mota a watan da ya gabata direba me Lamba 37 sai na lura ya sauka daga kan titinsa sai naga tafiyar ta shi tana ƙara nesanta da titi, ina kan bincike ban gano abin da ke faruwa ba sai na ji kira a wayata da na ɗauka suka ce min kidnappers ne sun ɗauki Direban wai in sanar muku kuma in tura lambarku za ku yi magana to ni dai ban tura lambar ba na ce sai na tambayeku na ji."
Dukansu har Mommy da Inna da Malika kan Shahbeer su ka maida kallonsu cike da son jin abin da zai ce ga mamakinsu sai suka ga ya yi murmushi wanda baya baiyana manufarsa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ohh Ba komai a basu lambar sai mu yi magana."
Shahzain ya ce "Okay ka ba su Number sannan idan sun ƙara gaya maka wani abin sai ka sanar mana."
Salman Audu ya ce "To Ranka ya daɗe sai anjima na gode."
Shahzaib ya ce "To fa, abin da mu je ji a nesa yau gashi a kusa da mu."
Mommy ta ce "Hasbunallah! su kuma me suke so a gurinku? ba na son rayuwarki ta cutu fa don Allah meye haɗinsu da ku da za su ɗauki bawan Allah bai ji ba bai gani ba."
Shahmeer ya ce "Ni iyalinsa ma na ke ji, ba mu san abin da za su yi masa ba dan ba su da imani har kashewa su na yi, ina tsoron ta sanadinmu su kashe rayuka"
Shahbeer ya ce "Allah na nan ai Jariri, ba na son hakan ya dameku, Yauwa da daddare zan haɗu da wasu baƙi dan haka zan fita ni kaɗai Shahzain ya zauna a gida tare da Mommy ku kuma sai ku fita Zuwa in da ku ka ce."
Shahzaib ya ce "To Boss."
Shahzain yace "Inya ka san ni da son yawo ka je da ni mana?"
Murmusawa ya yi gami da cewa "Auta kai fa ɗan drama ne wani son yawo gareka kai da ba yaro ba?"
"Amma ai Auta ne ni.
Malika ta yi saurin cewa "Ka fi Autan, ni takaici ma na ke ji idan na ji ana kiranku da sunayen yara kuma duk Mommy ce ta janyo hakan."
Mommy ta murmusa gami da cewa "Su kaɗai gareni fa Dr Malika."
Shahzaib ya ce "Bar shashasha ba sai kin yi mata bayani ba, an faɗa ki yi maganin abin."
ta ce "A dai yi Zuciya a girma sai zafin rai ga tarin Ƙuruciya, ai sunan nan da irinmu yara ya dace ba ku iyayen su wance kakan-nin su wane ba."
Shahzain ya ce "Ke dai kin cika shiga shara ba shanu wallahi."
Shahbeer ne ya ce "Ya ishe ni haka ku yi min shiru, ba kwa iya riƙe addu'a a bakinku na wani lokaci sai surutun jaraba ko gajiya ba kwa yi.
shirun su ka yi dan shi ya fi dacewa da su.
08:00PM
tare su ka fito falon sun haɗe cikin dakakkiyar shadda fara da hula, komai iri ɗaya sak sun yi matuƙar kyau kamar ka sace ka gudu.
Tin da su ka fito Idon Dr Malika ya na kan Shahbeer sai murmushi ta ke saki, shi kuwa bai san ta ba yi ba, ba ko da yaushe ma yake ɗaga idonsa ya buɗe tangaras ba bare ya dinga kalle-kalle har ya kalli wata mace duk hakan ba ɗabi'a da tsarinsa bane.
Da Addu'a Mommy ta bi su har suka ɓacewa ganinta, Malika kuwa ta kasa janye idanunta daga kan hanyar da su ka bi Mommy ce ta ce "Malee akwai wata damuwa ne??"
sirrintacciyar ajiyar Zuciya ta sauke sannan ta ce "A'a Mama ba komai kawai na ga sun yi kyau ne."
Mommy ta murmusa ta ce "Ma sha Allah, ni ma na ga hakan.
ɗan murmushi kawai Malika ta yi ta kasa cewa komai.
Sai da Shahzain ya tabbatar sun bar gidan sannan ya koma ciki.
11:20pm
tafiya me kama da sanɗa Mommy ta ke yi jikinta ya yi sanyi ƙalau, Inna ta tarar a falo ita kaɗai ta zuba tagumi cikin tunani me zurfi.
Danne ta-ta damuwar ta yi sannan ta ce "Innata meke damunki ne??"
"Abubuwa da yawa"
ta bata amsa cike da damuwa.
zama Mommy ta yi a kusa da ita sannan ta ce "Nima damuwar ce ta fito da ni yanzu, amma kin ga ban zauna ina ta tunani ba hakan na haifar da matsala musamman ga manya Inna, amma dai gaya min abin da ya dameki indai zan iya ni me yi miki maganinsa ce."
ta ce "Da farko dai har yanzu wannan uban zurfin cikin da tsaurin halin bai dawo ba, na biyu kuma idan na ajiye abu a kicin ko wani gurin sai in ga babu, har kayan abinci sai in ga an ɗibaa na rasa waye ya ke ɗauka, ni dai ba na ɗaukar abin wani kuma ina tsoron a yi tunanin ni ce na ke ɗauka amma na san da ke da iyalinki ma ba za ku ce hakan ba sai dai duniya ta zargeni."
tattausan Murmushi Mommy ta yi kafin ta ce "Inna kwantar da hankali, a gidan nan kinsan mutane taruwa suke suna karɓar tallafi kullum ba fashi to ko ma waye ya ɗauka ya na buƙata ne dan haka ba buƙatar ki tashi hankalinki ko ranki ya ɓaci sabi da hakan, shi kuma Shahbeer zai dawo in sha Allah nima fitowa na yi na duba ko ya dawo ɗin.
"To Allah ya sa, shi kuma ɓarawon Allah ya shirya shi.
Mommy ta ce "Amin."
Shahbeer ne zaune a Kujerar da ke kallon ta Dr Kamal idanunsa a ƙasa gaba ɗaya ya ƙagu ya ganshi a gida.
Dr Kamal ya ce "Ya akai garin aiki ka yi aika-aika?? yarinya ce fa ƙarama me yasa ba za ka lallaɓa ta ba ka yi mata ƙarfa-ƙarfa? ka na da kuɗi da ikon da za ka mallaki kowace irin mace bare wannan ƙaramar yarinyar wadda da alamunta ma ƴar matsiyata ce talakawan da ba su da komai, gaskiya ka bani kunya kamar ka rasa mata a duniya?"
idanunsa ya ware akan Dr Kamal cikin rashin fahimtar abin da ya ke nufi, "Ban gane ba me ka ke nufi ne akan mara lafiya da na kawo maka ne ko kuwa da wani ka ke magana daban??"
Murmushin takaici Dr Kamal ya yi ya ce "Ashe bayan Zina ma har shaye- shaye ka ke yi? ni fa na yi mamaki dan nasan a haiyacinka ba zaka danne ƙazamar talaka kamar yarinyar nan ba, ka je ka yi shaye-shaye ka yiwa ƴar mutane fyaɗe kuma yanzu ka nuna min kamar ba kai ka yi ba, ka ji tsoron Allah baya bacci kuma ya na kallon lokacin da ka aikata idan ka ɓoyewa mutum ba za ka ɓoyewa Allah ba kuma shine me hukunta duk wanda ya aikata ashsha."
"FYAƊE????????????????????????????"
Shahbeer ya maimaita kalmar cikin sigar tambaya.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/7, 6:56 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
10
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
MOONASH Alƙaluma Shida.
Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS.
BANI DA HUJJA
Maimoon
SARƘAƘIYA
Shaahd
BARRISTER SHAHEEDA
Ayush
AUREN ƘAUYE
Nazlarh
ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe
WATA HANYA
Indo
"Fyaɗe??????"
Shahbeer ya mai-maita kalmar cikin sigar tambaya.
"Binciken likitoci hakan ya nuna kuma ba tare da daɗewa ba hakan ta faru, bayan haka kuma ina me yi maka albishir da cewa ka yi nasara dan kuwa ba wanda zai samu hujjar kamaka da laifinka, Yarinyar ta yi losing memory ta manta rayuwarta ta baya yanzu akan turbar da ka ɗorata anan za ta tashi sannan kuma da yuwuwar wata alaƙa fin haka ta shiga tsakanin..."
dakatar da shi ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu da kyar ya ce "Ka bani ita zan kula da ita da kaina."
Dr Kamal ya ce "Ba zan riƙewa me kaya kayansa ba dan BANI DA HUJJA (Littafin Maimoon) faɗa min sunanta da naka zan rubuta."
shiru ya yi ya na nazari kafin ya ce "Shahbeer."
"Ai duk mun san wannan sunan ba shi nake buƙata ba, cikakken suna."
idanunsa da suka sauya kala ya zuba masa ya na binsa da wani kallo me cike da ɓoyayyun manufofi, "Mukthar.
shu'umin murmushi Dr Kamal ya yi gami da cewa "Ashsha abin ya zo in ji me faɗen Aurensa, ai kowane ɗa akwai sunan ubansa dan haka shi nake buƙata idan da hali har na Kaka, ko dan ba lallai in da uban ba."
wani mugun mashi ne ya soki Zuciyar Shahbeer, lokaci ɗaya tsananin ɓacin rai da zugin da Zuciyarsa ke yi su ka baiyano kan fuskarsa har ma da gangar jikinsa, "Mukthar Aminullah"
ya yi maganar a ƙagauce.
Dr Kamal ya ce "Wow Yayi, Muktar Aminullah Aminullah Muktar, daibabayin sunayen naku ya na burgeni, yanzu faɗa min sunanta."
Kamo gefen leɓensa na ƙasa ya yi ya taune shi da ƙarfi gami da rintse ido, cikin sarƙaƙƙiyar murya ya ce "Aisha, sunan Mahaifinta ka sa sunana idan haka bai yi maka ba ka haɗa da na Babanka."
Da sauri Dr Kamal ya miƙe ya na dariyar rainin hankali, "Matashin ɗan-kasuwa me jin kai da izza ga zarra ga abokan Dabi, bansan ya akai hakan ta faru ba, ba ka so asan ko yar waye?? ko dai itama ba uban ne kamar kai?? anko ku ka yi kenan?, to shi kenan zan sa mata sunan naka, amma fa abokina sai ka haɗa da haƙuri ka san ita Duniya Juyi-Juyi ce..."
dakatawa ya yi da maganar ya na murmushi, dafa teburin da ke tsakaninsu ya yi su ka fuskanci juna, kallon Zaki da Damisa su ka shiga yiwa juna har na wani lokaci sannan Kamal ya ci gaba da cewa "Gashi yau mun sake haɗuwa bayan wani lokaci, ni likita kai ɗan-kasuwa ka ga rayuwar kowa da inda ta ajiye shi, shin ka gane waye a gabanka kuwa Shahbeer?? ka tuno WATA RAYUWA??"
miƙewa Shahbeer ya yi ya na takawa ɗaya-bayan-ɗaya sai da ya yi taku biyar sannan ya juyo cike da mazantaka ya ce "Jagab!!! Kamal Hashim inkiyarka (Jagab ko Acoge), dama can kai ba mutum ne na kirki ba, Yaro na ga bara na ga bana kuma na ga shekarar basasa, a zahiri na fi ƴan-uwana salihanci a sirrince kuma na fi su hatsabibanci, Ashirrr Acoge ka shiga tai-tayinka, dan har yanzu Ina nan a WUTAR ƘAIƘAYI, ina ƙoƙarin gyara rayuwar ƴan-uwana ne ta hanyar nuna musu salihancina sabi da su ba su san WATA RAYUWAR ba, ka fi kowa sanin waye ni sabi da na hanaka zama da mazaunanka dan haka iya gani iya ƙyalewa, kuma ka kula ba kowace magana ake gaya min in jure ba, ni ta ƙasa nake illa Koren Maciji ne ni me sajewa da ciyawa ƴan-uwana kuma ba sa shakkar yaro ko a gaban Babarsa, kuma abin burgewar ko da Ido na kalli abu sai sun kalla Idan na ce ayi sai sun ƙaddamar dan haka ka guji faɗowo Komar Ƴan-huɗu Haihuwar Al'ajabi wannan ba kashedi bane Shawara ce ɗauka ko zubarwa ya rage naka, ka fito min da ita ko gobe in turo su su ɗauketa da kansu kasan Halin kowai ai."
jikin Kamal tuni ya fara tsuma sabi da tsoron Shahbeer ya kafa sansani a cikin Zuciyarsa tin ba yanzu ba, dama ya yi tunanin zamansa ɗan-kasuwa ka'in da na'in da shiga mutane iri-iri ya sa Yayi sanyi shi yasa ya fara tinkararsa da maganar banza a gaban idanunsa, ya riga ya yi masa abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba.
Cikin tsawa Shahbeer ya ce "Ba za ka ban ita bane??; Shiga yawan jama'a ba abin da ya ke ƙarawa face zafin kai dan haka ka bi ni a sannu."
hanyar fita Kamal ya nufa gami fa cewa "Yanzu zan sallameka amma don Allah maganar nan a barta anan, ka biyo ni ka karɓeta."
Murmushin yaro man-kaza Shahbeer ya saki sannan ya mara masa baya, ɗakin da aka kwantar da ita su ka nufa ba wani ɓata lokaci ya tarkata ya maida ita ga Shahbeer.
Ko sallama bai ba ya fara ƙwalawa Mommy kira, har lokacin suna Falo Malika ma ta fito suna ta hira tare da tsammanin shigowarsa, jin gigitaccen kiran ya sa duk suka tashi tsaye su ka zubawa hanyar shigowa ido.
rungume da ita a ƙirjinsa ya shigo idanun nan a ƙasa kai tsaye inda Mommy ta ke tsaye ya ƙarasa ya dire Aisha ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Su Shahzain ne su ka fito har suna rige-rige dan kuwa sun ji shigowar motarsa ganin mace kwance magashiyyan a gaban Mommy ya sa su yin turuss su na kallon yarinyar da Shahbeer ɗin.
Kowa kallon tuhuma ya ke watsa masa cike da mamaki.
A daddafe ya ce "Haɗari ne ya faru na bugeta."
daga haka ya raɓe zai wuce sashinsu.
"Muktar!!!!!!"
Mommy ce ta kira sunansa a kausashe, sai da ya rintse idonsa sabi sa muguwar bugawa da Zuciyarsa ta yi, lallai yau ya yaro match ba shi da ƴan-wasa tin da har Mommy ta ɗaga baki ta kira shi MUKHTAR kai tsaye.
takowa ta yi ta zo har inda ya ke cikin razani da kaɗuwa ta ce "Inya!!! Ina matuƙar tsoron mugun jinin mahaifinku ya bibiyeka, me ya faru???"
sabi da tsabar ɓacin rai da tafasar Zuciya harshensa ya harɗe maganar ta kasa fito, cije leɓe ya yi da ƙarfi gami da rintse ido ya fizgi numfashi da kyar ya fizgo maganar laɓɓansa na kakkarwa ya ce "Mom..Mommy.. kin fi kowa sanin abin da ki ka haifa domin ke kaɗai ki ka raini Ƴa-ƴa huɗu a lokaci ɗaya, Mukhtar ɗin da ki ka haifa ba haka ya ke ba, ba irin wannan tarbiyar ki ka bashi ba, na san darajar mace tin akan ke da na fara buɗe ido na gani, Mammi in kina zargina to ki fara tuhumar kanki."
Daga haka ya ci gaba da tafiya.
jiki a sanyaye ta koma inda ta bar Aisha kallon kowa da ke gurin ta yi sannan ta ja numfashi ta sauke ajiyar Zuciya, "Malika zo ki duba yarinyar nan na ga kamar ta na buƙatar temakon likita"
Mommy ta faɗa gami da durƙusawa a gaban Aishan.
Kukan da ta ke dannewa ne ya samu damar fitowa ta sanadin maganar Mommy, cikin kukan ta ce "Mommy ba zan iya ba, Bazan iya kallon wannan mummunar fuskar ba na tsaneta Mommy."
ta na kaiwa nan ta juya da gudu ta koma ɗaki ta garƙameshi, jikin ƙofar ta bi ta sulale a wajen ta ci gaba da razgar kuka.
Da ido kowa ya rakata cike da mamakin maganar ta-ta da dalilin kukan da ta ke yi.
Shukriya zuwa yanzu sun saba sosai da Safyan kullum hira su ke sha a waya sai dai har yau zancen soyayya bai shiga tsakaninsu ba, ta na son faɗa masa amma ta na matuƙar tsoro da shakkar abin da zai biyo baya hakan ya sa ta ke fasawa a duk lokacin da ta tuna, duk ta gaji da zaman gidan ba abin da ta ke muradi a yanzu sama da komawarta gidansu acan za ta fi sakewa ta yi abin da ta ke so in kuka ne ko farin ciki duk sai ta fi yin su ba tare da wani ya takura mata ba.
yau ma kamar kullum waya su ke ita da Safyan sai murmushi ta ke yi yanayin hirar tasu ya yi mata daɗi har ta manta a inda ta ke.
Dada ta ɗan jima a ƙofar ɗakin ta na kallonta duk da ba ta san da wa ta ke wayar ba sai ta ji hankalin bai kwanta ba a sanin da ta yi ba su fiye jituwa ita da Maalik ba har a yanzu bare su yi wannan wayar cikin farin ciki kamar yadda alamun Shukriyan su ke nunawa.
ƙarasawa ciki ta yi ta kira sunanta, a firgice ta katse wayar ta na zazzare ido ta amsa da "Uwmm?"
"Kusun uwaki"
Dada ta faɗa gami da watsa mata daƙuwa.
cikin rawar baki ta ce "Da..dda... ban...ban ji sallamar bane sai yanzu. "
"To dama yaushe za ki ji sallama ki na can kina waya??, dama na zo ne in sanar miki cewa mun gama maganar aurenku ni da Babanki sa lokaci da abin da dai ya kamata duk ya bar su a hannuna, Shukriya kasancewarki Matar Maalik hakan mafarkina ne kuma ina son cika shi dan haka ki shirya.
daga haka ta fice ba tare da ta jira abin da Shukriya za ta faɗa ba.
"Na shiga uku ni Hauwa'u."
Shukriya ta faɗa gami da zamewa ta zauna a kusa da gadon, "Shi kenan tawa ta ƙare, a lokacin da Zuciyata ta cika taff da son wani a lokacin ake neman aura min wanda ba na son shi ba na ƙaunar munanan ɗabi'un shi, anya kuwa wannan adalci ne??"
Cikin Zuciyarta ta ke wannan surutan, tunane-tunane suka shiga karyo mata, da su ta kwana da su ta tashi ko karin kumallo ba ta yi ba ta haɗa kayanta ta fito da nufin tafiya....
Shahzaib ne ya ce "Mommy ki bar saka waccan mahaukaciyar a shirginki; ki kira Baba ki gaya masa gobe ya zo da wuri tin da yanzu dare ya yi."
gyaɗa kai ta yi a sanyaye ta ce "Ku shigar da ita ɗakin can kafin gobe."
Shahzaib ya ce "Okay Mama; ai da zarar ta farko sai a nemi iyayenta a mayar da ita."
yanzun ma gyaɗa kai ta yi ba tare da magana ba, sama ta nufa ta na tafiya ta na saƙe-saƙe iri-iri.
Shahzaib ne ya taitayi Aisha ya kaita ɗakin da ke ƙasan ya na direta ya fice ya nufi sashinsu.
Ko zama ya kasa yi sai zagaye da kaiwa da kawowa ya ke, Shahzain ne ya ƙarasa in da ya ke a tausashe ya ce "Shahbeer, Mommy fa ba abin da ka ke tunani ta ke nufi ba kar hakan ya ɓata maka rai."
lumshe ido ya yi ya buɗe kafin ya ce "Ba Mommy ce ta ɓatan rai ba, Yau na Haɗu da Kamal shi ne likitan da ya dubata kuma ya shaida min fyaɗe akai mata."
haɗa baki su ka yi wajen mai-mai-ta "fyaɗe??"
ya ce "E sannan ya ke gaya min ni na aikata, ba gaira ba sabar ya ɓata min rai akan wata yarinyar da ba ni da tabbacin mutumce ko wata halittar, ni ban santa ba ina cikin tafiya na ji na yi ciki da mutum to ni kuwa wane rashin imani ne zai da na tafi na bar ƙaramar yarinya a cikin wannan mawuyacin halin?"
"Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un!"
kalmar da Shahmeer ya furta kenan cikin kaɗuwa gami da razani, shi ba me son tashin hankali bane kwata-kwata rayuwar farin ciki ta fi burge shi akan ko wace rayuwa yau kuma ga wata masifar ta na neman kunno musu kai.
"Ba zai yuwu ba"
Shahzain ya yi maganar a kausashe.
Shahzaib ya ce "Ka yi gaskiya Auta hakan ba mai saɓuwa bace lallai akwai wanda ya ke shirin yaƙarmu ta bayan fage, to waye shi??"
Shahzain ya ce "Ba shakka tarkon wani ka faɗa Shahbeer ni na yarda da hakan, kuma na yi maka alƙawarin ko waye ya ke neman yi maka mugun tabon nan sai n.."
dakatar da shi Shah beer ya yi ta hanyar cewa "Kar ka ɗau mugun alwashi akansa har zuwa lokacin da za ka gane ko waye shi sannan ka yi tunanin irin hukuncin da ya dace da shi."
Shahzaib ya ce "Da wa ka haɗu yau?"
Tsaki ya zuba kafin ya ce "Safyan tare da wani wai shi Maalik da kuma babansa, na kasa gane abin da ya ke faruwa ko kuma ya ke shirin faruwa kuma na kasa ɗora zargina akansu dan kuwa Maalik ɗin ba halin Safyan ne da shi ba."
ShahZaib ya ce "Kassh rashin sani ya fi dare duhu, nasan da ka sani da ba za ka saurare su ba, ni kuma ko zai shiga kogin rantsuwa ba zan dena zarginsa ba; Inya mu je mu kwanta sai da safe."
tsaki ya kuma yi sannan ya nufi hanyar bedroom duk suka mara masa baya.
Washe-gari
da wurwuri Baba ya zo ya duba Aisha ya na gamawa ya shaidawa Mommy Abin da ya faru da yarinya, fatan Alkairi ta yi mata tare da bin ɗanta da addu'o'in neman tsari da sharrin me sharri, ta san halin kayanta tin ya na ciki.
Ko tambayar yadda ta kwana bai yi ba har yau ransa a ɓace ya ke ya kasa mantawa da jiya baccin ma ba wani na kirki ya yi ba sai tarin damuwa da ta yi masa sallama.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/8, 12:20 PM] INDO CE: *WATA HANYA*
11
Free Book
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
MOONASH Alƙaluma Shida.
Daga Ƙungiyar ELEGANTA ONLINE WRITERS
(Team Shahbeer ya kasuwa?😂
Team Shahzaib Yane?🤨
Team Shahmeer ya kuke?🤓
Team Shahzain Yaya dai?🧐
Team Maalik I luv u all😍
Team Alhaji Boza And Safyan Ya kujiba-kujiba🫣🤭🤭
Team Ma'arufa Yaa?😎
Team Shukriya ina gaisuwa🥳
Team Maleeka How Market?🤣
Team Aisha Ya jiki?☹️
Ina fatan Duk muna cikin farin ciki😊😊😊 *INDO CE*)
Cikin nutsuwa Mommy ta ce "Inya Ka ji abin da DR Ya faɗa ko??"
ba tare da ya kalleta ba ya ce "Na ji."
"Hankalina a tashe ya ke Shahbeer ban san meke shirin faruwa da mu ba''
Mommy ta yi maganar a marai-raice.
"Ba abin da zai faru sai abin da Allah ya ƙaddara wa rayuwarmu Ummi"
Shahbeer ya faɗa cike
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 30