nan da shekara uku ne kila da sauki sauki amma
ni yanzu ina tunanin tafiyar makarantar Salmanu wato polytechnic Katsina ina naga wani abun aure?" Halima tace, "Duk
Allah zai rufa asiri domin Malan Kado ya yafe maka komi" Yusufà
yace "To Gwoggo ba kya tunanin zaman ita yarinyar a gidan
nan shi ma wani nauyi ne?" tace, "Kai dai ka cika kakale ba ka
ji abinda aka ce ba ne? Aure fa babbar rahama ce ga baligin da
ya isa". Ya yi shiru ya ce, "To Gwoggo ku ba ni lokaci idan na
koma makaranta zan yi tunani komi kenan idan na dawo za su
ji."
Cikin sati uku cif Yusui dan makaranta ya sake dawowa
garinsu. Yau Jumma`a da la` asar sakaliya Yusuf na sanye cikin
T-shirt baka an yi rubutu da manyan haruffa da kuma jan launi
inda aka rubuta `I'M PROUD TO BE A MOSLEM', wandon
jikinsa fari ne sol yana kwance bisa irin kujerar nan wato (kwanta
ka huta) gadonta ya yi wajen mahaifinsa Malam Kanti, ya yi
zurfi wajen karatun wani novel na ches. Inuwar kukar kofar
gidansu ta kara saukar da ni`imar sakaliyar la`asar. Can daga
sama ya ji an ce, "Yusufa za ka sai goro?" Ya karkato fuskarsa
zuwa inda ake magana ya aje littafin da ke hannunsa bisa kirjinsa
ya dubi yarinyar sosai tana sanye cikin irin abayar nan ta `yan
İslamiya a bisa kanta akwai farantin goro, da goro farare tas.
Ya yi murmushi sannan ya dan yunkuro kadan ya zauna a
karkace ya ce, "Wai shin ke don Allah me yasa ki ka bar
makarantarki sai tallace tallacen tsiya?" Ta sauke turen ta durkusa
ta yi murmushi ta ce, "To ina yini?" Ya amsa "Lafiya lau". Tа
ce "Wallahi ba laifi na ba ne, ina son karatu fiye da komi a
rayuwata amma Babana ya ce karatun ya isa haka to ya zan yi
tunda ni abun ikonsa ce?" Ya ce, "E, haka ne kin yi gaskiya, to
10
amma yaya Baba Kado zai amince ki rinka talla?" Та се, "Кa san
Allah bai sani ba, su Gwoggo Sabura ne da Gwoggo Ankudi. Ya
san dai suna sayar da goro kuma ana zuwa saye, amma da zarar
sun lura ya tafi cin kasuwar wani kauye dole mu je talla ni da
kanne na, wato `ya`yansu". Yusuf ya girgiza kai ya ce, "Allah
ya jikan Tasi` u idan da yana da rai wane su da dora maku tallah?"
Suka yi shiru kanta na sunkuye tana kallon fararen goro
yayin da Yusuf ya sami damar kallace sirrin fuskarta, E to, Dije
na da kyau amma ba irin kyan da Yusuf ke kwadayin samu ba,
illa dai kawai ya san Dije na iya shiga cikin fararen mata itama ayi da ita hakan idan fannin wankan tarwada ne, Dije na iya
sajewa cikinsu. To ya amshi wannan kyautar Malam Kado ba
wai don yana da kwadayi ba sai dai mu ce kila wahalar Dije ta
zo karshe amma da ma maza `yan wa` anda suka cudu da
rayuwar jami` a zai fi kyau a kyale su da irin ra`ayin `yanmatan
da su ke da sha`awa domin mafi akasari ba su cika yin jami`a
ba sannan su nemo`yanmatan jami`a suna da irin wa`anda
suke da ra`ayi na kashin zuciyarsu.
Ya ce, "Dije wannan goron ya yi na nawa? Ta ce, "Na
naira ashirin ne amma na yi cinikin naira biyu a hanya". Ya
fiddo naira ashirin ya mika mata ya ce, "Sai ki koma masu da
goron su". Ta dafe kirji ta çe, "Ashe ko yau da na ba ni ace wa
ya ba ni?" Ya yi dariya ya ce, "Ki ce saurayinki!" Sai ta yi wal
da idanu ta dube shi duba na rikita da tsananin kauna a cikin
idon Dije, nan da nan'wannan kallon ya huda so a zuciyar Yusuf.
Yace, "kina nufin ki ce min duk garin nan ba ki da saurayi?"
Ta kara rusunar da kanta a kasa yace, "En Dije?" ta amsa "To ka
tambaya mana" yace "Ni ba zan tambayi kowa ba sai ke. Don
Allah gaya min samarinki" ta yi`yar sheshekar dariya tace, "To
tsokana ta kake son yi". Ya ce, "To idan kin je gida ki ce masu Gwoggo mijinki ya hana ki tallah! ta kara yi mai wal da idanu
tace, "Ka san halin su Gwoggo kuwa?" Ya kyalkyale da dariya
yace, "Ai miji ya fi su gwoggo idan kin je islamiyya ki tambayi
malaminku, ba ni goro guda biyu sauran ki kai ma inna Tambai
kice ina gaishe ta gobe mu hadu gidan inna Tambai kamar yanzu
akwai abunda na ke son gaya ma ki, ta zabi goro biyu ta mika
11
masa suka hada ido aya yin da hannunta ke ba shi goron su ka
yi ma juna dariya mai faranta rai, ya fada a hankali goron auren
Yusuf da Hadiza, Allah shi yarda; ta sa hannu ta rufe fuska
yace, Dije sarkin kunya, ke banda shirmenki wa ke jin kunyar miji? tace, wallahi miji ko shi ne abin jin kunya; yace, Dije kin iya
magana ko? na ga ni da ke wa ya fi baki? tace `To ko dai jakar
magori za'a kai mu sai jama'a su tantance mana? yace, "Lalle
za'a yi da ke Dije!"
Ta isa wajen Inna Tambai a lokacin Tambaya na gindin
rijiya tana tatar koko. Dije ta dauki wata `yar karamar, kujera
`yar tsugunne ta isa inda Tambaya ta ke ta zauna suka gaisa ta
ce, "Gwaggo kawo na karasa maki tatar". Ta ce, "A`a rinka
zubo min ruwa ai na kawo karshe."
Suna cikin tatar ne Dije ke cewa, "Gwoggo ba ki san wani
abu ba wannan Yusufan dan dan aminiyarki ya aiko ni na kawo
maki dukkan goron da ke bisa farantin can". Tambaya ta yi
dariya ta ce, "A gaida dan arziki haihuwar albarka". Dije ta kara
rankwafar da kai ta ce, "Ya kuma ce wai na zo nan gidan gobe
za mu hadu da shi akwai abinda zai gaya min".
Gwoggo Tambaya ta ce, "Mun dai godewa wannan yaro
dan albarka Allah ya ida nufinmu akan ku, Allah ya nuna min na
ga ranar da zan kama hannunki zuwa gidan angonki Yusufa
Maitama".
A hankali Gwoggo Tambaya ta warware ma Dije yadda
Malam Kado ya aike ta gidansu Yusuf akan ya ba su ita. Dije ta
yi tsit tana saurare a zuciyarta duk murna da dadi sun baibayeta
wai yaya a kai ra`ayinsu ya zo daya da na mahaifinta? Domin a
duniya ba ta da mutumin da ke burgeta a rayuwarta irin Yusuf,
don haka ne ma take murna da taliar da su Gwoggo Ankudi kan
dora mata don kawai ta je layin su Yusuf ta yi masa talla, a duk
lokacin da ya ke a gida. Duk wata addu arta mafi akasari akan
Allah ya bata Yusufa ne ko kuma miji kamarsa, to a yau gashi
Allah ya bata.
Kamar yadda ya umurceta Dije ta sami mahaifinta a daki
bayan sallar azuhur ta ce, "Baba Yusufa ya aiko na je gidan
Gwoggo Tambai anjima da la`asar". Ya dan gyara zama.cikin
12
jin dadi ya ce, "To ai sai ki shirya ki je. Kya ce ina gaida Gwoggon
ta ki".
Dije ta sheka wanka ta fiddo atamfarta wakas mai tambari
wadda Babanta ya yi mata da sallah ta daura, tun safe ta wanke
abayarta fes ta dora a bar ta, ta ce ma su Gwoggo za ta gidan
Gwoggo Tambaya, suka kalle ta shekeke, suka ce, "Wani ya се
kada ki je? Kya dai karaci gulmarki".
Bayan ta fita Sabura ta ce, "Ko wanne makircin ake kuilawa
gidan Tamban?" Ankudi ta ce, "Bai dai wuce zancen neman
miji! Kin san abunda ya damu uban kenan". Sabura ta ja tsaki
ta ce, "Mahaukatan banza in dai don wannan `yar ta shi mara
fasali sai dai ya gaji ya bada ita sadaka, kin gane min yarinya
somaye kamar wadda ta shekara tana jinya? Duk namijin arziki
ai bai auren wannan in dai da kudinsa, banki ba idan sadaka
za`a ba shi".
a
Ankudi ta ce, "Wo ni ko sadakar ina amsarwa dan uwana
wannan? Ai kowa na son ya auri iri mai kyau, can dai na su
gada, sun gama kumbiya-kumbiyarsu shi da makirar kanwarsa
muna nan labari zai zo mana, wai don sanabe har da daura` yar
atanfar ta ganin Sarki". Dije na bullowa ta lungun hagu na gidan Gwoggo Tambaya
shi ma Yusuf na bullowa ta titin da ke kallon yamma na gidan
Tambaya.
Yana sanye da wani yadi fari kar da ganinsa maí arha ne
ya yi janfa da wando amma an zizira wani adon sirfani a wuya
da hannu, kube ya saka mai dinkin zare baki da ruwan kasa
takalmansa silifas ne`yan Italy.
Suka tsaya bakin zauren gidan Inna Tambai, ko wanne cike da annashu dauke da murmushin kauna, babu wanda ya
iya cewa komai sai Dije ta cije ta ce, "Lah Yusuf mun iso tare
ko?" Ya ce, "Kin ga na fi ki zafin nama ya dace a ce kin riga ni
isowa fiye da awa daya, ko dan ki kara gyara `yan like-liken na
gazar da jan baki idan kin je an ce, "Dije ga Yusuf nan ya zo".
Suka kyalkyale da dariya ta ce, "To mu karasa mana cikin gidan,
amman ni dai ina tabbatas maka na fika hanzari anan". Ya kira
sunanta cikin jan hankali irin na maza ya ce, "Dije". Ta amsa
13
cikin dariya da nuna jin dadin yadda ya kira sunan ya ce, "Ina so
ki rike abu daya a yau kada ki yadda ki manta da abinda zan
fada maki a yanzu, wato na fi ki hanzari amma zan tabbatas ma
ki da haka ran da duk muka yi aure abinda duk zamu fara haihuwa
Insha-Allah zai kasance namiji".
Ya shige gaba zuwa cikin gidan su Inna yana dariya yayin
da ya bar Dije lullube da gundumemiyar kunya, domin ya bantaro
mata wata irin magana da ba` a taba yi mata irin ta ba.
Inna ta rinka taya shi dariyar duk da bata san abinda suke
ma dariya ba. A nan gidansu Inna Tambaya yayi sallar mangariba,
a nan yayi issha`i, aka sako masa tuwo. Dije ta kawo masa ya
ce ta zo su ci tare idan ba haka ba bai ci, a dole Dije ta zauna
suka ci a kunyace.
Malan, mijin Inna Tambaya ya leko ya ce yana son magana
da Yusuf. Yusuf ya mike ya nufi zaure wajen Malan ya ce Dije ta
jira shi zai raka ta gida.
Maian ya ce, "Yusuf kada ka zargi kowa a bisa dalilin
wannan kira da na yi maka. Wallahi! Wallahi!! babu wanda ya
sani, ni ne kawai tunani na ya ba ni naga ya dace na shawarceka,
kuma shawara zan ba ka idan ka ga bata yi maka ba, ka bar ta
anan inda mu ka yi ta bana son kowa ya ji. Akan zancen Malan
Tukur ne da ku ke ta korarsa kai da mahaifiyarka? Nan da nan
sai Yusufa ya murtuke fuska ya bata rai sosai ya ce, "Mu ke
korarsa kamar yaya? Malan ni fa ba yaro ba ne na san ciwon kai
na don me zai nemi ya matsa mani ne?"Malan ya ce, "Ni ma
don na san kai ba yaron ba ne shi yasa na ke son mu yi zancen
manya da kai, ko ka ga na nemi su Basiru? Abinda na ke son ka
fahinta anan shi ne, matsayin mahaifiyarka itama fa mutum ce,
haka nan akwai nauyi akan ta na aure tunda bata wuce shi ba.
Abinda za kai la`akari anan.shi ne zamanin da mu iyayenku mu
kai aure ba daya ba ne da na ku, wanda sai yarinya ta sami
shekara ashirin gaban iyayenta na karatun boko ba`a kai ta
dakin aurenta ba, mu kuwa an kawo mana iyayenku suna yan
shekara goma sha biyu. Lokacin da ta shekara bivu da aure, sai
haihuwa to idan ka lissafa ba su shige shekara goma sha hudu
zuwa sha biyar ba za su haifi dan su na fari. To ka lissafa mani,
14
shekara nawa ke tsakaninku ku diyansu na fari? Na san dai
yanzu baka wuce shekara ashirin da biyar ba idan ka hada da
sha biyar ka ga mahaifiyarka bata wuce shekara arba`in ba. To
yanzu kai ina mutuncinka ace tana zaune babu aure? Domin
akwai sauran kuruciyarta dole ne kuma maza su yi sha` awarta
in ta fito waje."
"Babban farincikin mahaifinka ace yau ta auri wanda ba
mutumin banza ba sannan ya rungume masa zuri` arsa wannan
shi ne fatan duk wani namijin kwarai. Tabbas akwai ciwo idan
aka ce wani dan duniya ko yaro karami ta rakito ma ku, amma
kamar Malan Tukur me za ku ba shi sai dai ya yi ma ku domin
arzikin auren mahaifiyarku. Ina son. ka yi tsam da ranka anan
tun kafin ka zo duniya ake mutuwa ake kuma auren matan
wa anda suka 'rasu, kai bari ma na tuna maka idan ka manta
ingantaccen hadisi ya zo mana Annabin Rahama (S.A.W) kusan
duk matansa zawarawa ne in banda Nana A`isha ita kadai ya
aura budurwa. Yawancin zawarawan nan kuwa wa` anda
mazajensu suka rasu ne, to kai don me za ka harantawa
mahaifiyarka abinda ya halatta gare ta? Haba Yusufa uwarku fa
natsatså ce don haka ne ma Ubangiji ya kawo mata natsattsen
miji kamar Malan Tukur".
Anan idanun Yusuf su ka dan canza launi sannan gashinsa
ya rinka fitas da zufa ya fid do hankicinsa ya goge zufar ya yi ajiyar zuciya ya dan dago kai ya dubi Malan na Tambaya a sanyaye
cikin natsuwa da jin nauyinsa fiye da da. Ya yi godiya ya mike
ya ce, "To Malan na fa gode zan koma sai mun sake zagayowa",
ya koma cikingida.
"Salamu Alaikum Inna Tambai, kar dai na ce wannan
malalaciyar bacci ta ke yi?" Inna Tambai ta yi dariya ta ce, "Ba
ka dai gajiya da zolayar diya ta daga ka ganta a kwance bisa
tabarma? Hira dai mu ke yi". Ya ce, "To in banda lalaci hira a
kwance Inna? Ni taso mu je na rage maki hanya tunda dare".
Dije ta mike tå gyara daurin kallabinta zuwa daurin zaninta
sannan ta dauko abayarta da ke jikin kofa ta dora, duk Yusuf ya
yi mata kyar da ido, har yasa Inna Tambai ta ji nauyin kallon ta
kawad da fuskarta gefe daya.
15
Dije ta dubi Yusufa ido cikin ido ta ce, "To na shirya mu je ko?" Shi ma ya nutsar da na shi idon ya dube ta, nan da nan sai suka kyalkyale da dariya. Tambaya ta ce, "Kai wa`annan yara dariya ba ta yi maku wuya".
Dije ta dubi Tambaya ta ce, "Gwoggo sai da safe". Ta fara
fita sannan Yusufa ya bì bayan ta, suka jera suna tafiya cikin
nishadi, su ka isa bakin wani shago ya ce, "Tsaya nan na sawo
maki cingam ko kya wartsake gyangyadinki" ta yi murmushi.
Ya fito rike da bakar leda ya sawo mata cingam da biskit
da alawar akelas, sai ya zaro cingam biyu ya bare masu ya jefa
daya a bakinsa ya mika mata daya. Ta ce, "Nagode". Ya ce,
"A`a bari saurin godiya ni ma wata ran za ki sai mani sannan ki
bare mani ki kuma fara tauna mani kafin ki ba ni" Ta kyalkyace
da dariya ta ce, "Ni kam ban taba jin inda aka taunawa wani
cingam ba, to ai zakin ya kare, gam din na baka kenan" Ya ce,
"Yauwa shikenan kin ga mun zama gam-gam"
Yusufa ya cе, “To gobe fa na ke son komawa Zariya
makaranta idan zan dawo me zan kawo maki?" Ta yi murmushi
ta ce, "Kai da za ka makaranta? ina dai son ka kawo min irin
litattafanka na sakandire" Ya fiddo ido ya ce, "Kina da sha awar
karatu ne nan gaba Dije?" Ta ce, "Kwarai kuwa, ai kai ba za ka
bar ni na wuce ba nan gaba?" Ya ce, "Wallahi ban yi wannan
tunanin ba, amma me zai hana na bar ki ki ci gaba da karatunki.
ko yanzu ni da Baba Kado zai amince min Dije ai makarantar zan
maida ki domin lokacin da za ki gama babbar sakandare ni ma
lokacin zan dawo hidimar kasa kin ga ai dai dai aurenmu kenan".
Dije ta nisa ta ce, "Anya Baba zai amince kenan? Amma
ka yi tunani kafin ka san dabarar da za ka yi masa ni ma kam da
an taimaka min".
"To Dije bari na bar ki anan domin ga Baba Kado can ina
hangensa zaune shi da Malan lliya sai in ce sai na dawo bayan
sati biyu ko?" Ta ce, "Aí ba za ku je ku gaisa da su Baban ba?"
Ya ce, "A`a da dai ba tare mu ke ba, kya dai ce ina gaishe shi
sai na zo zan zo mu gaisa, mu kwana lafiya".
Sai da ya ga shigarta cikin gida sannan ya yi murmushi
ya juya, ya yi nisa da tafiya sai dai ba gida ya nufa ba, ya je ya
16
nemi wani lungu inda babu yawan jama` a ya yi zaune a gindin
wani durimi ya shiga lissafin duniya inda duk ya auna maganar
mijin Inna Tambai sai ya ga gaskiya ya sanar da shi, amma da ya
tuno fuskar Malan Tukur zai shigo gidansu sai kishi ya turnike
shi, amma idan ya tuna mahaifiyarsa ya tuna irin kuruciyarta da
yadda take zullumin kin kada ta bata masa rai sai ya rinka jin tausayinta lalle ya zalunce ta har na lokaci mai tsawo domin ta
ba da abinda ta ke so saboda shi, a karo na biyu kuma ya dawo
da tunanin Malan Tukur shi ma anan sai kunyar sa da tausayinsa
ya kama shi domin sau tari da yawa Malan Tukur na stian gamuwa
da shi ya nuna son girmama Yusuf amma sai shi Yusuf ya rinka isgilanci a gare shi.
Jikinsa ya yì sanyi ina shawara? Ya mike a sanyaye ya
tafi, bai zame ko ina ba sai anguwar su Malan Tukur. Ya hango Malan na zaune bisa wata makekiyar darduma, manyan malamai
sun kewaye shi yana yi masu karin karatu. Ya dauki lokaci yana tsaye yana kallonsu har su ka kai aya a kai addu`a kowa ya shafa, shi ma Yusuf ja ke can nesa ya shafa.
Ya yi tattaki inda su Malam su ke ya yi sallama gaba daya
aka amsa masa. Malan Tukur ya dago ya dubi Yusuf sosai, mamaki da al`ajabi suka cika sa nan da nan ya mike ya mikawa Yusuf 'hannu, a haka hannuwansu na rungume suka zaune kowanne cike da anņuri a fuskarsa.
Sai bayan da Malan ya yi sallama da almajiransa sannan Yusufa ya kara matsawa wajen Malan ya rusunar da kan shi sosai tamkar dai yaron da ya je gaban mahaifinsa neman gafara.
Yusuf ya ce, "Allah gafarta Malan na zo neman gafara a bisa
wani shishigi da na so na yi maku, amma idan an yi la`akari da shekaruna za`a ga ban kai munzulun da zan lakanci komi na al`amuran duniya ba, ku yi hakuri Malan ku zartas da sunnan Manzon Allah Annabi Muhammadu (S.A.W) kamar yadda ka bukaci yi akan mahaifiyata. Ubangiji Allah ya ba ku ikon fahintar juna da cimma rayuwa mai albarka".
Malan dai ya yi kasake yana sauraron Yusufa, tunda ya fara magana bai tari lunfashinsa ba, har sai da ya dire, amma a
zuciyar Malan ta yi kal saboda zai cimma ribar hakurinsa akan
17
kaunarsa da Halimatul Sa` adiya. Ya ce, "Haba Yusuf na gafarta
maka, ai babu komi. Haka ake son samun namijin duniya, ina
anfani a kyale gida sakakah wannan wofi yazo gobe ma yaron
da bai isa ba ace ya zo neman auren mahaifiyarka ai ka ga
martabarku da kimarku ta zube a idon mutane".
Yusuf ya gyara zama ya ce, "Malan idan zai yiwu ina son
ka zo mu je yanzu wajen mahaifiya ta a gabanka na nemi gafarka
domin ni gobe zan koma". Malan ya dan sosa kai yana dariyar
jin dadi ya ce, "Anya ko haka ta yiwu Maitama?" Yusuf yana
murmushi ya ce, "Allah gyara aikin Malan me zai hana? Ai gara
mu je domin duk abinda ke gudana bata da ma saniya"
Malan ya mike ya kira daya daga cikin yaransa ya ce, "Kai
zo nan ka zauna ko an zo nemana ka ce na fita, ina zuwa yanzu
in Allah ya yarda".
Suna tafe suna hira Malan na buga wata lafiyayyar
sandarsa. Alhaji Uba ne ma ya sawo masa sandar har da lema
daga kasar Alkahira.
Suna isa kofar gidan Malan ya ja tunga a zaure sai Yusuf
ya dube shi ya ce, "In ka so shigo abin ka daga yau gida ya
komo mulkinsa a hannunka". Malan ya ce, "Au to haka ne?"
Yusufa ya ce, "Kada ka ji komi Allah gafarta Malan"
Gwoggo Halima na zaune bisa tabarma tana gyara wani
daushen goro, sannan ta karo karar rediyo lokacin da ta ji an
fara labarun dare na karfe goma, ta fara tunanin yau ina kuma
Maitama ya je doguwar hira. Ta saba a irin wannan lokacin idan
har yana gari ya na nan dakinta suna hira. Bata kai karshen
tunanin Yusuf ba, ta ji sallamarsa amma a yadda ta ji hayaniyar
gaishe-gaishe a tsakar gida ta san ba Yusuf ba ne shi kadai.
Ya dage labule ya shiga ya na kwashe kayan da ke bisa
kan wata kujera ya ce, "Gwoggo tare fa mu ke da Allah
Sabbinani", kafin ma ta kai neman karin bayani Malan Tukur
abin son ta ya bayyanar da kan shi a dakin.
Duk dai bayanin da ya dace Yusuf ya yi a gaban Malan da
mahaifiyarsa ya yi amma Malan din ne ke kokarin amsa masa,
Gwoggo Halima ta rasa abin cewa, har Yusuf ya fice ya bar ta
da Malan. 18
Da misalin karfe sha daya na safe Yusuf ya kammala shiryeshiryensa zai tafi Zariya ya shiga dakin mahaifiyarsa don su yi
sallama, bayan sun gama zantuttukansu wanda ya shafi gida ya
mike zai tafi sai Halima ta dan kawad da fuska ta ce, "Au maganar
Malan fa na manta na sanar da kai wai yau da azuhur za su je
can Danja wajensu Baba Karami a dauro aure". Yusuf ya yi
murmushi ya ce, "To madalla, Allah yasa alhairi amma fa nan
gidan za ki ci gaba da zama sai dai shi ya rinka zuwa". Tа се,
"To daman ka ji wani ya yi zancen zan tashi ne?"
Ya sasa kai kai ya tafi abinsa a rannan aka dauro auren Malan
Tukur da Halima, a wannan rana ya fara kai ziyara gidan
amaryarsa.
To sai me kuma zai faru? Wata daya, wata biyu zuwa
wata na uku bayan aurensu Malan da gwoggo Halima, a
kodayaushe Yusuf na zuwa gida amma sai ya rinka samun sabon
canji a gidan na su, misali kamar ita kan ta gwoggo Halima da
kannensa a kullum suna cikin daukar karatu a wajen Malan to
shi ma Yusuf sai ya kashe duk wani karatun novel ya rinka zama
da yamma anan kofar gidansu wajen Malan ya rinka kwasar
karatu. Haka nan kuma ya yi farin ciki da yadda yanzu kofar
gidansu ta kan cika da jama` a albarkacin Malan Tukur wanda ko zamanin mahaifinsu ba` a cika haka. Sai wani karin budi shi
ne abinci a gidansu, yanzu kámar gidan wani hakimi, bai zullumin
ko ya kawo ma Gwoggonsa kudi ko bai kawo ba domin Malan Tukur ya dauki nauyin komi.
Akwai wani zuwa da ya yi ya samu Gwoggo Halima na ta
yin kunshi ta sanar da shi za ta biki Faskari wanshekare amma
abin mamaki a wanshekaren har la`asar bai ga Gwoggo ta yi
tafiyar ba sai ya ce, "Wai Gwoggo ba na ji kun ce za ku Faskari
ba ne?" Sai ta dan yamutse fuska ta ce, "Malan ya hana wai sai
dai shi va jë mun bikin, ko ina ya taba ganin namiji a bikin
mata?" Yusuf ya noke ya rinka dariyar mugunta ya ce, "Kash!
Gaskıya babu dadi, ga shi kuma har kun yi kunshi". Ta galla
masa harara ta ce, "To shi ne me? Ko da ma can ai ina da niyyar
kunshi na, da za ka ce babu dadi, ni abokiyar wasanka ce? Kai
ne har za ka tausaya min don an hana min zuwa anguwa?" Ya
19
dai fice zuwa dakinsa na zaure yana yi ma Gwoggo dariya.
Wannan ma yana kayaten da zuciyar Yusuf wato kullen da Malan
ke yi ma Gwoggo domin a da kusan kullun Gwoggo sai ta fita
anguwa, yanzu kuwa shi bai iya tuna ranar da ya zo bai cimma
Gwoggonsa a gida ba.
To shi ma a can Malan Kado ya gamsu ya amince a cikin
`yan watannin nan uku Yusuf ya amince da Dije idan ya lura da
irin dawainiyar da ya ke yi mata, ba su dai shige`yan kayan
ciye-ciye ba kamar na naira hamsin, zuwa dari sai ko tsaffin
litattafansa.
Malan Kado sanin cewa Malan Iliyasu dan uwa ne ga
Malan Tukur sai ya nemi lliya ya yi ma Malan Tukur magana azo
a ja bikin Dije da Yusuf.
Da farko da Malan din ya nemi Yusuf akan maganar sai
Yusuf ya ce, no za`a yi hakuri a mayas da Dije makaranta, in
ya so idan ta gama shi ma ya gama ayi bikin?" Malan ya sha
mur ya ce, "A kul na sake jin.wannan maganar, ka san dalilin da
ya sa ya hana diyarsa karatun? Ka dai kyale shi ya yi iko da
diyarsa yadda ya ke so."
Aka ja ranar bi' wata biyu domin a lokacin Yusuf ya ke
ganin za su sami hutu mai tsawo.
Bayan kwana goma da sa ranar auren Yusuf da Dije sai
ga Yusuf ya dawo cikin matsanancin ciwo wanda ba komi ke
damunsa ba illa maleriya da ta yi mai kamari, daga zazzabi mai
zafi sai ciwon kai mai radadi sannan yawan haraswa akai-akai.
Da ya kwana daya a kwance a gida abokinsa Garba nas ke
zuwa duba shi da yi mai allurai akai-akai, sai ya daure ya rubutawa
Dije wasika domin ya san bata san halin da ya ke ciki ba.
Tana tsakar wanke-wanke, Sarai kanwar Yusuf ta yi sallama
ta