.
"Idan Me guri ya zo sai me tabarma ya naɗe, Shahbeer na dawo gareka, Yanzu Halimata ta na hannuna ina so ka dawo mini da ɗan cikinta domin shi ɗin mallakina ne, Da Halima da Ɗanta duk nawa ne.
"Waye kai??"
"Tambaya me kyau YaYanka ne ko kuma Babanka RAMADAN, Ramadan YaYanka, idan ka shirya dawo mini da ɗana zan faɗa maka inda za mu haɗu, idan kuma girman kai ya hanaka zuwa inda nake to ni baƙon sauƙi ne zan zo in sameka in karɓi abina.
"Ba na da wani ɗan-uwa in banda mutum biyar ka dai canja tunani.
"Dama in zaki ya girma ai ba dai Yaro ba Sai dai Baban Yaro, ka je ka tambayi A'i za ta gaya maka kowaye Ramadan.
"Ban damu da sanin ko kai waye ba, iya abin da zan iya cewa shine ba zan baka Shahzad ba don ba zan taɓa bari ka gurɓata masa rayuwa ba, bansan me Halima ta yi maka da ka tsinka mutuncinta ba ban san meke tsakaninka da ita ba amma ka sani yanzu ba da bace, ta riga ta zama wani kuiɓi na rayuwar Shahbeer don hakan idan ka sake ka taɓa mutuncinta lallai naka mutuncin zai zube kaf!!!!.
"Idan ba za ka iya dawo mini da Shahzad ba ni zan ɗauke shi da kaina, Halima kuma ta na gurina ko a yanzu idan na so za ta iya haifa mini wani Shahzad ɗin.
wani mugun tuƙuƙi Zuciyarsa ta ke yi cikin tsawa ya ce "Ƙarya ne!!!! ba za ka iya ba, Ƙarya ka ke, ƙarya ka ke, idan kuma za ka iya ka jarraba, Wallahi da sai ka gwammace wuta ka faɗa ta ƙonaka da irin ƙunar da zan yi maka, ni ba irin Mahaifiyata bane ni idan aka taɓa ni ƙonewa ake!!!!!"
"Ayya, ƙasa, ƙasa, ƙasa, mana Ɗan-uwana irin wannan fusata haka? to ai ko Boza ba fusatacce ne har haka ba, wayyoh amma fa na ji tsoro.
"Ɗaukata ka ke a matsayin mutum me sauƙin kai, za ka ga saƙona zuwa anjima a inda ka ke ta'addancinka.
daga haka ya katse kiran cikin matuƙar ɓacin rai.
ya na katse wancan kiran wani ya shigo, ba dan ya ga Mommy ce ke kira ba da ba zai ɗauka ba, ya na ɗagawa ya ji ta na kuka, hakan ya matuƙar ɗaga hankslinsa, dafa tebur ɗin da ke gabansa ya yi ya ɗan sunkuya cikin rawar baki ya ce "Mommy meke faruwa??"
Zakiyya duk cikin kwanakin nan cikin sharar Hanya ta ke don ganin shigowar Maalik amma sai ta ji shiru har zuwa yanzu da aka rufe kwanaki Biyar da yin Auren.
Yau da yamma ta na zauna a ɗan madai-daicin Falonsu Ta ji ana bubbuga ƙofa, ta tashi ta buɗe ba tare da ta tambayi ko waye ba, Gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin Maalik tare da wata tantiriyar Budurwa da an ganta anga cikakkiyar mara kunya mara tarbiya, sun wani maƙale juna, wani shegen kallo da take bin Zakiyya da shi ne ya sa cikinta ya fara kaɗawa.
Maalik ya ja hannun Budurwar su ka raɓe ta gefenta su ka wuce, bin bayansu ta yi har su ka shige Bedroom su ka turo ƙofa sai ƴan ƙananun surutansu ta ke ji.
Kamar ta mutu don baƙim ciki haka ta ke ji, ta ma kasa zama sai lelewa ta ke yi, ta na tunanin ta yadda za ta ɓullowa lamarin.
Halima a wani ɗaki wanda babu komai Ramadan da Mamarsa su ka jefata bayan sun ƙulle mata hannu da ƙafa, abinci a wuni sau ɗaya su ke bata shi ma ɗan kaɗan, sai ruwan da ko ƙishirwar lokaci ɗaya ba zai kashe ba, ta yi kukan har ta gaji ta dena sai dai na Zuci idanunta sun ƙeƙashe ta gama asalin galabaita, sai yanzu ta ke matuƙar Nadamar barin kusa da Babanta.
Baban Halima kuwa da ya tabbatar ita ta fita da kanta sai ya bar cigiyarta ya koma binta da Addu'a da neman kariya.
"Malika ba ta da lafiya ta na cikin Mawuyacin hali Shahbeer, mun rasa cikin da ke jikinta gashi har yanzu jininta ke zubarwa, Likitoci su na ta ƙoƙartawa amma ƙara yin baya lafiyarta ta ke, Shahbeer nima irin wannan Zubewar cikina ya yi kafin na samu naku, na tabbata Bokan da ya ke yiwa Alhaji Boza tsafi ne ya cinye Ɗan cikinta, ina tsoron mu rasata itama.
Zamewa ya yi har ƙasa ya durƙusa akan guiwoyinsa, da kyar ya finciko magana "Mommy Malika Me ta yi musu da baza su ɗau Fansa akaina ba sai akanta??"
"Ban sani ba Inya, Ni dai ina roƙon Allah ya bata lafiya kawai, zalumcinsu ba sai wanda ya yi musu laifi ba.
ya kasa cewa komai sabi da wani irin turnuƙu da Zuciyarsa ke yi lokaci ɗaya kansa ya fara wani mugun ciwo wanda ya sa idanunsa su ka fara gani dishi-dishi, tinda ya durƙusa ɗin ya kasa tashi har bayan wani lokaci me tsayi Allah ya jefo Shahmeer Office ɗin.
cikin sauri ya ƙarasa ya na yi masa sannu kafin ya temaka masa ya miƙe sannan ya ɗora hannunsa kan kafaɗarsa su ka fice zuwa wajen Mota.
Kai tsaye Asibitin su ka nufa sai dai ba damar ganinta.
iya ƙololuwar tashi hankalinsa ya gama tashi, izaya biyu ce ta haɗe masa ga Ramadan a gefe ga Rashin lafiyar Malika.
Sai dare Mommy ta lallaɓa su su ka koma gida sai dai dukansu cikin mugun yanayi su ke.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
INDO
[1/4, 11:48 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
33
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
washe-gari da wuri ya fito don halartar Asibitin, a falo ya tarar da Ma'arufa ta na ƴan-aikace-aikace Shahzad ya na kan kujera a zaune ya yi shiru sai tunane-tunane ya ke yi. gaishe shi ta yi ya amsa sannan ta ce "Jiya Shahzad kuka ya yi mini da daddare."
shafar kansa ya yi gami da cewa "Ohh." ya ƙarasa inda Shahzad ɗin ya ke ya zauna kusa da shi sannan ya ce "Shahzad! tunanin me ya ke??"
tattaɓe baki ya yi zai yi kukan ya yi saurin janyo shi jikinsa ya na rarrashinsa "Me ya sa shi kuka Shahzad?"
cikin Muryar shagwaɓa ya ce "Inna, Mammi (Malika)" Murmushin ƙarfin hali ya yi gami da cewa "Za su dawo in sha Allah zuwa anjima zan dawo da su, nima ban yarda da zaman Asibitin nan ba, kwantar da hankalinka ba Mommy ta na nan ba?"
ya turo baki tare da cewa "Zan je." "Ohh Ashsha Shahzad ba daɗewa zan yi ba nima kuma zan wuce wani gurin ne, ka yi haƙuri ka ji Ɗana." "Mommy baya nan. kallon Ma'aruda ya yi tare da cewa "Mommyna ba ta na to ina ta je?" Ma'arufa ta ce "Tin sassafe ta fita kuma ba ta sanar mana inda za ta je ba."
miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita gami da cewa "Okay"
Asibitin ya nufa, acan ya tarar da Mommy tare da Shahmeer da Shahzaib, sai lokacin hankalinsa ya kwanta don kuwa ya yi tunanin wani gurin ta tafi.
Tin a lokacin ya tuburewa Baba da Mommyn akan su mayar masa da ita gida dole su ka Amince masa tare da yi masa Alƙawarin da yamma zuwa dare za ta dawo gida.
sai da ya ji haka sannan ya wuce gidan Alhaji Boza.
Shahzaib tare da Shukriya su ka shigo sashen Mommy hannunsu sarƙe da na juna, har zuwa lokacin Ma'arufa da Shahzad su na nan sai rikici ya ke mata ita kuma ta na ta ƙoƙarin rarrashinsa.
da sauri Shukriya ta zame ta ƙarasa inda su ke ta na cewa "Ɗanlele meke damunka?"
Ma'arufa ta murmusa gami da cewa "Ina kwana; Wallahi dai tin da su Mommy su ka fita ya ke rikici gashi Ya Shahbeer ma ya ce ba zai je da shi ba."
Shukriya ta ce "Kashh, gaskiya sai ka je dashi za mu tafi."
Shahzain ya ce ''Amma mu da za mu je Asibiti?"
da sauri ta ce "A'a ba wannan maganar Asibitin ba naku bane?, ai kuwa yaro kamar ka je ma kwantar da hankalinka.
Shahzain ya rausayar da kai ya ce "Sai ki tashi mu wuce ai."
Shahzad kuwa tini ya saki ransa ya fara dariya.
kafin su tafin Shahmeer ya kira wayar Shahzain ya sanar masa kar su zo in ji Mommy Ankusa Dawo da Malikan gida.
bayan ya katse kiran ya yi dariya tare da cewa "To Mrs Gigi ance kar mu je." baki ta saki kafin ta ce "Da gaske wai?" "Au tambayata ma ki ke yi?" "A'a ka yi haƙuri, amma gaskiya za mu fita ni da Ɗanlelena, dama Matar YaYan Fatima ta Haihu yau kwana uku to zan je barka."
Shiru ya yi mata ya nemi guri ya zauna, Ya maida kallonsa kan Ma'arufa tare da cewa "Arufa ina ƙannenki da Mamarku? kwana biyu ni kam ban je ziyara ba."
murmushi ta yi tare da cewa "Suna lafiya, kullum in mun yi waya Umma ta na ce mini in gaida kowa da kowa."
"To ai ba kya faɗe."
ta ce ''Ina faɗawa Mommy da Inna dai."
ya ce "To ai kin yi ƙoƙari, Abbanki fa har yanzu bai dawo ba?" ƙasa ta yi da kai cikin sanyi ta ce "Eh" ya ce "Allah zai dawo da shi kwana kusa, mu dai ci gaba da Addu'a.'' ta gyaɗa kai ba tare da ta yi magana ba.
Shukriya ta ce "Ba ka ji ba, Wai za ka barni in je barkar kuwa?" kai tsaye ya ce "Ba za ki je ba." ta rausayar da kai ta ce "Shi kenan, idan ƴar ta girma sai in ganta." ya ce "Ku ta shafa ke da Fatiman taki."
Shahbeer da ya isa Gidan Alhaji Boza me Gadi ya sanar masa baya nan don haka ya juya akalar Motar zuwa gida, lokacin da ya dawo su Mommy ma sun dawo.
zama kawai ya yi a gurin amma hankalinsa ya yi nisa, Mommy ta ce "Inya tunanin me ka ke ne?"
Girgiza kai ya yi alamar a'a, ta ce "Bai kamata ka dinga ɗorawa kanka tunane-tunanen da za su illata ka ba, ya kamata ka dinga manta wasu abubuwan, indai Malika ka ke tunani ta ji sauƙi sosai yanzu abin da ya rage ƙwarin jiki kawai duk wata matsala babu ita yanzu, sai dai mu yi Addu'ar Allah ya karemu da kowane irin sharri."
ya amsa da "Amin" sannan ya ci gaba da cewa "Mommy ki na da wani Ɗa ne bayanmu??" cike da mamaki ta ce "Ɗa kuma??" "E, wai sunansa Ramadan na rasa ko ta yaya muka haɗa alaƙa da shi."
girgiza kai ta yi ta ce "A'a gaskiya ni bani da wani Ɗa in ba ku huɗu ba Haihuwata Ɗaya sai kuma Ɓari sau Biyu."
"To kuma Babanmu fa? ko dai Mamar su Safyan ta na da wani Ɗan?" "A'a gaskiya ta yuwu ƙarya ya yi maka.
zuwa yanzu lamarin ya fara bashi tsoro, "Momma!! ki tuna dai, idan ba jininku bane Ramadan ɗin ta yaya Shahzad zai yi kama da ni??, Dole duk inda ta je ta zo Shahzad jininmu ne Mama, ki tuna don Allah kuma fa cewa ya yi in tambayeki ke kin san shi. "Ni??" ta yi tambayar gami da nuna ƙirjinta. Ya ce "E, haka ya ce." shiru ta yi ta na Nazari kafin ta ce "Shahbeer!! kenan da gaske Shahzad ba ɗanka bane?" gyaɗa kai ya yi kafin ya ce "Haka ne , ranar da Maalik da Safyan su ka gaiyaceni domin tattaunawa, a tsakiyar Hanyata ta dawowa na hangeta tin kafin na ƙaraso wajen har na iso sai na fahimci mutumce a gurin, da na duba na ga ƙaramar Yarinya ce kuma ta na cikin halin neman temako shine na kaita Asibiti, acan na haɗu da wani Abokin faɗana tin na yarinta, Kamal ya ke sanar mini cewa wai na yi mata fyaɗe, tin daga lokacin na fahimci Sharri ake son yi mini ta hanyar nan, amma duk wannan bai dameni ba akan zarafin yarinyar da aka ci; kasancewar ko ta farka ba ta san kanta ba bare danginta ya sa na yanke hukuncin kawota nan gidan da zummar idan na samu danginta in maida ita garesu, sai gashi kafin lokacin Allah ya jarrabeni da soyayyarta har naji ba na son rabuwa da ita, kuma na yanke hukuncin karɓar laifin bisa tunanin ko da na ce ba ni bane ba za a yarda ba domin kuwa ba dalili ko Hujjar da za ta nuna ban aikata ba, sai kuma a wannan datsin Ramadan ya shigo rayuwata har ya ke barazanar rabani da Shahzad sabi da ɗansa ne, a yanzu haka Halima ta na hannunsa."
Hawaye Mommy ta shiga goge wasu su na ƙara zubowa, cikin tausayin ɗan nata ta ce "Allah ya yi ka me karɓar ƙaddara duk yadda ta zo maka, wannan babbar kyauta ce Allah ya bani, Don Allah Mukhtar ka ceto Yarinyar nan kar ka bari wani abin ya ƙara samunta, kuma ban yarda a rabamu da Shahzad ba don har yanzu ɗanka ne shi." jinjina kai ya yi ya ce "Umma har yanzu ba ki tuna kowaye Ramadan ba?"
ta gyaɗa kai alamar "E" miƙewa ya yi zai bar gurin har ya fara tafiya ta dakatar da shi da cewa "Ya Sunan Mahaifiyarsa?"
''Na manta!" ya faɗa tare da ci gaba da tafiya, cikin sauri Shahzaib ya ce "Furairatu" "Furairatu?" a razane ta maimaita sunan cikin sigar tambaya, hakan ya sa Shahbeer ya dakata da tafiyar.
miƙewa Mommy ta yi sannan ta ce "Furairatu Matar Babanku ce, lokacin da ya Aureni ta na da Juna biyu, kuma da shi ta fita, bai daɗe da Aurena ba ya saketa, ita a tunaninta ni ce na sa ya saketa ba shi yasa ta ƙuduri cutar da ni, ashe da gaske take ba da wasa ba?? ashe ba ta manta da ni ba??"
Murmusawa Shahbeer ya yi tare da cewa "Ya yi, Haka na ke son ji, wato dai Ɗan-uwan Safyan ne? Okay ba komi, Sai ya haƙa ya ga in zai samu ruwa."
Kasa magana Mommy ta yi cikin sauri-sauri ta wuce samanta.
Shahzaib ya ce "Allah Sarki Bawan Allah, ya zo a zamanin da ba za'a iya saurara masa ba, har na ji tausayinsa." Shahmeer ya ce "Ni ai ba wanda na fi tausayawa Irin Babanmu, bansan adadin Alhakin da ya ɗauka ba, kuma duk wani bala'in da ya samemu shine ya jawo mana da kanshi.
Shahzain ya ce "To Allah ya kyauta."
Zakiyya tin ta na ganin abin na Maalik wasa ne har ta gane da gasken fa ya ke, iskancin safe daban na yamma daban, salon na yau ya bambanta da na gobe.
yau dai ta gaji da halin nashi don haka ta yanke hukuncin tararsa ta yi masa magana.
Sai da ta bari ya fito zai yi waje sannan ta tare masa hanya cikin tsiwa da bala'i ta ce "Ya kake da suna Maalik ka ke kowa??, na gaji da wannan iskancin naka da rashin mutunci ka ji ko??, indai ka san ba Aurena za ka yi ba me yasa ka yarda aka ɗaura? to wallahi ni ba me ɗauka bace, ba zan iya zaman wannan wulaƙancin ba."
cikin ɓacin rai da takaici ya ce "Ke ki bini a hankali kafin na lahantaki yanzun nan, har ni za ki tarewa hanya ki na gaya mini wata maganar banza, ai dama na bari a kawo ki ne don na gana miki azabar-da da kanki za ki ce na sake ki, Tinda YaYanki ya rabani da Shukriyata ku ma sai na rabaku da farin cikinku." "Kutumar-uba!!" ta faɗa cikin sigar jinjina maganar tashi. ci gaba ta yi da cewa "Lallai Maalik kai mahaukaci ne, ina ruwana da su da za ka ɗau fansarka akaina?? ka je ko kashe Shukriyan ka yi mana ni ba ruwana amma wallahi ka den......" wani hamagon mari ya zuba mata, ta ɗago a fusace ta ce "Ni ka mara??" wani marin ya ƙara afa mata wanda ya sa bakinta ya kulle na ɗan lokaci, kafin ta ce wani abu ya fara jan hannunta kiiiii, sai da ya kaita wani ɗaki dake can ƙuryar gidan sannan ya jefata ya kulle ƙofa ya koma ya nemo lafiyayyar igiya ya ɗaureta tamau har bakinta sannan ya fice ya bar gidan.
Malika ce kwance kan gadonta ta yi lakur sai tunani ta ke yi, irin muguwar wahalar da ta sha har yanzu ta na jin motsinta, ko tashi zaune sai ta yi mazantaka sannan ta ke iya yi, jikinta ya yi ruɓus kamar wadda aka zarewa Laka. Da sallama ya shigo ɗakin bai jira ta amsa ba ya ƙarasa inda ta ke kwance ya zaune gefenta, cikin tausayawa ya ce "Ya jikin?" Kamar za ta yi kuka ta ce "Da sauƙi" shiru ne ya biyo baya har na ɗan wani lokaci.
ya zuba mata idanu kamar zaiyi kuka, Zuciyarsa ta gama karyewa, "Malee ki yi haƙuri fa Don Allah.
Murmushin ƙarfin hali ta yi kafin ta ce "Na me? ka yi mini laifi ne?" "A'a, amma dai ta sanadina ki ke shan wannan wahalar, asali da Babanmu bai yi wannan kuskuren na shiga lamarin tsafe-tsafe ba da ba lallai hakan ta faru ba, kuma nasan ni su ka nema ba su samu ba shine su ka ɗauki Ɗanki.
ta girgiza kai, duk da itama abar a tausaya mata ce amma ta na bala'in tausayinsa ba ta damu da ta-ta rashin lafiyar ba akan yadda ta damu da damuwar da ya ke fama da ita. fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Komai rubutacce ne daga Allah, ba wanda ya isa ya canja hukuncin Allah, ko da ban Aureka ba ma idan ya so hakan za ta faru da ni, kar ka ɗauki hakan a matsayin laifinka ko na Mahaifinka, ni dai fatana Allah ya dawo maka da farin cikinka, Ba na son ganinka cikin damuwa."
Murmushi ya yi tare da cewa "Na san haka ne amma ba zan yi shiru ba dole ne na nemi yafiyarki kuma na nemawa Mahaifina." "To ai dama a koda yaushe cikin yafe muku nake kuma ku yafe mini Don Allah ba don Halina ba, nima na san ba za'a rasa kuskuren da na yi muku ba, Yauwa dama ina son tambayarka akan Halimatu na ga har yanzu ba ta dawo ba.
Idanunsa sun ka ciko da ƙwalla Rauninsa ya ƙara baiyana akan fuskarsa, numfashi ya ja ya sauke tare da nannauyar Ajiyar Zuciya, cikin son kwantar mata da hankali ya ce "Halima ta na lafiya kuma in sha Allah za ta dawo, Ta na gurin Ɗan-uwana Ramadan, Babanmu Ɗaya da shi."
ta yi murmushi kafin ta ce "Don Allah ka inganta rayuwarta ka ga ba ta da kowa sai Allah sai kai sai Babanta, ni kam Alfarmar da na ke nema a gurinka ka daure ka bar mini Shahzad kar ka bari Baban shi ya ɗauke shi, ban sani ba ko ba zan haifi wani ɗan ba."
cikin sauri ya ce "Malee dena irin wannan maganar kar ki sa hankalina ya kasa kwanciya, idan ba ki haifi wani Ɗan ba wacece za ta haifa Mini me sunan Ummata?, ba na son ji kar ki ƙara faɗe."
gyaɗa kai ta yi alamar "To" ya ci gaba da kwantar mata da hankali har bacci ya kwasheta.
Wayarsa ce ta yi ƙara ya yi saurin kashe kuwwar, sai da ya fice daga Ɗakin sannan ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 30