An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[10/15, 6:05 PM] +234 903 657 2265: 👸🏼 AUREN KADDARA👸🏼
Na Aysha
Humairah(humeeynah)
1_5
Cikin talaitani dare take gudu kamar ranta xai fita,gudu take sosai tana waige waige,bata Ankara ba ta daki kirjin wani bakin mutum mai mumunan kama,a tsorace tasaki wani ihu,tafada akasa sumamiya,cikin karaji wani kyakyawan saurayi yaxo ya dauketa da ga gurin,karar wayarsa CE ta farkar dashi daga mafarkin da yake,a hanxarce ya mike yana duban wayarsa, ya dauka ya kara a kunnesa yace kinsan yau ma nakara ganinta a cikin mafarkina,da ga daya bangaran taja tsaki tace plzz Khalid karabu da zancen mafarki let face reality,ni CE xahirinka ba wata ba stop dreaming about ur dream gal,I love u Khalid kasoni kamar yadda nake sonka,cikin fushi Khalid yace no jameela ki bar maganar nan amma I promise u sai na gano Inda wannan yarinyar take,da sauri ya kashe wayar ya fito falo ya nufi Inda yake yin zanansa wato Art ya shiga,birgik duk hotan wata budurwa ne a gun wanda sai dai gangar jikinta amma kuma ba fuskarta,cikin murmushi ya shafi daya daga cikin picture din yace inshallau sai naga face Dinki ma dream gal,kuma sai na naimoki where ever u are,ya dau drawing pen yafara xane
Sauko wa take da ga matatakalar jirgi tana murmushi, tace welcome back 2nigeria ma swt home,da sauri ta nufi Inda taga mamanta da yayanta,ta rungume mamanta tace mum INA dad,tayi murmushi tace yaje meeting ne but yace a baki hakuri,ta daki kafadar yayanta tace bros ya akayi ne? yace toh ai ni ke hibbat mamaki ki kaban irin wannan girma haka,hibbat tayi daria tace oh bros u will never change,suka dunguma suka tafi mota gaba daya
Suna xaune dukansu a falo dady yayi gyaran murya yace mashallah hibbatu kin gama makaranta yanxu sai aure,cikin sauri hibbat tace no dady gsky ni ba yanxu xan yi aure ba,sai nayi aiki tukunna sannan sai ayi maganar aure,dady yayi murmushi yace OK dis is a good idea I will gv u enough time, cikin jin dadi tace tanks dady
Zaune take a kusa dashi ta nayi masa magiya plzz Khalid accept me as a wife,yayi murmushi yace jameela INA sonki amma ba so na aure ba sone kawai na child hood,karkimanta ni bantaba cewa INA sonki ba,amma insonki as musilimat,ta durkusa gabansa ta CE wlh mutuwa xanyi da sonka,idan baka amince dani ba akwai mastala kai baka San yadda nakeji ba,cikin fushi Khalid yace yadda kike ji nima haka nakeji akan tawa masoyiyar so plzz lv me alone,a kufulce ta mike tace Khalid ka xare,wlh baka da hankali ,u need 2c a dct 4 mental disorientation,ya xaayi kadunga son abinda ba rayayeba,cikin xafin hannun ya wanka mata mari ya nunata da Dan yasta yace abinda nakeso rayayiyace,kuma xantabatarmiki da hakan,ya ja tsaki ya fice da ga gurin,tayi murmushin takaici tace wlh Khalid sai na aureka ,ta dau Jakarta ta fice
Da sauri2 take shiryawa xata tafi office,kwankwasa kofar dakin da akeyi ne ya dakatar da ita da ga sa talminta ta CE yes shigo,ta daugo kai tace bros kaine,cikin murmushi fudail yashigo yace hibbat yaune XAKI fara fita office ko,ta gyada kanta,yace plzz sis ki kula nasan ki akwai kamun kai so plzz kici gaba da kamun kanki,sbda najiyo labarin wanna CEO din company da zaki fara aiki wlh hibbat shidin akwai son yammata,hibbat ta masto kusa dashi tace ya fudail karkadamu sbda kasan yadda maxa suka dunga chasing dina a London amma ba Wanda na taba muaamala dashi olmost 5yrs INA karatu a London bantaba kula saurayi ko daya ba,kaga kenan Anna ma ba baxan kula kowa ba ,ya fudail yayi murmushi yace I trust u ma sis
Meeting din gagawq company yahada,kowa ya tashi yayi bayani,itama hibbat ta tashi ciki kwanancewa akan turanci tayi Nata bayanin kowa sai kallonta yake cike da shaawa da birgewa tana gamawa akayimata tafi,Anwar kallonta kawai yake Dan ya Dade baiga macen da ta tafi da hankali sa ba irin wannan
NA CHANXA SUNAN NOVEL DINA DAGA MATAR WAYE ZUWA AUREN KADDARA sorry 4 d in convinces
[10/15, 6:06 PM] +234 903 657 2265: 👸🏼AUREN KADDARA👸🏼
Na Aysha
Humairah (humeeynah)
6_10
Anwar duk yagama rudewa da ganin hibbat jikinsa har rawa yake yi,har aka tashi da ga meeting din hankalin sa baya jikinsa,suna fitowa ya janyo manager yace gsky wannan yarinyar ta hadu dayawa manager yanxu ya xaayi,manager yayi daria yace oga wannan ba irin taku bace,bincike yanuna cewa wannan yarinyar ta Dade alondon tana karatu amma bata taba saurayi ba kuma haka xalika anan ma bata taba yin saurayiba,Anwar yayi shiru sanna ya numfasa yace,kana nufin ita din cikakiyar budrwa ce ma'ana she is a virgin,manager ya daga kansa yace haka nake nufi,Anwar ya sheke da daria yace toh ni xanyi breaking wanna record din nata,manager ya saki baki yana kallonsa da mamaki sannan yace oga wannan Abu dakamar wuya yake yarinyar Nada kamun kai sosai,Anwar yayi murmushi irin na cikakun yan duniya yace watch nd see,sukayi daria gaba dayansu sannan kowa ya nufi nashi office din
A durkushe take tana naiman wasu takardu,tana dagowa suka hada ido,tayi saurin gyara mayafinta tace welcome sir,Anwar yayi murmushi yace ya aiki? bai jira tayi magana ba yajawo kujera ya xauna,cike da mamaki take kallonsa,Anwar yayi gyaran murya yace naxo nai nayabamiki akan irin kwaxonki a wannan company, hibbat tayi murmushi tace is ma pleasure sir,ai dama aiki na ne,yayi murmushi yace toh nima nagode,ya mika mata hannu alamar gaisawa,da sauri ta kalleshi tace no sir,ya Dan kalleta sannan yatashi yace OK badamuwa ya daga kafadarsa sannan ya fita
5 ta fito daga office xuwa gida,tashiga motarta kenan sai ga wani Massinger da kaya a hannunsa ya na haki,tayi hanxarin bude motar ta fito tace baba lpy dai nagan ka a haka,ya numfasa cikin gajiyan gudun da yayi sannan yace oga ne yace akawo miki wannan,ta xaro ido tace oga kuma yace eh,takarba tana mamakin mai aciki,ta kalli Massinger tace baba nagode, ta shiga motar ta ta nufi gida
Ta na shiga gida direct dakinta ta huce,tayi wanka tayi sallah sannan ta dauko ledar kayan xata bude,sai taji ana kwallamata kira sauri tafito,ta nufi kitchen tace momi gani,momi ta kalle ta tace dama wai wani ke kiran ki a waje,hibbat ta xaro ido tace wani kuma,momi tace eh mana kije kiga waye,hibbat ta nufi kofar fita tana mitar waye wannan,ta na bude kofar falo taga manager rike da wasu kaya a hannsa ,ta Dan kalleshi tace manager lpy kuwa naganka,yayi murmushi yace oga ne yace nakawo miki,ta karba tana kallon ledar,sannan ya mika ta wayarsa yace oga on line,ta karba tace hello,Anwar dake kwance akan lafiyayen carpet dinsa dake falo yayi saurin tashi xaune sbda yadda yaji muryar ta daki kunnasa ya ja numfashi yace hibbat kiyi hakuri ki karba ba yawa,zaki ga ticket din jirgi guda Shida na kasashe shida,duk Wanda kikayi raayin xuwa kiyi wa manager magana xai miki komai akan visa,wanna kuma bandir din dolla CE kiyi hakuri da ita,ki siya kayan kwalliya,hibbat da ta daskare a tsaye ko mosti bata iya wa ,da kyar tace toh nagode ,sanna tabawa manager wayan yayi mata sallama yafita ita kuma ta koma ciki,cikin jin dadi Anwar ya dungule hannusa a daya hannun yace YESS
Tana shiga gida ta janyo ledojin gaban ta,ta bude ledar farko ta dauko wani Dan akwati karami tana budewa taga wata haddiyar sarkar gwal tare da awrwaronsa taja numfashi ta rufe,ragowar duk turarukane masu tsadar gsky ,ta bude daya ledar da manager ya kawo ta dauko wasu haddadun dogayan riguna guda biyar,ta leka ledar ta hako wani box mai kyua,ta bude wata Yar takardar CE aciki hade da wani agogo silver da zobe silver, ta bude takardar taga ansa plzz accept my lov
[10/15, 6:07 PM] +234 903 657 2265: 👸🏼AUREN KADDARA👸🏼
Na Aysha
Humairah (humeeynah)
11_15
Hibbat taci gaba da kurawa takardar ido kawai sai ta tsinci kanta da yin murmushi, ta numfasa tace oh toh ai bashi da mastala guy din gashi yahadu,bakine dogo mai faddadan kirgi,gashi da idanuwa,ga dogon hanci,ga kuma sajen shi daya kwanta kan fuskar shi,ta lumshe ido tace gsky u are every woman's dream but I need time 2 think
After 2 wks
Da sassafe ta fito cikin wata haddadiyar shaddar ta red tasha aiki tamkar mai xuwa dinner,cike da nishadi ta shiga dakin yayanta ta kwankwasa kofar,yace yes tabude tana daria,ya kalleta da mamaki yace hibbat y are u so happy dis morning,ta kalle shi tayi murmushi tace yaya fudail yau xanyi wani crazy abu da bantabayi ba arayuwata,ya gyara tsayuwarsa yace toh inaji wani Abu kenan,tace yaya fudail yau xanje gurin boss dina nace masa na amince da soyayyarsa ni ma inasosa,ya fudail ya xaro ido yace hibbat dis is crazy,ta kyalkyale da daria tace shine nafada maka 2day am crazy,yaya fudail ya masto kusa da ita yashafi kumatunta yace dama tun sati biyu da suka wuce na fuskanci u are n lov wiz ur boss,so plzz be careful,ta rike hannusa tace ma one nd only bros kar kadamu I will take care of ma self tafada tana bude kofar dakin,yayi murmushi yace toh sai kindawo,ta daga masa hannun tafita da sauri gun motarta.
Jitakeyi yau kamar ranar sallah dan itama ta kamu da son boss din nata,ta naxuwa office ta ajiye jakarta da wasu files sannan tafita zuwa office din boss dinta
Ya na xaune a doguwar kujera dake office dinsa,manager kuma a gefensa yana tsiyayamasa giya yana sha,ya karba ya Dan kurba sannan ya ajiye,ya kalli manager yace wlh yarinyar nan wahalar dani kawai take yi,wai har nine nake wa mace hidima,Adaidai nan hibbat tabude kofar office din, tasa kafarta kenan sai taji boss yana cewa ,wlh tsakanina da mace kwana daya idan tayi min ne nake kara mata biyu,manager yayi gyaran murya yace oga wannan yarinyar fa da bantake Dan nafada maka she is a virgin,Anwar ya mike tsaye cikin fushi yace virgin fa kace,toh Kayi kokarin zakayi wani Abu da ita ta hanakane,manager ya yi saurin girgixa kansa yace aa wlh,Anwar ya ja tsaki yace aikin banxa,mata nawa nayi taraya da su amma bantaba samun virgin ba,nayi taraya sama da mata dari baka,fara,doguwar,gajeriya,
Yar Sudan,Yar larabawa,baturiya,inyamura,bahausiya,amma duk cikin su bantaba cikin karo da virgin ba,sai ita kadai,sama da wata uku yanxu INA lalaba yarinya amma na kasa samun hadin kanta,ya juya ya dauki cup din giyarsa yasha sannan ya kuna sigari zuka daya yayi mata,ya take ragowar a kasa,ya kalli manager yace Allah sai nasamu yarinyar nan,ko da kuwa takarfine,yana kaiwa nan hibbat ta dafe kirginta,kanta na wani irin sarawa,sannan ta juya xata fita,sai kuma ta chanxa shawara,ta kara koma wa office din amma wannan karon da karfi da bude office din yadda xasu ganai wani ya shigo office din, ai kuwa tana shigowa suka chanxa akalar hirar tasu,manager ya kalle ta yace tabbas hibbat kin tafi da xuciyar oga sbda kullum bashi da aikin yi sai maganar ki,cikin daure fuska hibbat tace kware kuwa naga alama,manager ya kalli Anwar yace oga bari na barku yafita daga office din,Anwar ya kalleta yace ma lov ya akayi ne?kinga duk na susuce akan ki,hibbat tayi murmushin takaici tace hakane,ya taso daga Inda yake ya masto kusa da ita yace yau akwai wani party da na shirya miki sbda mutane suna min korafin banyi aure ba,so shine na keso na nunaki as ma wife 2 b,ta kalleshi cike da tsana tace wlh gashi kuma kaina ciwo yake baxan iya hallarta partyn ba, yanxu dama naxo nace maka xan tafi gida ne sbda am not ma slf ,da sauri ya Dafe kansa yace oh sannu ma lov bari nasa akaiki gida,tayi saurin cewa no I can drive bata jira komai ba ta fice da ga office din, ya xauna akan kujera shawab yace I most know what 2 do
Tana tafe tana shara kwalla,sai kuma tayi saurin daukar wayarta ta kira tasa a kunnata,tace hello boss naji kamar nasamu sauki xan iya xuwa gun party nan,cikin jin dadi ya tukude budurwarsa da take rugume dashi yace are u serious tace yes,karfe nawa ne?yace 8 na dare tace toh sai naxo,ya ajiye wayar sannan ya rugume budurwarsa cikin jin dadi yana shafata ya dauketa suka cika daki suna tambadewarsu
[10/15, 6:08 PM] +234 903 657 2265: 👸🏼AUREN kADARA👸🏼
Na Aysha
Humairah (humeeynah)
16_17
Karfe 8 daidai tayi wa hibbat a kofar katafaran hotel din da ake party,ta kara duban kanta sosai blue jeans da red top ta saka sai kuma wani haddaden red hill a kafanta,kanta sai kalli ya keyi ya sha gyara ta nanadeshi da wani karamin gyale blue,fuskar nan tasha make up farar fatarta ta fito sosai,ta numfasa ta kashe motarta ta fito sai zuba kamshi take,ta nufi hotel din tana wani shuumin taku,inda kidan yake tashi nan ta nufa,ta shiga fuskar nan a daure,manya mutane tagani agurin masu ji da kansu ,kowa kagani agun kasan ba karamin mai arxiki banai,kowace mace ta kure adaka sai yauki suke,tayi murmushi Wanda ita kadai tasan maanarsa,ta karasa gun bata Ankara ba taji ana tafi,Anwar tagani da manager da sauran abokanasa yana yimata murmushi, ya tako har Inda take,ya kama hannunta ya jata tsakiyar filin,ya karbi loudspeaker gurin m.s din,ya yi gyaran murya yace,jamaa yau ranar farinciki ne agurina,yanuwa, da abokannan arxiki sun damu suga nayi aure,toh mastala daya CE dama shine bansamu matar da tadace dani ba,amma a yau INA mai shaida muku na samu matar da tadace dani,ta kuma sacen rayuwata gaba daya ,kowa ya shaida itace wannan,yanuna hibbat da hannu,cike da murna kowa ya dauki tafi,hibbat bata jira komai ba ta fisge hannunta daga gun Anwar, ta dadage ta wanka masa mari kafin yasan abun yi takara kifamasa wani Wanda ya tilastamasa gani wasu taurari,ya dafe kuncinsa da sauri,hibbat tayi taku daya zuwa biyu, sannan ta fisgo loudspeaker din daga hannusa,ta kalli jamaar gurin duk sun rude komai ya tsaya cak,tayi guntun tsaki sannan tace,ni bani CE farinciki sa ba,kuma ni ban sace masa rayuwaba,ta juya gurin da Anwar yake ta tako Inda yake,ta nunashi da Dan yasta ,tace kai kamanta da akwai Irina acikin mata,har da karfinka kudinka ,mulkinka xai rudeni na yi lalata da kai,ba kace Kayi amfani da mata sunfi dari ba, baka samu virgin ba ,toh Albishirinka akwai Irina dubu suna nan acikin duniyar nan ,sbda baka kai mastayin da xakaje kusa ma dasuba shiyasa baka taba cin karo da irinsu suba,banxa Dan iska,wlh nafi karfinka harabada,ta masta kusa da wani table ta dauki lemo a cup ta wasta masa tace mazinaci kawai,tayarda cup din yafadi akusa dashi ya fashe,Anwar ya ruste idonsa sbda wani irin bugu da kirjinsa yake mai ga kunyar mutanan gurin duk takamashi,har ta danyi gaba sai kuma ta juyo tana rankwada ta kalle shi tace idan kana tunanin korata da ga companyn ka toh am sorry 2 say na bar aiki,tayi sauri ta fice da ga gun tana ajiyar xuciya
Gudu take ta na haki,sbda galaibaita da tayi,zubewa tayi akasa kamar mataciya wasu gardawan mutane ne suka hau kanta da duka,da gudu ya taho,cikin xafin nama ya daki daya daga cikinsu ,ya dauketa yana mata sanu ,itama dago kai tayi tana amsawa,cikin tashin hankali ya mike daga nanauyan mafarkin dayake,ya dafe kirjinsa ya bude baki da karfi yace na ga fuskarta yau,da sauri yanufi gurin xanan sa ya dauki drawing pen dinshi yafara drawing din fuskarta, ya xaro wayarasa daga aljihunsa ya dadana num sannan yasa a kunnasa,daga daya barin tace hello my lovly man,ya yi gudun tsaki yace jameela naganta wlh yau naganta,ta ja tsaki tace Khalid u always give me dsame story,dama ai nasan kana ganinta but amma nasan xaka dawo daidai kadaina ganinta,nasan aljanu ne suka shafeka,yayi murmushin takaici yace oh jameela u will never change,toh yau naga fuskarta a mafarki,kixo kitayani murna ,kuma duk Inda take a duniya nan sai na naimota I give u ma word,ta tabe baki tace ganinan xuwa
Yana durkushe kusa da picture din da ya xana,sai surutai ya keyi ,sai kace wani sabon kamu,bai ma San tashiga ba,jameela ta girgixa kanta cikin takaici ta masto dab dashi,tace gani naxo ganin aljana,yayi saurin riko hannuta yajata,yace jameela 2 day I will prove u dat am not insane,ya masto da ita daidai gun hoton ya yaye Dan yanki da yasa mata,gaban jameela yafadi sa sauri ta dafe kirginta tace HIBBAT MUSTAFA
[10/15, 6:10 PM] +234 903 657 2265: 👸🏼AUREN KADDARA👸🏼
Na Aysha
Humairah (humeeynah)
18_19
A firgice ya dago kai yana kallonta yana nanata sunan da tafada hibbat mustapha,ya bude baki da sauri yace Jameela kinsan ta ne?kina nufin rayayiyace?akwai irinta a duniya? Kina da tabbacin ita din mutum ce?ta xaro ido tace kawarai kuwa Khalid,toh ai ni abin ne ya daure min kai,kana nufin wannan kake mafarki? Ya daga kansa yana kallon hoton da yaxana,ta kara xaro ido tace wannan abin da ban alajabi ya ke,Khalid ya jiyo cikin raunin xuciya yace kinsan Inda take?har tabude baki xatayi magana sai kuma tayi shiru,tayi saurin cewa kabani kwana biyu xanxo maka da full details dinta,ya riko hannunta yace jameela plzz make ma dream comes ture,tayi murmushi tafita ba tarai da tace komai ba,
Tana isa gida ta dauko wata Jakarta ta bude ta dauko wani Album tana dubawa caraf idonta ya tsaya akan hoton hibbat sai murmushi take a harabar makaranta su dake birin London,jameela ta tsurawa hoton ido sosai tace tabbas u are d one hibbat,but how comes kika xama dream gal din masoyina,dana Dade INA so amma shi yake wulakantani a sanadiyar ki,ta dafe kanta,tace ohhhh wannan lamari kamar a film,chan kuma tadago kai da sauri ta na murmushi tace yes wannan hanyar da ita xan cika burina, tayi tsalle ta dira kan gadonta ta na murna
Zaune take tana game a wayarta,tana kuma jin wakar a earphone dinta,ya fudail ne yafito daga cikin gida ya hangeta a harabar gidan, cike da mamaki yayi sauri ya dubi a gogon hannusa ya ga takwas da rabi na safe,da hanxari ya nufi gunta,bata Masan ya shigo ba sabda ta toshe kunnan ta da earphone din wayarta,yaxare earphone din yace sis kinsan ko karfe nawa yanxu baki dama niyyar shirin tafia gurin aiki,ta yi murmushi tace bros wlh na ajiye aikin ne,da hanxari ya xagayo yana kallonta suna facing din juna,ya rike mata hannu yace hibbat hope every thing is OK,ta Dan ya musta fuska sannan tayi murmushi tace wlh yaya fudail ba komai kawai INA son Hutu ne yanxu, shiyasa na ajiye aikin, ya daga kai badan ya gamsuba,ya shafi kumatunta yace OK toh ni xan fita office, ya daga mata hannu ya fice, tayi ajiyar xuciyar tana so tafada masa amma batason wani abinda xai daga ma yayanata hankali
Karar wayarta CE ta dawo da ita daga xanchan xucin da take,ta dauka ta kara a kunne daga daya bangaran akace plzz kufito kofar gidan Ku INA son magana dake,tayi murmushin takaici cike da masifa tafara magana,look Anwar kadaina bibiyata mai xanxo nayi maka,Anwar ya marairaice fuskar yace plzzzz hibbat I know I hurt u amma kiyi hakuri, kixo ki saurareni,ta yi tsaki tace toh ganinan,
Tafito daga gida ta hango shi a cikin mota,ta nufi motar ta bude tashiga ta daure fuska tace gani hope bawani kuma tashin hankali kaxo dashi ba,cikin sanyi murya ya dubeta yace hibbat kiyi wa Allah da Annabi kiyafemin nasan na bata miki sosai,so nake kikoma office Dinki munfara jin dadin aiki dake wlh,kar ki daukeni a mastayin wani saurayinki kidaukeni a mastayin boss Dinki plzzz,Dan Allah ki dawo,kowa yana missing Dinki plzz, karkice A'a,ta numfasa tace toh naji amma karka samun damuwa baruwanka da ni,ya gyda kai cike da jin dadi yace toh nagode
Bacci yake mai cike da mafarke2 mai dadi,budewar kofar dakin ne yasa shi tashi a firgice,ta bude kofar dakin tana murmushi sanye take da Riga da wando Pakista, kanta ya sha gyara sai kamshi take zubawa, ta masto kusa da shi,ya ja tsaki yace jameela wai mai haka ne INA cikin bacci na XAKI xo har daki kitasheni,da sauri ta hau kan gadon ta rugumaishi tana wani shafashi ta sa bakinta daidai kunnasa tace plzz Khalid kabiya min bukatata nikuma nayi maka alkwarin nemo maka dream girl dinka,Cikin bacin rai Khalid ya tunkude ta yace jameela dama baki da hankali,da sauri ta bude Jakarta ta dauko hoton hibbat tace look Khalid wannan itace dream gal dinka ko?da rawar jiki Khalid ya karba yana kallon hoton yana surutai, tabbas itace plzz jameela yanxu tana INA,cikin murmushi ta masto kusa dashi tana kissing dinshi tace wlh xangayamaka amma kafara biyamin bukata ta plzz,A fusce ya tsinka mata mari,yace look ni bansaki nemanta ba kamar yadda ni kadai nake mafarkinta haka na xana ta , haka ni kadai xan naimota,dan haka kifita Kibani guri, A zuciye tace ohh yau ni kake kora sbd wannan,toh Albishirinka wannan yau ake daura AUREN ta wlh Khalid baxa kataba samun taba ,ta figi Jakarta ta fice da ga dakin
👸🏼AUREN KADDARA👸🏼
Na Aysha
Humairah (humeeynah)