Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Ummee Garkuwa · . AGOGO . "A a, me zan gani? yanzu-yanzun nan daga tafiya yin alwala har an samu wacce ta sace min agogona ?" a razane matan da ke cikin ɗakin su ka kalleta haɗe da nuna tsananin mamaki a fuskokinsu, cigaba da bincike jakarta ta yi tana yi tana haki kamar wacce ta yi gudun mita dubu da ƙafarta. wata da ke gefe ta ƙaraso kusa da ita cikin yanayin lallashi-lallashi ta ce, "haba baiwar Allah duba jakar ki dai da kyau." a ƙufule ta waiwayo bayan ta mata wani irin rikitaccen kallo. "ba ga shi ba kina kallo ba agogon a cikin jakar, wacce irin dubawa zan yi wacce ta wuce wannan?" ta nuna mata ƙasan jakar. itama cikin ƙuluwar ta mayar mata da amsa. "to, ko ma meye nan ba wacce ta tunkari inda jakar ki take sai dai in wani wajen kika jefar da shi." jefo jakar ta yi wajen da matar take. "ki yi wa Allah ki duba da kanki tunda kina ganin sharri nake.." da sauri ta katseta. "Ni asuwa? ke dai da take taki ke zaki duba, kin ga ni na matsa ma." ta ja gefe da sauri. "na rantse da rabbil izzati ko a fito min da agogona ko kuma na yi rashin mutumcin da ba shi da magani." wata kakkaurar mace ce ta shigo ɗakin da sauri jikinta sanye cikin danƙareran leshi. cikin yanayi na firgici da mamaki ta ce, "Hajiya Sa'adatu menene ? me ya faru?" matar da a ka kira da sunan ne ta yi tsaki. "hmmm, Hajiya A'i, daga na fita ɗauro alwala aka samu wata ta yashe min agogona na gwal." wacce aka kira da Hajiya A'i ta kama baki da yatsunta haɗe da salati, kallon mutanen ɗakin ta yi su biyar cif ta sauke numfashi, cikin ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "gaskiya bana jin ɗaukar shi a ka yi sai dai in jefar da shi kika yi Sa'adatu." "ai ga jakar nan a gabanki ki duba da kanki ki gani." sunkuyawa ta yi ta ɗauko jakar, duk wani lungu ta saƙo sai da ta bincike babu alamar a gogo a ciki. cike da mamaki ta ɗago kai tana kallon Sa'adatu. "a ina kika yi alwalar?" kasa magana ta yi sai nuna mata banɗakin da ke cikin ɗakin. da sauri A'i ta tafi banɗaki ta shige ta daɗe tana dube-dube ba abinda ta gani hakan ya sa ta dawo cikin ɗakin jikinta na rawa. "ki yi haƙuri Hajiya Sa'adatu, zan duba miki a nutse." "ban gane ba ? wanne wani irin zance ne mara kan gado ? haƙuri fa kika ce ? agogon zinaren zan yi zaman jiran haƙurin har a ganshi ? taɓ ! na rantse da Allah ba wacce ta isa ta fita daga ɗakin nan sai na caje ta, ba zan yarda ba fa sai ɓarauniyar matar nan ta fito min da agogona." duk matan wajen ba wanda ya iya magana saboda kiɗima da mamaki. daƙyar wata gajera ta yi magana ta na wa Hajiya Sa'adatu kallon banza. "baiwar Allah ki yi duk abinda kika ce zaki yi amma ki ji da kyau na fi ƙarfin satar agogo ko da kuwa na lu'ulu'u ne." ta ƙarasa da jan dogon tsaki. ɗakin ne ya kaure da hayaniyarsu kowacce na magana akan tafi ƙarfin satar agogon da Hajiya Sa'adatu ke ikirarin an ɗauke mata. "ya isa don Allah ku yi shiru." Hajiya A'I ta ce tana goge gumin kan goshinta. "Zo ki ji, Hajiya Sa'adatu." ware ido ta yi tana wa A'i banzan kallo. "in je ina ? taɓ! ni da daga nan ba inda zan ɗara sai da agogona." cikin ƙosawa da halin Sa'adatu, A'i ta ce, "abinda yasa na ce miki ba satar miki a ka yi ba, matan dake cikin ɗakin nan sun fi ƙarfin satar agogonki, kinga waccen?" ta nuna wata mata dake zaune tana danne-dannen waya, yanayinta babu damuwa ko kaɗan. "matar chiyaman ɗin garin nan ne, waccen ta kusa da ita ƙawar ta ce, matar Sanata, wannan kuma matar." ta nuna wacce ta ce tafi ƙarfin satar agogo. "matar Alhaji Ali dala, kin san dai shi ne ya fi kowa kuɗi a garin nan, wannan kuma..." ta nuna wacce ta fara yin magana. "matar Kwamishina ce, wannan kuma." wata mace dake zaune tana watsa musu kallon banza. "matar mataimakin gwamnan da ya sauka ne, don Allah ki faɗamin cikin su wace ce bata fi ƙarfin agogon gwal ba." cikin tsananin mamaki Sa'adatu ta ce, "Allah ya sa matan shugaban ƙasa ne, ba abinda ya shafe ni agogona kawai na sani." AGOGO Group 7 Nafseen Fahad Ko kallon ta basuyi ba domin dukkan su ransu a bace yake hajiya sa adatu ta sake dawo cikin dakin fuskar ta a murtuke tana kallon su,Kai nifa afitomin da AGOGO Na domin bazan taba yafewa ba,ko Kuma kowacce tazo Na cajeta,hakan ya sake fusata hajiya larai wadda tunda aka fara wanna Abu Bata ce komeba ranta a bace take magana ke angaya Miki matsiyata ne mu kidube mu ki gani shin ga alamun talauci ko Kuma yunwa me za ayi da wani rubabben agogon ki to bara kiji wallahi ko a cikin nan aka daukar miki Baki Isa ki caje wani ba,ta koma gefe ta tsaya gajerar macan da ke zaune ta Mike tsaye tana kallon hajiya sa adatu cike da takaisa irin Na manyan mata ke bara kiji idan tujara kike ji muma a shirye muke kudi kuwa talakawa akema kyalkya ba mu ba,Don haka ki kiyayeni idan ba haka ba zansa ai Miki checking out Zan sanya rayuwar ki cikin ukuba Zan gigita rayuwar ki,hajiya A'i da ke tsaye hankalinta a tashe tana kallon su da sauri ta karaso tana magana kasa kasa haba ku kuwa ai Ina ganin wanna maganar Bata Kai Nan ba bai kamata ace akan wannan kankanin Abu antashi hankula ba Kamar ya fadin hajiya sa adatu ai wallahi bazan yarda ba tayaya idan ba acikin subane to waye ya dauka nide banga wani ya shigo ba Don haka a fitomin da AGOGO Na *********** Acan kuwa cikin gida hayaniya ce Kai ta tashin mata sun cika gida makil Ana ta shagaili hankalin su kwance hajiya binta ce ke kaikawo a tsakiyar gidan tana raba abinci cike da mamaki take kallon amaryar jego wato hajiya bilkisu ta tafito daga nata bangaren sanye take ta wata dandasheshiyar leshi hajiya binta ta karasa inda take tana magana Wai ina hajiya sa adatu tundazu bangan taba,tana dayan bangare tare su hajiya A,'i cewar hajiya bilkisu to bara naje domin inasan magana da ita Kai tsaye ta wuce dayan bangare ta bude kofar falon ta karasa maganar hajiya sa adatu ne ya karasa cikin kunnan ta,wallahi ko kufito min da AGOGO Na ko Kuma hukuma ce zata rabani da ki mamaki matuka ya kamata tana ka AGOGO Nafseen Fahad Group 7 (cigaba) Ta karasa tana mamakin jin Abunda kunna yen ta suka ji kallon su daya bayan daya take har ta karasa cikin falon hajiya sa adatu tana cika tana batsewa kallon hajiya binta ya menene haka me nakejin haka ne meke faruwa hajiya sa adatu ta karasa tana magana ceke da fushi matuka a fuskanta wai daga in zagaya Na daura alwala Na dawo cikin dakin banga AGOGO Na ba, da mamaki matuka tana kallon matan da suke cikin dakin idon hajiya binta ya sauka Kan hajiya Fatima dake zaune tana latsa wayar ta alamun hankalinta baya kansu hajiya binta karasa inda take tana magana cike da nuna Isa malama fito Mana da abunda Kika sata sai yanzu ta sauke wayar ta Mike a hankali kau kau hajiya binta taji saukar mari a fuskan ta sannan hajiya Fatima ta kalle ta idan aikin ki Shan kwaya to kisani wuri wuri nake zuwa asalin matatar giyar ki kalle Ni kinga nayi Miki Kama da barauniya,sauran matan da suke tsaye suna kallon su cike da mamaki matuma hajiya sa adatu ta karaso tana kallon ta kinga malama ki fito min da gwal Dina wannan hargagin bazai fisshe kiba kawai ki fito min da AGOGO Na ba tare da wani magana ba itama taji saukar Mari kau ko jira hajiya sa adatu batayi ba itama ta wanke hajiya Fatima da Mari Nan fa fada ya kaure Duke Duke falon ya hargitse kuruulruwar mata kawai kakeji Hajiya sa adatu tai wani kururuwa Tai Kan hajiya Fatima suka kaure da dakeni indake ki fada sosai matan dake cikin falon suka rasa yadda zasuyi dasu haka yasa duk suka fito daga cikin dakin izuwa harabar gidan a guje hajiya Fatima ta fito hajiya sa adatu tana biye da ita rike da wuka a hannun ta duk matan suka tsarwatse kowa ce ta Kama gaban su, *AGOGO* 003 LABARIN HADAKA RUKUNI NA 7 MUHD AL'AMEEN Duk da cewa ba yau ne Hajiya A'i ta san halin mutumiyar tata ba wajen tsananin masifa da bala'i, amma duk da haka ta yi matukar mamakin abin da tayi. Shiru ne ya biyo baya har na 'yan wasu dakiku da ba za su wuce goma sha bakwai ba, wanda hakan ne ya baiwa HAJIYA sa,adatu damar ci gaba da magana. "in ba ma matacciyar zuciya da rashin sanin ciwon kai ba me zai sa baka rasa ci da sha da duk wani jin dadin rayuwa ba ka dauki kayan wani!!? ni dai na gode Allah da ba mu yi gadon sata ba a zuri'armu!!!" Wannan furuci nata ba karamin kona zuciyoyin wadannan mata ya yi ba, musamman wannan gajeruwar matar, cikin dacin rai ta fizgo kallabinta ta daurashi a kugunta ta nufo kan HAJIYA SA'ADATU tana maida mata da martani. "Ah hayyeh!! mun gode Allah ma da a iya gadon satar kawai muka tsaya tunda mu ba mu yi ta maita ba!!" Aikuwa wannan martani yayi matukar taba zuciya Hajiya Sa'adatu domin Jinsa ta yi tamkar an soka mata mashin da aka ciro daga wutar makera.... *AGOGO* CI GABA + Domin Jinsa ta yi tamkar an soka mata mashin da aka ciro daga wutar makera a kahon zuci, nan take idanunta suka canja kada ta soma hucin fusata tamkar wata rikakkiyar gamsheka kallo daya zaka yi mata ka san cewa an kaita bango, wanda duk yasan tsananin bala'i da tashin hankali irin nata to dole ne ya yi matukar tausayawa wacce take shirin afkawa. Ita kuwa Hajiya A'i gaban wannan gajeruwar mata tasha. "don Allah Hajiya Rabi ki yi hakuri kar kema ki biye mata ku zama daya, idan ita tana jin bata da hankali ai ke kina da shi, haba wannan abu sai kace..... katse maganar tata ta yi. "don Allah maman hanif ki rabu dani in koya mata hankali duk rashin kunyar da take ji da shi muna daidai da ita kar taga ko don mun yi shiru ta yi tsammanin ko tsoronta ake ji!" Ita kuwa Hajiya Sa,adatu tuni ta yi kukan kura ta suri wani murfin tukunya ta wurgeta da shi, tana kaiwa aya a maganarta sai ta ji saukar abu gau! gau!! akan goshinta nan take goshin nata ya dare jini ya soma tsartuwa..... *AGOGO* CI GABA* Wani irin zogi ne taji a goshin nata wanda ya sanyata kwarma wani uban ihu nan take ta sulale kasa sumammiya!! duk wannan abu dake faruwa akan idon Hajiya Binta ya faru, al'amarin da ya sanya ta dora hannayenta biyu aka tare da kidimewa lokaci guda. kai! ba ma Hajiya Binta kadai ba hatta dukkanin matan dake wajen sai da suka tsorata, da yawa daga cikinsu suma sun dora hannu aka ganin irin wannan aika-aika da Hajiya Sa,adatu ta yi. Kash! rashin sani yafi dare duhu, inda Hajiya Sa,adatu tasan me zai biyo baya da ba ta yi yunkurin aikata wannan mummunan abu ba! nan take jama,ar dake wajen taron sunan suka soma sulalewa saboda sanin tsananin bala'i da masifar da zata iya biyo baya kasancewar sanin hatsabibancin mijin wannan mata Alhaji Ali Dala, idan Hajiya Sa,adatu naji da musiba to ya ninkata sau dari, mutum ne da ko kadan baya tsoron rikici ko wane iri ne hasalima shi yake taro bala'i kuma yayi amfani da dukiyarsa yaci nasara, shekararsa 40 kullum cikin shari'a yake na cin ye hakkin AGOGO Cigaba. (Rukuni Na bakwai) Nafseen Fahad Alhaji Ali dala mutun ne Mai son zuciya gadara jiji da Kai ga uwa uba Kuma rashin mutunci domin baya gani kowa da gashi muddun ka shiga hanyar shi ko Kuma fara takun saka da shi bazai taba barci ba harsai yaga ya ci mutuncin ka A harabar gidan taron suna kuwa kowa ta fara sabewa domin ganin aika aikar da hajiya sa adatu ta aikata hajiya binta dake tsaye hankalin ta a tashe ta karaso tana kallon hajiya sa adatu cike da rudu da firgici kin San abunda Kika aikata kuwa kinsan waye mijin ta kuwa kin San abinda zai biyo baya kuwa dukkan wadan Nan tambayiyi da hajiya binta ta amto ko gyezau ajikin hajiya sa adatu sai wani irin kallo ma tayi mata taja wani dogon tsaki mtsss idan nata Kuma sani nima yau kunga nawa ko waye mijin nata yazo Ina jiran shi,hajiya bilkisu me jego tsaye ta rasa meke Mata dadi kallon su kawai take cikin bacin Rai da bakin ciki aiyana wa take a zuciyar ta uwar me yasa Na gayyaci wadan Nan mahaukatan dama rashin mutunci da zasumin kenan maganar hajiya binta ya waiway da ita daga dogon tunanin data fada muje asibiti tana zubar da jini karda mu rasa ta duk suka kinkime ta Baki daya suka fita ******** A kofar gida sukai birki ganin motar Jami an Yan sanda da suka tare su hankalin kowacce a tashe hajiya Amina ta karasa inda Yan sanda suke lokaci daya suka fara girmamata sannan ta kalle su karda ku bar wata tabar Nan ku wuce da kowa police station sai ayi maganacan,Nan fa hankalin su ya sake tashi kowa Yana kallon ta,, Haba hajiya amina wannan ai rashin adalci ne cewar hajiya binta Wanda jikin ta yake ta rawa tun zuwan Yan sanda kalmar adalci Ana Dan ganta tane ga Wanda aka cuta bayan Sherri da kukai Mana kina ganin Zan zuba ido a cimun mutunci wallahi kowa sai jikin shi ya gaya me ku tafi dasu Nan aka tattarasu sai cikin mota hajiya Amina ta shiga suka wuce A bayan kanta aka tattarasu su aka ajiye hayan ya ya kaure da sauran surutai a tsakanin su wani mutun kakkaura ya karaso cikin wajan Kallon su kawai yake daya bayan daya fuskar shi murtuke ko alamun fara a babu Ina hajiya bilkisu cewar dpo jikin ta Yana tsuma ta Mike tana magana ganinnan yallabai fito da sauri tafito ya kalle zakije gida Amma ki sani idan muna da wani Karin baya dole zamu nemeki jikin ta Na rawa babu damuwa Zaki iya tafiya cewa dpo da sauri sauri ta tattara kayan ta ta fita ya juya bazan iya zama cikin wanna kuntatar ba ya kamata afitar Dani domin niba barauniya bace afusace dpo ya juyo Yana kallon ta ke har kin Isa kibamu umurni yan aikin da Kika dauka a gida su zakiba wannan umurni Amma ki sani Nan office din hukuma Kuma hukumar Bata uban ki bace duk suka Kara razana ganin yadda yake ma hajiya sa adatu magana yaci gaba da cewa muddun Kuma Na sake jin wata magana daga bakin ki lallai Zan dandana miki ukuba ta juya wa yayi ya fita duk suka kalle ta hajita sa adatu ta fara kuka wallahi bazan bari acimun mutu ci ba wannan ai rashin adalci ne tayaya zasu sace min AGOGO sannan Kuma azo a rufeni nima Ina da gata Na Kuma idan yazo ku lallai Kuma bazaku Sha ba haka ta ci gaba da kuka babu wadda ta kuka ta amatan domin ko wacce tashin hankalin ta ya ishe ta ******* Daga cikin gari kuwa ko Ina ya dauka harta gidan jaridu sun buga abunda ya faru a gidan hajiya bilkisu Na sace agogon da akayi ra ayoyi Na ta gudana daban daban wasu nanfarin ciki da cewar Allah yara kwamma da hakan dama ba kyauta take da shi ba ga rashin mutunci Kai abunde ba acewa kome,hajiya bilkisu dake zaune a falin gidan ta tayi jugun cike da tashin hankali da mamaki yau itace aka Kai police station harda zargin ta cewa tasaci agogo ta sauke wani gwauron numfashi sannan ta Mike ta nufa cikin dakin ta shigar ta keda wuya cike da mamaki take kallon cikin dakin domin yadda aka yamutsa cikin dakin hankalin ta a tashe ta karasa ciki tana kalle kalle do min ganin yadda dakin yake,Kai tsaye ta karasa inda wadrop dinta yake ta bude amma cike da mamaki babu kome ankwashe Tsaye hajiya bilkisu take akan kanta tana kallon s *A SANADIYYAR AGOGO* RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 MUHD AL'AMEEN C "Amma dai yanzu ban san wata amintaka ba" kawai sai ta juya ta bi bayan D.p.o da niyyar fita daga caji'ofis din ta koma gida, ta barsu cike da jimami da tashin hankali..... Shi kuwa D.p.o ofishinsa ya nufa da yake ba bangare daya yake da na kantar ba. ACAN kuwa bakin kofar shiga caji'ofis din wadansu sabbin jifa-jifaine guda 7 bakake suka nufo wajen cikin matsanancin gudu tamkar za su tashi sama, kararrakin take birkine kawai ke tashi yayin tsayuwarsu a gefe guda, cikin hanzari wadansu mutane daga cikin wadannan motoci suka firfito domin budewa uban tawagar motar tasa. da sauri wani farin dattijo gajere mai karamin ruwa ya fito ya doshi bakin kofar caji'ofis din da dan sauri-sauri fuskarsa a murtuke sai wani faman zazzare jajayen idanuwansa yake yana ta muzurai tamkar yaci babu. Ko da ya karaso sai ya tarar da kofar a rufe batare da wata fargabar komai ba ya sa kafarsa guda da dukkan karfinsa ya doki kofar, kasancewar kofar dama. ** A SANADIYYAR AGOGO!! ** RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 Kasancewar dama kofar tana bukatar canji domin ta gama tsufa tun zamanin marigayi Alhj Shehu Shagari har yanzu dai ita ce ba,a canja ba, hakan yayi matukar bayar da gudumawa wajen faduwar kofar kasa ricaaa!!! Karar faduwartata ne ya janyo hankulan dukkanin wani dan sanda dake caji'ofis din nan take suka nufo kofar don ganin abin da ke faruwa, ganin wanda ya aikata wannan danyen aiki ne yasa kowane dan sanda shiga taitayinsa wadansu ma sai komawa wajen zamansu suka yi don gudun kar tsautsayi ya hau kansu. Ita kuwa Hajiya Bilki tuni ta ruga da gudu bangaren kanta saboda tsananin razana da ta yi. Kicibis!! suka yi da D.P.O yayin da yake hanyarsa ta komawa ofishinsa. "yellaboi lafiya na ganka anan kuma cikin iri wannan yanayi?" D.P.On ya tambaya cike da tashin hankali a tattare da shi domin tabbas! ya san akwai wata babbar matsala data kawo ALH ALI DALA cikin caji'ofis dinsa musamman ma ganin irin yadda ya shigo wajen a harzuke...... **A SANADIYYAR AGOGO!!** RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 Wani irin kallo yabi d.p.on da shi mai cike da razanarwa ba tare da yace komai ba ya nufi bangaren kanta. Da gudu-gudu d.p.on ya biyo bayansa har ma ya wuce shi kafin ya karaso tuni d.p.on da kansa ya nema masa kujerar zama mai kyau. Aiko yana karasowa ya zauna kan kujerar ya harde kafa daya kan daya cikin nuna isa da takama, su ko abokan rakiyar tasa duk sun tsaitsaya a bayansa. shiru ne ya ratsa wajen tamkar babu wani abu mai numfashi a wajen har na kusan tsawon dakika sittin sannan wani dan sanda mai tsatstsauran ra,ayi kuma sabon shiga aikin yayi ta maza ya katse shirun da cewa. "yellaboi kai din wanene?" kafin ya karisa kai aya a maganar tasa tuni ALH ALI DALA ya zaro wata 'yar karamar bindiga (pistol) daga al'jihun babbar rigarsa ya harbi kafar wannan dan sanda tare da fadin, "to yanzu kaji amsar tambayarka ko akwai mai wata tambayar kuma?" wata irin razananniyar kara wannan dan sanda ya yayi saboda azaba nan take ya fita daga wajen.... **A SANADIYYAR AGOGO!!** RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 Nan take ya fita daga wajen yana ta ihu da kururuwar neman taimako, sai a lokacinne shi kuma ya sami damar zaro kwalin sigari daga al'jihunsa tare da ciro kara biyu sannan ya dubi wani dake gefen damarsa, cikin sauri wannan mutum ya zaro Lighter ya kunna mar duka kara biyun yasa a bakinsa yana zukarsu a tare yana fitar da hayaki ta baki da hanci sannan yana duban wannan 'yar karamar bindigar tasa yana shafata. "wacece Sa,adatu cikinku?" ALH ALI DALA ya tambayi matan dake bayan kantan tare da mayar da dubansa garesu!! Tunda Hajiya Sa,adatu take bata taba gamuwa da musiba da tashin hankali irin wannan ba saboda tsananin razana da kidimewa ba ta san lokacin da fitsari yayi fitar burgu ya bata mata zani ba!! sai a yanzu ne nadamar rashin hakurin da ta yi yazo mata tabbas a yanzu ta san ta tsokano tsuliyar dodo, duk da cewa ba,a fada mata ko wanene wannan mutum ba amma ta rayawa kanta cewa shine mijin Hajiya Rabi da ta yiwa wannan aika-aika.. **A SANADIYYAR AGOGO!!** RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 Duk da tsananin razana da Hajiya Sa,adatu ta yi amma hakan bai hanata karewa fuskarsa kallo ba, domin fuskartasa tana da dan fadi amma ba sosai ba, in ka dauke tulin gashin bakinsa da ya mummurde tamkar kahon wani rikakken rago to babu ko silin gashi kwara 1 a duk illahirin jikinsa, sam bai yarda da barin gashi a jikinsa ba sai wannan gashin baki wanda yake yawan yiwa mutane barazana da shi. Cikin fushi ya daka musu tsawa. "tambayar ku na ke wacece sa,adatu cikinku?" al'amarin da ya sake dugunzuma musu hankali kenan kamar hadin baki su duka suka soma nunata cikin karyayyar murya. "gatanan! gatanan!! a daidai

Chapter 1 of 3