Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Downloaded From https://tknovels.com.ng Murfin Jallo Dan Uwa,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 1 1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Hayaniya irin na babban gida shine ya tayar da mama daga barcin data dan samu ta runtsa na safe ,bayan idar da zikirin safe data sabayi a duk safiya . Wanan dabi,an kusan ya zama mata jiki akullum idan ta idar da sallah zata zauna tayi zikiri har sai rana ya foto sosai kafin ta dan kwanta ta ba ido hakkinsa. Daga inda take kwance din tana jin yadda yaran gidan nasu da manya ke kara,kaina a tsakar gidan kusan hayaniyar babban gidan nasune ma ya tayar da ita a lokacin. Salati tayi tana dagawa a kasa inda take kwance saman sallayanta ta dan jima a zaune don gargadin likitoci dake fadin. Idan ka tashi tsaye barci kada kayi saurin mikewa tsaye a lokacin don min a daidai lokacin jinin dake kwaranya a zuciya bata gama sauka ba yana yuyuwa ka mike hakan ya ja maka matsala a rayuwanka a cewarsu. Ana son Sai ka dan bada yan mintuna a zaune kafin ka mike tsaye don kariya ga lafiyan ka a lokacin wanan dokan da mama taji illanshi. Baga yaro ba baga babba ba dokace da likitoci suka bayar don gujewa fitinan lafiyan jikin bawa daka iya haifarwa mutum ciwarwutan zamanin nan . Hakan yasa wanan boyar Allah ta rike wanan akidan ta dan bada lokaci a wajen zaune daidai lokacin da aka turo kofan dakin nata tare da daga labulen dakin aka shigo ciki da sallama muryan danta na ukkune yake sallaman tare da fadin ashema baki tashi ba mama ?. Daidai lokacin ta dago kai tana sauke mai kallo tare da fadin na tashi Habu badai har rana tayi hakaba kuna shirin fita ? Rana tayi mama yanzu kusan karfe takwas da rabi ake nema zuwa nayi muyi sallama don yau balaguro zamuyi har wani kasan ba lalai bane mu dawo a yau ko gobe saidai kun ganmu dai zance. Kallon mamaki take binsa dashi tana fadin haba Habu wai sau nawa zan maka fadan irin haka don Allah ? Mutum zaiyi tafiya mai nisa irin haka bazai fada a gida ai masa addua ba ka raina da dan adduan da muke binku dashi ko yaushe ke nan ? Zaune yakai saman kujeran dake gefe ciki da kaya yayiwa kansa wajen zama a gefe yana fadin mama muko muka san amfanin adduan ku akan mu don duk abinda muka dafa muna ganin alheri a cikinsa. Murmushi matar tayi tana fadin yanzu dai ina kuka dosa Habu ko kudun zaku kuma yau dinma ? a,a mama wajajen Camero muka dosa wajen wani taron gargajiya da za,ayi a can kinsan aikin mu ya kumshi hakan sai munje don dauko rahoto. Shine zamu dauko rahoto akai da zamu yadawa al,umma su gani ikon Allah yanzu habu har camaro zaka hankalinka kuma a kwance ? Batare daka sanar da mu ba sai yanzu ka shirya tafiya kazo kana fada min Habu ? Wai meyasa kudai maza baku mayar da tafiya a bakin komai bane wai ? Kako san nisan dake tsakanin zaria zuwa camero ? camero din nan da kake ji kawai a baki tafiyace mai nisa fa daga nan . Ya amsa da fadin kuma tafiyan mota zamuyi mama saboda kayan aikin mu dole mubi mota zuwa wajen taron wanan yasa zamu tashi tun yau ai a dai muna addua muje lafiya mu dawo lafiya. Insha Allahu lafiya zakuje ku dawo lafiya Abubakar alherin dake cikinsa ubangiji Allah ya sadaku dashi sherin dake cikin tafiyan kuma Allah ya nisantashi daku alfarman Annabi da alkur,ani ya amsa da amin cikin jin dadin adduan mahaifiyar tasu a gareshi. Sallamu Alaikum ga nakiyar baby muryan wata dattijuwa dauke da kwala a kai data shigo babban gidan Alh talle din ta tsaya daga kofane ya karade gaba daya gidan. Daga can dakin mama din inda take bankwana da danta taji muryan wanan matar cikin mamaki take sake zancen da sukeyi da dan nata. Cikin mamaki take fadin nakiya kuma da safen nan ? Har yakai a fara tallan nakiya gida gida haka me mutane ke nema da bindan kudine wai nakiya dai a sanina sai bukin aure ake nakiya don ango. Murmushi Abubakar yayi yana fadin barin inje mama kada in makara abokan tafiyana suna kirana tun dazun. Nan uwar ta dago tana fadin kaje kuyi sallama dasu hjy kafin ka tafi bana son irin korafin su na baka sallamesu ba din nan. Insha Allahu ya fada yana mikewa tsaye barin dubasu in dawo mama ya fada yana mai barin dakin cikin kuzarinshi irin ta namiji mai jin lokacinsa. Dakin hjy babba ya nufa ya gaida ita tare da fada fada mata inda suka dosa a ranan ba yabo ba fallasa tayi mai Allah ya kiyayye hanya. Ya fito yana kokarin shiga wajen hjy Nana ya hangosu gaban wanan matan dake faman kwada sallama suna leken wani abu a cikin kwalan da matar ta shigo dashi. Hakan yasa ya doshi wajen saura kiris ya karasa yaga yara da manya sun watse wasu harda faduwa kasa don tsoro ga ihun da sukeyi suna neman inda zasu shiga saboda firgici . Wanan ihun ya dakatar dashi yaja ya tsaya yana binsu da kallo fuska daure kafin ya mayar da hankalinshi wajen matar da sai murmushi take a fuskanta. Lafiya boyar Allah tace nakiyar babyce na kawo masu gashi kuma sun watse sun barni dashi . Kallon matar yayi cikin mamaki murmushin yagani a fuskanta yasa ya karasa wajen yana kokarin kallon kwallan dake gabata bude. Ido ya runtse lokaci guda don wani katon maciji kalan da sai a cikin film yake ganinsa. Ya nade a waje daya ya cika kwallan har baki sai kansa daya dora a saman jikinshi yana kiu kiu da idanuwansa dake bude. ALLAHU LAH ILLAHA ILLAH ANTA SUBBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZULLUMIN ya ambata a fili . Muryan matar yaji tana fadin kada kaji tsoro kai namijine kuma sadauki ba asan maza da razana ba sadauki. Daga can bayanshi yaji muryan dayan kanwarsa tana fadin yaya Habu kada kaje kusa don Allah macijene a cikin kwallan nan babba. Jin sunansa da aka ambata yasa matar fadin Garba sadauki garba gagare kai sadaukine ko a fagen fama kafiran makka sun buga sun barka sarki rikon amana mai alkawari ya cika har bayan rai,,,,,,,,,, Dubu biyu ya zaro a cikin aljihunsa ya mikawa matar takai gwiwa biyu tana zabga mashi addua da neman tsarin ubangiji gaba da bayanshi. Ya juya da niyar komawa dakin muryan hjy Nana yaji tana fadin boyar Allah aida kin fada kwai a miko maki abinda Allah ya hore ki tafi . Yayin da matar tacigaba da fadin da yardan Allah kayi gaba saudaki sara da sassaka bai taba cima a rayuwa insha Allahu sai dai makiya su buga su barka. Mama data samu ta mike don ganin abinda ke faruwa a wajen taji yadda matar kewa danta Abubakar addu,a ta fahinci kudine ya bata yasa ta dauki dari biyu ta fita ta mikawa matar nan ta dasa sabon addua kuma tanawa mama jam,i ga duk zurianta. Ta dauki kwallan ta tafi don taga sauran iyalin gidan basu da niyar fitowa balle su sallameta saida sukaji fitanta suka fito suna mayar da ba,asin zancen a tsakaninsu kowa na fadan abinda yagani a cikin kwallan hankali tashe. Mama dai bata gani ba amma ta mikawa matar sadaka don tasan wanan matar banza ba zai fito da ita gidanta haka basai neman rufin asiri da taga wanan hanyarce mai sauki a gareta. Zancen mai nakiyar ya hana su mayar da hankalinsu ga Habu da zaiyi tafiya don da tsegumin tafiyan shi za,a fara sai Allah ya fabeshi a ranan dan shigowan wanan matar mai yawo da macijin maisa a cikin kwala tana cewa ga Nakiyar baby. Idan kuma tasan sunan wani gida a gidan zata ambaci sunan maishi tace ga nakiyar wani sai wanan abin tashin hankalin da mamaki ya tsaya masu a rai har mahaifiyarshi ta fito rakiyarshi da iya kofa ta tsaya tanawa danta fatan Narsara da Allah ya tsare ya kare wamda sai lokacin hankalin hjy babba ya dawo garesu. Daga kofanta take tambayan yau Habu kuma ina za a haka tunda safe ni yazo muna gaisawa hankalina yana gun wanan bakar matar data tayar muna da hankali da safen nan. Daga kofa mama din take bata amsa da camero suka nufa lokaci guda matan da yara dake wajen suka amsa da fadin camero kuma ? Wasu na Allah ya tsare wasu kuma sunyi gun suna zancen zuci inda sabo ta saba da hakan zaman gidan yawane duk yadda kayi sai wani yaga bakai masa daidai ba irin wanan zaman. Ya fito daga cikin gidan yana kallon agogon hannunsa saboda ymshi kansa yasan da ya makara saidai dole su jirashi sai yaje wajen aiki inda zasu hadu. Kamar daga sama yayi ido biyu da wanan matar ta sauke kwallan macijinta sai faman murmushi take zabga mai a fuskanta kai ya kawar da sauri yana barin kallonta. Habu bakari don ka na tsaya nan duk da dai shigan tsugula zan ma tunda na kula sauri kakeyi ka kula da addua don kai din kana tare da tsarin Allah ga kuma tarin mahassada a tare dakai. Nagode mama ya fada yana kokarin wuce ya sake jin muryanta tana fadin ka kula sosai don alherin ka da nasara yana inda ka dosa . Kudi dai wanan matar keso gareshi ya nasa hakan a zuciyarshi ya sake cusa hannu a aljihu yana dauko dubu daya ya mika mata. Murmushi tayi tana fadin wanda kabani dakai da mahaifiyarka nagode maku Sarkin da akaiwa ya sani. Naso magana da mahaifiyar ka saidai gidan ku gidan yawane dana fada mata wani magana amma ba laifi idan tana son ji ko kai ina can gidan hjy indo mai kosai a nan na sauka. Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin yana aje mata dubu dayan da taki karba a hannunta saman kwallan yasa kai ya tafi don ya dauka zancen shirme take masa a lokacin don kawai ta yaudareshi yasan halin mutanen yau da yaudara. [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Tafiyace ta mota da zai dauki dogon zango haka suka fara tafiya tun suna dan hira a tsakaninsu har abin yakai da anyi shiru kowa na tunane a kansan zuciyanshi. Dosan mabila da sukayine yasa su fara bayana mamakinsu a fili kowa na fadan albarkacin bakinsa ga albarkan kasan yankin mabila din. Abin sha,awane da daukan hankali ga bakon zuwa wajen harma wanda ya saba sai yabi dabbobinsu da kallon shawa yadda suke daban da wanda aka saba gani. Lokacin da suka zo wajen wanan hawan kusan kowansu hannushi a gaba yake yana ganin kamar ba zasu iya hawan nan ba don yadda sukaga wajen. Sai gashi cikin yardan ubangiji sun hau lafiya sun gangara kuma lafiya a sannu suka fara barin cikin nahiyar kasan Najeriya zuwa cikin kasan camero dake da iyaka da Nageria. Abin sha,awa don basai ka tambaya ba alakansu da addinin musulunci don har yan wani addinin shigarsu shigen na musulmaine su a kasan sukeyi. Tafiya dai tayi tafiya don shi driver yasan yankin da za ayi wanan taron wanan yasa basu damu da yada zango ba sai tsatsaya ko ina ba. Saidai idan lokacin sallah ya riskesu sai kuma shan man a hanya sukama hanya amma sam basu tsaya kwana a hanya basu kamar yadda wasu da yawa suka yada zango. Hakan yasa sukai wa wanan yankin shigar safiya duk da alokacin wurin sha dayan ranane a lokacin duk wani mai lalura ya fito a lokacin. Sai wanda ke gida baida abinyi sannu a hankali yake bin garin da kallo daga bayan motan yayin da driver ke aikin kutsawa acikin garin zuwa babban filin da za,ayi taron gwajin na gargajiyan shekara. Suna wanan al,adanne bayan ko wani shekara goma idan ya shige in rayuwa ya kewayo ake haduwa wajen wanan shagalin nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya. Abaya kasan Nageria tana irin bukukuwan nan na nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya wanda yake kawo dankon zumunci da habbaka sana,an mutane da cigaban kasuwanci harma da zumunci a tsakanin yan garuruwa na nisa dana kusa. Sai a yanzune da abubuwan kasan suka tabarbare wanan al,adan ya mutu mutus a arewancin Nageriaa sai dan abinda ba,a rasa ba dai kawai da akeyi yanzu. Sai dai al,adan kamun kifi da wasan ruwa da sauran al,adun har yau har gobe mutanen kasan kebbi a garin Argungu kabawan asali basu daina hakan basu a wajensu. Don suna raya garinsu basu bar al,adansu da suka gada tun kakanin farko ba da kakani baya, don manyansu sun rike da wanan abin sosai tare da kawo cigaban nahiyar tasu ta Argungu din har gobe. Wanan kadai za ace an saurayi a yanzu cikin arewancin Najeriya da har wasu kashe duniya suke zuwa kallon irin al,adunmu na hausawa tare da fasahan malam bahaushe dake tafiya da al,adanmu na Nageria. Bayan shishi din a gaskiya yana da wuya ace an saura wanan habbaka al,adan da sauran kasashen africa dake kewayen nageria irin su Niger, ghana, camero kwatano da benin da sauransu su basu yarda sun bar al,adunsu ba kamar mu. Zama ya gyara daga bayan motan yana sauraren Sahabi mai daukan photonsu dake wanan sharfin akan nahiyar ta arewacin Nageria da yanzu abubuwa suke ta kara lalacewa a kasan saboda sanyi da rashin sanin ciwon kan malam bahaushe a yanzu. Ai baka sani ba malam Sahabi zance dakai wanan abin tun lokacin da aka ragewa gidan Redio Kaduna karfi da power abubuwan da dama duk suka shiga tabarbaremuna kai in maka na mahaukaci kamar anyi wanan abin da manuface zance dakai. Don wallahi ba karamin koma baya haka ya mayar da Arewa baya akayi ba da hakan hakan ya taba kima da mutuncin arewa sosai a kasan nan. Dama sune masu haskawa suna yadawa amma tunda wanan ya faru sai sannu a hankali kaga abubuwan sun fara ci baya. Hakane kwarai malam ibrahim maganan ka dutse wallahi wanan abin ya taba arewa sosai don kashe wanan gidan redio da sauran waje irin masakan kaduna su gidan kada da wajen fata wanan abin ya kawo muna cibaya sosai a arewa yanzu don da suna raye matasa zasu samu aikin yi a kasa. Salatin Abubakar ne daga bayan motan ya dawo da hankalin driver ya maida hankalinshi sosai ga a saman dan wani tsukaken haya da suka biyo inda wasu yan mata ke gara amalanken shanu. Wanda saura kiris su gwauro da juna Allah dai ya gyara ya takaita masu wahala dole sukaja burki suka tsaya suna maida numfashi. Malam ibrahim ne ya soma fitowa daga cikin motar yana fadin kaga min almuran yarinya kawai Allah ya kawomu lafiya saida mukaga mun shigo gari muna murna zaki ja muna tsiya. Allah dai ya gyara malam ibrahim barta ta tafi kawai itama kauyancine bata sanda mota a bayanta ba sun dauka sai masu kafa kawai suke tafe a hanyar. A daidai lokacin da hakan ya faru uwa mai kulawa da yawan addu,a ga yayanta takanji wani yanayi na daban aduk lokacin da wani mumunan abu zai samu danta. Irin wanan yanayin ne ya ziyarci mama a lokacin sai ta shiga maimaita innalillahi a kasan zuciyanta da sauran addu,oin da zasu aikawa yayan ta dake cikin duniya dama wa yanda ke kusa da ita kariya. Kasa hankalinta gida biyu tayi tana tunanen Abubakar ko Jafar mai yawan tafiye tafiye don shi ko yaushe a hanya yake dan kasuwane bai tsaya ga aikin gwaunati ba ya aje ya soma kasuwanci da yake ganin yafi mai aikin gwaunati a rayuwansa. Alhamdullahi kuma an samu cigaba sosai a wanan harkan da yanzu har yakai lamarinsa ya fara tsone idon makiya. Su ukkune diyanta maza da Allah ya bata da marigayi din sai mata ukku shidda ke nan matan biyu kananane koda mahaifisu ya kwanta dama autar ta ko yayeta batayi ba a lokacin. Wanan yanayin daya bakunceta yasa ta fita da sauri ta yafa hijjab dinta dauke da kwalin sugar a hannunta wanda ta saya a cikin hijjab dinta. Kofan gida ta nufa akwai tsangaya gaba dasu kadan can takai a rabawa yara sadaka shi kuma malam ta bashi naira dubu sadaka. Tun kan tayi nisa take jin an fara raba sadakan sugar tana tafe da dan saurin don ba fita sukeyi haka ba don wai mijinsu ya rasu suna cikin gida ko yaushe zakice mijin nasu yana rayene. Don komai da akeyi gidan ba a fasa ba don ko wani daki na gidan yayansu suna rike da uwayensu da kannensu da wa yanda basuyi aure ba. Rayuwan gidan marigayi Alh Sanda rayuwace ta ba yabo ba fallasa ga iyalinsa daya bari duniya don ko yabar masu abinda zasu duba kansu ko bayanshi. Daidai wadata gwargwadon hali dai ba cancan ba kowansu ya samu kaso daga abinda marigayin fitacen dan kasuwan tsohon yabari. Wanda bayan rasuwansa duk kokarinsa da yake raye wajen ganin ya tsaya ya hada kan iyalinsa koda bayansa ba wani matsala ko barakan rashin hadin kai da zai biyo bayan hakan . Sai gashi a karshe bayan Allah ya karbi rayuwansa an samu dan matsala a tsakani iyalin nasa saidai ankai zuciya nesa da wasu bangare sukayi don kawai a zauna lafiya. Haka din ne kuwa ya biyo baya a yanzu masu zaman hakkuri sunayi yan bamu damu da gado ba ko dashi ko babu muna tsaye da kafafun mu. Irin bangaren dakin mama ke nan dake da yara kana a cikin gida don ita Allah bai bata haihuwa da wuri ba har mata biyu sukazo a bayan ta sukai ta haifo yayansu sai can kwatsam ubangiji ya azurta da samun ciki. Dama kamar camfi haka zancen yake kuma ga duk matar da bata haihuwa zakiga ubangiji ya azurta hannunta da arziki duk sana,an data dafa zaiyi albarka sosai a rayuwanta. Saidai da zaran mace ta soma haihuwane zakiga arzika ta ya soma jayewa sannu hankali ya koma ga yaya kuma wanan abin kamar wani camfi haka yake idan mutum ya duba. Haka har in Allah bai azurta ta da haihuwan ba zakiga mace komai ta dafa da sunan neman kudi abin nan zaiyi albarka sosai a rayuwanta. Anan dai kamar wani baiwane ko hikima na ubangiji daya barwa kansa sani akan hakan saidai kiga mace ba haihuwa tanata wahala da yan uwa bata gajiya da hakan. Irin wanan rayuwan mama Dubu tayi da farko a rayuwan zamanta gidan mijin nasu abaya tana da abin hannunta sosai datake juyawa wanda har yakai ta mallaki wani fili babba a lokacin . Saidai ta boye hakan ga yan uwan zamanta tabar wanan tsakaninta da dan uwanta da yai mata jagora a lokacin har ta mallaki wanan filin a wani sabon unguwa da gwaunati ke yankawa mutane filin. Wanan dan uwan nata shine ya karfafa mata ta soma gina da sunan saita bada haya inda taja daku part part har hudu a gidan saidai Allah bai nufi ta karasa ba Allah ya karbi ran mijin nasu inda ya barta da yara kanana tare da ita. Sai bayan rasuwan mijin nasu da son kai ya shigo cikin rabon gadon sune manya dake da diya masu girma da kuma yan uwa dake fada aji suka shiga suka fita aka tauyewa marasa galihu hakkinsu. Dan abinda ta samu ita da yaranta shine suka sayar ta karasa gina wanan gidan nata data soma gina sai kuma hakan ya dawo ya tsonewa abokan zamanta idanu daga baya. Wanan ya kara ja mata tsana da tsangwama daga ita har yaranta saidai duk da wanan mama Dubu bata yarda ta bargidan mijinsu wanda ba a kai ga rabashi ba har lokacin tana zaune ciki har yanzu a part dinta anan take rayuwanta da yaranta kanana da basuyi aure ba. Bayan ta dawo daga kai sadakan hayaniyan yan cikin gidan ne ya tareta tunda ta doso gidan hakan baisa ta tsaya kula mai sukewa hayaniya ba don indai da sabo ta saba da hakan

Chapter 1 of 4