yi mɛ
ki ko ita Amina mahaifiyarku. Ni kuma ina nan a kodayaushe
zan kasance cikin yi maki kyakkyawar addu'a."
Lokaci lokaci Dije na sanya haban farin gyalenta na share
kwalla tare da cewa 'To Baba'.
Sun sami mota bus kimanin mutun shidda ake jira, suna
ciki suna zaune, Dije kusa da taga, Malan Kado kuwa yasa gwiwar
hannu ya dogare daidai tagar da Dije ta ke zaune, tare da yir
tagumi, kowa ya wuce zai dube shi ya dan tausayawa yanayir
fuskar Kado.
Ya kira ta a hankali ya ce` Dije', ta amsa "Na'am Baba",
Ya ce "idan kin ga Malan Isa na tsangwama maki ki hado kayar
ki ki dawo gida kin ji ko?" Ta се, To Вaba'.
Mai tallar biredi ya zo ya tsaya a gaban Malan Kado, yɛ
ce, "Malan ba za a sai biredin ba?" Malan Kado ya waiwaya ya
dubi Dije yace, "ya ki na son birdin a saya?" Ta girgiza kai tace
"A bar shi Baba". Tambaya ta dan zakudo tace "wane irin a bai
shi? A saya mana ko yara ai ma yi ma tsaraba". Malan ya saya
ya mika masu ta taga sai da ya ga tashin su sannan ya tafi gida.
Dije ta takure can gefe daya a dakin mahaifiyarta tanɛ
sauraron Gwoggo Tambaya tana bayyana dalilin zúwan su, taj
Tambaya ta ki fadin irin fallasar da Yusuf ya yi ma halittarta kc
me yasa? Nan da nan idonta ya kara cika da hawaye da ta tunc
muryar Yusuf na fallashe ta.
Amina ta waiwaya ta dubi Dije a sanyaye ta ce, "lalle
kina da aiki, don yace bai sonki shi ne abun kuka? In dai sha'anir
namiji ne ba ki ga komi ba, ai ni wannan mai kyau ya yi maki,
idan da sai an yi auren fa! Ya ce bai yi? Ni dai farin ciki na dayt
da za'a bar ta ta yi karatu amma duka duka shekararta nawa de
har da namiji zai dada ki da kasa? In don ni Allah ya raka tak
42
gona."
A ranar da Dije ta sauka gidan Malan Isa bai kwana ba
sai da ya je akan maganan makarantar Dije. A da can Dije na
makarantar 'yan mata ta Kabomo ne, da aka yi masu jarabawar
zuwa babbar sakandire ita ce ta zo ta daya don haka aka kai ta
makarantar 'yan mata ta Malumfashi, saboda haka shugaban
makarantar tayi ma Malan Isa alkawarin shigar da Dije aji hudu
kamar yadda ta ke, illa dai idan bata yi kokari ba za'a kara barin
ta aji hudu yayin da za su biyar. Da wannan bayanin Tambaya
ta koma Bakori cike da murna da kyakyawar addu'ar Allah ya
baiwa Dije miji wanda ya fi Yusuf.
Yawan aiki a gidan mahaifiyarta bai bata isasshen lokacin
tunanin da zai haddasa mata kuka ba domin Amina na da sana'a
mai karfi kamar dafadukan shinkafa da kunun zaki da fanke ana
kai mata karamar hukumar Malunfashi inda kanin mijinta Shittu
ke Sakatare a karamar hukumar.
Da yamma su zaune lissafin cinikin da aka yi. Dije ta
lura da irin kudin da innarta ke samu sai ta amince lalle mai
sana'a ba zai yi ciwon zuciya ba.
Kwanan ta biyu aka shirya ta zuwa makaranta.
A can kuma Bakori bayan tafiyar Dije da kwana daya
ciwon Malan Kado ya tsananta dole Malan lliyasu ya nema
mota ya kai shi babban asibitin Funtua, babu bata lokaci su ka
kwantar da shi. Ya rinka rokon Malan Iliya don Allah kada ka
aika ma Dije a kyale ta tunda an ce ta samu makaranta. Can
Malam Kado ya dan juyo da fuskarshi daidai saitin Malan lliya
ya rage kaimin harshe ya ce, "lliya wai yaya aiken da Malan
Tukur ya yi wajen Yusufa, ka ji wani zance mai karfi?" Malan
İliya ya dan sunkuyd da kai "Haba Malan Kado kai fa babba ne,
don me ba za ka iya sawa zuciyarka dangana ba ne? Ko ka san
wannan matsalar ta tayas maka da-hawan jininka, in kuma ba
ka fid da damuwa ba a ranka, to likitoci sun tabbatas mana za
ka sami shanyewar barin jik. Ka kwantar da hankali, insha Allah
Dije zata sami miji wanda ya fi Yusufu."
Malan Kado ya fid da wasu kwalla daga idanunsa ya ce,
"Ni wallahi ko shugaban kasa zai ce yana son Dije bai kai
43
Yusufa ba a zuciyata, kamar Tasi'u ne fa na ke ganinsa".
Aiken da Malan Tukur da Gwoggo Halima su ka yi ma
Yusuf a can makarantarsu shi ne, yana cin abinci a daki, Awal
ya turo kofa ya shigo yace, "Yusuf ka yi bako". Ya ce “wanene?"
Kafin ya rufe baki Basiru ya shigo nan da nan ya hade fuska
suka gaisa sama-sama, ya kawo wasika ya ba shi ana tabbatas
ma shi aure da Dije babu fashi za'a ci gaba da biki a kawo ta
dakinshi in yaso ya bi uwa duniya. Malan Tukur ya snriya wannan
dabaran, amma gogan na ku ga amsar da ya rubuta a takaice:
Na ji aikenku, to tunda kun zabi Dije fiye da ni, shi
kenan ni na yi sallama da ku.
lafiya.
Ina fatan za ku yi min aikin gafara ku zauna da Dije
Danku Yusuf Kanti.
KASHI NA BIYAR
Da aka yi hutu sai Yusuf ya yi zamansa a Zariya gidansu
Awal, kullun yana gidansu Fa'iza zaune wajen masu gadi yana
taya su hira domin sai da yayi zuwa hudu sannan ya sami ganin
Faiza, a wannan rana sai ya ji kamar an yi masa gafara.
Suna zaune a wani yammaci bisa dakalin gidansu Awal
sai kawai ya kafta ido ya ga Malan Tukur da Basiru, kunya da
mamaki suka dabaibaye shi ya rasa kalmar da zai yi ma Malan
Tukur anfani. A karshe Malan Tukur ya ce wai sun zo biko. Sun
amince ba'a auren.dole.
Yusuf ya yi godiya ya tabbatas masu yana nan tafe nan
da kwana biyu.
Bayan sun tafi Yusuf ya dubi Awal ya ruke habar baki
yace, "Wato da man barazana su kai min, da na firgita da yanzu
ina can da amarya sokoko a daki?"
Awal rike da casbi a hannunsa yana lazimin ya yi
44
murmushi yace,`ka dai bi a hankali'. Yusuf ya yi shiru tunanin
bikin cika shekararFa`iza ya gallabe shi wai wace hobasan zai
nuna mata? A ina ma zai samu kudin, duk dai karyar shi bata
wuce rufin asirin dubu daya, sai ya kara tuno da wata galleliyar
matar da ya ga ta zo wajen Fa'iza, ya tambaya ko shi ne Isma'il
din? Ance ba shi ba ne, to har yaushe irin wa` annan na zuwa
wajen Fa'iza zai dube ta da kyautar kasa da dubu daya? Ya sami
dabara saboda haka dole jibi ya je Bakori.
Da la'asar ya isa Bakori ya shiga cikin borin kunya ya
gayas da mahaifiyarsa ya lura duk ta dan rame, ya tabbata ba
komi ne ya jawo hakan ba illa kin aurensa da Dije. Ya fice zuwa
dakinsa don ya yi abinda ya kawo shi, ya jawo wani fayal dinsa
inda ya ke aje mahimman takardunsa, ya rinka dubawa daya
bayan daya har ya kai bisa ta kan wata gonarsu ta gado, an
mallaka masa takardun gonakin su ne da na gidan da suke zaune
da wa su feguna guda biyu, shi da kannansa, tun lokacin da
kanin babansu ya fara sayarwa yana danne kudin. To yau ma
ga Yusuf Fa'iza ta rikita shi zai shiga dukiyar maraya.
Bayan ya fito masallaci sallar isha'i bai zarto gida ba sai
ya nufi gidan Alhaji Murtala wanda jama'a su ka yi ma lakabi da
Ba ruwanka da bashi sai neman arha'. Ya kashe kimanin minti
arba'in kafin ya sami ganin Alhajin domin an ce Alhajin na can cikin gida yana yin sulhu akan wani auren diyarsa da ke neman
lalacewa.
Yana ganin Yusuf ya ce, "A'a Yusufa yai kau ne da kan
ka a gidan nawa! Yusufa dan makaranta ya mutan gidan?";
"Lafiya lau Alhaji.
Sai Yusuf yasa hannu aljihu ya fiddo masa takardun
gona ya mikawa Alhaji ya ce yana son sayarwa ne. Alhaji ya
duba, ya duba ya ce, 'Allah ya jikan Malan Kanti', Yusuf ya cе, 'Amin'.
Alhaji ya kammala nazarinsa ya ce "menene dalilin sayar
da wannan gona ta ku?” Yusuf ya gyara zama ya karkace kai ya
ce, "matsala ce ta can wajen fannin karatuna". Alhaji ya ce, "ya
yi daidai, haka nan na dade da sanin gonan, amma duk da haka
ba za mu yanke ciniki na yızu yanzu, sai gobe ka zo mu je
45
gonai na kara dubawa. Allah ba shi daga can ma ina iya yir cinikin na biya ka, ka amince?' Ya ce ya aminçe.
Da ya koma gida ya yi murna da ya cimma Malan Tukur
a nan gidansu ya ke, ba batun zuwa hira wajen Gwoggo kenar
balle har ta sami halin nuna mai bacin ranta.
Ya kulle dakinsa yana tunanin abubuwan da zai yi ma
Fa'iza idan ya amshi kudinsa a gobe.
Yana kammalawa da kalaci sai gidan Alhaji Murtala. Bа
yi dogon jira ba Alhajin ya fito domin yana murna da irin cinikir
yara kanana kamar su Yusuf.
Suka shiga motar Alhaji su hudu, da Yusuf da Alhaji da
yaran Alhaji. Suna isa gonar sai da aka zagaye ta tas, sannar
suka ja birki a gindin wata cediya, Alhaji ya ce "Yusuf na ge
gona kuma ta yi mani, ko ma bata yi min ba, ni dole ne na saya
domin taimakonka tamkar na taimakawa Bakori ne gaba daya.
A nawa za ka sayar mani?" Yusuf ya ji dadin kalaman Alhaj
yace, "Ai ni Alhaji duk yadda ka saya babu ja a tsakaninmu."
Alhaji ya yi dan nazari yace, "Tunda haka ne, zan bake
dubu ashirin da biyar?" Gaban Yusuf ya fadi domin shi yasar
gonarsu za ta yi dubu hamsin da wani abu. Ya ce "Alhaji ka sar
tafi haka". Alnaji ya ce "kai ni fa ban iya ciniki kwan gaba kwar
baya ba, to na saya ashirin da takwas". Yusuf ya yi shiru car
daya daga cikin yaran Alhaji ya ce, "kai muna da abun yi, yaya
za ka debo mu ka kawo mu daji kana wahalasshe mu?" Alhaj
ya ce, "Tsaya, tsaya Barau. Idan ya amince dubu talatin ku be
shi kudinsa idan bai amince ba ya nemi wani mai saye."
Yusuf ya amshi kudi rai bace ya isa dakinsa a shirinse
ya so ya sami ko dubu hamsin, ya fara kashe ma Fa'iza da sh
kan shi dubu talatin, zuwa can gaba ya kara yi mata hidimai
sauran dubu ashirin din.
46
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels