hare-hare guda biyu, daya da takobi da nufin ya cisge Masa Kai, dayan kuwa ya Kai Masa mugun duka da kafa.
Nan fa RA'UFUL KALLUS yayi iyakar kokarinsa don kaucewa duka hare-haren shugaban dodannin nan Amma Abu ya faskara, domin da kyar da sidin goshi yayi nasarar kaucewa harin takobin.
Amma kafin ya Ankara tuni shugaban dodannin ya mako shi da kafarsa, saboda karfin dukan sai da RA'UFUL KALLUS yayi sama tamkar an harba kwallo, yaje ya gwaru da rufin dakin sannan ya fado da rubda-ciki, Wanda har sai da yaga taurarin wuya.
Saboda tsananin buguwar da yayi har sai da yayi aman wani gudan jini baki-kirin, sannan ya fara gani dishi-dishi.
Shi kuwa shugaban dodannin Koda yaga haka sai ya sake daka wani wawan tsalle sama Yana Mai daga takobinsa da nufin sokata a jikin RA'UFUL KALLUS.
Cikin zafin nama na gaban kwatance RA'UFUL KALLUS ya goce da dukkan karfinsa, takobin shugaban dodannin ta lume a cikin Kasa.
Kafin ya samu nasarar zaro takobin daga cikin karkarshin Kasa, tuni RA'UFUL KALLUS yayi wata katantanwa a Kasa ya tattara dukan karfinsa ya doki kirjin shugaban dodannin nan da kafafunsa biyu.
Saboda karfin dukan sai da ya jujjuya sau arba'in sannan maku a jikin bangon dakin Wanda yayi sanadiyyar fashewar Kansa jini ya kama zuba.
Cikin tsananin zafin nama RA'UFUL KALLUS ya wurwura takobinsa sannan ya daka tsalle sama da nufin fillewa shugaban dodannin nan Kai.
Koda ya rage saura taku biyu jal! Ya Isa gareshi sai kawai yaga ba zato ba tsammani wani tsohon mutum tukuf ya bayyana Tsulum a gabansa ya kare saran da wata hisgar tsafi.
Tsohon mutumen yana sanye ne da wasu kayan fatar giwa, sannan daga Saman Kansa an makala kahonnin jimina.
Babu wani makami a jikinsa face wadansu manya-manyan guraye da layu dake daddaure a jikin hannuwansa da kugunsa.
Kafafunsa ko takalma babu, sannan ya shafe fuskarsa da wani bakin shuni Wanda babu ratsin fari ko kadan.
Nan take RA'UFUL KALLUS yaji tamkar akan wani Katon Dutse takobinsa ta sauka.
Kafin yayi wani yunkuri tuni wannan tsohon mutumen ya girgiza hisgar tsafinsa, take wata kakkarfar Guguwa ta doki RA'UFUL KALLUS.
Saboda Karfin dukan sai da RA'UFUL KALLUS yaje ya gwaru da bangon dakin sannan ya Burma shi ya fice fit ta cikinsa, haka yaci gaba da dukan gine-ginen cikin gidan har sai da fice daga gidan gaba Daya.
Ficewarsa gidan keda wuya sai ya tsinci Kansa a kofar gida na biyu, dake unguwar dodannin nan.
Kafin ya dawo hayyacinsa tuni wata iska ta fito daga cikin gidan sannan ta jashi izuwa ainihin cikin gidan..
ME ZAI FARU A WANNAN GIDA NA BIYU DA RA'UFUL KALLUS YA SHIGA?
WANE BALA'I ZAI GANI A CIKIN WANNAN GIDA NA BIYU?
SHIN RA'UFUL KALLUS ZAI SAMU NASARAR KASHE BOKA DUNKAZUL MANNAS, HAR YA FITA DAGA CIKIN WANNAN BIRNI?
WANE IRIN BAKIN ARTABU AKEYI A CAN KOGON BAHAR DURGAFUL KALLUS?
Don son Jin wadannan amsoshi sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na 11.
Ina maku fatan Alkhairi ♥️❤️**HATSABIBIN ALJANI**
Assalamu Alaikum warahmatul lahi wa barakatuhu ♥️
Ina yiwa Al'ummar wannan gida masu bibiyarmu akan littatafan da muke kawo maku na yake-yake barka da wannan lokacin Mai albarka tare da fatan Kuna lafiya ✍️🙏
Bayan haka Ina Mai Baku hakuri akan tsawon lokacin da Baku samu posting din komai ba..
Kuyi sani cewa hakan ya faru ne sakamakon accident da nayi Wanda yayi sanadiyyar gocewar hakarkarina🥺
A iya tsawon lokacin da ku ka ji ni shiru, Ina Kan yin jinya ne.
Amma yanzu Alhmdllh na samu sauki sosai har Ina iya yawo inje duk Inda nake so da yardar Allah ♥️🙏
Saboda haka Ina Mai sanar daku cewa in-sha Allah nan ba da dadewa ba, zamu dora daga inda muka tsaya.
Muna fatan Allah ya Kara karemu daga dukkan sharri na kowace irin halitta walau mutum ko Aljan ko abun Hawa na Fili da na boye ✍️✍️🙏🙏🙏
Ina yiwa kowa fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya taimakemu akan dukkan harkokinmu na Alkhairi ♥️🙏
Najibullahi Muhammad ke cewa ku huta lafiya 🙏🙏🙏
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels