Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta na jan ƙafafunta da su ka yi tsami ta isa wajen Motar, cikin sa'a ta na dubawa ta samu ta ɗakko ta dawo wajen Haj Saudah ta yayyafa mata ruwan. A firgice ta farka ba tare da ta jira wani abu ba ta miƙe za ta ci gaba da gudu, Haj Laure ta sa iya ƙarfinta ta riƙota ta na cewa "Ki tsaya mana, tinda Allah ya sa kin farko ki yi maza ki shiga Mota mu gudu." Haj Saudah ta na jin haka ta yi saurin buɗe Motar ta shige ta rufe baram don kar ma wani abun ya biyota. Haj Laure ma cikin sauri ta ɗakko wata babbar Darduma da ta gani a cikin Motar ta ɗaura a ƙugunta domin ɓoye ɓacin da kayan jikinta su ka yi. Haj Saudah ta zama ba baka sai kunne, Haj Laure ma ba magana, tinda ta fara tuƙa motar Ta ke ƴan addu'o'inta ta kama waccan ta saki ta kama waccan. Sai da ta biya ta ajiye Haj Saudah ko sallama ba su yi ba ta shige gidanta, Haj Laure ma ta ƙarasa nata gidan da ƙyar don kuwa tuni zazzaɓi ya rufeta. Yazeed na gama yin parking itama ta yi parking ta fito da kyar da kyar, turuss!! ya tsaya ya na kallonta sabida ganinta wujiga-wujiga kamar an ƙwatota daga bakin kura, ga Darduma da ta ɗaura a ƙugu jikinta ko mayafi babu. Cikin tsananin mamaki ya ce "Mommy! meye haka kuma?? lafiya??" wata sahihiyar kunya ce ta lulluɓeta sai ta ma kasa ɗaga ido ta kalli ɗan nata bare ta san amsar da zata bashi, suɓur-suɓur ta yi cikin gidan ba tare da ta saurare shi ba. Talatu ce kawai a Falon a lokacin da ta shigo, Talatu ta zuba mata ido cike da mamaki, "Sannu da zuwa Hajiya" ta faɗa ta na ƙara zuba mata ido. Banza ta yi mata, tsabar baƙin ciki da takaici ji take kamar ta haɗiyi Zuciya ta mutu, kai tsaye Ɗakinta ta nufa daga can ma ta wuce Toilet domin gyara jikinta. Yazeed kuwa tinda ya saki baki ya fara tunane-tunane sai da ya kwashi lokaci me tsayi sannan ya samu ƙwarin guiwar shiga cikin gidan, Zuciyarsa cike taf da tambayoyi akan Mommynsa. Husnee ta na shiga cikin gidan ta yi kaciɓus da Momy a tsaye sai safa da marwa take yi hankalinta a matuƙar tashe. Raɓe-raɓe ta fara yi Zuciyarta na tsananin bugawa, daga ganin yadda ran Mommy yake a ɓace ta san itama nata ran zai ɓaci. Mommy kuwa ta na ganinta ta yo kanta ta na cewa "Zo Dan ubanki!! wato kin kangare ba kya jin magana ko??" Cikin rawar murya ta ce "Don Allah Mommy ki yi haƙuri ba zan ƙara......" shiru ta yi sabida fizgota da Mommy ta yi ta fara ɗirka mata dundu da iya ƙarfinta ta na yi ta na cewa "Dan Ubanki ashe da ƙafarki ki fita? kin tashi hankalina na zata ma sace ki aka yi; gidan uban wa kika je???" Kuka kawai ta ke yi ta na bata haƙuri amma ba ta fasa ba sai da ta gaji tukunna ta saketa, a hakan ma ba ta haƙura ba ta ci gaba da faɗa kamar ta ari baki. Husnee ta ja ƙafarta da kyar za ta wuce ciki ta na tafe ta na sharar ƙwalla, Ɗaga hannun da ta yi ya bawa Mommy Damar ganin Zoben da Akhiee ya bata, ta sanya salati kafin ta ci gaba da cewa "Zo in gani, uban waye ya baki Zoben nan?? wato wajen Ɗan iskan Yaron nan kika je ko? sabida ke ga gantalalliya mara mafaɗa, to ba dani ba zo ki cireshi ko kuma in yi miki dukan kawo gishiri yanzun nan." jin abinda Mommy ta ce ya sata sake fashewa da wani sabon kuka me cike da tashin hankali gami da tausayin kanta. Ɓoye hannun ta yi a baya ta na ce "Don Allah Mommy kar ki cire mini ki bar mini shi, wallahi in na cire ransa ɓaci zai yi!!!". Kuka take yi tamkar ranta zai fita amma hakan bai sa Mommy ta tausaya mata ba. Cikin tsawa ta ce "Ni kike gayawa ransa xai ɓaci?? iye??? ni abokiyar wasanki ce ina magana kina magana???" Girgiza kai ta shiga yi domin kuwa ta kasa magana sabida kukanta da ke ƙara ƙarfi. Fizgota Mommy ta yi ta na ƙoƙarin cire zoben, Husnee kuwa ta damƙe hannunta katamau ta na kuka harda shiɗewa. Daidai lokacin Muddassir ya yi sallama ganin su na ta kici-kici ya sa shi saurin ƙarasowa ya na cewa "Lafiya kuwa, me ya faru??" cikin ɓacin rai Mommy ta ce "Wai Yarinyar nan sabida ta rainamu ta mayar da mu mutanen banza ita ce da fita ta tafi wajen wannan ɗan iskan harda karɓar zobe a hannunsa?, Ni fa ba za ta jawo min zagi ba gwara in shaƙareta in ta mutu ma dan ubanta ba ni da asara." Karyar da murya ya yi kamar wani mutumin kirki ya fara cewa "Haba dai Mommy, don zobe dai? don Allah ƙyale mata mana haba? ba wani abin tashin hankali ba ne, shi so ai ba a yi masa shamaki ku barta ta rayu da wanda take so don Allah." Mommy ta ce "Haba kai ma faɗe kake yi!, ina sane dai da hankalina ka san ba zan aurar da ƴata a inda za ta dinga ci da haram ba, Yaro ɗan ta'adda, taƙadari, ɗan iska, ɗan daba shi kake cewa mu bashi ƴarmu? " "To wai Mommy ba Allah ne me shiryawa ba? addu'a ya kamata mu yi masa ba mu dinga kiransa haka ba, don Allah Mommy kwantar da hankalinki; ke Husnee wuce ciki" ya ƙarasa maganar ya na kallonta, jin haka kuwa ya sa ta yi zuruf ta wuce ta na ci gaba da razga kuka. Mommy ta raka bayanta da harara kafin ta yi ƙwafa alamar zamu ƙara haɗuwa. Muddassir kuwa kwantar da kai ya yi ya dinga rarrashin Mommy gami da haƙurƙurtar da ita, ba don komai ba sai don ya na son su cimma manufarsu akan Akhiee. Husnee duk da hankalinta ba a jikinta yake ba ta na jinsu, kuma ta fahimci Muddassir ya na goyon bayanta don haka ta wani gefen farin ciki ya lulluɓeta. Kasancewar Sheikh Auwal ya kira shi ya sa ya shigo gida da wuri tin ƙarfe shaɗaya na dare, Lokacin wasu daga cikin Yaran Gidan sun yi bacci, Wasu kuwa Su na zazzaune curko-curko a tsakar gida kowa na jiran shigowarsa, wasu sun shirya yi masa rashin mutunci wasu kuwa gulma ce ta tsayar da su don su ji yadda za ayi. A tsaye ya tsaya fuskarsa ba walwala a taƙaice ya ce "Ga ni" a tsawace Yaya Babba ya ce "A tsaye za ka tsaya mana sabida rashin ɗabi'a?" Sai da ya doka dogon tsaki kamar ya tsaga gini sannan ya durƙusa cike da tsanar ƴan uwan nasa ya ce "A faɗa mini abinda ya sa aka nemo ni, idan kuma bala'in ne ya motsa kowa sai ya yi nashi duk zan iya ɗauka." Yaya Aminu ya rarumo takalmi a kusa da shi ya jefo masa gami da cewa ''Buhun Ubanka! mara kunyan banza shashasha; Baba Sa'idu bashi takardar nan ya ga tsiyar da ya jawowa kansa." Baba Sa'idu da ya zuba tagumi da duka hannayensa sai a lokacin ya ce "Uhm! to" Takardar ya miƙa masa gami da cewa "Yarinyar da ka je ka Aura to iyayenta ne su ka kai ƙararka Kotu Ranar Alhamis me zuwa za a zauna sai ka tanadi abin gaya musu, Bai kamata ka yi haka ba Muhammad, ka ga mu ba mu san ka yi ba amma ka jawo mana maganganun da zagi na jama'a, gidanmu gidan mutunci amma ta sanadinka ana yi mana wani banzan kallo, ka ƙoƙarta ka saki yarinyar nan tin kafin ka ƙara jawo mana wani mugun tabon." A duniya in akwai abinda Akhiee ya tsana to na biyunsa a ce sanadinsa mutuncin gidansu ya zube, cikin ɓacin rai ya fizgi takardar sannan ya ce "Ba kotu ba ko Duniyar za su haɗo ta taru a kaina ba zan saki Asma'u ba bare wata Kotu, gwara ma ku dena wahalar da kanku kowa ya je ya yi baccinsa, Asma'u tawa ce saɓanin ni kuma sai dai Mutuwa domin zan zubda jini akanta. Inna Huwaila Matar Baba Sa'idu ta sa salati da sallami kafin ta ce "Kai ɗannan ka ji tsoron Allah, wai ni Huwaila ina ganin masifa a gidan nan!!, Yaro ɗaya amma ya zama wake ɗaya me ɓata miya??" Ai kuwa kamar jira su ke yi ta buɗe musu hanya nan fa wasu daga ciki suka fara sako tasu maganar, duk cikinsu ba me faɗar da daɗi sai baƙaƙen maganganu abin har ya wuce kansa ya koma kan Mahaifiyarsu, wasu ma cewa suke yi ba Jinin gidan ba ne. Sheikh Auwal dai da abin Duniya ya ishe shi sai ya zame jiki ya wuce Turakarsa, ya na shiga ya nemi wajen zama dirshan sannan ya bawa kukan da ke cin ƙarfinsa damar fitowa. "Allah ka fi mu sanin abinda ke tattare da Yaron nan, Ya Allah ka sani Mahaifiyarmu ba halinta ba ne haka Mahaifinmu ma Ya Allah indai ba jininmu ba ne Allah ka nesanta mu da shi ka fitar da shi daga cikinmu ka bayyanar da gaskiyar asalinsa." Addu'ar da yake yi kenan a cikin kukan nasa, Zuciyarsa cike take taf da ƙunci da tarin damuwa ga zafi da ƙunar abinda ke faruwa a cikin wannan Babban gida nasu. Zara kuwa ta kasa fitowa daga ɗakinsu, ta na jin yadda suka ƙare masa tatas ba abinda ta iya yi sai aikin kuka, har cikin ranta ta na baƙin cikin irin abinda ake yiwa ɗan uwan nata. Sai da ya gama saurarensu ɗaya-bayan-ɗaya sannan ya kakkaɓe rigarsa ya tashi, kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya zauna gefen gado ya zuba tagumi, jin idanunsa yake yi tamkar an ɗora su akan garwashi ana gasa su, Zuciyarsa kuwa har wani turnuƙu take yi tamkar za ta fito ta baki, da zai iya yin kuka da ya yi ko zai samu salama sai dai kash!!! shi da kuka sun riga sun yi hannun riga tin kafin Mutuwar Mahaifiyarsa. "Come hare my son!" muryar Mother ce ta karaɗe kunnuwansa ya yi saurin ware idanunsa domin ganin ta inda ta ɓullo. Kasancewar ɗakin ba haske ya sa ba ya ganinta sai dai hasken idanunta da su ka yi kalar Golden ya iya gani. Da sauri ya miƙe ya nufi inda take ta yi saurin rungume shi tsam!!!!. nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke Kafin ya fara maga cikin rarrabewar Murya "My Mo...therh!!!... me..yasa..... suke yi min haka??? Shin da gaske..... ni ba.....Jininsu ba ne???????" Yadda yake maganar ba ƙaramin taɓa Zuciyarta abin ya ƙara yi ba, ranta ya ƙara ɓaci Zuciyarta ta ƙara dugunzuma, a gefe guda kuwa tsananin tausayin ɗan nata ya na ƙara taso mata, ba ta iya bashi amsar tambayarsa ba sai dai ta ce "Yau ban amince ka kwana a gidan nan ba, ka kasance tare da ni Ɗana....." Ba ta jira abinda zai kuma cewa ba ta ɗauke shi su ka ɓace daga ɗakin. *©️INDO* [9/6, 7:41 PM] INDO: *🪻S-K🪻* Ep 22 Tinda ta ɗaukeshi bai ƙara sanin inda kansa yake ba har sai da Asbah ta yi da ya ji Masallacin cikin gidansu an yi kiran Sallah sannan ya farka. Tin kafin ya buɗe idanunsa ya ji ɗumin Mutum a kusa da shi, ya yi shiru ya na sauraren Bugun zuciyarta da ya tabbatar masa ba kowace ba ne face Razia. Cikin nutsuwa ya sauke wata nannauyar ajiyar Zuciya kafin ya buɗe idanunsa ya ɗorasu akan kyakkyawar fuskarta. Bacci ta ke yi cikin mutsuwa da kwanciyar hankali, kallo ɗaya ya yi mata ya gane ba ƙaramin jin daɗin baccin take ba don da alamu ma ta daɗe ba ta yi me daɗinsa, a take kibiyar tausayinta ta soki Zuciyarsa, ya zuba mata ido tamkar ba zai dena kallonta ba, ya daɗe cikin wannan yanayin kafin ya ƙara janyota jikinsa ya ringumeta tsam, ya na jinta har cikin ransa. Cikin baccinta ta ƙara jin sauyin yanayi don haka ta ƙara duƙunƙuneshi ta ja mumfashi ta sauke ta ci gaba da baccinta. Mother ta ce shigo Ɗakin cikin suffar Mage, bayan ta zo daf da Gadon ta koma suffar Mutum, cikin tattausar muryarta ta ce "Rislan! kar ka biyewa Razia ka makara a Sallah fa." Lumshe ido ya yi gami da sauke wani gwauron nishi kafin ya yi magana tamkar wanda aka yiwa dole "Uhm! Uwa zan tashi; ba na so na nesanta da ita ne ta farka." Mother ta murmusa kafin ta ce "Abinda ya zama dole ne Ɗana, a Masallaci fa har an idar da Sallah." Bai ce komai ba ya janye Razia daga jikinsa a hankali ya gyara mata kwanciya sannan ya sakko ba don ransa ya so ba, haka kawai yau ya tsinci kansa da son kasancewa tare da ita. Ya na idar da Sallah ya yi musu Sallama ya wuce wajen su Rahma don jin yadda suka kwana. Yau Ta kasance Ranar Alhamis, Ranar da wasu ke ɗokin zuwanta wasu kuwa su na cike da fargabar ganinta. Sheikh Auwal, Babban Yaya, Baba Sa'idu, Akhiee Daddy, Mommy, Muneeb, Muneer, Husnee... Malam Kabiru, Malam Usaini Duk sun hallara a cikin Kotun yayin da ta ɗauki shiru kowa ya mayar da nutsuwarsa akan abinda ke faruwa a cikinta. Ana kammala sauraren ƙarar Wasu aka karanto ta su Akhiee, Me Shari'a ya buƙaci Matar da Mijinta su fito. Bayan sun fito inda aka tanadarwa duk wanda zai yi magana su ka tsaya, Mai Shari'a Ya yiwa Husnee tambaya akan da gaske ne an Ɗaura Aure ta amsa masa da eh. Sannan aka dawo kan Akhiee aka tuhumeshi akan amsa laifinsa sai dai shiru bai ce ƙala ba, juyin Duniya ya yi musu banza har mai Shari'a ya gaji ya ɗaga ƙarar tare da cewa Akhiee ya nemo Lauya. Da haka aka tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba kowa ya san inda dare ya yi masa tare da tunani iri daban-daban, musamman a ɓangaren Husnee wadda ta cika da tsoro da firgici sabida jin ya yi shiru, ta na matuƙar tsoron ya ce zai saketa. Akhiee kuwa ko ta kansu bai ƙara bi ba shima ya kama gabansa, Su Yaya Babba sai faɗa su ke yi kamar za su ci babu, shi dai Sheikh Auwal ya yi musu banza. Hajiya Laure Sanye take cikin lintsumemiyar Atamfa tsadaddiya ɗinkin riga da Zani ta cokara ɗauri ture ka ga tsiya. Cikin takun Ƙasaita ta fito Falo ɗagwas-ɗagwas kamar budurwar agwagwa. Ma'u da Talatu su na ta ƴan gyare-gyare kasancewar Yamma ce, kafin ta zauna ta kallesu fuska a dake cikin nuna ƙyama da wulaƙanci ta ce "Menene haka? wannan aiki ku ke yi ko iskanci?? wai ba na ce kar wannam ƙazamar ta ƙara shigo mini Falo ba ma??" Ta ƙarasa maganar ta na tsare Ma'u da idanu. Ma'u kuwa tin da ta ganta jikinta ya ɗau karkarwa domin kuwa mugun tsoronta gami da tsanarta ta ke ji, ko hanya ba ta son haɗawa da ita a yanzu. Talatu ta rissina gami da cewa "Ayi haƙuri za mu gyara." Dogon tsaki ta lafta kafin ta ce "Ƙazamar banza tarin najasa; za ku fice ku ban wuri ko sai na daddallawa Yarinya mari?? ƴaƴan matsiyata." Jiki na rawa Ma'u ta yi gaba ta na kuka ƙasa-ƙasa Talatu ta bi bayanta cikin sanyin jiki. Hajiya Laure ta yi ƙwafa kafin ta karkace ta yi jaɓar a kan Sofa. wani mugun ihu ta zurmuƙa jin ta zauna akan wani abu tamkar Allura, azaba ta ratsata har tsakiyar kanta, a durƙushe ta miƙe ta ma kasa tashi tsaye sabida azaba gabaki ɗaya mazaunanta sun ɗauki wuta, lokaci guda idanunta su ka ciko da hawayen azaba. Sai da ta ɗan huce sannan ta juya ta dudduba inda ta zauna ɗin ko za ta ga wani abu sai dai fayau ba wani abu ba alamunsa. Canja mazauni ta yi zuwa kan kafet don kuwa ta ji attaruhu ko za ta ƙara zaman kan kujerar ba yanzu ba, a ƙasan ma a karkace ta zauna ta na yi ta na yatsine fuska don kuwa har yanzu ba ta dena jin zafi ba. Ta na nan zaune ta na hutawa ba a fi minti biyar ba ta ji wani irin taku ƙwaras-ƙwaras ya na tinkarota, ta shiga kalle-kalle amma ta ga fayau kamar ba a taɓa halittar mutum ba, tsoro da firgici su ka ɗarsu a Zuciyarta lokaci ɗaya, Talatu ta fara ƙwalawa kira da tunanin ko itace a wajen, jin shiru kuma ga takun ta na ji ya sa ta yunƙura ta miƙe cikin sauri ta nufi hanyar da zata bar Falon. Garam!! ƙofa ta rufe, nan take wata muguwar dariya irin ta Boka Barore ta karaɗe Kunnuwanta, Ihu ta fara kwararawa sai dai kash!! ta na farawa ta ji kamar an sa buredi an toshe mata maƙogoro muryar tata ta dena fita. Inuwar Mace ta gani a gabanta ƴar siririya sai yalwar gashi har ƙugu shima ga inuwarsa nan buzu-buzu, Haj Laure ta ƙara zazzaro ido gwale-gwale kamar sa faɗo ƙasa, Zuciyarta na wani mugun duka tamkar ana surfe da sussuka a cikinta. Da kyar ta samu ta taka da gudu don komawa Bedroom, ta na zuwa ƙofar bedroom ɗin taga wannan inuwar a gabanta, sai juyi take ta na kwarkwasa ga ɗan ƙugun nan tamkar na babe sai faɗin mazaunai ƴan ciri-ciri. Wani mugun burki ta ja wanda ya sa ta kusa shiɗewa sabida Salon bugun Zuciyarta da ya canja. Tsere su ka shiga yi ita da Inuwar a Falon ta na gumi ta na kuka ta na majina ta na yarcewa ita kuwa Inuwa ta na ci gaba da razanata, sai da ta galabaita sosai har ta kai ba ta iya tafiyar ta zube a wajen turuss!! sannan inuwar ta matso daf da ita ta na wata mahaukaciyar dariya, ba tare da ta dena dariyar ba take magana cikin murya marar daɗin ji "Ba a raina aikin Boka Barore!!!, sannan ba a cin Amanarsa a canja wuri, ba a zaginsa ko a bayan idonsa!!!!, idan ya fara yiwa mutum aiki har sai ya yi nasara yake denawa ba zai taɓa ƙyale ku ku je wajen wani Bokan bahahahaha!!!!" ta ƙarasa maganar gami da ƙaro sautin dariyarta, Ta kai minti ɗaya a haka sannan ta ɓace tamkar ba ta taɓa wanzuwa a wurin ba. Haj Laure ba ta iya tashi ba sai ƙara bajewa da ta yi ta kwanta ta saki wani ɗanyen kuka me matuƙar taɓa Zuciya. Su Ma'u su na fita su ka ci karo da Yazeed ya na ƙoƙarin shigowa, ya na ganinta tana kuka ya yi caraf ya riƙo hannunta, a zafafe ta fara ƙoƙarin fizgewa sai dai ya hanata damar hakan, Cikin sassanyar murya ya ce "Ki nutsu don Allah ki faɗa min abinda ke damunki, Mommy ce ko???" A tsiwace ta ce "Ni ka ƙyaleni, ka sakar min hannuna ni ba ƴar iska ba ce wallahi, kuma zalumcin da aka yi mini Allah zai saka min." "Ke Talatu yi tafiyarki" ya faɗa ya na kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta ci gaba da tafiya. mayar da hankalinsa ya yi kan Ma'u tamkar me shirin fashewa da kuka ya ce "Don Allah ki yi haƙuri ki saurareni, ki karɓi kukana sannan ki jiƙaina Ma'u! maganar gaskiya kin jefani cikin wani yanayi, na rasa nutsuwata ba dare ba rana tunaninki nake yi, ina son sanin abinda ke damunki." Cikin tsananin tsanarsa ta ce "Ba zan taɓa gaya maka abinda ke damuna ba azzalumi, kuma ka ƙyaleni ba na son ganinka na tsaneka!!!" ta yi maganar ta na kuka tamkar ranta zai yi fitar burgu ya bar gangar jikinta. Kiɗimammun idanunsa da su ka rikiɗa zuwa kalar ja ya zuba mata na ɗan lokaci kafin ya fara magana tamkar zai yi kuka "Ma'u gareki sam ban zamo azzalumi ba kuma ba zan taɓa zamowa Azzalumi gareki ba, burina kullum na inganta rayuwarki domin ina buƙatar rayuwa tare da ke, Ina...sonki Ma'u, ko da za ki tsaneni hakan ba zai sa na canja ba, sai dai in kasheni ki ka yi shine na san dole zan barki, kuma in na mutu ki sani na mutu da tsananin Sonki, ko da ba ki kasheni ba idan na mutu ko a yanzu ko anjima ke ce silar mutuwata domin ba ni da wata damuwa a yanzu face ke!!" ya ƙarashe maganar cike da son nuna asalin gaskiyarsa. "Ni ba zan taɓa yarda da kai ba, kuma ba zan taɓa sonka ba, na tsaneka!! na tsaneka!!!! kuma tsakanina da ku sai Allah ya yi mana Hisabi, ni ka sake ni in tafi." Gudun zuciyarsa ne ta ƙaru, lokaci guda yanayinsa ya ƙara canjawa damuwa da tashin hankali su ka kawo masa hari lokaci ɗaya, "Ma'u me na yi miki? me yasa ba za ki soni ba??, indai wani hali nawa ne ba kya so Wallahi zan dena indai har za ki zamo gatana; Ma'u Bansan ya akai ba kawai na wayi da narkon Sonki a Zuciyata, wallahi ji nake idan na rasaki tamkar zan rasa raina, idan na ji kin ce kin tsaneni tamkar ana watsa min ruwan wuta haka nake ji, ki tausaya min kar ki hukunta ni ta wannan hanyar ko da kuwa na yi miki laifi, wallahi ba wasa ba yaudara a cikin zancena; duk yawan Matan Duniya ke kaɗai nake yiwa irin wannan Makahon so, Ma'u kar ki bari rayuwata ta salwanta ta sabauce sabida soyayyarki Please!!!" daga yadda yake maganar za ka gane ya na cikin mawuyacin hali gami da tashin hankali, Ma'u kuwa ta gaji ma da jin muryarsa, ji take da akwai wani makami a kusa da ita ba abinda zai hanata buga masa ta ƙwace hannunta, ba ta ce masa cikal ba sai kuka da take yi kamar maƙogoronta zai tsage sabida shashsheka. Sakar mata hannun ya yi gami da cewa "Allah ya huci Zuciyarki, ba yadda na iya ne dole sai na gaya miki, na kamu da cuta kuma ke ce kaɗai maganinta." "Allah ya sa ma ka mutu na huta azzalumi" abinda Ma'u ta faɗa kenan ba tare da ta jira amsa ba ta arta da mugun gudu. Da ido ya rakata har ta ɓacewa ganinsa sannan ya kutsa kai Falon Haj Laure. Su na gama turnuƙu da inuwarta ta kwanta ya shigo. Ya yi mamakin ganinta a tile a gefe kamar kayan wanki, amma da yake hankalinsa ba a

Chapter 15 of 19