Share this page
5 / 7
ƴaƴanta, shiyasa Mama ma ta kama sana'ar waina kafin rasuwarta, ga shi yanzu har an ɗora Khadija a kai, dama tare suka yi Candy da Nuratu, kuma babu maganar miji, ballantana cigaba da karatu. A cikin satin da aka yi arba'in, sai ga Baba ya zo cikin gida da zancen gobe iyayen Abdul za su kawo sadaki a ɗaura aure, zuciyarta ta dinga dokawa, sai ta nemi farinciki ta rasa, ba ta taɓa hasashen aurenta da Abdul zai zo ta wannan yanayin ba. Matan na shi suka tambaye shi za a yi biki ko ita Nuratu za ta yi ƴar walima? Ya ce babu wani taron banza da za a yi, a wannan auren na larura, da an ɗaura aure a masallaci shikenan, shi babu wani gayyata da zai yi ma. Duk da haka sai da suka kira ƴan'uwan babarta da na Baban suka sanar da su, washegari misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Nuratu da Abdulmalik a kan sadaki naira dubu hamsin, duk da an ce babu taron sai da ƴan'uwa na kusa suka zo, ƴan'uwan babarta suka auno shinkafa kwano biyu aka dafa kowa ya ci, an yi sa'a Baba ya zo ya damƙa mata kuɗin sadakinta, ta ajiye a gefe tana kuka, yayar babarta ta ce"Kawowa za ki yi a adana miki, wannan uban naki tsaf zai biyo ya ce ki bada". Wata ƴar'uwarta ta ce"Kamata ya yi a dinga juya su, ƙila zuwa sanda zai dawo ta tare su isa a siya mata katifa mai inganci". Duk suka yarda da shawarar. Nan suka tambaye ta batun lefe,ta ce ita ma ba ta sani ba, suka hau faɗa suna cewa wannan ai rainin wayo ne, babu lefe kuma ya ba da sadaki dubu hamsin? Ai arahar ta yi yawa, ita dai ba ta ce komai ba, domin ta san ita ce ta ja komai, a ganinta Abdul ya yi mata halakci ma da ya yarda zai aure ta, ya kuma ɓatawa kansa suna a duniya, don haka ba ta da ta cewa, zuwa magriba kowa ya kama gabansa. Da daddare sai ga Baba ya shigo yana kiran Nuratu, ta zo ta tsuguna, ya ce"Ina kuɗin sadakin? Ai sai ki kawo gobe a siyo miki katifa". Ta ce"Baba ai na za ta sai ya dawo". Ya ce"Au dama nufinku auren kawai aka ɗaura, na siyar da akuya kuma za ta cigaba da cin dangata? To wallahi ba zai yiwu ba, ko dai ya kama miki haya, ko ki tafi can gidan iyayensa ki tare, ni dai tun da na aurar da ke, to ya zama dole na gani a ƙasa, me za ki zauna ki yi a gida, da aurenki? A'a ba za a yi wannan shashancin da ni ba!". Nuratu jikinta ya yi sanyi, har ta fara hawaye, ta kuma kasa cewa komai. Baba ya ce"Ni shiga ki fito mini da kuɗin, na kama gabana!". A raunace ta ce"Ƴan'uwan Mama sun tafi da shi, su ma katifar za su siyo mini yau". Sai kuwa Baba ya rafka salatin da har mutanen gidan suka fito, ya ce"Yanzu ni na haifi ƴar, babu shegen da ya san cinta da shanta, har ta kawo moro, a ce ni ban kai a yi shawara da ni ba a kan sarrafa sadakinta!? Saboda tsabar rainin hankali! To maza shige mu je ki karɓo su!". Mama Karime ta ce"A'a Malam, wannnan fa ba wani abun tayar da jijiyar wuya ba ne, ni na tabbata mutanen nan ba za su cinye mata kuɗi ba". Mama Asabe ta ce"Wannan gaskiya ne, kuma su ma suna da haƙƙi a kanta, bai kamata a ce don an ba su kuɗi ka je ka karɓo ba". Ya ce"Cikinku nan akwai wacce ta siya mata wani abu na gudunmawa? Ko za ku bayar nan gaba? Ku fita harkar ƴata, babu ruwanku da tsarina!" Ya kalli Nuratu"Ke wuce mu je!". Dama da hijjabi a jikinta, sai ta wuce ya bi bayanta, suka tafi, suna zuwa ƙofar gidan ya tsaya, ta shiga a sanyaye, Mama tana ganinta ta ce"Nuratu! Lafiya kuwa cikin daren nan?" Ta fara kuka ta faɗa mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Ai dama na san ba zai bar wannan kuɗin ba, ai shikenan dole a bi yadda ya tsara, kunya ce dai za a sha ta daga baya". Ta ɗakko kuɗin ta ba ta, tana cewa"Ki yi haƙuri da duk abin da za ki gani Nuratu". Ta karɓa ta fita ta miƙa masa, sai da ya ƙirga su cif sannan ya saka a aljihu suka tafi, a hanya ma yana ta sababi yana cewa zuwa gobe ya ba su, dole su zo su san inda za ta tare. Ta idar da sallar isha'i ta kasa tashi daga sallayar, gabaɗaya rayuwar ta yi mata zafi, ta rasa inda za ta saka ranta, a gaskiya ba ta son zaman gidansu Abdul, gabaɗaya ɗaki uku ne a gidan, na iyayen ɗaya, na Abdul da ƙannensa maza ɗaya, sai na ƙannensa mata, yanzu a ina za a saka ta kenan? Ba gara ma a bar ta a nan ɗakin babarta ba, idan ya zo ya dinga turo mata da kuɗin abinci. Da shi ya kamata ta yi shawara, amma ya ƙi sauraonta sam, ba ta da mafitar da ta wuce ta sake tuntuɓarsa, don haka ta ɗakko wayarta, ta kunna data, yawanci datarsa a kunne take, sai dai idan ya ji shigowar saƙo ya duba, ta same shi online, ta yi masa sallama, tare da stikar hawaye, ya duba bai ce komai ba, ta yi masa voice ta ce"Assalamu alaikum, Yaya ina wuni? Fatan kana cikin ƙoshin lafiya, a yau burin nan namu na tsawon lokaci ya cika, mun zama mallakin juna, sai dai kuma abun ya zo mana akasin hasashenmu, wannan yana rubuce cikin ƙaddararmu, ya kamata mu karɓe ta, Yaya tun da an cire cikin nan don Allah ka manta da komai, wannan ya zama tarihi, a tunanina soyayayyar da muke yi wa juna ta yi ginuwar da wannan ɗan saɓanin bai kai ya rushe ta ba, ina ƙaunarka har gobe angona". Ya saurara bai ce komai ba. Ta sake cewa"Yaya ya ka tsara bayan auren nan? Yanzu zan zauna a nan gidanmu ne, ko haya za ka kama mini?" Sai ta ga ya fara typing bayan ya saurara, tana ta zumuɗin ganin me zai rubuto, sai ta ga ya ce"Ni na ba wa kura ajiyar nama? Kin san maza sannan kuma na kama miki haya? Mtwsss" Ya ƙarasa da tsaki. Hawaye ya sakko mata, ta ce"Ko kowa na duniyar nan zai zarge ni, ban taɓa tunanin har da kai ba Yaya, tabbas na yarda a yanzu duniya ba ta da tabbas, na gode da komai, sannan zan ɗauki ƙaddarar zama da kai a duk yadda ka tsara zaman namu". Sai ma ya kashe data ba tare da ya sake cewa komai ba, sabon kuka ya zo mata, ta rasa da wa kuma za ta yi shawara, wa zai saka Baba ya yarda ta yi zamanta a gidansu? Ta ya za ta fara zama a gidan su Abdul, bayan ko shi kansa bai damu da ita ba, ballantana ya tilasta wa ƴan'uwan shi kula da ita? Ta samu kanta da kiran lambar Yaya Kabir, ya ɗauka suka gaisa, ya ce"Amarya, dama ina da niyyar kiranki, ɗazu Baba ya ce an ɗaura". Sai ta fara kuka ba tare da ta ba shi amsa ba. Ya ce"Nuratu, akwai wata matsalar ne?" Ta ce"E Yaya". Nan ta faɗa masa duk yadda Baba ya tsara, amma ba ta faɗa masa wulaƙancin da Abdul ɗin yake yi mata ba, ta ɗora da faɗin"Don Allah ka cewa Baba gara zamana a gidanmu, can gidan nasu ban ga inda za su ajiye ni ba, kuma ni ba zan iya zama gidan haya ni kaɗai ba". Yaya Kabir ya ce"To zan yi masa magana in sha Allah! Ki daina damuwa". Suna gama wayar kuwa ya kira Baba, yana jin wannan wata dama ce ta zo masa wacce zai cika muradin da ya daɗe a zuciyarsa, bayan sun gaisa da Baba ya tambaye shi, Nuratu ta tare? Baba ya ce"Ina fa? Babu ma mai zancen tarewar, ni dai zuwa gobe na ba su, ko ba su zo ba zan tura ta, ta tafi can gidan iyayen nashi". Kabir ya ce"A'a Baba kar ka yi hakan, ni a ganina kamar Nuratu za ta takura a can ɗin, me zai hana ta zo nan gidana ta zauna kafin a tsayar da maganar yadda za a yi?" Baba ya ce"To indai za ta je ni ai ba ni da wata damuwa, ta tattara ta tafi". Ya ce"To zuwa gobe zan turo mata kuɗin mota sai ta taho, kamar za ta fi samun nutsuwa a nan ɗin". Suka yi sallama Baba yana ta godiya. Sannan ya kira Nuratu, ya fala mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Amma Yaya har tsawon wane lokaci zan zauna?" Ya ce"Har sanda zai dawo ƙasar mana". Ta ce"Amma Yaya babu takura kuwa?" Ya ce"Wa za ki takurawa? Ni da nake ɗan'uwanki ko matata wacce tun tuni take sha'awar ki dawo gidanta da zama?" Ta yi shiru. Ya ce"Babu wata matsala, sai dai ko idan kin fi son zaman can gidan nasu, don ban ga alamar Baba zai yarda ki cigaba da zama a nan ba, idan kuwa ya yarda to nan gaba abinci ma sai ya gagare ki, ki dai yi tunani, idan kin amince ki turo account na saka miki kuɗin mota, idan ba ki amince ba sai ki sanar mini, daga haka ya katse wayar. Nuratu ta zauna shiru tana tunani, ta san matarsa tana da hal mai kyau da son mutane, sai dai kuma wannan fa dogon zama ne, tana tunanin anya kuwa abun zai ɗore ba za ta ƙosa da ita ba? A zuciyarta dai ta ji ta amince, amma a yanzu a ƙarƙashin ikon mijinta take, saboda haka dole ta shawarce shi, ko ma a ce ta nemi izininsa, don haka ta kunna data ta yi masa sallama, ta rubutu ta ce masa"Yaya ina ta magana ka ƙyale ni, Baba ne ta ce bai yarda na zauna a gida da aurena ba, to ni ma ban goyi bayan ka kama mini haya ba, ko don ka samu nutsuwa a zuciyarka, amma na san gidanku babu inda zan zauna, ba wai na raina ba ne, kawai ba zan ji daɗin zaman ba, tun da zan takurawa ƙannenka, to yanzu dai an ce na nemi izininka na koka gidan Yaya Kabir da zama, har zuwa lokacin da za ka dawo. Ka amince?" "Ki je duk inda za ki je, sai dai ina tunasar da ke, ki ji tsoron Allah!" Amsar da ya ba ta kenan, sai ta tura masa godiya. Daga nan ta kira yayar babarta a waya, ta sanar mata halin da ake ciki, ta ce mata indai ta ga ana neman kai da ita ta dawo gidan kawun Hadi ta yi zaman ta, shi yayan Mama ne, Nuratu ta ce babu damuwa za ta je ta gwada zaman ta gani, idan da takura za ta dawo, ta yi mata nasiha sosai a kan ta kama kanta ta riƙe mutuncinta, sannan ta mu'amalanci kowa cikin mutunci, ta dinga kamawa Nawwara aikin gidanta. Suna gama wayar, ta turawa Yaya Kabir account lambar, nan take ya turo mata dubu goma, ta tura masa godiya. Kabir ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wani kaso na nauyin da yake ɗauke da shi a zuciyarsa tun lokacin da ya ji Nuratu tana da ciki, ya ragu, ya ce"Yanzu za a fara yaƙin". LITTAFIN ZUCIYAR MACE NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL, ZA KU IYA FARA BIYAN KUƊIN KARATUNKU DAGA YANZU TA NAN 8028966015 Sadiya Abdulrazaƙ opay bank Shaidar biya ta nan 08028966015 [11/23, 12:45 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 9 GIDAN NURA Zuwa yanzu Hasana ta saba da kwana ita kaɗai, ta yi nacin da za ta iya har ta gaji ta watsar, wataran haka za ta je ta ce masa ba ta da lafiya wai ko zai zo ya kwana a ɗakinta, amma bai taɓa yin hakan ba, sai dai ya ba kawo mata magani ya yi tafiyarsa, yanzu ko ta buga masa ƙofar ma ba ya buɗewa, washegari idan ta yi masa maganar sai ya ce shi ya yi bacci a lokacin, alhalin tana kallon shi ta windo. Daga baya sai take kunna datar ita ma, ta dinga tura masa stika ko ƙananun kalmomi irin su i love you, i miss you, sai ya duba ya yi banza da ita, wai ita a nufinta abin da ƴan'matan suke faɗa masa kenan, ita ma sai ta koya ta dinga yi, da haka har ta samu hankalinsa ya dawo kanta, ya ƙyale su, amma daga ƙarshe sai ya kafa mata dokar chart ɗin dare, ya ce duk inda aka idar da sallar isha'i ya ganta online sai ya hana ta chart ɗin ma gabaɗaya. Haka ta zuba masa ido yake ta shagalinsa, a tsawon kwanakin nan sau biyu ya kira ta ɗakin nasa, tana tunawa a farkon aurensu Nura ba ya taɓa kwana uku bai kira ta ba, amma yanzu sai ya yi sati uku har fiye da haka ma bai kira ta ba, to ita kanta ta san a yanzu babu wani gyara da take yi, saboda gani take asarar kuɗi ne, uwa-uba ma ba ta da kuɗin gyaran ne, a da bayan ya yo mata cefanen komai wataran haka kawai idan kasuwa ta yi kyau yakan ɗauki dubu ɗaya ko biyu ya ba ta, amma yanzu ta manta ma rabon da kyautar kuɗi ta shiga tsakaninsu, ko data Husainarta ce take saka mata, da kyautar katin waya. Sannan zuwa yanzu ta yarda Ramla ita take yi wa habaici, ta gane da gaske mijinta yana soyayya da ita, abun yana yi mata ciwo sosai, indai wata ƙawarta za ta zo, ko kuma ƴan'uwanta to fa sai sun ba ta labarin Nura yana son wata wacce ta sani, ta rasa me yake damunsa, kamar wanda baki yake bibiyarsa. Daga baya ma Ramla sai ta saka a ka mayar da ita group ɗinsu na makaranta, ta yi habaici tana ba da labarin mijin wata ƙawarta ya maƙale mata, a ba ta shawara ya za ta yi da shi? Hasana sai dai ta yi shiru, don ta san ba laifinta ba ne, komai shi ne ya ja mata.Ta taɓa tambayarsa ina Ramla? Ya fara faɗa yana cewa"Wannan wace irin tambaya ce?" Ta ce"To ai na ji labarin kun jone da ita, kuna soyayya, kuma ita da kanta ta faɗa mini". Ya ce"To an yi ɗin, Hasana ki ɗauki mataki don Allah!". Ta ce"Babu wani matakin da zan ɗauka, kawai dai zan ba ka shawara ne, ya kamata ka riƙe mutuncinka, ni ma kuma ka sama miji aji a cikin jama'a, ana ta zagina a gari saboda wannan halin naka na son mata, wai da me na rage ka ne don Allah? Ka sanar da ni matsalata sai na gyara..." Ta fashe da kuka. Duk da jikinsa ya ɗan yi sanyi, amma ya danne bai nuna ba, ya ma tashi ya bar mata ɗakin, shi dai bai ga wata matsala ba saboda yana kula mata, ai namiji mijin mace huɗu ne, yana da ra'ayi da burin auren mata huɗu idan har ya samu dama, saboda haka ba ta isa ta hana shi ba. Daga baya ta yanke hukuncin jan hankalinsa don ta gane wace kalar mu'amula yake yi da mata a wayar? Sai ta saka Husainarta ta aiko mata d sabon layi, saboda akwai ƙanin mijinta wanda yake siyarwa, ta saka a wayarta, ta saita sabon whatsApp da shi, ta nemi lambar Nura ta yi masa sallama, ya amsa suka gaisa, ya ce bai gane mai magana ba, a rubuce ta ce"E dama ba ka san ni ba ai, yanzu dai nake ganin lokaci ya yi da ya kamata ka san ni, saboda ka daɗe kana azabtar da zuciyata da soyayyarka, burina ko yaya ne na samu matsuguni a zuciyarka, wanda za ka dinga tuna ni ko da sau ɗaya ne a sati". Sai ya tura stikar murmushi, ya ce"Ikon Allah! Da farko dai ya sunanki?" Ta ce"Sunana Suhaila, kuma a kasuwa nake ganinka, wallahi kana burge ni sosai, na daɗe da samun lambarka, amma sai na yi ta jujjuya ta, na kasa yi maka magana, saboda a zotona za ka yi wulaƙanci duba da ganin yadda ka haɗun nan kake da aji, na ji an ce ma mata ba sa gabanka, shi ne nake ta fargaba". Nura ya yi murmushi ya ce"Wannan dalilin ai ba shi zai saka mutum ya yi wulaƙanci ba, sai dau idan dama can halinsa ne, ita mace ai ba abar wulaƙantawa ba ce, mace abar riritawa ce da tarairaya, kuna buƙatar kula ta kowane fanni, wannan shi ne burin da na ci a kan matar da zan aura har tsufanmu". Ta ce"Kenan yanzu ba ka da aure? Zan so a ce ni ce zan samu wannan kulawar". Ya ce"Ina da aure har da yara, sai dai wancen burin nawa yana neman zaɓa tarihi, saboda wata kidahumar mace Allah Ya haɗa ni da ita, wallahi sam ba ta san kanta ba, ballantana ta san mijinta". Kalmar kidahuma ta daki zuciyar Hasana ba kaɗan ba, nan take ranta ya yi baƙi, sai ta ji kamar ta yi voice ta faɗa masa ita ce, sai dai kuma ba wannan gaɓar take nema ba, don haka ta daure zuciyarta suka cigaba, ta ce"Ikon Allah! Yanzu duk wannan haɗuwar taka ba ka yi dacen mace ba? Amma ai kai ya kamata ka canza ta, ka mayar da ita yadda kake so ku zauna". Wannan karon voice ya yo, yana ƴar dariya ya ce"Malama Suhaila kenan, wato ba ki san wace ce matata ba, shiyasa kike zaton za ta canza hali, yanzu haka zancen da nake yi miki fa kin gan ni kwance a ɗakina ni kaɗai, na kasa bacci saboda tsananin buƙatarta nake, amma na kirata ta ƙi zuwa, yanzu ya dace a ce mace ta dinga nisa da ɗakin mijinta wai sai sanda ya kira ta?" Hasana ta daskare da mamaki, sai ta kasa riƙe hawayenta, ashe dama haka Nura yake tona wa aurensu asiri? Kuma ma duk bin ta yake yi da sharri, indai har wacce ta fara yi masa magana yau bai santa ba, bai san inda take ba, zai saki jiki ya dinga tsara mata wannan ƙaryar, to ina ga wacce ya saba da ita har ma yake zuwa gidansu? Yanzu haka yake faɗawa Ramla ma? Tabbas dole ta raina ta. Ta share hawaye ta ɗauki wayar, sai ta ga ya turo mata stika, tana buɗewa ta ga mace ce da namiji rungume da juna suna bacci, ta daure ta rubuta masa"To ko ni ɗin na zo na taya ka baccin?" Ya tura mata dariya ya ce"Da gaske ba za ki ji tsorona ba?" Ta ce"To tsoron me?" Ya ce"Ai za ki zo ne matsayin mai ɗebe mini kewa". Ta ce"Hmm, za ka same ni fiye da matarka, kwatanta mini gidan naka yanzu zan zo". Ya ce"Ki dai gwada ta waya don na yarda idan kin zo ɗin za ki iya taɓuka abun arziƙi". Sai ya turo mata wani vedio, tana buɗewa, ta yi saurin kifa wayar, ganin blue film ne ƙarara, ta dinfa maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!", ta kashe wayar duka ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ta samu kanta da fashewa da kuka, ashe irin mijin da take aure kenan? A daren nan da ƙyar bacci ya ɗauke ta, da safe har ta makara, sai da ya tashe ta, har da faɗansa yana cewa"Wannan wani sabon salon ne kuma salon yara su makara?" "Ba ni da lafiya ne" Abin da ta ce kenan kawai, wani irin mugun haushinsa take ji, ji take kamar ta kama shi ta shaƙe, ta tambaye shi me yasa yake zaune da ita ba zai sake ta ba? Ta je ta kunna wuta, sai dai tunawa da kalmar kidahuma ya sa ta fara hawaye, idan ya tashi wulaƙancinsa har jaka yana ce mata, amma a jiya fa wata yake faɗawa ita kidahuma ce, tabbas ta san duk wacce zai auro nan gaba ba za ta kalle ta da mutunci ba. "Kukan me kike yi?" Ya tambaye ta yana yamutsa fuska. Ta ce"Na ce maka ba ni da lafiya". Ya ce"To Allah Ya sawaƙe, sai ki yi ƙoƙari ki dafa shayi, bari na siyo biredi". Ya fita, ta bi bayansa da kallo, tana tuna wannan ƙazamin vedion, wa ya san adadin matan da ya turawa shi? Wa ya san adadin yawansu a wayarsu, lallai wata wayar za ta iya yi wa mutum jagora zuwa jahannama, haka ta dafa shayin, suka karya, ta shirya yara, tana yin komai a sanyaye, yana taɓa aljihunsa ya ce"Ga shi ba ni da kuɗi da kin tafi asibiti". Ta ce"Ciwon kai ne, zan sha magani yanzu". Ya ce"Allah Ya sawaƙe ya fice". Wajen ƙarfe goma ta kunna data, ta gan shi online, zuciyarta tana ba ta shawarar ta ajiye layin nan, tun da har ta san wane ne mijinta, ta samu abin da take so, wani ɓangare na zuciyar kuwa zugata yake yi, a kan ta cigaba don ta gano iya waya abun nashi ya tsaya ko zai yarda su haɗu a zahiri? Ta fi yarda da wannan don haka ta yi masa sallama, sai da ma ya duba chart ɗin baya har farko, sannan ya tuna ta, saboda yawan matan da yake chart da su, ya amsa ya ce"Matsoraciya jiya sai kika gudu ko?" Ta ce"La ba fa guduwa na yi ba, wayar ce ta mutu, caji ya ƙare, ban ma kai ga ganin me ka turo ba". Ya ce"Kin bar ni da kewarki, har da mafarkinki na yi". Ta ce"Daga haɗuwa?" Ya ce"Ai haɗuwar ce ta yi daɗi shiyasa, yau za ki rage mini dar ko?" Ta ce"Me zai hana? Ni fa da gaske nake, ka ga ni ban saba ta waya ba, a ina za mu haɗu?" Sai ya tura mata dariya ya ce"Kamar gaske". Ta ce"Tun da ba ka shirya ba shikenan mu bar zancen". Ya ce"Wai ke ba kya yin voice note?" Ta ce"Ai ni kurma ce, ba na magana kuma ba na jin komai". Ya tura stikar dariya ya ce"Ban yarda ba, sai ranar da na ganki a zahiri". Ta ce"To yaushe zan zo taya ka kwana?" Ya ce"Yau". Ta ce"Za kuwa ka gan ni, da gaske fa". Ya yi dariya. Ta ce"Zan zo ƙarfe sha ɗaya daidai, saboda haka ka koma gidanka da wuri yau". Ya ce"Allah Ya kawo ki, zan shirya miki abubuwan mamaki kuwa". Daga haka ta kashe data, ta tashi ta ɗora girki, a ranta tana ayyana tabbas yau ɗin kuwa za ta je, ta fito masa a mutum, don ya san ta gane badaƙalar da yake yi a wayarsa. Da ya zo cin abincin rana ba ta nuna komai ba, sai dai sam ba ta da walwala, da daddare yana dawowa ya gama komai ya shiga ɗakinsa, ta kunna data, ta ga saƙonsa ya shigo, yana ce mata"Kyaun alƙawari dai a cika, yana jiranta". Ta ce"Ka tashi ka buɗe ƙofa yanzu za ka ji na turo na shigo". Ya ce"Na buɗe". Ta ce"Ba ka buɗe ba, ina kallonka fa, kana kwance a katifa da gajeren wando bulu". Ya yi ƴar dariya ce"Kuma wallahi kin canka". Ta ce"Na ce fa ina kallonka, yanzu na ƙaraso ƙofar ɗakin zan ƙwanƙwasa, ka buɗe, amma don Allah ko a yaya ka gan ni kar ka ji tsorona, wallahi ni mai sonka ce". Ya ce"Kai Suhaila kenan". Hasana ta buɗe ƙofarta a hankali, ta fito, ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Nura da ƙarfi, gabansa ya faɗi rass, ya ce"Wane ne?" Ta tsaya da bugun ta rubuta masa cewar"Ni ce mana, ya kake haka, ko na shigo ta saman ɗakin?" Sannan ta cigaba da bugawa. Nura bai san sanda ya yi wulli da wayar ba, ya fara karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa, ya yaye zanin gadon da aka shimfiɗa a katifa ya lulluɓa, yana ta addu'o'i. LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL! ZA KU IYA FARA BIYAN KUƊINKU TUN YANZU TA NAN 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay bank Sahaidar biya ta nan 08028966015 [11/24, 1:16 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST

Chapter 5 of 7