Share this page
3 / 11
dafa a can din, hjy ta tambaye ta da sauri ? Lami ta gyara zama tana fadin ruwan shayi ne mai kauri sai kwai suke ci a plate . Da sauri hjy tace Lami kardai ince kwan da aka ajewa Alh na amfanin shi ne ta diba ta dafa da yaranta ? Lami tace ai shine nazo na fada maki kar aga ya kare a tuhumay mu muda ke aiki ko yaushe a cikin kitchen din . Kwarai kuwa don kune a kitchen din ko yaushe dama nasan a rina wanan shiga kitchen din din da takeyi ba banza bane a gidan da akwai zanban da take shukawa. To yau ya kare don asirin ta ya tono a gidan nan gaskiya idan ankai mata abincin suke kin tabawa sai dai ta dawo muna dashi kitchen. Abincin da hjy Jummai bata karasa ci ba ke nan dama tana da takaicin hjy maimunan a ranta yanzun kuma an kara dada mata wani sai taji duk abincin ya fita ranta ga baki daya. Da kyat ta yaki zuciyar ta har maigidan ya dawo ansan wace ake don ba zai yuyu maimuna ta dinga nuna masu tsageranci hakaba a ckin gidan. Ita wacece da bazata ci wanda aka girka wa kowa ba sai tayi nasu ita da yaranta akoda yaushe lami tana ganin ta hada wanan ta mike zuwa aikin ta don tasan yau ko ba komai ta gyarawa uwar dagin nata rai da wanan maganan. A bangaren hjy jummai kuma bayan sun gama karyawa ne ta tasa yaranta gaba don suje su gaida kakar su Amma tare da daukan kulan data sakawa hadiye dan abinda ta soya din. Da sallama suka shiga dakin Amma inda ta samu hadiye a dakin suna hira da mahaifiyar ta da murna Amma ta tari yan jikokin nata inda hjy maimuna ke fadin. Ashema kina nan tana fadin haka ne lokacin da take mika mara kulan data riko masu din. Hadiye sai cewa tayi mai muka samu kuma a nan tana kaiwa zaune take fadin dan sauran kwanda yaya mustapha ya bamu ne ranan na gidan gonar shi na soya. Kin san yaran kin ga har yau basu iya cin wanan abincin safen da ake girkawa a gidan nan yau ai kinga basu zo shan kunun gwago ba. Cikin tabe baki Amma tace na rasa may ake da wanan uban kayan girkin da ake shigowa dashi gidan nan sai ga an shigo da kayan girki mai yawa. Amma karshe haka za a kawo abincin nan ko almajiri kaba almajiran nan na yanzu ba zasu karba ba. Hjy ke nan ana ko amfani dashi sosai don da yanzu zaki sashen yar mulkin gidan kiga abincin ta ita da yaranta sai kice ba guri daya aka girka da wanan din da ake kawo muna ba. Hadiye ce ke fadin wanan magana ta karasa da fadin ni yanzun haka ko budeshi yaran nan basuyi ba don ba zasu iyaci ba ma ko sun bude din. Nina rasa wanan akidar ace gida kamar wanan wai sai gaba daya za ai girkin da za a ci ranan dana shiga na samay ta tana ci nayi mata magana sai cewa tayi babban goro ai sai budin karfe dole itace za a fara zubawa don hakane na ga nata a hakan. Tsuki Amma taje tana fadin wanan yarinyar tana daukarwa kanta nauyi da yawa ina zata da wanan alhakin haka a kanta. Nina rasa hali irin na jummai a ce mutum baida abinyi a rayuwa sai kokarin danne hakkin wasu abin nan ana bayarwa ba ba a kawowa bane amma don kawai ta cutawa yan uwan zama ta kawo wanan akidar banzan haka. Hjy ni indai zata barmu mu zauna lafiya duk wani akidar ta baya damuna kamar rashin kwanciyar hankalin nan da babu a gidan nan a kullun. Hjy maimuna ce take wanan maganar cikin nuna damuwan ta da yanayin gidan nasu. Kasancewar bata da girki yasa takai har sha biyu da wani abu tare da hadiye suna hira kafin ta koma part din ta da yaranta. Wanda hakan ba karamin bata ran saura natan gidan yakeyi ba don a zaton su zaman zagin su akeyi gurin hadiye din. Basu san abin ba haka bane kokarin kulla alakan business suke a tsakanin su shine yawan zuwa part din juna da sukeyi. Bata fito ba tunda ta shige tana cikin sashe nata wanda haka ne komai a ciki duke da yaranta idan ba maigida ya dawo ya nemi yara a gurin shi ba sam bata yarda su fita daga sashen nasu. Don da farko tana bari har i yaran suki fita ta tillasata masu wai don su saba da yan uwan nasu take yarda su fita da farko. Sai daga baya ta gane fitan nasu cuta masu akeyi idan sun fita cikin tan uwan nasu don duk sun fisu girma a gidan da yawa kuma. Shine dalilin da bata yarda su fita ko ina hakan kuma yana ma yaran dadi sosai na rashin fita inda za,a duke su da zagi iri iri. Karfe biyar duk wani wanda ke gidan yasan lokacin dawowan maigidan gidane hakan ke sa kowa na gidan yake natsuwa. Matan gidan kuma kowa takan dauki kwalliya don burge mai gida sukan shiga daya bayan daya wani lokaci ida yana da magana zai tsayar dasu yayi masi shi a cikin jam,i. Idan ko ba wani magana sai a bar wace ke girki ita kadai tare da maigidan ta dauke mai sauran dawainiya kafin ya fita sallah mafariba. Irin bada abinci miko min yi min wancan sai idan yana da baki suka dan samu su sarara. Inda shi kuma yakan zauna da yara shi kanana suna hira kafin su fice masallaci dashi da yaran nasa. Yauma irin hakan ya kasance a wurin hjy maimuna din inda take saye cikin atamfar code, voi,re dinkin zanin da riga half gun sai yaran da ke saye da yar katin su uku ta tasa su a gaba. Ta makara zuwa gaida maigidan nasu a yadda ta saba zuwa idan ya dawo hakan ya samu dalili ne na tsayar da ita da yan biyun ta sukayi na yin kashi bayan ta shirya su kinsan abu ga mai kananan yara. Da sallama ta shigo fallon kallon yanauin su kawai tayi tasan da akwai matsala don haka tana gaida shi da ta juya zata bar fallon. Muryan mijin nasu taji yana fadin dakata maimu samu wuri ki zauna inda ya kalli yaran mm nata yace kuje ku jira maman ku ta dawo ko . Yaran suka juya don bin umurnin mahaifin nasu yayi da yar mulkin ke zaune a gefen shi tana harare hararen yaran da suka saba da irin kallon da take masu a gidan. Dan shiru ya biyo a falon sai can Alh ya kira sunan ta inda ta karba da fadin na,am yaya don haushi hjy jummai ta wani kawar da fuska tana mayde bakin ta. Maimuna wani magana nale jin yanzu wanda banji dadin jin shi daga gare ki in ma har haka kike so ai sai ki gabatar da zancen a gabana in san abinyi ko ? Hjy jummai bata so haka ba sai haushi ya kamata sosai na yadda yake mata magana a cikin tsigar lalashi itako a cikin sanyin murya tace wani abin akace nayi kuma tunda ba, a raina abin laifi a gidan nan. Alh baikai ga magana ba yar mulkin ta karbe da fadin kina nufin kake akai maki ko may wa kikafi a gidan nan da bazaki ci abincin da kowa yaci ba sai kin fake ga satan kayan gida kin shige daki kin dafa da yaran ki kuci. Salati hjy maimu ta saka tare da fadin yau kuma sherin yakai a laka min satan abinci a gidan nan ? Ji munafuka waisheri cikin tsawa da daga hannu Alh ya dakatar da ita da fadin ke Jummai banson irin haka don Allah ki bari muji dalilin ta na yin hakan saboda Allah. Falon ya danyi shiru kafin ya nisa yace hajiya babba da hakuri fa aka sanshi kila tana da wani hujjan yin hakan kamar yadda na fada da farko. Hjy ta sake fadi may ye kuwa hujjanta illar son nuna gadara da isa ita a dole fata matar gida a yanzu za ta iyayin komai a gaba gadi. Yace wai ba zaki shiru muji ta bakin ta bane ko may ko ke zaki daukarwa kanki mataki in kyale ku da ita. Ai idan ya kama sai mu dauka don batafi karfin kowa a gidan nan ba ke nan ita gata yar gida muko bare ke ba zakici abinda aka girka kowa yaci ba ke nan sai ki fito da naki fi, ilin. Don kina takama da hjy na cikin gidan da zance ya tashi abi bayan ki to ko hjy ba zata yarda da wanan halin da kika dauko yiba. Irin maganganun da take fadi dole suka saka mata ido har ta kai aya don bata jin taro a lokacin kishin ya motsa sosai kan dan abinda baikai ya kawo ba. Sai fadi take ai ba akanki na fara zama da kishiya ba a gidan nan balle kizo ki min aikin gaba gadi ke gaki yar gatan dangi . To ki sani nan din dai gidana do a ciki kika samay ni balle kice zaki zo ki kafa min wani iyayi can a gida . Wallahi tunda na gane abin naki tsiyane yanzu zamu saka kafa wando daya dake a gidan nan gobe ko ance ki raina ma wani hankali ba zaki sake ba. Abinci ne yadda na tsara ayi dole haka zakici dake da yara ki don ba fin mu kukayi ba a gidan don shi ko wan mu ke ci har yaran mu. A fusace hjy maimuna da ta gaji daji abinda hjy jummai ke fada mata kamar ita ta ajeta a gidan yayi yawa bata san lokacin da ta bude baki ta fara bata amsa ba. Ke hjy jummai zancen ya isa hakan koda nayi balle van san da nayi wani abu a gidan nan makamancin hakan ba don ni kinfi kowa sani kayan gidan nan basu taba tsone min ido ba ko kadan. Kuma ki sani idan kin bada doka a dafa muna abunda kike so ai ba zaki shiga dakin Alh ki bashi dokan ga yadda zaiyi dani a gado ba ko ? Yau wanan bakin halin naki na gadara da nuna isa yasa dan sauran mutuncin ki da nake gani a gidan nan ya zube wallahi. Shi yaya din kika raina da ita wanan ta nuna hjy maryam dake zaune tana kada kafa wai itama ta hasala da zancen ke nan. Dokan ki na banza tunda ba dokar Allah da annabi bane ra,ayine hakan idan mutum ya ga zai iya yabi do a zauna lafiya idan ba ka iyawa ba dole bane tunda takardana ba a hannun ki yake ba. A fusace hjy Jummai tace haka kika ce zan ko nuna maki wata abu nake a gidan nan don kina ji kina gani sai zaman gidan nan ya gagare ki zama da duk wani wanda ya daure maki gindi, a gidan nan. Ta Allah ba taki ba idan kin saba batar da mutane ni maimuna nafi karfin ki wallahi zaman gidan nan gare ni mutu ka raba tunda nariga da na shigo. Da dai ace ban shigo bane sai barazanan ki ya dan tsoratani sakariyan banza kawai wace bata amfani da ahekaruta uwargidancin naki na zalunci har kike gadara dashi. Ba hjy jummai ba har hjy maryam da Alh ranan sunyi mamakin hjy maimu din yadda ta tsaya tana fadin magana ga yadda kowa ya santa mace mai hakkuri da kawar da kai ga komai na gidan. Tashin muryan su ya dawo da hankalin mutanen gidan gare su cikin sauri Hadiye da Amma suke rige rigen zuwa inda suke a garden suke maganan. Tu daga nisa Amma ke tambayan abunda ke faruwa a tsakani shi da kyar aka samu sukai shiru Alh sani ya fara bayani abinda hjy jummai ta samay shi dashi daga dawowan shi. Salati hadiye ta saka tare da fadin hakika Allah yayi gaskiya da ya ce zato zunubi ne koda yazama gaskiya. Kwanan da muka samo gidan yaya mustapha da muka samu an debo a gonan shi shine ya dibarwa su yan biyu mai yawa muna zuwa gida ta raba ta aikawa kowa da nasa sauran da take dafawa yaran ne yau ta soya masu shine kuka gani kuke wanan magana. Hadiye dakin kyalesu ai har ina naga kwan gidan da zan diba bayan makuli store din yana gurin ta ko gishiri kake so sai da umurnin ta za a baka. Alh sani yace to ke kinji da kike ta wanan irin tayar da jijiyoyin wuyan akan abinda baikai ya kawo ba tun dazun na fada maki abi maganan nan sannu don a gane gaskiyar maganar kin kiya. Yanzu ga gaskiyar maganan ya fito may gari ya waya da hakan da kukayi shiyasa ake son bincike kafin yanke hukunci. Amma da dakyar ta kawo kanta ta samu wuri ta zauna tana fadin to ai yanzu shike nan gara da Allah yasa haka ya faru yau din nan. Abinda nake so dakai daga yau aiwa kowa cefanen ta a bata ita da yaranta mace ta dafa abinda ranta dana yaranta ke so suci. Wanan bakar akidar ba dai don baka dashi bane ake hakan don shiga hakkin wasu ne kawai wanan maganan kuma umurni na baka ba son jin ra,ayin ka nake nema ba kan magana ta. Gaba dayan su sunyi mamakin jin fyrucin tsohuwar da bata faye sa baki a cikin zancen da ke wakana a gidan dan nata ba don kawaici. Sai gashi yau da rana tsaka tana bada umurnin kawar da dokan da hjy jummai ta kafa take ganin ba mai iya ta da wanan dokan a gidan. Tsohuwar ta kawar akan dalilin fadan ta da yar ta kuma amaryam su sai take gani anyi hakane don dama a kuntata mata a gidan. Har taso tayiwa tsohuwar rashin kunya nan Alh sani ya falfalle ta a gaban kowa abinda take ganin gazawa ne hakan da yai mata din. Tun daga wanan ranan suka kulla da hjy maimu a gidan wanda zaman lafiya ya kara kawuwa a tsakanin su. Ta dauki kiyayyan duniya ta dora akan hjy maimuna da yaranta bata kaunar abinda ya shafesu ko kadan ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU SARKA MAI , , , , , , , , , 4️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA SAKON GAISUWA DA FATAN ALHERI HAR KULLUN GARE KU MASOYANA DA BAKU LISSAFUWA A GARENI DA MA WA YANDA BAN SAN DA SU BA NAGODE NAGODE UBANGIJI I A SADAMU DA RAHAMOMIN SA AMIN ALLAH YA BIYA MUNA BUKATUN MU NA ALHERI. MASU FADON ZAINAB NADA NAKASA DA GIRMAN KAI RASHIN SANI NE YASA KUKE DAUKANA HAKAN AMMA INA MAI BAKU HAKKURI GA DAUKAN DA KUKAI MIN DIN. YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A NATSE BA TARE DA DAUKAN NAUYI A KANKI BA MALAMAI SIN SUN CE NAUYIN AMMA KADAN SAI YA HANAWA MUTUM NASARAN SHI ALLAH YASA MU DACE. DARI UKU NE KACAL KATI KO TA BANK ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 2254380105 ALLAH YA BADA IKON BIYA AMIN Idan nace maku masu jin dadin wanan tsari da tsohuwar gidan ta kafa yau sunfi wacce akai case din domi ta sun fi yawa a gidan don hjy maryam tafi kowa farin ciki da wanan tsarin da akayi masu. Hjy maimuna bata so wanan hukuncin ya fado a sanadin ta ba don sanin halin waye hjy jummai da riko a ranta sai dai batai wani damuwa ba iya kokarin watsar da zancen da tayi a ranta taci gaba da harkokinta. Bayan kwana biyu da yin wanan maganan mota dake kawo masu kayan masarufi ya tsaya a kofan gidan tare da yaron shagon Alh sani babban yaron shi dake kula da al,amuran komai na Alhajin daya shafi shago da gida da duk wani al,amuran daya shafi rayuwan Alh din. Ahmed yaro ne mai rikon ammana da sanin ya kamata sosai shi din ba wani hadi tsakanin shi da Alh sani haduwa ce ta irin gamon jinin nan ya hadasu tun yana yaro yana yawon almajiranci suka hade da Alhaji a kofan gidan shi. Yayo bara bai samu ba ya dawo kofan gidan Alh sani ya kwanta ga hadari ya gama gari a lokacin ruwa na barazanar saukowa a ko wani lokaci a garin . Hakan yai daidai da dawowan Alh sani daga kasuwa don ganin hadarin da yayi suka rufe shago don sun san idan ruwa ya gwauce wanan hadarin sai yadda hali yayi a lokacin . Yana sauri zai shiga gidane ya ankara da yaron a waje kamar ya shige ya kyale shi sai kuma yanayin yaron ya bashi tausayi sosai ya dawo baya yana tambayan shi komay yake a nan ? A ciki yanayi damuwa yaron ke fada mai yayi bara bai samu bane ga hadari ya dawo nan ya fake tausayi shi ya kara shiga ran Alh sani kaaancewan shi mutum mai tausayawa na kasa dashi. Sai yaji ba zai iya barin yaron a yanayin wanan hadarin da ya gama hade gari bai dace ya bar wanan yaron a waje haka ba sai ya umurce shi da ya biyo bayan shi zuwa ciki. Hjy jummai na ganin shi shigowa da yaro a bayan shi ga yaron bagidaje dashi kana ganin shi kasan almajirine don yana dauke da dan kwanon baran shi. Nan ta hau fada don ko tariyan arziki ranan Alh bai samu ba a gurin ta sai fadan ina ya kwaso wanan yaron dake binshi a baya haka. Dan murmushi Alh sani ya sauke a fuskan shi tare da fadin yanzun dai bashi abinci kafin ki fara tambayana zan shiga in fito sai in fada maki komai akan yaron. Yana fadin haka ya shige ya barta da yaron a wurin tana binshi da harara mai nuna kiyayya a gare shi inda yaron ya sha jinin jikin shi da kallon da take aika mai din. Cikin tsawa ta dubi yaron tare da fadin bace min da gani ni banda wani abincin baka daga ganin ka irin almajiran nan ne munafukai ka fake ka marairaicr mai kamar na kwarai ashe mayau dari. Da wanan kazantar naka zai wani kwaso min kai har cikin falona haka kana wani irin bashi da tsami kazo ka kakkaba min keyan kuna almajirai iyayyen ku ma sin gaji daku a can suke turo ku cikin duniya da sunan almajiran ci. Haba jummai wai mai yasa ke baki da tunane ne wai idan idon ki ya rufe ai ba yaron zakiwa fada ba nida na kwaso shi ya kamata kima fada yanzu. Alh sani ne daya fito daga daki yake wanan maganan rai bace inda bai tsaya jin amsata ba ya tambayi abincin sa ta mike tana cika tana batsewa ta tafi dauko mai abincin nasa. Zo nan yace wa yaron tare da tambyan sunan shi yaron ce dashi Amadu yace kace Ahmed kake mai babban suna samu wuri ka zauna kaci abinci idan ruwa ya tsaya sai ka wuce makaranta kaji. Nan yaron ya samu wuri daga nesa ya dan tsugun na yana ma Alh sani godiya irin wanda almajirai kewa wanda ya kyautata masu sukaji dadi. Lokacin ta fito dauke da tire din abincin data shiryawa maigidan ta nufo inda yake sai dai ganin shi tare da yaron yasa ta bata ranta sosai. Sai da ta aje abincin ta samu wuri ta zauna tana kallon ikon Allah a cikin plate din da ta dora mai saman kayan don cin abincin shi ya fara zubawa da yawa ga mamakin hjy sai taga ya mikawa yaron abincin a cikin plate din. Haba kaiko a cikin plate dinka ma zaka bashi gaskiya ya kawo kwanon shi a zuba mai kuma da ka kwashe abincin ka zuba mai kai wani zakaci yace . Jummai ke na ai cin wanan yaro yafiye ma cin dani zanyi albarka baki sa wanda ya taimaki iri yara nan ba ga Allah shike da lada ciyarwa Ko banza fa yaro na kowa ne don baka san abinda Allah zai mai dashi watarana ba kaima har ka more shi. Yana ci yana mashi tambayoyi akan garin su yaron yana fada mai komai nasa har izon da yake sai da Alh sani ya tambayi yaro a karshe dai ya juya wuri hjy jummai yana mata nasiha aka taimako, Bayan a gama ruwa ne yaro yace zai tafi sai godiya yake zabga masu akan taimako shi da sukayi din Alh sani bai barshi haka ba yasa hannun a aljihun shi ya ciro sabuwar naira dari yabawa yaron yare da fadi ya dinga zuwa kullun ana bashi abinci ba sai yaje bara ba. Ran hjy jummai ya kara baci sosai da wanan sabon yaye yayen da miji ta ke kokarin mata don ita a rayuwanta bata iya daukan dawainiyar dan kowa. Ai da iyayyen shi na son sa da ba zasu sako shi cikin duniya da niyar yin bara ba tunda akwai tsangaya a kowani gari ana karatu kuma. Taso ta musa ya murtuke fuska tare da fadin umurni na baki na yin hakan har yaron ya gwauta ya sake kiran shi tare da fadin da karfe biyar nake dawowa gida. Kullun zaka zo da safe kafin karfe tara ka karbi abin karyawan ka a nan gidan kaji Allah ya tsara muna ku a duk inda kuke ya karasa fadawa yaron. Na gode Alh Allah ya biyaka da gidan Aljanna sarki da akaiwa ya sani Allah ya daukaka a cikin duniya dakai da zuri,an ka baki daya Allah ya kara maku soyayya dakai da matar ka. Inda hjy Jummai take tsaye Alh sani ya kalla tare da fadj kinji cikin dan sake rai da adduan da yaro yayi masu tace ai yawan adduan kai yaiwa bani ba. Alh sani yace in banda abinki idan addunan ta kamani aikema ya shafe ki don Allah jummai ina rokon ki arziki ki dinga sawa yaron nan abinci fisabillilah. Sai da ta nisa tace naji amma kuma nima ya zama dole in har zan bashi abinci gidan nan sai yai min dan aiki shima a gidan nan. Jummai wani irin aiki kuma wanan dan yaron zai iya maki kamar wanan in ba hali na wasu iyayye ba ai baici ace an barshi ya shigo duniya ba haka. Don Allah ki jaye wanan zancen aikin ki bashi abinci saboda Allah kamar yadda na bukata kiyi din ba don ni ba sai saboda Allah. Tace naji cikin wani irin murya dake nuna rashin jin dadi ta ga maganan mijin nata

Chapter 3 of 11