da kuma tattausar murya ya ce "Muhammad! Aure fa ba abin wasa ba ne, idan har da gaskr ka ke yi mini me yasa ba ka sanarwa Mahaifinka da ƴan-uwansa ba? me yasa kuma sai yanzu-yanzu kake so a ɗaura?"
Sam ba ya son yawan tambaya don kuwa ransa ɓaci yake yi, amma da yake Malam Kabiru tamkar uba yakw a wurinsa sai ya danne.
Kai tsaye ya ce "Ba buƙatar kowa ya sani har sai bayan anyi, ka manta da batun gaya musu kawai."
"A'a fa, ko ba ka so Malam Muhammad ya sani ai ya kamata ko yayyenka ka sanarwa, Muhammad Aure fa ba a yi masa gaggawa, idan aka jira lokacinsa ya yi sai a yi shi cikin kwanciyar hankali, kafin Ɗaura Aure ana buƙatar Dangin Ɗiya domin a gana a san juna kuma a nemi yardarsu."
SHARE FISABILILLAH
Na Kuɗi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632
AN FARA PAYMENT
*©️INDO*
[8/24, 9:23 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 17
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*M.W.A🦅*
"Wannan shine Wakilinta" ya faɗa ya na nuna Amadu, kafin ya ɗora da cewa "Ni kuma kai za ka yi mini komai; Ba na so na aikata ba daidai ba shi yasa na ke bin komai a maslaha."
(Ohh! ni Indo su Amadu an zama Wakili🤣)
Zaro ido Amadu ya yi cikin matuƙar razani da firgici ya ce "Iye? wallahi Malam Allah ɗaya ba zan iya ba, a je a nemo wani dai don Allah." wani shegen kallo Akhiee ya aika masa wanda ya sa shi saurin haɗiye surutun nasa.
Malam Kabiru ya san halin Akhiee sarai, zai iya tuɓe rigar kunya ya zuba masa rashin mutunci duk da cewar Abokin babansa ne don haka ya jinjina kai kana ya ce "Shi kenan, na san zan iya yi maka komai amma ina son sanin dalilin da ya sa kake so ayi hakan."
"Ina so ta dawo ƙarƙashin kulawata ne sabida za'a iya cutar mini da ita idan na tsaya ɓata lokaci, Yanzu abin da za'ayi ka tattaro dattawan Abokanka ɗinnan ku yi komai tare."
Malam Kabir ya ce "To Sadaki fa?"
"Yanzu za a kawo" ya faɗa a taƙaice.
Malam Kabir dai a gefe cike yake da fargabar ɗaura auren don kar wani abun ya je ya zo, a gefe guda kuma ya na shakkar iya shegen Akhiee, don haka ba shi da zaɓin da ya wuce ya ɗaura Auren kawai a huta.
Ɗaya daga cikin Ɗalibansa ya tasa ya ce ya je ya gayyato masa Dattawan da ke zaune a wajen Masallaci.
Ba tare da wata daɗewa ba suka shigo Tare da su Salansa.
Kusa da Akhiee ya zauna sannan ya miƙo masa kuɗin, Akhiee ya ce "Ka lissafa?" "Eh Dubu Tamanin ne kamar yadda ka ce" bai ce komai ba ya miƙawa Malam Kabiru gami da cewa "Ga shi nan idan da ciko su yi bayani zan basu ko nawa suke buƙata."
Malam Musa ne ya dubi Malam Kabir cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa ya ce "Me za a yi ne Malam?"
Dalla- dalla Malam Kabir ya yi musu bayanin duk abinda ya faru da kuma wanda zai faru anan gaba, ba su yi musu ba su ka gyara zama domin ɗaura Aure.
Malam Kabir ya miƙawa Amadu da ya gama rikicewa kuɗin gami da cewa "To gashi, idan an yiwa iyayenta bayani idan suna buƙatar wani abin sai a sanar" Amadu ya karɓa hannunsa na rawar mazari, ko uffan ma ya kasa cewa.
Tare da sauran Ɗaliban Malam Kabiru manyansu da yaransu aka ɗaura Auren. Bayan an gama su Gwaja su ka kawo Alewa da Biskit da Dabino aka rarraba, sannan kowa ya san inda dare ya yi masa.
Akhiee ma sallama ya yiwa Malam Kabiru sannan ya fito, su Salansa na biye da shi ciki kuwa har da Amadu da jikinsa duk ya gama mutuwa.
Ta na ganin sun fito ta fito daga cikin motar ta tsaya ta na binsa da kallo.
Tinda su Gwaja su ka faɗa mata abinda aka yi ta fara kuka ta cika da tsoro da fargabar abinda za ta tarar a gidansu.
Har ya ƙaraso inda take shi take kallo har ya zo gaf da ita, idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali ya zuba mata ya na jin kukan nata har cikin ransa, wani farin hankicif ya zaro a Aljihunsa ya fara goge mata ƙwallar ya na hura mata iskar bakinsa a hankali, hakan ya sa ta fara fizgar numfashi ta na sauke ajiyar Zuciya, cikin wata tattausar murya wadda duk wanda ya jita zai so ya ƙara saurarenta ya ce "I'm so sorry Asma'u, ba ni da zaɓin da ya wuce haka, Allah ya riga ya ƙaddara ke ce abokiyar rayuwata, kuma abubuwa da yawa na cutarwa su na bibiyar rayuwarki shi yasa na yanke wannan hukuncin, da zarar na kai ki gidanmu babu wani abu da zai ƙara barazana wa rayuwarki sai dai in kin fito daga cikinsa."
ɗan jinkirtawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ki dena kuka, ko da duk Duniya za ta juya miki baya ni ina tare da ke, tinda ki na so na a ganina ba abin tashin hankali ba ne hakan, kuma ba na yi ne dan na ɓata miki ba sai dan ba na son na ga kin cutu, ki na da muhimmanci a rayuwata kuma ke ta musamman ce a wurina; Yanzu ki bi Amadu ya kai ki gida kafin na zo Ɗaukarki."
Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa zuciyarta cike da tunane-tunane, ganin ta kasa ko motsawa ya sa shi kamo hannunta ya buɗe mata motar gami da cewa "Shiga mana" shigar ta yi har lokacin ba ta ce ko uffan ba, wata tamfatsetsiyar waya ya zaro cikin Aljihunsa ya miƙa mata gami da cewa "Ga wannan a koda yaushe idan ki na nemana za ki sameni, lambobin ciki duk nawa ne."
Karɓa ta yi gami da gyaɗa kai ba tare da ta yi magana ba, ido ya zuba mata a ransa ya na jin kamar ya tafi da ita tin a yanzu sai dai ya na so iyayenta su fara sani ya ga iya gudun ruwansu, don ya san mawuyaci ne su amince da shi.
Cikin sigar zolaya Salansa ya ce "Me House ko za ka bi ta ne?"
rufe motar ya yi gami da yin baya, Su Salansa kuwa sai dariya suke a ciki-ciki don kar ya ji su.
Amadu ne ya matso kusa da shi kamar zai fashe da kuka ya ce "To Yallaɓai ni dai wannan ƴa a matsayin amana take a wurina da zarar na rabota da gidan iyayenta, sai gashi yanzu kai kuma ka mallaketa ta hanyata ba ta hanyar iyayenta ba, nima na shiga matsala ban san wane kallo za su yiwa hakan ba, ina fatan ba don cutarwa ka yiwa wannan baiwar Allah haka ba."
Dafa kafaɗarsa ya yi kafin ya fara magana cikin salonsa na izza "Ita ɗin matata ce kuma mallakina, Ka kula mini da ita sosai, ba ka cikin matsala don kuwa ina da kafaɗun da zan iya ɗaukar komai akanta, inda zan iya cutar da Asma'u da na daɗe da rabata da rayuwarta ko kuma wani abu mafi muhimmanci nata, ku je kawai a gaishe mini da mutan gidan".
Amadu ya jinjina kai, yanzu ya samu ƙwarin guiwar da zai iya komawa gidan saɓanin da da ya cika da tsoro.
Sai da motarsu ta bar layin sannan Akhiee da tawagarsa su ka ɗaga.
Kai tsaye Makwantarsu su ka koma inda suke yiwa laƙabi da suna Masarautar Sarƙa.
Har cikin Fadarsa su ka raka shi a memakon su bashi wuri kuma sai su ka zauna su ka mamaye shi, kowa cikinsa cike taff da tambayoyin da yake son yi masa, ciki kuwa har da su Laita da duk sauran yaransa.
Zabira ce ta fara buɗe musu fagen tambayar da cewa "Wai dama ka na soyayya Abba?"
Da sauri Ɗan Bakwai ya ce "Yauwa!! abinda nake son ji kenan nima, daɗina da ke kanki ya na kawo wuta ta gidana"
Nan fa kowa ya fara tarkato tashi tambayar ya na jefowa, shi kuwa Akhiee sai shan wiwi ɗinsa yake yi ya ƙi cewa komai.
Sai da su ka gama su ka fara yin slow sannan ya ɗan yi gyaran murya duk su ka nutsu, "Ni ba na soyayya hasalima ban san ya akeyinta ba, abinda nake so ku sani shine Asma'u ita kaɗai gareni, idan a cikinku ne aka illata wani to ina da wani, amma ita duk Duniya ba ni da tamkarta, kuma ba ni da wadda za ta zamo kamarta, duk tsawon rayuwarku da ni bayan Iyalina akwai wata mace da kuka taɓa ganin ina saurara?" amsawa su ka yi da "A'a" ya ci gaba da cewa ''Nima kaina na yi mamakin ta yadda aka yi na fara saurararta har ta yi nasarar sa ni abubuwa da dama a cikin waɗanda ba na yinsu, haka kawai nake jinta tamkar Ruhina idan aka cutar da ita tabbas an yi mini babbar cuta, hakan ne ya sa nake so ta dawo ƙarƙashin kulawata hankalina zai fi kwanciya, ga bayani nan na yi muku wanda bai fahimta ba kuma ba zai taɓa fahimta ba don haka ku tashi ku ban wuri ba na buƙatarku a yanzu."
miƙewa su ka yi su na ta murna su ka rankaya su ka yi waje, can gefe su ka haɗa majalisa su ka fara tattaunawa, Gwaja ya ce "Ai na godewa Allah tinda yanzu ya samu mata mu ma ƙila zai barmu mu dinga kula mata har mu yi Aure"
"Mewtchh!!!" Salansa ya doka tsaki kafin ya ci gaba da cewa "Kai ta Aure ma ka ke yi, idan shi ya iya kula da ita kai yadda kake kai a sama ɗinnan ba abinda za ka iya yi mata, ƙarshe ka sa ya kasheka a banza" ɗan sassauta murya yayi kafin ya ce "Wai kun san me? ya ce bai san so ba ko? to wallahi sonta yake yi."
Laita ta yi dariya kafin ta ce ''Bar ɗan iska ya na son kayarsa mana." su ka ƙara kwashewa da dariya, hira su ka ci gaba da yi cikin farin ciki domin kuwa su daɗi abin ya yi musu.
A Ɓangaren Husnee kuwa kamar ɓarauniya haka ta shiga gida da sanɗa, ta yi muzu-muzu da ita kamar jiƙaƙƙiyar kaza.
Mommy da Yaya Muddassir su na zaune su na hirar yaushe gamo ta shigo Falon cikin takunta me kama da na masu koyo.
Yaya Muddassir ya bita da kallo kafin ya ce "Lafiya kuwa Ƙanwata?" kusa da shi ta zauna kafin ta yi magana cikin muryarta da ta dishe, "Lafiya lau"
Mommy ta ce "Lafiyar Kura ba? in gaya maka gaskiya sai an haɗa da addu'a don kuwa Aljanu ne su ka shafeta, ka ga yadda tafita ɗazu lafiyar Allah ko? to ka ga yanzu yadda ta dawo, to haka take kan da lafiya jikin ba daɗi, kwanaki haka su ka dinga lallanƙwasa kamar tsutsa, ni dai naga abin al'ajabi, na ce ma zan kaita Islamic Center ko Allah zai sa a samu sauƙi"
Muddassir ya bi Husnee da kallo, shi dai a rayuwarsa Allah ya ɗiga masa so da ƙaunar ƙanwar ta shi fiye duk sauran ƙannensa, tausayinta ya gama kama shi, cikin sanyin jiki ya ce "Sannu kin ji ƙanwata?, meke miki ciwo yanzu."
"Ba komai" ta faɗa ta na turo baki gaba.
Ya ce "Kin tabbata?, to idan ki na buƙatar wani abin sai ki gaya mini kin ji? ko mu je ki sha Ice Cream?" rasss ta ji gabanta ya faɗi, "Ba ka san cewa ni yanzu matar Aure ba ce Yaya" abinda ta faɗa a zuciyar kenan a sarari kuwa ta yi saurin girgiza masa kai.
Ya ce "Shi kenan yanzu ki samu ki ci abinci ki huta in anjika zan baki labarin Kaduna, kin ce ma za ki bini ko?" girgiza kai ta yi alamar "a'a" gami da cewa "Na fasa" ya yi dariya a ransa ya ce "Nima ba za ni da ke ba" a sarari kuwa ya ce "To shi kenan."
Tashi ta yi ta koma ɗakinsu ba ta nemi abincin ba ta baje anan bacci me cike da mafarkai masu daɗi da marasa daɗi ya yi tafiyar ruwa da ita.
Hajiya Laure na zaune ta na waya ita da Hajiya Saudah, ƙorafi take yi akan Boka ya ƙi kiransu har yanzu, Hajiya Saudah ta ce "Ke fa kin fiye gaggawa Ƙawata, ki jira mana ai komai ya na da lokacinsa indai Boka Barore ne za ki sha mamaki, ai ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin faɗa ne."
Hajiya Laure ta sauke wani gwaurin nishi gami da murmushi, cikin jin daɗi ta ce "Allah i nuna mini wannan ranar Ƙawata, na haƙura ai ni da na ji shiru har na yanke shawarar za mu canja wuri."
Hajiya Saudah ta ce "Ina!! ai ba wannan maganar, ke wai ba ki ga yadda nake ba a gidana? Boka Barore fa ba wasa ba ne in gaya miki gaskiya."
Hajiya Laure za ta yi magana ta ankara da Yazeed akanta, fasa maganar ta yi daga ƙarshe ma sai ta katse wayar, ta bishi da kallon rashin gaskiya ta wani ci mur, a masife ta ce "Kai kuma mara Zuciya ƙalau kake kallona? mara kishin nasa?"
Zama ya yi kafin ya ce "Ni indai irin kishin nan naki na bin bokaye ne ba ni da shi, In da ƴan daba ki ka haɗa ma da tuni sun yi miki abinda kike so amma sai wani ƙarar min da dukiya ki ke yi akan bin bokaye, ai Ɗan Daba da ɗan Daba ake haɗa shi."
Ta yi tsaki kafin ta ce "Kai dallah rufe mini baki shashasha, kai ai soko ne na asali, yaron da ya gagari hukuma shine ka ke tunanin wasu Ƴan daba za su iya da shi? shima fa ɗan daban ne kuma ya na da ƴan daban, ni na fi son abinda zan yi masa illa lokaci guda."
"Allah ya bada sa'a" ya faɗa ya na taɓe baki.
"Amin" ta amsa a gadarance gami da miƙewa ta bashi wuri, a cewarta ya katse mata magana.
Kashingiɗa ya yi a kan kujera ya na lumshe ido, sanyin AC na ratsa shi, Kwatsam! tunanin Ma'u ya faɗo masa, musamman yanayinta a da ta na da fara'a ga ladabi da biyayya ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba "To wai meye ya sameta da ta dena walwala?" tambayar da ya yi wa zuciyarsa kenan sai dai ba shi da amsarta, ya daɗe ya na tunaninta kafin ya yanke hukuncin zuwa ya tambayeta ko za ta faɗa masa damuwarta.
miƙewa ya yi ya fice daga sashin Mommy ya nufi ɗan sashin da aka ware domin ƴan aiki.
Da Iya ya fara kaciɓuss ta yi saurin buɗa masa hanya gami da gaishe shi, bai amsa ba ya ce "Ni fa ba na so ki dinga gaishe ni tsofai-tsofau da ke"
Ta ce "To Ɗannan ai ni baiwarku ce, Hajiya ta yi mana umarnin mu dinga gaishe da kowa."
Ɗan tsaki ya yi kafin ya ce ''Ni ba na so, yanzu dai ina wannan baƙar yarinyar Ma'u?"
Iya ta ce ''Aff! Ta na kicin ita da Talatu bari in kira maka ita."
Da sauri ya ce "No ba buƙatar hakan zan je can in sameta."
Iya ta amsa da "To" a ranta ta na mamakin neman nata da yake yi.
Ta na cikin yankan Albasa kamar ance juyo ta na kallon hanyar shigowa idanunta su ka yi katari da shi, Gabanta ya yanke ya faɗi har ƙasa, da sauri ta sunkuyar da kanta ta na jin wata irin tsanarsa da shi da mahaifiyarsa, shi kuwa kallonta kawai yake yi kamar tsohon maye.
Sai da Talatu ta gaishe shi sannan ya farga ashe ba su kaɗai ne a wurin ba.
Haɗe fuska ya yi cike da manyance da nuna isa ya ce "Maza ki bar nan" Talatu ta ce "To" jiki na tsuma ta ajiye abinda take yi ta raɓa ta kusa da shi ta wuce.
Ma'u kuwa jin abinda ya cewa Talatu ya ƙara firgita ta jikinta ya ɗau karkarwa, tunanin abinda Mommynsa ta yi mata ne ya fara dawo mata, musamman irin tashin hankaki da azabar da ta fuskanta a wajen Boka.
Ta lula duniyar tunani hakan ya sa ba ta san ya zo kusa da ita ba sai jin muryarsa ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta tamkar an kauɗa mata baƙin ƙarfe a ka, zaburar da ta yi ta sa wuƙar hannunta ta kufce ta shigi ɗan yatsanta, da sauri ta watsar gami da damƙe yatsan ta saki ƴar ƙara.
Zazzaro idanunsa ya yi a kanta yana sa cewa "Lafiya??" ganin ta riƙe ɗan yatsa ya sa shi saurin riƙo hannun nata ya na cewa "Mu gani?" ƙoƙarin fizgewa ta fara yi ta na yi masa magiya akan ya saketa.
kamar zai fashe da kuka ya ce "Sannu! Ki dinga bi a hankali, kin ga kin yanke kanki ko tunanin me kike yi oho." ya na sakar mata hannun ta yi sauri matsawa gefe ta na fashewa da kuka.
Cike da takaicin kukan nata ya ce "Ai ka ji!!!! dama na zo tambayarki akan matsalarki ne amma yanzu kin ƙara ƙirƙiro wata matsalar."
Cikin kuka ta ce "Ba abinda yake damuna don Allah ka dena nemana"
"Dole in nemeki mana tinda kin barni cikin tunaninki? ki faɗa mini damuwarki ki ka sani ko zan iya yi miki maganinta?"
"Ba abinda yake damuna fa!' ta yi maganar ta na shashshekar kuka,
ɗan tsaki ya yi kafin ya ce "Ke na ga abin kukan ma ba ya yi miki kaɗan, ranar da ba kya kukan sai ki gaya mini abinda aka yi miki" ya faɗa tare da juyawa ya nufi hanyar fita Zuciyarsa sam ba daɗi.
Husnee misalin 02:40 juyi kawai take yi akan katifa yayin da bacci ya ƙauracewa idanunta, ba abinda take tunani sai Akhiee da kuma abinda zai iya faruwa idan iyayenta su ka san gaskiya, ta yi nisa a tunanin ta ji motsin wayar da ya bata wadda ta zo ta turata a ƙarƙashin filonta don gani take idan ta ajiye a wani wurin kamar za a iya dubawa a ganta.
Da sauri ta tashi ta zauna ta na dube-dube, babu alamar kowa a kusa Khausar ma sai baccinta take lakadan, zaro wayar ta yi daidai lokacin da wani sabon kiran ya kuma shigowa, Lamba ce sabuwa ma'ana ba save, gabanta ya yanke ya faɗi dandanan jikinta ya ɗau karkarwa ta shiga firgici da razani gami da kokonto akan me kiran nata da tsohon daren nan, shawarwari take yi akan ta ɗauka ko a'a wata zuciyar ta na gargaɗinta wata kuma na tunzurata akan ta ɗauka ɗin, zuciyarta na dakan sha-lugude ta taɓa kore gami da ɗora wayar akan kunnenta..............
SHARE FISABILILLAH
Na Kuɗi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632
*©️INDO*
[8/26, 4:38 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG
*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 18
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*M.W.A🦅*
"Kin Ƙi yin Bacci ko??" muryarsa ce ta doki dodon kunnenta, ta zazzaro ido a ɗan razane kafin ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya ba tare da ta yi magana ba,
Jin ta yi shiru ya sa shi ƙarawa da cewa "Me yasa to?" kamar za ta fashe da kuka ta fara magana cikin muryar shagwaɓa, "Tsoro na ke ji Akhiee!!" ɗan jim ya yi kafin ya ce "Haka ne? ko in zo mu tafi gidanmu?"
Ƙara firfito da zara-zaran idanunta ta yi "Tsakar dare ne fa yanzu!! kai ka na ina ba ka tafi gida ba??!" ta yi maganar cikin firgici.
Cikin wata kasalalliyar murya ya ce "Asma'u ni dare ba ya hanani yawo hasalima ban fiye bacci da daddare ba da rana nake yi, ina kusa da ke in ki na so na zo mu tafi zan zo idan kuma ba kya so to ki yi baccinki cikin kwanciyar hankali."
Ajiyar Zuciya ta sauke gami da sassauta murya a sanyaye ta ce "Ka na kusa da ni Akhiee to ta ya kenan?"
Ɗauke wayar ya yi daga kan kunnensa kafin ya furzar da wata zazzafar iska, ya so ya yi ɓaram-ɓatama kuwa, kiran sunansa da ta yi ne ya dawo da shi hayyacinsa, cikin nutsuwa ya ce "Ina nufin ki sa hakan a ranki kawai, Sai da safe yanzu zan shiga gida." da sauri ta ce "Akhiee!!" cikin wata irin shagwaɓa ta yi maganar kamar wata ƴar shekara biyu na kiran Ummanta, rasss zuciyarsa ta buga ya lumshe idanunsa da su ka fara canja launi kafin ya mayar mata da martani ta hanyar kiran nata sunan "Asma'uhh!!" murmushi ta saki kafin ta ce "Da gaske ne ka na kusa da ni? kuma ka na tare da ni Akhiee? "
"Kin san ba zan faɗa miki ƙarya ba don hankalinki ya kwanta, ki yi baccinki ina tare da ke, kuma za ki yi mafarkina." gyaɗa kai ta yi ta na murmushi cike da farin ciki da shaukin sonsa ta ce "Allah i tsare min kai Akhiee."
kai kawai ya gyaɗa ba tare da ya yi magana ba ya kashe wayar.
Sumar kansa ya cafka gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya me tafe da wata Zazzafar iska.
Ji ya yi an dafa kafaɗarsa ya yi saurin cewa "Russlan!!" Russlan ya zauna a gefensa kan katafaren gado irin na sarakuna da yake zaune a gefensa.
Cikin sanyin jiki Russlan ya ce "Ko shakka ba na yi ka na son matarka Risslan, ya zama dole ka dinga iya bakinka kar ka faɗa mata abinda dole ne sai ka kasheta da hannunka." jinjina kai ya yi kafin ya yi magana "Ban san me yasa Asma'u take da tasiri a kaina ba, na kasa samun nutsuwa sai tunaninta na ke yi, ji nake tamkar na je na kwana a kusa da ita domin na bata dukkan kulawata."
Russlan ya ce "Na gane hakan ai duba da yadda ka ke zagewa ka na gaya mata gami da nuna mata iyakar abinda ke ɓoye a Zuciyarka wanda ba kowane me wannan Darajar ba, amma fa ina ji maka tsoron Uban Dawa kar ya hukuntaka akan aurenta ba tare da sanin iyayenta ba."
Shiru ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce "Asma'u! itace mahaɗin rayuwata ko da so ko babu da ita zan rayu, ko da Father zai yi fushi zan jure duk hukuncin da zai yi mini, abu ɗaya kawai na yarda da shi kuma na sa a Zuciyata, ko da ta sanadin Asma'u za a yi mini izayar da ban taɓa fuskanta ba duk tsawon rayuwata ba zan Saketa ba ina tare da ita kamar yadda na yi mata alƙawari har sai in itace ta so rabuwa da ni wannan zan iya amincewa; Bayan haka kuma sama da ƙasa, Duniyar Mutane da ta Aljanu har ma da sauran Duniyoyi babu wanda ya isa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 19