Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Akhiee ba? lokacin da ki ka zo makarantar nan me hankali da ke amma yanzi ya lalata ki kin zamo mara jin magana, to tinda ba ki ji faɗan da na yi miki ba zan samu iyayenki sai in sanar musu halin da ki ke ciki, ba za mu lamunce wannan lalata a cikin Islamiyya ba" sake fashewa ta yi da kuka ta na cewa "Don Allah Don Annabi Ya Sheikh ka jiƙaina kar ka gayawa iyayena, wallahi ina son makarantar nan ina so na yi karatu sosai nima na zama malama idan ka faɗa musu cireni za su yi don Allah ka temaka mini" Tabbas kalamanta sun ratsa zuciyarsa nan take tausayinta ya kama shi, shiru ya yi ya na ƴan nazare-nazare kafin ya ce ''Na haƙura amma ki sani indai ba ki fita shirginsa ba da kaina zan koreki ba sai na memi shawarar iyayenki ba, kuma idan na koreki ba dawowa kin ji ko?" da sauri ta gyaɗa kai ta na sauke ɓoyayyar ajiyar Zuciya har cikin ranta ta ji daɗi. Ci gaba ya yi da cewa "Ki na so ki zamo Malama amma ki ka mayar da hankalinki akan wanda ko fatiha ba lallai in ya iya ba? ki san da cewa Akhiee tin ya na yaro bai taɓa furta kalma ko guɗa ɗaya daga cikin Alƙur'ani ko Hadith ba; duk zuwan da yake yi makaranta ba ya taɓa yin karatu komai yawan dukan da za mu yi masa, gashi yanzu har mun gaji kafin mu dake shi ma ana daɗewa sabida ya riga ya kangare ba ya jin dukan don ko kuka bai taɓa yi mana ba, ina fa gaya miki ne ba don ki yi koyi da shi ba sai don ki gane shi ba aboki na ƙwarai bane, ki barshi ya yi rayuwarsa kema ki je ki yi taki." gyaɗa kai ta yi jiki a sanyaye ta ce "To zan kiyaye in sha Allah" a zuciyarta kuwa abinda ta faɗa a zahiri ba shi bane don kuwa ba ta jin duk wanman zai sa ta iya ƙauracewa Akhiee. Yau ta na shirin fitowa zuwa makaranta Zaheer ya yi sallama a gidansu, tin da ta gaishe shi take son silalewa ta gudu amma Mommy ta hanata a cewarta don ita ya zo bai kamata ta tafi ta barshi ba, dole ta zauna ba don ta so ba sai zumɓure zumɓure ta ke yi a zuciyarta kuwa ta sauke masa zagi yafi Cikin carbi dubu, sai yanzu ma ta ke jin gabaki ɗaya ta tsane shi, a hakan kuma har an riga an ba shi ita, tunani ta ke ma da ta yarda ta Aureshi gwara ma ta gudu ta bar gidan kowa ya rasata. Akhiee ne durƙushe a gaban Abhi bayan sun gaisa Abhi ya ce ''Kai na ke ta nema Dattijo, Saudi Arabia nake son a kaini amma tare da kai na ke son mu tafi." zaro ido ya yi gami da cewa "What? Abhi ni zan je Makkah yanzu? impossible Abhi a dai ƙara dubawa don Allah" cikin matuƙar mamaki Abhie ya ce "What Happened Muhammad? na ga ka sauya lokaci ɗaya, ka tuna fa sau ɗaya ka taɓa zuwa Makkah ya na da kyau ka ƙara zuwa, a wannan karon ni dai ina son tafiya tare da kai." Gyara zama ya yi ya koma dafa'an murar kwaɗi kafin ya fara da cewa "Abhi...................... (Sai Gobe😒) SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 AN FARA PAYMENT *©️INDO* [8/22, 3:44 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 16 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* "Abhi Don Allah ka yi haƙuri ku tafi tare da wani, yanzu ina yanayin da ba zan iya zuwa ko'ina ba, ga ka Kaka ta kusa ina buƙatat duk noman da na yi ayi aikinsa a gabana, ga Hamza ko Adamu ko Jaafar sai su rakaka, ni na yarda zam yi komai kawai sai ky tafi, ayi mimi afwa Abhi." Abhi ya jinjina kai ba don ransa ya so ba sai don jin an ambaci Gona, "Lallai ya na da kyau ka zauna a gida sannan ya na da kyau ka ƙara ziyartar Makkah, amma a wannan lokacin ka yi zamanka kawai sai mu tafi tare da Jaafar." Ya na jin haka ya yi zaram ya ce "Yauwa Abhina ai na san akwai fahimta a tsakaninmu, ni yanzu bari in tafi zan je Gezawa ne." Abhi ya yi murmushi irin nasu na manya cike da ƙaunar ɗan nasa ya ce "Allah i tsare mini kai Dattijo, lallai a gaishe mini da Mutanen Gezawa." "Za su ji" ya na gama faɗen haka ya miƙe bai ƙara yin magaa ba ya fice cikin sauri don kar Abhi ya ƙara taso wata maganar. Ma'u na harabar gidan Hajiya Laure maƙale a jikin bango sai ɓarza kuka take yi me cin rai da cin Zuciya, gabaki ɗaya ta rasa inda za ta tsoma rayuwarta ta ji sanyin, tin lokacin da su Hajiya Laure su ka lalata mata rayuwa duk ta rasa farin cikinta, gashi dai ta na son gayawa wani abinda ke damunta da ma abinda su ka yi mata amma ta kasa, a duk lokacin da ta yi yunƙurin hakan sai ta ji kanta ya hau juyi ya fara wani bala'in ciwo hakan ya sa dole ta haƙura. da wannan sassafiyar Yazeed ya dawo daga gantalinsa don jiya bai kwana a gida ba. Har ya wuce da nufin shiga ciki ya fasa don jin sautin kuka da ya yi, saɗaf-saɗaf ya yo baya cikin sanɗa don har cikin ransa ya yi tunanin Aljanu ne domin kuwa sassafiya ce sosai. Juye-juye ya fara yi don ganewa indonsa me kukan, can gefe da shi kaɗan ya hangota ta rufe ido sai kukanta ta ke yi ba ji ba gani. Ganin Ma'u ce ya sa hankalinsa ya kwanta tsoro ya gushe, idanu ya zuba mata har na ɗan lokaci kafin y matsa kusa da ita, cikin muryarsa da maye bai gama sakinta ba har yanzu ya ce "Me kike yiwa kuka anan da sassafe kamar Aljana?" zumbur ta matsa gefe ta na zaro masa idanu domin kuwa har ga Allah tsoronsu ta ke ji daga shi har Mominsa, tuni ta fara kiciniyar tsayar da kukan don kar ta ɓata masa rai har tarihi ya ƙara maimaita kansa don ta san shima tamkar bunsuru haka yake don neman mata. Ga mamakinta sai ta ji ya karya murya ilai ya na ƙara cewa "Me aka yi miki? ko kin gaji da aikin ne?" Girgiza kai ta yi alamar a'a gami da cewa "Ba komai." Jinjina kai ya yi kafin ya ce "Hmm! to maganar gaskiya kin iya ƙarya, dama ina lure da ke kin daɗe ba kya walwala kamar da, kuma kina yawan kuka daga ganin idanunki ma ai amsan kin yi, yanzu ma Allah ne kaɗai ya san adadin lokacin da lika ɗauka ki na kukan." Ƙasa ta yi da kai ba tare da ta ce komai ba don kuwa ba ta da bakin magana, ba ƙarya ya yi ba gaskiya ya faɗa sai dai ba za ta iya gaya masa abinda ke damunta ba. sun ɗan ɗebi lokaci a tsaitsaye kamar Dangin soja kowa da abinda yake tunani a ransa, shi kuwa Yazeed sai zubawa kyakkyawar fuskarta ido ya ke yi, shi tuni ɓa ya manta akan me suke magana ya tafi wani tunanin. Ta na shirin zamewa ta koma ciki ya dakatar da ita da cewa "Kin yi baƙi da yawa ya kamata ki fara Bleaching." ido ta zaro masa kamar za su faɗo ƙasa cike da mamakin jim furucinsa. Wani sassanyan murmushi ya sakar mata wanda shi kansa bai san lokacim da ga kufce masa ba, cikin wata kasalalliyar murya ya ƙara da cewa "Ki na kyau sosai musamman ƙwayar idanunku, shi yasa na ke son kallonki a koda yaushe, hakan ne ya ba ni damar gane ki na cikin damuwa tin ba yau ba, amma kinsan wani abu? sam ba na son ganin mace Baƙa na fi son Fara shi yasa ma na ce ki fara Bleaching sabida za ki fi kyau." Zuwa yanzu Zuciyar Ma'u ta koma tamkar ganga sabida yadda take bugawa da ƙarfi kuma akai akai, Cikin rawar baki ta ce "Ka yi haƙuri ba zan iya ba, ni gwara na zauna a yadda Allah ya bar ni, Rayuwata ma sam ba ta da amfani, ni yanzu jiran mutuwa kawai nake yi za ta fi mini sauƙi akan rayuwa." Ta ƙarasa maganar gami da fashewa da wani sabon kukan. "Oh! Ashsha ai ban san abin ya yi zafin haka ba, Mutuwa ki ke son yi Ma'u? to mutu mana? ni zan kawo miki guba ma ki sha ala raka tali gona, da wata baƙar fuskarki" ya faɗa ya na gyatsine fuska, daga haka ya wuce ciki ya barta nan, da harara ta raka shi har ya ɓacewa ganinta kafin ta zame a wajen ta na cewa "Allah ya isar mini abin da ku ka yi mini, ai idan kun fi ƙarfina ba ku fi ƙarfin Allah ba." Nan ta zame ta kwanta ta na ci gaba da kuka kaɗan-kaɗan har bacci ya yi nasarar sunkutarta. Yau ta kasance Ranar Asabar hakan ya sa Husnee ta shirya tsaf domin zuwa Islamiyya da safe. ta na jefa ƙafarta a harabar makadanta ta hangi Akhiee a sunkuye ya na gyara takalminsa, ba ta san lokacin da murmushi ya zuɓuce mata ba, har cikin rai ta yi matuƙar farin cikin ganinsa, da sauri ta ƙarasa kusa da shi cikin taku wanda ba zai ji motsin tawowarta ba, har lokacin ya na sunkuye don haka ta dunƙule hannunta tamau ta ɗaga za ta ɗirka masa dundu ta gudu don ta tsokane shi, sai dai kash!!! ta na kai hannun kansa ta ji ya maƙale a take wata azaba ta ratsata wadda ta ji tamkar hannun ya karye. Ƙara ta sako gami fa ƙwalla masa kira, ya ɗago ya na kallonta cike da mamaki. Har lokacin hannun nata azaba yake yi sai ƴar ƙaramar ƙara take saki idanunta tuni sun kawo ruwa, a taƙaocr ya ce "Ya akai?" kamar za ta yi kuka ta ce "Tsokamarka zan yi na zo dukanka kawai na ji kamar hannuna ya karye, sai zafi yake yi mini tamkar ƙashushuwana sun rugurguje." Lokacin da ya ta kai ƙarshen maganar ƙiris ya hana ba ta fashe da kuka ba amma sai ta maze ta cuje bakinta da ƙarfi. Hannun nata ya zubawa ido kafin ya ce "Ba ki nemi izimin dukana ba, ta baya ki ka zo shi yasa?" baki ta saki ta na kallonsa cike da mamakin abinda ya faɗa "Me kake nufi da hakan?" ɗan matsowa ya yi kusa da ita kana ya ce "Allah ne ya yi ba za ki ci zalina ba, nan gaba sai ki kula kar ki jawowa kanki babbar jinya." Daga haka ya ratse zai ci gaba da tafiya ta yi saurin shan gabansa ta na murmushi ta ce "Akhiee jiya Yayana ya zo daga Kaduna, in ce ya zo ku gaisa?" zuba mata idanu ya yi yana ƙara yaba girman wautarta ta wurga shi Duniyar tunani sai da ya ji ta ƙara cewa "Ka yarda?" sannan ya ja numfashi ya sauke, a taƙaice ya ce "A matsayinsa na wa? meye alaƙata da shi da zai zo mu gaisa? ni ba na buƙatar hakan ya sha zamansa, ke ɗin ma ba na fatan ƙara ganinki." Turo baki ta yi zuciyarta sam ba daɗi, ba ta ƙara ce masa kanzil ba ta wuce cikin aji cike da tausayin kanta. Jikin bango ya koma ya maƙale sannan ya zaro Wiwi ɗinsa ya bata wuta, sai da ya yi ja uku sannan ya ciro wata ƴar Keypad ya yi latse-latse a cikinta sannan ya kara a kunne. Shiru na kusan sakanni bakwai kafin ya buɗe baki ya ce "Yau Dodon Lungu zai shigo Fagge sabida bikin Abokinsa, a wannan wasan da za su yi nake so ku ɗanɗana masa kuɗarsa, Yaransa Uku kawai na ke so a kashe bayan su kar a ƙara mini, sannan ina so duk su ji a jikinsu musamman shi ɗin da yake jin ya kai." a ɗaya ɓangaren Wuta ya ce "An gama Ya me Jama'a, jiya wasu ƴan- sanda su ka kawo mana hari yankin nan wai sai sun kama Wiwi nace ai Ogana ya fi Ƙarfin wannan." Risslan ya ce "Yanzu ba wannan ba ina so ku aiwatar da abinda na ce kuma cikin salo yadda zai ƙayatar da ni." Wuta ya ce "Kamat an gama da yardar Rabbi." bai ƙara cewa komai ba ya katse wayar gami da soketa a Aljihu. ya na ƙoƙarin shiga Aji wata wayar ta shi ta fara ƙara, zarota ya yi ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa tare da yin shiru. a Ɗaya ɓangaren cikin Muryar kuka ta ce "Zakiyya da Farhana ba a gansu ba Muhammad tin jiya mu ke nemansu amma har yanzu shiru, wai sai yaushe ne wannan abin zai zo ƙarshe? na san an ɗebe su ne domin a ci galaba akanka wai me yasa ba za ka watsar da harkar nan ba Muhammad?" Shiru ne ya ratsa tsakani na ɗan lokaci kafin ya ce "Me yasa ba ku gaya mini da wuri ba?" "A tunaninmu abin bai kai haka ba, ashe har ya wuce nan, mun ƙi gaya maka ne don kar hankalinka ya tashi amma yanzu ya zama dole ka sani domin kai ne Babansu." "Relax Rahma! in sha Allah za a gansu, ki dena kuka Please" numfashu ta ja ta na ƙoƙarin tsayar da kukan, cikin sanyin murya ta ce "Shi kenan, amma ina so ka sani da ni da su duk da kai mu ka dogara, sai anjima" daga haka ta katse wayar. Bin wayar hannunsa ya yi da kallo cikin tashin hankali da mamaki sai dai a kan fuskarsa sam babu wata damuwa. A gefe guda kuwa tunanin wanda ya yi masa wannan ɗanyen aikin yake yi. Tsugunne ba ta ƙare ba, an sayar da Biri an sayi Mage, don haka bai ga ta zama a makaranta ba. CP ya turawa kira, har ta katse bai ɗauka ba sai da ya ƙara kira sannan ya ɗauka. "Yallaɓai akwai damuwa fa!" Rass ƙirjin CP ya buga da sauri ya ce "What Happen Risslan?" "An sace mini yara guda biyu, kuma Mata, hankalina ya tashi domin kuwa an samu wanda ya iya gane Lagona, za su yi mini illa ta ɓangaren iyalina, amma ba komai ina so ka tayani binciken waye ya ɗaukesu da kuma wanda ya sa a aikata, sannan ina buƙatar in gansu." CP ya jinjina kai kafin ya ce "Gaskiya kuwa in haka ne an samu matsala, amma su da aka rasa in sa Allah za su dawo, ba za su iya yin galaba akanka ta kowace hanya ba, ya kuma zama dole ka ruɓanya tsaro ka sa taka-tsan-tsan akan duk waɗanda su ka shafeka, domin da alama kowaye ya aikata hakan ba ƙaramin shege bane don ba wanda ya san ka na da iyali bayan wanda ake ganinku tare, lallai ka kula nima zan yi iya ƙoƙarina daga nan." "Okay" kawai ya ce ba tare da ya ƙara magana ba ya katse wayar. Yasayyadi Usman Jaafar Adamu Hamza, su na zaune suna tattaunawa akan batun Abhi da Akhiee. Adamu ne ya taɓule baki kafin ya ce "Wallahi ina jin haushin wannan son kai na Abhi, ban san me yasa ba ya fi son lalataccen Yaron nan." "Aikin banza kai ma ba ka ji ance lalataccen Ɗa ya fi shiga rai ba?" Hamza ne ya yi maganar cike da tsanar Akhiee. Jaafar ya ce "Ni ba wannan ne tashin hankalina ba, wai Makkah na fa ya ke son zuwa amma Abhi duk yawan ƴan gidan nan da yayyen Akhiee ɗin waɗanda da can su suke kai shi Makkahn amma wai yanzu Akhiee ya nema, shi kuma sabida munafurci har da wai shi zai yi komai." "Ai ba zai yuwu ba, ba za mu bari akai Mahaifinmu Makkah da kuɗin Haram ba ya zama dole mu nemi Yaya Sani da Yaya Bello mu sanar musu tsiyar da ake shirin tufkawa, ko Sheikh Auwal ma ba za mu bari ya sani ba in sun ji sai su sanar da shi." Adamu ya ce "To banda abinku ai Sheikh Auwal ɗin ne ya ke ɗaure masa, wallahi shi ya ke goyon bayansa shi yasa ma ba ya jin maganar mutane, munafukan banza." Yasayyadi Usman ya ce "Ina sane da su ai, kar ku damu mu ma lokacinmu zai yi ai." Jafaar ya tafka tsaki kafin ya ce "Ni fa da ni na ke so a je Makkan nan idan an tashi, ato! " Adamu ya ce "Yo dama kai Abhi ɗin ya ce ai bayan Akhiee sai ku yi ta tafiya Allah i tsare." A gadarance Jaafar ya amsa da "Amin" surutu su ka ci gaba da yi akan Akhiee kowa na tofa tashi. A ɓangaren Akhiee komai ƙara cin tira yake yi, don kuwa gashi har wuni ya na neman ƙarewa la'asar ta yi ba a ji ko da labarin su Zakiyya ba. ɓacin rai da takaici sun yi masa caa! ya ma rasa me zai yi gabaki ɗaya. Sai la'asar ɗin ya shigo makaranta shima ba don ya so ba sai don ya rasa inda zai je ya ji daɗi. Bai bi takan kowa ba ya wuce inda ya saba tsayawa. Idanunsa a ƙasa ya na tunanin ta inda zai ɓullowa lamarin wanda ya ke bibiyarsa kamar daga sama ya ji Muryar Husnee a kusa da shi...... "Ai na zata ba za ka zo ba" kallonta ya yi kafin ya doka tsaki cikin ɓacin rai ya ce "Wai ke kunnen ƙashi gareki ne??" Jingina ta yi a jikin makari ta na murmushi, cikin sanyin jiki ta ce "Kunnena irin na kowa ne, ka yi haƙuri Akhiee na ma yi ƙoƙari da na jure rashinka na ƴan lokutan da su ka wuce a baya, ni fa da gaske da kai nake so na yi rayuwata, kuma idan ka shiga tsakanina da kai to tabbas abinda ba ka so na zama zan zama, ba za a kuma ganina a makarantar nan ba, kwanan gidan iyayena ma zai gagareni, nima zan lalace na dawo irinka, bai zama lallai ka yarda ba amma za ka gani a aikace." "To wai ke me kike so na yi miki? na gaya miki shiga rayuwata ba burgewa ba ce, ban yi miki wani abu na ƙuntatawa ba duk da irinn takurawar fa kike yi mini, na kasa ɗaukar mataki akanki, har yau kuma ki na samun damata, to me ya rage miki? ni na ce miki ban san menene so ba. "To Akhiee tinda ni na so hakan ai ban damu da sai na burge wasu ba indai na burge kaina, dan dai ka na ganin kamar da wasa na ke yi maka ne, amma har cikin raina ni ina ƙaunarka, ban damu da halinka ko wani abu ba iya abinda na sani shi ne ina sonka!" Shiru ne ya ratsa tsakani na ɗan lokaci sanna Akhiew ya katse shirun da cewa "Kin shirya Rayuwa da ni?" Lumshe ido ta yi ta na murmushi cikin ƙwarin guiwa ta ce "I'm ready" "Okay good, i want you to vote for me" Idanu ta zuba masa cikin sauri ta ce "Ban fahimci inda maganarka ta dosa ba." gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ce "Ina nufin ki zaɓeni ki bar kowa, in kin yi hakan shine zan san ki na tare da ni duk rintsi duk wuya, nima zan fi jin daɗin kasancewa a tsaginki" ya yi maganar ya na zuba mata kaifafan idanunsa, sai da ta sunkuyar kai sabi da kallon da yake binta da shi, ta ɗan numfasa sannan ta ce "I already voted for you, tin tuni kai na zaɓa shi yasa ma na gaya maka iya gaskiyata" Cikin sassanyar murya me sanya nutsuwa ya ce "Kin tabbata?" kai ta gyaɗa gami da cewa "Eh" Bai ce uffan ba ya kama tsintsiyar hannunta ya shiga janta, da kallo ta bishi a ranta ta na tambayar kanta ina zai kaita? kuma gashi ta kasa cijewa ta dena binsa. Haka ya ratsa jama'a da ita ba tare da damuwa da kallon da ake yi musu ba, sai da su ka dangana da wajen da Amadu ya ajiye mota sannan ya tsaya, daidai lokacin Zara ta ƙaraso da gudu-gudu hankali tashe ta ce "Ina za ki je Husnee??" "Nima ban sani ba tambayi Akhiee" ta faɗa ta na kallonsa. "Ki koma makaranta kar ranki ya ɓaci" ya faɗa ya na zuba mata wani shegen kallo wanda ya sa ta yi saurin juyawa. Amadu tuni ya fito daga cikin Motar cike da mamaki ya ce "Lafiya dai?" Akhiee ya ce "Ki shiga mota Ni zan tafi akan Dokina, amma kar ku bari na ɓace muku duk inda na yi nan za ku yi." Amadu ya ɗan yi gyaran murys cike da tsoro ya ce "To Malam ina za mu je haka?" Rikitattun idanunsa ya watsawa Amadu gami da cewa ''Kar ka bari ka yi mini ba daidai ba." daga haka ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Dokinsa. Husnee dai sai rarraba ido ta ke yi duk ta rasa ma tunaninta gabaki ɗaya. Amadu ne ya katse mata tunani da cewa "Innata ki na ganin mu bi shi ko kuwa?" buɗe motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba hakan ya sa shima ya shiga ya bata wuta ya shiga bin bayan Akhiee. Bakin wani masallaci ya tsaya wanda Almajirai ke ta karatu a ciki da wajensa. wajen Motar ya dawo ya ɗan leƙa gami da cewa ''Ki jirani anan Asma'u! kai kuma ka zo mu shiga ciki" gyaɗa kai ta yi gami da sa hannu ta buga tagumi ta na tunanin abinda ke shirin faruwa sai dai duk iya nazarinta ta kasa fahimtar komai. A cikin Masallaci kuwa gaban Babban Malamin Makarantar Allon su ka durƙusa daga shi har Amadu. Malam Kabiru da fara'a akan fuskarsa ya ce "A'hh! yau ɗan namy ne a gabana haka?" Akhiee ya ce "Ni ne Baba Kabiru, wata alfarma na zo ayi mini." Malam Kabiru ya jinjina kai cikin dattako da manyance ya ce "To ina saurara Allah i sa abinda bai fi ƙarfina ba ne, duk ya wajen manyan ina Baban naku ya na lafiya? kwana da yawa ban zo mun gana ba" Akhiee ya gyara zama sannan ya ce "Yana lafiya, Aure nake so a ɗaura mini a yanzu-yanzu, Baba Kabiru kai Aminin Mahaifina ne, hakan ne ya sa ba ni da wurin zuwa ayi mini haka in ba wurinka ba" Kamar saukar aradu haka Malam Kabiru ya ji maganar Akhiee ta faɗo masa, tsananin mamaki da kaɗuwa su ka lulluɓe shi lokaci ɗaya, sai dai abin manya sam bai nuna alama ba, cikin nutsuwa

Chapter 10 of 19