Share this page
komai yau zamu fayyace musu abinda muka b'oye musu muna jiran lokaci, to yau lokaci yayi..... " Murmushi Ayya tayi. "Allah nagode maka daka nunamin wannan rana da raina ban mutuba za'a fad'i wannan sirrin da muke b'oyewa shekaru da dama...." Cikin rashin fahimta Aryan yace. "Daddy wani sirrine wannan....? " Mommy ce ta harareshi. "Yi ma mutane shiru..... " Maida baki yayi ya tsuke, Mansu kam idanta na runtse in banda hawaye ba abinda ke sintiri bisa kuncinta, a cikin zuciyanta kam " Innalillah wa'innan ilaihir raji'un. " kawai take maimaitawa. Daddy ne ya nisa. "Uhmmmm. " Kana yace. "Shekaru tara da suka wuce lokacin Mansu nada shekaru goma sha uku a duniya, muka zauna nida Ayya muka yanke hukunci dukkanmu bamuda buri daya wuce muga mun had'a Mansu da Aryan aure, sedai su sun tsani junansu hakan yasa muka yanke shawara a wannan lokacin muka nemi dangin mahaifin Mansu muka d'aura musu aure batareda sanin suba dan lokacin Mansu ko hankalin kanta bata saniba, hakan yasa muka maida Mansu gaban Ayya inda Aryan yakeyi da niyyar in suka taso tare qila su fara san junansu duk randa suka bud'e baki sukace sunasan juna semu bayyana musu wannan sirrin da babu wanda yasani daga ni se aminina Alh. Abubukar da wakilan Mansu se mommynku da Ayya, Amma se gani mukayi tsanan kullum qaruwa yakeyi hakan yasa muka jinkirta ba tareda mun sanar dasu wannan sirrin ba mun qudurta ko za'ayi shekaru dubu d'ayanku be bud'e baki yace yanasan d'ayaba bazamu fada mukuba, Shiyasa na haramtawa Mansu kula kowa kuma nima bana amsan duk wanda yazomin da maganan neman aurenta. Munyi matuqar farin ciki da Dikko da kanshi ya bud'e baki yace mana yanasan Mansu kuma yayi nadaman duk abinda yayi a baya, Princess ki gafarcemu munsan bamu kyauta mikiba amma ki fad'a mana idan bakisan Dikko se a raba auren dake da Dikko duk yaran mune bazamu tauye miki haqqinki ba a matsayin ki na yarinyar mu......" Mansu kuka takeyi na fitan hankali dan gaba d'aya ba wanda bejin kukanta, tarasa ina zatasa kanta . "Allahumma ajirni fi musibatin wakhlifni khairan minha, innalillah wa'innan ilaihir raji'un....." Shine abinda take fad'a cikin ranta tana kuka, cikin kuka muryanta na cracking tace. ".... Da...ddy.....har abaaa...da....ni me biyayya ce....a gareku......bazan ta'ba bijirewa umarnin kuba akoda yaushe za'bin ku shine nawa..... " Ba wanda beji dadin abinda ta fad'a ba, Dikko kam ya rasa ina zesa kanshi saboda murna baki har kunni, Farhan kam cike yake da tausayin Mansu haka Lubna. Cikin jin dad'in magananta daddy yace. "Mungode sosai Mansu Allah muku albarka gaba d'ayansu yabaku zaman lafiya, zanyi magana da mommynku se asa ranan tarewan naki kinji ko.....? " Batace komai ba taci gaba da kuka, nan daddy yayi addu'a ya rufe taro da addu'a ya tashi. Da gudu Mansu tayi d'aki tana kuka, kowa ya bita da kallon tausayi Aryan ya bita da wani irin murmushi dake qunshe daso ji yakeyi yau yafi kowa murna ya mallaki Jewel dinshi, da sauri ya tashi yafice cikin murna yana dialing numban Atif, Shima da kallo suka bishi Farhan ne ya tashi jiki a sanyaye ya rasa murna zeyi ko baqin cikin an quntatawa Mansu dan yana matuqar tausayin ta, Farhan na ficewa itama Lubna tayi d'akin aunty Angle inda Mansu ta shige, suka bar mommy da Ayya kawai. Tana kwance kan gado tana kuka sosai, d'agota Lubna tayi. "Ki dena kuka Mansu..." Fad'awa tayi jikin Lubna. "Lubna na shiga uku dama ni matar aurece dama Dikko shine mijina, wata zuciyan mara adalci na rad'amin su daddy basu yimin adalciba da suka min aure tun ban mallaki hankalin kainaba batareda sani naba dan sunga ni marainiya ce amana ce a gunsu shiyasa sukamin haka ga Aunty Angle nan meyasa basuyi mata hakaba ko dan ni basu suka haifeni ba..... Amma zuciya me adalci na fad'amin cewa aisu ma matsayin iyayene a guna kuma suna ganin sun isa danine shiyasa kuma ai inasan Aryan kawai inaso in koyamai hankaline..... " Tayi murmushi. "Huuummm Lubna zuciya ta biyu tayi gaskiya tabbas su daddy sunfi qarfin haka a guna danko yanka namana sukayi suka bani inci banda bakin magana, kuma inasan Dikko sosai kawai dai ban shirya rayuwa dashi yanzu bane seya gane kurenshi amma yanzu banda freedom komai nayi da nufin d'aukan fansa ni zunubi zan samu a gurin ubangiji na, Lubna banida hujja Dikko yayi nasara a kainaaaaa.......... " Ta fashe da kuka..... Itama kuka Lubna takeyi sosai ta kasa lallashin Mansu, Mommy ce ta turo kofa hakan yasa Lubna sauke Mansu kan bed ta fice, karisawa mommy tayi wacce da alama itama taci kuka, ta d'ago Mansu dake kuka dan bata sanma mommyce ta shigoba, Kan jikin mommy ta fad'a ta qara sakin kuka, shafa yalayalan gashinta mommy tayi. "Baby gurl.... " Kuka taci gaba dashi, . "Mansu na kiyi shiru kinji am a woman i can feel what u're feeling nasan bamu kyauta miki ba amma kiyi hakuri kinji baby na....." D'ago kan Mansu tayi da idanunta ke rufe tana kuka sosai, share mata hawaye mommy ta soma tana zubda hawaye a sanyaye tace. "Mansu u're my daughter inasanki sosai fiyeda tunaninki kuma nasan na isa dake, amma zan roqeki wani alfarma badan ban isaba, Mansuna ki temaka kiso Dikko ki rayu dashi ki temaki rayuwarshi ki manta da duk abubuwan da suka faru tsakaninku a baya ku shinfid'a sabuwar duniya Dikko na buqatarki Mansu, nasha wahala a haihuwanshi sosai yafi wata shida baya motsi seda yafi shekara d'aya a cikina sannan na haifeshi kuma dazan haifeshi aiki akamin bansha zan rayuba shima yasha wahala bamu d'auka ze rayuba inasanshi sosai Mansu inajin tsoron in rasashi nafi qaunarshi fiye da Farhan da Angle amma nafi sanki dashi domin qaddaranku d'ayane Mansu, ina matuqar tausaya miki tun kina ciki Allah ya d'auramin sanki, tun kina ciki nake roqon mahaifiyarki ta bani ke bamu ta'ba sanin cewa ashe a hannuna zaki tasoba nizan raine kiba. Please ko badan niba ko dan soyayyan da Dikko yake miki ki temaka ki rayu dashi ki bashi farin ciki inaso yanda kuka taso tare kuqare tare pleaseeeeee......... " Rungume mommy tayi sosai dukkansu suna kuka...... ********* Da kyar Mansu ta dawo yanda take amma sam taqi yarda ta koma gidan Ayya dan bataso ta had'u da Aryan tana ganinshi. Yau daddy ya kira Dikko, bayan yazo yake ce mishi. "Munyi magana da mommynku tace tanaga se nanda wata d'aya Mansu zata tare, domin itama tanaso ayi babban biki a tarewan 'yarta kuma akwai abubuwan da takeso tayi, kaima inda abinda kakeso kayi kaje kagama kafin lokacin sannan ka za'bi gidan daya maka inda zaku zauna a cikin gidajena...... " . "Toh.... " kawai yace. Ya tashi ya fice jiki a sanyaye rai duk a 'bace, main falo yaje ya zauna ko ze ga fitowanta domin yanzu koya kira wayanta baya zuwa duk ya shiga damuwa, amma yanajin matuqar dadi idan ya tuna itad'in matar shice. Sedai harya qaraci zamanshi ya tafi bata fitoba. Yau Nadiya ta kawo mata ziyara. Suna zaune kan gado a d'aki, Duban Mansu tayi ganin tana walwala a fuska kaman bakomai a ranta yasata cewa. . "Matar Aryan yanzu kin sadaqar kenan kin miqa wuya.... " Murmushi me ciwo tayi "Nadee mommy ce da kanta ta roqeki inso Aryan in rayu dashi wallahi ko bana sanshi zan fara koyawa kaina sanshi balle kuma inasanshi kawai dai zanja mishi aji ne baze gane da wuriba.... " Dariya Nadiya tayi. "Lallai wallahi nayi mamaki dajin cewa dama can Aryan mijin kine duk zagin da kika mishi yanzu kin samu zunubi.... " Dafe kai tayi. "Itama dai Aunty Angle taci dariya haka ta kirani tana tamin iskanci yanzu wai ashe matarshi ya dinga cewa mahaukaciya kinga aunty Angle akwai mugunta, Amma kinsan meye Nadee ai ubangiji baze kamani da laifin da nayi cikin rashin saniba.... " Murmushi Nadiya tayi kafin tace. "Kinsan d'azu muka gama maganan da Sweet Atif kinsan meyace wai dama tun tuni an fad'a muku ku mata da mijine kuna cikin tsanan nan se muga yanda zakuyi.... " Da sauri Mansu tace. "Ai wallahi dase an raba auren kinsan ko meye ake kira da tsana.... " . "Hummm tsana kam soyayyace me karfi domin kam inya juye ya koma soyayya se yaba kowa mamaki, Domin kam dama duk inda kukaga tsana me tsanani tayi yawa to qasanshi qunshe yake da soyayya me qarfi dan ga babban alama nan mun gani..... " Nadiya ta fad'a cikin zolaya. Duka Mansu ta d'aka mata. Please manage, kunsan an mana rasuwa daurewa nakeyi ina muku typing. Taku koda yaushe. Halima Isah (Mimeey). Matar Abdul ce ✍️. 2022-10-12, 9:00 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT* _Daga Alƙalamin_🖊️ Haleema Isah (Mimi Queen) Marubuciyar: Rayuwa Sai dakee. Labarina. Barrister Shulaifat. Son Zuciya. Nisful hayat. And now on _MANSURAT_ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A* _Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._ https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa _____________________________________ Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_ Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance. Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁. Bismillahir rahmanir raheem. 41&42. An sanar da tarewan sosai dan en uwama duk sun fara hallara, Sosai Mommy ke ba Mansu kulawa tana gyarata, wacce ita Mansu ba abinda takeyi kullum se kuka, 'Bangaren Aryan kam ya shiga cikin matsananciyar damuwa dan sam tun ranan da aka fad'a musu cewa su ma'aurata ne be sake ji ko ganin Mansu ba duk ya shiga damuwa. Tuni an gyara gidan Daddy dake Gwamna road wanda dama sabone an zuba kaya d'an ubansu tarewa kawai ake jira. Mommy tace se Aryan yama 'yarta lefe hakan yasa, yasa aka hado mishi kaya daga Dubai d'an ubansu set biyar kusan akwatuna 30 masu bala'in tsada ga wanda mommy ta had'o mata daga Madina kusan set uku guda 20, se santin kayan akeyi Mansu dai ba bakin magana. Aryan yaso ayi event masu yawa, amma mommy ta hana ganin za'a takurawa Mansu dan haka walima da saukan alqur'ani kawai aketa sha. Tuni en uwan Abban Mansu daga Cameroon sun zo da dama hakan yasa gidan ya cika ga en uwan daddy da saura en uwan mommy. Angle ma taso tazo daga England amma shari'a ne daya mata zafi yasa ta fasa zuwa dan ta fara aiki tuni. Yau saura kwana biyu tarewan. Yau dai Aryan ya kasa jurewa yana office ya tashi ya zuri key ya fice. Gidan mommy ya nufa. Ta qofan baya yabi ya shige wanda ya sadashi da matattakalan benen, hakan yasa da sauri ya haye dan yanada tabbacin Mansu na d'akin mommy. Mansu na kwance kan bed ta lumshe ido bacci takeso tayi amma ta kasa tunane tunane takeyi kala da kala, hawayene ke sintiri bisa kuncinta. Ji tayi an bud'o kofan hakan ya qarasa ta lumshe idanu. Jingina yayi da jikin qofan yana sauke ijiyar zuciya ji yayi kaman an d'auke mashi duk wani damuwa dake ranshi, Kamshin turaren daya ziyarci hancinta ne yasa da sauri ta bud'e ido, a razane ganin Aryan yasa ta miqe da sauri. "Meya shigo dakai d'akin nan kafita ko ni in fita in bar maka d'akin.... " Murmushi yayi. "Mijin naki kike kora.....? " Had'e rai tayi ta kauda kai, ganin bashi da niyyar fita yasa ta nufi qofan da niyyar fita, Key yasa ya kulle qofan ya zira key din a aljihu ya qarisa kan bed ya zauna, Murd'a kofan tayi jinshi a kulle yasa ta juya tana kallonshi duk ta qulu. . "Nika bud'e min in fita.... " Murmushi yayi. "Zonan.... " Noqe kafad'a tayi. "Wallahi ka bud'emin ko in kira mommy.... " . "Ki kirata d'in ai mijinki ne yazo ba waniba...." Murgud'a baki tayi, Dariya yayi seyaga abun ya qara mata kyau. . "baki ji umarni na bakiba I said come here.....kindai san mala'iku na tsinema macen da batabin umarnin mijinta ko...? " Jin ya fad'i hakane yasa a sanyaye ta qarisa ta tsaya a kanshi. "Gani..... " D'ago kai yayi ya kalleta. "Is dat how gani shikenen.... Okey zauna.... " Yawani murtuke fuska shi a dole ya bada umarni. Zama tayi acan nesa dashi, Hannu yasa ya janyota ta wani fasa ihu, tana tuttureshi. . "Nika sakeni.... " Rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta wani irin ijiyar zuciya yahau saukewa yanajin wani irin yanayi da be ta'ba jiba. Lamo tayi akan kirjinshi itama tanajin wani irin yanayin da bata ta'ba jiba. A sanyaye yace. "Jewel......" Batai magana ba yakan yasa yakai hannu kan waist dinta da sauri ta zabura. "Na'am.... " Murmushi yayi ya kuma matseta a qirjinshi. . "Jewel inasanki sosai ban ta'ba tunanin zan miki irin wannan sanba please ki rayu dani kinji inaso ki soni please....." Batace komaiba hakan yasa yaci gaba. "I vow to be truthful with you at good and bad times and hopely I promise to be best husband for you my wife and best father for our children and best grandfather for our grand children...... Please forgive me Jewel am regret am apologize please ki yafemin kinji Mansu na.... " Lumshe idanu tayi hawaye na sintiri bisa kuncinta, jin ruwa ya d'iga a hannunshi yasa da sauri ya d'ago kanta. A rud'e yace. "Please Jewel stop crying oh my God, meyafaru dan Allah kiyi hakuri..... " Hannu yakai yafara share mata hawayen fashewa tayi da kuka sosai..... Harshe yakai da sauri kan kuncinta yana lashe hawayen a hankali ya kai tongue din ya lashe idanunta in circular form saida ta saki ijiyar zuciya kafin slowly yafara kissing idanunta both, Sosai takejin yanda yake kissing idanuwan nata qura mata ido yayi yana kallon yanda take runruntse idanu..... Hawayen ne suka kafe chak, hakan yasa ya d'ago yana shafa Sumarta. "What Jewel meyasa kike kuka....? " Cikin muryan kuka a shagwabe tace. "Leave me along......I don't want to see you... " Ji yayi kaman ya kwarma ihu hakan yasa yace. "Mansu baki sona ne.....? " D'aga kai tayi... "I don't love youuuuu........ Da sauri ya tura bakinshi cikin nata saboda bayasan yaji abinda zatace, zafi zuciyan shi keyi sosai da karfi yake tsotsan bakinta dake kamshi sosai, sam yaqi bata daman yin numfashi.... Tureshi taketa yi tanaso ta samu daman numfashi ko kuka zezo, kaman yasamu Loli pop haka ya dingi tsotsan bakinta yana raruman bakin. Tun tana qoqarin kwacewa har jikinta yayi sanyi ta koma ta lafe a jikinshi, Yafi 30 minutes sannan a sanyaye ya d'ago ya saki la'b'banta a hankali kaman jira takeyi yana saki ta fashe da wani irin masifaffan kuka, Ido ya zuba mata yanda take kuka kaman wacce yake yankan naman jikinta, zubewa yayi a kan gwiwwon winshi ya d'ago kanta.... Cikin wani irin murya me ban tausayi yace. "Jewel I know you has all the reason in this world kimin abinda kikeso domin yanda nai treating d'inki was awful, but am sorry kiyafemin kinji.... " Shiru tayi batare data kalleshiba jiyayi kaman ya kwarma ihu saboda yanda yaga tayi se yaji kaman about to cry, hannunshi ya daura kan gwiwwanta bakinshi na rawa yace. "My heart is breaking Jewel my mind is clouding because of you fa, I am sorry kinji nasan nime laifi ne a gunki I've hurt you am a bad person....am sorry for everything I said... I take it all back the love is have for you is stronger than anything dakike tunani a duniya I love you, can you ever forgive me my Jewel? Please not for me not for u please for the sake of auranmu..... " Fashewa tayi da kuka sosai rungumeta yayi sosai yanajin yanda take kuka. "Please stop crying nasan nime laifine please tell me anything u want I will do it, please don't hate me I love you Mansu...." Cikin kuka tace. "I just want to be alone..... " Da sauri kaman zeyi kuka yace. "No Jewel.... Please... " Kukan taci gaba dayi tana kan kirjinshi, daidai lokacin Mommy ta murd'a handle tana fad'in. "Mansu open the door.... " Zabura tayi da sauri zata tashi ya maida kanta kan kirjinshi cikin kuka tace. "Kaga mommy tazo please ka tafi.... " . "Indai kinaso in tafi se kinmin wani abu... " D'agowa tayi tana kallonshi da ido ya mata alama da shirt din jikinshi yace. "Remove it up.... " Zaro ido tayi tana shirin musawa. "Umarni na baki I said ki ciremin zafi nakeji... " Cikin kuka takai hannu tafara 'balle bottles din rigan idanshi na kanta ganin tana jujjuyar da kai, Tana gama 'ballewa ta sunkuyar dakai qasa, cire rigan yayi ya ijiye a gefe ya cire singlet dinshi kafin yace. "Look at me... " Kanta na qasa cikin isa yace. "Nace ki kalleni ko.... " A sanyaye ta d'ago kai domin ita Aryan inyai magana da isa mugun tsoro yake bata. Wow..... kirjinshi cike yake da soft skin wa'inda suka kwanta lufluf gunin ban sha'awa jikinshi farine fat kaman ka tab'a jini ya fito nipple's d'in shine kawai ya bada kalan chocolate ga cibiyarshi me ban sha'awa, Da sauri tayi qasa da kanta dan wani irin tashi da tsigar jikinta yayi. Murmushi yayi ya bud'e mata hannu. "Come.... " Noqe kafada yayi. "Aiko bakisan na tafi kenan come.... " A sanyaye ta matsa kusa dashi. "Kwanta.... " Ya nuna mata kirjinshi, tana shirin sakin kuka yace. "Kul in kikamin kuka sena fad'awa su mommy ince kece kika kirani dan haka kwanta, kinji I will not repeat.... " A sanyaye ta kwanta a kirjin nashi wani abu na mata yawo, lumshe ido yayi ya kai hannu ya rungumeta sosai. Sunfi minti 10 a haka sannan ya d'agota yana fadin. "Cire rigan jikinki mu kwanta muyi bacci me dad'i... " . "Innalillah wa'innan ilaihir raji'un na shiga uku ni... " tafad'a a ranta cikin kuka. A zahiri kam kuka ta saki. "Dan Allah Dikko kayi hakuri.... " Murtuke fuska yayi. "Oh Dikko ma ko, to maza cire rigan ko daddy a zan cewa kece kika kirani kikace kina buqatana kinga gobe dole a bani ke.... " Kukan taci gaba tana murza idanu, Tausayi ta bashi yanda take kuka hakan yasa yace. "Shikenan naji na hakura amma yimin kiss sannan in tafi...." Da sauri ta kamo hannunshi tamai, . "A hannu..? Aa anan... " Ya nuna kumatu. Bakinta takai kan cheeks din nashi labbanta na rawa tamai. Murmushi yayi. "Saura nan.... " Ya nuna baki. Murza ido ta hauyi tana kuka, hakan yasa ya janyo riganshi ya mayar yana fadin. "Yau kinsha saura na gobe... " Tashi yayi har yakai bakin qofa ya juyo. "Babu se anjima honey d'innan ko sena dawo. " Da sauri cikin kuka tace. "Se anjima.... " Murmushi yayi yasa key ya bud'e kofan ya fice. Fad'awa tayi kan gadon tasaki wani kuka. Yanzu haka za'a kai ta gidanshi ya dinga cin zalinta yana mata mugunta. Shiko cikeda nishad'i ya sauko yana mamakin wannan wani irin so yakewa Jewel dinshi, wanda ya shafi Mansu dan ko a mafarki be ta'ba tunanin ze sotaba yarinyar da yafi tsana duk duniya yau itace ya nemi wannan tsanan da yake mata ya rasa, yanzu soyayyanta ya girmi komai a duniyanshi wanda besan dalili ba besan ya akaiba lokaci d'aya komai ya canza mishi shigowan jewel rayuwar shi ya canza shi , be dauqa ze so Mansu ba kodan kasancewanta Jewel amma se gashi ikon Allah ya canza komai, qilama haqqin tane ya kamashi dan ba abinda ya gagari ubangiji. Amma yanzu dai yayi nadama ya qudirci faranta mata ze goge duk abinda ya mata a baya da yardar Allah. (Nidai nace uhmmmm... Allahsa nagaji sosai wallahi kuma System din ze dauke ba chaji, amma naso in kai muku har tarewanta. Anyway dai se kun jini gobe.) Matar Abdul ce✍️. 2022-10-14, 10:50 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT* _Daga Alƙalamin_🖊️ Haleema Isah (Mimi Queen) Marubuciyar: Rayuwa Sai dakee. Labarina. Barrister Shulaifat. Son Zuciya. Nisful hayat. And now on _MANSURAT_ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A* _Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._ https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa _____________________________________ Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_ Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance. Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁. Bismillahir rahmanir raheem. 43&44. Tun daga ranan Aryan be sake sa Mansu a idanunshiba. Yau ta kama Friday kuma yaune ranan tarewa, tun safe Mansu keta faman rusan kuka, haka su Nadeeya suka tasata a gaba da ban baki. Taro akayi na gani na fad'a ba muna taroba. Dan Fans din *MANSURAT* group sun hallara. Su _Ummin yahzeed ai sune qirjin biki an hallaci bikin tarewan takwara, dasu Hafsat Jaeh, Nanah Ruqayyat, Mrs Jarma, Abar qaunata Ammy , Hasina Datti, Eeshat, Mommyn muneebah, Hauwa'u Nasir (Mmn Yusra), Miemah, Ruqayyat Dalhat, Matar Hayat_. Kai gasunan dai Abun baze fad'i ba da yawa, Har Jama'ar ```Deeyat Novels dana Princess Novelist``` Dama sauran wa'inda ban lissafoba duk sun hallara dan gaskiya sunyiwa Mansu one love kuma taji dad'i sosai. Bayan magrib. An shirya Mansu tayi kyau sosai cikin Alkebba da yasa ado da zinare kamar d'iyar sarauta, tunda daddy da Ayya suka fara mata nasiha kanta na qasa cikin hulan Alkebban, ba abinda takeyi daya wuce kuka. Mommy ce ta riqota d'agowa tayi tareda zame hulan suna had'a ido da Mommy ta qara sakin wani irin kuka ta fad'a jikin mommy da sauri. Rungumeta Mommy tayi sosai itama tana kuka, kwata kwata yaushe aka rabata da Angle itama Mansu gashi yanzu zasu rabu, haba ai abun ze mata yawa dadinta d'aya ma ga Lubna, Daddyne yace. "Haba me makon ki lallasheta se kika tsaya tayata Mtsww..." Ya dubi qanwar mahaifin Mansu da sukazo daga Cameroon me suna Riyaama, yace. "Jata ku tafi motoci na jiranku. " Cikin kuka ta qara qanqame mommy. "Dan Allah mommy karda ki bari su tafi dani wallahi banasan na tafi na barku...." Ta qarasa kuka, Da kyar aka 'ban'bareta a jikin mommy, Kanwar Mommy da qanwar mahaifin Mansu suka riqeta zasu fita, Seda suka kusa fita sannan ta fizge ta juyo, Da gudu ta ruga ta fad'a jikin Ayya ta qanqameta tana kuka sosai tana fadin. . "Ayya U're my second Mother please karki bari su tafi dani ni nafisan gidanmu banaso nayi nisa dake.... " Kuka takeyi sosai. Itama Ayya batasan san kuka yazo mata ba, nan suka dingi kuka. Juya baya Daddy yayi domin shima kuka ne ke shirin kufce mishi dan harya fara hawaye. Yace. "Me kuke jira dare nayi ku tafi da ita.... " Haka Mansu na kuka suka fice da ita, tana kuka. Da kyar suka dannata cikin motan da sauri tasa hannu zata bud'e motan akayi saurin dannawa motan lock, Haka taita dukan glass din motan tana kuka, Farhan dake gaba shine zeyi driving din motan da sauri yace. "Sis shut up Jor....gidan Ya za'a kaiki fa ba gidan yankan kaiba...." Nadiya ce ta bud'e d'ayan gefen ta shiga, Mansu ganin Farhan ne a gaba ga kuma Nadeeya a gefenta yasa ta kwantar da kanta kan kafad'an Nadeeya, tana zubda hawaye. Sauran mutane kuma suka hau sauran motocin suka nufi gidan Mansu dake Gwamna road....... Basuyi tafiyan minti 30 ba suka karisa. Tun daga gate din zaku fahimci tangamemen gidane. Bud'e wagegen gate din akayi duka motocin suka shige ciki tas sukai parking, Nadiya ne ta tabota. "Oya mun iso... " Maqe kafad'a tayi, Farhan ne ya fita ya zagaya ya bud'e kofan da take. "Fito kinji Baby gurl.... " Qara lafewa tayi a jikin Nadeeya, duk kowa ya fito a motan anyi anyi Mansu ta fito taqi, Cikin fad'a Ammy (mahaifiyan Lubna), ta qarisa. "Haba Mansu ki fito mana anata fama tun d'azu.... " Cikin kuka ta sauko da kafafunta sannan ta fito, itama Nadeeya ta fito, Duk aka qariso sukayi cikin gidan. Gidan na walwace da haske tako ina ba qaramin gida bane gidane tsandarere me dauke da bangarori da dama. Nan suka nufi flat din. . "ki shiga da qafan dama... " Auntynta Riyaama ta fad'a. Aiko hakan tayi. Suna shiga ciki kowa sakin baki yayi yana kallon kayan alatu kai duniya in baka mutuba zakasha kallo. Ita kanta Mansu seda tayi mamakin irin dalolin da Daddy

Chapter 9 of 14