ba'ason macce mai ciki tana zama acikin damuwa shine kuka boyemun halin da kuke ciki kiyi hakuri mom nikaina nadauka ko don tanada cikine shiyasa take shiga acikin wannan halin, nisawa mom tayi sannan tace toshikenan zanje gurin malam Haruna inyimasa bayanin halinda ake ciki saboda tunfarko kunyi yarinta acikin lamarinan amma Insha Allah komai zaizo dasauki tashi kaje nizanje can gidan inyimishi bayanin komai.
Bayan sungaisa take gayamishi wajenshi tazo amma zatashiga cikin gidan sugaisa da mutanen gidan kafin yasallamai bakinsa to to babu damuwa, tana Shiva taci karo da uwar gidan malam wato Safeeya suka gaisa akashinfidamata tabarma tazauna suka gaisa sosai da matan gidan yaran gidan ma duk sukazo suka gaidata tare da tambayar Fadeela da ya Fauzaan, sunjima suna fira da matan gidan sannan takoma bangaren Mama Asma'u suka sake gaisawa domin anan malam yake samunta duk lokacin da tazo gidan.
Sunjima suna hira sannan malam yashigo nan suka sake gaisawa cikin mutunci da girmamawa domin kowa yana ganin kimar kowa acikinsu, bayan gaisuwa mom takeyimasa bayanin duk abinda yake faruwa wanda itama batada labari sai yau da Fauzaan yazo yakegayamata.
Shiru malam yayi domin shikanshi bazaice aljannu bane tunda tunda yake da Fadeela baitaba ganin wani abu makamancin haka atare da itaba, kallon mom yayi sannan yace gaskiya nayi mamakin wannan abun sosai, wlh nima nayi mamaki inbanda kurciya yarinya tayita zama da ciwo har tsawon wadannan watanni batare da sunsanar da kowaba, amma bakomai kibar komai ahannuna zanduba lamarin domin musan tayadda matsalar take.
Mom din Feezah CE zaune wajen boka tagayamasa kawai ayi aikin badamuwa Insha Allah babu abinda zaifaru, kallonta yayi yace badamuwa zamuyi aiki amma zaki samomuna jariri sabuwar haihuwa dakuma gashin kanta da farce akaifanta idan kinsamo kizo dasu zamufara aiki dasu......
*Yawan comments dinku shine cigaban lbrnku*
Maman Umar CE..........
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: ππππππππππππ
*FAUZAAN*
*NA*
*SARATU MUSA*(maman Umar)
*71-75*
Bayan takoma gida takira Feezah tagayamata abinda za'asamo ayi amfanidashi wannan karon kam hankalin feezah yatashi domin batasan ina zasu sami jariri sabuwar haihuwaba, garama gashin kanta da farcen akaifan bazasu gagaraba, yanzu yakike ganin za'ayi mom? Nidai dacewa nayi musami wani musakar masa kudi yasamomuna yaron cewar Mom, haba mom muna haukane dazamuce wani yayi muna irin wannan aikin mai kasada, kawai nidai abinda nakeganin shine mafita kikoma wajen boka kiyimasa bayanin bamusami jaririnba amma zaki bada kudi asamo tundasu aikinsune bazai gagaresuba, sauran kuma kibarmin zansan yadda zanyi insamo, idan akasamu zanzo dakaina inkawomiki, to shikenan sai kinzodin sukayi sallama.
Haka kuwa akayi bayan sun gama waya da Mom dinta direct part din Fadeela tanufa kamar yadda sukasaba dama lokaci2 sukan ziyarci juna amma ita duk lokacin da feezah taje part din Fadeela to akwai abinda yakaita bazuwan Allah tayiba.
Sallama tayi cikin palon tana zaune tana kallon wani shirin dasukeyi a tauraruwa, tana matukar son shirin domin tun agidan Mom tasaba da kallon shirin, dago kanta tayi tare da amsa sallamar lokaci guda murmushi dauke a fuskarta tace Aunty Feezah sannu da zuwa yanzu kike nima naso inje tundazu kitsefemin kaina amma kingani nan ina kallon shirin nan don banason yawuceni wlh, dariya Feezah tayi tace aini danakeson inganki tare dajin lafiyar babynmu kinga nazo tana kokarin zama kusa da Fadeela, tace dauko cemini muna kallon intsefemiki tunda gani nazo, yauwa auntyna bari indauko tatashi tawuce bedroom dinta daukan ceminin, wata irin shewa Feezah tayi tasamun nasara domin komai yazomata da sauki bakamar yadda tayi tsammaniba domin azahirin gaskiya batasan yadda zatayi harta sami gashin kantaba sai gashi komai yazo mata cikin sauki, zuwan Fadeela ne yakatse mata tunani aje kayan tsefan tayi tanufi kichin domin takawomata lemu da zuwa.
Tana gama tsefemata kan tace tabata aron reza zata cire akaifanta domin yadameta kuma gashi batasamu cirewaba, haka Fadeela tadauko mata reza tabata tanacewa kinga nima shiyake ciremun amma kwana biyu baiciremunba idan kingama kibani nacire nima yana damuna, badamuwa kibari idan nagama zanciremiki aibazakiji dadin cirewarba kina dauke da babynmu, dariya Fadeela tayi tace kai auntyna kuna shagwabani wlh irin wannan riritawa haka, badoleba tunda zamu sami dankanmu ai dole muyimiki bauta Fadeela bakisan yadda nakeji da cikinnan bane shiyasa, to aunty kema Allah yabaki masu albarka ameen kedai qanwata, sunjima suna fira har azahar sannan Feezah takoma part dinta.
"Bakaramin mamaki da tashin hankali malam yayiba dayaga abinda yake faruwa da yarshiba.
Nan da nan shima yashiga aiki domin yakaiwa yarshi taimakon gaggawa saboda duk abinda yake faruwa yana gani acikin irin nasu ilmin, yayi aiki sosai sannan yakira fauzaan yace yazo yanzu yana nemansa, rubutu da wani magani na karya sammu da kuma tsari ya hadawa Fadeela da Fauzaan,
Babu bata lokaci fauzaan yazo gurin malam bayan sun gama gaisawa yadauko wannan hadin rubutun yabaiwa fauzaan yakaiwa Fadeela tarika shansa kuma yace inason ingayamaka dakai da ita karkuyi bacci yau kudauro alwala kuyita nafilla nima nan ina tayaku bazankwantaba, sannan inason kakula da shan maganinta, tashi kaje Allah yashigemuna gaba, tashi yayi cikin girmamawa yayi godeya yanufi motarsa sai gida.
Bayan tabar part din Fadeela gidan Mom dinta tanufa takaimata tare dabata kudi domin akaiwa boka, nan da nan mom tashirya tare suka fito takama hanyar kauyen ita kuma takoma gida cikin tsananin farin cikin bukatarta zata biya domin tasha alwashin saita wulakanta rayuwar Fadeela da abinda yake cikinta, sannan tamallake fauzaan da dukiyarshi wanda hadda mom dinshi saitaga dama zaikulata balle yace zaisake wani auren.
Wannan karon ma bata taba tunanin aure akanshiba tunda tasani bayada shawar auren mata biyu, amma wannan karon kam bazatayi sakeba.
Gidan Mom fauzaan yawuce yayimata bayani dare dacewar itama tatayasu addu'a duk malam baigayamun abinda yake faruwaba natabbatar lamarin bakarami abu bane shiyasa nazo ingayamiki domin kisan abinda yake faruwa, ita kanta mom shiru tayi kawai domin lamarin akwai saka hannu aciki amma dayake batada tabbas akan zarginta shiyasa kawai tayi shiru da bakinta.
Nisawa tayi sannan tace babu komai Allah yashigemuna gaba kuma karkayi wasa da abinda malam yagayamaka, nima insha Allah zantayaku da addu'a Allah yasaukake, ameen cewar fauzaan.
Tana zuwa tayiwa boka bayani kamar yadda sukayi da Feezah, wata irin dariya boka yayi marar dadin sauraro sannan yace lallai kudin shaidanune irinku ne shaidanunmu suke bukata don haka zamushiga aiki ayau zansa akawomuna jariri sabuwar haihuwa, wanda dayan biyu kodai nasara kokuma faduwa tashi kije zakuga aiki, tazubemasa kudin tafito daga bukar.
Bayan tayi sallar isha tashiga wanka tayi minti talatin sannan tafito daman tundazu tasha maganin da fauzaan yakawomata, fauzaan take jira yadawo daga masallaci suci abincin dare domin tariga tasaba indai part dinta yake tobazataci abincin dareba sai tare dashi.
Sallamarshice yasata juyowa tana kallonshi murmushi dauke a fuskarta ta amsa sallamar tare cewa meyatsayar dakai ne natsuwata bayan kasan ina jiranka, baiyi maganaba harya karaso wajenta yahada jikinsu waje guda yana shafa cikinta dayayi girma kamar yau zata haihu, yace nabiya part din aunty ne takirani awaya shine murmushi tayi tace badamuwa aikam nayafe maka tunda wajen auntyna kaje cikin shagwaba tayi maganar, hade bakinsu yayi yana kissing dinta bakaramin sha'awar matarsa yakeba amma karfi da yaji ansashi hakurin dole.
Maman Umar CE .........
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: ππππππππππππ
*FAUZAAN*
*NA*
*SARATU MUSA* (maman Umar)
*81-85*
Tsawa yasake dakamata yana kokarin kare fadeela domin ita kawai takeson takama, dariya kawai takeyi maitsananin bantsoro duk yadda tayi dariya sai ko'ina ya amsa saboda tsananin karfin da dariyar takeda gashikuma darene, wani irin karfine yazomasa yayi saurin tura fadeela cikin mota sannan yasamu nasarar kamata yakaita cikin part dinta yarufe da key sannan yafita domin har yanxu jini baibar fita ajikin fadeela ba.
Dawani irin mugun gudu yafixgi motar shikanshi mai gadin saida yatsorata domin baitaba ganin uban gidansa cikin irin wannan halinba, yana bisa hanya yakira wayan mom kamar jira take yakira tadauki wayan cikin tashin hankali yayimata bayanin abinda yake faruwa yanxu haka suna bisa hanyar zuwa hospital ne kashe wayansa yayi domin bayacikin nutsuwarsa.
Da'isarsu hospital akashiga bata taimakon gaggawa domin hartafara ganin juwa yana daukanta saboda bleeding din datayi yayi yawa, babu abimda yake sai shafe zufa domin baisai cewa son dayakeyiwa fadeela ya kai hakaba gabadaya bayacikin nutsuwarshi jiyake inama zai iya daya daukemata ciwon.
Likitocin sunjima sosai sannan suka tsaida zubar jinin, bayan anyimata allurar bacci sannan suka fito daga dakin anan suka sami Fauzaan yana safa da marwa duk yahada wani uban gumi natashin hankali, kallonsa doctor yayi cikin kwantarda hankali sannan yace yasameshi office yawuce abinshi, sai dayashiga dakin yaga tana bacci sannan yafito yabi bayan doctor, kallonshi doctor yayi yace meye dalilin zubar jinin? Wlh nikaina banacemaka ga daliliba abinda kawai nasani tagayamin tayi mafarkin jini yana mata zuba , shine koda tafarka sai taga jinin yana zuba shinefa mukazo hospital, bayani doctor yakemasa cewar cikinta yana nan lafia babu abinda yasameshi amma gaskiya tazubar da jini sosai don haka sai ankaramata jini, to doctor aduba idan nawa yanayi sai asakamata OK badamuwa, nan dai akadibi jininsa aka karamata, lokacin har asba tayi anakiraye- kirayen sallar asba sai ga Mom tazo cikin tashin hankali domin tsoronta kar yar mutane tarasu ahannunsu.
Kuwa kawai take tana dariya kamar zata rusa gidan saboda amon muryarta mai ban tsoro da firgitarwa, wani irin karfine yazomata tacire gambun part dinta tayi jifa dashi ko takalma batada balle dan kwali tafito da mugun gudu tanufi get din gidan tana xuwa mai gadi yanamata magana hajiya lafia ina zaki haka wani irin kallo tajefeshi dashi saida gabanshi yafadi wani abu mai kamar mashi yafito acikin idonta yanufi wajen maigadi aibabu shiri yabude get yayanka ana kare itama dafamasa baya tayi gudu kawai sukeyi harsuka shiga wata unguwa mai bala'in duhu anan yasamu tashige wani gidan yaboye Allah yasoshi bata ganshiba shine yatsaya a bayan gambun gidan tana zuwa dagudu tawuce atunaninta yatafi, inbanda rawa babu abinda jikinshi keyi saboda arayuwarshi baitaba ganin tashin hankali irin wannan ba.
Dakin da aka kai fadeela tanufa tana shiga tasami ansakamata jini haka tazauna agurinta har jinin yakare sannan takira doctor yaciremata ana cikemata tana farkawa da mom taci karo zaune kusa da ita doctor yace asami wani abu abata taci sannan tasha magani, jawo kwandon abincin da Haule mai aikin mom takawo tayi sannan tahadamata tea tasha akabata magani tasha.
Bude kofar yayi mom yagani zaune tana hadamata magunguna zama yayi akusa da mom yadora kanshi asaman kafadar ta shafa kanshi tayi tacce yajikinka my son dasauki Mom, shima shayin tashiga hadamasa dago kansa yayi yana kallon fadeela itama shitake kallo murmishi yasakarmata itama tamayarmasa da nata kalar murmushin mai burgewa yace natsuwata ya jikinki? Ware ido tayi jin sunan da yakirata dashi a gaban Mom kasa tayi da kanta ahankali tace naji sauki domin bazata iya kyaleshiba, kaima ya jikinka kannemata ido daya yayi alamar dai2 murmushi tasakeyi nan Mom takatse firar tare da mikamishi kofin tea din da tahadamishi, doctor yadubata yaga babu wata matsala don haka yasallamesu tare dabata umarnin shan magani.
Gidan mom suka wuce gabadaya sai lokacin yatuna da Feezah dayarufe acikin daki, yana saukesu yajuya da motar yawuce gidansa domin yabudeta, yana zuwa yaga kofar gidan bude domin tunfitarsu basu dawoba shima maigadi kasa komawa cikin gidan yayi saboda tsoron karta iskoshi shikadai ta kasheshi domin yafahimci ba lafia ba irin wannan tashin hankali, yajima yana order ba'a budeba dole yafito dakanshi yashiga cikin gidan yabude get din gidan sannan yashga da motarsa yanaxuwa part dinta yanufa karo yaci da gambun palon agefe cikin sauri ashiga cikin palon yana kwalamata kira shiru kakeji duk inda yake tunanin zai ganta yaduba amma bai gantaba.
Can sai ga baba mai gadi yashigo don yaga lokacin da akabude get din domin banisa yayi da gidanba amma baizai shigaba gudun tarutsa dashi, yana zuwa yayiwa mai gidan bayanin abinda yafaru bayan fitarsu, hankalin Fauzaan bakaramin tashi yayiba, nan dai yawuce part din fadeela domin yadebomusu wasu kayan tunda mom tace bazata komaba sai ta haihu gara tazauna a gabanta hankalinta yafi kwanciya.
Maman Umar CE........,
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: ππππππππππππ
*FAUZAAN*
*NA*
*SARATU MUSA*(maman Umar)
*91-95*
*KARSHE*
*FANS NA FAUZAAN INA MIKA TARIN GODIYATA AGAREKU, NAJI DADIN YADDA KUKE QAUNAR WANNAN NOVEL DIN ALLAH YABARMU TARE, NAGODE SAI MUNHADU ASABON NOVEL DINA MAI ZUWA INSHA ALLAH*.
*SAURAN GROUPS DIN DA KUKE BIBIYAR WANNAN NOVEL DIN KUMA BAZAN MANTA DAKUBA ANA TARE INSHA ALLAHπ KAMARSU*
*MAHMU GEE NOVELS*
*AISHA GARKUWA NOVELS*
*NIDA KAWATA NOVELS*
*DAN DALIN MARUBUTA NOVELS*
*HAUWA NOVELS*
*UWAR GIDA*
*AMAL*
*DA DAI SAURANSU INAGODIYA ALLAH YABAR QAUNA.*
Anyi buki lafiya yaro yaci sunan malam suna kiranshi *hainal*, masha Allah hainal yaro gwanin bansha'awa gashi bayada kyuya koya yadda yake dashi, Mom tana kulawa da fadeelah sosai domin duk wata kulawa dayakamata ace tasamu amatsayinta na mai jego tanasamunshi awajen Mom.
Yau watan hainal biyu da haihuwa amma idan kika ganshi zaki dauka yakai wata biyar saboda girma da koshin lafiyar da yakeda ita, FAUZAAN ne rungume dashi zasuje gidansu fadeelah yana masa wasa sai bangala dariya yakeyi, lokacin da zaishiga mota yamikawa fadeelah shi kuka ya'aza alamun bazaije wajentaba, tsaye tayi tana kallon abin mamaki yau hainal ne da yimata kyuiya, dariya kawai FAUZAAN yayi yajefamata keys din motar tayi driving dinsu haka kuwa akayi dayake yakoyamata mota.
Bakaramin murna malam yayi daganin yadda jikanshi yazamaba, yayi wayo sosai yana taramasa hannu kuwa sai yafada jikinsa kamar daman yasaba dashi, bayan sungaisa suka shiga cikin gidan domin yagaisa da mutanen gidan.
Bayan sungaisa yayimusu alkhairi kamar yadda yasaba koda yaushe sannan yawuce dazumar sai zuwa dare zaizo daukansu, rakashi tayi har bakin garka sunjima suna musanyar kalamai sannan yawuce itama takoma cikin gida inda yan uwanta suke tashiga cikinsu anata hirar yaushe gamo, mama safeeya tadubi hainal dayake dauke ahannun Aisha kanwar Fadeela amma badakinsu dayaba tayi tace kai girman dan mutum babu wuya wlh, mai sunan malam kam yayi saurin wayo tubarkalla, to mama soyake yayi sauri yagirma koyafara kawomuku kudin cefane domin yaga matan nasa bana wasa bane cewar Aisha, aikam yakamata kuwa ko nakarfen yahuta shima, cewar mama safeeya, dariya sukayi gabadayansu, sunajim suna fira sannan fadeelah tayuce nasu bangare.
"Mutanen garin bakaramin tashi hankalinsu yayiba jincewar mahaukaciya tashigomusu acikin qauyen kuma gashi idan tarike mutum duk karfinshi indai ahannuntane bazai iya kwatar kansaba, don haka maigarin garin yahada dajijawan garin da matasan garin domin anemo mafitar yadda za'a bullowa wannan lamarin.
Bayan sunyanke shawarar asami raga idan tayi bacci adaureta aciki akaita gidan mahaukata domin xamanta acikin garinsu yanada hadarin gaske, haka kuwa akayi bayan sundaureta yadda bazata iya kwancewaba suka sakata amota sukayi hospital din mahaukata da ita suka barta acan sukayi tafiyarsu.
Gudu takeyi bata koduban gabanta duk rigar jikinta tayage kana ganin jikinta tafiya kawai take bata duban gabanta tsallaka titi zatayi, yayi kokarin tsaida mortar amma ina saida yabugeta tafada gefen titin kwance jini yana zuba akanta dasauri yayi parking din motarsa yafito lokacin har jama'a sunfara taruwa awajen, wani bawan Allah ne yataimakamasa suka sakata amota hospital din da take aiki yanufa da ita domin yabata taimakon gaggawa, dagudu akashiga da ita emargency domin ceto rayuwarta.
Bayan wani lokacin akayi nasarar tsaida jinin amma haryanxu bata farkaba, saboda allurar baccin da akayimata, office dinshi yawuce kamin tafarko domin alamu sunnuna cewar batada hankali duba dayanayin jikinta.
Yau Fadeelah zasu koma gidansu dayasha gyara kamar gidan shugaban kasa, komai sai da FAUZAAN yacanzashi part din Feezah ma yasa angyara itama komai sabo ne akasaka, tafiya sukeyi bayan sunyi sallama da Mom fira sukeyi cikin tsananin son junansu da burin faranta ran junansu, basu fatan abinda zaishiga tsakanin farin cikinsu kallonta yayi cikin tsananin kewarta yace amma gaskiya nutsuwata daren yau gabadayansa nawane ko? Kallonsa tayi da idonta masu saukarmasa da kasala tace haba bananata kasani komai nawa hadine da naka, taya dayan zaiji dadin rayuwa idan babu daya, hannunta Yakama yana murzawa ahankali sannan yace hakane natsuwata kinsan mom takasa ta tsare tahanani nayi yadda nakeso amatukar matse nake sake wlh karka damu zaka fanshe kaji, sai dasuka tsaya suka sayi abunda suke bukata sannan suka wuce gida, mai gadi yabude musu get yashiga ciki.
Bayan tafarka afirgice tamike domin Dan baccin da tayi tadan sami karfin jikinta ballet gashi yadda ruwa aka sakamata, kokarin fizge Karin ruwan take sai gashiyashigo nosing tana bite dashi abaya, addu'a yafara tofamata nan da nan jikinta yasake takoma tazauna tana zare ido, allura yasake yimata sannan yabawa wannan nosing din damar taje toilet tayimata wanka tasake mata tufafi zaije yakira likitan kwakwalwa, fita yayi daga dakin domin yayi waya da doctor din.
Binciken farko doctor yace shibaiga wata matsalaba acikin kwakwalwartaba asalima batada wata matsalar atare da ita, don haka shawarar dazaibashi akoma ayi na musulunci yana yuyuwa shafar aljannune suke damunta, haka kuwa akayi *DOCTOR NURADEEN KABIR* kenan mai tausayin nakasa da shi, Sam baidauki duniya da zafiba kowa nasane bayada kyamar talaka kokadan matarsa Nafisa rasuwa tayi wajen haihuwa da ita da abinda yake cikinta duk Allah ya'amshi abinshi, bakaramin maraicin rasa matarsa yashigaba, daman aikine yakawoshi anan katsina amma shi mutumin garin Jo's ne.
Bayan yayiwa wani malamin addinin bayanin halinda ake cikine shine take gayamasa cewar wannan aikin jinnune, amma zaibashi taimako da izinin Allah zatasami lafia.
Bayan wata biyu dafara yimata magani cikin ikon Allah tasami sauki sosai har tana iya magana kuma cikin hankali, yau asabarce bayazuwa aiki suna zaune a harabar gidansa suna fira yake bata labarin halinda yatsinceta aciki dakuma irin taimakon dayabata, kuka takeyi sosai tana tsinewa kanta saboda tasan duk abinda yasameta itace tajanyowa kanta, nan itama tagayamasa irin dalilinda yasakata shiga cikin wannan mugun halin.
Hankalin Nuradeen bakaramin tashi yayiba jin irin wannan aiki da tayi, yaji takaicin kansa daya taimakamata tunda wata rayuwar akaso asaka cikin irin wannan halin datasami kanta aciki, Allah kadai yasan iya adadin abunda sukashuka ita da mahaifiyarta, sannan abun tashin hankalin Ashe da matar aure yake zaune baisaniba, nan dai yabaiwa kanshi hakuri tare da alkawarin gobe zaimadata garinsu kuma hannun mijinta.
Jin faduwar abu ne yasa tayisaurin ajiye wukar datake hannunta tafito Palo dai dai lokacin da Hainal yafashe dawani irin kuka saboda yatsorata da fadowar da kayan sukayi, FAUZAAN yarigata isa inda take, jijjigashi yakeyi alamun rarrashi ahaka Tayi sallama tashigo cikin palon, mutuwar tsaye sukayi gabadayansu, dukkansu sun dauka mafarkin dasuka sabayida itane shiyasa ko motsawa basuyiba, sai da tasakeyin magana sannan suna tabbatarda Cesar bamafarki sukeyiba.
Bayan angama murnar ganin juna sannan take gayamusu cewar tare da bako take tashi yayi yafita domin yashigo da bakon, bakarmin tashi hankalin FAUZAAN da fadeelah yayiba jincewar duk abunda yake faruwa Feezah ce *silah* nan da nan FAUZAAN yakira wayar mom yace duk abinda take yanxu tazo ga Feezah nan tadawo, haka yakira malam babansu fadeelah, duka kominti shabiyar basuyiba saigasu agidan.
Nan wannan akasake maimaita abunda yafaru mom kuka tasaka kamar ranta zaifita saboda jin yadda akaso rayuwar baiwar Allah tasalwanta amma dayake Allah ba'azzalumin sarki bane saiyajuyamusu mugun abunsu yakoma kansu.
Shikam malam baice komaiba tunda Allah yakaremishi yarsa, nan take FAUZAAN ya yanke igiyoyin aurensa da Feezah.
Hainal yaro mai hazaka zaune take yana sauraren malaminsu namakarantar islamiya yana koyardasu yadda. Yaron Allah yabashi hazaka sosai kodayaushe yabada aiki sai karatu.
Bayan hainal fadeelah tasake haifar yara biyu duka mata *Fairah* da *Feedah* yaran gwanin kyau dasu.
*Masha Allah anan nakawo karshen littafina mai FAUZAAN*.
*Kuskuren dayake ciki Allah ya yafemin*
*nagode*
Maman Umar CE.........
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: ππππππππππππ
*FAUZAAN*
*NA*
*SARATU MUSA*(maman Umar)
*86-90*
"Yana zuwa yagayawa mom halin da ake ciki game da ficewar Feezah dakuma yadda sukayi da mai gadi, ita kanta mom bakaramin tashi hankalinta yayiba, nan da nan tadauko wayarta domin takira Mom din Feezah tagayamata halin da ake ciki, wayar hartakare ringing ba'a daukaba har sau hudu tana kira amma ba'a daukaba, hankalinta kara tashi yayi tacewa Fauzaan yayi sauri yaje can gidansu yayimasu bayanin halin da ake ciki to mom amma kibari agayawa police tukunna, badamuwa Allah yabayyanata ameen cewar fauzaan.
Bayan yayi parking din motarsa shiga yayi cikin gidan yake tambayar mai gadi mom tana ciki kuwa? Domin awaje ya ajiye motarsa, a a Alhaji daman haka yake kiransa ai tun jiya datafita bata bata dawoba kuma batagayamin zatayi tafiyaba nima dai nayi tunanin ba lafia ba, to bakuyi waya bane ? A a bata kiraniba cewar mai gadi OK badamuwa idan tadawo kagayamata cewar taje gidan Mom dina tana son ganinta to to bamtsala insha Allah tana zuwa zangayamata.
Daganan police station yawuce domin yakai report din ko Allah zaisa aganta, yana zuwa yayimusu bayanin abinda yake faruwa suka rubuta statement tare dabashi tabbacin xa'aganta insha Allah, sannan yabaro wajen.
Can wani qauye mai suna dabo acikin karamar hukumar sokoto anan suka wayi gari da wani mummunan tashin hankali, garin yakasance kusa da rafine wasu matasa suna kamun kifi sukaga wata mahaukaciya tasheko dawani mugun gudu kamar zata tashi sama tana zuwa dai2 wadannan samarin taja burki tatsaya cekkk kamar gunki sai rabon ido take jajawur dasu kamar ansaka barkono, kalle2 takamayi can idonta yafada akan wadannan samarin dasuke kamun kifi nan da nan tayi cikinsu tana kokarin dangosu aikuwa damugun gudu suka dare kowa yayi takansa can tabi daya da gudu kamar walkiya saigashi ahannunta wata irin matsa da takaimasa saida idonshi sukafito waje saboda azaba kokari yake yakwaci kansa amma yakasa saboda bakaramin riko tayimasaba, inbanda dariya babu abinda take wanda dariyar kanta abintsorone , ganin haka 'yan uwansa suka ruga dagudu cikin gari domin asamo maza suzo suceceshi kar takasheshi, cen Allah yabashi sa'a yasami kufcewa yabi bayan abukansa da gudu suka shiga cikin gari itama dagudun tadafamusu baya sai tayi kusa