Share this page
7 / 7
sai ta kasa yi masa godiya tun da zuwa yanzu ta fahimci ba don Allah yake yin komai ba. Da suka dawo gida sun tarar da Nawwara a falo, ta yi mamakin ganin shi ne ya ruƙo kayan ba Nuratu ba, sannan ba ta ce komai ba, ta wuce ɗaki, shi ma sai da ya ji ƴar fargaba, Nawwara ta ce"Lafiya kuwa, na ga ranta a ɓace?" Ya ce"Wallahi wani ne ya biyo mu wai yana son ta, na faɗa masa matar aure ce, to shi ne fa a mota har da kukanta, tana cewa ban da ƙaddara da tana tare da mijinta ai da wani bai ganta ba ma, ballantana ya ce yana sonta". Nawwara ta yi murmushi ta ce"Nuratu kenan, ni dai ban ga abun fushi a nan ba". Ya ajiye kayan, ta ɗauka ta buɗa tana cewa"An samo curryn?" Ya ce"To ina ma ta bi ta kan wani curry, lokaci ɗaya fa ta birkice kamar mai aljanu". Nawwara ta ce"To Allah Ya kyauta". Ta kwashi kayan ta miƙa mata, ta tafi ɗakin mijinta. Nuratu ta zauna tana ta tunanin mafita, indai wannan manufar ce tabsaka Yaya Kabir ya nemi ta zo ta zauna a gidansa, to kuwa gara ma ta zauna a gidan su Abdul ɗin, ba ta fatan ta sake aikata wani kuskuren a kan wanda ta yi, zina babban bala'i ce, ga shi ta sanadin aikatata sau ɗaya ta shiga masifar da take neman yi wa rayuwarta juyin waina cikin baƙar tanda, lallai gidan Yaya Kabir ba wajen zamanta ba ne, ya zama wajibi ta tattara ta koma inda ta fito. Bayan ta gama shirin bacci, sai ta ɗauki wayarta, ta kunna data, ta yi wa Abdul sallama ta gaishe shi, sannan ta ce"Na sauka lafiya tun ɗazu, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya". Yana dubawa sai ta ga ya fara typin, daɗin zai kula ta da kuma fargabar abin da zai rubuto suka dira a zuciyarta lokaci ɗaya, yanzu har tana fargabar jin furucinsa a kanta, saboda ba ya faɗa mata magana mai daɗi. "Ke da waye yanzu a ɗaki?" Abin da ya rubuto kenan. Ita ma rubutun ta yi masa ta ce"Ni da kewarka ne, ka san gidan babu yara, ni kaɗai ce a ɗakin da aka sauke ni". Ya ce"Za ki iya yi mini vedion kanki a halin yanzu?" Ta ce"Gaskiya ba zai yi ba, saboda wayar babu flash". Ya ce"To gobe da safe ki yo mini vedion jikinki, ban ce ki saka kaya ba, saboda ina buƙatar ganin halal ɗina ne". Sai da ta ji gabanta ya faɗi da ta karanta, ta sake maimaita karantawa, ta yi mamaki, tun da ta ga yana ta nuna rashin damuwarsa a kanta, sannan ma ta lura kamar dole ce ta saka ya yarda da aurenta, amma har a ce yana jin kewarta da ta kai har yana neman ganin ko da hoton jikinta ne?" Ganin ta duba saƙon ba ta ce komai ba, ya sake rubuto"Ko ba zan samu ba?" Ta rubuta masa"Allah Ya kai mu goben". Ta ma rasa ta ina za ta fara wannan abun da ba ta taɓa yi ba, amma ta sani a yanzu Abdul mijinta ne, wannan ba haramci ya nemi ta aikata ba, sai dai tana jin nauyi kuma ta ga abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Tana cikin duba saƙonni sai ga saƙon Yaya Kabir ya shigo, stika ce ya turo mata ta mace da namiji rungume da juna, sannan ya yi gajeren rubutu ya ce"Zan kwana da kewarki". Don takaici ba ta san sanda hawaye ya sakko mata ba, ta kashe data ta kwanta tana jin zuciyarta babu daɗi, ga kuma rashin nutsuwa a tare da ita, ta san a yanzu idan ta ce za ta koma gida ba ƙaramin yaƙi ta ɗakko ba tsakaninta da Baba, da haka ta yi bacci kanta a cushe. Washegari da sassafe ta ji motsin Nawwara, ta fito ta gano ta a kitchen, ta shiga ta gaishe ta, sannan ta fara taya ta aiki, suna gama komai ta koma ɗaki, sanda suka fito karyawa Nawwara ta zo ta kira ta, ta ce"Anti sai anjima zan karya". Saboda ko ganin Kabir ma ba ta son yi. Bayan sun gama karyawa Nawwara ta leƙo tana ce mata "Za mu tafi" Ta ce"To Anti, me za a dafa muku kafin ku dawo?" Ta ce"Ki dafa duk abin da kike ra'ayi, sai mun dawo". Ta ce"A dawo lafiya". Bayan sun tafi, ta fito ta ci abinci, ta yi wanke-wanke, ta share gidan ta gyara komai tsaf, maganar Abdul tana maƙale a zuciyarta, don haka ta tashi ta yi wanka, ba ta ji a zuciyarta za ta iya yin vedion kamar yadda ya ce ba, don haka ta yanke za ta saka rigar bacci, sai kuma ta tuna ba ta da wata rigar bacci, rigunanta marasa nauyi ma duk sun tsufa sun ji jiki, ba za ta iya yi wa miji kwalliya da su ba, ta tsinci kanta da duba ledar kayan da suka siyo jiya, ta kuwa ga kayan bacci kala uku, ciki har da wata riga ta net mara kirki sosai, sai ta saka ta, ta ɗauki kanta a hoto, ta kunna data, da saƙon Kabir ta fara cin karo, da alama tun jiya ya turo, don cewa yake yi"Na zo na taya ki bacci?" Ta yi tsaki, ta shiga lambar Abdul ta yi sallama ta gaishe shi, sannan ta tura masa hoton da ta ɗauka yanzu, yana dubawa ya ce"Mene ne wannan?" Ta ce"Ba zan iya yin hoto babu kaya ba". Ya ce"Amma za ki iya ba wa wanu kanki ai ko? Kuma vedio na ce, sannan ina son ganin fuskarki sosai a vedion". Ta sauke gwauron numfashi, sai dai ta kasa cire rigar, don a ganinta rigar nan ta jikinta da ita da babu duk ɗaya suke, ta yi vedion a haka da rigar, ta tura masa. Tana turawa ta ajiye wayar tana jin babu daɗi, duk da ba haramun ba ne, sai can anjima ta ɗauki wayar domin ta ga amsar da ya bayar, ƙirjinta ya yi wata mummunar bugawa ganin kamar mutum biyu ta turawa, da sauri ta kalli lambar Yaya Kabir wanda har saƙon ya nuna blue tik alamar ya gani, ta miƙe tsaye tana ɗora a ka, ita ta ma manta da ana delete saboda yadda kanta ya ɗauki zafi, salati kawai take jerowa, wajen minti biyar kafin ta dawo cikin nutsuwarta, ta zo ta goge da sauri. Kabir wanda daɗi ya gama rufe shi, don wannan alama ce da take nuna ta gama amsar tayinsa, tuni ya tura shi zuwa laptop ɗinsa don ya more kallo da kyau, saboda haka ko da ya ga ta goge bai wani damu ba, sai ma stikar godiya da ya turo mata. Shi kuwa Abdul a na shi ɓangaren, yana kallon vedion zuciyarsa tana tafasa, wani kishi ne yake azabtar da zuciyarsa, a fili ya ce"Nuratu in sha Allah wannan vedion sai ya zama silar shigarki ƙunci na har abada, wannan vedion sai ya hana ki zaman aure, sai kin dawwama a gida kin tsufa kin mutu babu aure, babu ɗa babu jika, wannan ce hanya ma fi sauƙi da zan rama cin amanar da kika yi mini" . LAST FREE PAGES! To mutanena mu numfasa a nan, ko kun hango girman matsalar da Nuratu ta jefa kanta kuwa? Shin da gaske Abdul zai iya take ƙauna ya aiwatar da furucinsa a kan wacce ya fi so duk duniya, ashe ƙauna tana rikiɗa ta zama ƙiyayya? Yaya Kabir zai yi da wannan vedion? Shin zamanta a gidansa zai yi tsayi ko na ɗan lokaci ne? Na ba ku satar amsa? Nura zai yi ta aure-aure a wannan labarin, amma a ƙarshe ya zamansa da Hasana zai kasance? Akwai tarin ƙadarori a kan Nuratu, ku dai kar ku bari a yi babu ku, da ɗarinki biyar ki sha karatu. 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay bank Shaidar biya ta nan 08028966015 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7