lokacinne wayarsa ta soma kara cikin sauri ya zarota daga cikin al'jihunsa ya karata a kunnensa. "hello, what! likita kace me!!? ta farfado? nan take ya dan yi murmushi mai dauke da fassarori daban-daban, cikin nuna isa ya tako ya zo daf da Hajiya Sa,adatu Ya kura mata ido kafin daga bisani ya sakar mata harsashi a hannunta na hagu.......
5y
Reply
Share
Muhd Al'ameen
*A SANADIYYAR AGOGO!!* RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 Wata irin razananniyar kara ta sakin sannan ta sulale kasa sumammiya. Sai a lokacinne ya juyo kan d.p.on tare da nuna masa wadanda ke tare da shi sanye suke da kaya irinna ma,aikatan kotu. "ka ga wadannan wasu daga cikin kwararrun lauyoyina ne guda 25 sauran suna Abuja suna jirana akan wata babbar shari'a da za mu soma gobe, sauran al-kalan gari kuma duk mun gama magana da su za,a yiwa sa,adatu daurin rai da rai akan abin da ta yiwa iyalina, suko wadannan" ya nuna sauran matan "shekaru bibbiyu kawai za su yi saboda sakacin da suka yi har aka raunata iyalina a idonsu ba su hana ba" yana kaiwa aya sai ya zaro wadansu makudan kudi dauri-dauri ya mikawa d.p.on, shi ko baki a washe ya karba yana godiya. "yanzu mu za mu tafi asibiti duba iyalina zuwa yamma zamu dau hanyar Abuja suko wadannan lauyoyi za su same ka a gida ku karasa magana na san ka san hannunka don haka ba sai na tsawaita magana ba" baki har kunne d.p.on yace. "an gama yellaboi ai ka san bani da
5y
Reply
Share
Muhd Al'ameen
*A SANADIYYAR AGOGO!!* RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 .....Ai ka san bani da wasa cikin al'amarina don haka komai kamar ya faru yadda ka tsara" murmushin mugunta ALH ALI DALA ya yi sannan ya juya da tawagarsa suka fice daga caji'ofis din. Ba su jima da tafiya ba sai ga tawagar mazajen wadannan mata cikinsu har da mijin Hajiya Sa,adatu ALH ANAM DORAYI tsohon sakataren gwamnati, ko da isarsu bakin kanta sai ya lura da irin mummunan halin da matarsa take ciki aiko nan take shima ya rude da gudu ya je ya ciccibeta yana kiran sunanta ganin yadda take bukatar taimakon gaggawa yasa bai tsaya tambayar abin da ya faru ba sai ya fita da ita da niyyar kaita asibiti don ceton rayuwarta. su ko sauran mazajen ko da suka ga halin da matar abokinsu take ciki sannan su ko nasu matan babu abin da ya sami lafiyarsu sai kowa ya dauki iyalinsa da sauri suka bi bayan abokin nasu. Alh Anam Dorayi Da Alh Jibrin Ajr Barister Mijin Hajiya Bilki shine tsohon koshinan shari,a na gwamnatin data shud tare da sauran......
5y
Reply
Share
Muhd Al'ameen
**A SANADIYYAR AGOGO!!** RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 Alh. Anam Dorayi Da Alh Jibrin Ajr Barister Mijin Hajiya Bilki shi ne tsohon komishinan shari'a na gwamnatin data shude tare da sauran mazajen wadannan mata da aka tsare a caji'ofis. zaune suke cikin wani kayataccen gidan gona suna nazarin irin matakin gaggawa da za su dauka akan wannan cin mutunci da ALH ALI DALA yayi musu. Wani dan kakkaura dogo waishi ALH ADAM ABDULLAHI GUNDUTSE tsohon mataimakin gwamna ya tashi ya soma magana. "ku sani wlh idan muka hada kai ko shakka bana yi za mu yi nasara kan wannan shaidanin mutun ta han yar daukar kwakwkwarar mataki akan wannan abu da yayi mana. caraf! sai wani wai shima babban daraktan gwamnati ALH. SHURAIH USMAN ya karbi zancen da cewa. "kuma idan za mu dauki matakin mu yi shi cikin gaggawa in son samu ne ma kar ya wuce zuwa gobe" duk zancen da ake sai yanzu ne tsohon minista MUBARAK ABUBAKAR SAULAWA ya sanya baki. " kuma ko da kararsa za mu yi to sai daidai mu kaishi kotun ABUJA domin al'kalan......
5y
Reply
Share
Muhd Al'ameen
*A SANADIYYAR AGOGO!!* RUKUNI NA 7 ZAGAYE NA 2 ......Domin al'kalan garinnan kusan duk yaransa ne" shi ko chair man mai ci na karamar hukumar NAFSEEN FAHAD tare da ALH. IMAM BANDIRAWO,SHUAIBU AHMAD SHU'AIBU,MUNTANSIR SHEHU tun da ake wannan tattaunawa bakinsu gum! ba su ce komai ba sakamakon tunanin irin karon battar da suka yi da shi ALH ALI DALA basu share ba. Haka dai wadannan mazaje suka dinga shawarwari wanda daga karshe Dan Majalisan Jiha HON. ILIYAS ISHAK GUNDUTSE da komishinan harkar noma mai ci ALH. REAL BUKAR MUSTAPHA DAMATURU ne suka yi jawabin karshe kuma koya ya gamsu da irin shawarwari da hujjoji da suka bayar daga nan majalisar ta watse. Alh Anam Dorayi ne ke gefen gadon matarsa a asibiti wacce tuni ta dade da farfadowa bayan anyi nasarar zaro harsashin da ya makale a hannunta sai dai a halin yanzu bacci take saboda allurar da aka yi mata. kurawa kyakkyawar fuskarta idanu yayi idanunsa cike da kwalla yana tuno irin soyayyar da suka sha a baya.... mu hadu a fage din karshe
A SANADIN AGOGO
Ajiyar zuciya ya yi yana tunanin abin yi duk da zuciyarsa na masa gargaɗi akan hatsabibin, mashahurin, babban attajirin nan Alhaji Ali Dala tsananin son matarsa na fusgarsa Kan son ɗaukar mata fansa. buɗe idonta ta yi tar akan na shi dake kallonta cikin murna ya ce, "Sa'adatu ! sannu ya jiki ?" ƙoƙarin miƙewa take. da sauri ya dakatar da ita. "tsaya kada ki miƙe." duk da Sa'a masifaffiyar mace ce tana matuƙar biyayya ga mijinta, cikin jin azabar ciwon hannunta. "Kaga cin mutumcin da aka yi min ko ?" ta faɗa hawaye na zubo mata. cikin rashin jin daɗi ya ce, "Na gani Sa'a, ki kwantar da hankalinki don ba zan taɓa yarda ba sai....."
"Me zaka yi masa?" ta katse shi. "Mun tsaida magana tare da sauran mazajen Matan da ya sa a ka rufe saboda gadarar mai kuɗi ne." cikin jin haushi ta ce, "Da a ce zan ƙara ganin matar tasa da sai na zubar mata da haƙoran gaba in ya so ni ya yi layya da tsokar jikina ƙarshen harbi kenan, kuma wllh gidan rediyo zani na tona masa asirin yana yawo da bindiga, da kuma cin hancin da ya baiwa D.P.O har da harbin da ya yi wa kurtun nan."
"A a Sa'a, ba sai ta kai ga haka ba mun san yanda za mu ɓullo masa don wannan karon shi ma ya taɓo tsuliyar dodo." "Ina agogona ya ke ?" "Wanne agogo kuma a na ta rai?" "A she masifa bata ƙare ba ? na rantse da Allah ba zan taɓa yarda ba sai an fito min da agogona sai na ga shegiyar da ta iya sa hannu ta sace min shi." ta ƙarasa da haki tana kallon mijinta. "Ba ke kaɗai ba ce kike jiran ganin ɓarauniyar, duk gari da ƴan jarida, soshiyal media duk sun zuba idon su na jiran ganin wacce ta ɗauka Sa'ade."
Cikin masifa Hajiya Bilkisu take tattara wargatsatstsan ɗakinta, tun tana iya gyarawa har ta kai ta kawo ta fara wulli da duk abinda ta ci karo da shi a gabanta. a haka ƙaramar ƴarta Amal ta shigo hannunta ɗauke da buhun kayan wasanta. tana zuwa gabanta ta ajjiye ɗan ƙaramin buhun tana kallon Mamata. cikin takaici Hajiya Bilkisu ta wafce buhun ta yi jifa da shi, da sauri Amal ta matsa haɗe da fashewa da kuka ta yi kan kayan wasanta da rabinsu su ka watse a ƙasa, cikin kuka ta ɗauki ƴartsanan ta. takaicine ya rufe Hajiya ta yi mata tsawa. "fice min da gani, ki tattara shegen buhun wasanki ki fita da shi ko na watsa shi a bola." da sauri Amal ta fara haɗa kayan tana sheshsheƙar kuka, dogon tsaki Hajiya ta ja, karaf idonta ya sauka kan hannun Amal da ta ɗauki Agogon da ya fito cikin kayan wasanta zata saka cikin buhun. cikin kuzari Hajiya ta fuske Agogon. "A ina kika samu agogon nan ?" "Agogona ne na tsinta a banɗakin Hajiya....." a fusace ta fuske buhun Amal ta zazzage abinda ke ciki sai ga tarin sarƙoƙinta da awarwarayenta. cikin mugun jin haushi ta ce, "Su kuma waƴannan fa ?" taɓe baki Amal ta yi irin na yara masu kuka da shagwaɓa ta ce, "Ni ce dana ga irin agogonki shi ne na yi ta neman naki sai na gan shi a wancen wajen da kike ajjiye wa sai na ɗauko na haɗa na ajjiye a cikin buhun zan ɓoye miki da kuma agogon da na tsinta idan na gama bikin ƴartsana ta sai na....." Wani lafiyayyen mari ta wanke Amal da shi har sai da yarinyar ta tuntsira, daidai lokacin da Babanta ya shigo ganin marin yasa shi ma ya wanke Hajiya da mari, cike da jin haushi. cikin mamaki da kukan da ya zo mata ta ce "Kasan kuwa me ta yi ?" cikin ɗaga murya ya ce, "Rai ta kashe?" "Agogon da ake ta bala'i akansa ashe ita ta gan shi a...."
"Aikin banza, shi ne me ? sai ki je cen police station ɗin ki faɗa musu komai amma kada ki ƙara dukan min yarinya."
Labarin zancen ganin agogo ya tumbatsa a gari da kuma kafafen yaɗa labarai, abin sai ya zama abin dariya da son bada labari a wajen kowa.
Alhaji Ali Dala Kan hanyarsa ta dawowa daga Abuja ya yi mummunan hatsarin da ya ka mu da lalurar karyaewar ƙashin baya, wanda tasa baya iya yin komai sai dai a yi masa. Sauran Matan da suka halarci bikin Sunan Hajiya Bilkisu hankalinsu ya kwanta musamman mai agogon Hajiya Sa'a.
ƙarshe !
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA GOMA 10 ✍️
PART A ♥️💯
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING:- Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷
Idan baku manta ba a baya mun tsaya ne a inda aka finciko RA'UFUL KALLUS izuwa cikin teku.
Bugu da Kari Kuma da shigarsa sai yayi arba da manya-manyan gine-gine na Zamani da na gargajiya birjik a karkashin tekun. Haka Kuma duk Inda ya duba sai yayi arba da mutane suna ta harkokinsu a karkashin tekun tamkar ba'a a cikin ruwa suke ba.
Babban abinda yafi bawa RA'UFUL KALLUS mamaki a cikin wannan birni shi ne, ganin yadda mutanen birnin suke ta mu'amalarsu batare da wani shamaki ba.
Kuma shi kanshi yayi matukar mamakin ganin yadda yake iya yin numfashi har ma yayi tafiya a karkashin ruwan batare da wata matsala ba.
Hakika wannan birni ya cika abun Al'ajabi domin Mafi yawan gine-ginen birnin duk da zallan Zinari akayi su, wannan yasa gaba dayan karkashin tekun ta haskake da matukar haske tamkar wasu fitilu ne aka kunna.
Haka Kuma duk unguwar da RA'UFUL KALLUS ya gifta sai yaga mutanen birnin suna ta harkokinsu ko kallonsa babu Mai Yi.
Sa'annan Kuma Al'ummar wannan birni suna da sana'o'i mabambanta.
Domin duk da kasancewarsu a karkashin teku, hakan Bai hanasu aiwatar da sana'o'insu ba.
Hatta manoma suna zuwa bayan gari suyi shuka, sannan shukar ta fito Kuma tayi girma sosai ayi Amfani da abinda ta fitar.
Haka Kuma a wata unguwar zalla makera ne suna ta kera makamai da abubuwan amfanin jama'a iri-iri.
A wani bangaren kuwa masu sana'ar rini ne, suna ta faman rina tufafi babu dare babu Rana.
A bisa wannan dalili ne yasa jama'ar wannan birnin suka mallaki dukiya Mai tsananin yawa, domin kowa Yana da abinda yake kawo Masa kudi.
Haka dai RA'UFUL KALLUS ya rinka ketawa lungu-lungu sako-sako na cikin birnin Yana kallon abubuwan mamaki da Al'ajabi, har ya shigo wata karamar unguwa wadda babu komai a cikinta sai wasu rubabbun gidaje wadanda ko kofofi babu a jikin kowane gida.
Kuma dakunan wannan unguwa sun haura Dari biyu da arba'in, dukkaninsu kamanninsu Daya ne babu Wanda yafi wani.
Koda yazo wucewa ta kofar gidan farko na wannan unguwa sai kawai yaga wani kyakkyawan Yaro ya fito daga cikin gidan ya tsaya a kofar gidan Yana Masa murmushi.
Har RA'UFUL KALLUS ya Bude Baki da nufin yiwa Yaron magana, Amma sai Yaron ya koma cikin gidan a guje.
Nan take RA'UFUL KALLUS yaji a ransa cewa lallai Yana so ya shiga cikin wannan gida domin ganin koma menene a cikinsa.
Nan take ya kunna Kai cikin wannan gida.
Da shigarsa sai yayi arba da wata 'yar mitsitsiyar hanya wadda za'a bi takai mutum izuwa cikin wannan gida.
Haka RA'UFUL KALLUS ya rinka bin wannan hanyar tinkis-tinkis har tsawon dakika dari da tamanin sannan ya iso karshenta.
Da zuwansa sai yayi arba da wani wawaken daki Mai tsananin girma Wanda babu tagogi a jikinsa, Amma Kuma Yana iya jiyo ihu da kururuwa a cikin dakin.
Nan take hankalinsa ya tashi, ya ayyana a ransa cewa," babu shakka wani bala'in ne a cikin wannan daki.
Kawai sai ya juya da baya da nufin fita daga gidan.
Ba zato ba tsammani sai kawai kofar shiga dakin ta wanzu a kusa dashi, sannan wani lafcecen hannu ya fito daga cikin dakin ya fincikoshi izuwa cikin dakin.
Cikin tsananin razana RA'UFUL KALLUS yayi duba izuwa abinda ke cikin dakin.
Kawai sai yaga wadansu jibga-jibgan DODANNI sun daddaure mutane da Aljanu da wasu murtuka-murtukan sarkokin karfe, suna ta faman Zane su da bulalar wuta Mai bacewa.
Su kuwa sai faman kwallara ihu suke.
A duk lokacin da aka laftawa mutum ko Aljan wannan bulalar wuta sai tsokar wurin ta kone kurmus har Kashin wurin ya fito fili muraran
Amma da an cire bulalar sai fatar wurin ta ciko, ta lullube wurin tamkar babu abinda ya faru.
Su dai wadannan dodanni adadinsu yakai dubu Kuma gaba dayansu idanuwansu na wuta ne.
Haka Kuma gurnaninsu ma kadai ya Isa ya zama Annoba ga duk halittar da ta makwabcesu.
Sun kasance jibga-jibga masu tsananin girma tsawo da kauri tamkar bishiyar kuka.
Haka zalikha Kuma basa gajiya da azabtar da wadannan fursunoni da suka kama.
A kowace Rana wadannan dodanni na azabtar da wadannan fursunoni sau dubu uku da arba'in da hudu.
Bugu da Kari wadannan dodanni sun kasance a wannan wuri tsawon shekaru sittin.
Su dai wadannan dodanni Asalin wanzuwar su a wannan wuri shi ne," wani shedanin Boka ne daga cikin jinsin DODANNIN DUNIYA Mai suna DUNKAZUL MANNAS.
Shidai Boka DUNKAZUL MANNAS Yana can bangon duniya na bangaren Arewa inda yake tafiyar da rayuwarsa a cikin wani kasurgumin daji Mai suna JAHAGUS.
Shidai wannan daji na JAHAGUS ya kasance daji Mafi hadari a duk fadin duniya.
Kuma komai sihirin tsafin mutum ko Aljan da zaran ya shiga wannan daji take yake rasa gaba dayan sirrikan tsafinsa sannan yake zama gawa.
Ba komai ne ke kashe mutum ko Aljan a wannan daji ba, face Boka DUNKAZUL MANNAS wannan yake Amfani da karfin sihirin tsafi ya zukewa duk halittar da ta shigo dajin jini, kawai sai dai aga kwarangwal din halittar ta fadi Kasa.
Boka DUNKAZUL MANNAS shi ne hatsabibin Bokan da ya shiga karkashin Kasa sannan ya dulmiyar da wannan birni izuwa karkashin teku, batare da su kansu mutanen birnin sun San abinda ya faru ba.
Kuma yayi hakane domin cikar wani buri nashi. Bayan ya samu nasarar dulmiyar da birnin ne sannan ya Samar da wannan unguwar tare da Saka wadannan dodannin a matsayin masu gadin unguwar.
Kuma Boka DUNKAZUL MANNAS ya gargadi wadannan dodanni akan cewa lallai duk tsautsayin da ya gifto da wani mahaluki wannan unguwa, to suyi Masa su kamashi sannan su rinka gana Masa azabobi kala-kala har izuwa karshen rayuwarsa.
A bisa wannan dalili ne yasa duk lokacin da tsautsayi ya Koro mutum ko Aljan izuwa wannan unguwa, to Nan take ake cafko shi sannan a daddaure shi a rinka Zane shi da bulalar wuta Mai bacewa.
Kuma ba za'a dena Masa wannan azaba ba, har sai ruhinsa ya fita daga Gangar jikinsa.
Koda RA'UFUL KALLUS yaga yadda ake azabtar da wadannan Aljanu da bil'adama, Kuma ya tabbatar Shima haka zasuyi Masa.
Sai ransa ya Baci zuciyarsa ta harzuka..
Nan take yayi kukan kura ya zare makamansa sannan ya tunkari dodannin gaba dayansu ya hau su da Sara da suka baji ba gani.
Amma Koda ya fara yakar dodannin sai ya karaya Kuma nadama tazo Masa bisa wannan babban kuskure da ya tafka, domin duk lokacin da yakai Sara da takobinsa sai dai yaga takobin ta keta ta cikin dodon ta wuce tamkar yadda haske ke ketawa a sarari Yana wucewa, domin tamkar ya sari iska haka yake gani.
Amma duk da haka bai karaya ba, haka ya kasance tamkar mahaukaci Yana ta Kai Sara da suka Amma ko sau Daya ya Kasa samun nasarar saran su.
Haka ya kasance har tsawon sa'a biyu, a wannan lokaci tuni ya fara gaji ainun harma yana faduwa Yana tashi.
Su kuwa dodannin sai suka tuntsire da dariya mara dadin ji tamkar ana ruwan kwarankwatsa.
Ba tazo ba tsammani sai kawai aka ga dodo Daya daga cikinsu yasa Dan yatsa guda jal sannan ya mangare RA'UFUL KALLUS da shi.
Saboda karfin dukan sai da RA'UFUL KALLUS yayi sama tamkar an janye shi da Kugiya sannan gwaru da bangon dakin ya fado Kasa a matukar galaibace.
Kafin yayi wani yunkuri tuni shugaban dodannin nan ya nuna RA'UFUL KALLUS da hannu hagu, take wasu murtuka-murtukan sarkokin tsafi suka bayyana sannan daddaure shi tamau.
Sannan shugaban dodannin yace, lallai yau mun kama Aljani Mai tsananin taurin kai da son nuna Jarumtaka.
Saboda haka na rantse da Karfin sihirin Shugabanmu Boka DUNKAZUL MANNAS cewa sai na gana ma wannan hatsabibin Aljani azabar da bamu taba yiwa ba.
Nan take shugaban dodannin ya bawa yaransa Umarnin cewa suyi Masa azaba Mafi radadi, daga cikin azabobi guda dubu.
Nan take dodanni dari daga cikinsu suka ruga izuwa cikin wani daki Mai hayaki sannan suka dawo dauke da wasu karafuna masu matukar Kaifi da tsini wadanda sukayi jawur da wuta.
Da zuwansu basuyi wata-wata ba sai suka mammana wadannan jajayen karfunan a jikin RA'UFUL KALLUS a lokaci guda, Nan take fatar wurin ta kwalle tayi fari fat har sai da tsokar ta kone kurmus ya zamana cewa ana ganin Kasusuwan jikinsa sannan suka cire karafunan, suka sake rugawa a cikin dakin domin dauko wasu karafunan.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya kwarara uban ihu sakamkon tsananin zafi da zogin da ya ji.
Nan fa yaji nadama tazo Masa bisa karambani da kuskuren da yasa har ya shigo wannan gida.
Saboda tsananin wahala har sai da hawayen wahala suka fito daga idanunsa.
Bayan cikar dakika hamsin ne da faruwar hakan sai fatar wurin ta ciko, komai ya koma dai-dai tamkar babu abinda ya faru.
A dai-dai wannan lokaci ne dodannin nan suka sake dawowa dauke da wasu jajayen karfunan.
Da zuwansu basuyi wata-wata ba sai suka sake manna wa RA'UFUL KALLUS duka karafunan a sassan jikinsa a lokaci guda...
Kai saboda tsabar rashin Imanin wadannan dodannin yasa ni kaina na tsorata ainun, Wanda yasa har naji bazan iya cigaba da typing ba nake cewa mu hadu a Nan gaba.
Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰 Najibullah Muhammad ke cewa ku huta lafiya 🥷🥷✋✋🙏🙏🙏🙏🙏**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA GOMA 10
PART B ✍️💯
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING:- Najibullah Muhammad 🥷🥷
Lokacin da wadannan dodanni suka dawo dauke da karafunan wuta a karo na biyu, da zuwansu sai suka sake manna wa RA'UFUL KALLUS su a sassan jikinsa.
Faruwar hakan keda sai fatar wurin ta kone kurmus har sai da aka rinka hango Kashinsa, cikin tsananin rudewa da dimaucewa RA'UFUL KALLUS ya sulale Kasa sumamme.
Su kuwa ragowar dodannin sai suka rinka kyalkyala dariyar mugunta tare da yin wani irin mugun gurnani mara dadin ji, Wanda inda Mai ciki zata ji shi tuni zatayi 6ari.
Bayan kamar shudewar dakika arba'in da suman RA'UFUL KALLUS, sai babban cikin dodannin ya tako yazo dai-dai inda yake sume sannan yayi Masa fitsarin jini Wanda yayi sanadiyyar farfadowarsa.
Cikin ajiyar zuciya RA'UFUL KALLUS ya farfado. Amma har a sannan Yana daddaure a jikin sarkokin Nan.
Nan fa shugaban dodannin nan ya takarkare iyakar karfinsa Yana ta kwarara wa RA'UFUL KALLUS fitsarin jini Kuma Yana kyalkyala dariyar mugunta sauran yaransa na tayashi.
Saboda yawan fitsarin har sai da ya jike gaba dayan jikin RA'UFUL KALLUS, wani lokacin ma sai dai yaji fitsarin a cikin bakinshi.
Bisa dole ya rinka Shan wannan fitsarin ba don ya so ba.
Sai da aka shafe dakika dari da arba'in dodon nan na yiwa RA'UFUL KALLUS fitsari a jiki sannan ya dena.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga gaba dayan fatar jikin RA'UFUL KALLUS ta cicciko ta koma sumul tamkar wuta Bata taba Kona ta ba.
Haka Kuma sai aka rinka ganin jikin RA'UFUL KALLUS Yana ta kumbura, fatarsa tana yin tauri tare da canza launi.
A hankali a hankali dai sai da gaba dayan siffar jikinsa ta juye izuwa ta wadannan dodannin sak, tamkar an tsaga Kara.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga gaba dayan sarkokin da suka daure shi sun bace bat, haka Kuma su kansu sauran fursunonin dakin sarkokin da aka dauresu sun bace bat.
Koda ganin wannan Ala'mari sai dukkan dodannin suka cika da tsananin mamakin faruwar wannan Ala'mari.
Nan take shugaban dodannin ya dakawa yaransa tsawa akan lallai su kama RA'UFUL KALLUS su kara daure shi, domin aci gaba da gana Masa azaba.
Gama rufe bakinsa keda wuya sai gaba dayan DODANNIN nan suka ruga izuwa kan RA'UFUL KALLUS da nufin yi masa rubdugu.
Koda ganin haka sai Shima RA'UFUL KALLUS ya ruga da izuwa kan dodannin nan Yana ihu da gurnani irin na sauran dodannin.
Ana haduwa aka kacame da azababben fada Mai ban mamaki da ban tsoro.
Domin a tsakaninsu babu Mai rike da mamaki, Amma Kuma irin fadan da suke yi har ma yafi na makaman hadari, saboda yanda suke kaiwa junansu mugayen hare-hare Kai da gani Kasan cewa duk Wanda aka samu dole ne ya bakunci lahira.
Nan fa dodannin nan gaba daya suka zage dantse wajen kokarin tumurmushe RA'UFUL KALLUS Amma Abu ya gagara, saboda ya same musu alakakai.
Domin a wannan lokaci RA'UFUL KALLUS ya samu karfi na musamman fiye da Wanda yake dashi da sau arba'in, haka Kuma girmanshi daya da sauran dodannin nan.
Bugu da Kari Kuma zafin naman da yake Amfani dashi ya ninka na sauran dodannin, domin a duk cikin dakika guda Yana iya Kai naushi sau arba'in.
Duk lokacin da RA'UFUL KALLUS yakai naushi to sai ya Bazar da dodanni hamsin sun baje Kasa sumammu, Amma shi Koda sun samu nasarar naushinsa sai dai suga ya shanye dukan nasu.
Nan fa dodannin nan suka Kara kaimi wajen kokarin kama shi, Amma a banza domin sun Kasa Koda lakutar jikinsa.
Kafin cikar Rabin sa'a ya kashe kaso daya daga cikin ukunsu.
Kai Koda suka ga cewa idan fa aka cigaba a haka, to lallai sai RA'UFUL KALLUS ya Karar da su duka.
Kawai sai akaga sun daga kawunansu sama suna wani irin gurnani Mai matukar razanarwa Wanda yasha bamban da na farko.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wasu zabga-zabgan takubba suka bayyana a hannunsu, Nan take suka sake yiwa RA'UFUL KALLUS Kawanya suna Shirin afka Masa.
Koda RA'UFUL KALLUS yaga abinda ya faru, sai Shima ya jaraba sihirin tsafinsa bisa mamaki sai yaji tsafinsa Yana aiki.
Batare da Bata lokaci ba Shima yayi Amfani da karfin sihirin tsafinsa ya Samar da zabga-zabgan makaman yaki masu ci da wuta a hannuwansa.
Girman kowane makami ya ninka bil'adama sau tamanin, haka Kuma kaifin wadannan makamai ya wuce misali domin duk abinda aka Sara da su sai abun ya rabe gida goma, sai dai kawai aga gutsin-gutsin din Abun tsube a Kasa.
Nan take dodannin nan suka sake rugawa izuwan RA'UFUL KALLUS karo na uku, ana haduwa aka sake kacamewa da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro.
A duk lokacin da Takubbansu suka hadu, sai dai aga tsawa da tartsatsin wuta yana zuba a Kasa.
Tsananin zafin nama da RA'UFUL KALLUS ke Amfani dashi a wannan yaki ya wuce misali.
Babban abinda yafi bawa RA'UFUL KALLUS mamaki shi ne, ganin yadda makamansa suke tasiri a jikin dodannin yanzu.
Domin cikin kankanin lokaci ya fillewa dodanni dari da tamanin kawuna, tuni sun zube a Kasa matattu.
Koda aka Kara samun shudewar wata rabin sa'ar sai RA'UFUL KALLUS ya lura da cewa, Ashe ya kashe gaba dayan DODANNIN.
Babu Wanda yayi saura a cikinsu face shugaban dodannin Wanda ya rike kugu Yana kallon duk irin gumurzun dake faruwa.
Har a sannan yana jingine a jikin bangon dakin rike da zabgegiyar takobi ya kurawa RA'UFUL KALLUS idanu cikin tsananin fusata, Wanda jikinsa har karkarwa yake tamkar Wanda aka tsoma a cikin ruwa.
Koda RA'UFUL KALLUS ya lura da shugaban dodannin a tsaye kusa dashi, sai ya ruga gareshi Yana kururuwa tare da ihu da Karaji.
Koda ya rage saura taku biyar ya Isa gareshi sai ya daka wani wawan tsalle sama da nufin ya tsargeshi biyu.
Kash!! Hakika rashin sani yafi dare duhu, domin inda RA'UFUL KALLUS yasan abinda zai biyo baya da bayyi nufin haka ba.
Cikin tsananin zafin nama tamkar na tauraruwa Mai wutsiya, sai kawai akaga Shugaban dodannin nan yayi fitar burtu daga inda yake tamkar walkiya ya tari RA'UFUL KALLUS.
Da zuwansa sai ya kaiwa RA'UFUL KALLUS mugayen