Share this page
" Daidai lokacin Dr Aryan ya kuma kiran wayan dan duk ya damu, Miqama Mansu wayan Lubna tayi. "Twinkle dinki nasan magana dake....." Ammy ne ke fadin. "Yi shiru baby gurl magen na baba me gadi ne amma zansa ya fitar da ita daga gidan tunda bakiso, maza amsa wayan....." Amsan wayan tayi tareda kangawa a kunni tana shashsheqan kuka, ijiyar zuciya ya sauke. "Jewel......" Batai maganaba taci gaba da kuka, Hakan yasa yace. "Am with yhu ba abinda ze faru dake kinji.....? " "Uhmmmm....." tace. "Oya stop crying Jor banasan jin kuka daga d most sweetest voice nd lovely in the hole earth. Oya laugh all the world want a laughing u telling me stories u calling me my Twinkle Okey......." Fashewa tayi da kuka cikin shagwaba tace. "Bakaga magen ba it Ugliest gata qatuwa am scared please hide me......" ta fad'a tana qara shigewa jikin Angle, kai kace za'a cinyeta. Yanda tayi maganan cikin shagwaba kaman wata er baby yasa besan sanda yayi murmushi ba. Cikin sigan kwantar da hankali yace........"Stop crying am with yhu okey jewel......" Lumshe ido tayi a hankali tasoma jin natsuwa, Kiran wayan daddy daya shigo wayan shine yasa shi cewa. "I will call letter daddy na kirana......." Da sauri ya yanke ya d'aga na daddy...... Yau hakanan taji wani bala'in kewan Aryan da batasan daliliba, tun wajen 10 ta kwanta amma ta kasa bacci har 11 se juyi take, wayan tane yayi ringing da sauri tayi picking takai wayan kunninta...... Cikin zolaya yace. "Rigima gurl baki bacci ba....." Turo baki tayi. "Niba rigima gurl bace....." Dariya yayi. "Can I ask....? " Tace. "Ehem am with you. " "How old are yhu.......? " "20years......" Ta bashi amsa Jinjinawa yayi. "You're 20 u are not dat small but why do you like crying and acting like a baby.......? " . "am the last born....." Murmushi yayi. "And the only gurl in d house right.....? " Shiru tayi, sekuma tace. "Yes......" Murmushi yayi. "Dat why you lyk pamper.....did yhu know what?? , I lyk ur childish behaviors...." Lumshe ido tayi. "Ya Atif kwana biyu bamu gaisaba...." . "Yana lafiya me tsoron mage...." Qara tasa cikin shagwaba. "Kabari banaso....." Cikin dariya yace. "Sorry matsoraciya, can I ask...." "Uhmmm. " "Are we still friends.....? " Jin tambayan tayi wani iri hakan yasa tace. "Ehem yes now, meya faru....? " "Bakomai I just ask...." Ya bata amsa. Kafin yace.. "Let sleep jewel Okey....? " Cikin shagwaba tace. "Nakasa bacci ne...." . "Okey if u can let's perform ablution nd pray 2 raka'at semu kwanta right...." . "Okey inama da Alwala...." Katse wayan yayi, tashi Mansu tayi ta shinfid'a praymet tuni Lubna tayi bacci dan d'akin Angle dabanne, Raka'a biyu tayi tayi addu'oi nan danan bacci ya dauketa, Bangaren Dikko se around 3 yayi bacci yanata nafilfili dan akwai shi da sallan dare. Washe gari cousin din Anita me suna Muhammad ya aiko Mansu tazo amma atifir tace bazata ba, Lubna na dariya tace. "Wai Mansu nikam meyasa baki kula samari duba fa duk in muka fita se samari sun biyoki amma baki kulasu, ko dai twinkle kikeso? ....." Wani murmushi Mansu tayi. "Lubna kenan, akwai wani abu a qasa amma ni dai abinda na sani banasan Twinkle kuma bazan ta'ba san shiba....." Murmushi kawai Lubna tayi zata kuma magana Mansu tayi saurin daga kiran Nadiya. . "Hello my sweet Nadee....." Ciki tayi da sauri dan fad'awa Nadiya abinda ke tafiya. Bangaren Aryan kam, zaune suke shida Atif magana Atif yake tama Dikko amma Aryan gaba d'aya wani tunani yakeyi hankalinshi baya kan Atif. Hakan yasa Atif ya ta'boshi firgigit ya kalli Atif. Murmushi yayi . "Abokina me kake tunani haka? ...." Shiru yayi, Atif ne yace. "Ko dai tunanin jewel kakeyi....Abokina na fadama san yarinyar nan kakeyi amma kaqi yarda inba hakaba kaida ba ruwanka da mata amma lokaci d'aya wata ta shigo rayuwarka ta canza ka, kai anya yakamata koma wacece ka nemota ka bayyana mata soyayyanka domin na tabbata alkhairy ce ita a gunka tunda gashi daga shigowanta harta fara canza mana our Pride fellow....." Shiru Aryan yayi yana tunanin maganganun Atif. Mimi queen. 2022-10-01, 4:15 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT* _Daga Alƙalamin_🖊️ Haleema Isah (Mimi Queen) Marubuciyar: Rayuwa Sai dakee. Labarina. Barrister Shulaifat. Son Zuciya. Nisful hayat. And now on _MANSURAT_ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A* _Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._ https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa _____________________________________ Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_ Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance. Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁. Bismillahir rahmanir raheem. 27&28. Aiki sukeyi a kitchen ita da Lubna wayan tane yahau ruri ganin twinkle ne yasa tayi saurin yin picking.... "Hello twinkle...." ta fad'a a shagwabe, Ijiyar zuciya ya sauke "Jewel can I ask...." Murmushi tayi. "Uhmmm...." "Are we still friends....? " Juya ido tayi. "Ehem meyasa kake tambaya.." ". Bakomai..." ya fad'a kafin yace. "We talk letter...." Ya katse wayan, shiru tayi tana wani irin murmushi kafin a hankali ta lalubi numban Nadiya.... Aryan dake zaune a falo shima shiru yayi yana kallon screen din wayan, ta'boshi akayi hakan yasa yayi saurin d'agowa, murmushi Farhan yayi. "Ya....Dikko tunaninfa ko ka fad'a sone...? " Hararanshi Aryan yayi tareda miqewa yana fadin. "Let go jor...." Jerawa sukayi suka fice zuwa masallaci. ****** Yau Friday kuma yau ya rage saura sati biyu bikin Aunty Angle wanda yau saura kwana biyar su Mansu su koma kaduna........ Message din Dikko ne ya shigo wayanta.... "```Hey Jewel..."``` Reply ta mishi. "```How u doing? ...."``` Lumshe ido yayi kafin ya rubuta. "```Not well, jewel did yhu know something...."``` ```"A'a.....``` Ta bashi amsa. . ```"Am Shy bazan iya fad'iba....``` Murmushi tayi kafin ta rubuta. ```"Just feel free am ur jewel Ok...."``` Shima murmushin yayi kafin ya rubuta. "```Am feeling something about yhu...."``` . "```Oh what is it....? "``` Ta tambaya. "```I don't know.."``` Ya bata amsa, kafin cikin barkwanci tamai reply da. "```Ayya Allah sarki Twinkle...."``` Tana turawa, taga ya kirata dauka tayi tana dariya. Tsaki yaja. "Jewel banasan iskanci Allah sarki for wot...." Dariya takeyi bata bashi amsaba, katse wayan yayi kafin ya rubuto mata. "```am feeling lyk I....LUV..YOU.....uhmmm please Jewel trust me I wound cheat u, ban ta'ba yarda da kowacce mace a duniya ba seke Jewel I don't know why kuma bansan kiba ban ta'ba ganin kiba, amma zuciyata da rayuwata sun yarda dake sun aminta dake har nakejin I can't do with any lady except u saboda dake kadai na saba, jewel I hate females amma bansan meyasaba nakejin ke kin fita daban a cikinsu inasanki sosai jewel...I Luv yhu with oll my system organs till eternity, please don't reject me......"``` Wani uban ihu tasa tana gama karantawa, wanda yasa aunty Angle fitowa daga bayi da sauri, Tana tambayan. "Lafiya Mansu...." Tashi Mansu tayi dan murna tarasa ina zatasa kanta, yau haqanta yacinma ruwa yanzu zuciyan Aryan na tafin hannunta se yanda taso zatayi dashi, . "bakomai Aunty...." Ta fad'a tareda ficewa falo.. Kan kujera ta zube tana dialing numban Nadiya.... Nadiya na dauka Mansu cikin murna tafara fadin. "I luv yhu so much Nadee, thank for ur advice shawarki tayi aiki Dikko ya furtamin kalman so yau am very very happy today, yanzu zuciyan Aryan na tafin hannuna am so excited zanyi amfani da wannan daman na rama duk abubuwan da yamin sena maidashi abun tausayi sena garashi kaman taya....." Shiru Nadee tayi tana sauraran Mansu, jin Nadiya tayi shiru yasa Mansu cewa. "Ya naji kinyi shiru kuma ko murna bakiyi.....? " Huci Nadiya ta sauke. "Mansu ni yanzu ke nafi tausayi....." Tsaki Mansu taja. "Tausayi kuma... Ni bansan iskanci Nadiya nice abun tausayi yanzu ko Dikko.....? " . "Wallahi kece Mansu...ke nafi tausayi saboda ke mace ce zuciyanki me rauni ce ba lallai bane duk ki iya cika wannan burin da kika d'auka akan DrAryan ba saboda zaki iya fara sanshi kuma kinga daganan bazaki iya mai komai ba saboda kina sanshi kinga......." Da sauri Mansu ta katseta... ....."Dakata Nadee wallahi kin bani mamaki da kike wannan tunanin akaina ke kin sanni kinsan yanda na tsani Aryan bazan ta'ba iya san shiba amma shine kike irin wannan maganan...." Nadiya ce tace. "A'a Mansu kindai san zuciya batada qashi ko kuma koda yaushe d'an adam canzawa yakeyi...." "To ni insha Allah bazan canzaba akan wannan wawan kuma kiji sena cika qudirana a kanshi insha Allah...." Murmushi Nadiya tayi. "Allah yasa...." Katse wayan Mansu tayi ranta duk a 'bace, miqewan da zatayi sukayi ido hudu da Lubna dake tsaye kofar kitchen wanda taji komai tun daga farkon fara wayan Mansu..... . "Yanzu Mansu dama Ya Dikko shine Twinkle.....? " Da sauri Mansu ta qarisa tareda rufewa Lubna baki. "Please kiyi shiru kada wani yaji..... " Ture hannunta Lubna tayi. "Ni rabu dani tunda har zaki 'boyemin to sena fad'a kowa yaji....." Da sauri Mansu ta rungumota....."haba babyn Noor kiyi hakuri ba haka bane akwai daliline shiyasa....." Nan Mansu ta zauna bata 'boyewa Lubna komaiba seda ta fad'a mata, Dariya Lubna tayi. "Abun naku gunin ban sha'awa kaman a Novel kinsan yawanci da fad'a ake farawa...". Duka Mansu ta d'akawa Lubna cikin wasa Lubna tace. "Wannan alwashi haka ammafa Nadee tayi gaskiya daga baya fa reshe ze iya juyewa da mujiya....." Hararan Lubna tayi. Kafin Lubna tace. "Qila shiyasa ma baki kula kowa har Ya Muhammad saboda kinada Secret Love dinki a 'boye......" Pillow Mansu ta d'auka tayi kan Lubna wanda da gudu Lubna tayi ciki tana dariya, Mansu ta bita da gudu itama.... ***** Sosai Aryan ya shiga damuwa domin tun randa yama Mansu message din yana santa bata qara daukan wayan shiba yau kwana biyu kenan, kuma koya mata message ba reply duk ya shiga damuwa domin ba kad'an yakejin san Jewel a ranshi ba, Atif kam se shawara yake bashi. Sunata shirya shiryen komawa kaduna harda Ammy da Lubna domin jibi flight dinsu ze tashi. Anyiwa Aunty Angle lallen maiduguri me kyau da gyaran kai haka Mansu da Lubna qannin Amarya sosai suke sheqi abunku da fararen fata. Yanzu sam bata daukan kiran Aryan hakanan takeso taja mishi aji. """" Gobane tafiyansu Kaduna yau sunje sunyi sallama da en uwa sunyi siyayya sunsha yawo sosai suka gaji, Bayan magrib. Wayan Mansu ne tayi quwa, ganin twinkle yasa Lubna da sauri tayi picking, Mansu data fito daga bayi d'aure da towel iya cinya da sauri tace. "Wayace ki daukan min waya....? " Da sauri Lubna ta katse wayan, tana fadin. "Yi hakuri Aunty...." Cikin shigan lallashi Mansu tace. "Dan Allah Lubna in mukaje kaduna karki wani abu dazesa Aryan ya gane kece Lubna ko kiyi abinda zesa ya gane nice Jewel please dat's our secret...." Cikin zolaya Lubna tace. "Ok Maa...." Daidai lokacin kiran Aryan ya sake shigowa.... Tsaki Mansu tayi. "Miqomin wayan ya zanyi tunda kin riga kin dauka...." Miqa mata wayan tayi tana fadin. "Yarinya er gidan miskili man kina wuta ina binki da fetir..." Bata kula iskancin Lubna ba picking tayi tareda kai wayan kunninta,. "Helloooooo....." Ta furta a sanyaye. . "Hummmm....Uhmmm...Jewel have I done something wrong please tell me with inaji kaman nayi kuka...." Cikin shagwaba tace. "Bakomai fa..." ".Jewel ko dan nace inasanki ne shine kike jin haushina....? " Girgiza kai tayi. "Uhmmm...uhmmm..." . "To ko baki sona ne Jewel shiyasa kikeso ki yanke alaqa dani...? " Qara girgiza kai tayi. "Uhmmm...Uhmmm.." Huci ya saki a marairaice yace. "To meye laifina please Jewel tell me, wat my fault dan nace inasanki tell me pleaseeee......? " . "Twinkle...." Ta kira sunanshi. Bud'e idanuwanshi yayi tar ya saukesu kan qofar office dinshi. . "Na'am...." ". Twinkle nima inasanka sosai sedai abu d'aya nake tsoro....." Da sauri yace. "What jewel tell me mekike tsoro...? " "Twinkle inajin tsoro kada kaganni kace ban makaba baka sona ba irina kake soba....." Katseta yayi da sauri. "Jewel inasanki inasanki sosai zan iya rayuwa dake duk yanda kike, zan rayu dake a ko wani hali kike jewel...." Murmushi tayi. "Kace zaka soni a yanda nike kuma ko wacece ni zaka soni....? " Da karfi kaman wani wanda wutar santa ke cinshi yace. "Yes jewel I said it and I will always said it, inasanki a duk yanda kike kuma ko wacece ke zan rayu dake koda ko ace ke makauniyace to kam zan kasance dan jagora a gareki, idan kuma ke gurguwace to nizan dinga d'aukanki inmiki duk abinda kikeso, domin inasanki kuma na aminta dake ke kadaice 'ya macen da nake so kuma na kejin zan iya rayuwa dake fatana d'aya ki bayyana kanki a gareni nikuma a ranan zan tura magabatana gidanku a daura mana aure, burina be wuce ki zama tawa har abada ba jewel please inaso naganki I want u too be mine forever....." Murmushi tayi. "Allah sarki Twinkle dina, niba gurguwa bace kuma niba makauniya bace inada lafiyana sannan zamu hadu very soon insha Allah zan bayyana maka kaina, nima inasanka sosai my Twinkle...." Huci ya saki. "To when nifa na kosa please ki fad'amin...." Murmushi tayi. "Ai zanzo bikin Angle dinku, find me inkuma ka kasa shikenan se sanda naga dama zamu had'u...." Cizan lips din kasa yayi. "To shikenan ni kuma zanyi trying insha Allah....." . "Twinkle lemme need my self...." Huci ya saki. "Am not tired of hearing ur voice Jewel amma shikenan zan kiraki kafin kiyi bacci...." . "Okey...." ta furta kafin ta cire wayan a kunninta. Dariya Lubna tayi da takejin su tun d'azu. "Lovers....." Mugun harara Mansu ta watsa mata. Wani irin farin ciki Aryan yake ciki, ji yakeyi yafi kowa murna a duniya yanzu, dama haka akeji in ana soyayya. Around 10 ya gama komai, da wuri ya shiga d'aki dan yayi waya da Mansu sedai ya kirata sosai bata d'auka ba dan tayi bacci tun 9 dan tayi mugun gajiya kuma gobe akwai hawa flight, hakan yasa ya mata messages...... Yau ne zasu juya kaduna tana tashi taci karo da message din Aryan. "```Only my jewel I call no answer nasan kuma u want be happy 4 not hearing my voice, me too naji bacci but anyway we will talk, 2 day is chocolate dream bye and smile my jewel...."``` Murmushi tayi, kafin tamai reply.... "```And morning my Twinkle my one nd only cute, please hove u r fyn nd continue be fyn, missed ur call means I missed night happiness, nd I will continue be missing u, till d time u see my Message and call. Nayi bacci da wuri nasa phone dina a silent dat why srry. "``` Lokacin yana shirin fita zuwa asibiti, be mata any message ko call ba, se bayan yagama duba patient. Sukuma lokacin suna cikin mota zuwa airport, taga message dinshi. "```I miss you like am crazzy, inasanki sosai fiyeda tunanin me tunanin and I need u to feel my love in your soul...."``` Reply ta mishi. "```I swear I feel it deep inside of me....I lose my control...."``` Kiranta yayi amma batayi picking ba, domin lokacin suka isa airport. Basu jimaba flight dinsu ya d'aga zuwa Kaduna..... Mimi queen ✍️. 2022-10-02, 10:04 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT* _Daga Alƙalamin_🖊️ Haleema Isah (Mimi Queen) Marubuciyar: Rayuwa Sai dakee. Labarina. Barrister Shulaifat. Son Zuciya. Nisful hayat. And now on _MANSURAT_ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A* _Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._ https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa _____________________________________ Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_ Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance. Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁. Bismillahir rahmanir raheem. 29&30. Jirgin su Mansu na sauka lokacin motocin su Farhan, ya iso airport din burin shi d'aya yayi ido hudu da Mansun shi. Suna fitowa daga jirgi, Angel ne ta hango Farhan da Mommy da sauri tace. "Gasu mommy....." Da gudu Mansu tayi gaba tana karisawa ta fad'a jikin mommy tareda sakin kuka....."I missed you more mommyna....." Qanqameta mommy tayi dan itama tayi kewan daughter dinta sosai, jikin Farhan Angle ta fad'a ta rungumeshi sosai Janye Mansu mommy tayi tana fadin. "Is OK baby gurl...." Karisawa tayi suka rungume juna da Ammy cikin farin ciki, nunawa Mansu tayi kaman bataga Farhan ba shima ko seya basar..... Riqo Lubna mommy tayi suka nufi motoci. Mommy da Ammy mota daya suka hau se Angle da Farhan, se d'ayan motan Mansu da Lubna, ahaka suka nufi gida........ Bayan sunyi parking kowa ya fito se lokacin Mansu tadubi Farhan cikin mamaki. "La Ya Farhan dama dakai akaje airport.....? " Lubna ce tace. "Dama ke baki ganshiba se yanzu...? " D'aga kai tayi. "Eh idona ya rufe da shauqin san ganin mommyna ita kadai na gani....." Ta'be baki yayi yayi gaba, da gudu tabi bayanshi.... "Brother tsaya ka rungumeni nayi kewanka sosai....." Be kulata ba yayi gaba, dansu mommy sunyi ciki abinsu..... Yana gama shiga falon ta janyo hannunshi baya. "Ya Farhan ko kewata bakayiba ko....? " Kwafa yayi. "Meyasa zanyi kewanki ni dama baki dawoba kinyi zamanki acan kawai, ki samu wani Old man ki aura kawai mu huta..." Baya taja da sauri tareda dafe kirji cikin muryan kuka tace. "Ya Farhan ni kake cewa dama nayi zamana acan, kasan irin kewanka da nayi kuwa har Doll na siyo maka kullum senayi magananka koba hakaba Lubna....? " Lubna dake dariya ta d'aga kai cikin dariya.... Kafin Mansu taci gaba. "Amma shine zakace in samu wani tsoho in aura kenan ka fasa aurena ko....? " Ta had'a kai da bango ta fara kukan qarya. Kai ya dafe dan ya gaji da shirmen Mansu hakan yasa, ya fincikota..... "Oya hug me baby gurl I really really really missed yhu alot my tiny sister...." Da sauri ta rungumeshi tana fadin. "Nima nayi kewanka sosai my huge bro...." Dariya sukaba Lubna sosai dan ita burgeta sukeyi. Mommy ce ta sauko tana fadin. "Farhan barmin yarana suje su huta su fito suci abinci, Lubna maza jeki huta dena biye musu....." Ciki Lubna tayi da sauri tana dariya. Bayan duk sun huta suka fito dinning suka zauna sosai sukaci abinci. Ana haka daddy ya shigo da gudu Mansu ta tashi ta fad'a jikin daddy.... Rungumeta yayi sosai. "Princess dita kin qara kyau, ruwan maid ya amsheki...." Sinnar dakai tayi qasa tana murmushi, Kafin yace. "Anata zuwa neman aurenki sosai princess...." Da sauri ta d'ago, murmushi yayi. "Nidai nace suyi hakuri ba yanzu zanyiwa babyna aureba akwai lokaci...." Cikin murna tace. "Yawwa daddyna..." ". Princess ko akwai wanda kikeso ki fad'amin se a had'a ayi tare da Angle...." Da sauri tace. "Bakowa daddy na." Murmushi yayi. "Yawwa kada ki kula kowa kinji akwai lokaci yanzu ban shirya miki aureba dan haka karki fara soyayya yanzu kinji ko..." Cikin jin dadi tace. "To daddyna..." Murmushi kawai mommy tayi domin duk abinda suke cewa dukkansu sunaji, Seda daddy ya shige ciki bayan sun gaisa dasu Ammy, sannan Farhan ya dubi mommy. "Yanzu mommy wannan yarinyar ne daddy zece baze mata aure yanzuba kuma kinaji...? " Cikin tsiwa Mansu tace. "Ya Farhan to meye matsalanka da aurena kai waya matsa maka qato ma dakai...." Murmushi yayi. "Ai ni kinsan akwai wani qaton a gaba nane shiyasa amma....." Duka Angle ta d'aka mishi. "Ya akwai mommy da Ammy kar kai rashin kunya...." Mummy nunawa tayi kaman batasan me suke cewaba sema tashi da tayi ta nufi gurin mijinta, Ammy kam dariya kawai tayi. . "Eh naji koma meye amma dai nasan Mansu tafara soyayya inba hakaba to ta fad'a mana waye Twinkle....." Da sauri Mansu ta d'ago cikin mamaki jin abinda Farhan yace, kwalo ya mata.... "Lol...." Duban Aunty Angel tayi, da sauri Angle tace. "Bani bace....." Miqewa tayi tareda marairaice wa. "Ya Farhan please waya fadama ko Lubna ce....? " Da sauri Lubna tace. "Bani bace wallahi. " A fusace ta dauki qaton plate tayi kan Farhan . "Seka fad'amin waya fadama, ko in buga maka.." Tashi yayi da gudu yayi ciki ta bishi da gudu..... Seda ya wahalar da ita sannan yace. "Text message dinshi na gani dazu wai baki picking wayan shiba yanata kewan muryanki....." huci ta saki. "Ya Farhan please banaso ka kuma kiran sunan twinkle a gidan nan please...." Ta marairaice. Tsaki yaja. "Munafuka meyasa kika 'boyemin..." . "Zan fadama komai Yayana amma sekamin alqawari kaji please...." ."Okey nayi fad'amin..." . "ba yauba...." Ta fad'a tareda ficewa da gudu, murmushi kawai yayi yabi bayanta. Ranan kwana sukayi fira su duka barinma yau ga Farhan uban surutu, mommy tacewa Ayya se bayan biki Mansu zata koma, Unin ranan Aryan be leqa gidanba amma sunyi waya da daddare da Jewel..... ****** Yau itada Lubna da Nadiya sukaje suka amso dinkin ankunan su gaba daya kusan kala takwas da mommy ta bada d'inki nasu su ukun, dan yanzu an hana Angle fita. Tuni Ya barrister ya turo da Invitation card (Sunan da Mansu take kiranshi dashi kenan hakan yasa kowama yake kiranshi da hakan, dan har ita kanta Angle takan kirashi da Ya barrister, amma asalin sunanshi Barrister Fu'ad Nasir...) Tun a mota suketa faman waya da Twinkle, har suka iso Driver na ijiye su dukkansu en matan suka fito, gaba Mansu tayi tana wayan tana dariya ta barsu Lubna zasu dauko d'inkunan. Daidai lokacin da yake tambayanta, yaushe zatazo biki dan an fara zuwa. Ta bud'e baki zata bashi amsa kenan taji ta bangaje mutum, Wayan dake kunnin shine ta fad'i kasa, a firgice ta d'ago Yana sanye da sky blue din hoodie yadi yayi kyau matuqa Mansu bata ta'ba ganin kyanshi irin rananba..... Wani irin kallon tsana yake jefa mata da sauri a rud'e ta duqa ta dauko wayan nashi tamiqa mishi... Tsaye yayi yana jefa mata wani mugun kallo, a hankali yasa hannunshi ya zaro sim card dinshi dan tunda Mansu ta ta'ba wayan yaji ya tsani wayan gaba d'aya.... Yana zare sim card din yayi gaba yabar mata wayan a hannunta, jujjuya wayan tayi iPhone 14 ce sabuwar shigowa wayan data tasamma miliyan biyu, wani irin mugun haushin shine ya kamata, fad'in ranshi da jiji dakai d'inshi da nuna isa sunyi yawa, Hakan yasa tana shiga falo ta ijiye wayan kan center table tayi sama abinta, domin ita kam ba abinda zatayi da tsiyar Aryan. Ranshi 'bace ya nufi parking lot, daidai lokacin Nadiya ke cewa. "Lubna kiyi sauri kinsan anjima zamuje raba IV...." Chakkkkkkk...... Aryan ya tsaya jin sunan da Nadiya ta kira wato Lubna, tunani ya farayi, Ra'bawa su Nadiya sukayi suka wuce ta gefenshi ido ya bishi dasu har suka shige. Da sauri wata zuciyan tace mishi. "Ina hakan baze yiwuba wannan ba Lubnan Jewel bace, ai suna linzamine, sunan sune iri d'aya..." Kad'a kai yayi yama motanshi key, ya shiga. Kasancewan Angle batada wasu qawaye a Nigeria, dan ita karatunta duk a waje tayisu yasa komai Mansu keyi se su Nadiya da Lubna dake tayata, dan Nadiya ma ta dawo gidan se bayan biki zata koma. Haka Ayya itama ta dawo gidan. Tuni en uwa daga ko wani 'bangare sun fara zuwa, gida ya cika maqil se bidiri akeyi...... Zaune Mansu take a haraban gidan suna waya da Twinkle se dariya takeyi sosai, Farhan ne ya fito tsaki yaja. . "Yarinyar nan ta kwance akan Twinkle dinnan..." Gaba yayi, yana zuwa parking space yaga Aryan tsaye bakin mota se bude qofan motan yakeyi yana rufewa, Se dariya yakeyi yana wani irin annashuwa da ba koda yaushe kake ganinshi a cikiba dan da alama soyayya yakeyi, Ta'be baki Farhan yayi..."Shima wannan ya kwance akan wata...." Da sauri wata zuciyan tace. "Ko tare suke waya....? " Dafe kirji yayi yana girgiza kai..."Ina it's impossible baze yiwuba..." Wata zuciyan ne tace. "To ka bincika kagani...." Cikin sand'a ya karisa ya 'boye bayan wata mota inda yana jiyo muryan, Aryan yana fadin. "Saying I love you can't explain irin kaunar da nake miki, I don't know how to explain but alhamdulillah u can understand more I love yhu more Jewel...." Riqe baki Farhan yayi. "Yaushe miskilin nan ya fara soyayya haka?..." Da gudu ya rarrafa ya koma gun Mansu ya la'be a bayan flower yanda ze jiyota. Murmushi tayi me sauti. "Twinkle kenan naka kadai ka sani ko, bakasan nawaba I love you kaman nayi hauka...." Cikin mamaki yana tunanin, To meya canza wa'innan dutsunan lokaci daya kowa ya fara soyayya?. Kowama yayi daidai lokacin, Aryan ke fadin. "Inasanki sosai fiyeda tunanin me tunani and zan cigaba da hakuri zan jira har lokaci yayi in ganki, in rungumeki sosai sannan naita miki waqa, ke kuma kiyita min shagwa'ba and u be calling me ur Twinkle, I love you plenty plenty Jewel...." Qafan Farhan ne ya fara rawa, kenan dama Aryan ne twinkle?, dama soyayya

Chapter 6 of 14