Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KOWA YA RAINA TSAYUWAR WATA 1 NA BILKISU SALISU AHMAD FUNTUA KAREWA Ya musulmi `yan uwana don Allah a rinka kiyayewa a daina shiga kewaye da litattafanmu domin akwai sunan ALLAH. Saboda ba shi yiwuwa mu yi rubutu mu kare mu kasa anbaton Allah a ciki. Don Allah ina fata ana anfani da gargadinmu na cewa a daina shagalta da barin ibadar da ta hau kan mu, kada karatun littafinmu ya shagaltar da kai daga barin addininka, in ka yi haka kai da AIlah. iv Daga Anti Bilki 25/11/99. Malam Kado ne ke tafe ya na janye da kekensa, ga kuma fatanya rataye a kafadunsa, a bisa dukkan alamu daga gona ya fito. Can daga nesa amininsa Mallam lliyasu shi ma bisa nasa keken ya kira Malam Kado in da ya ke cewa "A`aha Malan Kado, kada dai ka ce har ka baro gonan kenan?" Malan Kado ya waiwaya ya dubi Malan lliyasu ya dan matse fuska nuna alamun damuwar ciwo sanna ya amsa, "Bar ni kawai lliyasu ciwon kai ke neman kai ni kwance. Na rasa wane irin magani zan saya a kemis ko kuma wane irin sauyu zan jika domin duk wanda na sani na yi anfani da su har na kai makura". lliyasu ya kafe kekensa ya rike kan ya zubawa Malan Kado ido cikin damuwa, ya dan lunfasa sanman ya ce "Malan Kado ban san ka da kafiya ba, sai akan ciwon kan nan, wai har sau nawa zan gaya ma ne kaje asibiti su yi maka gwaje-gwaje don su san abinda ke damunka? Ka ga anan za'a san maganin da ya dace da irin ciwon ka, amma har yaushe za ka yi kwance a gida kana shanye-shanyen maganik daban cuta daban". Malam Kado ya ce "Ai ni tsoro na Allah tsoro na asibiti yanzun nan sun labta maka cutar da tunda iyayena suka zo duniya har su ka bar ta ba su taba jin ko sunanta ba amma ace mutun na da ita, haka nan kuma ga wani tsire-tsire ace kada mutun ya ci kaza kada yaci wancan, shin ina dalili? An taba ganin abinci ya haddasa cuta? Sai dai ya yi sanadiyar warkewar cutar, to ni kaji abunda ke hada ni da asibiti". Iliyasu ya yi dariya yace, "Har yanzu dai kana nan da halayyarka ta mutanen da? Don Allah ka janye wannan ra'ayin ka shirya gobe na raka ka asibiti, yanzu idan da Allah ya raya mana Tasi'u haka zai dinga wahala da kai akan zuwa asibiti?" Malan Kado ya dan yi murmushi yace, "Ka san ko Tasi'u har ya rasu ba shi da wani buri illa na son ya zama likita". lliyasu yace, "Allah ya jikan Tasi'u ai ga kanwarsa nan Dije na ga tana da natsewa sai mu kai ta aikin koyon jinya". Malan Kado vace, "Anya ko hakan na yiwu akan Dije?. Ni wallahi ma lliyasu duk na kagu na kawas da Dije ko na sami kwanciyar hankalin iyalina ace kamar su Ankudi da Sabura baza su zauna lafiya da Dije ba, sai`ya` yan da su ka haifa da cikinsu sune 'ya'ya? Kai yau da safen nan sai da Ankudi ta rinka tikar Dije a gabana wai don bata share mata akurkin kajinta ba da kyau, bayar ga wankin 'ya'yansu na jiran Dije to ire-iren wa'annan fitinu na cikin gidana suke kara haddasa min ciwon kai". Malan lliyasu ya hasala yace, "Kai ai dai maganinka kenan su Ankudin, har yaushe yarinya zakakura, zaruma mai hazikanci kamar Dije za ka hana ta ci gaba da karatun sakandire bayan ta zo mana da sakamako mai kyau, daga kammala karamar sakandire ka kama yarinya ka hana ta ci gaba da babbar sakandire wai don fitinar su Ankudi". Malan Kado ya bata rai yana girgiza kai yace, "Kai Malan lliya, gara dai na yi ma Dije aure. Ina anfanin irin zaman da take yi a gidana sai kace baiwa ba `ya ba?" Iliyasu yace, "To yanzu mijin ta samu?" Kado yace, "A'a tunda maganar Malan Dahiru ta rushe har yanzu babu wani tsayayye, sai dai ni a zuciyata akwai yaron nan dan gidan Sarkin Makera wanda ke karatu a jami'ar Amadu Bello da ke Zaria, wato Yusufa kasan sa'o'en juna ne shi da Tasi'u marigayi na wajena, to ku san kullun ya zo daga Zariaya sai ya zo ya gaishe ni, ni kuma sai na ji dadi na ga tamkar Tasi'u nawa, don haka na ke son Yusufa, dalilin kenan na kallafa rai da son na ba shi auren Dije. lliyasu yace, “Ai ko idan a kai haka an kyauta domin ma ganin natsuwa a wajen Yusufa illa dai kawai na sha jin cewa ance yace ba zai yi aure ba sai ya mallaki aikin kansa yadda zai iya tallafa nauyin kan shi da nauyin iyalinsa, domin ka san mutanen na su ba wani abu ne da su ba”. Nan da nan Malan Kado ya saki jiki amma sai ya nuna`yar damuwa a tare da shi yace,`Ahaf lliyasu, ai kai ka san hali na ba wani abu na ke so ba, ko wani kwadayin abun duniya illa buri na in ga cewa Dije ta auri mijin da ya san ciwon kan shi sannan sai ga mutuncinta har bayan ranta, haka nan kuma su mike tare babu wani kace nace, saboda haka vanzu zan shawarci kanwata Tambaya aminiyarta ce, kusanma na ce Tambaya ta yi ma gwoggon Yusufa babbar kawa wadda ta rufa zuwa daki. Abinda shawara ta bayas zan nemekа." Suka yi sallama da wannan shawarar ta kulla auren Dije 2 da Yusufa kowanne ya doshi gida kodayake Malan lliya ba komawa gidan zai yi ba. Ya zauna cefane ya mika ya kara ficewa zuwa kasuwa wajen harkokinsa na sayar da tabarmi yana ko isa ya cimma wasu baki sun kawo masa damman tabarmi don ari, aka shiga ciniki. Shi ko mutumin sai ya kutsa kai zaurensa yana kokarin jingina kekensa inda ya kan jingine sa amma ya rinka tsinkayo kukan Dije daga can tsakargida, zuciyarsa ta kara hasala har yaushe za'a rinka yi ma budurwa haka, ai kannanta ma sun rainata, haka nan yaushe wani namijin kirki zai zo auren Dije gidan nan? Ya shiga gidan zuciyarsa a cike ya dubi inda Dije ke tsaye tana kuka ya galla mata harara ya ce, "Ke maza daura zani kada in kara ganinki tsaye sai riga da dan fingilin siket kamar wata kabila". Ta dafe ido cikin kuka tace `Ai zanin na dakin Gwoggo Sabura inda ta shake ni da duka kuma idan na koma kara min zata yi". Yace, "Shige mu je dakin Saburar". "Ke Sabura ina zanin Dije?" Sabura a fusace cikin tsiya tace, "Ai kazo tare mata din ne ko? To wallahi sai dai in yau ba za ka ci abinci ba amma dole sai Dije ta yi yadda na ke so ko za ka ci abinci gidan nan haka kawai ka daure ma yarinya gindi daga ni har yaya Ankudi ta mayas da mu banzaye? Daga cewa je ki ki debo min ganyen gwanda sai ga ta da ganyen zogala, ita mahaukaciya ce koko karamar yarinya ce?" Malan Kado ya ce, "Ni kam ban tambaye ki abinda ya hada ku da Dije ba, na dai ce, a bata zaninta, haka nan ban hana ku dukan ta ba amma a dai na yi mata tsirara domin shekarunta sun kai munzuli yanzu". Malan Kado yasa kai ya shige turakarsa a yayin da ya ga Sabura ta wurgo ma Dige zanin ta. Ya nemi filon matashi ya danne kan shi wai ko ya samu saukin azalzala masa da ya ke yi amma ina! haka ya kasance a kwance babu sauki sai wajen Allah. Da azuhur ya lallaba ya je masallaci dan ya bada faralli bayan ya dawo ya zauna a gindin wani kuturturen dutse da ke aje gaban gidansa, ya dafe gefen kan da ke masa guda tamkar zai rabe biyu don ciwo a lokacin wata 'yar filani tare da yarinya 3 mai hura suka ratsa ta gabansa yasa baki yayi kiransıu, ya sayа, mai rionan ce ma yasa ta dama masa ya kafa baki ya kwankwade. A cikin gidansa su Sahura da Ankudi ko wacce ta yi tanadin abinci ita da 'ya'yanta suna ta ci amma Dije na zaune a falo sanye da abayanta da casbi a hannunta a bisa dukkan alamu itama sallar ta idas. An daulki lokaci Malan Kado bai ji motsin sun Ikira Dije sun bata abincin ba, sai yasa baki ya kira ta ya tambayi ko ta ci abinci? Ta ce, "Tun kokon safe". Ya fiddo naira shidda yace ta je ta sayi ko da alalan gidansu Talatu ne. Ta isa gidan su Talatu mai alala amma ta yi rashin sa'a aka ce, Talatun ta tafi da alalaın talla. Nan da nan ta nufi gidansu Inna sa'ade tana sayar da shinkafa da wake. Inna Sa'a mahaifiyar kawair Dije ce, wato Jummai sai dai ita Jummai ta yi sa'a ta ci gaba da karatun ta na babbar sakandire don haka ne ima ta rabu da zuwa gidan, haka nan kuma su Inna Sa'ade da saıran matan anguwa ansan irin azabar da matan uban Dije ke gallaza mata don haka ko da Malan Kado ya ce zai fidda Dije ya yi mata aure kowa ya yi murna da jin hakan. Ta yi sallama Inna Sa'a na shirya ma yaro dan talla shinkafa da wake, ko da ta hangi Dije da 'yar roba tace, "Kin yi sa'a, 'yar gidan Baba Kado saura kiris a tafi da ita talla." a Dije ta yi murmushi jikinta har rawa ya ke yi saboda yunwa tace, "Wai, amma na ji dadi Inna domin yunwa ta gallabe ni". Inna ta yi murmushi tace, "Ai da ganin idanunki an san da labari cikinsu, to miko min robar, kin ga tuwon shinkafa can da Babanku ya ci ya rage dauki ki fara ci ko?" Dije ta zauna tana sharar tuwo miyan taushe don dadi ta rasa a wace duniya take? Bayan ta gama aka dafe mata roba da wake da shinkafa sannan Inna Sa'a ta ki amsar naira shidda. Dije ta iske babanta kwance a dakinsa ta lissafa masa yadda a ka yi da Inna sa'a, sainnan ta aje masa wake da shinkafar a gabansa ta matsa masa akan ya tashi ya ci domin ita ta cika cikinta amma ya nuna mata ba zai ci ba, taci gaba da yi masa korafi, har ya kare ya shaida mata ciwon kansa ne ya matsa masa, ta ce, "To Baba na ze da kankara ko na kawo maka ka danna a kai?" Ya ce, "E, kawo min". Ta zauna a gefensa yana 4 dannawa ita kuma tana fadin "Sannu Baba, Allah ya baka lafiya" Yana cewa "Amin Dije". Can yace "Dije ki rinka kiyayewa da neman abinda matan gidan nan za su rinka dakarki kaman jaka, a kodayaushe ki rinka sauraren aiken da suke ma ki, bana son yawan fitina ko kadan" Kanta a sunkuye tace, "To Baba amma Allah ne shaidata sai ko Shehu tunda yana nan ta aike ni domin da na dawo tace, ba haka ba, shi Shehun ne ya ce, kai gwoggo zogala kika aike ta mana." Malan Kado yace, "Bana son tashin-tashi. na ke dai ki rinka kiyayewa da abinda su kace kin ji." Wanshekare Malan Kado ya lallaba bisa kekensa zuwa gidan 'yar uwarsa Tambaya, bayan la'asar sakaliya kenan. Sun jima suna hiran zumunci sannan Malan Kado ya kawo zancen da ke tafe da shi. Tambaya ta yi shiru har sai da Malan yace, "Ya na ji kin yi shiru, ko hadin nawa bai yi ba ne?" Ta yi sauri ta lunfasa sannan ta gyara daurin kallabinta, ta ce, "Ва haka ba ne Malan abin ne na yau wuya ne da shi, ka san ita ma uwar yaron nan ba komi ne da ita ba, haka nan mahaifinsa mutumin arziki ya rasu sai wannan fitinannen kanin uban na su wanda bai tsinana masu kome illa fitina ko ka san ya sayar masu da gonan su Yusufa shi da kannansa? Haliman da zata kai shi kara amma shi Yusufan ya hana ya ce wai a bar shi da Allah ai gidan biyu ne. To kaji irin matsalolin da su ke fuskanta don haka na ke ganin anya Yusufa zai amince da yin aure yanzu domin ya sha fadan cewa ba zai yi aure ba sai ya mallaki abinda zai rike iyalin". Malan Kado yace "Ku san duk ina sane da abinda ki ka Ilissafà mani, sai dai abinda na ke son ki fahinta har ki fahintar da mahaifiyar Yusufa wato Halima shi ne ba komi zai kashe ba akan auren Dije haka nan wannan gida da suka ci godo inda ita Halima da kannansa ke zaune anan zai aje Dije in ya so ya tafi Zariya yaita neman iliminsa mu kuma muna nan muna bin su da addu'a, ko me ki ka ga ni?" Tambaya ta gyara zama tace, "Zancen ka a bisa hanya ya ke, hakan yayi daidai. Allah kuma ya hada mana hankullansu, amin." Malam Kado ya sadda kai yace, "Ni wallahi duk fadin 5 garin nan ban ga yaron da ya kwanta min a rai ba irin Yusufa, son yaron na ke da zuciya daya, kin ga idan Ubangiji ya hada hankalinsu da Dije shikenan na huta kunne na shiru da rigingimun su Ankudi da ita Dijen". Tambaya tace, "To halin su Ankudi da Sabura ai sai dua'e amma idan. Dije ba wani gari ta yi aure ba suna ko shafa mata lafiya? Ko ka san don a zauna lafiya na ki sanar da kai cewa su ne su kai sukar wancan auren na Malam Dahiru da Dije?" Malam Kado ya bude baki hangangan yana mai kakahi Tambaya taci gaba da cewa "Ni ma ina kyakwawan zamana Ladi mai aiki gidan hakimi ta kawo min labarin, amma don Allah wannan kada ta dame ka, ka ji an ce wani hanin ga Allah baiwa ne, idan Allah ya bata Yusufa dan makaranta ai ya fi Malam Dahiru mai neman na tuwo, ni dai fata na da kai idan har wannan maganan ta kullu kada a bari su ji sai dai su ji daurin aure". Malan Kado yasa habar rigarsa ya goge goshinsa yayi ajiyan zuciya yace, "Duk abinda mutun ya yi shi da Allah, ba su yi min ba, kan su su kai ma wa. Ina ganin ma idan Allah yasa Yusufa ya yi na'am da maganar sai su rinka haduwa nan gidan ki". "Inna Tambai ce yau a gidan?" in ji basiru kenan daya daga cikin`ya`yan Halima, ta amsa "Ni ce, Basiru ina gwogwon ta ku in ce ko tana gida?" Basiru ya aje bokitin da ke hannunsa wanda ya ke wanke rigunansa da kayan gwoggo Halima ya ce, "Inna Tambai, gwoggo ta shiga nan makwafta yin barka yanzu za ki ganta ko kuma na tura Hassi ta kira ta?" Inna Tambaya tace, "kyale ta Basiru, ina Hassi din ta ba ni ruva a Duta zan yi alwala domin na ji ana kiran azuhur ko?" Basiru ya rafkawa Hassi kira ta fito tana tsifar gashi ta tsugunna ta gayas da Tambaya ita kuma ta umurce ta ta kawo mata ruwa a buta. Tambaya na tsakiyar sallah Gwoggo Halima ta dawo bayan ta yi sallama ta aje gyalenta bisa gado ta yi murmushi tace, "Yau kuma kawalliyata larabar duk ta wace? Lalle na taki sa'a, dama `yan iya magana kan ce tabawa ranar samu ko samu da ke ya kara, kamar kin san ina nemanki akwai wani albishir da zan ma ki". Halima ta fice ta nufi kicin ta dauko 6 masu abincin da ta bar wa`ya yanta su dafa, taliya murjin hannu, ta zo ta dire gaban Tambaya, sannan ta fice don ta yo ta ta alwalar sai da ta kammala, ta kwallawa Sarai kira tace, "Maza kawo mana ruwan sanyi". Ta dubi Tambai tace "Ranki shi dade Gimbiyata kamar kin san ko da ba ki zo gidan nan yau ba gobe ni dole in neme ki?" Tambaya cikin murmushi tace, "Me kuma ya faru aminiyar tawa?" Halima ta ce, "Babu komi sai alhairi. Wallahi Tambaya wata magana ce na ke ta kunbiya-kunbiya da ita yau kusan shekara biyu kenan na rasa wanda zan fasa ma ita wata kin tsane da Malan Tukur mai almajirai na bisa kan kwanar gidan nan?" "Ke ina yawan ganin shi wajen mai gidanki - Sarai ta yi sallama ta shiga tace, "Af gwoggo ga wannan gujiya ce da kindirmon nono da danyen manshanu Malam Tukur ya aiko Inusa yaronsa har ma na bashi naira goma". Halima ta juya ta dubi Tambaya su kai murmushi sannan Tambaya ta sadda kai kasa ya yin da Halima ta dubi Sarai ta ce, "Ina man shanun?" Sarai tace "Yana kicin, zan soya, ai gujuyar ma danya ce, ni ce na dafa ta". Tambaya ta ce, 'Sannu Saratu samo kwano ki zubo mana gujiyar". Halima ta yi tagumi ta ce "To abinda duk na ke kokarin bayyana ma ki ya bayyanar da kan shi, ina fatan kin fahinta?" Tambaya cikin siririyar murya ta ce, "Na fahinci kina son shaida min Malam Tukur na neman aure, amna kuma na wa?" Halima ta harzuka tace, "Ban gane ba, kina nufin tsofai-tsofai da shi zai zo neman auren su Sarai ne ko Hassi?" Tambaya ta ce "ba nufi na kenan ba ina nufin ko cikin zuri'arsa ya ke son a hada jini?” Halima tace "Ni da haka ya ke nufi da ban ji sanyi a rai na ba Tambai? Amma shi Malan wai ni ya ke so da aure, na yi korar amma ya manne yau shekara biyu kenan yana irin wa'annan wahalhalun". Tambaya ta sha mur tace, "To ke ko Halima ki rufawa kan ki asiri mana, aurenki da Malan Tukur ai ba karamin gatanci ba ne gare ki dà 'ya'yanki saboda mutun ne kamulalle kuma duk wani hakkinku da akan danne maku da gangan Malan Tukur zai taimaka ta wani fannin da zai iya a matsayin mijinki." Halima ta yi jagale Tambaya ta kara tsumata, zuciyarta ta kara kwadaita da son Malan Tukur nan da nan idanunta suka dan kada, ta dan girgiza kai tace, "Yadda duk ki ke nufi ba haka nan ba ne Tambaya". Tambaya tace "To menene, ke dai ba yarinya bace, haka nan ke ba wani abun duniya ki ka tara ba balle ace kwadayin dukiya ya kawo Malan, sai dai in ba kya son shi." "Ko kusa babu zancen kiyayya tsakani na da Malam ina son Malan Tukıur fiye da zaton dan adam matsala ta daya wannan yaran Maitama ya tsani maganar aure na da Malan Tukur, na yi iyakar kokari na don na fahintar da shi amma ya nuna min a gaskiya mutunci na zai zube idan aka ce na sake aure bayan rasuwar mahaifinsu wai idan ba kwadayi ba me zan ci da Malan Tukur?" Tambaya tace, "Ke ni rigima ta kenan da 'ya'ya maza muddin aka ce mahaifinsu ya rasu sun fi kowa kishi idan ance ana sonka"; Halima ta ce, “Ni dai Maitama ne kawai ya kawo mana tsama armma su Basiru sun runguimi Malan Tukur da hannu bibbiyu, abin haushin ma shi ne, ya kafa dokar cewa idan na auri Malan kada ya shigo masu gida, mun ce mun amince domin Malan yana da wani gida ya ce sai na koma can tare da yara na domin ba zai hada ni da matansa ba, anan ma Maitama yace wai bai amince kannensa su je agolanci ba sai dai na tafi ni kadai. Ke akwai ranar da na yi ciwo Malan ya zo gaishe ni, wallahi, a rannan Maitama yasa na ji kunya, kiri-kiri ya ki gayas da Malan sai shi Malan din ya gayas da shi, amma yaron nan ya amsa a dakale". Tambaya ta yi dariya tace, “Ka ji aikin manya kenan sai a bisu a sannu." "To ni abinda yasa ki ka ga ina kyale Maitama yana yi min gadaza akan zancan aurena da Malan abu daya ne, wato duk hanyar da zai shiga don ya kare mana mutuncinmu ni da kannan sa yana yi. Misali wannan shagon na jikin gidanmu shi ne ya yi iyakar kokarinsa ya ciri ya kullu a irin kudaden da gwamnati kan biya masu don sayen litattafai ya cira ya zuba mana abin masarufi, kanin Basiru ke tsarewa anan mu ke fid da na sabulun wankanmu da man shafawa zuwa ornon wanke wanke hatta ashana da za mu kunna cikin ribar shag o mu ke ansowa, wannan kenan haka nan duk inda ya ji wani dlan aiki yana nan manne idan ya sami alhairi bai tunanin kan shi daga ni sai kannensa, 8 yanzu kwanan baya wani Alhaji mai kudi a Katsına zai yı aike Kwatano sayen motoci abokinsa ya neme shi da ya bi ayari shi ma ya tuko mota daya, ya ko je wallahi abinda aka biya shi dubu biyar. Tun a Kwatanan ya sawo mana shirgegen firij yanzu haka a rana daya sai mu daura ruwan sanyi zuwa kankara da kunun zaki kimanin na dari uku, to saboda Allah ko ke ce Tambaya yaro na nuna maki irin wannan gatancin ai kya danne kwadayinki?" Suka kyalkyale da dariya suka tafa hannuwa "To ni kam kin ji abinda ke damu na Tambai kullun sai kara shishige min Malan ke yi yayin da na ke kara kaunarsa ina kuma tsoron batawa Maitama rai don haka na ke son dama na same ki kiyi ma maigidanki magana ya baiwa Malan hakuri ya nemi wata matar ni kam ba zan aure shi ba". Tambaya tace "Kina so amma yaro bai yadda ba?" Suka bushe da dariya ta ce "ke ko da raha ki ke!" “To na ji na ki bangaran abinda mu ka yi da maigidan game da batunku ke da Malan zan sanar da ke sai ni kuma abinda ke tafe da ni game da yaron ne Maitama Yusufa, yayana ya aiko ni. Malan Kado yace, shi dai ya hanga ya duba duk girman garin nan bai ga wanda ya ke so ba irin Yusufa don haka idan har ba zai takura ma rayuwarsa ba ya je su daidaita da Dije ya ba shi ita". Gaba daya dakin su ka yi tsit sai zuwa can Halima tace, "Ni wannan kauna ta Malan Kado da Maitama har ban san irin ta ba? Har da karin marigayi Tasi'u fa!" Tambaya tace, "Ai Yusufa abun so ne, yanzu 'ya'ya nawa ne sao'en marigayi Tasi'u a garin nan? Amma babu mai kula Malan Kado kamar Yusufa". Halima tace, "Wannan fa tabbas, idan dai ya sauka a garin kafin ya anbaci kanin babansu ya ce zai je ya gaida Baba Kado wannan aure na shi da Dije fa ya yi daidai kadaran kadahan irin wa'anda suka san usulinmu suka san matsayinmu kin ga har abada raini ba zai shiga ba, zai juya matarsa yadda ya ke so. Da man tsoro na Allah tsoro na ya nemo min wa'anda suka fi karfinmu don na ga bokon na shi ya yi yawa, Allah ya kawo shi wannan satin zan turo maki shi. 9 Da wannan suka rufe zancen, ta ce a dibar mata nono da manshanun zawarcin itama ta je gida ta lasa, anan kuma aka dawo da shegantaka baya kamar wasu 'yan mata. Yusufa Kanti dan makaranta ya je gida kamar yadda Halima tace, ta kuma yi masa zancen Dije ya fashe da dariya yace, "Aure gwoggo, da irin halin matsalar ciyar da kan da mu ke ciki? Da dai sai

Chapter 1 of 5