Share this page
3 / 4
shimkafan da Saiba tayi ya fado saman hijjab din jikinta kafin ya gangara ya sauka kasa daidai kafanta ya tsaya. A hankali mama tabi plate din da kallo haka kuma take kallon yadda sauran shimkafan dayake gangarowa daga saman jikinta zuwa kasa. Kaita girgiza ta dago ta saukewa Nusaiba kafin ta mayar kan Asmau data dafe baki cikin tsoro da firgici kai ta sada kasa tana mai tsananin jin kunyar uwar mijin nasu. Da kyat mama ta iya budan baki tace yaran nan har abin yakai haka a gareku daga haka ta juya don bari part din taga hjy Iya a tsaye itama cikin takaici take kallonsu. Gara dai da kuka gwada ga uwarku yau tunda ni kun raina min arzikina mata kamar dabbobi kullum fada dan abu kadan fada kamar karnuka. Akanku aka fara zaman kishine wai in ba auro mata ana haihuwan ku kun mayar da gidan yaro gidan yan tasha gidan dambe . Badon makwabta na tsoron jidalina ba da yanzu gidan nan ya cika da yan kallo tunda kun zama mutanen bamza. Kishi haukane wai mijin ku yana wajen nemawa kansa rufin asiri ku kuna nan kuna tona masa asiri a cinkin unguwa sai yaushe zaku bar wanan bakin kishin nakune wai ? A hankali mama da ranta yake bace ta zagaya Iya tani dake masifa ta karasa ficewa daga part din zuwa nasu wajen kokarin cire hijjab dinta da suka bata takeyi kada ya lalace ban daki ta nufa taja bucket ta jikashi tare da yayafa omo ta barshi a jiki. Fita tayi waje don bata zauna ba kayanta dake can ta waje ta shiga kwasowa zuwa cikin falon mahaifiyar ta din a daidai lokacin Iyan tani ta kara fada ta juyo zuwa wajensu rai bace. Ta samu mama na kokarin zuge zip din dan jakar kayanta data dauko wanda zatai dan kwana biyu dashi a nan zani ta dauko daga ciki tana sauyawa. Wuri ta samu ta zauna iyace ta soma magana tana fadin yau naga yaran banza a gidan nan yara kamar tashin gareji ace babu wanda zakaiwa fada yaji. Sallaman Asmauce data shigo tana sune kai hannunta dauke da cooler abinci tazo ta dire a gaban mama a daidai lokacin kuma itama Nusaiban ta shigo da ruwan data surka da postard cleak ya rine a cikin jug ta aje gaban mama din cikin girmamawa. A,a ku dauki abinku ni a koshe nake daga gidan mijina nafito yanzu koda bai raye bayansa basu barmu a cikin yunwa ba Alhamdullahi nagode. Zaune Asmau takai tana dan dukar dakai Allah ya gani tasan mama mace ce mai kawaici da kawar da kai daga abinda sukeyi bata kulawa koda ance ga abinda sukeyi a kullum nasihanta dasu shine su zauna lafiya suba mijinsu farin ciki ga nemansa. Fitansu koma bayansane ga harkokinsu tasan zaman kaunace ya hadasu da danta don haka suma dul biyun tana kaunarsu tunda dantane ya daukosu ya kawo matasu amana a cikinsu. Yau sai gashi iya shegensu yakai har plate din abincin danta suka watsa mata saman jiki ya watse a tufafinta ita yanzu me zatace da boyar Allah nan mace mai zurfin tunane da kawar da kai irin mama. Kaita kara sadawa kasa ta soma magana mama don,,,,,, Asmau jeki kawai kuci gaba kada ku bari zaman nan dai ina son ku sanin na bautan Allah kuyi akwai hakki da amana a tsakanin mu daku da mijinku dake can yana neman abin rufin asirin mu. Idan kun zauna lafiya kuji dadin hakan idan kuma kunki kome ya biyo bayan hakan kuka da kanku kada ku kuka da wanin mu nan Allah ya gani munyi iyakar yinmu akan ku kun kasa kwantar da hankalinku ku daina wanan shashancin kishin a tsakanin ku. Sauran mata da suke zaune da kishiyoyi ake ganin kamar zaman lafiyane a tsakaninsu kokari suke suna danne kishinsu a idon jama,a kowa da kuke ganin yana zaune lafiya danne abin yake kasan ransa shin ku ba zaku iya hakan ba don Allah. Mama wanan yarinyar yar rainin wayauce waini Asmau zata zubawa abinci a plate a kawo min don ta raina min wayau kome Saiba ke fadan hakan ga mama. Hannu mama din ta kara daga mata tana fadin ban tambayi ba,asiba don Allah komai mutum yayi kansa yaiwa ina dai son ku sani ba a wullakanta abinci a zauna lafiya. Wanan shine maganata dukkan ku nan ba zance bakusan abinda nake nufi ba tunda kowacen ku uwarta tana da kishiya a gida. Mama bani wullakanta abinci wullakancintane kawai ya mota innice nace ta ban abinci cewa take naje cikin tukunya in daba shin laifine ni har na zuba mata a plate mama ? Amma dai kinsan niba wullakantata bace da zaki ban abinci a cikin plate kamar nazo bara a wajen ki kema kinsan nafi karfin hakan wallahi. Yanzu dai sai kuyi ai garara ku nunawa uwar naku halinda kuke kwana kuke tashi dashi a cikin gidan nan ta gani ksllon Iya din mama Dubu tayi tana fadin mama kin hada kayan na soma wankewa ? Don dama duk aka kwana biyu mama tana zuwa gidan ta gyarawa mahaifiyarta waje tayi mata wanki da sauran gyaran waje sai idan yan matanta sun dawo hutu suna gari suke dauke mata hakan. A cikin matan Jafar din babu wace zatace bari ta dan gyarowa Iya part din ta matukar basu din bane sukazo sukayi wurin zai koma fes. Ganin mama din ta fita batunsu yasa Saiba fita cikin hasala tabar Asmau nan saida zata mike take kara fadin mama kiyi hakkuri don Allah. Jeki Asmau a kula don Allah kece dai babba a gidan nan kanninku da abinda kukeyi sukr koyi don Allah Asmau arika tausan zuciya idan rai ya baci. Fita tayi tana tunanen irin halin mama dubu na sanyi hali macece datake rike girmanta da kawar da ido akan duk abinda ke faruwa danta dasu iyakarta nasihan da zaiwa mutum amfani gaba idan yabi. Saidai ko tayi kokarin bin nasihan da ake mata hakan bai samuwa don Nusaiba taza fito da sabon fitinan da sai tabiye mata sunyi fitina. Ita wanan tana da dama sosai fiye da wacan fitsarariyar da tafita duk wani fitina daga wanan nusaiban yake fitowa a gidan nan Iyace ke wanan maganan bayan fitansu. Taron yarane kurciya shike rudinsu a wanan lokacin wanda sukeyi a kansa yana can baima san suna yiba zasu zauna su halaka kansu haka a banza kan namiji. Wata rana ko ance suyi hakan ba zasuyi ba ai don girma yazo a lokacin saidai su koma kishin mumuke wanda yafi wanan da sukeyi zafi. Mamace take fadan hakan ta mike ta dauko tsintsiya don ta fara gyaran dakin Iya din da yayi kaca kace ga kura ko ina a falon har makewayin data shiga yana bukatan gyara idan zai samu. Komai a wajen taron nan yana gudana daidai sun fara hasko wa duniya abindake wakana wanda hakan yasa hankalinsu daukuwa da aikin don abune da yake son natsuwa don kada a samu kuskure. Sallah ya tayar dashi da yunwan da yakeji ya fito daga cikin motar tasu mai na,ura zuwa lokacin wajen taron ya cika makil da jama,a tare da Sahabi suka nufi masalacin sukai ibada ya jima kafin suka fito tare da dan zaga wajen suna kallon irin baiwan ni,iman da Allah ya shimfidawa yan Africa. Malam Habu zokaga kayan nono a wajen nan Sahabi ya fada ya doshi wani hanya dashi yana biye dashi a bayansa koreni gasu nan birjit iya ganin mutum da matan fulani dake ta kaida komo a wajen. Sahabi din ya tsaya yana taya wani kwaryan nono hakan yasa Abubakar ya fara raraban ido yana bin ko ina na wajen da kallo direct ya nufi wajen wasu da suka tsabtace nasu da komai a cikin tsabta gwanin ban shawa . Malam zoka saya baida tsami ko karni lafiyanyyen nonoce tatsin yau din nan muryan wata bafulatana ke fadan hakan ya karasa gabansu cikin mamakin jin yadda take hausanta na yan Nageria sak a bakinta. Sahabine ya karaso yana fadin aina fadama sai inda kallonka ya kare a wajen nan yaji matar fulani din na fadin wanan na shanune wanan kuma na rakumi ga wananshi da akecewa wara da wani hausan nonoce sahihi ake dafawa ya hade haka. Sai wanan kuma cikwai ce mai dadi baida mixed a cikinsa zakaso ka kara idan kayi amfani da kayan don babu algus a cikinsa ko wani mixed . Kai amma ke yar Nageria ce ko sahabi ya tambaya tace meka gani tana murmushi a fuskanta. Kafin tace dashi daga dai can muke ta fada tana juyawa da alaman neman wani takeyi alokacin a cikin harshen fulatanci take kwalawa wata kira da YANDA yanda yanda tana mata hannu tazo. Sai ga wata doguwar yar matashiyar budurwa ta juyo wace aka kira da Yanda din takaraso zuwa wajen matar tana mata fulatanci. Ido ya kafe ta dashi yana kallon yadsa ta karaso tanawa matar magana acikin yanayinta. Yayi da Abubakar yake tsaye yana kallonta cikin mamaki yana fahintar me take kokarin fadawa yarinyar. Daidai lokacin kuma Sahibi ya juya harshe a cikin turanci yake fadin ko ya saye yana da wuya yakai gida bai lalace ba iyakarsa idan a nan zaiyi amfani dashi kawai. Sai sukaji muryan matashiyar na basu amsa da fadin ku saya daga nan har sati biyu baya komai koda ba a saka a cikin fridge ba. Kayan mu suna dakyau da inganci bawai ina yabo bane don kusaya ko don na cuce ku saboda nasan zakuso shi ko nan gaba. Ta kara fada a cikin turanci da alaman gajiya karara a fuskanta lokacin tana dan kakabe kuran dake taba koren nasu da wani dan gashin dake hannunta na dabba da akaiwa ado da duwatsu . Tsaye sukayi galala suna binta da kallo tare da tambayan wai dama kuna jin turanci haka ashe da zaginku mukayi shike nan kunjimu. Ta dan kai zaune tare dan murmusa tana fadin kadan kadan ba balle nasan ba kuyi kama da wayanda zasu zagemu ba ai. Dagajin hausan mamanku na gane ku mazauna Nageriane don hausanta daban da wanda kukeyi a kasan nan. Eh daga can muke koma ince a can aka haifemu rayuwace ta dawo damu gida bayan rasuwan mahaifiyar mu rikon mu ya dawo nan. Sosai ta bashi tausayi tsab ya gama kallonta yana karance yanayinta turancine neat a bakinta amma kuma gata ta saje da dabi,un mutanen wajen ba zaka taba cewa ita din tasan ko zo inkasheka ba da hausa balle turanci. Yanda din ta kawar da shirun take fadin ku saya zakace nace idan kuje dashi aka saka a fridge zaiyi rabin shekara a can bai baci ba wanan karon a cikin hausa tayi maganan tana kara bude manyan koren dake gabansu. Sahabi bai yarda da zancen ta ba don abar zancen yake fadin wai ina zamu samu abinci mai kyau a wajen nan ? Ta dan juya kafin ta fara masa kwantace ganin baigane ba yasa ta kwalawa wata yarinya kira da Maria zoki nan saiga wanan yarinyar dake firgitashi tun zuwansu garin itace aka kira da Maria din. Yarinya ce karama saidai da gani ba sai an tambaya ba don kamarsu da yar uwar nata da aka kira da yanda sukayi kama sosai ita wanan din dai ta girmewa yarinyar a shekarune kawai zace sai dan haske da karamar ta dara babban dashi. A cikin yare take fada mata ta kaisu wajen saida abincin yan maiduguri ta amsa da to tana watso masu idanuwanta masu kama da madaran tana wani irin juyasu alaman suje din tayi gaba suka bi bayanta . Zansu tafi babban matar ke fadin ya zancen sayan kayan sahabi yana kokarin fadin su barshi kawai shi kuma Abubakar din yace dasu a bari su dawo zasu saya hakan yasa yaga fara,a a fuskan yar budurwan data kashe zuciyarshi da mamakinsu. Sun kama hanya tana gaba da dan kwarya karami a hannunta bata ko tsaya wani jerawa dasu ba tasha wani kwana suna biye da ita har zuwa wanan wajen da basu san dashi ba. Oya mun gode ki tafi kada a nemeki Sahabi ya fada sai ta amsa da to tana kallonsu saidai taki gusawa daga inda take. Abubakar daya kula yace da yarinyar yaki zo nan Abubukar ya fada yana kallonta da sauri ta biyoshi a baya zuwa inda suka nufa. Tare suka shiga shagon yasa aka hada mata take away guda ukku ana mika mata ta juya a guje cikin murna bata ko tsaya godiya ba ta nufi sansaninsu kai tsaye da gudunta a cikin murna. Murmushi yayi ya juya wajen sahabi dake mamakinshi yace mutumina yaya dai nisawa yayi yana zama ya soma fadin tausayi suka bani wallahi. Haka duniya take ai dama ba ko yaushe mutum ke samun yadda yake so ba a duniya sahabi ya fada yana kallon abinci gabansa da aka aje masu. Abincine lafiyayye mai kyau irin na hausawa ga kamshin man shanu yana tashi acikinsa sukaci sukaiwa yan uwansu take away. Duk abinda yake hankalinsa na gun wa yan nan mutanen don hakane ya saci jiki ya koma sansanin nasu saidai ya samu basa nan don lokacin yamma tayi sai wata mace dake zama a kusa dasu. Yake tambaya take fada mai ai basu kai dare a wajen sun koma gida saidai gobe tunda safe zai samesu sun fito insha Allahu. Washegari kuwa rana ta biyu da taron mutane sun fara tattara kayansu don shirin komawa garuwansu daga ciki har dasu Abubakar duk daidai su sai an rufe taron suke son su kama hanya komai dare a ranan. Bai manta da zancen yaran nan ba don da zancensu ya kwana a zuciyarshi yana son ya san wani abu a game dasu din. hanya kama ya nufi runfarsu tun daga nisa ya fara hango ita babban wacce yake kyautata zaton mahaifiyarsuce ga wasu yan Nageria suna sayan kayansu. Don kayan nasu gaskiya yayi kyau sosai haka ya karasa gaban ya dan tsaya yana dakon su gama cinikaiya da wa yanda ya sama din a wajen. Karamar ya fara gani a gabansa tana binsa da kallo kafin ya tsinkayo babban dake tafe da amalanken shannunsu dake dauke da kore. Yana wajen suka sauke kayan tsab suka jera kafin ta dago ta soma gaiyar dashi a cikin dan fara,a kafin tace dashi na dauka kun muna wayaune ai kun tafi koda yake bakai kama da mayaudariba ba kai kan. Jiya kuma sai kukayi wahala haka kuka saya muna abinci mai yawa angode Allah kara arziki me za a baka daga ciki ta fada tana kallonshi tana dago kai ? Samu tayi ya zuba mata ido baya ko kiftawa sai tayi murmushi ta sake maimaita wane kake so yace yanzu ni ina na san me zance dake ?. Tace wanan zaka iya saya kakaiwa iyali mata ko mama da yan uwa zasuji dadin tsaraban shi ansan ka shigo kasan cameron . Ko data dago kai still yana kallonta sosai sai taji ta tsargu da hakan ta dan dukar da kanta kasa tana wasa da zara zaran yatsunta. Bakayi magana ba ta kara fada kallon yadda ake durawa mutane a jarka yayi yace nawa duka kayan nan da kika sauke ? Ido ta zaro waje tace dukka fa kace zasu iya kaiwa dubu hamsin da kudinku na Nageria ga mamakinta sai taga yana kokarin zaro kudin daga jikinsa. Kuyi min parking dinshi yadda ba zai samu matsala ba kudin abinda zakiyi amfani dashi ayi parking yana ciki saidai don Allah ? Saita dago ta kalloshi yayi mamakin ganin idonta da hawaye jikinshine yai sanyi ya dan matsa kusa yana fadin. Lafiya dai tayi kasa da kai tana fadin bansan irin godiya da zan maka ba a yau da an watse taron nan bamu saida kayan nan ba ba karamin fitina zamu shiga ciki ba don zamuyi hasara sosai zamu kuma shiga cikin ukuba. Saboda me ya tambaya yana kasheta da ido donson jin karin bayani shidai yanayin yarinyar yayi mashi sosai tana da natsuwa sosai dayake hangowa a gareta. Murmushi tayi tana fadin dogon labarine mundai gode da wanan taimakon da kayi muna Allah ne kadai zai sakama da alherinsa. Amma meya dawo daku kasan nan kuda kuka saba da rayuwan Nageria kuka zabi dawowa nan ku zauna ? Ya zamuyi bamu da kowa a can yanzu wanda yayi sanadin zuwanmu can Allah ya karbi abinshi dole muka dawo kasan nan tunda ba yadda zamuyi. Kina da waya in naje mu dinga gaisawa daku tace da ina dashi wanda nake amfani dashi a school saidai zuwan mu nan gaskiya mun kadar saboda yanayi saidai ka ban number wata rana zan kira insha Allah. Ai har karatu kinyi ashe kuma kika kare a nan kina tallan nono tace wanda baida gata ai duk yadda rayuwa tazo mashi haka zai rungumeta mun rasa gatanmu tunda mahaifinmu ya rasu Allah ya jikansa yace ta amsa da amin. Sai wata rana kenan zaki kira ba zaki kira kiji ko mun sauka lafiya ba ko kuma ina da bukatan wanan abin ki turo muna dashi. Dariya abin ya bata cikin dan kunya take fadin kayi hakkuri banda wayace kona karba ba zan kira ba din kaga ai gara dai kar nayima karya. Kinsan wajen motar mu ko ta amsa da ehh yace a shirya komai kusamemu can ya juya ya tafi ta bishi da kallo tana yaba irin kirkinsa da halarci. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A tsaye ta sameshi suna hada kayansu sallama tayi daga bayanshi cikin yar siriryar muryanta ganin kalkon mamakin da Sahabi ke mata a bayanshi yasashi juyawa da sauri yagame sahabi din ke kallo a wajen ? Kasa tayi da kai tana kokarin gaidashi da aiki ta hada da fadin ga kayan ka an hada komai yadda ya dace daga nan ko lagos zaka ba zaiyi komai ba insha Allahu. Ba lagos zani dasu ba zariya zan kaiwa mahaifiyata ya bata amsa tace Allah sarki aiko yayi daidai da bakin tsofi don komai baida tsami da zai hanata bukatansu. Mungode kwarai wallahi yadda ka taimaki rayuwan mu Allah ya taimaki naka kaima ta fada cikin yar siririyar muryanta. Wai tsaya Habu wanan duk kayankane wanan haka kome nifa ban gane ba wuceshi yayi yana fadin ba zaka gane ba kuwa kai matso ku saka min a bayan mota kunji ? Lokacin ibrahim ya karaso yana fadin oga kace da shirinka dama muma bari mu debo namu ashe dama ina son saya ina jin tsoro. Kaje gunta kayansu yana da kyau sosai tace dariya sosai Sahabi ya kwashe dashi yana fadin ashe mun saura dawowa garin da alama zamu dawo wani karon kenan kuma ? Yar filo akwai saura a wajen ku tace eh za a samu bari na duba idan akwai a wajen maman mu ta juya ta soma tafiya . Kai dan iskane yacewa Sahabi dake ta kwasan dariyan shakiyanci sahabi din yace dariya nake don yadda na hasko kayi tsaye ana shadinka kasan wanan aiba karamin shadi zakasha akanta ba wallahi. Shima zancen sahabin saida ya sakashi dariya in akwai abinda ya tsana a taba lafiyan jikinshi balle shadi ta ina zai tsaya kan mace ai mai shadi ko gudane balle ba adadi. Zama yayi saman motan yana sauraren Sahabi dake bayani akan shadi da yadda akewa wanda ya gaza motsin wayarshi ce da tayi dan tsuwa daga Aljihunshi hakan yasa yaciro ya duba alert ne na lokaci har yayi niyar mayar da wayar sai kuma ya fasa hakan sim din ya debe daga cikin wayar ya mike tsaye. Wani wuri dayaga ana sayar da waya ya dosa layin waya ya saya duk da tsadansa bai tsaya neman ragi ba ya biya ya juya ya koma inda ya fito. Ya gama turo komai a dayan wayan nasa kafin ya goge na wanan wayan yana gamawa tana karasowa wajen da kayan ibrahim. Kudi ibrahim ya ciro ya bata yana fadin Allah yasa dai yadda kika yaba haka yake don kada muje gida mu samu ba gaskiya bane yana da matsala ? Irin duban mamaki din nan ta danyi masa kafin ta rausaya kai tana fadin Allah ya tsareni da cutar daku idan na cuceku ina zan ganku ku yafe min ? Daga haka tasa kai ta juya ta zoma tafiya inda kayansu yake daga bayanta muryan Abubakar ne yake tsayar da ita a bayanta ta juyo ta dakata har ya tako zuwa inda take. Baiyi wani magana ba wayan hannunshi kawai ya mika mata bata karba ba kallonshi tayi cikin mamaki ki karba mu rika gaisawa idan nakoma gida. Kaita fara girgiza mashi tana fadin ka barshi bayan wanan alherin dakai muna mai yawa zaka kuma mika min waya ? Ko haka mun gode kasan girman taimakon da kaimuna a yanzu har in mutu ba zan manta da hakan ba a rayuwata zan kuma cigaba dayima addua a kullum kan wanan alherin. Haba dai ya fada yana dan dariya kafin ya saita kansa yana fadin wai zaman me kike a wanan kasan yanzu ko wasan nan ya kawo kuma nan ? Yanayin fuskanta ta sauya lokaci guda tana fadin na fadama kaddaran zaman mu nan sanadin mahaifinmu daya rasu shine zaman mu ya dawo nan kasan don bamu da kowa can Abuja da muke zaune. Nan kuma mun dawone a cikin yan uwa saidai duk da mun dawo cikinsu da zama har yanzu suna,,,,,, Yanda warre ? Wata bakar mace ta sa mata kira daga wajen saida kayansu hakan yasa ta juya da sauri da zumar ta wuce saka mata wayan yayi a cikin kwaryan dake rike a hannunta ya juya ya koma inda ya fito ta dan tsaya ta kalleshi kafin ta nufi wajen nasu saidai kafin takai tacire wayan cikin dabara ta kada a kasan lalitan dake rataye a wuyanta. Basu dauki lokaci a wajen ba taba da umurnin su shirya su soma hanya don ganin yadda mutane keta haramar bin hanya tunda wuri kada suyi dare. Lagos Nageria. Tafe yake cikin motarsa kiran kiran benz wace bai dade da mallakanta ba a yanzu sai kira,a dake tashi a cikin sautin malam Ahmed sulaiman kano. Yake dan bin kira,an shima kafin wayanshi ya dauki kara hamnu yakai yana rage sautin dake tashi na muryan malamin addini a Nageria don ya dauki kiran Saiba amaryansa daya gani din saman layi. Ya akayi Saiba i will call you bank idan na isa yanzu ina hanya ina tukine don Allah ? Sweet J kada ka kashe don Allah ka saurareni don bansan idan ka kashe wani ya rigani kiraka a fadama abinda bashi ba. Meya faru kuma ya fada cikin kaguwa da yaji kome ke bakinta a lokacin dama akan wanan Asmaun ne wallahi idan Asmau bata kama kanta dani ba sai na illanta mata rayuwa. Tseweeee ya tsoki yana fadin akan sakarcinku kika kirani ina saman hanya haka bashi bafa Sweet J mama mukayiwa laifi muka kifa mata abinci saman jikinta. Yana kokarin kashe waya yaji karshen furicinta a dan razane yace wata maman dai kodai Iya kike son kira kikace mama ? Mama dai ta tudun wanda ita nake nufi ta fada

Chapter 3 of 4