ai.
Wayanta dake makale a caji ne ya ta samu ya kara ta dauka muryan Habu dintane
taji yana sheda masu saukansu lafiya tare da mata bayanin irin nisan tafiyan da
sukasha a hanya.
Murmushi tayi tana fadin a godewa Allah daya kaddara saukanku lafiya Habu tunda
ankai lafiya ai Alhamdullahi.
Sukai sallama don sahabi ya shiga nema masu abinda zasu dan samu suci a wajen
shi kuma lokacin ya shiga masallaci ya yayi sallah ya fito shine ya nemi mahaifiyar
tasu .
Akwai sabo da shakuwa sosai tsakanin mama Dubu da yaranta ta koyar dasu shakuwa
da ita irin ko wani hali suke din nan ko a inane kuma zasu kira mama su sheda mata
halinda suke ciki din.
Suna gama wayan ya sauke ajiyan zuciya tare da shafo fuskansa yana bin garin da
kallo wanda yake kallonsa tankar a Nageria yake bawai kasan waje ba.
Komai nasu rayuwan da komai zaka iya kirasu da yan Nageria don hatta shigan
suturunsu iri dayane da mutanen Nageria .
Mazan shaddane ko yadi ajikinsu da kalan dinki kuma iri daya dana yan Nageria
saidai ya fahinci suma suna da yawan kabilu don yanayin shigar tasu daya sha bambam
.
Ya fahinci akwai masu siffan larabawa a yanayin shigarsu haka kuma a take wajen
ya fahinci bambamcin dake akwai da wa yanda basa sallah a cikinsu.
Mota ya bude ya zauna yana dakon abokan tafiyanshi da sukayi tattaki don duba
abinda zasu dan iyaci a wajen don suna son su fara haka na,uransu da zai watsowa
al,umman duniya shirin kai tsaye.
Ido ya dan lumshe a cikin gajiyan dake dibansa don ba abinda yake nema a yanzu
sai inda zai dan saka hakarkarinsa ya huta duk da yasan hakan yana da wuya.
Inda ka dosa Habu alherin ka yana wajen muryan boyar Allah nance ta safiyan jiya
da yabaro kofan gidansu da kwallan maciji yaji ya ziyarceshi a karo na biyu ke nan
tun bayan barinsu gida zuwa nan .
Don ko acikin mota yayi wanan tunanen inda ya zabura ya daga cikin dan firgita
dajin muryanta kamar a gefenshi take zaune.
Me wanan matar take nufi da zancen haka din don sai a lokacin ya tsaya yana
nazari a kan wanan matar mai yawan murmushi da fara,a a fuskanta.
Kana da tarin mahassada da makiya ka kula da addua da sadaka a rayuwanka inda
ka dosa alherinka na wajen zancenta ya dawo mai karara a zuciyarshi.
Raba kanka da irin mutanen nan masu neman abincine kawai ba wani abuba kadama ka
bari zancenta ya zauna a zuciyanka.
Wani sashe na zuciyarshi ya gargadeshi da hakan lokaci guda tsuki yaja yana mayar
da kanshi saman kujera zubur ya mike zaune don karan gugan motar tasu da yaji anayi
ya duba .
Wata bakar yarinya daba zata wuce shekara takwas zuwa tara ba haka ya gani tana
zoza hannunta jikin motar alaman dai abin ya bata sha,awa har takai hannunta tana
wasa da kuran da motar ta kwaso a hanya.
Ido ya kurawa yarinyar ya kasa magana data jaye sai binta kawai da yake da
kallo gata bakace amma kuma kyakyawan gaske.
Han din boniyo ke maria ki jaye wajen nan kada ki daukowa mutane magana ke
kadaice yarinya a wajen kowa bai kai hannunsa ba sai ke ?
Addah barin taba na koma naba da labari a ruggan mu naga motan tv har na taba da
hannuna da sauri yar uwar tazo ta jaye yarinyar tana dangwarar mata kai cikin jin
haushi da takaicinta.
Yare ta soma cikin fada fada har lokacin tana kai hannu tana dangwaranta kan ta
taba mota zata ja masu matsala suna zaune kalau.
Baisan lokacin daya bude baki yace da ita barta mana ki daina dukkanta hakana
jin hausanshi yasa yar matashiyar budurwan daga kai ta kalleshi kamar zatayi magana
sai kuma ta fisgi hannun yarinyar sukai gaba .
Binsu yayi da kallo kawai daidai lokacin daya daga cikin abokan tafiyansa ya dawo
yana fadin oga akwai matsalan abinci fa a wajen nan.
Son mun duba gaskiya abincin nan sai a hankali wallahi saidai fura kan da nono
wanan gaskiya ko kamfani za a bude a nan albarka.
Baida damuwa ibrahim akwai dan abinda na riko gudun haka ban manta da rafiyan mu
zuwa calabar ba ai.
Ku karya mu soma aiki kada lokaci ya kure yana fadin haka ya mike zuwa bayan
dogon motan nasu da suka loda kaya ya bude ya shiga ciki.
Wani jakka da kula ya jawo ya bude bread ne da cake a cikin jakkan sai wani leda
dake cike da kayan cima na gwangwani ya debo ya fito daga cikin motar ya nufi dayan
motan da yan uwan nasa ke ciki suna hira mikawa kowa yayi suka dauki murna da mashi
godiya sai sahabine ke fadin.
Kai Habu habu yaushe kayi wanan dabaran haka bamu sani ba murmushi yayi kawai ya
nemi waje ya zauna ya bude kifin gwangwanin ya soma ci da bread .
Daga kan da zaiyi wanan yarinyar dai ta dazun ya hango daga nesa ta zuba masu
ido tana kallonsu cikin shagala tana magana da wata ta kusa da ita.
A zatonshi abinda yake ci take kallo sai yaga ba haka ba motar dai tasu take
kallo cikin mamaki don yadda take gwada tukin mota da hannunta cikin yanayin wasa
da tukin mota.
Dago kai yayi suka hada ido yayi mata alaman tazo ta karba ba bata lokaci tazo
da saurinta ya mika mata bread din da kifin daya soma ci ta juya da sauri ba alaman
tsayawa godiya a gareta ta nufi hanyar da sukabi dazun da yar uwarta.
Goran ruwa ya jawo ya soma dauraye hannayesa yana dan yarfarwa kafin ya bude
mota yana fito da na,uran daukan rohoto ya soma saitawa yadda zasu samu service a
wajen taron
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Baiwa da albarka yana ga yayan baiwa da Allah yasawashi yai masu arzikin duniya da
lahira saidai yana da wuya mu yan adam mu gane hakan da sauri .
Ko wani mahaluki yana da kalan tasa baiwan arziki da Allah yai mai sai mai
natsuwa da kula zai gane hakan mama Duba ta yarda da hakan akan diyanta sun taso da
baiwansu saidai rashin hayaniyansu ya boye wanan baiwan da Allah yai masu.
Yana da kyau uwa tasaka hope akan yayanta ta zamo mai kawar da ido da son nuna
kaunar yayaa fili irin yadda wasu uwayen na yanzu keyi.
Yana da kyau nuna kaunar amma idan kun kebe da yaran don nunawan a fili yana kai
idon mahassada su illanta maki yara ko da bada mugun nufi ba kuwa don wani nasa
baiwa a hassada yafi aiki wani ko daya furta ba daidai ba ga mutum sai hakan ya
tabbata akansa din.
Ansan ko wace uwa tana kaunan danta manya sunce badon kaza bata son danta bane
take takashi sai don ya kula da duniya.
Wanan akidar ta mama Dubu shine ta shammaci mutane ta kawar da kanta gun
yayanta tun suna kanana take turasu koyon sana,a basu zama gida ana nuna masu kauna
ko so da gata da akewa yaran yanzu ana kashe masu zuciya daga boko sai boko ko
islamiya sai anyi wa yaro jan ido zai tafi islamiya din.
A bangaren mama Dubu wanan tsare yake yaro zai tafi boko daya dawo yaci abinci
zai sauya tufafi zuwa kayan aiki ya fita wurin sana,anshi hudu nayi dole ka dawo
daukan karatun Allah wanan kai,dace a wajenta don dokan data sakawa yaran nata ke
nan a gidan.
Yana da wuya ka kyala ido da rana kaga dan mama dubu a gida yana shawagi haka
kwana bibiyu dan uwanta zai ziyarci wurin aikin yaran yagano mata halinda yayan
nata suke ciki.
Yayin da ita kuma takan ware lokaci da yayan nata da dare suna hira tana jin
shakuwar kowansu na gyara ta gyara masu maikyau kuma ta kara dorasu a hanya
madaidaiciya akai goma zasu watsa zuwa neman wajen kwanciya zata kashe kallo cikon
hikima da nisa tana fada masu akwai boko da safe ga zuwa wajen aiki gara ka kwanta
da wuri ka samu natsuwa yafi zaman wanan kallon .
A cikin irin hakan tasan weak point din dukkan diyanta kuma tana tsaye a kansu
idan suna dakin nan zaki dauka yaya da kannentane suke hira a tsakaninsu.
Yar uwa mai karatu idan Allah ya halicceki gidan gadu ma,ana gidan dake da iyali
fiye da daya mata biyu zuwa ukku ko hudu zaki fahinci abinda nake son maki bayani a
nan.
Zama a irin gidajen nan zamane mai kama da zaman haya idon kowa na akan danuwa
wani bai kaunan wani da karuwa ko cigaba.
Amma a zahiri zamane zakiga anayi a fili kamar ana kaunan mutum da ciganbanshi
sai a badili abin ba haka yake ba yadda ake nunawa a zahirance.
Mama Dubu ta fahinci haka ta dalilin tsaikon haihuwan da tayi ta fahinci yadda
abubuwan suke tafiya a tsakanin abokan zaman nata ta fahinci wanan akidar sosai ga
yayansu.
Za anunawa dakin ana kaunarsa a gabanki amma a bayan ki kamar Allah Allah akeyi
yayi wanin abin magana da kowa zai tofa albarkacin bakinsa a kai gidan yawa kenan .
Irin wanda iyayyen mu ke tara mata fiye da daya zuwa hudu ko wace mace da kalan
tarbiyan da zataba yayanta ko wani daki zakiga shige dabiansu gudane dama hausawa
sunce Nono alkalin da.
Don kowani da irin tarbiyan da uwarsa ta bashi zai taso a cikinsa kusan haka
wanan abin yake idan ka bibiya mafi yawa suna tasowane bisa ga irin jajircewan uwa
a garesu wanan ke nan.
Mama Dubu yau ta tashi da zuman zuwa gidansu idan nace gidansu ba wai ina nufin
gidan iyayyenta bane a,a gidan da suka gadane ita da yayanta data haifa .
Gidan da suka saida gadonsu suka hada da na wajenta data soma gidana suka mallaki
wanan din da yanzu yaya Jafar yake rayuwa a cikinsa shida mahaifiyar mama Dubu da
suke kira da Iya mai mai.
Iya ita ta haifi mama dubu da kawu dauda sai mama dije dake aure a kaduna
unguwar sarki sune Allah ya bar mata a raye amma a baya iya ta haihu basu tsayawa
sai ukun nan suka tsaya raye.
Itama iya suna da dan nasu rufin asiri daidai gwargwado saidai ba can can ba
auren yaya jafar da zai tare a gidansa saboda girman gidan sukai shawara da iya ta
dawo nan da zama tunda akwai wadattacen waje a gidan wanan dalilin yasa ta dawo
gidan don ta zauna dashi.
Ance a wajen aurensu babban kawarta da tayiwa amaryanshi kawance tunda ta kyala
ido taga yaya Jafar ta daga hankalinta da ita taga miji .
Don bai dace ace wanan hadaden guyen dan bokon irin da take mafalkin aure shine
mijin kawarta da take kamar bagidajiya da ita dai ya dace kuma shi take so .
Ita din yar kadunace don a kuduna iyayyenta suke da zama yayin da ita kuma uwar
gidannasa Asmau mutumiyar Gwambe ce amma mazauna garin zaria aikine ya kawo
mahaifinta zaria har yai ginan kansa zama ya kamasu a garin zaria.
Da farko ance shi yaya Jafar din baya son Nusaiba don yarinyar da ba tsarinsa ba
saidai kamar abin sihiri kuma ya dan soma kulata har abu yai karfi a tsakanisu ta
shawo kansa sai zancen aure.
Wata shidene tsakanin aurensa da Asmau dashi da kuma ita a lokacin zancen
aurensa da Saiba kamar yadda nickname dinta yake a wajen kawayenta shi kansa mijin
haka yake kiranta da wanan sunan sai ba.
Lokacin farkon komawansa Lagos da harkan business dinsa ne don ya fahinci can
akwai harkokin da zai iya wanda zai hada da nan arewa.
Sai sana,anshi ya karbu sosai dan kudi sun fara shigo masa sosai a lokacin don
haka bai samu matsalan komai ba don bai bukatan taimako a wajen wani.
Haka akasha wanan bukin amare biyu a kusan lokaci guda duk ko da tashin hankalin
da uwargida Asmau tayi kan ba zata zauna da kawar nata ba.
Amma abu da manya kuma tsakanin miji da mata ance sai Allah haka ya shawo kan
abinsa manya suka inmata ta zauna.
Don hakane babu shiri ko zaman lafiya a tsakaninsu ko kadan ita uwargida tana
ganin anci amananta dashi da kawarta.
Yayin da amarya take ganin abinda yai mata kome mutane zasu fada su fada mana ita
dai bata damu ba tunda ta kama mijinta irin yadda take so.
Nusaiba Best friend din Asmau ce sosai saidai wanan kaddaran da Allah ya kawo
tsakaninsu ya hanasu kwantar da hankali su fahinci kaddaran rayuwansu ce hakan.
Na hada miji daya da sunan aure a tsakaninsu zauna suba kansu lafiya a tafi tare
zama yayi dadi.
Tun daga wanan lokacin kawance ya watse aka koma zaman kishi kinshin ma irin na
hauka din nan sukeyi a tsakaninsu.
Ga miji ba mai zama baneshi iyaka yazo yayi yan kwanaki ya koma ya barsu nan da
iya da itace zasu zauna har zuwa lokacin daya dawo kuma.
Wani irin zama mai wuyan fasara a tsakanin su suke gudanarwa agidan zama duk da
part daya suke zaune wanda ya kara fadada girmansa lokacin auren Saiba ya mayar
masu dashi two two bedroom babban falo a tsakiya.
Wanda haukan kishi ya saka babu mai tsayawa daga cikinsu ya gyara part din
zakice wa yanda basuyi boko bane a cikin gidan.
Sai in sun fito waje zaki gansu fes dasu kamar ki wanke hannu ki taba sai kinje
gidansu ki raina masu ni dai zee nace har da hali a irin hakan .
Don wani baiyi ba aiba zance ba zanyi ba ko don lafiyata sai idan miji yazone
dole mai girki zata tsaya ta tsabtace mashi falon koshi bawai can ba don kowa na
bakin ciki da dan uwansa kada ya gyara dan uwa ya huta.
Haka kuma bangaren abinci akwai matsala a nan ma din don kuwa idan ba miji ke
gari ba haka zasuyi ta horar da junansu da takaici har sai lokacin daya dawo.
Farkon zuwan saiba taso ace miji ya tafi da ita lagos don ta fadawa yan uwa da
abokai ita ba zata yarda ya barta zaria ba don ba sakarai take irin Asmau ba miji
yana lagos ita ta zauna a gida.
Sai bayan ta shigone taso nuna hakan amma uwar miji tace bata kai can ba yadda
ta sama sun tsara abinsu haka zata bi dole shine wanan rawan kan nata ya dan fara
lafawa tun lokacin.
Saboda ta fahinci ashe a karkashin iyayyensa yake wanan yasa Asmau dake gabata
bata motsa ba take biye dasu a zauna lafiya.
A cewan mama ba zata bari ya dauki iyali yaje zaman lagos ba don kada ya
shagala da dukiyan marayu dake hannunsa .
Haka zalika zaman shi a can din zai iya dauke masa hankali da gida dudu nawa
Jafar din yake inbada rigima yaushe ma ya isa iya aje mace daya balle yace biyu.
Allah ya taimaka jafar da yan uwansa mutanene dake matukar girmama iyayyensu a
yadda suka taso da tsoron mama da iya kakarsu har girmansu haka suke masu biyayya
sau da kafa.
Zaman iya a wani bangare na gidan yayi tasiri sosai a rayuwansu dontane suke
rage wani iya shege idan su fara yanzune iya zata tsaya tayiwa wace bata da gaskiya
fes hakan yasa suke dan ragewa.
Rayuwan malam bahaushe akwai kalubali da yawa a cikinsa inda wani zubin ake
yawan tauyewa mace incinta da sunan aure.
Akwai part din da babu kowa a cikinsa instead daya ta zauna a cikinsa amma iya
tace sam hakan ba zai yuyu ba wanan din dai shine kasonsa don haka shida ya dauko
auren mata biyu lokaci guda dole ya zauna a cikin nasa hakana.
Sani Allah sani ma,aiki aka samu kawu Dauda ya rokan masa wanan filin daya
fadada girman ginansa har ya bambanta dana yan uwa saboda kara fadin wajesa da
akayi.
Saboda raba gado da akayi yasa yaran mama Dubu tun bayan auren yayansu Jafar da
hjy Iya ta koma gidansa da zama suma kusan rayuwansu a can gidan suke da zaran sun
dawo hutu zasu tare a wajen kakansu suna tayata zama wanda shi jafarne ya tilasta
masu yin hakan.
Haka kuma idan suna gidan wajensa yana da wuya ka samu gida kaca kaca a cikin
kazanta don suna tsayawa su gyara tsakani da Allah.
Tsab mama Dubu ta gama shiryawa don zuwa ta dubo mahaifiyarta da iyalan danta
don tana hasashen Asmau ta samu karuwa a jikinta yadda hjy Iya ta fada mata .
Idan zata zakice ba a gari daya suke zaune ba don shiri takeyi sosai sayi wanan
sayi wancan taje masu dashi sai kice tazo daga kauyene ganin su.
Saida ta gama shirin da komai ta fito tana fadawa mutanen gidan nasu zataje ta
duba su iya ta dan kwana biyu wanan ba bakon abu bane sunsan data saba yin hakan .
A zaton suma basu dauka zata zauna kamar take zaune din nan ba a cikinsu da Allah
ya albarkaci yayan nata sosai fiye dakowa a gidan kusan ace dai sune sukaci moriyan
gadonsu da aka raba na marigayin.
Tunda wasun su har sunka ga saida kadaran da suka gada din sun koma rabe rabe
duk da mahaifin nasu bai wani dade da kwantawa dama ba sosai.
Dama ance mai zari a wajen rabon gado shine nasa bai faye albarka ba kusan haka
dinne ya faru don kuwa su yan dakin hjy babba da aka tsaya masu suka samu kaso mai
tsoka sune suka fara wullakanta dukiyan nasu.
Wanan ya jawo tsaiko da iyayyen mata suka hana yayan nasu raba wanan baban gidan
da suke zaune ciki a yanzu inda sukai rayuwa da mijin nasu.
Tunda gidan mata hudune ras irin ginan malam bahaushe duk da ko wace bangarenta
a kewaye yake sai babban falon marigayin inda turakasa yake a nan yayi rayuwa har
Allah ya karbi ransa.
Don haka har gobe idan ka shigo kaga yadda suke rayuwansu zakice ko maigidan
nasu yana rayene amma kuma kowa a yanzu yana cin gashin kansa sai dan abinda ke
shigo masu da akan kasa kamar yadda dai aka sabayi tun baya Allah yasa mu dace ya
jikan iyayyen mu da rahama Allahuma Amin.
Daki daki tabi tana masu sallama da sai ta dawo yadda kowansu keyi idan zai dan
fita sukai mata Allah ya kiyayye zakice ba wani abu na rashin jittuwa a yadda
sukeyi din.
Saidai hakkurin wani ya dara na wanine a zaman don anyi ba daidai ba an nuna
hadama da zalama daga bayane suka sulhunta kansu kan hakan.
Yan jikokin gidan da almajirai suka dauko mata kaya suka nufi bakin titi inda
zata hau keke zuwa unguwar su iya din.
Fitanta soma zancen ta ukkunsu dake fadin yau kuma ta haka aka fito muna ba Habu
yayi tafiya ba kada ya dawo ya sauke abinda ya dawo dashi mugani a bamu tabon mu .
Sai ita amaryansu tace aiko yaya bata da haka kowa ya sani nan gaskiya ko bamu
gani ba sai an bamu in rabon mu ya ratsa.
Ni bance bata bamu ba ai maganace kawai nakeyi ta fada a hasale don ba a kama
mata yadda taso aja zancen da nisa ba ta katseta.
Yaran da suka rakata zuwa titi ta sayawa rake sai dari dari data basu suka dawo
gida da murna hakan yasa data dau kaya zata fita suke taso durrrr subi bayanta da
sunan rakiya don dan wanan ihisanin da take masu.
Itama hakan yana mata dadi tana jin dadin rakiyan yaran wani lokaci takan
daukosu suzo su wuni su koma in Jafar na gari mota tana a wadace .
Daidai kofan shiga gidan mota ya ajeta da kayanta sanin da mai adaidaita din
yai mata yasa ya taimaka har cikin get ya shigar mata da kayan kuma bai tsaya
karban kudi ba duk da tsawan da take mashi akan ya tsaya ya karbi hakkinsa amma
yaki saboda mutunci.
Kauyen Zakuwande ya samu halartan baki daga sassa na duniya mu sanman a yan
nahiyar africa manoma da masu kiyo da suka cika wanan gari dam ko ina bakine dake
halartan taron mafi girma da akeyi bayan shekaru.
Engineer Abubakar daya gama hada duk wani na,ura da zai hasko masu tauraron dan
adam dinsu ya sauko daga saman motan yana kara duba saitin dayayi da kyau kafin ya
nufi bayan mota ya bude yana dauko goran ruwa ya balle yana kokarin zuba don
dauraye hannunsa.
Hankalinsa sam bai kaiga dandazon mutanen da suka kewayesu suna kallon aikin
nasu ba sai lokacin daya gama wanke hannun ya kwankwade sauran ruwan ya cillan da
goran gefe .
A lokaci ya kula da jama,an dake waje ashe akwai inda yafi Nageria kauyanci don
goran daya cillan suka taru suna wasoson dauka .
Har da manya wani dattijo daga cikin masu rige rigen daukan gora da aka tureshi
tare da kekensa yasa Habu din fadin subbahanallahi yaje da sauri ya kama tsohon
yana tayar dashi tare da kekensa yana mashi sannu.
Tare da tambayan baba bakaji ciwo ba ko yace banji ba dana naso dai in samu
wanan jallon nasaka ruwa a ciki yara kuma sun hana.
Ina zuwa yace ya koma ya dago gora biyu cike da ruwa ya kawowa dattijun ya bashi
cikin girmamawa godiya tsohon ya fara mashi sau ba adadi yaja kekensa ya tafi.
Juyawa yayi yaje gun yan uwansa da suka zubo mai idanu saida ya karaso ibrahim
ke fadin wanan yasa danasha ruwa saina jefa gora a bayan mota.
Tausayi tsohon yabani yana bukatan gorance da ganin haka yafada ibrahim yace
tun dazun yake tsaye ai yana kallonka .
Watau wanan gari gashi dai babbane cike da jama,a kuma amma kullum basu wayewa
su kasan abinda ya kawo hakan yace ina zansan hakan ni dana fari shigota yau din .
Yace gargajiya donsu har yanzu gargajiyansu yana nan basu yarda sun dauki akidar
nasara sunsawa kansu ba aikinsu ke nan noma da kiyo komai arzikin mutum ata wanan
hanyar zai nuna halinsa.
Gaga kuwa ba zasu taba cigaba ba matukar basu yarda da nasara ba a rayuwansu
gargajiyace tsantsanta a garin nan ka duba ko tsarin shigarsu mafa dabanne kuma
kowa da irin al,adansa wajen nan.
Hakan yafi masu sauki kallo daya zakai masu kagane basuyi sakaci da addinin su
ba har yanzu yawan kabilu kuma ai duk zubin fulanine garesu ko larabawa.
Haka sukai ta hira tsakaninsu suna jiran lokacin da zasu fara gabatar da shirin
nasu don komai a yanzu hada lokaci kadai suke jira.
Kuyi hakkuri mu dauko tushen labari don fahintarku masu karatu nagode.
ZAINAB IDRI MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sallaman mama Dubu yayi daidai da jefo plate din