Share this page
3 / 7
ce"E". Ya kwashi kanukan abinci ya wuce gaba. Mama ta ce"Sai ki tashi mu wuce, ƙiyamarki ta tsaya cak yau". Wani sabon kuka ya zo mata, duk nuƙu-nuƙun da ta tsaya yi don Mama ta yi gaba, abun bai yiwu ba, haka ta saka ta a gaba suka shiga mota, a ciki suka tarar da Alhaji Hashimu, sai kunyar duniya ta rufe Nuratu, duk da ba son shi take yi ba, amma ba ta so a ce zai yi mata kallon mara tarbiyya ba, haka motar ta yi tsit har suka ƙarasa gidan. Baba da abokansa biyu suna zaune a ƙofar gidan, ya taso da sauri ganin motar Alhajin, sai dai Nuratu tana fitowa ya gimtse fuska, yana huci. Wani mugun haushinta yake ji, gabaɗaya ta canza masa lissafi. Suka shiga daga ciki, a zaune Alhaji ya ce su tsaya, Nuratu za ta wuce ya ce ita ma ta tsaya, ta dawo ta tsugunna kanta a ƙasa tana hawaye. Baba ya ce"Don Allah Alhaji ka yi haƙuri, wallahi da na san da wannan badaƙalar a jikinta da ban yi maka alƙawari ba, ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba!". Alhaji ya ce"Na sani, kuma a yadda na samu labarin tarbiyyar Nuratu na san wannan ƙaddara ce, kar ku damu, ni tsakani da Allah nake son yarinyar nan, musamman yanzu da wannan ƙaddarar ta faru da ita, na san rayuwarta za ta iya shiga garari, saboda Baba ni na ji na gani, zan aure ta na kau da ido a kan komai, da an cire cikin shikenan". Baba ya fara jero godiya har da kukansa, Alhaji yana cewa "Babu komai". Sannan ya yi wa Nuratu nasiha sosai, tamkar tsakanin uba da ƴarsa, har ta ji a ranta wannan mutumin ƴaƴansa sun yi sa'ar uba, ba kamar ita ba, ya ƙara da roƙon Baba kan kar ya ce zai dake ta, ko wani hukunci, addu'a ita ce kaɗai mafita, daga haka ya tafi, ita ma ta shiga gida, ta saka sakata a ɗaki, duk bugun da Baba ya yi ba ta buɗe masa ba. Ba ta taɓa zaton mutumin nan zai ce zai aure ta a hakan ba, ta san auren nasa rufin asirinta ne, amma ya za ta yi da soyayyar Abdul ɗinta? Sai ta ɗakko wayarta, ta yi masa sallama ta whatsApp, yana online bai duba ba har tsawon mintuna, sai ta danna voice, sai dai ta kasa cewa komai, har tsawon sakan goma, sai ta sake shi a hakan ya tafi, wannan karon da wuri ya duba, bai ce mata komai ba, ta ajiye wayar ta kwanta. Can tsakar dare kuma ta tashi ta fara haɗa kayanta a wata tsohuwar akwatin Mama, wanda ta bar mata ita, kayanta ne dama a ciki, ta saka komai ta ajiye ta tsaf, sam ba ta runtsa ba, kiran sallar farko a kunnenta, ta fito a hankali, tana jan akwati ta fice daga gidan a hankali, ta karo ƙofar, ta fara sauri don gudun wani ya biyo bayanta, tafiya mai nisa ta kai ta tasha, ta tarar da tsirarun mutane, ta zauna ta fara hawaye tana fatan Allah Ya sa a karɓe ta a inda za ta je, sannan ta samu buta, ta yi alwala ta yi sallar asuba wanda har an kusa idarwa. Ta faɗawa kwandasta Kaduna za ta je, aka saka ta a motar, ta yi zaune tana jira ta cika, zuciyarta tana ta dukan uku-uku. A daidai lokacin ne kuma Mama Asabe ta leƙa ɗakinta, ta ga ba ta nan, nan ta hau cikiya a tsakar gida, kowa ya fito ana jajantawa. ******** Misalin ƙarfe goma Nura ya kira Hasana a waya, tana ɗagawa ya ce"Ke maza ki buɗe wannan ɗakin ki share shi tass! Gani nan zuwa". Ta san dai ɗakuna uku ne a gidan, ciki da falon da take ciki, sai kuma falle ɗaya, wanda take saukar baƙinta, da kuma keken ɗinkinta a ciki, ta san shi yake nufi, amma hakan bai hana ta tambayarsa ba"Wane ɗakin?" Ya ce"Wannan wace irin tambaya ce? Ɗayan ɗakin nan dai, da kike saka shirgi, ba na so na zo na tarar da komai a ciki". Ta ce"To saboda me? Yanzu ina zan kai keken nawa?" Ya ce"Wannan kuma ya rage naki, idan za ki kai shi bola zan taya ki". Ya kashe wayar. Ta zauna tana mamakin me zai saka a cikin ɗakin? Ta san halinsa yanzu sai ya zo ya fara yi mata hayaniya, don haka ta tashi, ta fito da komai, ta share kamar yadda ya ce, ta janyo ƙofar ta koma ɗakinta, can anjima sai ga shi yana shigo da kaya, katifa ce madaidaiciya, da kayan kallo, har da ƙaramin firji, ta cika da mamaki, tana tsaye ya fara shiga da kayan yana ƴar waƙarsa, da alama yana cike da nishaɗi, ganin ko kallo ba ta ishe shi ba, sai ta shige ɗakinta, tana jira ya gama ta ji bayanin da zai yi mata. Ai kuwa yana gamawa ya ƙwala mata kira, ta fito tana amsawa, ya ce"Shigo mana". Ta shiga tana ƙarewa ɗakin kallo, ya ce"To yanzu saurana sif, zan sa a yi mini sif mai biyu ƴar madaidaiciya haka, wacce zan zuba kayana a ciki, kin ga komai na zai zauna lafiya, idan zan fita na rufe ɗakina shikenan". Da mamaki ta ce"Kamar ya ɗakinka? Au wai nan turaka ce ka ware kenan?" Ya ce"Ai ya wuce wai, ni na gaji da yadda nake bacci rabi da rabi, yara su hana ni bacci su hana ni sakat, tsakar dare a farka a yi ta kuka, don haka na ware ɗakina". Hasana ta ce"Baban Salim kenan! Kuma ban da abunka na ga dai yaran nan naka ne, sannan abu ba na farko ba, ba na biyu ba ai ya kamata zuwa yanzu a ce ka saba, kuma ma yanzu don ka yi hakan ai ba shi zai hana ka jin kukan Aiman ba, tun da dai ka san ba zan zo na kwana a nan na baro yaro ƙarami mai shan nono ba, dole da shi zan dinga tahowa". Nan take fara'ar fuskarsa ta gushe, ya ce"Ki taho ina? Wai kina nufin saboda na ware ɗaki sai ki kwaso jiki ki biyo ni? Kenan ma na gudu ban tsira ba! A'a ba zai yiwu ba, ki yi zamanki da yara, ni duk sanda na buƙace ki zan kira ki, amma gaskiya ba don mu tare mu biyu na ware ɗakina ba". Ta ce"To shikenan!" Ta juya ta fice, ranta bai so ba, sam ba za ta samu nutsuwa ba, saboda zarginsa da take yi ne zai ƙaru sosai, haka kawai ma tsakar dare farkawa take yi ta ga ba ya ɗakin, sai ta ji shi a tsakar gida yana waya, ko ta gan shi a falo yana vedio call, sai ya ganta ya yi tsaki, ya koma ya kwanta, to ina ga kuma ya ware ɗakinsa shi kaɗai? Tabbas zai ci karensa babu babbaka kenan, ta san ba ta isa ta ja da shi ba, amma kuma za ta yi iya yinta ta saka masa ido, don ganin bai kauce hanya ba, don haka ta ayyana bacci da ido ɗaya ya kama ta. Haka ya wuni yana shige da fice, ya saita kayan kallo tsaf, dama akwai babbar setilait a tsakar gidan, tun da risibarsu ta lalace take ajiye kawai, bai kai musu gyara ba, yanzu sai ya sa aka saita da sabuwar risibar da ya siyo, firji ma nasu ya lalace bai kai gyaran ba, don ya ce ya gaji da gyarawa suna lalatawa, ita kuma a ganinta tsufa ya yi, tun da tun na aurenta ne, shekararsa takwas kenan. Ya ɗakko yara daga makaranta, suna zaune suna cin abincin rana, yake cewa"Ma sha Allah! Ɗakina ya haɗu, yanzu mun yi magana da wani kafinta, zuwa jibi sif ɗina za ta zo, sai na samu ɗan kafet, na saka a tsakiyar ɗakin, ina ga ma sai na sayi senta tebur". Hasana ko kallonsa ba ta yi ba, saboda takaici duk ya ishe ta. Ya cigaba da cewa"Yadda tsarin gyaran ɗakin zai kasance, da safe idan na gama shiryawa, ina zaune ina karyawa, ke kuma sai ki shiga ki gyara, idan zan fita na rufe abuna, salun-alun karatun yankan jaki". Har yanzu dai ba ta ce komai ba. Sai ya ajiye kofin hannunsa yana haɗe gira ya ce"Wai ni Hasana me kike nufi ne? Ya ina magana kina manna mini hauka? Ko hassada kike yi da ɗakin nawa?" Ta ce"Hmm! A kan me zan yi maka hassada? Kawai dai gani na yi tsarin kamar bai yi ba, a ce kana da mata ita tana ɗakinta, kai kana naka, wai sai ranar da ka kira ta? Ka manta sai ka yi wata ba ka kira ni ba?" Ya ce"To mene ne? Ke ba hutunki ba ne ba ma? Ki sake a ɗakinki, na sake a ɗakina". Salim Ya ce"Abba wane ɗakin?" Gwab! Hasana ta buge bakin yaron, tana cewa"Ban hana ka saka mana baki a magana ba? Waye sa'anka a nan?" Sai kuwa Nura ya hartsuƙo kamar zai dake ta, yana cewa"Kar ki sake ki ƙara dukan shi, saboda ya tambaye ni? Da ke yake? Ba ki iya komai ba sai shirme!". Ya tashi yana ɗaukar mukullin babur ɗinsa ya fice zuwa tsakar gida, yana kiran Salim ɗin, ya je ya buɗe masa ɗakin suka shiga, sai da ta ga za su yi lattin islamiyya sannan ta leƙa tana cewa"Ku zo ku tafi makaranta". Salim Ya noƙe kafaɗa yana cewa"Daddy ni yau ba sai na je ba". Hasana ta ce"A kan me? Ai kuwa ya zama dole ka je!". Nura ya ce"Ƙyale shi, ƙila ya gaji ne". Ta juya ta koma ɗaki, tana jin sanda suka fita, ya siyo musu biskit ya dawo da su, tana zaune ranta a ɓace, saboda ta gaji da yadda yake ɗaurewa yaran akan rashin son karatun addini, ya ce"Ki biya musu karatun, tun da ba su samu zuwa ba". Ko kallonsa ba ta yi ba, ya fice daga gidan. Ta ja kunnen yaron ta murɗe tana cewa"Idan ka girma za ka gane ba gata yake yi maka ba!". Ƙarfe sha biyu na dare, Hasana ta kasa bacci, tana tunanin me Nura yake yi a halin yanzu? Ya yi bacci, ko yana ta waya da ƴan mata? Tunanin ya kasa barinta, don haka ta tashi, ta saka hijjabi, ta buɗe ƙofa a hankali ta fito, ta je daidai windon ɗakin ta leƙa, ta kuwa hango shi zaune ya yi ɗaiɗai a kan katifa, yana ta danna waya, wani abu ya zo ya dunƙule mata ƙirji, kamar ta buga masa ƙofar, sai kuma ta ga me ma za ta ce masa? Ta daɗe tana kallonsa ba tare da ya sani ba, sannan ta juya ta koma ɗaki, ta kwanta, sai ta ji ɗakin ma yau ya mata girma, gadon ya yi mata faɗi, duk da dama yawancin daren da bacci suke raya shi, amma duk ranar da ba ya nan tana jin babu daɗi. 08028966015 [11/20, 3:36 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee PAGE 5 Washegari da safe Hasana ta gama haɗa abun karyawa, tana shirya yaran, Nura ya shigo yana cewa"Ki je ki gyara mini ɗakina". Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ya sake cewa"Hasana magana fa nake yi". Ta ce"Ni fa wannan raba ɗakin ba lallai ya zama maslaha ga rayuwar aurenmu ba, saboda haka ya kamata a sake sabon tsari". Ya tsaya yana kallon ta da mugun mamaki, ita kuwa da ba kallon shi take yi ba, ballantana ta lura da yanayinsa, ta cigaba da faɗin"A gaskiya sai dai ni ma na koma can ɗin, idan saboda Aiman ne, ni zan dinga yin shimfiɗata a ƙasan katifar mu kwanta". Takaici ya ma hana shi tsayawa jayayya da ita, dogon tsaki kawai ya ja, ya ce"Allah Ya raba mu da jahilci". Ta ce"Ni ce jahilar!?" "Duk yadda kika ɗauka haka nake nufi!" Ya faɗa yana jan kwanon abincinsa. Ta shige ɗaki ta yi zaune a bakin gado, ta rasa ta hanyar da za ta bi ta daƙile wannan sabuwar badaƙalar da yake son ƙullawa, sam ba ta yarda da shi ba, ta san bayan uzurin da ya kawo mata, dole yana da wata manufa ta raba ɗakin nan da ya yi. Haka suka gama karyawa suka fita tare da yaran, ya kulle ɗakinsa yana mamakin sabon hali na raini da take son tsiro da shi a zaman nasu. Da azhar da ya ɗakko su daga makaranta, yana shigowa fuska a murtuke, ya ɗauki tsintsiya ya share ɗakin, sannan ya haɗa ruwan mopping, har ya fara zuciya ta ciyo shi, shaiɗan ya yi zuga, ya fito a fusace, tana cirewa yaran unifom ya ce"Ke Hasana wai me kike nufi ne? Ɗan iska kika mayar da ni ko yaya?" Ta ce"Kamar ya?" Ya ce"Ta ya za a ce ga ki a gida ni zan share ɗakina? Mene ne amfaninki!?" Ta ce"Ka fi kowa sanin amfanina". Ya ce"Ki je ki gyara mini ɗaki Malama, ku mata sam ba ku da tunani wallahi, ba dole ma mutum ya ƙara aure ba? Hmm Allah dai ya hore, zan huce takaici tabbas". Hasana ta yi murmushin takaici ta ce"Ai wallahi ni na fi so ma ka ƙara auren, ta nan za ka san haƙurin da nake yi da kai". Ya ce"Ki kwantar da hankalinki, ai in sha Allah aski ya zo gaban goshi, wallahi da wannan siyayyar da na yi, kuɗin aure zan kai, to kawai na fi so lissafin komai ya tafi daidai shiyasa na jinkirta, amma kar ki damu indai aure ne dole zan yi shi". Ta ce"Allah Ya nuna mana". Ya yi ƙwafa, ta fice ta shiga ɗakin, ta ga wayarsa a kan katifa, ta raya ƙila mantawa ya yi, ta yi saurin ɗauka, sai dai da pasaword kuma ba ta san mene ne ba, ta yi ƙwafa ta ajiye ta, ta gama gyara ɗakin ta fito. Ta same shi a falo ta ce"Yanzu haka za mu dinga ganinka kai kana yin kallonka mu ko oho?" Ya ce"Tun da haka kika zaɓa ba!Na gaji da kai gyaran kayan kallo wallahi". Amir ya ce"Don Allah Daddy a gyara mana". Salim ya ce"To ai sai mu dinga yi a ɗakin Daddyn". Bai ce komai ba, ta kawo musu abincin rana suka fara ci, Nura ya yi kamar cokali uku ya taɓe baki ya ce"Abinci ma ba za a nutsu a yi shi ba, Allah Ya kyauta". Hasana ta yi kamar ba ta ji shi ba, don ita ma ta san gishirin ya yi yawa, ta manta shaf ta zuba, dab da za ta gama girkin ta ƙara zubawa, don haka ba ta da ta cewa. Ya sake tsaki ya ce"Wannan abincin dai ci kar ka mutu kawai, an zabga wa mutane gishiri a abinci" Ya sake tsaki. A fusace ya ce"Ina ta magana...!" Ta ce"To me kake so na ce? Ku maza dama haka kuke, sai mace ta yi daidai sau dubu, ba za ku tabe ta ba, amma idan ta yi ba daidai ba sau ɗaya sai kun yi ƙorafi, hannuna ne ya kufce na saka da yawa". Ya ce"Hmm! Gaskiya na yarda, duk wanda ya mutu da mace ɗaya shi ya ga ƙarshen wulaƙanci, gida biyu maganin gobara, Allah dai Ya kai damo ga harawa!". Ba ta sake bi ta kansa ba, har ya gama ya fice. Yau da daddare da wuri ya dawo, hakan ya sa Hasana ta raya a ranta ƙila yau ɗin ya kira ta, amma sai ta ji shiru, don ko leƙo su ma bai yi ba, tana jin lokacin da ya saka sakata a ɗakin, bayan ya gama uzururrukansa, kamar awa ɗaya a tsakani ta tashi ta sakko daga gadon, ta kalli agogo, sai yanzu goma ta yi, ta manta rabon da ya dawo gida kafin ƙarfe goma, sai dai idan ana tsananin sanyi, ko kuma da damuna. Ta saka hijjabi, ta fito a hankali kamar jiya, ta leƙa ta windo, ta ga ɗakin da hasken tv ga kuma sauti alamar ya kunna kallo, amma yana kwance a katifa waya kare a kunnensa ga murmushi shimfiɗe a fuskarsa, da alama yana cike da shauƙi, takaici ya rufe ta, duk abin da Nura yake yi mata na ɓacin rai, har yanzu tana ƙaunarsa, soyayya ce aka sha ta nuna wa sa'a kafin aurensu. Ta gama yankewa a zuciyarta sai ta hana shi sukuni, don haka ta koma ta wajen ƙofar ta fara ƙwanƙwasawa. Nura da ya nutsa a kofin soyayya da wata wacce ya yi mata laƙabi da baba Leemat, sosai ya yi mamakin wannan bugun ƙofar, da ya dawo sai da ya duba ƙofar Hasana ya ga a rufe, kuma ya santa da baccin wuri, ya ce da baba Leemat yana zuwa, ya katse kiran yana haɗe gira ya ce"Wace?" Ta ce"Ni ce". Ya zo ta buɗe yana cewa"To ya aka yi, ni har na fara bacci ma?" Za ta kutsa kai ciki, ya ɗan tare yana cewa"Wai mene ne?" Ta ce"Akwai wani film da nake kallo a bollywod, shi ne na ce tun da akwai wuta ga ka, ka dawo da wuri bari na zo na ci albarkacin turakar Oga". Ta ƙarasa da murmushi. Sai ya matsa ta shige ta zauna, ta canza tasha, amma gabaɗaya hankalinta yana kanshi, wayarsa tana ta kawo haske ya ƙi ɗauka, can dai ya tashi ya fice daga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakinta a hankali ya shiga, ya haska ya ga Aiman ya baje yana ta baccin shi, ya ji fanka, ya kai hannu ya fara jijjiga shi, yaro kuwa ya fara mutsu-mutsu, sai ya tashe shi ya zaunar, ai kuwa ya fara ƙananun kuka, ya yi saurin ficewa daga ɗakin. Ya koma nashi ɗakin yana cewa"Na ji kamar kukan Aiman". Ita ma ta jiyo sama-sama, don haka ta tashi, ta ce"Bari na ɗakko shi". Ya ce"Ina? Kin ga Malama ki yi kwanciyarki kawai, saboda ni ma bacci nake ji". Tana fita ya mayar da sakata. ********* Baba ransa ya kai maƙurar ɓaci, ya kai ya kawo a tsakar gida rungume da hannuwa a bayansa, ya ma kasa cewa komai. Can Mama Karime ta ce"Malam ba fa shiru za ka yi, kamata ya yi a bi sahunta tun kafin ta yi nisa". Sai kuwa ya zaburo kamar mai jira, ya ce"To a gidan uban wa zan nemo ta? Ni dai na san abu ɗaya, yanzu Nuratu baƙinciki da hassada kawai take yi mini, wallahi saboda ta hango ɗan abin da zan samu a jikinta shiyasa ta yi mini haka, amma babu komai". Ya shige ɗakinsa. Ita kuwa Nuratu motarsu tana harbawa titi, ita ma ta harba duniyar tunanin makomarta, sam ba ta hango haske a gobenta, ta san babu ta yadda za a yi Abdul ya karɓi uzurinta, fatanta ya yarda da ita ko da ba zai aure ta ba, ita ta yarda ta sadaukar da mutuncinta don farincikinsa. Sai dai idan bai aure ta ba, wa zai aure ta ya kalleta da mutunci? Gani take shi ma Alhaji Hashimu da ya yi alƙawarin aurenta ya yi maganga ne kawai a cikin mayen giyar so, bayan auren ba lallai ya riƙe ta da daraja ba, sannan yana da mata har uku da yaran da ba ta san adadinsu ba, ta tabbata wasu sun girme mata, yanzu ya za ta yi idan suka ji ta yi ciki a waje kafin auren? Anya gori zai bar ta ta zauna lafiya? Da wannan tunane-tunanen fal zuciyarta aka ƙarasa Kaduna, kowa ya sauka, ta samu babur ya ƙarasa da ita unguwar da za ta je, sai da ta kai ƙofar gidan sannan ta fara fargaba, ta san dai wannan tafiyar ba gudu sunanta ba, don inda ta zo ɗin ba mafaka ba ce ba, kawai ta zo ne saboda ƙwaƙwalwarta ta samu hutu, kuma zuciyar Baba ta yi sanyi, don idan ya tashi yi mata hukunci ta samu sassauci. Ta kai hannu tana ƙwanƙwasa get ɗin gidan, sai da ta buga sau uku, sannan daga ciki aka tambaya waye, ta ɗaga murya ta ce"Ni ce". Babu jimawa aka buɗe, wata mace ce wacce za ta kai shekara ashirin da bakwai ta buɗe, ta ɗan saki fuska ta ce"Nuratu" Tana kallon tsohuwar akwatinta. Nuratu ma ta ɗan saki fuska ta ce"Anti Nawwara". Ta matsa mata, ta shiga jaye da akwatin, Nawwarar ta yi gaba tana binta har zuwa falo, ta zauna, ita kuma ta ƙwala wa mijinta kira"Honey!". Sai ga shi ya fito, yana gyara agogon hannunsa, ya yi turus ganin Nuratu, da mamaki ya ce"Nuratu, ke ce kuwa?" Sai idonta ya kawo ruwa, ta ce"Ni ce, Yaya Kabir ina kwana". Bai amsa gaisuwar ba, ya ce"Amma dai ba lafiya ba ko Nuratu?" Nawwara ta ce"Ina fa lafiya? Ko sadakar ukun babarta ba a yi ba, ka ga ta yo nan ai ka san akwai matsala". Ya ce"Mene ne ua faru Nuratu?" Sai ta fashe da kuka. Nawwara ta ce"A'a yi haƙuri, ta huta tukunna, kafin nan zuciyarta ta yi sanyi ma". Ta ja hannunta, ta kai ta ɗaki, ta zaunar a bakin katifa, ta koma kitchen ta haɗo mata shayi da biredi, har ma da sauran dankali da suka rage, ta kai mata, ta ce"Maza ki ci". Dayake gidan ba baƙonta ba ne, sai ta fara tashi ta yi wanka, ta canza kaya, sannan ta ci abincin, ta ɗakko wayarta, ta kunna data, saƙonni suka gama shigowa tass babu na Abdul, hawaye ya sakko mata, ta san yana can cikin ƙunci, ta yi masa sallama a rubuce, ba ya online, babu jimawa kuma ta ga tik biyu, alamar ya hau, ya duba saƙon nata, sai ya fara typing, tana ta fargabar abin da zai rubuto, har ya gama ya turo, "Wannan shi ne sakayyar soyayyata a gare ki ko? Na gode Nuratu, Allah Ya saka da alkhairi". Abin da ya rubuta kenan, sai ya bi bayansa da stika ta namiji yana kuka sosai. Ita ma kukan ta fara, ta danna viice ta ce"Na san ban cancanci ka saurare ni ba, amma don Allah ka daure ka ji bayanina, ba don halina ba, na yi komai ne saboda cika maka burinka, rayuwarka ta inganta". Bayan ya saurara ya tura mata emoji na mamaki, ta sake yin voice ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, ka fahimce ni, na fi kowa shiga ƙunci sanadin wannan kuskuren da na yi". Ta typin ya ce mata"Cikin wane ne? Kar ki ba ni amsar da za ta wuce kalma uku, don ba ni da lokacin sauraron tsarinki". Sarai ta san halinsa, tun da ya ce haka, idan ta ba shi amsa akasin yadda ya buƙata, zai iya yin blocking ɗinta, don haka ta rubuta masa "Agent ɗin da ya yi maka hanyar tafiyarka ne" Ta tura masa. Abdul yana karantawa, ƙirjinsa ya doka da ƙarfi, ya fara karanto innlillahi wa inna ilaihi raji'un! Ya fara tunanin yanzu a kan shi ta ba da kanta ga wani banza? Nan ya tuna ranar da yake tunanin abun ya faru, da abokinsa Usman ya ce masa, ya ganta ta fito daga mota tare da Agent ɗin nan, amma Abdul fir ya ce ba ita ba ce, sannan a ranar mutumin ya kira shi ya yi masa alƙawarin tafiya. Ya kashe data yana mamakin irin _zuciyar mace_. 08028966015 [11/21, 11:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 6 Shiru bai ma sake kunna data ba, ballantana ta ji hukuncin da zai yanke, ta sake tura masa saƙo, ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, ni ban ce dole sai ka aure ni ba, kawai dai ka yarda ba yaudara ce ta saka na yi haka ba, ba kuma son abin duniya ba, kawai na yi ne saboda na taimake ka". Ta ajiye wayar tana tuna ranar da ya zo ƙofar gidansu, jikinsa a mace, yana faɗa mata Agent ɗin ya ce yau ce rana ta ƙarshe, idan bai kawo kuɗin nan ba, babu shi a tafiya, sai dai ya sake nema a gaba, abokansa uku duk sun biya, shi ne kaɗai ba shi da shi, ga shi mahaifinsa

Chapter 3 of 7