kai mata wasikar Yusuf. Dije sai da ta gama wanke-wanke
sannan ta nufi falo da Sarai in da `yar shinfidar katifar ta ta ke
amma wannan bai sa an baiwa Dije`yancinta ba, domin sai ga
yaran gidan sun zo sun yi mata cincirindo ana tambayarta cewa,
"Dije menene cikin ambulan din? Ko kudi ne aka aiko
20
ma ki ba
kya son su Gwoggo su sani?" Haba sai ga su Ankudi tsigil cikin
falon ana antayawa Dije zagi, Ankudi na fadin "Ke ja can
shashashar banza ina tsiya ina dan gidan mariga Kanti. Me tsiya
ta ci ta rage balle har ya tsinana ma ki wata tsiya? Idan ba irin
dan gidan Kanti ba, wa zai kwashe ki, shi ne har za ki ma
mutane yanga da shegiyar ambulan? Me ya taba baki a garin
nan, in ban da alewa da cingam kullun?" Sabura ta ja tsaki ta
ce, "Yusufan banza za`a yi mana yanga da aikensa?” Nan da
nan Dije ta daga idanu taf da kwalla ta dubi Sarai. Ita ma Sarai
ta dubi Dije kowacce ta share kwallan da ke zuba mata.
Bayan sun fita ne ta yage wasikar Yusuf sai kawai ta kara
tsananta hawayenta, ta dubi Sarai ta ce, "Saratu tun yaushe ne
yayan bai lafiya?" Saratu ta ce, "Jiya ne ya dawo daga Zariya
yanzu haka ko masallaci bai iya zuwa”. Har ta fara rubuta masa
amsa, sai ta ji matsin shigowar Babanta dakinsa, ta yi sauri ta
goge fuskarta ta nufi dakin Babanta. Ta durkusa ta ce, "Baba
yanzu Yusufa ya aiko Saratu da wannan wasikar, ashe bai lafiya
kwarai yana nan gida kwance" Ya ce, “Assha, assha, ciwo tun
daga Zariya lalle jiki ya yi zafi, sai ki shirya maza ki je duba shi,
kya ce muna gaida shi sai na zo".
Nan da nan ta shirya ta fito ita da Sarai suka rankaya a
bisa hanya ne ta ce, “Saratu na roke ki don Allah mana”. Ta ce,
"Menene?" Dije ta ce, “Don Allah kada ki gaya ma Gwoggo zagin da su Gwoggo Ankudi su kai mana" Sarai ta dan tsuke
fuska ta се, “To kо ma an fada mata me za ta yi? Komi mutun ya
yi ai kan shi”. Dije ta ce, "A to kin ga ni fa, don haka na ce kada
ki gaya mata ran ta ya baci a banza".
Suna isa ta dan yi sallama ta daga labulen kofar dakin
Yusuf ta ga Garba na yi masa allura. Ta saki labulen da sauri ta
ce, "Sannu, ku bari na gayas da Gwoggo. Ta shige cikin gida ta
tsugunna har kasą ta gaida Gwoggo ta ce, "Ashe kuma yaya bai
ji dadi ba?" Gwoggo ta ce, "E, ai yau ma babu laifi, amma jiya,
abun ba a cewa komi". Dije ta ce, "Allah ya ba shi lafiya".
Gwoggo ta ce, “Amin".
Salmanu ya leko ya ce, "Dije ki je yaya na kira". Ta mike
ta nufi zaure inda dakin Yusuf ya ke, ya na kwance duk ya rame
21
ta nemi kujera wadda ta ke ita kenan guda daya dakin ta zauna
ta ce, "Sannu Yusut, ya jikin?" Ya ce, "To Alhamdulillahi Dije,
yaya su Baba Kado?" Ta yi tagumi nan da nan idanunta sun cika
ta ce, "Lafiyarsa lau" Ya ce, "Na gaisheka sai ya zo an jima".
Yusuf ya ce, "Wash!" Dije ta kasa cewa uffan domin sai
ta ji Wash! din har cikin kwanyarta, a lokacin ba ta ki ba a се
ciwon da ke jikin Yusuf ya dawo kan ta. Ta sa bayan hannu ta
goge idanunta da karan hancinta.
Basiru ya shigo da maheci a hannunsa ya zauna bakin
gadon Yusuf yana yi mata hita, nan da nan tunani ya shigi Dije
zai fi kyau ta je ta yi masa domin ta san halin Yusuf yanzu yana
warkewa zai fara yi mata tsiya cewa ita`yar kauye ce, bata
kula da shi lokacin ciwonsa illa sokancin kuka, da dai sauran irin
wa`annan maganganun, saboda`yar shakuwar da su ka yi na
wata uku ta fahinci halin Yusuf kamar bayan hannunta. Mutun
ne mai son komi mace ta yi masa.
Don haka ta matsa ta amshi maheci daga hannun Basiru
ta zauna bakin gado tana yi masa hita, har bacci ya dauke shi
bata daina ba, lokaci lokaci ta rinka sa tafin hannunta bisa
gashinsa tana jin yadda zazzabin ke sauka. Bayan awa biyu ya
fara zufa kasharban ya aike ta wajen Gwoggo ta amso ruwan
kan shi da tawul. sanyi ta zo ta rinka goge masa zuwa wuya
Ya fara amai Dije ta tsugunna gindin robar da ya ke aman
tana fadin "Yau ni na shiga uku ni Dije kada ka hazas da`yan
hanjinka." Nan da nan sai kuka rau rau, tana goge masa jiki
tana kwalla.
Ta shiga cikin gida ta zud da aman. Ta na wanke robar
Gwoggo ta leko ta ce, "To ke Dije haka za`ai jinyar, wannan
aikin ma ai na su Basiru ne. Sannan kuma duk kin gwalje idanunki
wajen kuka, wa ya ce maki ana yi ma ciwo kuka? Ai sai addu`a,
kin ji?"
Bayan sallar la` asar Dije na can dakin su Sarai, mahaifinta
Malan Kado da Malan lliya da Malan Tukur na zaune dakin Yusufa
su na tausaya masa zafin da jikinsa ya yi, a lokacin da Malan
Kado ya tashi tafiya ne yà ce ma Dije sai ta rinka kwana nan
wajen su Sarai tana duba jikin Yusufa domin dai ko taje gida
22
hankalinta ba zai kwanta ba.
Bayan tafiyarsu ne, ta koma dakin Yusuf ta zauna ta zuba
mai ido yayin da shi ya sami bacci, tunani barkatai ya rinka
zuwa ma Dije, 'to yanzu idan Yaya ya mutu fa? Ga shi ana gaf
da aurensu? Auren da ta ke ganin zai kawo karshen duk wani
magudin wahalhalun da take fuskanta wajen matan ubanta?
Rayuwar da take mafarkin shinfidawa a gidan nan, ita da su
Gwoggo Halima da kannan mijinta, tamkar wata rayuwace wadda
ta ke jin babu wata diya macen da ta taba dandanar zumar
zakinta domin ita a ganinta ko a matsayin ` yar aiki za su dauko
ta lalle za ta mori gardin rayuwa fiye da ta gidan mahaifinta
Baba Kado. To balle kuma a matsayin matar Yayan gidan? Yayan
da babu kamarsa wajen kowa da kowa a gidan, shin wai wacce
irin sa`a ce da ita? Haka nan kuma ta zamo daya da daya abar
son Yaya Yusuf, yayin da ita ma bata da na biyunsa wajen so da
kauna, ta amince ta rasa komi ta mallaki Yaya Yusuf hatta
tsananin son karatunta na boko a darajar Yaya za ta iya jingine
ilmin waje daya, haka nan a zuciyarta ta na jin za ta iya bautawa Yusuf tamkar yadda take bautawa ubanta, sai dai kash!' ta kawo
gwauron lunfashi tare da wasu sabbin kwallan 'yanzu idan na
rasa Yaya fa a dalilin wannan shegiyar: maleriyar da ta addabi jama` a? Amma dai na, cika mara sa`a a duniya, saboda a ina
zan kuma samo wanda na ke so tamkar Yaya? Na san zan iya
samun mai so na kamar yadda Yaya Yusuf ke so na, to amma ni
fa?' Ta fashe da kuka a fili wanda har shi Yusuf na jin ta illa dai kawai bai iya ce mata komi domin jikinsa ya yi zafi. Ta yi kuka ta yi kuka na tunanin rashin Yusuf a karshe ta hakura ta mike ta yo
alwala ta dawo bisa kafet din Yusuf ta shiga sallar nafila rokon Allah ne dai ya raya mata Yaya Yusuf.
Sai misalin karfe goma sha daya na dare, tana makure
bisa tabarma a dakin Yusuf, ta yi tagumi tana gyangyadi shi ma
Basiru na zaune bisa kujera yana gyangyadin, sai Malan Tukur,
ya yi sallama ya shiga, ya ce, "To Dije koma cikin gida mana ki
kwanta ai kin ga shi ma ya sami bacci ko?" Ta mike tana mai
cewa 'To', ta yi ma Basiru sai da safe.
A dakin su Sarai da Hassi ta kwana illa dai ba wani baccin
23
kirki ta yi ba, ta rinka saurare ko Basiru zai ta da Gwaggo ya ce,
"Yaya ya rasu."
A kalla sai da suka sami kwana biyar ana jinyar Yusufa
robar ruwa kuwa an yi mai kari har babu adadi.
Dije na zaune bisa tabarma ta ce "Yaya na gama alalen, а
zubo maka ko?" Ya dan kanne ido yace, "Kada ki sake ce min
yaya din nan, na gaya ma ki bana so". Ta dan harare shi ta се,
"Haba don Allah dubi fa girman ka, amma sai na rinka ce ma
Yusuf bayan su Sarai na kiranka Yaya? Gaskiya ni ba zan iya ba"
Ya ce "Amma ai ni mijinki ne don haka sai ki min lakabin da
akan kira miji a madadin Yaya", ta ce, "To rnaigida ga alalan na
kammala", ya ce, 'A haf har kin sa kai na ya sara! wannan ai
kalmar mutanan da ce, wai maigida kamar wani tsoho, ba na
son kauyanci ki rada min sunan zamani dan Allah', ta ce, 'ka yi
hakuri ka ci alalen suna kan idan Allah ya yarda ai zan rada ma
ne, abinda ma idan na fara lissafo maka sai ka zaba', ya dube ta
ya yi murmushi ya ce, " Hadizan Yusuf ko? Ni kin san abinda ya
fi ba ni dariya da bahaushe, ko kuma na ce ya fi bani haushi
wallahi yadda su ke cima sunayanmu zarafi wai wani abu a
rinka kiran mai suna Yusuf dan Yusufulle ko Yusufa don Allah
dubi sunan Baba Kado mai dadi amma bahaushe ya watsa shi
maimakon Abdulkadir wai kado', Dije ta yi dariya ta ce, 'Au ai
gara na ka sunan da nawa suna Khadijah amma an mayas min
Dije ko Dijengala haır Ingali ce mani a ke dubi Saratu shi ne Sarai
Hafsat am mayas Hassi, malan bahaushe da iya fasali ya ke'.
Salmanu ya yi sallama ya leko ya ce, "Gaskiya yau Dije
alalenki ta yi mugun dadi", nan da nan Yusuf ya sha mur ya ce,
"Kai Salmanu daga yau kada na ji ka kara kiran ta Dije, Khadijah
fatan za ka sanarwa da su Hassi." za ku rinka cewa ina
ta Bayan Salmanu ya tafi Dije ta dubi Yusuf ta yi dariya
ce, 'To anan ai ba ka yi adalci ba, don me za ka ce Hassi itama
sai ka ce a gyara mata na ta', Yusuf ya ce, 'wannan bai shafe ni
ba, na matata na sani itama mijinta ya mai da mata Hafsat idan
ya na da sha'awa', Yusuf ya kara kashe ido ya nutsar da kwayar
idon sosai ya lumlumshe fuska ya ce, 'Kin ma san wani abu
Hadiza?" Ta dan grigiza a hankali domin irin kallon da ya ke
24
mata ya kashe mata jiki, illa tsigar jinkinta ta rinka yarari ya ci
gaba da magana a hankali cikin natsuwa da rudar da mace, ya
ce, "ran da duk ki ka kammalu a dakina a daren da zan fara
shiga daki, kin san irin kazar nan da ango ke kawe ma amarya?
To ni zabuwa zan sawo ma ki amma ta radin suna ce" Dije cikin
siririyar murya ta ce "wane irin suna kuma haihuwa na yi?" Ya
yi murmushi ya ce, "A'a sunan ki dai zan rada ma ki sunan da
ya dace da ke, sunan da aka yi dace na fi so a rayiwa ta", ta dan
lumshe ido ta ce, "yaya sunan ya ke?" Ya ce, "KUBRA kuma ba
zan yadda kowa ya rinka kiran ki da sunan ba illa ni kadai Yusuf".
Ya bude kwanan alale sai ya yi murmushi ya dubi Dije ya
ce, "Ya ya a kai ki ka san alalen gwangwani na ke so? Wallahi na
tsani alalen ledan nan", Dije ta yi dariya ta ce, "Gwoggo ta
sanar da ni har yadda zan hada yajin alalen ita ta koya min". A
haka dai Dije ta sami kwana bakwai cif gidansu Yusuf soyayya cikin ruwan sanyi ya ke koyar da ita irin ta samarin ilmi wadda
tafi zuma zaki sannan tafi kudi gardi da dadin gani a ido. Yusuf
da kan shi ya raka Hadizarsa gida ya iske Baba Kado suka gaisa
ya sanar da shi kwanan baya ya je Malunfashi inda mahaifiyar Dije ke aure ya gaishe ta har sun ce a gaishe su. Malan Kado ya yi murna da jin haka. Sai su kai sallama a kan gobe zai koma Zariya.
Wanshekare Malan Kado ya je wajen 'yar uwansa Tambaya bayan sun gama gaishe-gaishe da juyayin awon Yuşuf wanda ya gigita su, sai ya zarce da zancen da ya kawo shi, ya ce, "Tambaya na ga ya kamata ki shirya gobe ki je Malunfashi wajen Amina mahaifiyar Dije ki kai mata na ta kason na sa ranar bikin Dije da Yusuř ki shaida mata Dijen ma na nan zuwa ta yi mata kwana biyu kafin bikin, sai kuma shawara ta biyu ga dubu goma sha biyu na kulle ina son ki yi hikimar da za ki yi, ki ga kin sai
ma Dije gado mai fameka da kabet din sa da madubinsa sannan da 'yan kujeru guda biyu, da ledar tsakar daki, sauran 'yan kwanoni abinda Allah ya sake ba ni daga baya na kawo ma ki". Tambaya ta ce, "Tirkashi! Na yi zaton Malan za kai kokarin ko da dubu ashirin da biyar a samu a sai mata masu kwari? Don
samu za'a samu na hakan to amma kwana biyu sun karye balle
25
dakin yaro", ya ce, "wallahi Tambaya Idan da hali abinda ya fi
haka sai na yi ma Dije, babu ce ta sa hakan, ko kin san dubu
hudun ma Malan lliyasu ya ba ni su da ya lura abubuwan sun
cude min?"
Ta ce, "Insha Allah, Allah zai rufa mana asiri baza mu ji
kunya ba".
Wanshekare karfe goma sha daya na safe Tambaya na
dakin Amina mahaifiyar Dije. Tambaya ta dubi Amina ta ce 'Wai
ke don Allah ba kya tsufa ne dube ki shar da ke sai ka ce yau
aka kwareki a leda', Amina ta yi ma Tambaya gatsine ta се,
'Eye! Sannunku ai-so ku ke ku rinka gani na a matse kuna min
jaje? To ina nan shar kuma kwalelenku nan ga ni nan bari kun
ji!' Tambaya ta ce, 'Allah ba da hakuri, ga haihuwa Amina! To
na ce yanzu dai kin hakuri ki bar wa diya ta fagen haihuwar
ko?" Amina ta yi tsaki ta ce, "ina kuma ruwa na da haihuwar
diyarki ni zan goya mata? To bude kunne ki sha labari haihuwa
yanzu na fara", Tambaya ta ce, "ke dai ki ka sani, ni ga goronki
na sa rana aka ce na kawo ma ki, amma banda na wajen iyayenki
su an kai masu na su, wannan na ki ne da dangin mijinki na
nan."
To yanzu Amina ta saki layin wasan kanin miji da su ke yi
da Inna Tambai albarkacin aurenta da Malan Kado, ta zauna ta
takure kafafu ta bata fuska da gani ka san maganan auren nan
ba ta gamshe ta ba. Ta waiwayo ta dubi Tambaya ta ce, 'Wai ke
yanzu saboda Allah Tambai ba kya iya baiwa Malan shawara
yaya za ai a yi ma wannan 'yar mitsitsiyar yarinya aure? Bayan
ko wani kugun kirki bata da shi haka nan ga shi muna zamani
na ci gaba wajen ilimin 'ya'ya mata, wallahi diyarsa ya kashe,
domin in dai mazan nan na yanzu kiri-kiri nan gaba zai watsar
da ita ya debo ma`aikaciya`yaruwarsa, ta zaune su mayas da
ita yar bora'. Tambai ta tarbi lumfashinta ta ce, 'Haba Amina
ba kya tausaya ma Dije irin zaman da su ke yi da su Ankudi?"
Amina ta ce, "shi ne me, in ce wuya ba ta kisa, kuma ai gara
wuyar gidan uba da ta gidan miji, in dai ya yi hakuri ai wucewa
komi zai yi", Tambai ta ce, "Ke ma fa kin yi magana anan Amina,
illa dai kawai hankalinki ba zai tashi ba sai kin shiga gidan Malan
Kado kin ga yadda rayiwar Dije ta ke, to ni kuma da ya dace ace
ta zauna a hannuna kin ga lalurar irin auren da na ke yi, wato
Malan dan ci rani ne, yвu muna Kano gobe muna maiduguri, kai
wannan shokarar dai na ce masa mu hakura haka nan, in ko ya
ce sai ya je, to ya yi amarya',
Suka bushe da dariya Amina ta ce, 'Tambaya da Malan
Iro masu auren zobe ba saki ba yaji kishiya har abada'. Ta ci
- gaba da cewa "To ni dai farin ciki na ma daya ne anan da wannan
auran dan gidan marigayi Kanti, yaro ne da ya yi tasiri da halin
manya kuma sanin halin Halima tun muna `yanmata da tsegumi
ko ganin kyashi to kin ga anan za ai zaman ganin girman juna da
mutunta juna kuma Yusufa ma fa yaro ne karami har da girman
jiki ko kin san sai watan gobe ya ke cika shekara ashirin da
uku?"
Tambaya ta rike baki tace, "A gaisheki raskwana uwar
lissafi, amma fa Amina ba kya da mantuwa, irin wannan
tantancewa?" Amina tace, 'Ba haka ba ne Tambai, kin san
kwana uku ne tsakanin wannan yaron mai rasuwa da
Maitama domin bana mantuwa ina kwance a ranar da
Halima ta aiko min da kunun jego da kauri na kwana uku
nace ma` yan aiken suce ma Halima iina nan zuwa da yamma
na ga jariri, amma ina! kafin la`asar ni ma na haihu, to kin
ji abin da yasa lissafin su Maitama bai shige min'. Tambaya ta ce, "haka ne, kin ga ashe ba mu fi shekara
talatin da takwas kenan a' duniya ba amma shine ne wannan takadarin yaron Maitama ya so ya hana Halima aure ba don
Malam na waje ną ya bude mai nasiha ba'. Amina ta yi murmushi tace, "E haka na sami labari Halima ta auri Malam
Tukur nace, ta dai kyauta ma kanta aure ai yafi zama haka nan,
ka zubawa iyaye da `ya` ya ido'.
Tambaya ta warware ma Amina yadda su kai da Malan
Kado game da batun sayen gadon Dije, Amina ta yi iyakar
tunaninta sannan tace ma Tambaya "babu komi, a yi na dubu
ashirin din, akwai wani dan marakin ta zata aika a sai da mata
shi don haka za ta aiko ma Tambaya da kudin. Batun tarkacen
daki kuma duk sun hada ita da 'yan uwanta sai lokacin biki za
27
su kawo, suka fara batun towe-towe kaman su alkakı da cin cin
da nakiya zuwa su manja da man gyada, Tambaya ta ce ta
dauke wannan nauyin.
KASHI NA BIYU
Usilin Malan Kado wato uban Dije mutanen Bakori ne
iyaye da kakanni, garin Bakori gari ne mai albarkar jama'a haka
gari ne mai anfanin gona. Darajarsa da kimarsa ta kara fitowa a
dalilin fuskar garin da shi ainihin garin ya fito a fili ne bakin
hanya ba sai an yi kurda-kurdar shigansa ba duk da bai faye
girma ba Ubangiji ya albarkatai da jama'a masu dinbin ilmi da
fasaha zuwa hazikanci, haka nan matasa sun rinjayi ainihin garin
Bakori.
Abdulkadir wato Mallam Kado ya taso matashi abin alfahari
ga karaman hukuman Bakori domin a kalla yana daya daga cikin
manoman garin wanda karaman hukuman ke amfana da
albarkacin nomansu. Yana gaban kuruciyarsa ya kallafa ransa
akan Amina bata ko isa auren ba iyayenta suka wanke ta suka
ba shi, kwanci tashi ta haifa masa Tasí`u; bayan Tasi` u ya sami
shekara uku ta haifi wani dan amma bai zo da rai ba saboda
bakwaini ne. Tasi`u na da shekara takwas cif aka haifi Dije.
Tasi`u ya zama abin son Mallan Kado ko ina yana nan tare da
shi, don haka ne ma abokan Tasi'u kamar su Yusufa suka saba
da Mallan Kado a wannan lokacin kwatsan Tasi'u ya sami shekara
goma a duniya Dije na da shekara biyu kenan me zai faru? Wata
alhamis su Tasi'u da su Yusufa sun je kogin da ke can hanyan
Kabomo yin kurme irin na yara, sai gawan Tasi'u aka kawo ma
Mallan Kado anan ne fa Yusufa ya rinka kuka yana kumaji shi a
doje sai a rufe su tare da Tasi'u. Haka Allah ya nufa, to abin
karewar zama a daidai wannan lokaci rudani da rikiwar mutuwar
Tasi'u sai ta sa Mallan Kado ya tsani komi hatta Amina sai ya
dora mata karan tsana, da abinda ya isa fada ba sai ya fada
mata da fada wata ran ta nuna masa damuwanta game da
abinda ya ke mata, sai ya bude baki yace, "zama da ke bai zame
min tilas ba, na rasa Tasi'u ma balle ke?" Sai ta ce, "au haka ne,
28
to iná shaida" Nan da nan ya ce ya sake ta saki daya.
Wannan shi ne mafarin rabuwan Kado da Amina, bai shiga
nadama ba sai da aka ce yau Amina ta cika idda har Mallan Isa
mai aiki a ma'aikatar gona a Malumfashi ya fito neman aurenta,
nan da nan da Amina ta lura Mallan Kado zai matsa mata aka
daura mata aurenta da Mallan Isa wanda ya ke da mata daya sai
dai babu haihuwa. Mallan Kado ya hura wuta akan son Amina
amma ina! Isa ya kwace, don wauta ya ce, a ba shi diyansa Dije,
su kuma suka ba shi.
Bakin ciki goma da ashirin suka tararwa Malam Kado, a
dole yayi hakuri ya auro Ankudi, aiko ko wata uku ba a yi ba
Ankudi ta soma ganawa Dije azaba, da shi kan shi Mallan Kado.
A haka nan Dije ta sami shekara tara cikin azaba, shi kuma
Mallam yayi alkawari bai sake sakin aure domin sakin Amina ya
zame mashi darasi, don haka sai ya nemo auren Sabura, wai don dai Dije ta ji sanyi.
Da-farkon auren Sabura bata fara fid da maitata a fili bа,
domin Malan Kado tun farko ya ce zai aure ta ne don ta rungumi Dije saboda haka ta fara nunawa Dije gatanci domin har gyara
ta ake yi, haka nan idan ta ga Ankudi ta bata aikin da ya fi karfinta ita Saburar kan amsa ta yi.
To ganin haka yasa Ankudi ta canza dabara, inda ta rinka jan ra'ayin Dije a siyasance a hankali a hankali ta rinka cusa
mata mugayen akidodi, na guje ma Sabura wanda ta kai su ko dakintaa ka haramta mata shiga kai ta kai lokacin kiri-kiri aike
wannan Sabura ba ta isa ta aiki Dije ba' to sha'anin yaro kenan bai san makircin wasu tsaffin ba. Ita kuma ganin haka Sabura
ta tettara Dije ta watsar muguwan tsana ta shiga tsakaninsu, a
karshe Ankudi ta janye ta suka game gam, suna ta zuba 'ya'yansu
tare da mulki mai radadi ga su Dije. 'Ya'yan Ankudi Shehu da Kuluwa da Juma sai Sabura tana da Laraba da Munari.
A ko yaushe soyayyar Amina ta juyo ma Mallan Kado ya
kan shiryawa Dije ya ce ta je hutu, daga nan yana kulla wa Dije ce wa ta rinka zuga Amina ta dawo gidan su ko ta huta da
azaba, to a irin wannan hirar ne Malan Isa ya ji Dijen na lallashin
Amina ta koma gidansu amma sai ya ji ita Amina na cewa,
29
Cya yau kada ki kara zuwa min da maganar gidanku ance
maki ni yanzu ko mutuwa mijina ya yo inma da sha'awar
gidanku?"
Wannan shi ne dalilin da Malan Isa ya tsani ganin Dije a
gidan sa har wataran Amina ta tambaye shi wai ko Dije ta yi
masa laihi ne? Ya amsa da cewa, "Munafinkin ubanta ne kawai
ya hada mu, domin kwanan baya na ji zancen da kuke da ita,
idan tana son ki koma gidansu saboda ita, anan 'ya'ya nawa ki
ka haifa min ko su ba 'ya'ya ba ne? Kuma tun farkon aurenmu ai
na yi alkawarin rike Dije amma ya nuna zuciya ya karbe ta, to
shi ne yanzu don munafunci zai rinka aiko ta don ta kashe mana
aure?" Amina ta ce, "To ni dai ka yi hakuri ka daina tsuke mata
fuska tunda ka san yarinya ce wadda bata mallaki hankalin kan
ta ba". Ya ce, "shikenan zancen ya wuce, ai tun farko na ji kin
gyara maganar.
Ire-iren wannan tsegumi na ciwon son Amina ke jagula
gidan Malan Kado, sai su Ankudi su debi tsanar su dora kan
Dije.
KASHI NA UKU
A jami'ar Amadu Bello ta Zariya a can sashen maza a
dakin su Yusuf shi da Awalu wanda suke dakinsu daya. Yusuí
na daga kwance ya yi rigingine yayin da ya dage kafafunsa ya
kurawa wata kalanda da ke rataye jikin bangon ido, ya kira sunan
Awalu ya ce, "ka san kuwa duk a yi a kare karshenta a kawo
min Dije dakina ran laraba domin haka na ga ranan ta nuna a
jikin kalandar can". Awalu da ke zaune yana `yan rubuc
rubucensa ya ce, "yau sauran kwana nawa kenan?" Yusuí yа сe
"Arba'in babu daya". Awalu yayi dariya ya dubi Yusuf yaca,
"Yusuf angon Dije yau fa ake zuwa ziyarar yara ina faten da
la'asar za ka raka ni na gano tawa amaryan". Yusuf yayi
murmushi yace, "kai ni fa ban manta nan shiga makarantun yau
matan nan ba, sun faye innaranci `yan sakandiren nan". Awalu
yayi murmushi yace, "kai dai ka mallaki Dije kawai shi yasa
yanzu ko wacce mace tsananta ka ke, ka san wani abu Yusuf
30
wallahi na raina maka yadda na ga hoton Dije, saboda sanin
halayyar ka akan 'yan mata kowacce sai ka yi mata sharri, sannan
ga ka da shegan farin jinin 'yan mata amma ace farin jinin ka ya
kare akan wannan yarinyar mara fasali, kai Yusuf a gaskiya Dije ta kwareka!"
Yusuf ya yi galala yana kallon Awalu, yace, "Amma a
gaskiya Awalu ban taba ganin mutun mai cin fuska irin ka ba, w
annan yarinya ba ka san yadda mu ke da ita ba da har za ka fara kushe ta, haka nan ba ka san dalilin da yasa zan aure ta ba, а
gaskiya ka daina irin wannan cin fuskar bai da anfani". Awalu
ya ce, "Ashe babu dadi ka ke kallon budurwa ka