ta faɗa a ƙasan Zuciyarta lallai wannan ya iya ɗaure mutum, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ji ya ce "Ki na taya ni ki na bani labarin ƴan-gidanku ko?"
da salati da sallallami a bakinta ta dawo baya, ko uffan ta ƙi ce masa sai ya ce ta miƙo masa abu sai ta miƙa, shi kuwa ta gefen ido ya ke ankare da ita, yadda ta ke rarraba idanu ba ƙarin nishaɗi ya ke sa shi ba.
har su ka kammala ba ta bashi labarin ba shi ma bai tambayeta ba hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba.
Bayan Kwana Tara.
Duk suna kan makeken gadonsu, Shahbeer ya na zaune Shahzain ya yi matashin kai da cinyarsa Shahzaib kuwa a kashingiɗe yake kan filo Shahmeer kuma zaman dirshan ya yi yana danna Laptop. ɗakin shiru ba wanda yake magana a cikinsu dan kuwa duk hankalinsu yana ga abin da suke yi.
Shahmeer ne ya ce, "Inya! ina ganin fa ya kamata mu samu sabbin ma'aikata a wasu Kamfaninmu."
Ba tare da ya kalleshi ba ya ce, "ayi hakan."
Shahmeer zai yi wata maganar Auta ya dakatar da shi da cewa, "la kun ga wani abin mamaki, wani makaho ne ƴarsa ta ɓata amma duk yasan kalarta"
Shahzaib ya ce, "kuma wai da gaske?"
"da gaske mana gashi ma kuna gani? ku saurari abin da yake cewa ku ji, nima yanzu na ga labarin."
Rasss gaban Shahbeer ya yanke ya faɗi har ƙasa....
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/10, 6:25 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
13
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
MOONASH Alƙaluma Shida.
Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS.
Rasss Gaban Shahbeer ya yanke ya faɗi har ƙasa, cike da fargaba ya ce "Mu gani?"
miƙo masa Laptop ya yi gami da cewa "Wai sunanta Halima."
"Halima???.
ya maimata sunan cikin sigar tambaya, Zubawa bawan Allahn ido ya yi don ya fahimci inda maganga-nunsa su ka dosa.
"Baba menene sunanka?"
"Sunana Sani Ana kirana Baban Halima.
"A ina ka ke zaune?" " ina zaune a Dala Unguwar makafi tare da ƴata guda ɗaya tal, sunanta Halimatus-sadiya amma ana kiranta ƳAR-MAKAFI, itace gatana ita ke kula da ni, mahaifiyarta ta rasu daga ni sai ita mu ke zaune a ɗan kufan gidanmu ita ce ke min jagora idan zan fita bara da haka mu ke samun abin da mu ke ci.
"Yaushe ne ka nemeta ka rasa?"
"ranar nan kwanaki goma sha uku kenan daga fitarta zuwa kanti za ta sayo mana garin rogo mu ci ba ta kuma dawowa ba, na yi jiranta tin ina sa rai har na fitar na shiga gari nemanta rariya-rariya da ƴar sandata har zuwa yau ɗinnan da ta kwan goma sha uku ban ganta ba nemanta na ke yi har na baro yankinmu ina ta tambayar mutane yanzu ni ban ma san a inda na ke ba, yanzu na haɗu da wani bawan Allah ya ce zai kunna min Salularsa in yi bayani zai nuna ko za'a ganta.
"Kamar yaya Halima ta ke?"
"To ita dai Halima yarinya ce Ƙarama idan azumin nan ya shigo shekararta Goma sha Takwas ciff, ba ta da hasken fata sosai amma ba baƙa ce sosai ba sannan siririya ce kamar iska ta kayar da ita ƴar sirit kamar Allura amma ta na da tsayi.
"Wane irin kaya ne a jikinta?"
" ban san kayan da ke jikinta ba amma dai nasan shaida ɗaya a jikinta bayan kamanninta, akwai mulmulallen Zoben farar Azurfa da na jar Tagulla an ɗauresu da Zaren Abawa suna nan a wuyanta a maƙale kamar sarƙar ado, da iya wannan kawai zan iya gane ƴata.
"Wane roƙo za ka yi ga Al'umma?"
"Don Allah bayin Allah idan kun ganta ku dawo min da ita bani da kowa sai Allah sai ita itace ke min komai ku tausaya min idan ma sace ta aka yi.
Wanda ya ke masa bidiyon ne ya ke jero masa tambayoyi shi kuma ya na amsa su daki-daki.
"Allah ya baiyanata dai kawai zan ce"
Shahmeer ya faɗa gami da komawa gefe.
"Zoben azurfa da tagulla?"
Shahbeer ne ya jefawa kansa tambaya cike da nazarin inda ya san su.
da mamaki Shahzain ya ce "Boss na ji ka na tambayarmu?"
"Kaina na ke tambaya Auta, Kenan sunanta Halima??, duba cikin locker za ka ga Zoben da ya ke magana a kai na wannan yarinyar ne.
da sauri Shahmeer ya tashi ya fara dubawa bai sha wahala ba kuwa ya ciro ya kawowa Shahbeer, karɓa ya yi ya na kallonsu kafin ya ce "Ko shakka babu wannan itace domin kuwa inda na tsinci yarinyar ya na da alaƙa da yankin da ya ce sannan kamanninta da ya wassafa ba wanda bai yi dai-dai da nata ba ga kuma wannan abin."
Shahzaib ya ce "Allah ya nufa, ka ga yanzu mun huta bari ma in je in ce Mommy ta shiryata mu mayar da ita."
"A'a Shahzaib!!"
idanu su ka ware akansa cikin kaɗuwa da jin abin da ya furta ɗin, "A'A??"
"To a wane dalilin?"
"meye haɗinka da ita?"
Shahzain Shahmeer Shahzaib su ka haɗa baki wajen jefa masa tambayar.
"Sabi da ina son ta dawo ƙarƙashin kulawata, ba zan iya maida ita wannan unguwar kuma gidan da ko ƙofa ba lallai in akwai ba, ku fahimce ni mana! ko ba kwa iya fahimtar halin da na ke ciki ne Shahzaib?"
numfashi Shahzaib ya ja ya sauke kafin ya ce "Na kasa fahimtar komai Inya, idan da hali ka fahimtar da mu."
murmushin takaici ya yi gami da cewa "Hmm!! ko motsi ku ka yi ina gane me ya ke nufi ina iya fahimtar halin da ku ke ciki komai dare komai rana amma ku kun kasa fahimtata, na riga na faɗa kuma kun ji don haka ku san yadda za ku yi ku nema masa gida ya zauna a ƙarƙashin kulawarmu ita kuma Halima ta na tare da mu, yanzu idan mun maida masa ita shi kansa ba zai iya ganeta ba sabi da ba'a haiyacinta ta ke ba, yarinyar da ta ke kirana da Baba ai ko Baban nata ya ganeta sai dai wani baƙin cikin ya kashe shi dan ba za ta taɓa yarda dashi ba, Do Allah ku yi abin da na ce ba tare da jayayya ba, ina son ganinta a tare dani kullum ba zan iya rabata da gidan nan ba."
a sanyaye Shahzaib ya ce "In sha Allahu za mu yi hakan YaYa, Allah ya warware maka abin da ya shige maka duhu."
Shahmeer ya ce "Auta bincika ka ga ina za mu same shi."
Auta ya ce "To, amma dai dole mu zamo ƴaƴansa dan kuwa in ba ma ƙoƙarin mantar dashi ba zai manta da ita ba."
Shahmeer ya ce "Haka ne gaskiya, Boss Amma dai ka fara son yarinyar ne ko?"
"Ka san ba na ɓoye-ɓoye ai gashi na gaya muku iya gaskiyata.
Shahzain ya ce "Allah ya sa hakan Alkairi ne ba wani sharrin ba."
Shabeer ya ce "Ai kuwa idan ma sharrin ne to an yi nasara a kaina don kuwa na mato akan ƙaunarta kuma ni tamkar guguwa na ke idan na yunƙura me dakatar da ni sai Allah."
Shahzaib ya ce "Da yardar Allah mun fi ƙarfin sharri, ba abin da zai faru sai Alkairi."
Inna ce ta bubbuga ƙofar gami da sallama, Shahmeer ya amsa ya ba ta izinin shigowa.
"Ba zan shigo ba Ummanku ce ta ke nemanku, wannan rigimammiyar yarinyar ce ta ƙi cin abinci shi ne ta ce in kira ku.
"Okay Mu na zuwa"
Shahmeer ya bata amsa, sai da su ka ɗauki lokaci kafin su je kiran Mommy.
Rai ɓace Dada ta ce "Ai sai ka je ka yi hukuncin da ya yi daidai tin da ni ban iya maka ba, na gaya maka nima ba'a son raina aka ƙara sati ɗayan ba amma ka sa ni gaba da mita, Shukriya za ka je ka yiwa ba ni ba nasan itace ta tsare Ibrahim ɗin da baƙin naci har ya nemi alfarmar ɗaga auren naku kuma ubanka ne ya yarje masa ba ni ba."
Maalik tamkar zai yi kuka ya ce "Ki yi haƙuri Mom na ga ranki ya ɓaci, wallahi idanuna ne su ka rufe na gaji da haƙurin gani nake kamar lokacin ba zai zo ba."
"Lokaci kuwa zai zo tin da har aka riga aka sa shi, kwana nawa ne maye ya yi Amarya ya cinye abarsa?"
"Ammi don Allah a ɗaura gobe in ya so ranar Asabar ɗin sai ayi duk abin da za'ayi.
"Wallahi Ka fara siƙe ni Maalik, na ce ka je ka nemi matarka a'a?, Ba fa zai yuwu ba goben nan ya riga ya jaza maka da ya yarda.
"Shi kenan Ammi, kuma wallahi na taɓata ta yi min kuka sai na karyata.
ya na kaiwa nan ya tashi a fusace ya bar gidan sai gidansu Shukriya.
03:13pm
Kuka me yawa ta sharɓa har lokacin da bacci ya yi awon gaba da ita, Cikin bacci ta ke jin bugun gida kamar za'a ɓalle get ɗin a wuce.
Da addu'a a bakinta ta farka ta na muetsike ido, Waye wannan? ta tambayi kanta, Mami da su Abida duk ba sa gidan ita kaɗai ce kuma yanzu ba su isa dawowa ba ko ma ba wannan ba cikinsu ba me yin wannan bugun haukan, cike da takoki ta nufi wajen get ɗin ba tare da ta tambayi waye ba ta buɗe, ya na shigowa ya maida ƙofar ya rufe garam.
a razane ta yi baya ta na zuba masa ido ganin yadda ya ke a fusace. cikin rawar baki ta ce "Maalik kai ne?"
"Ba ni bane ke ce, kin sa Abba ya hana ɗaura mana aure ko? to ki tsammaci duk hukuncin da ya zo kanki.
"Wallahi Maalik ba laifina bane, kuma dama yanzu na ke so in nemek...
katse ta ya yi da cewa "Me za ki ban da ki ke nemana?, ko ƙara ɓata min rai za ki yi?"
fashewa ta yi da Kuka ta na cewa "Na san Ba wanda zai fahimceni sai kai Maalik sabi da ka na sona, Abba ma don na yi masa bayanin abin da ke raina fushi ya yi dani kuma duk Dada ce ta jawo hakan na gayawa Mamina ta ƙi ban goyon baya na gayawa Dada ta ƙi saurarata shi yasa na ce zan sanar maka kai ne kawai za ka cika min burina Maalik."
Jikinsa ne ya yi sanyi ganin yadda ta ke kuka magashiyan kuma alamunta sun baiyana damuwa me tarin yawa a tattare da ita, hannunta ya riƙo cikin tattausar murya ya ce "Gaya min Shukriya ina jin ki, ni zan iya haƙura da abin da Zuciyata ta ke so indai zai zamo silar farin cikinki."
"Maalik ina da wasu mafarkai a rayuwata da na ke son tabbatar da su kafin na yi aure ina da burika kamar kowane ɗan-adam nima mutum ce ina da wasu abin da na ke son cimmawa, ka temaka min ka janye maganar aurenmu har zuwa wani lokaci hakan zai bani damar cika burina Maalik don Allah, na san dai za ka ji ba daɗi amma ka tausaya min.
Shiru ya yi ya na nazari har kusan mintuna biyar ya yi zugum sai da ta ce "Maalik ba ka yarda ba ko?"
sannan ya ja dogon numfashi wanda ya sauke shi tare da nannauyar ajiyar Zuciya, a take alamar rauni ta baiyana akan fuskarsa, kamar zai yi kuka ya ce "Shukriya son gaskiya na ke miki ba zan iya watsa farin cikinki ta hanyar tilasta miki aure a lokacin da ba ki so ba, zan bar ƙasar nan har zuwa wani lokaci, amma Don Allah kar ki watsar da ni Shukri, ki cika burinki cikin kwanciyar hankali.
farin ciki ne ya lulluɓeta ta saki murmushi me haɗe da hawaye, ba shakka tana matuƙar tausayinsa sai dai ba yadda za ta yi don kuwa ta riga ta haukace akan Safyan ya zama dole ta san yadda za ta yi ta ɓamɓare shi.
da baya-baya ya ke tafiya har sai da ya kai jikin get sannan ya buɗe ya fice, ya na shiga mota ya fashe da kuka me zafi da raɗaɗi.
Da gudu ta koma ɗaki ta na ƙara sakin wani sabon kukan na tausayin Maalik, a gefe ɗaya ta na ji ba ta kyauta masa ba amma a wani gefen ta na jin hakan shi ne dai-dai.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/13, 11:23 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
14
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
MOONASH Alƙaluma Shida.
Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS.
Ya na komawa gida bai saurari kowa ba ya nufi sashinsa, kaya ya fara haɗawa ido rufe ba shi da burin da ya wuce ya bar ƙasar nan ya huta ji ya ke kamar a wuta ya ke.
Dada ce ta shigo cikin tashin hankali ta ke cewa "Maalik Lafiyarka kuwa?? me na ke gani haka???"
"Lafiyar tawa ce ta kawo hakan Ammi, don Allah kar ki dakatar da ni tafiya zan yi, ba yanzu Shukriya za ta aureni ba dan haka zamana ba amfani.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un!! wai yarinyar nan wane irin kunnen ƙashi gareta?? sabi da rashin imani ta rufe ido neman kashe min kai ta ke da baƙin ciki?"
"Ba ta da laifi Ammi, ita fa yarinya ce ba tare da shawararta ko son ranta ba za ku yi mata aure ba shiri, ba ta gama shiryawa ba ni kuma me bata dama ne fiye da haka don ba amfanin Auren da babu farin ciki a cikinsa ku kanku ba zai muku daɗi ba, duk lokacin da ta shirya nima a shirye nake amma don Allah kar ku ƙara yi mata dole iya yarda da umarninku da ta yi ma ai ta yi ƙoƙari.
"Ka na nufin kai ne ka ɗaure mata abar auren sai nan gaba?"
"E Ammi ni ne kuma ba na son a ƙara ɗago zancen.
Rausayar da kai Dada ta yi gami da cewa "Tohh, Allah ya sauwaƙe ya rage wahala domin an gama shanta, ba ka san sharrin mace ba Maalik da har za ka ɗagawa yarinyar nan ƙafa, ni dai ina tsoron abin da zai je ya zo amma ba komai ka yi tafiyarka Allah ya tsare.
"Amin, amma ba na son faɗanki Ammi don Allah kar ki yi fushi da Shukriya idan ma hakan laifi ne to laifin nawa ne, asali ni na fara sonta kuma na ce zan Aureta sannan ba mu tambayeta ra'ayinta akan Auren ba kuma gashi ta na da wani buri kuma shi ɗan-adam ba'a raba shi da buri.
"Ai har yanzu ban ce komai ba Maalik kuma ba zan ce ba har sai abin da ka ce, Allah ya tsareka ya kai ka lafiya, nima inaga ai zan zo in ganka kwana kusa dan ka na cikin damuwa sosai.
"Okay Ammi.
ya na cewa haka ya ja travel bag ɗinsa ya yi waje.
kasa kataɓus Dada ta yi gashi dai abin ya na yi mata ciwo amma idan ta tuna shi ne ya jawowa kanshi sai takaicinta ya koma kansa.
Bai shiryawa tafiyar ba kuma ba zai iya zaman Kano ba gaba ɗayanta hakan ya sa ya ɗauki hanyar Kaduna don ya kammala shirin tafiyarsa cikin kwanciyar hankali.
Cikin haɗe fuska kamar yadda ya saba ya ce "Zan fita sai ku kula da komai."
"Okay Boss"
Shahmeer ya faɗa gami da zama kan sofa.
Shahzain ya ce "Ko shakka babu da ni za ka fita, ko Inya??"
"Ba tarkacen gwarama na ke nema ba ni kaɗai zan fita, ka yi magana da Cibiyar Kasuwancinmu da ke Jigawa ka ji yadda lamuran ke gudana, ina so kafin wani lokaci komai ya ƙara canjawa fiye da yanzu.
Shahzaib ya yi dariya gami da cewa "Shi Tinkiya Uwar tumɓele daga jn tafiya wai da shi za'a je Allah ya daɗo na ji daɗi da ya sola ka."
Shahzain ya ce "Ba komai wata ran zamu haɗu."
"Shahzaib yau ba ka yi wani abin arziki ba ka bar Shahmeer da aiyuka kafin na dawo ka san abin yi wanda za ka ban labari akansa.
Sosa ƙeya ya yi gami da cewa "Bakina ya jawo min ina murna yau ban da hayaniya."
Shahzain ya kwashe da dariya sai da ya tilliƙi me isar shi sannan ya ce "Da ka ce kai Arne ne."
Ya ce "Ai na muslinta."
Shahmeer da Shahzain su ka kwashe da dariya Shahzaib kuwa haɗe girar sama da ta ƙasa ya yi, Shahbeer kam murmushin da bai wadaci fuska ba ya yi cike da son ƴan-uwan nasa, ganin za su ɗora da surutu ya sa shi miƙewa tare da faɗin "Sai na dawo."
fatan Alkairi su ka yi masa sannan ya fice.
Ya na tuƙa motar ya na tunane-tunane har ya isa gidan gonarsa, ya na yin Parking wasu matasa su biyu su ka ƙaraso wajen, ɗaya a cikinsu ya ce "Shugaba! Allah ya ja da rai, Allah ya iya maka me gida, Allah ya taya ka riƙon matsayinka Shugaba, me kuɗi uban matsiyata manya-manya maganin ƙanana-ƙanana, ka na haƙa muna binne ma, ka na faɗe muna cikasa ma, Arziki jinin Oga ne ba wani shege wallahi Allah, akanka ranmu ma fansa ne Boss."
Gefe ya koma ɗayan kuma ya ci gaba da cewa "Ni ne kwari da bakarka Jagayya da ka harba ni ban jira sai aiki, Uban zuga uban Ƴan-iska, Allah ya rufa ma kuma ya ce ka yi ba wanda zai hana ka sai shi da ya baka Shu...
katse shi ya yi da cewa "Kacau!!!
matashin ya ce "Sai Oga.
Shahbeer ya ƙara da cewa "Zagarido!!!!
ɗayan da ya yi gefe ne ya matso gami da cewa "Ga ni gabanka Madugu Dodon Shegu Ɗan Aisha yayansu Aminu."
ƙasaitaccen murmushinsa ya saki gami da cewa "Kacau! ga ka ga Zagarido ga kuma Jagayya ba."
"Wannan haka ya ke Shugaba, ga ni ga Kacau a gabanka, umarninka kawai mu ke jira."
Gyara tsayuwarsa ya yi kafin ya ce "Da fari dai mu je mu zauna ko?"
"Yadda ka ce Jagayya"
Kacau ya yi maganar cike da girmamawa.
Gaba ya yi su ka bi bayansa, bayan sun zauna Shahbeer ya kunna Laptop ɗinsa ya yi ƴan danne-danne sannan ya juya musu ita, ƙarewa Hoton da ya bayyana akai kallo su ka yi sannan su ka maida hankali gareshi.
cikin yanayinsa na ko- in-kula ya ce "Makaho ne, ina son ku kawo min shi zan tura muku Address na inda za ku kai shi, ku gayawa Shahmeer ya tura muku kuɗi amma fa duk wanda ya sayi abin banza da kuɗina zai san ya yi wa Jagayya Laifi."
Kacau ne ya fara ɗan sosa ƙeya ya na cewa "Ai da ya ke ma duk mun basar da lamarinnan Boss Zagarido ne kawai ya ke ɗan kora Ƴar-ficika to shi ma ya dena duk mun waɗaɗe yanzu ai Oga kawai abin da akeyi temakawa manya da ɗan sauransu, shi fa Zagarido ma har gidan Marayu yakan ɗan bada tallafi sabi da mun ga kana yi Oga, ɗabi'arka ta ƴaƴan ƙwarai ce kuma itace tarbiyar da ka bamu."
Zagarido ya ce "Wannan haka ya ke Jazuga wallahi duk mun waɗaɗar da lamuran nan."
Ya ce "Na ji daɗin hakan Allah ya ƙara shirya ku; Ina jiran na ga kun kawo min mutumin nan."
Zagarido ya ce "Wai meye alaƙarka da Makaho Oga? ka san ni fa ana ruwa ina kunna wuta ba na barin ta ta huce."
"Baban Yarinyar da zan Aura ne.
"Aure?" "Yarinya??"
Su ka haɗa baki wajen jefo masa tambaya.
"E In Allah ya yarda, ba na son yawaita tambaya; idan kun gama da wannan sashin zan baku wani aikin.
Da haka su ka yi sallama duk suka watse.
Shukriya ce ta fito jiki a sanyaye ta durƙusa a jikin kujera cike da fargabar abin da Abban zai ce "Gani" ta faɗa ta na zazzare ido.
"Shukriya garin ya haka ta faru?, mun riga mun tsayar da magana guri ɗaya ki ka sa Maalik ya tafi wani gurin wane irin buri ne ki ke son cimmawa haka?"
ƙasa ta yi da kai wasu zafafan hawaye suka shiga rige-rigen sauka kan kumatunta, a sanyaye ta ce "Ku yi haƙuri Abba, maganar gaskiya ba zan iya Auren Maalik bane ina da wanda na ke so."
"Amma da kin yi adalci wa yaron nan, ko laifi akai miki ai shi ba laifinsa a ciki, to Allah ya yi mana me kyau, ki ci gaba da addu'a Allah ya zaɓa mafi Alkairi, kar ki ƙara ɗaukar mataki a hannunki ba tare da shawarar manya ba.
"To In sha Allahu ba zan kuma ba.
"Tashi ki je, lallai ki riƙe Addu'a kar ki fasa yinta.
"To" ta faɗa gami da miƙewa, ɗaki ta koma ta zauna bakin gado tafukan hannunta ta sa ta tallafo gefen fuskarta ta zuba tagumi, tunanin ta yadda za ta furtawa Safyan ta na son shi kawai ta ke yi.
da wannan ta kwana ta hantse zuwa lokacin ba sosai ma ta ke tunawa da Maalik ba.
Bayan Wata ɗaya
Zaune su ke suna ɗan taɓa hira, Shahmeer ya ce "Allah sarki bawan Allahn nan tausayi ya ke ban, ko mene ya makantar dashi ?"
Shahzaib ya ce "Ba mu sani ba sai ka je ka tambayeshi."
"Kun ga ba na son sababi kun gane?"
Shahbeer ya faɗa cikin haɗe fuska.
Ma'arufa ce ta yi sallama hakan ya sa su ka maida hankalinsu wajen hanyar shigowa Falon nasu.
"Mommy ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 30